سورة المائدة
Suratul Ma’ida da fassarar Hausa
Teburin abinci
- 5
- ayoyi 120
- Madaniya
- Juz’i 6–7
- Shafuka 106–127
Suratul Ma’ida (المائدة) ita ce sura ta 5 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 120. Ma’anar sunanta ita ce “Teburin abinci”. Sura ce Madaniya, wadda ta sauka a Madina bayan Hijira, kuma tana cikin juz’i na 6 da 7.
A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Ma’ida gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.
Suratul Ma’ida cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ
-
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓا۟ أَوْفُوا۟ بِٱلْعُقُودِ ۚ أُحِلَّتْ لَكُم بَهِيمَةُ ٱلْأَنْعَـٰمِ إِلَّا مَا يُتْلَىٰ عَلَيْكُمْ غَيْرَ مُحِلِّى ٱلصَّيْدِ وَأَنتُمْ حُرُمٌ ۗ إِنَّ ٱللَّهَ يَحْكُمُ مَا يُرِيدُ١
Ya ayyuha allatheena amanoo awfoo bialʿuqoodi ohillat lakum baheematu alanʿami illa ma yutla ʿalaykum ghayra muhillee alssaydi waantum hurumun inna Allaha yahkumu ma yureedu
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! ku cika alkawurra. An halatta muku dabbobin jin dãɗi fãce abin da ake karantãwa a kanku, bã kunã mãsu halattar da farauta ba alhãli kuwa kunã mãsu harama. Lalle ne, Allah Yanã hukunta abin da yake nufi.
-
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ لَا تُحِلُّوا۟ شَعَـٰٓئِرَ ٱللَّهِ وَلَا ٱلشَّهْرَ ٱلْحَرَامَ وَلَا ٱلْهَدْىَ وَلَا ٱلْقَلَـٰٓئِدَ وَلَآ ءَآمِّينَ ٱلْبَيْتَ ٱلْحَرَامَ يَبْتَغُونَ فَضْلًا مِّن رَّبِّهِمْ وَرِضْوَٰنًا ۚ وَإِذَا حَلَلْتُمْ فَٱصْطَادُوا۟ ۚ وَلَا يَجْرِمَنَّكُمْ شَنَـَٔانُ قَوْمٍ أَن صَدُّوكُمْ عَنِ ٱلْمَسْجِدِ ٱلْحَرَامِ أَن تَعْتَدُوا۟ ۘ وَتَعَاوَنُوا۟ عَلَى ٱلْبِرِّ وَٱلتَّقْوَىٰ ۖ وَلَا تَعَاوَنُوا۟ عَلَى ٱلْإِثْمِ وَٱلْعُدْوَٰنِ ۚ وَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ ۖ إِنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلْعِقَابِ٢
Ya ayyuha allatheena amanoo la tuhilloo shaʿaira Allahi wala alshshahra alharama wala alhadya wala alqalaida wala ammeena albayta alharama yabtaghoona fadlan min rabbihim waridwanan waitha halaltum faistadoo wala yajrimannakum shanaanu qawmin an saddookum ʿani almasjidi alharami an taʿtadoo wataʿawanoo ʿala albirri waalttaqwa wala taʿawanoo ʿala alithmi waalʿudwani waittaqoo Allaha inna Allaha shadeedu alʿiqabi
Ya kũ waɗanda suka yi ĩmãni! kada ku halattar da ayyukan ibãdar Allah game da hajji, kuma da watã mai alfarma, kuma da hadaya, kuma da rãtayar raƙuman hadaya, kuma da mãsu nufin ¦ãki mai alfarma, sunã neman falala daga Ubangijinsu da yarda. Kuma idan kun kwance harama, to, ku yi farauta. Kuma kada ƙiyayya da wasu mutãne ta ɗauke ku, dõmin sun kange ku daga Masallãci Mai alfarma, ga ku yi zãlunci. Kuma ku taimaki junã a kan aikin ƙwarai da taƙawa. Kuma kada ku taimaki juna a kan zunubi da zãlunci, kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle ne Allah Mai tsananin uƙũba ne.
-
حُرِّمَتْ عَلَيْكُمُ ٱلْمَيْتَةُ وَٱلدَّمُ وَلَحْمُ ٱلْخِنزِيرِ وَمَآ أُهِلَّ لِغَيْرِ ٱللَّهِ بِهِۦ وَٱلْمُنْخَنِقَةُ وَٱلْمَوْقُوذَةُ وَٱلْمُتَرَدِّيَةُ وَٱلنَّطِيحَةُ وَمَآ أَكَلَ ٱلسَّبُعُ إِلَّا مَا ذَكَّيْتُمْ وَمَا ذُبِحَ عَلَى ٱلنُّصُبِ وَأَن تَسْتَقْسِمُوا۟ بِٱلْأَزْلَـٰمِ ۚ ذَٰلِكُمْ فِسْقٌ ۗ ٱلْيَوْمَ يَئِسَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ مِن دِينِكُمْ فَلَا تَخْشَوْهُمْ وَٱخْشَوْنِ ۚ ٱلْيَوْمَ أَكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ وَأَتْمَمْتُ عَلَيْكُمْ نِعْمَتِى وَرَضِيتُ لَكُمُ ٱلْإِسْلَـٰمَ دِينًا ۚ فَمَنِ ٱضْطُرَّ فِى مَخْمَصَةٍ غَيْرَ مُتَجَانِفٍ لِّإِثْمٍ ۙ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ٣
Hurrimat ʿalaykumu almaytatu waalddamu walahmu alkhinzeeri wama ohilla lighayri Allahi bihi waalmunkhaniqatu waalmawqoothatu waalmutaraddiyatu waalnnateehatu wama akala alssabuʿu illa ma thakkaytum wama thubiha ʿala alnnusubi waan tastaqsimoo bialazlami thalikum fisqun alyawma yaisa allatheena kafaroo min deenikum fala takhshawhum waikhshawni alyawma akmaltu lakum deenakum waatmamtu ʿalaykum niʿmatee waradeetu lakumu alislama deenan famani idturra fee makhmasatin ghayra mutajanifin liithmin fainna Allaha ghafoorun raheemun
An haramta muku mũshe da jini da nãman alade da abin da aka ambaci sũnan wanin Allah a gare shi, da mãƙararriya da jefaffiya da mai gangarõwa da sõkakkiya, da abin da mãsu dãgi suka ci, fãce abin da kuka yanka, da abin da aka yanka a kan gunki (shĩ ma an haramta). Kuma kada ku yi rabo da kibiyoyi na cãca wannan fãsiƙanci ne, A yau waɗanda suka kãfirta sun yanke ƙauna daga addininku. Sabõda haka kada ku ji tsõronsu kuma ku ji tsõroNa. A yau Nã kammalã muku addininku, Kuma Nã cika ni'imaTa a kanku, Kuma Nã yarda da Musulunci ya zama addini a gare ku. To, wanda aka sanya wa lalũra a cikin yunwa mai tsanani, bã yana mai karkata zuwa ga wani zunubi ba, to, lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
-
يَسْـَٔلُونَكَ مَاذَآ أُحِلَّ لَهُمْ ۖ قُلْ أُحِلَّ لَكُمُ ٱلطَّيِّبَـٰتُ ۙ وَمَا عَلَّمْتُم مِّنَ ٱلْجَوَارِحِ مُكَلِّبِينَ تُعَلِّمُونَهُنَّ مِمَّا عَلَّمَكُمُ ٱللَّهُ ۖ فَكُلُوا۟ مِمَّآ أَمْسَكْنَ عَلَيْكُمْ وَٱذْكُرُوا۟ ٱسْمَ ٱللَّهِ عَلَيْهِ ۖ وَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَرِيعُ ٱلْحِسَابِ٤
Yasaloonaka matha ohilla lahum qul ohilla lakumu alttayyibatu wama ʿallamtum mina aljawarihi mukallibeena tuʿallimoonahunna mimma ʿallamakumu Allahu fakuloo mimma amsakna ʿalaykum waothkuroo isma Allahi ʿalayhi waittaqoo Allaha inna Allaha sareeʿu alhisabi
Suna tambayar ka cewa mene ne aka halatta musu? Ka ce: "An halatta muku abũbuwa mãsu dãɗi da abin da kuka sanar (farauta) daga mãsu yin mĩki, kunã mãsu sakinsu daga hannuwanku, kunã sanar da su daga abin da Allah Ya sanar da ku. To, ku ci daga abin da suka kama sabõda ku, kuma ku ambaci sunan Allah a kansa, kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle ne Allah Mai gaugawar sakamako da yawã ne.
-
ٱلْيَوْمَ أُحِلَّ لَكُمُ ٱلطَّيِّبَـٰتُ ۖ وَطَعَامُ ٱلَّذِينَ أُوتُوا۟ ٱلْكِتَـٰبَ حِلٌّ لَّكُمْ وَطَعَامُكُمْ حِلٌّ لَّهُمْ ۖ وَٱلْمُحْصَنَـٰتُ مِنَ ٱلْمُؤْمِنَـٰتِ وَٱلْمُحْصَنَـٰتُ مِنَ ٱلَّذِينَ أُوتُوا۟ ٱلْكِتَـٰبَ مِن قَبْلِكُمْ إِذَآ ءَاتَيْتُمُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ مُحْصِنِينَ غَيْرَ مُسَـٰفِحِينَ وَلَا مُتَّخِذِىٓ أَخْدَانٍ ۗ وَمَن يَكْفُرْ بِٱلْإِيمَـٰنِ فَقَدْ حَبِطَ عَمَلُهُۥ وَهُوَ فِى ٱلْـَٔاخِرَةِ مِنَ ٱلْخَـٰسِرِينَ٥
Alyawma ohilla lakumu alttayyibatu wataʿamu allatheena ootoo alkitaba hillun lakum wataʿamukum hillun lahum waalmuhsanatu mina almuminati waalmuhsanatu mina allatheena ootoo alkitaba min qablikum itha ataytumoohunna ojoorahunna muhsineena ghayra musafiheena wala muttakhithee akhdanin waman yakfur bialeemani faqad habita ʿamaluhu wahuwa fee alakhirati mina alkhasireena
A yau an halatta muku abũbuwa mãsu dãɗi kuma abincin waɗanda aka bai wa Littãfi halal ne a gare ku, kuma abincinku halal ne a gare su, da mãtã mãsu kãmun kai daga muminai da mãtã 'yã'ya daga waɗanda aka bai wa Littãfi1 a gabãninku idan kun je musu da sadãkõkinsu, kuna mãsu yin aure, ba masu yin zina ba, kuma bã mãsu riƙon abõkai ba. Kuma wanda ya kãfirta da ĩmãni to, lalle ne aikinsa yã ɓãci, kuma shĩ, a cikin Lãhira, yanã daga mãsu hasãra.
Bayanai
[1] Wãtau Yahudãwa da Kiristãwa. -
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓا۟ إِذَا قُمْتُمْ إِلَى ٱلصَّلَوٰةِ فَٱغْسِلُوا۟ وُجُوهَكُمْ وَأَيْدِيَكُمْ إِلَى ٱلْمَرَافِقِ وَٱمْسَحُوا۟ بِرُءُوسِكُمْ وَأَرْجُلَكُمْ إِلَى ٱلْكَعْبَيْنِ ۚ وَإِن كُنتُمْ جُنُبًا فَٱطَّهَّرُوا۟ ۚ وَإِن كُنتُم مَّرْضَىٰٓ أَوْ عَلَىٰ سَفَرٍ أَوْ جَآءَ أَحَدٌ مِّنكُم مِّنَ ٱلْغَآئِطِ أَوْ لَـٰمَسْتُمُ ٱلنِّسَآءَ فَلَمْ تَجِدُوا۟ مَآءً فَتَيَمَّمُوا۟ صَعِيدًا طَيِّبًا فَٱمْسَحُوا۟ بِوُجُوهِكُمْ وَأَيْدِيكُم مِّنْهُ ۚ مَا يُرِيدُ ٱللَّهُ لِيَجْعَلَ عَلَيْكُم مِّنْ حَرَجٍ وَلَـٰكِن يُرِيدُ لِيُطَهِّرَكُمْ وَلِيُتِمَّ نِعْمَتَهُۥ عَلَيْكُمْ لَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ٦
Ya ayyuha allatheena amanoo itha qumtum ila alssalati faighsiloo wujoohakum waaydiyakum ila almarafiqi waimsahoo biruoosikum waarjulakum ila alkaʿbayni wain kuntum junuban faittahharoo wain kuntum marda aw ʿala safarin aw jaa ahadun minkum mina alghaiti aw lamastumu alnnisaa falam tajidoo maan fatayammamoo saʿeedan tayyiban faimsahoo biwujoohikum waaydeekum minhu ma yureedu Allahu liyajʿala ʿalaykum min harajin walakin yureedu liyutahhirakum waliyutimma niʿmatahu ʿalaykum laʿallakum tashkuroona
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! idan kun tãshi1 zuwa ga salla, to, ku wanke fuskõkinku da hannuwanku zuwa ga magincirõri, kuma ku yi shãfa ga kãnunku, kuma ku (wanke) ƙafãfunku zuwa idãnun sãwu biyu. Kuma idan kun kasance mãsu janaba, to, ku yi tsarki, kuma idan kun kasance majinyata, kõ kuwa a kan tafiya, kõ kuwa ɗaya daga gare ku ya zo daga kãshi, kõ kuka yi shãfayyar junã da mãtã, sa'an nan ba ku sãmi ruwa ba to ku yi nufin wuri2 mai kyau, sa'an nan ku yi shãfa ga fuskõkinku da hannuwanku daga gare shi. Allah bã Ya nufi dõmin Ya sanya wani ƙunci a kanku, kuma amma Yanã nufi dõmin Ya cika ni'imarSa a kanku, tsammãninku kunã gõdewa.
Bayanai
[1] Abin da ake halatta salla da shi ruwa mai tsarki domin ɗauke hadasi ƙarami da alwala, da hadasi babba da wanka. ldan bãbu ruwa a yi taimama da wuri na fuskar ƙasa wanda bai sãke ba da wata sana'ar mutum. Bauli da wadiyyi da kãshi da tusa da shãfar jin dãɗi na namiji ga mace ko mace ga namiji, da shafar zakarin kansa, duka suna wajabtar da alwalla. Fitar maniyyi da haila suna wajabtar da wanka. Maziyyi na wajabtar da wanke dukkan zakari sa'an nan a yi alwalla. Yankan hannun ɓarãwo yã nuna iyakar inda ake shãfar farilla na taimama, da sunna, kamar yadda ake yin sauran ayyuka duka a kan ƙiyãsinsu bisa ga wasu. [2] Wãtau ku yi taimama. -
وَٱذْكُرُوا۟ نِعْمَةَ ٱللَّهِ عَلَيْكُمْ وَمِيثَـٰقَهُ ٱلَّذِى وَاثَقَكُم بِهِۦٓ إِذْ قُلْتُمْ سَمِعْنَا وَأَطَعْنَا ۖ وَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمٌۢ بِذَاتِ ٱلصُّدُورِ٧
Waothkuroo niʿmata Allahi ʿalaykum wameethaqahu allathee wathaqakum bihi ith qultum samiʿna waataʿna waittaqoo Allaha inna Allaha ʿaleemun bithati alssudoori
Kuma ku tuna ni'imar Allah akanku da alkawarinku wanda Ya ɗaure ku da shi, a lõkacin da kuka ce: "Mun ji kuma mun yi ɗã'a Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle ne Allah Masani ne ga abin da ke a cikin zukata."
-
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ كُونُوا۟ قَوَّٰمِينَ لِلَّهِ شُهَدَآءَ بِٱلْقِسْطِ ۖ وَلَا يَجْرِمَنَّكُمْ شَنَـَٔانُ قَوْمٍ عَلَىٰٓ أَلَّا تَعْدِلُوا۟ ۚ ٱعْدِلُوا۟ هُوَ أَقْرَبُ لِلتَّقْوَىٰ ۖ وَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ خَبِيرٌۢ بِمَا تَعْمَلُونَ٨
Ya ayyuha allatheena amanoo koonoo qawwameena lillahi shuhadaa bialqisti wala yajrimannakum shanaanu qawmin ʿala alla taʿdiloo iʿdiloo huwa aqrabu lilttaqwa waittaqoo Allaha inna Allaha khabeerun bima taʿmaloona
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kasance mãsu tsayin daka dõmin Allah mãsu shaida da ãdalci. Kuma kada ƙiyayya da wasu mutane ta ɗauke ku a kan bã zã ku yi ãdalci ba. Ku yi ãdalci Shĩ ne mafi kusa ga taƙawa. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle Allah Masani ne ga abin da kuke aikatãwa.
-
وَعَدَ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ ۙ لَهُم مَّغْفِرَةٌ وَأَجْرٌ عَظِيمٌ٩
Waʿada Allahu allatheena amanoo waʿamiloo alssalihati lahum maghfiratun waajrun ʿatheemun
Allah Yã yi wa'adi ga waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai. Sunã da wata gãfara da lãda mai girma.
-
وَٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ وَكَذَّبُوا۟ بِـَٔايَـٰتِنَآ أُو۟لَـٰٓئِكَ أَصْحَـٰبُ ٱلْجَحِيمِ١٠
Waallatheena kafaroo wakaththaboo biayatina olaika ashabu aljaheemi
Kuma waɗanda suka kãfirta, kuma suka ƙaryatã, game da ãyõyinMu, waɗannan su ne abõkan wuta.
-
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ ٱذْكُرُوا۟ نِعْمَتَ ٱللَّهِ عَلَيْكُمْ إِذْ هَمَّ قَوْمٌ أَن يَبْسُطُوٓا۟ إِلَيْكُمْ أَيْدِيَهُمْ فَكَفَّ أَيْدِيَهُمْ عَنكُمْ ۖ وَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ ۚ وَعَلَى ٱللَّهِ فَلْيَتَوَكَّلِ ٱلْمُؤْمِنُونَ١١
Ya ayyuha allatheena amanoo othkuroo niʿmata Allahi ʿalaykum ith hamma qawmun an yabsutoo ilaykum aydiyahum fakaffa aydiyahum ʿankum waittaqoo Allaha waʿala Allahi falyatawakkali almuminoona
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku tuna ni'imar Allah a kanku a lõkacin da wasu mutãne suka yi niyyar su shimfiɗa hannuwansu zuwa gare ku1 sai Ya kange hannuwansu daga gare ku, kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma sai muminai su dogara ga Allah kawai.
Bayanai
[1] Wannan kiyãyewa ya auku a wurãre da yawa tun Musulmi suna da rauni kuma kãfirai suna da ƙarfi, kuma suna son su kashe Musulmi da Musulunci. Allah Ya tsare su. Saboda haka yanzu da Musulmi suka yi ƙarfi da ƙarfin Allah, yã wajaba a kansu su godewa Allah da taƙawa. Watau su riƙe alkawarin Allah, su yi abin da Ya aza musu gwargwadon hãli. -
۞ وَلَقَدْ أَخَذَ ٱللَّهُ مِيثَـٰقَ بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ وَبَعَثْنَا مِنْهُمُ ٱثْنَىْ عَشَرَ نَقِيبًا ۖ وَقَالَ ٱللَّهُ إِنِّى مَعَكُمْ ۖ لَئِنْ أَقَمْتُمُ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتَيْتُمُ ٱلزَّكَوٰةَ وَءَامَنتُم بِرُسُلِى وَعَزَّرْتُمُوهُمْ وَأَقْرَضْتُمُ ٱللَّهَ قَرْضًا حَسَنًا لَّأُكَفِّرَنَّ عَنكُمْ سَيِّـَٔاتِكُمْ وَلَأُدْخِلَنَّكُمْ جَنَّـٰتٍ تَجْرِى مِن تَحْتِهَا ٱلْأَنْهَـٰرُ ۚ فَمَن كَفَرَ بَعْدَ ذَٰلِكَ مِنكُمْ فَقَدْ ضَلَّ سَوَآءَ ٱلسَّبِيلِ١٢
Walaqad akhatha Allahu meethaqa banee israeela wabaʿathna minhumu ithnay ʿashara naqeeban waqala Allahu innee maʿakum lain aqamtumu alssalata waataytumu alzzakata waamantum birusulee waʿazzartumoohum waaqradtumu Allaha qardan hasanan laokaffiranna ʿankum sayyiatikum walaodkhilannakum jannatin tajree min tahtiha alanharu faman kafara baʿda thalika minkum faqad dalla sawaa alssabeeli
Kuma lalle Allah Yã riƙi alkawarin Banĩ lsrã' ĩla kuma Muka ayyana wakilai gõma shã biyu1 daga gare su kuma Allah Ya ce: "Lalle ne Nĩ, Inã tãre da ku, haƙĩƙa, idan kun tsayar da salla, kuma kun bãyar da zakka, kuma kun yi ĩmani da manzannĩ Na, kuma kuka taimake su, kuma kuka bai wa Allah rance mai kyau, haƙĩƙa, Inã kankare laifukanku daga gare ku, kuma haƙĩƙa, Inã shigar da ku gidãjen Aljanna (waɗanda) ƙõramu sanã gudãna a ƙarƙashinsu, sa'an nan wanda ya kãfirta a bãyan wannan daga gare ku, to, lalle ne, yã ɓace daga tsakar hanya."
Bayanai
[1] An ayyana wakilai goma shabiyu daga ƙabĩlun Bani Isrãĩla goma sha biyu domin su ɗaukar musu alkawari daga wurin, kuma su tsare mutãnensu ga ganin ba a sãɓa wa alkawarin ba. An gina addinin Bani Isrãĩla a kan ƙabĩlanci. Saboda haka addininsu bã ya fita daga dã'irarsu. -
فَبِمَا نَقْضِهِم مِّيثَـٰقَهُمْ لَعَنَّـٰهُمْ وَجَعَلْنَا قُلُوبَهُمْ قَـٰسِيَةً ۖ يُحَرِّفُونَ ٱلْكَلِمَ عَن مَّوَاضِعِهِۦ ۙ وَنَسُوا۟ حَظًّا مِّمَّا ذُكِّرُوا۟ بِهِۦ ۚ وَلَا تَزَالُ تَطَّلِعُ عَلَىٰ خَآئِنَةٍ مِّنْهُمْ إِلَّا قَلِيلًا مِّنْهُمْ ۖ فَٱعْفُ عَنْهُمْ وَٱصْفَحْ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلْمُحْسِنِينَ١٣
Fabima naqdihim meethaqahum laʿannahum wajaʿalna quloobahum qasiyatan yuharrifoona alkalima ʿan mawadiʿihi wanasoo haththan mimma thukkiroo bihi wala tazalu tattaliʿu ʿala khainatin minhum illa qaleelan minhum faoʿfu ʿanhum waisfah inna Allaha yuhibbu almuhsineena
To, sabõda warwarewarsu ga alkawarinsu Muka la'ane su, kuma Muka sanya zukãtansu ƙeƙasassu, sunã karkatar da magana daga wurãrenta, kuma suka manta da wani yanki daga abin da aka tunãtar da su da shi, kuma bã zã ka gushe ba kana tsinkãyar yaudara daga gare su fãce kaɗan daga gare su. To, ka yãfe laifi daga gare su, kuma ka kau da kai. Lalle ne, Allah Yanã son mãsu kyautatãwa.
-
وَمِنَ ٱلَّذِينَ قَالُوٓا۟ إِنَّا نَصَـٰرَىٰٓ أَخَذْنَا مِيثَـٰقَهُمْ فَنَسُوا۟ حَظًّا مِّمَّا ذُكِّرُوا۟ بِهِۦ فَأَغْرَيْنَا بَيْنَهُمُ ٱلْعَدَاوَةَ وَٱلْبَغْضَآءَ إِلَىٰ يَوْمِ ٱلْقِيَـٰمَةِ ۚ وَسَوْفَ يُنَبِّئُهُمُ ٱللَّهُ بِمَا كَانُوا۟ يَصْنَعُونَ١٤
Wamina allatheena qaloo inna nasara akhathna meethaqahum fanasoo haththan mimma thukkiroo bihi faaghrayna baynahumu alʿadawata waalbaghdaa ila yawmi alqiyamati wasawfa yunabbiohumu Allahu bima kanoo yasnaʿoona
Kuma daga waɗanda suka ce: "Lalle ne mu Nasãra ne" Mun riƙi alkawarinsu, sai suka manta da wani yanki daga abin da aka tunãtar da su da shi, sai Muka shushuta adãwa da ƙeta a tsakãninsu har ya zuwa ga Rãnar ¡iyãma. Kuma Allah zai bã su lãbari da abin da suka kasance sunã sanã'antawa.
-
يَـٰٓأَهْلَ ٱلْكِتَـٰبِ قَدْ جَآءَكُمْ رَسُولُنَا يُبَيِّنُ لَكُمْ كَثِيرًا مِّمَّا كُنتُمْ تُخْفُونَ مِنَ ٱلْكِتَـٰبِ وَيَعْفُوا۟ عَن كَثِيرٍ ۚ قَدْ جَآءَكُم مِّنَ ٱللَّهِ نُورٌ وَكِتَـٰبٌ مُّبِينٌ١٥
Ya ahla alkitabi qad jaakum rasooluna yubayyinu lakum katheeran mimma kuntum tukhfoona mina alkitabi wayaʿfoo ʿan katheerin qad jaakum mina Allahi noorun wakitabun mubeenun
Yã Mutãnen littãfi! Lalle ne, Manzon Mu yã je muku, yanã bayyana muku abu mai yawa daga abin da kuka kasance kunã ɓõyewa daga Littãfi, kuma yanã rangwame daga abu mai yawa. Haƙĩƙa, wani haske da wani Littafi mai bayyanãwa yã je muku daga Allah.
-
يَهْدِى بِهِ ٱللَّهُ مَنِ ٱتَّبَعَ رِضْوَٰنَهُۥ سُبُلَ ٱلسَّلَـٰمِ وَيُخْرِجُهُم مِّنَ ٱلظُّلُمَـٰتِ إِلَى ٱلنُّورِ بِإِذْنِهِۦ وَيَهْدِيهِمْ إِلَىٰ صِرَٰطٍ مُّسْتَقِيمٍ١٦
Yahdee bihi Allahu mani ittabaʿa ridwanahu subula alssalami wayukhrijuhum mina alththulumati ila alnnoori biithnihi wayahdeehim ila siratin mustaqeemin
Dashĩ, Allah Yanã shiryar da wanda ya bi yardarsa zuwa ga hanyõyin aminci, kuma Yanã fitar da su daga duffai zuwa ga haske da izninsa, kuma Yanã shiryar da su zuwa ga hanya madaidaiciya.
-
لَّقَدْ كَفَرَ ٱلَّذِينَ قَالُوٓا۟ إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلْمَسِيحُ ٱبْنُ مَرْيَمَ ۚ قُلْ فَمَن يَمْلِكُ مِنَ ٱللَّهِ شَيْـًٔا إِنْ أَرَادَ أَن يُهْلِكَ ٱلْمَسِيحَ ٱبْنَ مَرْيَمَ وَأُمَّهُۥ وَمَن فِى ٱلْأَرْضِ جَمِيعًا ۗ وَلِلَّهِ مُلْكُ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا ۚ يَخْلُقُ مَا يَشَآءُ ۚ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍ قَدِيرٌ١٧
Laqad kafara allatheena qaloo inna Allaha huwa almaseehu ibnu maryama qul faman yamliku mina Allahi shayan in arada an yuhlika almaseeha ibna maryama waommahu waman fee alardi jameeʿan walillahi mulku alssamawati waalardi wama baynahuma yakhluqu ma yashao waAllahu ʿala kulli shayin qadeerun
Lalle haƙĩƙa waɗanda suka ce: "Lalle Allah Shĩ ne Masĩhu ɗan Maryama," sun kãfirta. Ka ce: "To, wane ne ke iya mallakar wani abu daga Allah, idan Yã nufi Ya halakar da Masĩhu ɗan Maryama da uwarsa da wanda yake a cikin ƙasa gabã ɗaya?" Kuma Allah ne da mallakar sammai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu, Yanã halitta abin da Yake so. Kuma Allah a kan dukkan kõme, Mai ĩkon yi ne.
-
وَقَالَتِ ٱلْيَهُودُ وَٱلنَّصَـٰرَىٰ نَحْنُ أَبْنَـٰٓؤُا۟ ٱللَّهِ وَأَحِبَّـٰٓؤُهُۥ ۚ قُلْ فَلِمَ يُعَذِّبُكُم بِذُنُوبِكُم ۖ بَلْ أَنتُم بَشَرٌ مِّمَّنْ خَلَقَ ۚ يَغْفِرُ لِمَن يَشَآءُ وَيُعَذِّبُ مَن يَشَآءُ ۚ وَلِلَّهِ مُلْكُ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا ۖ وَإِلَيْهِ ٱلْمَصِيرُ١٨
Waqalati alyahoodu waalnnasara nahnu abnao Allahi waahibbaohu qul falima yuʿaththibukum bithunoobikum bal antum basharun mimman khalaqa yaghfiru liman yashao wayuʿaththibu man yashao walillahi mulku alssamawati waalardi wama baynahuma wailayhi almaseeru
Kuma Yahudu da Nasãra sun ce: "Mu ne ɗiyan Allah, kuma masõyansa." Ka ce: "To, don me Yake yi muku azãba da zunubanku? Ã'a ku mutãne ne daga waɗanda Ya halitta, Yanã gãfartãwa ga wanda Yake so, kuma Yanã azabta wanda Yake so. Kuma Allah ne da mulkin sammai da ƙasa da abin da ke tsakãninsu kuma zuwa gare shi makomã take."
-
يَـٰٓأَهْلَ ٱلْكِتَـٰبِ قَدْ جَآءَكُمْ رَسُولُنَا يُبَيِّنُ لَكُمْ عَلَىٰ فَتْرَةٍ مِّنَ ٱلرُّسُلِ أَن تَقُولُوا۟ مَا جَآءَنَا مِنۢ بَشِيرٍ وَلَا نَذِيرٍ ۖ فَقَدْ جَآءَكُم بَشِيرٌ وَنَذِيرٌ ۗ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍ قَدِيرٌ١٩
Ya ahla alkitabi qad jaakum rasooluna yubayyinu lakum ʿala fatratin mina alrrusuli an taqooloo ma jaana min basheerin wala natheerin faqad jaakum basheerun wanatheerun waAllahu ʿala kulli shayin qadeerun
Yã Mutãnen Littãfi! Lalle Manzon Mu yã je muku yanã bayyana muku, a kan lõkacin fatara daga manzanni, dõmin kada ku ce: "wani mai bayar da bushãra bai zo mana ba, kuma haka wani mai gargaɗi bai zo ba." To, haƙĩƙa, mai bãyar da bushãra da mai gargaɗi sunje muku. Kuma Allah ne, a kan dukkan kõme, Mai ĩkon yi.
-
وَإِذْ قَالَ مُوسَىٰ لِقَوْمِهِۦ يَـٰقَوْمِ ٱذْكُرُوا۟ نِعْمَةَ ٱللَّهِ عَلَيْكُمْ إِذْ جَعَلَ فِيكُمْ أَنۢبِيَآءَ وَجَعَلَكُم مُّلُوكًا وَءَاتَىٰكُم مَّا لَمْ يُؤْتِ أَحَدًا مِّنَ ٱلْعَـٰلَمِينَ٢٠
Waith qala moosa liqawmihi ya qawmi othkuroo niʿmata Allahi ʿalaykum ith jaʿala feekum anbiyaa wajaʿalakum mulookan waatakum ma lam yuti ahadan mina alʿalameena
Kuma a lõkacin da Musa ya ce wa mutãnensa: "Yã ku mutãnena! Ku tuna ni'imar Allah a kanku; dõmin Yã sanya annabãwa a cikinku, kuma Yã sanya ku sarãkuna, kuma Yã bã ku abin da bai bai wa kõwa ba daga tãlikai."
-
يَـٰقَوْمِ ٱدْخُلُوا۟ ٱلْأَرْضَ ٱلْمُقَدَّسَةَ ٱلَّتِى كَتَبَ ٱللَّهُ لَكُمْ وَلَا تَرْتَدُّوا۟ عَلَىٰٓ أَدْبَارِكُمْ فَتَنقَلِبُوا۟ خَـٰسِرِينَ٢١
Ya qawmi odkhuloo alarda almuqaddasata allatee kataba Allahu lakum wala tartaddoo ʿala adbarikum fatanqaliboo khasireena
"Yã mutãnena! Ku shiga ƙasar nan, abar tsarkakewa, wadda Allah Ya rubuta sabõda ku, kuma kada ku kõma da bãya, har ku juya kunã mãsu hasara."
-
قَالُوا۟ يَـٰمُوسَىٰٓ إِنَّ فِيهَا قَوْمًا جَبَّارِينَ وَإِنَّا لَن نَّدْخُلَهَا حَتَّىٰ يَخْرُجُوا۟ مِنْهَا فَإِن يَخْرُجُوا۟ مِنْهَا فَإِنَّا دَٰخِلُونَ٢٢
Qaloo ya moosa inna feeha qawman jabbareena wainna lan nadkhulaha hatta yakhrujoo minha fain yakhrujoo minha fainna dakhiloona
Suka ce: "Ya Musã! Lalle ne, a cikinta akwai wasu mutãne mãsu ƙarfi kuma lalle ne bã zã mu shige ta ba sai sun fice daga gare ta, to, idan sun fice daga gare ta, to, lalle ne mu, masu shiga ne."
-
قَالَ رَجُلَانِ مِنَ ٱلَّذِينَ يَخَافُونَ أَنْعَمَ ٱللَّهُ عَلَيْهِمَا ٱدْخُلُوا۟ عَلَيْهِمُ ٱلْبَابَ فَإِذَا دَخَلْتُمُوهُ فَإِنَّكُمْ غَـٰلِبُونَ ۚ وَعَلَى ٱللَّهِ فَتَوَكَّلُوٓا۟ إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ٢٣
Qala rajulani mina allatheena yakhafoona anʿama Allahu ʿalayhima odkhuloo ʿalayhimu albaba faitha dakhaltumoohu fainnakum ghaliboona waʿala Allahi fatawakkaloo in kuntum mumineena
Wasu maza biyu1 daga waɗanda suke tsõron Allah, Allah Yã yi ni'ima a kansu, suka ce: "Ku shiga gare su, daga ƙõfar, dõmin idan kuka shige shi, to, lalle ne ku, mãsu rinjãya ne, kuma ga Allah sai ku dogara idan kun kasance muminai."
Bayanai
[1] Maza biyu su ne Yusha'u da Kãlib daga Nuƙabã'u, watau wakilai goma sha biyu waɗanda Annabi Musã ya aike su domin su yiwo binciken hãlãyen mutanen da suke zaune a cikin Ƙudus. Yadda ya fãru shi ne, bãyan da Allah Ya halaka Fir'auna sai Bani Isrã'ĩla suka koma Masar, daga nan sai Allah Ya rubuta musu cewa su tashi su koma Ariha'a, a cikin ƙasar Sham alhãli mazaunanta kuwa Kan'aniyyawa ne. Sai Musã ya gaya musu cewa, ga ƙasar da Allah Ya bã su, su fitar da waɗanda ke a ciki su zauna. Musã ya aika da mutum goma sha biyu domin su yiwo leƙen asiri su zo masa da lãbãri, kada su gaya wa mutãne abin da suka gani domin kada su firgita. Bayan da suka kõmo, sai suka warware alkawarin; sai mutum biyu daga cikin su, Yusha'u da Kãlib. -
قَالُوا۟ يَـٰمُوسَىٰٓ إِنَّا لَن نَّدْخُلَهَآ أَبَدًا مَّا دَامُوا۟ فِيهَا ۖ فَٱذْهَبْ أَنتَ وَرَبُّكَ فَقَـٰتِلَآ إِنَّا هَـٰهُنَا قَـٰعِدُونَ٢٤
Qaloo ya moosa inna lan nadkhulaha abadan ma damoo feeha faithhab anta warabbuka faqatila inna hahuna qaʿidoona
Suka ce: "Ya Musa! Lalle ne mu, bã za mu shige ta ba har abada matuƙar sun dawwama a cikinta sai ka tafi kai da Ubangijinka dõmin ku yi yãƙi. Lalle ne mu, munã a nan zaune."
-
قَالَ رَبِّ إِنِّى لَآ أَمْلِكُ إِلَّا نَفْسِى وَأَخِى ۖ فَٱفْرُقْ بَيْنَنَا وَبَيْنَ ٱلْقَوْمِ ٱلْفَـٰسِقِينَ٢٥
Qala rabbi innee la amliku illa nafsee waakhee faofruq baynana wabayna alqawmi alfasiqeena
Ya ce: "Yã Ubangijina! Lalle ne nĩ, bã ni mallakar kõwa fãce kaina da ɗan'uwãna, sai Ka rarrabe a tsakãninmu da tsakãnin mutãne fãsiƙai."
-
قَالَ فَإِنَّهَا مُحَرَّمَةٌ عَلَيْهِمْ ۛ أَرْبَعِينَ سَنَةً ۛ يَتِيهُونَ فِى ٱلْأَرْضِ ۚ فَلَا تَأْسَ عَلَى ٱلْقَوْمِ ٱلْفَـٰسِقِينَ٢٦
Qala fainnaha muharramatun ʿalayhim arbaʿeena sanatan yateehoona fee alardi fala tasa ʿala alqawmi alfasiqeena
(Allah) Ya ce: "To, lalle ne ita abar haramtãwa ce a gare su, shekara arba'in, sunã yin ɗimuwa a cikin ƙasa1. Sabõda haka kada ka yi baƙin ciki a kan mutãne fãsiƙai."
Bayanai
[1] Wannan shi ne sakamakon sãɓawar alkawari, da aka ce wa magewaya kada su faɗi abin da suka gani, saboda aƙibar abin, kusan duka sai da suka mutu a cikin halin ɗimuwar. -
۞ وَٱتْلُ عَلَيْهِمْ نَبَأَ ٱبْنَىْ ءَادَمَ بِٱلْحَقِّ إِذْ قَرَّبَا قُرْبَانًا فَتُقُبِّلَ مِنْ أَحَدِهِمَا وَلَمْ يُتَقَبَّلْ مِنَ ٱلْـَٔاخَرِ قَالَ لَأَقْتُلَنَّكَ ۖ قَالَ إِنَّمَا يَتَقَبَّلُ ٱللَّهُ مِنَ ٱلْمُتَّقِينَ٢٧
Waotlu ʿalayhim nabaa ibnay adama bialhaqqi ith qarraba qurbanan fatuqubbila min ahadihima walam yutaqabbal mina alakhari qala laaqtulannaka qala innama yataqabbalu Allahu mina almuttaqeena
Kuma karantã musu1 lãbãrin ɗiya biyu2 na Ãdamu, da gaskiya, a lõkacin da suka bãyar da baiko, sai aka karɓa daga ɗayansu kuma ba a karɓa daga ɗayan ba, ya ce: "Lalle ne zan kashe ka." (¦ayan kuma) ya ce: "Abin sani dai, Allah Yana karɓã daga mãsu taƙawa ne."
Bayanai
[1] Ƙuraishawa ko kuwa al'ummarka. [2] Ɗiyan Ãdamu, biyu, Ƙãbĩla da Hãbĩla. Asalin maganar kamar yadda aka ruwaito, mãtar Ãdamu, Hauwa'u, tana haifuwar namiji da mace a kowane ciki, wajen aure sai a shirɓata dõmin bãbu wasu mutãne sai su. Sai Ƙabĩla ya ƙi yarda a bai wa Hãbĩla 'yar'uwarsa, har Ãdam ya sanya su yin baiko da abin sana'arsu. Ƙãbĩla manõmi ne, ya bãyar da munãna daga kãyan nõmansa, shi kuma Hãbĩla ya bãyar da rãgo mai kyau dõmin sana'arsa kiwo ne. Sai wuta ta sauko ta ɗauki rãgon Hãbĩla, alãmar karɓa. Wannan kuwa ya ɗauki Ƙãbĩla ga tunãnin kashe shi. Laifi guda yana sabbaba wasu laifuka mãsu yawa. -
لَئِنۢ بَسَطتَ إِلَىَّ يَدَكَ لِتَقْتُلَنِى مَآ أَنَا۠ بِبَاسِطٍ يَدِىَ إِلَيْكَ لِأَقْتُلَكَ ۖ إِنِّىٓ أَخَافُ ٱللَّهَ رَبَّ ٱلْعَـٰلَمِينَ٢٨
Lain basatta ilayya yadaka litaqtulanee ma ana bibasitin yadiya ilayka liaqtulaka innee akhafu Allaha rabba alʿalameena
"Lalle ne idan ka shimfiɗa hannunka zuwa gare ni dõmin ka kashe ni, ban zama mai shimfiɗa hannuna zuwa gare ka ba dõmin in kashe ka. Lalle ne nĩ inã tsõron Allah Ubangijin tãlikai.
-
إِنِّىٓ أُرِيدُ أَن تَبُوٓأَ بِإِثْمِى وَإِثْمِكَ فَتَكُونَ مِنْ أَصْحَـٰبِ ٱلنَّارِ ۚ وَذَٰلِكَ جَزَٰٓؤُا۟ ٱلظَّـٰلِمِينَ٢٩
Innee oreedu an tabooa biithmee waithmika fatakoona min ashabi alnnari wathalika jazao alththalimeena
"Lalle ne nĩ inã nufin ka kõma da zunubina game da zunubinka, har ka kasance daga abõkan wuta. Kuma wannan shĩ ne sakamakon azzãlumai."
-
فَطَوَّعَتْ لَهُۥ نَفْسُهُۥ قَتْلَ أَخِيهِ فَقَتَلَهُۥ فَأَصْبَحَ مِنَ ٱلْخَـٰسِرِينَ٣٠
Fatawwaʿat lahu nafsuhu qatla akheehi faqatalahu faasbaha mina alkhasireena
Sai ransa ya ƙawãtar masa kashewar ɗan'uwansa, sai kuwa ya kashe shi, sa'an nan ya wayi gari daga mãsu hasãra.
-
فَبَعَثَ ٱللَّهُ غُرَابًا يَبْحَثُ فِى ٱلْأَرْضِ لِيُرِيَهُۥ كَيْفَ يُوَٰرِى سَوْءَةَ أَخِيهِ ۚ قَالَ يَـٰوَيْلَتَىٰٓ أَعَجَزْتُ أَنْ أَكُونَ مِثْلَ هَـٰذَا ٱلْغُرَابِ فَأُوَٰرِىَ سَوْءَةَ أَخِى ۖ فَأَصْبَحَ مِنَ ٱلنَّـٰدِمِينَ٣١
Fabaʿatha Allahu ghuraban yabhathu fee alardi liyuriyahu kayfa yuwaree sawata akheehi qala ya waylata aʿajaztu an akoona mithla hatha alghurabi faowariya sawata akhee faasbaha mina alnnadimeena
Sai Allah Ya aiki wani hankãka, yanã tõno a cikin ƙasa dõmin ya nuna masa yadda zai turbuɗe gãwar ɗan'uwansa. Ya ce: "Kaitõna! Nã kãsa in kasance kamar wannan hankãka dõmin in turbuɗe gãwar ɗan'uwana?" Sai ya wãyi gari daga mãsu nadãmã.
-
مِنْ أَجْلِ ذَٰلِكَ كَتَبْنَا عَلَىٰ بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ أَنَّهُۥ مَن قَتَلَ نَفْسًۢا بِغَيْرِ نَفْسٍ أَوْ فَسَادٍ فِى ٱلْأَرْضِ فَكَأَنَّمَا قَتَلَ ٱلنَّاسَ جَمِيعًا وَمَنْ أَحْيَاهَا فَكَأَنَّمَآ أَحْيَا ٱلنَّاسَ جَمِيعًا ۚ وَلَقَدْ جَآءَتْهُمْ رُسُلُنَا بِٱلْبَيِّنَـٰتِ ثُمَّ إِنَّ كَثِيرًا مِّنْهُم بَعْدَ ذَٰلِكَ فِى ٱلْأَرْضِ لَمُسْرِفُونَ٣٢
Min ajli thalika katabna ʿala banee israeela annahu man qatala nafsan bighayri nafsin aw fasadin fee alardi fakaannama qatala alnnasa jameeʿan waman ahyaha fakaannama ahya alnnasa jameeʿan walaqad jaa thum rusuluna bialbayyinati thumma inna katheeran minhum baʿda thalika fee alardi lamusrifoona
Daga sababin wannan,1 Muka rubuta a kan Banĩ lsrã'ĩla cewa, lalle ne wanda ya kashe rai bã da wani rai ba, ko ɓarna a cikin ƙasa, to kamar yã kashe mutãne duka ne, kuma wanda ya rãya rai, to, kamar yã rãyar da mutãne ne gabã ɗaya. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Manzannin Mu sun je musu da hujjõji bayyanannu, sa'an nan kuma lalle ne, mãsu yawa daga gare su, a bãyan wannan, haƙĩƙa, mãsuɓarna ne a cikin ƙasa.
Bayanai
[1] Aikata ƙaramin laifi yana sabbaba babban laifi har ɓarna mai yawa ta wãtsu a cikin ƙasa. -
إِنَّمَا جَزَٰٓؤُا۟ ٱلَّذِينَ يُحَارِبُونَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ وَيَسْعَوْنَ فِى ٱلْأَرْضِ فَسَادًا أَن يُقَتَّلُوٓا۟ أَوْ يُصَلَّبُوٓا۟ أَوْ تُقَطَّعَ أَيْدِيهِمْ وَأَرْجُلُهُم مِّنْ خِلَـٰفٍ أَوْ يُنفَوْا۟ مِنَ ٱلْأَرْضِ ۚ ذَٰلِكَ لَهُمْ خِزْىٌ فِى ٱلدُّنْيَا ۖ وَلَهُمْ فِى ٱلْـَٔاخِرَةِ عَذَابٌ عَظِيمٌ٣٣
Innama jazao allatheena yuhariboona Allaha warasoolahu wayasʿawna fee alardi fasadan an yuqattaloo aw yusallaboo aw tuqattaʿa aydeehim waarjuluhum min khilafin aw yunfaw mina alardi thalika lahum khizyun fee alddunya walahum fee alakhirati ʿathabun ʿatheemun
Abin sani kawai sakamakon1 waɗanda suke Yãƙin Allah da Manzonsa, kuma sunã aiki a cikin ƙasa dõmin ɓarna a kashe su ko kuwa a ƙere su, kõ kuwa a kakkãtse hannuwansu da ƙafãfunsu daga sãɓãni, ko kuwa a kõre su daga ƙasa. Sannan gare su wulakanci ne a cikin rãyuwar duniya, kuma a Lãhira sunã da wata azãba mai girma.
Bayanai
[1] Muhãrib shi ne ɗan fashi mai tare hanya da makamai. Ana yi masa ɗayan abin da aka ga yã dãce da shi. Wanda aka yi wa "Salbu" sai kuma a kashe shi. Amfanin Salbu shi ne a gan shi, dõmin hankalin mutãne ya natsu. Korewa yanzu sai ta koma ga ɗauri har ya mutu ko ya tuba. -
إِلَّا ٱلَّذِينَ تَابُوا۟ مِن قَبْلِ أَن تَقْدِرُوا۟ عَلَيْهِمْ ۖ فَٱعْلَمُوٓا۟ أَنَّ ٱللَّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ٣٤
Illa allatheena taboo min qabli an taqdiroo ʿalayhim faiʿlamoo anna Allaha ghafoorun raheemun
Fãce fa waɗanda suka tuba tun a gabãnin ku sãmi ĩko akansu, to, ku sani cewa lalle ne, Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
-
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ ٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَٱبْتَغُوٓا۟ إِلَيْهِ ٱلْوَسِيلَةَ وَجَـٰهِدُوا۟ فِى سَبِيلِهِۦ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ٣٥
Ya ayyuha allatheena amanoo ittaqoo Allaha waibtaghoo ilayhi alwaseelata wajahidoo fee sabeelihi laʿallakum tuflihoona
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa, kuma ku nemi tsari zuwa gare shi, kuma ku yi jihãdi1 a cikin hanyarsa, tsammãninku, za ku ci nasara.
Bayanai
[1] Wasĩla ita ce dukkan aikin ibãda wanda zai kusantar da mutum zuwa ga Ubangijinsa, amma da sharaɗin an gina shi a kan taƙawa. Kuma taƙawa ita ce bin Allah kamar yadda Ya yi umurni a bi Shi, ta hanyar manzon Sa kawai. Jihãdi yana cikin taƙawa amma Yã kõma ambatonsa ne domin muhimmancinsa. Shi kuma iri biyu ne: ƙararmi, watau yãƙin abokan gãbã na bayyane, da babba, shi ne yãƙin abokan gãbã na ɓoye, watau rai da shaiɗan. Wanda maƙiyinsa na bayyane ya kashe shi yã mutu shahĩdi, wanda maƙiyinsa na ɓoye ya kashe shĩ ya mutu fãsiƙi ko kãfiri watau shaƙiyyi. -
إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ لَوْ أَنَّ لَهُم مَّا فِى ٱلْأَرْضِ جَمِيعًا وَمِثْلَهُۥ مَعَهُۥ لِيَفْتَدُوا۟ بِهِۦ مِنْ عَذَابِ يَوْمِ ٱلْقِيَـٰمَةِ مَا تُقُبِّلَ مِنْهُمْ ۖ وَلَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ٣٦
Inna allatheena kafaroo law anna lahum ma fee alardi jameeʿan wamithlahu maʿahu liyaftadoo bihi min ʿathabi yawmi alqiyamati ma tuqubbila minhum walahum ʿathabun aleemun
Lalle ne waɗanda suka kãfirta, lalle dã sunã da abin da ke a cikin ƙasa gabã ɗaya da misãlinsa tãre da shi, dõmin su yi fansa da shi daga azãbar Rãnar ¡iyãma, bã a karɓarsa daga gare su, kuma sunã da azãba mai raɗadi.
-
يُرِيدُونَ أَن يَخْرُجُوا۟ مِنَ ٱلنَّارِ وَمَا هُم بِخَـٰرِجِينَ مِنْهَا ۖ وَلَهُمْ عَذَابٌ مُّقِيمٌ٣٧
Yureedoona an yakhrujoo mina alnnari wama hum bikharijeena minha walahum ʿathabun muqeemun
Sunã nufin su fita ne daga wuta, kuma ba su zama mãsu fita daga gare ta ba, kuma sunã da azãba zaunanniya.
-
وَٱلسَّارِقُ وَٱلسَّارِقَةُ فَٱقْطَعُوٓا۟ أَيْدِيَهُمَا جَزَآءًۢ بِمَا كَسَبَا نَكَـٰلًا مِّنَ ٱللَّهِ ۗ وَٱللَّهُ عَزِيزٌ حَكِيمٌ٣٨
Waalssariqu waalssariqatu faiqtaʿoo aydiyahuma jazaan bima kasaba nakalan mina Allahi waAllahu ʿazeezun hakeemun
Kuma ɓarãwo da ɓarauniya sai ku yanke hannuwansu, bisa sakamako ga abin da suka tsirfanta, a kan azãba daga Allah. Kuma Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima.
-
فَمَن تَابَ مِنۢ بَعْدِ ظُلْمِهِۦ وَأَصْلَحَ فَإِنَّ ٱللَّهَ يَتُوبُ عَلَيْهِ ۗ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ٣٩
Faman taba min baʿdi thulmihi waaslaha fainna Allaha yatoobu ʿalayhi inna Allaha ghafoorun raheemun
To, wanda ya tuba a bãyan zãluncinsa, kuma ya gyãra (halinsa), to, lalle ne Allah Yanã karɓar tubarsa. Lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
-
أَلَمْ تَعْلَمْ أَنَّ ٱللَّهَ لَهُۥ مُلْكُ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ يُعَذِّبُ مَن يَشَآءُ وَيَغْفِرُ لِمَن يَشَآءُ ۗ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍ قَدِيرٌ٤٠
Alam taʿlam anna Allaha lahu mulku alssamawati waalardi yuʿaththibu man yashao wayaghfiru liman yashao waAllahu ʿala kulli shayin qadeerun
Shin, ba ka sani ba cewa lalle ne, Allah Shi ne da mulkin sammai da ƙasa, Yanã azãbtar da wanda Yake so, kuma Yanã yin gãfara ga wanda yake so, kuma Allah a dukkan kõme, Mai ĩkon yi ne?
-
۞ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلرَّسُولُ لَا يَحْزُنكَ ٱلَّذِينَ يُسَـٰرِعُونَ فِى ٱلْكُفْرِ مِنَ ٱلَّذِينَ قَالُوٓا۟ ءَامَنَّا بِأَفْوَٰهِهِمْ وَلَمْ تُؤْمِن قُلُوبُهُمْ ۛ وَمِنَ ٱلَّذِينَ هَادُوا۟ ۛ سَمَّـٰعُونَ لِلْكَذِبِ سَمَّـٰعُونَ لِقَوْمٍ ءَاخَرِينَ لَمْ يَأْتُوكَ ۖ يُحَرِّفُونَ ٱلْكَلِمَ مِنۢ بَعْدِ مَوَاضِعِهِۦ ۖ يَقُولُونَ إِنْ أُوتِيتُمْ هَـٰذَا فَخُذُوهُ وَإِن لَّمْ تُؤْتَوْهُ فَٱحْذَرُوا۟ ۚ وَمَن يُرِدِ ٱللَّهُ فِتْنَتَهُۥ فَلَن تَمْلِكَ لَهُۥ مِنَ ٱللَّهِ شَيْـًٔا ۚ أُو۟لَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ لَمْ يُرِدِ ٱللَّهُ أَن يُطَهِّرَ قُلُوبَهُمْ ۚ لَهُمْ فِى ٱلدُّنْيَا خِزْىٌ ۖ وَلَهُمْ فِى ٱلْـَٔاخِرَةِ عَذَابٌ عَظِيمٌ٤١
Ya ayyuha alrrasoolu la yahzunka allatheena yusariʿoona fee alkufri mina allatheena qaloo amanna biafwahihim walam tumin quloobuhum wamina allatheena hadoo sammaʿoona lilkathibi sammaʿoona liqawmin akhareena lam yatooka yuharrifoona alkalima min baʿdi mawadiʿihi yaqooloona in ooteetum hatha fakhuthoohu wain lam tutawhu faihtharoo waman yuridi Allahu fitnatahu falan tamlika lahu mina Allahi shayan olaika allatheena lam yuridi Allahu an yutahhira quloobahum lahum fee alddunya khizyun walahum fee alakhirati ʿathabun ʿatheemun
Yã kai Manzo! Kada waɗanda suke tseren gaugawa a cikin kãfirci su ɓãta maka rai, daga waɗanda suka ce: "Mun yi ĩmãni" da bãkunansu, alhãli zukatansu ba su yi ĩmãnin ba, kuma daga waɗanda suka tuba (watau Yahudu) mãsu yawan saurare ga wasu mutane na dabam waɗanda ba su je maka ba, sunã karkatar da zance daga bãyan wurarensa, sunã cewa: "Idan an bã ku wannan, to, ku karɓa, kuma idan ba a bã ku shĩ ba, to, ku yi sauna."Kuma wanda Allah Ya yi nufin fitinarsa, to bã zã ka mallaka masa kõme ba, daga Allah. Waɗannan ne waɗanda Allah bai yi nufin Ya tsarkake zukãtansu ba. Sunã da kunya a cikin duniya, kuma sunã da wata azãba mai girma a cikin ãhira.
-
سَمَّـٰعُونَ لِلْكَذِبِ أَكَّـٰلُونَ لِلسُّحْتِ ۚ فَإِن جَآءُوكَ فَٱحْكُم بَيْنَهُمْ أَوْ أَعْرِضْ عَنْهُمْ ۖ وَإِن تُعْرِضْ عَنْهُمْ فَلَن يَضُرُّوكَ شَيْـًٔا ۖ وَإِنْ حَكَمْتَ فَٱحْكُم بَيْنَهُم بِٱلْقِسْطِ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلْمُقْسِطِينَ٤٢
Sammaʿoona lilkathibi akkaloona lilssuhti fain jaooka faohkum baynahum aw aʿrid ʿanhum wain tuʿrid ʿanhum falan yadurrooka shayan wain hakamta faohkum baynahum bialqisti inna Allaha yuhibbu almuqsiteena
Mãsu yawan saurãre1 ga ƙarya ne, mãsu yawan ci ga haram, to, idan sun zo maka, sai ka yi hukunci a tsakãninsu kõ ka bijira daga gare su. Kuma idan ka bijira daga gare su, to, bã zã su cuce ka da kõme ba, kuma idan ka yi hukunci, to, sai ka hukunta a tsakãninsu da ãdalci. Lalle ne, Allah Yanã son mãsu ãdalci.
Bayanai
[1] An bai wa Annabi zaɓi da ya yi hukunci ko kada ya yi, a tsakãnin kafirai biyu idan sun yarda da hukuncinsa. Wannan dãmã tana aiki a kotunan Musulmi ga abin da ya shafi haƙƙoƙi kawai, amma ga 'jara'im a ƙasar Musulmi tilas sai a bi shari'ar Musulunci domin tsaron aminci, sai dai kafiri yana iya shan giyarsa, ga misãli a ɓoye banda a cikin jama'a. Haka kuma laifuka na al'adunsu kuma Musulmi bã za su taɓa masu su ba, sai su yi hukuncinsu a tsakãninsu. -
وَكَيْفَ يُحَكِّمُونَكَ وَعِندَهُمُ ٱلتَّوْرَىٰةُ فِيهَا حُكْمُ ٱللَّهِ ثُمَّ يَتَوَلَّوْنَ مِنۢ بَعْدِ ذَٰلِكَ ۚ وَمَآ أُو۟لَـٰٓئِكَ بِٱلْمُؤْمِنِينَ٤٣
Wakayfa yuhakkimoonaka waʿindahumu alttawratu feeha hukmu Allahi thumma yatawallawna min baʿdi thalika wama olaika bialmumineena
Kuma yãya suke gabãtar da kai ga hukunci, alhãli a wurinsu akwai Attaura, a cikinta akwai hukuncin Allah, sa'an nan kuma sunã karkacewa a bãyan wannan? waɗannan bã muminai ba ne!
-
إِنَّآ أَنزَلْنَا ٱلتَّوْرَىٰةَ فِيهَا هُدًى وَنُورٌ ۚ يَحْكُمُ بِهَا ٱلنَّبِيُّونَ ٱلَّذِينَ أَسْلَمُوا۟ لِلَّذِينَ هَادُوا۟ وَٱلرَّبَّـٰنِيُّونَ وَٱلْأَحْبَارُ بِمَا ٱسْتُحْفِظُوا۟ مِن كِتَـٰبِ ٱللَّهِ وَكَانُوا۟ عَلَيْهِ شُهَدَآءَ ۚ فَلَا تَخْشَوُا۟ ٱلنَّاسَ وَٱخْشَوْنِ وَلَا تَشْتَرُوا۟ بِـَٔايَـٰتِى ثَمَنًا قَلِيلًا ۚ وَمَن لَّمْ يَحْكُم بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ فَأُو۟لَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلْكَـٰفِرُونَ٤٤
Inna anzalna alttawrata feeha hudan wanoorun yahkumu biha alnnabiyyoona allatheena aslamoo lillatheena hadoo waalrrabbaniyyoona waalahbaru bima istuhfithoo min kitabi Allahi wakanoo ʿalayhi shuhadaa fala takhshawoo alnnasa waikhshawni wala tashtaroo biayatee thamanan qaleelan waman lam yahkum bima anzala Allahu faolaika humu alkafiroona
Lalle ne Mu, Mun saukar da Attaura, a cikinta akwai shiriya da haske Annabãwa waɗanda suke sun sallamã, sunã yin hukunci da ita ga waɗanda suka tuba (Yahudu), da mãlaman tarbiyya, da manyan malamai ga abin da aka neme su da su tsare daga Littãfin Allah, kuma sun kasance, a kansa, mãsu bã da shaida. To, kada ku ji tsõron mutãne kuma ku ji tsõroNa kuma kada ku sayi 'yan kuɗi kaɗan da ãyoyi Na. wanda bai yi hukunci ba da abin da Allah Ya saukar, to, waɗannan su ne kafirai.
-
وَكَتَبْنَا عَلَيْهِمْ فِيهَآ أَنَّ ٱلنَّفْسَ بِٱلنَّفْسِ وَٱلْعَيْنَ بِٱلْعَيْنِ وَٱلْأَنفَ بِٱلْأَنفِ وَٱلْأُذُنَ بِٱلْأُذُنِ وَٱلسِّنَّ بِٱلسِّنِّ وَٱلْجُرُوحَ قِصَاصٌ ۚ فَمَن تَصَدَّقَ بِهِۦ فَهُوَ كَفَّارَةٌ لَّهُۥ ۚ وَمَن لَّمْ يَحْكُم بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ فَأُو۟لَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلظَّـٰلِمُونَ٤٥
Wakatabna ʿalayhim feeha anna alnnafsa bialnnafsi waalʿayna bialʿayni waalanfa bialanfi waalothuna bialothuni waalssinna bialssinni waaljurooha qisasun faman tasaddaqa bihi fahuwa kaffaratun lahu waman lam yahkum bima anzala Allahu faolaika humu alththalimoona
Kuma Mun rubuta a kansu, a cikinta cewa, lalle (anã kashe) rai sabõda rai, kuma (anã ɗebe) idõ sabõda idõ, kuma (ana katse) hanci sabõda hanci, kuma kunne sabõda kunne kuma haƙori sabõda haƙõri kuma a raunuka a yi sakayya. To, wanda ya yi sadaka da shi, to, shi kaffãra ce a gare shi. Kuma wanda bai yi hukunci ba da abin da Allah Ya saukar, to, waɗannan su ne azzãlumai.
-
وَقَفَّيْنَا عَلَىٰٓ ءَاثَـٰرِهِم بِعِيسَى ٱبْنِ مَرْيَمَ مُصَدِّقًا لِّمَا بَيْنَ يَدَيْهِ مِنَ ٱلتَّوْرَىٰةِ ۖ وَءَاتَيْنَـٰهُ ٱلْإِنجِيلَ فِيهِ هُدًى وَنُورٌ وَمُصَدِّقًا لِّمَا بَيْنَ يَدَيْهِ مِنَ ٱلتَّوْرَىٰةِ وَهُدًى وَمَوْعِظَةً لِّلْمُتَّقِينَ٤٦
Waqaffayna ʿala atharihim biʿeesa ibni maryama musaddiqan lima bayna yadayhi mina alttawrati waataynahu alinjeela feehi hudan wanoorun wamusaddiqan lima bayna yadayhi mina alttawrati wahudan wamawʿithatan lilmuttaqeena
Kuma Muka biyar a kan gurãbansu da Ĩsa ɗan Maryama, yãnã mai gaskatãwa ga abin da yake a gaba gare shi daga Attaura, kuma Muka bã shi Injĩla a cikinsa akwai shiriya da haske, yanã mai gaskatãwa ga abin da yake a gaba gare shi daga Attaura, kuma shi shiriya ne da wa'azi ga mãsu taƙawa.
-
وَلْيَحْكُمْ أَهْلُ ٱلْإِنجِيلِ بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ فِيهِ ۚ وَمَن لَّمْ يَحْكُم بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ فَأُو۟لَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلْفَـٰسِقُونَ٤٧
Walyahkum ahlu alinjeeli bima anzala Allahu feehi waman lam yahkum bima anzala Allahu faolaika humu alfasiqoona
Kuma sai mutãnen injĩla su yi hukunci da abin da Allah ya saukar a cikinta. Kuma wanda bai yi hukunci ba da abin da Allah ya saukar, to, waɗannan su ne fãsiƙai.
-
وَأَنزَلْنَآ إِلَيْكَ ٱلْكِتَـٰبَ بِٱلْحَقِّ مُصَدِّقًا لِّمَا بَيْنَ يَدَيْهِ مِنَ ٱلْكِتَـٰبِ وَمُهَيْمِنًا عَلَيْهِ ۖ فَٱحْكُم بَيْنَهُم بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ ۖ وَلَا تَتَّبِعْ أَهْوَآءَهُمْ عَمَّا جَآءَكَ مِنَ ٱلْحَقِّ ۚ لِكُلٍّ جَعَلْنَا مِنكُمْ شِرْعَةً وَمِنْهَاجًا ۚ وَلَوْ شَآءَ ٱللَّهُ لَجَعَلَكُمْ أُمَّةً وَٰحِدَةً وَلَـٰكِن لِّيَبْلُوَكُمْ فِى مَآ ءَاتَىٰكُمْ ۖ فَٱسْتَبِقُوا۟ ٱلْخَيْرَٰتِ ۚ إِلَى ٱللَّهِ مَرْجِعُكُمْ جَمِيعًا فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمْ فِيهِ تَخْتَلِفُونَ٤٨
Waanzalna ilayka alkitaba bialhaqqi musaddiqan lima bayna yadayhi mina alkitabi wamuhayminan ʿalayhi faohkum baynahum bima anzala Allahu wala tattabiʿ ahwaahum ʿamma jaaka mina alhaqqi likullin jaʿalna minkum shirʿatan waminhajan walaw shaa Allahu lajaʿalakum ommatan wahidatan walakin liyabluwakum fee ma atakum faistabiqoo alkhayrati ila Allahi marjiʿukum jameeʿan fayunabbiokum bima kuntum feehi takhtalifoona
Kuma Mun saukar da Littãfi zuwa gare ka da gaskiya, yanã mai gaskatãwa ga abin da yake a gaba gare shi daga Littãfi (Attaura da Injĩla), kuma mai halartãwa a kansa. sai ka yi hukunci a tsakãninsu da abin da Allah Ya saukar kuma kada ka bĩbiyi son zũciyõyinsu daga abin da ya zo maka daga gaskiya.1 Ga kõwanne daga gare ku Mun sanya sharĩa da hanya (ta bin ta). Kuma dã Allah Yã so, dã Yã sanya ku al'umma guda, kuma amma dõmin Ya jarraba ku a cikin abin da Ya bã ku. Sai ku yi tsere ga ayyukan alheri. Zuwa ga Allah makõmarku take gabã ɗaya. Sa'an nan Ya bã ku lãbãri ga abin da kuka kasance kunã sãɓãwa a cikinsa.
Bayanai
[1] Allah. Kuma Mun bai wa kowa shari'õ'insa da dõkõkinsa sa'an nan kuma da hanyar da ake bi wajen zartar da shari'ar. -
وَأَنِ ٱحْكُم بَيْنَهُم بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ وَلَا تَتَّبِعْ أَهْوَآءَهُمْ وَٱحْذَرْهُمْ أَن يَفْتِنُوكَ عَنۢ بَعْضِ مَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ إِلَيْكَ ۖ فَإِن تَوَلَّوْا۟ فَٱعْلَمْ أَنَّمَا يُرِيدُ ٱللَّهُ أَن يُصِيبَهُم بِبَعْضِ ذُنُوبِهِمْ ۗ وَإِنَّ كَثِيرًا مِّنَ ٱلنَّاسِ لَفَـٰسِقُونَ٤٩
Waani ohkum baynahum bima anzala Allahu wala tattabiʿ ahwaahum waihtharhum an yaftinooka ʿan baʿdi ma anzala Allahu ilayka fain tawallaw faiʿlam annama yureedu Allahu an yuseebahum bibaʿdi thunoobihim wainna katheeran mina alnnasi lafasiqoona
Kuma ka yi hukunci a tsakãninsu da abin da Allah Ya saukar kuma kada ka bĩbiyi son zũciyõyinsu, kuma ka yi saunar su fitine ka daga sãshen abin da Allah Ya saukar zuwa gare ka. To, idan sun juya bãya, to, ka sani cewa, kawai Allah yana nufin Ya sãme su da masĩfa ne sabõda sãshen zunubansu. Kuma lalle ne, mãsu yawa daga mutãne, haƙĩƙa, fãsiƙai ne.
-
أَفَحُكْمَ ٱلْجَـٰهِلِيَّةِ يَبْغُونَ ۚ وَمَنْ أَحْسَنُ مِنَ ٱللَّهِ حُكْمًا لِّقَوْمٍ يُوقِنُونَ٥٠
Afahukma aljahiliyyati yabghoona waman ahsanu mina Allahu hukman liqawmin yooqinoona
Shin, hukuncin Jãhiliyya1 suke nema? Kuma wane ne mafi kyau ga hukunci daga Allah sabõda mutãne waɗanda suke yin yaƙĩni (tabbataccen ĩmãni)?
Bayanai
[1] Hukuncin Jahiliyya shi ne wanda ake ginawa a kan son rai da al'ãda da kuma ra'ayin azzalumai, ba ya da wani asali daga wani littafi na Allah. -
۞ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ لَا تَتَّخِذُوا۟ ٱلْيَهُودَ وَٱلنَّصَـٰرَىٰٓ أَوْلِيَآءَ ۘ بَعْضُهُمْ أَوْلِيَآءُ بَعْضٍ ۚ وَمَن يَتَوَلَّهُم مِّنكُمْ فَإِنَّهُۥ مِنْهُمْ ۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهْدِى ٱلْقَوْمَ ٱلظَّـٰلِمِينَ٥١
Ya ayyuha allatheena amanoo la tattakhithoo alyahooda waalnnasara awliyaa baʿduhum awliyao baʿdin waman yatawallahum minkum fainnahu minhum inna Allaha la yahdee alqawma alththalimeena
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku riƙi Yahudu da Nasãra majiɓinta. Sãshensu majiɓinci ne ga sãshe. Kuma wanda ya jiɓince su daga gare ku, to, lalle ne shĩ, yanã daga gare su. Lalle Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai.
-
فَتَرَى ٱلَّذِينَ فِى قُلُوبِهِم مَّرَضٌ يُسَـٰرِعُونَ فِيهِمْ يَقُولُونَ نَخْشَىٰٓ أَن تُصِيبَنَا دَآئِرَةٌ ۚ فَعَسَى ٱللَّهُ أَن يَأْتِىَ بِٱلْفَتْحِ أَوْ أَمْرٍ مِّنْ عِندِهِۦ فَيُصْبِحُوا۟ عَلَىٰ مَآ أَسَرُّوا۟ فِىٓ أَنفُسِهِمْ نَـٰدِمِينَ٥٢
Fatara allatheena fee quloobihim maradun yusariʿoona feehim yaqooloona nakhsha an tuseebana dairatun faʿasa Allahu an yatiya bialfathi aw amrin min ʿindihi fayusbihoo ʿala ma asarroo fee anfusihim nadimeena
Sai ka ga waɗanda a cikin zukatansu akwai cuta, sunã tseren gaugawa a cikinsu, sunã cewa: "Munã tsõron kada wata masĩfa ta sãme mu." To, akwai tsammãnin Allah Ya zo da buɗi, kõ kuwa wani umurni daga wurin Sa, har su wãyi gari a kan abin da suka ɓõye a cikin zukatansu, sunã mãsu nadãmã.
-
وَيَقُولُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓا۟ أَهَـٰٓؤُلَآءِ ٱلَّذِينَ أَقْسَمُوا۟ بِٱللَّهِ جَهْدَ أَيْمَـٰنِهِمْ ۙ إِنَّهُمْ لَمَعَكُمْ ۚ حَبِطَتْ أَعْمَـٰلُهُمْ فَأَصْبَحُوا۟ خَـٰسِرِينَ٥٣
Wayaqoolu allatheena amanoo ahaolai allatheena aqsamoo biAllahi jahda aymanihim innahum lamaʿakum habitat aʿmaluhum faasbahoo khasireena
Kuma waɗanda suka yi ĩmãni sunã cewa: "Shin, waɗannan ne waɗanda suka yi rantsuwa da Allah iyãkar rantsuwõyinsu, cewa su, lalle sunã tãre da ku?" Ayyukansu sun ɓãci, sabõda haka suka wãyi gari sunã mãsu hasãra.
-
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ مَن يَرْتَدَّ مِنكُمْ عَن دِينِهِۦ فَسَوْفَ يَأْتِى ٱللَّهُ بِقَوْمٍ يُحِبُّهُمْ وَيُحِبُّونَهُۥٓ أَذِلَّةٍ عَلَى ٱلْمُؤْمِنِينَ أَعِزَّةٍ عَلَى ٱلْكَـٰفِرِينَ يُجَـٰهِدُونَ فِى سَبِيلِ ٱللَّهِ وَلَا يَخَافُونَ لَوْمَةَ لَآئِمٍ ۚ ذَٰلِكَ فَضْلُ ٱللَّهِ يُؤْتِيهِ مَن يَشَآءُ ۚ وَٱللَّهُ وَٰسِعٌ عَلِيمٌ٥٤
Ya ayyuha allatheena amanoo man yartadda minkum ʿan deenihi fasawfa yatee Allahu biqawmin yuhibbuhum wayuhibboonahu athillatin ʿala almumineena aʿizzatin ʿala alkafireena yujahidoona fee sabeeli Allahi wala yakhafoona lawmata laimin thalika fadlu Allahi yuteehi man yashao waAllahu wasiʿun ʿaleemun
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! wanda ya yi ridda daga gare ku daga addininSa, to, Allah zai zo da wasu mutãne, Yanã son su kuma sunã son Sa, mãsu tawãlu'i a kan muminai mãsu izza a kan kãfurai. Sunã yin, jihãdi a cikin hanyar Allah, kuma bã su tsõron zargin wani mai zargi. Waccan falalar Allah ce, Yanã bãyar da ita ga wanda Yake so. Kuma Allah Mayalwaci ne, Mai ilmi.
-
إِنَّمَا وَلِيُّكُمُ ٱللَّهُ وَرَسُولُهُۥ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ ٱلَّذِينَ يُقِيمُونَ ٱلصَّلَوٰةَ وَيُؤْتُونَ ٱلزَّكَوٰةَ وَهُمْ رَٰكِعُونَ٥٥
Innama waliyyukumu Allahu warasooluhu waallatheena amanoo allatheena yuqeemoona alssalata wayutoona alzzakata wahum rakiʿoona
Abin sani kawai, majiɓincinku Allah ne da Manzon Sa da waɗanda suka yi ĩmãni, waɗanda suke sunã tsayar da salla kuma sunã bãyar da zakka kuma sunã ruku'i,
-
وَمَن يَتَوَلَّ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ فَإِنَّ حِزْبَ ٱللَّهِ هُمُ ٱلْغَـٰلِبُونَ٥٦
Waman yatawalla Allaha warasoolahu waallatheena amanoo fainna hizba Allahi humu alghaliboona
Kuma wanda ya jiɓinci Allah da Manzon Sa da waɗanda suka yi ĩmãni, to, ƙungiyar Allah sune mãsu rinjãya.
-
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ لَا تَتَّخِذُوا۟ ٱلَّذِينَ ٱتَّخَذُوا۟ دِينَكُمْ هُزُوًا وَلَعِبًا مِّنَ ٱلَّذِينَ أُوتُوا۟ ٱلْكِتَـٰبَ مِن قَبْلِكُمْ وَٱلْكُفَّارَ أَوْلِيَآءَ ۚ وَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ٥٧
Ya ayyuha allatheena amanoo la tattakhithoo allatheena ittakhathoo deenakum huzuwan walaʿiban mina allatheena ootoo alkitaba min qablikum waalkuffara awliyaa waittaqoo Allaha in kuntum mumineena
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku riƙi waɗanda suka riƙi addininku bisa izgili da wãsa, daga waɗanda aka bai wa Littãfi daga gabãninku da kãfirai, masõya, Kuma ku bi Allah da taƙawa idan kun kasance muminai.
-
وَإِذَا نَادَيْتُمْ إِلَى ٱلصَّلَوٰةِ ٱتَّخَذُوهَا هُزُوًا وَلَعِبًا ۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمْ قَوْمٌ لَّا يَعْقِلُونَ٥٨
Waitha nadaytum ila alssalati ittakhathooha huzuwan walaʿiban thalika biannahum qawmun la yaʿqiloona
Kuma idan kuka yi kira zuwa ga salla, sai su riƙe ta bisa izgili da wãsa. Wannan dõmin lalle ne su, mutãne ne (waɗanda) bã su hankalta.
-
قُلْ يَـٰٓأَهْلَ ٱلْكِتَـٰبِ هَلْ تَنقِمُونَ مِنَّآ إِلَّآ أَنْ ءَامَنَّا بِٱللَّهِ وَمَآ أُنزِلَ إِلَيْنَا وَمَآ أُنزِلَ مِن قَبْلُ وَأَنَّ أَكْثَرَكُمْ فَـٰسِقُونَ٥٩
Qul ya ahla alkitabi hal tanqimoona minna illa an amanna biAllahi wama onzila ilayna wama onzila min qablu waanna aktharakum fasiqoona
Ka ce: "Ya Mutãnen Littãfi! Shin, kunã ganin wani laifi daga gare mu? Fãce dai dõmin mun yi ĩmãni da Allah da abin da aka Saukar zuwa gare mu da abin da aka saukar daga gabãni, kuma dõmin mafi yawanku fãsiƙai ne."
-
قُلْ هَلْ أُنَبِّئُكُم بِشَرٍّ مِّن ذَٰلِكَ مَثُوبَةً عِندَ ٱللَّهِ ۚ مَن لَّعَنَهُ ٱللَّهُ وَغَضِبَ عَلَيْهِ وَجَعَلَ مِنْهُمُ ٱلْقِرَدَةَ وَٱلْخَنَازِيرَ وَعَبَدَ ٱلطَّـٰغُوتَ ۚ أُو۟لَـٰٓئِكَ شَرٌّ مَّكَانًا وَأَضَلُّ عَن سَوَآءِ ٱلسَّبِيلِ٦٠
Qul hal onabbiokum bisharrin min thalika mathoobatan ʿinda Allahi man laʿanahu Allahu waghadiba ʿalayhi wajaʿala minhumu alqiradata waalkhanazeera waʿabada alttaghooti olaika sharrun makanan waadallu ʿan sawai alssabeeli
Ka ce: "Shin, in gaya muku mafi sharri daga wannan, dõmin sakamako1 daga wurin Allah? wanda Allah Ya la'ane shi kuma Ya yi fushi da shi, kuma Ya sanya daga gare su birai da aladai, kuma ya bauta wa ¦ãguta. Waɗannan ne mafiya sharrin wuri, kuma mafiya ɓata daga tsakar hanya."
Bayanai
[1] Kunã son in gaya muku ba dõmin ku bã ni wani sakamako ba, sai dõmin Allah Ya sãkã mini. Mutãnen da aka jũyar suka kõma birai da aladai kuma suka bauta wa wanin Allah, su ne mafi sharrin mutãne. -
وَإِذَا جَآءُوكُمْ قَالُوٓا۟ ءَامَنَّا وَقَد دَّخَلُوا۟ بِٱلْكُفْرِ وَهُمْ قَدْ خَرَجُوا۟ بِهِۦ ۚ وَٱللَّهُ أَعْلَمُ بِمَا كَانُوا۟ يَكْتُمُونَ٦١
Waitha jaookum qaloo amanna waqad dakhaloo bialkufri wahum qad kharajoo bihi waAllahu aʿlamu bima kanoo yaktumoona
Kuma idan sun zo muku sai su ce: "Mun yi ĩmãni." Alhãli kuwa haƙĩƙa, sun shigo da kãfirci, kuma su lalle ne, sun fita da shi, kuma Allah ne Mafi sani ga abin da suka kasance sunã ɓõyewa.
-
وَتَرَىٰ كَثِيرًا مِّنْهُمْ يُسَـٰرِعُونَ فِى ٱلْإِثْمِ وَٱلْعُدْوَٰنِ وَأَكْلِهِمُ ٱلسُّحْتَ ۚ لَبِئْسَ مَا كَانُوا۟ يَعْمَلُونَ٦٢
Watara katheeran minhum yusariʿoona fee alithmi waalʿudwani waaklihimu alssuhta labisa ma kanoo yaʿmaloona
Kuma kana ganin mãsu yawa daga gare su, sunã tseren gaugawa a cikin zunubi da zãlunci da cinsu ga haram. Haƙĩƙa, tir da abin da suka kasance suna aikatãwa.
-
لَوْلَا يَنْهَىٰهُمُ ٱلرَّبَّـٰنِيُّونَ وَٱلْأَحْبَارُ عَن قَوْلِهِمُ ٱلْإِثْمَ وَأَكْلِهِمُ ٱلسُّحْتَ ۚ لَبِئْسَ مَا كَانُوا۟ يَصْنَعُونَ٦٣
Lawla yanhahumu alrrabbaniyyoona waalahbaru ʿan qawlihimu alithma waaklihimu alssuhta labisa ma kanoo yasnaʿoona
Don me Malaman Tarbiyya1 da manyan malamai (na Yahudu) ba su hanã su daga faɗarsu ga zunubi da cinsu ga haram ba? Haƙiƙa, tir daga abin da suka kasance sunã sanã'antãwa.
Bayanai
[1] Don me malamansu bã su yin wa'azi ga jãhilansu? Tir da rashin wa'azi!. -
وَقَالَتِ ٱلْيَهُودُ يَدُ ٱللَّهِ مَغْلُولَةٌ ۚ غُلَّتْ أَيْدِيهِمْ وَلُعِنُوا۟ بِمَا قَالُوا۟ ۘ بَلْ يَدَاهُ مَبْسُوطَتَانِ يُنفِقُ كَيْفَ يَشَآءُ ۚ وَلَيَزِيدَنَّ كَثِيرًا مِّنْهُم مَّآ أُنزِلَ إِلَيْكَ مِن رَّبِّكَ طُغْيَـٰنًا وَكُفْرًا ۚ وَأَلْقَيْنَا بَيْنَهُمُ ٱلْعَدَٰوَةَ وَٱلْبَغْضَآءَ إِلَىٰ يَوْمِ ٱلْقِيَـٰمَةِ ۚ كُلَّمَآ أَوْقَدُوا۟ نَارًا لِّلْحَرْبِ أَطْفَأَهَا ٱللَّهُ ۚ وَيَسْعَوْنَ فِى ٱلْأَرْضِ فَسَادًا ۚ وَٱللَّهُ لَا يُحِبُّ ٱلْمُفْسِدِينَ٦٤
Waqalati alyahoodu yadu Allahi maghloolatun ghullat aydeehim waluʿinoo bima qaloo bal yadahu mabsootatani yunfiqu kayfa yashao walayazeedanna katheeran minhum ma onzila ilayka min rabbika tughyanan wakufran waalqayna baynahumu alʿadawata waalbaghdaa ila yawmi alqiyamati kullama awqadoo naran lilharbi atfaaha Allahu wayasʿawna fee alardi fasadan waAllahu la yuhibbu almufsideena
Kuma Yahudu suka ce: "Hannun Allah abin yi wa ƙuƙumi ne.1 " An sanya hannuwansu a cikin ƙuƙumi! Kuma an la'ane su sabõda abin da suka faɗa. Ã'a, hannuwanSa biyu shimfiɗaɗɗu ne, Yanã ciyarwa yadda Yake so. Kuma lalle ne abin da aka saukar zuwa gare ka yanã ƙãra wa mãsu yawa daga gare su, girman kai da kãfirci. Kuma Mun jefa a tsakãninsu, ƙiyayya da ƙeta, zuwa Rãnar ¡iyãma, kõ da yaushe suka hura wata wuta dõmin yãƙi, sai Allah Ya bice ta. Sunã aiki a cikin ƙasa dõmin ɓarna, alhãli kuwa Allah bã Ya son mãsu fasãdi.
Bayanai
[1] Suna nufin wai Allah marowaci ne. -
وَلَوْ أَنَّ أَهْلَ ٱلْكِتَـٰبِ ءَامَنُوا۟ وَٱتَّقَوْا۟ لَكَفَّرْنَا عَنْهُمْ سَيِّـَٔاتِهِمْ وَلَأَدْخَلْنَـٰهُمْ جَنَّـٰتِ ٱلنَّعِيمِ٦٥
Walaw anna ahla alkitabi amanoo waittaqaw lakaffarna ʿanhum sayyiatihim walaadkhalnahum jannati alnnaʿeemi
Kuma dã dai lalle Mutãnen Littãfi sun yi ĩmãni, kuma sun yi taƙawa, haƙĩƙa, dã Mun kankare miyãgun ayyukansu daga gare su, kuma dã Mun shigar da su gidãjen Aljannar Ni'ima.
-
وَلَوْ أَنَّهُمْ أَقَامُوا۟ ٱلتَّوْرَىٰةَ وَٱلْإِنجِيلَ وَمَآ أُنزِلَ إِلَيْهِم مِّن رَّبِّهِمْ لَأَكَلُوا۟ مِن فَوْقِهِمْ وَمِن تَحْتِ أَرْجُلِهِم ۚ مِّنْهُمْ أُمَّةٌ مُّقْتَصِدَةٌ ۖ وَكَثِيرٌ مِّنْهُمْ سَآءَ مَا يَعْمَلُونَ٦٦
Walaw annahum aqamoo alttawrata waalinjeela wama onzila ilayhim min rabbihim laakaloo min fawqihim wamin tahti arjulihim minhum ommatun muqtasidatun wakatheerun minhum saa ma yaʿmaloona
Kuma dã dai lalle su, sun tsayar da Attaura da Injĩla da abin da aka saukar zuwa gare su daga Ubangijinsu, haƙĩƙa, dã sun ci daga bisansu da kuma daga ƙarƙashin ƙafãfunsu. Daga gare su akwai wata al'umma mai tsakaitãwa kuma mãsu yawa daga gare su, abin da suke aikatawa yã munana.
-
۞ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلرَّسُولُ بَلِّغْ مَآ أُنزِلَ إِلَيْكَ مِن رَّبِّكَ ۖ وَإِن لَّمْ تَفْعَلْ فَمَا بَلَّغْتَ رِسَالَتَهُۥ ۚ وَٱللَّهُ يَعْصِمُكَ مِنَ ٱلنَّاسِ ۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهْدِى ٱلْقَوْمَ ٱلْكَـٰفِرِينَ٦٧
Ya ayyuha alrrasoolu balligh ma onzila ilayka min rabbika wain lam tafʿal fama ballaghta risalatahu waAllahu yaʿsimuka mina alnnasi inna Allaha la yahdee alqawma alkafireena
Yã kai Manzo! Ka iyar da1 abin da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka. Kuma idan ba ka aikata ba, to, ba ka iyar da manzancin Sa ba ke nan. Kuma Allah Yanã tsare ka daga mutãne. Lalle ne, Allah bã Ya shiryar da mutãne kãfirai.
Bayanai
[1] Wannan ãya tã kãfirta dukan wanda ya ce kõ yã yarda da cewa Annabi yã ɓõye wani abu daga Allah, ko kuma yã keɓe wasu mutãne da wani abu daga manzancinsa daga Allah. -
قُلْ يَـٰٓأَهْلَ ٱلْكِتَـٰبِ لَسْتُمْ عَلَىٰ شَىْءٍ حَتَّىٰ تُقِيمُوا۟ ٱلتَّوْرَىٰةَ وَٱلْإِنجِيلَ وَمَآ أُنزِلَ إِلَيْكُم مِّن رَّبِّكُمْ ۗ وَلَيَزِيدَنَّ كَثِيرًا مِّنْهُم مَّآ أُنزِلَ إِلَيْكَ مِن رَّبِّكَ طُغْيَـٰنًا وَكُفْرًا ۖ فَلَا تَأْسَ عَلَى ٱلْقَوْمِ ٱلْكَـٰفِرِينَ٦٨
Qul ya ahla alkitabi lastum ʿala shayin hatta tuqeemoo alttawrata waalinjeela wama onzila ilaykum min rabbikum walayazeedanna katheeran minhum ma onzila ilayka min rabbika tughyanan wakufran fala tasa ʿala alqawmi alkafireena
Ka ce: "Yã ku Mutãnen Littãfi! Ba ku zama a kan kõme ba, sai kun tsayar da Attaura da Injĩla da abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku."Kuma lalle ne, abin da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka, yanã ƙara wa mãsu yawa daga gare su girman kai da kãfirci. To, kada ka yi baƙin ciki a kan mutãne kãfirai.
-
إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَٱلَّذِينَ هَادُوا۟ وَٱلصَّـٰبِـُٔونَ وَٱلنَّصَـٰرَىٰ مَنْ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَٱلْيَوْمِ ٱلْـَٔاخِرِ وَعَمِلَ صَـٰلِحًا فَلَا خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلَا هُمْ يَحْزَنُونَ٦٩
Inna allatheena amanoo waallatheena hadoo waalssabioona waalnnasara man amana biAllahi waalyawmi alakhiri waʿamila salihan fala khawfun ʿalayhim wala hum yahzanoona
Lalle ne, waɗanda suka yi ĩmãni da waɗanda sukatuba (Yahũdu) da Karkatattu da Nasãra, wanda ya yi ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira, kuma ya aikata aiki na ƙwarai, to, bãbu tsõro a kansu, kuma bã su zamo sunã baƙin ciki ba.
-
لَقَدْ أَخَذْنَا مِيثَـٰقَ بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ وَأَرْسَلْنَآ إِلَيْهِمْ رُسُلًا ۖ كُلَّمَا جَآءَهُمْ رَسُولٌۢ بِمَا لَا تَهْوَىٰٓ أَنفُسُهُمْ فَرِيقًا كَذَّبُوا۟ وَفَرِيقًا يَقْتُلُونَ٧٠
Laqad akhathna meethaqa banee israeela waarsalna ilayhim rusulan kullama jaahum rasoolun bima la tahwa anfusuhum fareeqan kaththaboo wafareeqan yaqtuloona
Lalle ne haƙĩƙa Mun riƙi alkawarin Bani Isrã'ĩla, kuma Mun aiki manzanni zuwa gare su, ko da yaushe wani manzo ya je musu da abin da rãyukansu bã su so, wani ɓangare sun ƙaryata, kuma wani ɓangare sunã kashewa,
-
وَحَسِبُوٓا۟ أَلَّا تَكُونَ فِتْنَةٌ فَعَمُوا۟ وَصَمُّوا۟ ثُمَّ تَابَ ٱللَّهُ عَلَيْهِمْ ثُمَّ عَمُوا۟ وَصَمُّوا۟ كَثِيرٌ مِّنْهُمْ ۚ وَٱللَّهُ بَصِيرٌۢ بِمَا يَعْمَلُونَ٧١
Wahasiboo alla takoona fitnatun faʿamoo wasammoo thumma taba Allahu ʿalayhim thumma ʿamoo wasammoo katheerun minhum waAllahu baseerun bima yaʿmaloona
Kuma suka yi zaton cewa wata fitina bã zã ta kasance ba sai Suka makanta, kuma suka kurubta, sa'an nan Allah Ya karɓi tuba a gare su, sa'an nan suka makanta kuma suka kurunta mãsu yawa daga gare su, alhãli Allah Mai gani ne ga abin da suke aikatãwa.
-
لَقَدْ كَفَرَ ٱلَّذِينَ قَالُوٓا۟ إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلْمَسِيحُ ٱبْنُ مَرْيَمَ ۖ وَقَالَ ٱلْمَسِيحُ يَـٰبَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ ٱعْبُدُوا۟ ٱللَّهَ رَبِّى وَرَبَّكُمْ ۖ إِنَّهُۥ مَن يُشْرِكْ بِٱللَّهِ فَقَدْ حَرَّمَ ٱللَّهُ عَلَيْهِ ٱلْجَنَّةَ وَمَأْوَىٰهُ ٱلنَّارُ ۖ وَمَا لِلظَّـٰلِمِينَ مِنْ أَنصَارٍ٧٢
Laqad kafara allatheena qaloo inna Allaha huwa almaseehu ibnu maryama waqala almaseehu ya banee israeela oʿbudoo Allaha rabbee warabbakum innahu man yushrik biAllahi faqad harrama Allahu ʿalayhi aljannata wamawahu alnnaru wama lilththalimeena min ansarin
Lalle ne haƙĩƙa waɗanda1 suka ce: "Lalle ne Allah, shĩne Masĩhu, ɗan Maryama," sun kãfirta. Alhãli kuwa Masĩhu yã ce: "Yã Banĩ Isrã'ĩla! Ku bauta wa Allah Ubangijina, kuma Ubangijinku." Lalle ne shĩ, wanda ya yi shirki da Allah, to, lalle ne, Allah Yã haramta masa Aljanna. Kuma bãbu wasu mataimaka ga azzãlumai.
Bayanai
[1] Su ne Ya'aƙũbiyya, Bãyan bayãni a kan aibõbin Yahũdu sai Ya shiga bayãni a kan aibõbin Nasãra. -
لَّقَدْ كَفَرَ ٱلَّذِينَ قَالُوٓا۟ إِنَّ ٱللَّهَ ثَالِثُ ثَلَـٰثَةٍ ۘ وَمَا مِنْ إِلَـٰهٍ إِلَّآ إِلَـٰهٌ وَٰحِدٌ ۚ وَإِن لَّمْ يَنتَهُوا۟ عَمَّا يَقُولُونَ لَيَمَسَّنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ مِنْهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ٧٣
Laqad kafara allatheena qaloo inna Allaha thalithu thalathatin wama min ilahin illa ilahun wahidun wain lam yantahoo ʿamma yaqooloona layamassanna allatheena kafaroo minhum ʿathabun aleemun
Lalle ne, haƙĩƙa, waɗanda suka ce: "Allah na ukun uku ne," sun kãfirta, kuma babu wani abin bautãwa fãce Ubangiji Guda. Kuma idan ba su hanu daga abin da suke faɗa ba, haƙĩƙa, wata azãba mai raɗaɗi tãnã shãfar waɗanda suka kãfirta daga gare su.
-
أَفَلَا يَتُوبُونَ إِلَى ٱللَّهِ وَيَسْتَغْفِرُونَهُۥ ۚ وَٱللَّهُ غَفُورٌ رَّحِيمٌ٧٤
Afala yatooboona ila Allahi wayastaghfiroonahu waAllahu ghafoorun raheemun
shin fã, bã su tuba zuwa ga Allah, kuma su neme Shi gãfara, alhãli kuwa Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai?
-
مَّا ٱلْمَسِيحُ ٱبْنُ مَرْيَمَ إِلَّا رَسُولٌ قَدْ خَلَتْ مِن قَبْلِهِ ٱلرُّسُلُ وَأُمُّهُۥ صِدِّيقَةٌ ۖ كَانَا يَأْكُلَانِ ٱلطَّعَامَ ۗ ٱنظُرْ كَيْفَ نُبَيِّنُ لَهُمُ ٱلْـَٔايَـٰتِ ثُمَّ ٱنظُرْ أَنَّىٰ يُؤْفَكُونَ٧٥
Ma almaseehu ibnu maryama illa rasoolun qad khalat min qablihi alrrusulu waommuhu siddeeqatun kana yakulani alttaʿama onthur kayfa nubayyinu lahumu alayati thumma onthur anna yufakoona
Masĩhu ɗan Maryama bai zama ba fãce Manzo ne kawai, haƙĩƙa, manzanni sun shige dage gabãninsa, kuma uwarsa siddika1 ce. Sun kasance sunã cin abinci. Ka duba yadda Muke bayyana musu ãyõyi. Sa'an nan kuma ka duba yadda ake karkatar da su.
Bayanai
[1] Siddĩƙ shi ne mai yawan gaskatãwar Annabãwa, shi ne mafi ɗaukakar daraja a waliyyan Allah, kamar Abubakar siddĩƙ Sahãbin Annabi. -
قُلْ أَتَعْبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَمْلِكُ لَكُمْ ضَرًّا وَلَا نَفْعًا ۚ وَٱللَّهُ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلْعَلِيمُ٧٦
Qul ataʿbudoona min dooni Allahi ma la yamliku lakum darran wala nafʿan waAllahu huwa alssameeʿu alʿaleemu
Ka ce: "Ashe kunã bauta wa, baicin Allah, abin da ba ya mallakar wata cuta sabõda ku kuma haka wani amfani1 alhãli kuwa Allah Shi ne Mai ji, Masani?"
Bayanai
[1] Idan bauta wa Ĩsã, Annabin Allah ya zama kãfirci bauta wa waliy yã zama shirka kenen. Kuma idan Ĩsã bai mallaki kõme ba, to, waliyyi mene ne matsayinsa?. -
قُلْ يَـٰٓأَهْلَ ٱلْكِتَـٰبِ لَا تَغْلُوا۟ فِى دِينِكُمْ غَيْرَ ٱلْحَقِّ وَلَا تَتَّبِعُوٓا۟ أَهْوَآءَ قَوْمٍ قَدْ ضَلُّوا۟ مِن قَبْلُ وَأَضَلُّوا۟ كَثِيرًا وَضَلُّوا۟ عَن سَوَآءِ ٱلسَّبِيلِ٧٧
Qul ya ahla alkitabi la taghloo fee deenikum ghayra alhaqqi wala tattabiʿoo ahwaa qawmin qad dalloo min qablu waadalloo katheeran wadalloo ʿan sawai alssabeeli
Ka ce: "Yã ku Mutanen Littãfi! Kada ku zurfafa a cikin addininku, abin da bã gaskiya ba, kuma kada ku bĩbiyi son zuciyõyin waɗansu mutãne waɗanda suka riga suka ɓace a gabãni, kuma suka ɓatar da wasu mãsu yawa, kuma suka ɓace daga tsakar hanya."
-
لُعِنَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ مِنۢ بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ عَلَىٰ لِسَانِ دَاوُۥدَ وَعِيسَى ٱبْنِ مَرْيَمَ ۚ ذَٰلِكَ بِمَا عَصَوا۟ وَّكَانُوا۟ يَعْتَدُونَ٧٨
Luʿina allatheena kafaroo min banee israeela ʿala lisani dawooda waʿeesa ibni maryama thalika bima ʿasaw wakanoo yaʿtadoona
An la'ani waɗanda suka kãfirta daga Banĩ Isrã'ĩla a kan harshen Dãwuda da Ĩsa ɗan Maryama. wannan kuwa sabõda sãɓãwar da suka yi ne, kuma sun kasance suna ta'addi.1
Bayanai
[1] Ta'addi shĩ ne ƙetare iyãka da nufin zãlunci. -
كَانُوا۟ لَا يَتَنَاهَوْنَ عَن مُّنكَرٍ فَعَلُوهُ ۚ لَبِئْسَ مَا كَانُوا۟ يَفْعَلُونَ٧٩
Kanoo la yatanahawna ʿan munkarin faʿaloohu labisa ma kanoo yafʿaloona
Sun kasance bã su hana juna daga abin ƙi, wanda suka aikata. Haƙĩƙa abin da suka kasance sunã aikatãwa yã munana.
-
تَرَىٰ كَثِيرًا مِّنْهُمْ يَتَوَلَّوْنَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ ۚ لَبِئْسَ مَا قَدَّمَتْ لَهُمْ أَنفُسُهُمْ أَن سَخِطَ ٱللَّهُ عَلَيْهِمْ وَفِى ٱلْعَذَابِ هُمْ خَـٰلِدُونَ٨٠
Tara katheeran minhum yatawallawna allatheena kafaroo labisa ma qaddamat lahum anfusuhum an sakhita Allahu ʿalayhim wafee alʿathabi hum khalidoona
Kana ganin mãsu yawa daga gare su, sunã jiɓintar waɗanda suka kãfirta. Haƙĩƙa tir da abin da rãyukansu suka gabãtar sabõda su, watau Allah Yã yi fushi da su, kuma a cikin azãba su mãsu dawwama ne
-
وَلَوْ كَانُوا۟ يُؤْمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلنَّبِىِّ وَمَآ أُنزِلَ إِلَيْهِ مَا ٱتَّخَذُوهُمْ أَوْلِيَآءَ وَلَـٰكِنَّ كَثِيرًا مِّنْهُمْ فَـٰسِقُونَ٨١
Walaw kanoo yuminoona biAllahi waalnnabiyyi wama onzila ilayhi ma ittakhathoohum awliyaa walakinna katheeran minhum fasiqoona
Kuma dã sun kasance sunã ĩmãni da Allah da Annabi da abin da aka saukar zuwa gare shi, dã ba su riƙe su masõya ba. Kuma amma mãsu yawa daga gare su, fãsiƙai ne.
-
۞ لَتَجِدَنَّ أَشَدَّ ٱلنَّاسِ عَدَٰوَةً لِّلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ ٱلْيَهُودَ وَٱلَّذِينَ أَشْرَكُوا۟ ۖ وَلَتَجِدَنَّ أَقْرَبَهُم مَّوَدَّةً لِّلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ ٱلَّذِينَ قَالُوٓا۟ إِنَّا نَصَـٰرَىٰ ۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّ مِنْهُمْ قِسِّيسِينَ وَرُهْبَانًا وَأَنَّهُمْ لَا يَسْتَكْبِرُونَ٨٢
Latajidanna ashadda alnnasi ʿadawatan lillatheena amanoo alyahooda waallatheena ashrakoo walatajidanna aqrabahum mawaddatan lillatheena amanoo allatheena qaloo inna nasara thalika bianna minhum qisseeseena waruhbanan waannahum la yastakbiroona
Lalle ne kana sãmun mafiya tsananin mutãne a adãwa ga waɗanda suka yi ĩmãni, Yahudu ne da waɗanda suka yi shirki. Kuma lalle ne kanã sãmun mafiya kusantarsu a sõyayya ga waɗanda suka yi ĩmãni su ne waɗanda suka ce: "Lalle mu ne Nasãra." Wancan kuwa sabõda akwai ¡issawa da ruhubãnãwa1 daga cikinsu. Kuma lalle ne su, bã su yin girman kai.
Bayanai
[1] Ƙissĩsi shĩ ne lĩmãnin kiristãwa, ruhubãnanci shĩ ne mutum ya tsabbace daga mutãne dõmin ibãda, kuma ba ya yin aure. Baruhubãne guda, ruhubãnãwa jam'i. -
وَإِذَا سَمِعُوا۟ مَآ أُنزِلَ إِلَى ٱلرَّسُولِ تَرَىٰٓ أَعْيُنَهُمْ تَفِيضُ مِنَ ٱلدَّمْعِ مِمَّا عَرَفُوا۟ مِنَ ٱلْحَقِّ ۖ يَقُولُونَ رَبَّنَآ ءَامَنَّا فَٱكْتُبْنَا مَعَ ٱلشَّـٰهِدِينَ٨٣
Waitha samiʿoo ma onzila ila alrrasooli tara aʿyunahum tafeedu mina alddamʿi mimma ʿarafoo mina alhaqqi yaqooloona rabbana amanna faoktubna maʿa alshshahideena
Kuma idan suka ji abin da aka saukar zuwa ga Manzo, kanã ganin idanunsu sunã zubar da hawãye, sabõda abin da suka sani daga gaskiya, sunã cewa: "Yã Ubangijinmu! Mun yi ĩmãni, sai ka rubuta mu tãre da mãsu shaida.
-
وَمَا لَنَا لَا نُؤْمِنُ بِٱللَّهِ وَمَا جَآءَنَا مِنَ ٱلْحَقِّ وَنَطْمَعُ أَن يُدْخِلَنَا رَبُّنَا مَعَ ٱلْقَوْمِ ٱلصَّـٰلِحِينَ٨٤
Wama lana la numinu biAllahi wama jaana mina alhaqqi wanatmaʿu an yudkhilana rabbuna maʿa alqawmi alssaliheena
"Kuma mene ne yake gare mu, bã zã mu yi ĩmãni daAllah ba, da kuma abin da ya zo mana daga gaskiya, kuma munã gurin Ubangijinmu Ya shigar da mu tãre da mutãne sãlihai?"
-
فَأَثَـٰبَهُمُ ٱللَّهُ بِمَا قَالُوا۟ جَنَّـٰتٍ تَجْرِى مِن تَحْتِهَا ٱلْأَنْهَـٰرُ خَـٰلِدِينَ فِيهَا ۚ وَذَٰلِكَ جَزَآءُ ٱلْمُحْسِنِينَ٨٥
Faathabahumu Allahu bima qaloo jannatin tajree min tahtiha alanharu khalideena feeha wathalika jazao almuhsineena
Sabõda haka, Allah Yã sãkã musu, dõmin abin da suka faɗa da gidãjen Aljanna (waɗanda) ƙõramu sunã gudãna a ƙarƙashinsu, sunã madawwama a cikinsu, kuma wannan ne sakamakon mãsu kyautatãwa.
-
وَٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ وَكَذَّبُوا۟ بِـَٔايَـٰتِنَآ أُو۟لَـٰٓئِكَ أَصْحَـٰبُ ٱلْجَحِيمِ٨٦
Waallatheena kafaroo wakaththaboo biayatina olaika ashabu aljaheemi
Kuma waɗanda suka kãfirta kuma suka ƙaryata game da ãyõyin Mu, waɗancan ne abõkan Wuta.
-
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ لَا تُحَرِّمُوا۟ طَيِّبَـٰتِ مَآ أَحَلَّ ٱللَّهُ لَكُمْ وَلَا تَعْتَدُوٓا۟ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ ٱلْمُعْتَدِينَ٨٧
Ya ayyuha allatheena amanoo la tuharrimoo tayyibati ma ahalla Allahu lakum wala taʿtadoo inna Allaha la yuhibbu almuʿtadeena
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku haramta abubuwa mãsu dãɗi da Allah Ya halatta muku, kuma kada ku ƙetare haddi. Lalle ne, Allah bã Ya son mãsu ƙetare haddi.1
Bayanai
[1] Haramta abin da Allah Ya halatta kõ kuwa halatta abin da Allah Ya haramta kãfirci ne, dõmin wanda ya ƙetare haddi da kansa, yã yi da'awar Ilãhiyya kõ Annabci, haka wanda ya bi shi a kan wannan abin, ya yi shirki da Allah, dõmin yã sãmi wani mai waɗansu dõkõki wanda bã Allah ba, kuma ya bi shi a kansu, ko kuwa ya bi wani mai da'awar annabci, bãyan Alƙur'ãni yã ce an rufe annabci daga Annabi Muhammadu, tsĩra da amincĩ su tabbata a gare shi. -
وَكُلُوا۟ مِمَّا رَزَقَكُمُ ٱللَّهُ حَلَـٰلًا طَيِّبًا ۚ وَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ ٱلَّذِىٓ أَنتُم بِهِۦ مُؤْمِنُونَ٨٨
Wakuloo mimma razaqakumu Allahu halalan tayyiban waittaqoo Allaha allathee antum bihi muminoona
Kuma ku ci daga abin da Allah Ya azurta ku, halat mai daɗi, kuma ku bi Allah da taƙawa, wanda yake ku, mãsu ĩmãni ne da shi.
-
لَا يُؤَاخِذُكُمُ ٱللَّهُ بِٱللَّغْوِ فِىٓ أَيْمَـٰنِكُمْ وَلَـٰكِن يُؤَاخِذُكُم بِمَا عَقَّدتُّمُ ٱلْأَيْمَـٰنَ ۖ فَكَفَّـٰرَتُهُۥٓ إِطْعَامُ عَشَرَةِ مَسَـٰكِينَ مِنْ أَوْسَطِ مَا تُطْعِمُونَ أَهْلِيكُمْ أَوْ كِسْوَتُهُمْ أَوْ تَحْرِيرُ رَقَبَةٍ ۖ فَمَن لَّمْ يَجِدْ فَصِيَامُ ثَلَـٰثَةِ أَيَّامٍ ۚ ذَٰلِكَ كَفَّـٰرَةُ أَيْمَـٰنِكُمْ إِذَا حَلَفْتُمْ ۚ وَٱحْفَظُوٓا۟ أَيْمَـٰنَكُمْ ۚ كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ ٱللَّهُ لَكُمْ ءَايَـٰتِهِۦ لَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ٨٩
La yuakhithukumu Allahu biallaghwi fee aymanikum walakin yuakhithukum bima ʿaqqadtumu alaymana fakaffaratuhu itʿamu ʿasharati masakeena min awsati ma tutʿimoona ahleekum aw kiswatuhum aw tahreeru raqabatin faman lam yajid fasiyamu thalathati ayyamin thalika kaffaratu aymanikum itha halaftum waihfathoo aymanakum kathalika yubayyinu Allahu lakum ayatihi laʿallakum tashkuroona
Allah bã Ya kãmã ku sabõda yãsassa1 a cikin rantsuwõyinku, kuma amma Yanã kãmã ku da abin da kuka ƙudurta rantsuwõyi (a kansa). To, kaffãrarsa ita ce ciyar da miskĩni gõma daga matsakaicin abin da kuke ciyar da iyãlanku, kõ kuwa tufãtar da su, kõ kuwa 'yantãwar wuya. Sa'an nan wanda bai sãmu ba, sai azumin kwãna uku. wannan ne kaffãrar rantsuwõyinku, idan kun rantse. Kuma ku kiyãye rantsuwoyinku. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana muku ãyoyinsa, tsammãninku kunã gõdewa.
Bayanai
[1] Rantsuwa alkawari ce da sunãn Allah, cewa mai rantsuwar zai aikata ko kuwa bã zai aikata ba, kõ kuwa a kan tabbatar wani abu a kan sifar da ya ambata, kõ kuwa kõruwarsa daga wannan sifar. Wanda ya yi rantsuwa sa'an nan ya yi hinsi, to, sai ya yi kaffãra, kamar yadda aka ambata a cikin ãyar. Sai fa idan ta zama yãsassar rantsuwa ce, wadda mutum ya yi a kan saninsa, sa'an nan sanin nan ya warware, sabõda bayyanar wani abu. Wasu sun ce ita ce rantsuwar da ake yi a cikin magana bã da nufi ba, kamar ã'a wallãhi, ko ĩ, wallãhi. Kuma akwai rantsuwar gamusa a kan ƙarya. Ita ma bãbu kaffãra sabõda ita, sai tuba zuwa ga Allah da istigfãri, kuma tanã sanya tsiya. -
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓا۟ إِنَّمَا ٱلْخَمْرُ وَٱلْمَيْسِرُ وَٱلْأَنصَابُ وَٱلْأَزْلَـٰمُ رِجْسٌ مِّنْ عَمَلِ ٱلشَّيْطَـٰنِ فَٱجْتَنِبُوهُ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ٩٠
Ya ayyuha allatheena amanoo innama alkhamru waalmaysiru waalansabu waalazlamu rijsun min ʿamali alshshaytani faijtaniboohu laʿallakum tuflihoona
Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Abin sani kawai, giya da cãca da refu da kiban ƙuri'a1, ƙazanta ne daga aikin shaiɗan, sai ku nĩsance shi, wa la'alla ku ci nasara.
Bayanai
[1] Yin cãca da shan giya da refu da kiban ƙuri'a, aikatar da su warware alkawari ne na hana cin dukiyar mutãne da bãɗi1i (ƙarya), da tsaron salla da Allah Ya yi umurni a tsare; watau rashin taƙawa ke nan. -
إِنَّمَا يُرِيدُ ٱلشَّيْطَـٰنُ أَن يُوقِعَ بَيْنَكُمُ ٱلْعَدَٰوَةَ وَٱلْبَغْضَآءَ فِى ٱلْخَمْرِ وَٱلْمَيْسِرِ وَيَصُدَّكُمْ عَن ذِكْرِ ٱللَّهِ وَعَنِ ٱلصَّلَوٰةِ ۖ فَهَلْ أَنتُم مُّنتَهُونَ٩١
Innama yureedu alshshaytanu an yooqiʿa baynakumu alʿadawata waalbaghdaa fee alkhamri waalmaysiri wayasuddakum ʿan thikri Allahi waʿani alssalati fahal antum muntahoona
Abin sani kawaĩ Shaiɗan yanã nufin ya aukar da adãwa da ƙeta a tsakãninku, a cikin giya da cãca, kuma ya kange ku daga ambaton Allah, kuma daga sallah. To, shin, ku mãsu hanuwa ne?
-
وَأَطِيعُوا۟ ٱللَّهَ وَأَطِيعُوا۟ ٱلرَّسُولَ وَٱحْذَرُوا۟ ۚ فَإِن تَوَلَّيْتُمْ فَٱعْلَمُوٓا۟ أَنَّمَا عَلَىٰ رَسُولِنَا ٱلْبَلَـٰغُ ٱلْمُبِينُ٩٢
Waateeʿoo Allaha waateeʿoo alrrasoola waihtharoo fain tawallaytum faiʿlamoo annama ʿala rasoolina albalaghu almubeenu
Ku yi ɗã'a ga Allah, kuma ku yi ɗã'a ga Manzo, kuma ku kiyãye. To, idan kun jũya, to, ku sani abin da kawai yake kan Manzon Mu, iyarwa bayyananniya.
-
لَيْسَ عَلَى ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ جُنَاحٌ فِيمَا طَعِمُوٓا۟ إِذَا مَا ٱتَّقَوا۟ وَّءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ ثُمَّ ٱتَّقَوا۟ وَّءَامَنُوا۟ ثُمَّ ٱتَّقَوا۟ وَّأَحْسَنُوا۟ ۗ وَٱللَّهُ يُحِبُّ ٱلْمُحْسِنِينَ٩٣
Laysa ʿala allatheena amanoo waʿamiloo alssalihati junahun feema taʿimoo itha ma ittaqaw waamanoo waʿamiloo alssalihati thumma ittaqaw waamanoo thumma ittaqaw waahsanoo waAllahu yuhibbu almuhsineena
Bãbu laifi a kan waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, a cikin abin da suka ci, idan sun yi taƙawa kuma suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sa'an nan suka yi taƙawa kuma suka yi ĩmãni, sa'an nan kuma suka yi taƙawa kuma suka kyautata1. Kuma Allah Yana son mãsu kyautatãwa.
Bayanai
[1] Yã maimaita faɗin taƙawa sau uku ga wanda ya tuba da shan giya da cãca dõmin ya nuna nauyinsu. Wanda ya shã giya kõ ya yi cãca, yã keta haddin Allah da alfarmar mutãne da darajar kansa. Sai yã yi taƙawa daga waɗannan zai iya rabuwa da su. Tsare su yanã cikin cika alkawari a tsakãnin mutum da Allah da kuma mutãne da ransa. -
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ لَيَبْلُوَنَّكُمُ ٱللَّهُ بِشَىْءٍ مِّنَ ٱلصَّيْدِ تَنَالُهُۥٓ أَيْدِيكُمْ وَرِمَاحُكُمْ لِيَعْلَمَ ٱللَّهُ مَن يَخَافُهُۥ بِٱلْغَيْبِ ۚ فَمَنِ ٱعْتَدَىٰ بَعْدَ ذَٰلِكَ فَلَهُۥ عَذَابٌ أَلِيمٌ٩٤
Ya ayyuha allatheena amanoo layabluwannakumu Allahu bishayin mina alssaydi tanaluhu aydeekum warimahukum liyaʿlama Allahu man yakhafuhu bialghaybi famani iʿtada baʿda thalika falahu ʿathabun aleemun
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Lalle ne, Allah zai jarraba ku da wani abu, daga farauta, hannuwanku da mãsunku sunã sãmun sa dõmin Allah Ya san wanda yake tsoron Sa a fake. To, wanda ya yi ta'addi a bãyan wannan, to, yanã da azãba mai raɗaɗi.
-
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ لَا تَقْتُلُوا۟ ٱلصَّيْدَ وَأَنتُمْ حُرُمٌ ۚ وَمَن قَتَلَهُۥ مِنكُم مُّتَعَمِّدًا فَجَزَآءٌ مِّثْلُ مَا قَتَلَ مِنَ ٱلنَّعَمِ يَحْكُمُ بِهِۦ ذَوَا عَدْلٍ مِّنكُمْ هَدْيًۢا بَـٰلِغَ ٱلْكَعْبَةِ أَوْ كَفَّـٰرَةٌ طَعَامُ مَسَـٰكِينَ أَوْ عَدْلُ ذَٰلِكَ صِيَامًا لِّيَذُوقَ وَبَالَ أَمْرِهِۦ ۗ عَفَا ٱللَّهُ عَمَّا سَلَفَ ۚ وَمَنْ عَادَ فَيَنتَقِمُ ٱللَّهُ مِنْهُ ۗ وَٱللَّهُ عَزِيزٌ ذُو ٱنتِقَامٍ٩٥
Ya ayyuha allatheena amanoo la taqtuloo alssayda waantum hurumun waman qatalahu minkum mutaʿammidan fajazaon mithlu ma qatala mina alnnaʿami yahkumu bihi thawa ʿadlin minkum hadyan baligha alkaʿbati aw kaffaratun taʿamu masakeena aw ʿadlu thalika siyaman liyathooqa wabala amrihi ʿafa Allahu ʿamma salafa waman ʿada fayantaqimu Allahu minhu waAllahu ʿazeezun thoo intiqamin
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku kashe farauta alhãli kunã mãsu harama1. Kuma wanda ya kashe shi daga gare ku, yanã mai ganganci, sai sakamako misãlin abin da ya kashe, daga dabbõbin ni'ima, ma'abuta ãdalci biyu daga cikinku sunã yin hukunci da shi. Ya zama hadaya mai isa ga Ka'aba ko kuwa kaffãra da abincin miskĩnai ko kuwa a matsayinsa ya yi azumi dõmin ya ɗanɗani masifar al'amarinsa. Allah Yã yafe laifi daga abin da ya gabãta. Kuma wanda ya kõma, to, Allah zai yi azãbar rãmuwa daga gare shi, kuma Allah Mabuwãyi ne, ma'abũcin azabãr rãmuwa.
Bayanai
[1] Barin farauta a cikin Harami yanã a cikin cikãwa da alkawari. Wanda ya sãɓa, sai ya yi fansa da biyan misãlin abin da ya kashe daga dabbõbin gida na jin dãɗi; watau a biya barewa da akuya kõ tunkiya. Amma kuma sai an sãmi mutum biyu ãdalai sun hukunta abin da mutum zai bayar ɗin. Idan bã Ya da dabbar, sai ya biya ƙĩmarta da abinci, ya bai wa kõwane miskĩni ɗaya mudu guda. Idan bã ya iyãwa kuwa sai ya yi azumi, kõwane mudu guda kwãna ɗaya, guntun mudu a biya shi da cikakken kwãna. -
أُحِلَّ لَكُمْ صَيْدُ ٱلْبَحْرِ وَطَعَامُهُۥ مَتَـٰعًا لَّكُمْ وَلِلسَّيَّارَةِ ۖ وَحُرِّمَ عَلَيْكُمْ صَيْدُ ٱلْبَرِّ مَا دُمْتُمْ حُرُمًا ۗ وَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ ٱلَّذِىٓ إِلَيْهِ تُحْشَرُونَ٩٦
Ohilla lakum saydu albahri wataʿamuhu mataʿan lakum walilssayyarati wahurrima ʿalaykum saydu albarri ma dumtum huruman waittaqoo Allaha allathee ilayhi tuhsharoona
An halatta muku farautar ruwa da abincinsa dõmin jin dãɗi a gare ku, kuma dõmin matafiya. Kuma an haramta farautar tudu a kanku, matuƙar kun dawwama mãsu harama. Kuma ku bi Allah da taƙawa, wanda yake zuwa gare Shi ne ake tãra ku.
-
۞ جَعَلَ ٱللَّهُ ٱلْكَعْبَةَ ٱلْبَيْتَ ٱلْحَرَامَ قِيَـٰمًا لِّلنَّاسِ وَٱلشَّهْرَ ٱلْحَرَامَ وَٱلْهَدْىَ وَٱلْقَلَـٰٓئِدَ ۚ ذَٰلِكَ لِتَعْلَمُوٓا۟ أَنَّ ٱللَّهَ يَعْلَمُ مَا فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَمَا فِى ٱلْأَرْضِ وَأَنَّ ٱللَّهَ بِكُلِّ شَىْءٍ عَلِيمٌ٩٧
Jaʿala Allahu alkaʿbata albayta alharama qiyaman lilnnasi waalshshahra alharama waalhadya waalqalaida thalika litaʿlamoo anna Allaha yaʿlamu ma fee alssamawati wama fee alardi waanna Allaha bikulli shayin ʿaleemun
Allah Ya sanya Ka'aba ¦aki Tsararre, ma'aunin addini ga mutane, kuma Yã sanya watã Mai alfarma da hadaya da rãtayõyin Allah Yã san abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa, kuma cewa lalle Allah, ga dukkan, kõme, Masani1 ne.
Bayanai
[1] Dõmin ku san haka kuma ku himmatu ga tsare alkawurran Sa. -
ٱعْلَمُوٓا۟ أَنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلْعِقَابِ وَأَنَّ ٱللَّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ٩٨
Iʿlamoo anna Allaha shadeedu alʿiqabi waanna Allaha ghafoorun raheemun
Ku sani cewa lalle Allah Mai tsananin uƙuba ne, kuma lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
-
مَّا عَلَى ٱلرَّسُولِ إِلَّا ٱلْبَلَـٰغُ ۗ وَٱللَّهُ يَعْلَمُ مَا تُبْدُونَ وَمَا تَكْتُمُونَ٩٩
Ma ʿala alrrasooli illa albalaghu waAllahu yaʿlamu ma tubdoona wama taktumoona
Bãbu abin da yake a kan Manzo, sai iyarwa, kuma Allah Yanã sanin abin da kuke bayyanãwa da abin da kuke ɓõyewa.
-
قُل لَّا يَسْتَوِى ٱلْخَبِيثُ وَٱلطَّيِّبُ وَلَوْ أَعْجَبَكَ كَثْرَةُ ٱلْخَبِيثِ ۚ فَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ يَـٰٓأُو۟لِى ٱلْأَلْبَـٰبِ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ١٠٠
Qul la yastawee alkhabeethu waalttayyibu walaw aʿjabaka kathratu alkhabeethi faittaqoo Allaha ya olee alalbabi laʿallakum tuflihoona
Ka ce: "Mummuna da mai kyau bã su daidaita, kuma kõ dã yawan mummuan yã bã ka sha'awa. Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, yã ma'abuta hankula ko la'alla zã ku ci nasara."
-
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ لَا تَسْـَٔلُوا۟ عَنْ أَشْيَآءَ إِن تُبْدَ لَكُمْ تَسُؤْكُمْ وَإِن تَسْـَٔلُوا۟ عَنْهَا حِينَ يُنَزَّلُ ٱلْقُرْءَانُ تُبْدَ لَكُمْ عَفَا ٱللَّهُ عَنْهَا ۗ وَٱللَّهُ غَفُورٌ حَلِيمٌ١٠١
Ya ayyuha allatheena amanoo la tasaloo ʿan ashyaa in tubda lakum tasukum wain tasaloo ʿanha heena yunazzalu alquranu tubda lakum ʿafa Allahu ʿanha waAllahu ghafoorun haleemun
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku yi tambaya ga abubuwa, idan an bayyana muku (hukuncinsu) su ɓãta muku rai. Kuma idan kuka yi tambaya a gare su a lõkacin1 da ake saukar da Alƙur'ãni, zã a bayyana maku. Allah Yã yãfe laifi daga gare su, Allah Mai gãfara ne, Mai haƙuri.
Bayanai
[1] Wannan lõkacin yã nuna shiɗai ne lõkacin saukar hukunci kõwane iri ne daga Allah. Wanda ya ce Annabi yã faɗa masa wani hukunci a kan wata matsala, bãyan rasuwarsa, tsĩra da aminci su tabbata gare shi, to, bã zã a karɓar masa ba, dõmin yã sãɓã wa nassin Alƙur'ãni. Kuma mafarki bã ya zama hujja, balle a ɗauke shi hukunci wanda ake yin aiki da shi. Mafarkin Annabãwa ko mafarkin da Annabãwa suka tabbatar shi ne gaskiya, saura kuma sai abin da ya bayyana, kuma bai sãɓã wa sharĩa ba. -
قَدْ سَأَلَهَا قَوْمٌ مِّن قَبْلِكُمْ ثُمَّ أَصْبَحُوا۟ بِهَا كَـٰفِرِينَ١٠٢
Qad saalaha qawmun min qablikum thumma asbahoo biha kafireena
Lalle ne wasu mutãne sun tambaye su daga gabãninku, sa'an nan kuma suka wãyi gari da su sanã kãfirai.
-
مَا جَعَلَ ٱللَّهُ مِنۢ بَحِيرَةٍ وَلَا سَآئِبَةٍ وَلَا وَصِيلَةٍ وَلَا حَامٍ ۙ وَلَـٰكِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ يَفْتَرُونَ عَلَى ٱللَّهِ ٱلْكَذِبَ ۖ وَأَكْثَرُهُمْ لَا يَعْقِلُونَ١٠٣
Ma jaʿala Allahu min baheeratin wala saibatin wala waseelatin wala hamin walakinna allatheena kafaroo yaftaroona ʿala Allahi alkathiba waaktharuhum la yaʿqiloona
Kuma Allah bai sanya wata bahĩra ba, kuma haka sã'iba, kuma haka wasĩla, kuma haka hãmi1, amma waɗanda suka kãfirta, su suke ƙirƙira ƙarya ga Allah, kuma mafi yawansu bã su hankalta.
Bayanai
[1] Bahĩra da sã'iba da hãmi sunãyen dabbõbi ne waɗanda ake bari dõmin tsãfi Bukhãri yã ruwaito daga Sa'ĩd ɗan Musayyab Ya ce: "Bahĩra ita ce rãƙumar da ake hana nõnõnta dõmin aljannu, bãbu mai tãtsar ta daga mutãne. Sã'iba kuma sunã 'yanta ta dõmin gumãka, ba a ɗaukar kõme a kanta. Kuma wasĩla ita ce rãƙuma budurwa wadda ta fãra haifuwar mace, a ciki na farko, sa'an nan kuma na biyu haka mace. Suna barin ta ga gumãka idan ta sãdar da rãƙuma mata biyu bãbu namiji a tsakãninsu. Hãmi kuwa shĩ ne ƙaton rãƙumi wanda ya yi barbara shekaru sanannu a wurinsu. Idan ya ƙãre sai su bar shi ga gumãka, bã a aza kõme a kansa. Kuma waɗannan dabbõbin duka, mãsu hidimar gumãkan, su ne suke cin su.". -
وَإِذَا قِيلَ لَهُمْ تَعَالَوْا۟ إِلَىٰ مَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ وَإِلَى ٱلرَّسُولِ قَالُوا۟ حَسْبُنَا مَا وَجَدْنَا عَلَيْهِ ءَابَآءَنَآ ۚ أَوَلَوْ كَانَ ءَابَآؤُهُمْ لَا يَعْلَمُونَ شَيْـًٔا وَلَا يَهْتَدُونَ١٠٤
Waitha qeela lahum taʿalaw ila ma anzala Allahu waila alrrasooli qaloo hasbuna ma wajadna ʿalayhi abaana awalaw kana abaohum la yaʿlamoona shayan wala yahtadoona
Kuma idan aka ce musu: "Ku zo zuwa ga abin da Allah Ya saukar, kuma zuwa ga Manzo," sai su ce: "Mai isarmu shi ne abin da muka iske ubanninmu a kansa." Shin, kuma kõ dã ubanninsu sun kasance bã su sanin kõme kuma bã su shiryuwa?
-
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ عَلَيْكُمْ أَنفُسَكُمْ ۖ لَا يَضُرُّكُم مَّن ضَلَّ إِذَا ٱهْتَدَيْتُمْ ۚ إِلَى ٱللَّهِ مَرْجِعُكُمْ جَمِيعًا فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ١٠٥
Ya ayyuha allatheena amanoo ʿalaykum anfusakum la yadurrukum man dalla itha ihtadaytum ila Allahi marjiʿukum jameeʿan fayunabbiokum bima kuntum taʿmaloona
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku lazimci1 rãyukanku, wanda ya ɓace bã zai cuce ku ba idan kun shiryu, zuwa ga Allah makõmarku take gabã ɗaya. Sa'an nan Ya bã ku lãbari ga abin da kuka kasance kunã aikatãwa.
Bayanai
[1] Wanda yake son Ya gyãra wani sai ya gyãra kansa daga farko. Wanda ya gyara kansa ɓatar wani bã ta cutarsa. Ba a nufin a bar wa'azi wãtau a ƙyãle mutane da jãhilcinsu. -
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ شَهَـٰدَةُ بَيْنِكُمْ إِذَا حَضَرَ أَحَدَكُمُ ٱلْمَوْتُ حِينَ ٱلْوَصِيَّةِ ٱثْنَانِ ذَوَا عَدْلٍ مِّنكُمْ أَوْ ءَاخَرَانِ مِنْ غَيْرِكُمْ إِنْ أَنتُمْ ضَرَبْتُمْ فِى ٱلْأَرْضِ فَأَصَـٰبَتْكُم مُّصِيبَةُ ٱلْمَوْتِ ۚ تَحْبِسُونَهُمَا مِنۢ بَعْدِ ٱلصَّلَوٰةِ فَيُقْسِمَانِ بِٱللَّهِ إِنِ ٱرْتَبْتُمْ لَا نَشْتَرِى بِهِۦ ثَمَنًا وَلَوْ كَانَ ذَا قُرْبَىٰ ۙ وَلَا نَكْتُمُ شَهَـٰدَةَ ٱللَّهِ إِنَّآ إِذًا لَّمِنَ ٱلْـَٔاثِمِينَ١٠٦
Ya ayyuha allatheena amanoo shahadatu baynikum itha hadara ahadakumu almawtu heena alwasiyyati ithnani thawa ʿadlin minkum aw akharani min ghayrikum in antum darabtum fee alardi faasabatkum museebatu almawti tahbisoonahuma min baʿdi alssalati fayuqsimani biAllahi ini irtabtum la nashtaree bihi thamanan walaw kana tha qurba wala naktumu shahadata Allahi inna ithan lamina alathimeena
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Shaidar1 tsakãninku, idan mutuwa ta halarci ɗayanku, a lõkacin wasiyya, maza biyu ne ma'abuta ãdalci daga gare ku, kõ kuwa wasu biyu daga wasunku idan kun tafi a cikin ƙasa sa'an nan masĩfar mutuwa ta sãme ku. Kunã tsare su daga bãyan salla har su yi rantsuwa da Allah; idan kun yi shakka: "Bã mu sayen kuɗi da shi, kõ dã ya kasance ma'abucin zumunta kuma bã mu ɓõye shaidar Allah. Lalle ne mu, a lõkacin, haƙĩƙa, munã daga mãsu zunubi."
Bayanai
[1] Idan husuma ta auku a tsakãnin Musulmi da tsakãnin kãfirai, kuma su kãfiran suka zama mudda'a alaihim (waɗanda ake tuhuma), kuma bãbu wata shaida sai su, to, sai su yi rantsuwa a wurin ibãdarsu, a kan su ne da gaskiya, a hukumta musu da hakkin. Bayan haka, idan an sãmi wata shaida a kan ƙaryarsu ana warware hukuncin a bãyan mudda'i (mãsu ƙãra) biyu Musulmi sun yi rantsuwa cewa abin da waɗancan suka faɗa ƙarya ne, abin da shaidunsu suka yi shaida da shi, shi ne gaskiya. -
فَإِنْ عُثِرَ عَلَىٰٓ أَنَّهُمَا ٱسْتَحَقَّآ إِثْمًا فَـَٔاخَرَانِ يَقُومَانِ مَقَامَهُمَا مِنَ ٱلَّذِينَ ٱسْتَحَقَّ عَلَيْهِمُ ٱلْأَوْلَيَـٰنِ فَيُقْسِمَانِ بِٱللَّهِ لَشَهَـٰدَتُنَآ أَحَقُّ مِن شَهَـٰدَتِهِمَا وَمَا ٱعْتَدَيْنَآ إِنَّآ إِذًا لَّمِنَ ٱلظَّـٰلِمِينَ١٠٧
Fain ʿuthira ʿala annahuma istahaqqa ithman faakharani yaqoomani maqamahuma mina allatheena istahaqqa ʿalayhimu alawlayani fayuqsimani biAllahi lashahadatuna ahaqqu min shahadatihima wama iʿtadayna inna ithan lamina alththalimeena
To, idan aka gane cewa lalle sũ, sun cancanci zunubi to sai wasu biyu su tsayu matsayinsu daga waɗanda suka karɓa daga gare su, mutãne biyu mafiya cancanta, sa'an nan su yi rantsuwa da Allah: "Lalle ne shaidarmu ce mafi gaskiya daga shaidarsu, kuma ba mu yi zãlunci ba. Lalle mu, a lõkacin haƙĩƙa, munã daga azzãlumai."
-
ذَٰلِكَ أَدْنَىٰٓ أَن يَأْتُوا۟ بِٱلشَّهَـٰدَةِ عَلَىٰ وَجْهِهَآ أَوْ يَخَافُوٓا۟ أَن تُرَدَّ أَيْمَـٰنٌۢ بَعْدَ أَيْمَـٰنِهِمْ ۗ وَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَٱسْمَعُوا۟ ۗ وَٱللَّهُ لَا يَهْدِى ٱلْقَوْمَ ٱلْفَـٰسِقِينَ١٠٨
Thalika adna an yatoo bialshshahadati ʿala wajhiha aw yakhafoo an turadda aymanun baʿda aymanihim waittaqoo Allaha waismaʿoo waAllahu la yahdee alqawma alfasiqeena
Wannan ne mafi kusantar su zo da shaida a kan fuskarta kõ kuwa su yi tsõron a tũre rantsuwõyi a bãyan rantsuwõyinsu. Kuma ku bi Allah da taƙawa kuma ku saurara, kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne fãsiƙai.
-
۞ يَوْمَ يَجْمَعُ ٱللَّهُ ٱلرُّسُلَ فَيَقُولُ مَاذَآ أُجِبْتُمْ ۖ قَالُوا۟ لَا عِلْمَ لَنَآ ۖ إِنَّكَ أَنتَ عَلَّـٰمُ ٱلْغُيُوبِ١٠٩
Yawma yajmaʿu Allahu alrrusula fayaqoolu matha ojibtum qaloo la ʿilma lana innaka anta ʿallamu alghuyoobi
A ranar da Allah Yake tãra manzanni sa'an nan Ya ce: "Mene ne aka karɓa muku?" (zã) su ce: "Bãbu ilmi a gare mu. Lalle ne Kai, Kai ne Masanin abubuwan fake."1
Bayanai
[1] A nan hukunce-hukuncen alkawurra suka ƙãre a wannan sura daga ãyã ta sama da wannan. Kuma da wannan ãyã ta l09 Allah Yanã yi mana hikãyar abin da zai auku a Lãhira da bincinken Sa ga tsare alkawari, kõ rashin tsarewa. Ya fãra da Annabãwan Sa. Ya aiko, da ƙarin bãyani a kan irin muhãwarar da zã ta shiga a tsakãnin Sa da Annabãwa.Yã yi misãli da Ĩsã dõmin mutanensa nã nan a cikin wannan al'umma, anã kiran su zuwa ga musulunci, kuma domin shine Annabi na ƙarshen da ba a manta abubuwan da mutanensa suka yi ba a gabanin ɗauke shi ɗin. -
إِذْ قَالَ ٱللَّهُ يَـٰعِيسَى ٱبْنَ مَرْيَمَ ٱذْكُرْ نِعْمَتِى عَلَيْكَ وَعَلَىٰ وَٰلِدَتِكَ إِذْ أَيَّدتُّكَ بِرُوحِ ٱلْقُدُسِ تُكَلِّمُ ٱلنَّاسَ فِى ٱلْمَهْدِ وَكَهْلًا ۖ وَإِذْ عَلَّمْتُكَ ٱلْكِتَـٰبَ وَٱلْحِكْمَةَ وَٱلتَّوْرَىٰةَ وَٱلْإِنجِيلَ ۖ وَإِذْ تَخْلُقُ مِنَ ٱلطِّينِ كَهَيْـَٔةِ ٱلطَّيْرِ بِإِذْنِى فَتَنفُخُ فِيهَا فَتَكُونُ طَيْرًۢا بِإِذْنِى ۖ وَتُبْرِئُ ٱلْأَكْمَهَ وَٱلْأَبْرَصَ بِإِذْنِى ۖ وَإِذْ تُخْرِجُ ٱلْمَوْتَىٰ بِإِذْنِى ۖ وَإِذْ كَفَفْتُ بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ عَنكَ إِذْ جِئْتَهُم بِٱلْبَيِّنَـٰتِ فَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ مِنْهُمْ إِنْ هَـٰذَآ إِلَّا سِحْرٌ مُّبِينٌ١١٠
Ith qala Allahu ya ʿeesa ibna maryama othkur niʿmatee ʿalayka waʿala walidatika ith ayyadtuka biroohi alqudusi tukallimu alnnasa fee almahdi wakahlan waith ʿallamtuka alkitaba waalhikmata waalttawrata waalinjeela waith takhluqu mina altteeni kahayati alttayri biithnee fatanfukhu feeha fatakoonu tayran biithnee watubrio alakmaha waalabrasa biithnee waith tukhriju almawta biithnee waith kafaftu banee israeela ʿanka ith jitahum bialbayyinati faqala allatheena kafaroo minhum in hatha illa sihrun mubeenun
A lõkacin da Allah Ya ce: "Yã Ĩsã ɗan Maryama! Ka tuna ni'ima Ta a kanka, kuma a kan mahaifiyarka, a lõkacin da Na ƙarfafa ka da Rũhul ¡udusi, kanã yiwa mutãne magana a cikin shimfiɗar jariri, da kuma kanã dattijo. Kuma a lõkacin da Na sanar da kai rubutu da hikima da Attaura da Injĩla, kuma a lõkacin da kake yin halitta daga lãkã kamar surar tsuntsu da izinĩNa, sa'an nan ka hura a cikinta sai ta zama tsuntsu da izinĩ Na, kuma kanã warkar da haifaffen makaho da kuturu, da izinĩNa, kuma a lõkacin da kake fitar da matattu da izinĩNa, kuma a lõkacin da Na kange Banĩ Isrã'ĩla daga gare ka, a lõkacin da ka je musu da hujjõji bayyanannu, sai waɗanda suka kãfirta daga cikinsu suka ce: 'Wannan bã kõme ba ne, fãce sihiri bayyananne.'
-
وَإِذْ أَوْحَيْتُ إِلَى ٱلْحَوَارِيِّـۧنَ أَنْ ءَامِنُوا۟ بِى وَبِرَسُولِى قَالُوٓا۟ ءَامَنَّا وَٱشْهَدْ بِأَنَّنَا مُسْلِمُونَ١١١
Waith awhaytu ila alhawariyyeena an aminoo bee wabirasoolee qaloo amanna waishhad biannana muslimoona
"Kuma a lõkacin da Na yi wahayi zuwa ga Hawãriyãwa1 cewa ku yi ĩmãni da Ni, kuma da Manzo Na. Suka ce: "Mun yi ĩmãni, kuma ka shaida da cewa lalle mu, mãsu sallamãwa ne."
Bayanai
[1] Hawãriyãwa su ne sahabban Ĩsã, amincin Allah ya tabbata a gare shi. Sunã sanyãwar farãren tufãfi, dõmin haka aka yi musu suna da haka. -
إِذْ قَالَ ٱلْحَوَارِيُّونَ يَـٰعِيسَى ٱبْنَ مَرْيَمَ هَلْ يَسْتَطِيعُ رَبُّكَ أَن يُنَزِّلَ عَلَيْنَا مَآئِدَةً مِّنَ ٱلسَّمَآءِ ۖ قَالَ ٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ١١٢
Ith qala alhawariyyoona ya ʿeesa ibna maryama hal yastateeʿu rabbuka an yunazzila ʿalayna maidatan mina alssamai qala ittaqoo Allaha in kuntum mumineena
A lõkacin da Hawarãyãwa suka ce: "Ya Ĩsa ɗan Maryam! shin, Ubangijinka Yanã iyãwa Ya saukar da kaɓaki a kanmu daga samã?" (Ĩsã) Ya ce: "Ku bi Allah da taƙawa idan kun kasance muminai."
-
قَالُوا۟ نُرِيدُ أَن نَّأْكُلَ مِنْهَا وَتَطْمَئِنَّ قُلُوبُنَا وَنَعْلَمَ أَن قَدْ صَدَقْتَنَا وَنَكُونَ عَلَيْهَا مِنَ ٱلشَّـٰهِدِينَ١١٣
Qaloo nureedu an nakula minha watatmainna quloobuna wanaʿlama an qad sadaqtana wanakoona ʿalayha mina alshshahideena
Suka ce: "Munã nufin mu ci daga gare shi ne, kuma zukãtanmu su natsu kuma mu san cewa lalle ne, kã yi mana gaskiya, kuma mu kasance daga mãsu shaida a kansa."
-
قَالَ عِيسَى ٱبْنُ مَرْيَمَ ٱللَّهُمَّ رَبَّنَآ أَنزِلْ عَلَيْنَا مَآئِدَةً مِّنَ ٱلسَّمَآءِ تَكُونُ لَنَا عِيدًا لِّأَوَّلِنَا وَءَاخِرِنَا وَءَايَةً مِّنكَ ۖ وَٱرْزُقْنَا وَأَنتَ خَيْرُ ٱلرَّٰزِقِينَ١١٤
Qala ʿeesa ibnu maryama allahumma rabbana anzil ʿalayna maidatan mina alssamai takoonu lana ʿeedan liawwalina waakhirina waayatan minka waorzuqna waanta khayru alrraziqeena
Ĩsã ɗan Maryam ya ce: "Yã Allah. Ubangijinmu! Ka saukar da kaɓaki a kanmu daga sama dõmin ya zama ĩdi ga na farkonmu da na ƙarshenmu, kuma ya zama ãyã daga gare Ka. Ka azurta mu, kuma Kai ne Mafĩfĩcin mãsu azurtawa."
-
قَالَ ٱللَّهُ إِنِّى مُنَزِّلُهَا عَلَيْكُمْ ۖ فَمَن يَكْفُرْ بَعْدُ مِنكُمْ فَإِنِّىٓ أُعَذِّبُهُۥ عَذَابًا لَّآ أُعَذِّبُهُۥٓ أَحَدًا مِّنَ ٱلْعَـٰلَمِينَ١١٥
Qala Allahu innee munazziluha ʿalaykum faman yakfur baʿdu minkum fainnee oʿaththibuhu ʿathaban la oʿaththibuhu ahadan mina alʿalameena
Allah Ya ce: "Lalle ne Nĩ mai saukar da shi ne a kanku sa'an nan wanda ya kãfirta daga gare ku, to, lalle ne Nĩ, Inã azabta shi, da wata azãba wadda bã Ni azabta ta ga kõwa daga tãlikai."
-
وَإِذْ قَالَ ٱللَّهُ يَـٰعِيسَى ٱبْنَ مَرْيَمَ ءَأَنتَ قُلْتَ لِلنَّاسِ ٱتَّخِذُونِى وَأُمِّىَ إِلَـٰهَيْنِ مِن دُونِ ٱللَّهِ ۖ قَالَ سُبْحَـٰنَكَ مَا يَكُونُ لِىٓ أَنْ أَقُولَ مَا لَيْسَ لِى بِحَقٍّ ۚ إِن كُنتُ قُلْتُهُۥ فَقَدْ عَلِمْتَهُۥ ۚ تَعْلَمُ مَا فِى نَفْسِى وَلَآ أَعْلَمُ مَا فِى نَفْسِكَ ۚ إِنَّكَ أَنتَ عَلَّـٰمُ ٱلْغُيُوبِ١١٦
Waith qala Allahu ya ʿeesa ibna maryama aanta qulta lilnnasi ittakhithoonee waommiya ilahayni min dooni Allahi qala subhanaka ma yakoonu lee an aqoola ma laysa lee bihaqqin in kuntu qultuhu faqad ʿalimtahu taʿlamu ma fee nafsee wala aʿlamu ma fee nafsika innaka anta ʿallamu alghuyoobi
Kuma a lõkacin da Allah Ya ce: "Yã Ĩsã ɗan Maryama! Shin, kai ne ka ce wa mutãne, 'Ku riƙe ni, ni da uwata, abubuwan bautãwa biyu, baicin Allah?" (Ĩsã) Ya ce: "Tsarkinka yã tabbata! Bã ya kasancewa a gare ni, in faɗi abin da bãbu wani hakki a gare ni. Idan nã kasance nã faɗe shi, to lalle Ka san shi, Kanã sanin abin da ke a cikin raina, kuma bã ni sanin abin da ke a cikin nufinKa. Lalle ne Kai Masanin abubuwan fake ne."
-
مَا قُلْتُ لَهُمْ إِلَّا مَآ أَمَرْتَنِى بِهِۦٓ أَنِ ٱعْبُدُوا۟ ٱللَّهَ رَبِّى وَرَبَّكُمْ ۚ وَكُنتُ عَلَيْهِمْ شَهِيدًا مَّا دُمْتُ فِيهِمْ ۖ فَلَمَّا تَوَفَّيْتَنِى كُنتَ أَنتَ ٱلرَّقِيبَ عَلَيْهِمْ ۚ وَأَنتَ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍ شَهِيدٌ١١٧
Ma qultu lahum illa ma amartanee bihi ani oʿbudoo Allaha rabbee warabbakum wakuntu ʿalayhim shaheedan ma dumtu feehim falamma tawaffaytanee kunta anta alrraqeeba ʿalayhim waanta ʿala kulli shayin shaheedun
"Ban faɗa musu ba fãce abin da Ka umurce ni da shi; watau: 'Ku bauta wa Allah Ubangijina kuma Ubangijinku;' kuma nã kasance mai shaida a kansu matuƙar nã dawwama a cikinsu, sa'an nan a lõkacin da Ka karɓi raina1 Kã kasance Kai ne mai tsaro a kansu, kuma Kai, a kan dukkan kõme, Halartacce ne.
Bayanai
[1] Karɓar ran Ĩsã biyu ne, na duniya da na mutuwa. -
إِن تُعَذِّبْهُمْ فَإِنَّهُمْ عِبَادُكَ ۖ وَإِن تَغْفِرْ لَهُمْ فَإِنَّكَ أَنتَ ٱلْعَزِيزُ ٱلْحَكِيمُ١١٨
In tuʿaththibhum fainnahum ʿibaduka wain taghfir lahum fainnaka anta alʿazeezu alhakeemu
"Idan Ka azabta su, to lalle ne su, bãyinKa ne, kuma idan Ka gãfarta musu, to, lalle ne Kai ne Mabuwayi Mai hikima."
-
قَالَ ٱللَّهُ هَـٰذَا يَوْمُ يَنفَعُ ٱلصَّـٰدِقِينَ صِدْقُهُمْ ۚ لَهُمْ جَنَّـٰتٌ تَجْرِى مِن تَحْتِهَا ٱلْأَنْهَـٰرُ خَـٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدًا ۚ رَّضِىَ ٱللَّهُ عَنْهُمْ وَرَضُوا۟ عَنْهُ ۚ ذَٰلِكَ ٱلْفَوْزُ ٱلْعَظِيمُ١١٩
Qala Allahu hatha yawmu yanfaʿu alssadiqeena sidquhum lahum jannatun tajree min tahtiha alanharu khalideena feeha abadan radiya Allahu ʿanhum waradoo ʿanhu thalika alfawzu alʿatheemu
Allah Ya ce: "Wannan ce rãnar da mãsu gaskiya, gaskiyarsu take amfãninsu. Sunã da gidãjen Aljanna, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwama a cikinsu har abada. Allah Yã yarda da su, kuma sun yarda da Shi. wannan ne babban rabo mai girma."
-
لِلَّهِ مُلْكُ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ وَمَا فِيهِنَّ ۚ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍ قَدِيرٌۢ١٢٠
Lillahi mulku alssamawati waalardi wama feehinna wahuwa ʿala kulli shayin qadeerun
Allah ne da mallakar sammai da ƙasa da abin da ke a cikinsu kuma shi, a kan dukkan kõme Mai ĩkon yi ne.
Tambayoyin da ake yawan yi
Mece ce ma’anar sunan Suratul Ma’ida?
Ma’anar Ma’ida ita ce “Teburin abinci”.
Suratul Ma’ida tana cikin juz’i na nawa?
Suratul Ma’ida tana cikin juz’i na 6 da 7.
Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Ma’ida?
Suratul Ma’ida tana da ayoyi 120.
Suratul Ma’ida Makkiya ce ko Madaniya?
Suratul Ma’ida sura ce Madaniya.
Suratul Ma’ida ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?
Ita ce sura ta 5 a cikin Alƙur’ani.
Majiyoyi
- Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
- Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
- Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
- Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
- Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
- Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.
Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.