سورة الفاتحة

Suratul Fatiha da fassarar Hausa

Mabuɗi

  • 1
  • ayoyi 7
  • Makkiya
  • Juz’i 1
  • Shafi 1
Mushafi

Mishary Rashid AlafasySauke MP3Sauke PDF

Suratul Fatiha (الفاتحة) ita ce sura ta farko a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 7. Ma’anar sunanta ita ce “Mabuɗi”. Sura ce Makkiya, wadda ta sauka a Makka kafin Hijira, kuma tana cikin juz’i na 1.

A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Fatiha gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.

Suratul Fatiha cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko

  1. بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ۝١

    Bismi Allahi alrrahmani alrraheemi

    Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.

  2. ٱلْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ۝٢

    Alhamdu lillahi rabbi alʿalameena

    Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu;

  3. ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ۝٣

    Alrrahmani alrraheemi

    Mai rahama, Mai jin ƙai;

  4. مَـٰلِكِ يَوْمِ ٱلدِّينِ۝٤

    Maliki yawmi alddeeni

    Mai nuna Mulkin Rãnar Sakamako.

  5. إِيَّاكَ نَعْبُدُ وَإِيَّاكَ نَسْتَعِينُ۝٥

    Iyyaka naʿbudu waiyyaka nastaʿeenu

    Kai muke bautawa, kuma Kai kadai muke neman taimakonKa

  6. ٱهْدِنَا ٱلصِّرَٰطَ ٱلْمُسْتَقِيمَ۝٦

    Ihdina alssirata almustaqeema

    Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya.

  7. صِرَٰطَ ٱلَّذِينَ أَنْعَمْتَ عَلَيْهِمْ غَيْرِ ٱلْمَغْضُوبِ عَلَيْهِمْ وَلَا ٱلضَّآلِّينَ۝٧

    Sirata allatheena anʿamta ʿalayhim ghayri almaghdoobi ʿalayhim wala alddalleena

    Hanyar waɗanda Ka yi wa ni'ima, ba waɗanda aka yi wa fushi ba, kuma ba ɓatattu ba.1

    Bayanai
    [1] Da cewa Ubangijin halittu ya tara ilmin tauhidi na Ilãhiyya da Rububiyya, Mai rahama Ya tãra dukan rahamar dũniya da rãyarwa da matarwa da ciyarwa da shãyarwa da tufãtarwa. Mai jin ƙai yã tãra ni'imar dũniya mai dõgewa zuwa Lãhira kamar ĩmãni da na lãhira. Mai mallaka ko Mai nũna mulkin rãnar sakamako, yã haɗa dukan wa'azi. Kai muke bautã wa kuma Kai muke neman taimako, ya tara tauhĩdin Ilãhiyya da ibãda amaliyya ko ƙauliyya. Hanya madaidaiciya, tã haɗa dukan sharĩ'a da hukunce-hukunce. Waɗanda aka yi wa ni'ima, yã tãra dukan tãrihin mutanen kirki. Waɗanda aka yi wa fushi, yã tãra dukkan tãrihin mãsu tsaurin kai. Ɓatattu, yã tãra tãrihin dukan mai aiki da jãhilci ko ɓata.

Tambayoyin da ake yawan yi

Mece ce ma’anar sunan Suratul Fatiha?

Ma’anar Fatiha ita ce “Mabuɗi”.

Suratul Fatiha tana cikin juz’i na nawa?

Suratul Fatiha tana cikin juz’i na 1.

Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Fatiha?

Suratul Fatiha tana da ayoyi 7.

Suratul Fatiha Makkiya ce ko Madaniya?

Suratul Fatiha sura ce Makkiya.

Suratul Fatiha ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?

Ita ce sura ta farko a cikin Alƙur’ani.

Majiyoyi

  • Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
  • Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
  • Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
  • Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
  • Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
  • Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.

Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.

Saitunan karatu

Rubutun Alƙur’ani
Girman Larabci
100%
Girman fassara
100%
Kamanni

Ƙara zuwa Allon Gida

ReadSurahBuɗe ReadSurah daga allon gida, a cikakken allo. Surorin da kuka karanta suna buɗewa ko da babu intanet.

  1. A cikin Safari, taɓa maɓallin “Share”. A sababbin iPhone yana cikin menu na •••.
  2. Taɓa “Add to Home Screen”. Gungura ƙasa idan ba ku gan shi ba.
  3. Taɓa “Add”.