سورة البقرة

Suratul Baƙara da fassarar Hausa

Saniya

Mushafi

Mishary Rashid AlafasySauke MP3Sauke PDF

Suratul Baƙara (البقرة) ita ce sura ta 2 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 286. Ma’anar sunanta ita ce “Saniya”. Sura ce Madaniya, wadda ta sauka a Madina bayan Hijira, kuma tana cikin juz’i na 1, 2 da 3.

A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Baƙara gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.

Suratul Baƙara cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. الٓمٓ۝١

    Aliflammeem

    A. L̃. M̃.

  2. ذَٰلِكَ ٱلْكِتَـٰبُ لَا رَيْبَ ۛ فِيهِ ۛ هُدًى لِّلْمُتَّقِينَ۝٢

    Thalika alkitabu la rayba feehi hudan lilmuttaqeena

    Wãncan ne Littãfi, bãbu shakka a cikinsa, shiriya ne ga mãsu taƙawa.1

    Bayanai
    [1] Yã sifanta Littãfi; watau Alƙur'ãni da kamãla ya ce "Wancan" maimakon "Wannan" dõmin mãsu son su yi aiki da shi, su ne mãsu taƙawa. Taƙawa na da sharuɗɗa biyu, su ne ĩmãni da aiki da abin da manzancin Annabi Muhammadu ya ƙunsa. Sa'an nan mutãne a farkon Musulunci ko a inda Musulunci yake sãbo, sun kasu kashi huɗu. Kashi na farko sũ ne mãsu taƙawa waɗanda aka faɗi sifõfinsu a nan.
  3. ٱلَّذِينَ يُؤْمِنُونَ بِٱلْغَيْبِ وَيُقِيمُونَ ٱلصَّلَوٰةَ وَمِمَّا رَزَقْنَـٰهُمْ يُنفِقُونَ۝٣

    Allatheena yuminoona bialghaybi wayuqeemoona alssalata wamimma razaqnahum yunfiqoona

    Waɗanda suke yin ĩmãni game da gaibi, kuma suna tsayar da salla, kuma daga abin da Muka azurta su suna ciyarwa.

  4. وَٱلَّذِينَ يُؤْمِنُونَ بِمَآ أُنزِلَ إِلَيْكَ وَمَآ أُنزِلَ مِن قَبْلِكَ وَبِٱلْـَٔاخِرَةِ هُمْ يُوقِنُونَ۝٤

    Waallatheena yuminoona bima onzila ilayka wama onzila min qablika wabialakhirati hum yooqinoona

    Kuma waɗanda suke yin ĩmãni da abin da aka saukar zuwa gare ka, da abin da aka saukar daga gabãninka, kuma game da Lãhira suna yin yaƙĩni.

  5. أُو۟لَـٰٓئِكَ عَلَىٰ هُدًى مِّن رَّبِّهِمْ ۖ وَأُو۟لَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلْمُفْلِحُونَ۝٥

    Olaika ʿala hudan min rabbihim waolaika humu almuflihoona

    Waɗancan suna kan shiriya, daga Ubangjinsu, kuma waɗannan su ne mãsu cin nasara.

  6. إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ سَوَآءٌ عَلَيْهِمْ ءَأَنذَرْتَهُمْ أَمْ لَمْ تُنذِرْهُمْ لَا يُؤْمِنُونَ۝٦

    Inna allatheena kafaroo sawaon ʿalayhim aanthartahum am lam tunthirhum la yuminoona

    Lalle ne waɗanda suka kãfirta1 daidai ne a kansu, shin kã yi musu gargaɗi kõ ba ka yi musu gargaɗi ba, ba zã su yi ĩmãni ba.

    Bayanai
    [1] Kashi na biyu daga cikin jama'a sũ ne kãfiran da suka dõge akan kãfircin su, babu wani gisshi kuma Allah Yã san bã zã su musulunta ba.
  7. خَتَمَ ٱللَّهُ عَلَىٰ قُلُوبِهِمْ وَعَلَىٰ سَمْعِهِمْ ۖ وَعَلَىٰٓ أَبْصَـٰرِهِمْ غِشَـٰوَةٌ ۖ وَلَهُمْ عَذَابٌ عَظِيمٌ۝٧

    Khatama Allahu ʿala quloobihim waʿala samʿihim waʿala absarihim ghishawatun walahum ʿathabun ʿatheemun

    Allah Ya sa hãtimi a kan zukãtansu, da a kan jinsu, kuma a Kan ganin su akwai wata yãna; kuma suna da wata azãba mai girma.

  8. وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يَقُولُ ءَامَنَّا بِٱللَّهِ وَبِٱلْيَوْمِ ٱلْـَٔاخِرِ وَمَا هُم بِمُؤْمِنِينَ۝٨

    Wamina alnnasi man yaqoolu amanna biAllahi wabialyawmi alakhiri wama hum bimumineena

    Kuma akwai daga cikin mutãne wanda1 yake cewa: "Mun yi imani da Allah kuma da Yinin Lãhira." Alhãli kuwa su ba muminai ba ne.

    Bayanai
    [1] Kashi na uku su ne munãfukai da suka bayyana Musulunci da bãki amma zuciyarsu tanã a kan kãfirci.
  9. يُخَـٰدِعُونَ ٱللَّهَ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَمَا يَخْدَعُونَ إِلَّآ أَنفُسَهُمْ وَمَا يَشْعُرُونَ۝٩

    Yukhadiʿoona Allaha waallatheena amanoo wama yakhdaʿoona illa anfusahum wama yashʿuroona

    Suna yaudarayya da Allah da waɗanda suka yi ĩmãni, alhãli bã su yaudarar kõwa fãce kansu, kuma bã su sakankancẽwa!

  10. فِى قُلُوبِهِم مَّرَضٌ فَزَادَهُمُ ٱللَّهُ مَرَضًا ۖ وَلَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌۢ بِمَا كَانُوا۟ يَكْذِبُونَ۝١٠

    Fee quloobihim maradun fazadahumu Allahu maradan walahum ʿathabun aleemun bima kanoo yakthiboona

    A cikin zukãtansu akwai wata cũta. Sai Allah Ya ƙãramusu wata cũta, kuma suna da azãba mai raɗaɗi sabõda ãbin da suka kasance suna yi na ƙarya.

  11. وَإِذَا قِيلَ لَهُمْ لَا تُفْسِدُوا۟ فِى ٱلْأَرْضِ قَالُوٓا۟ إِنَّمَا نَحْنُ مُصْلِحُونَ۝١١

    Waitha qeela lahum la tufsidoo fee alardi qaloo innama nahnu muslihoona

    Kuma idan aka ce musu: "Kada ku yi ɓarna a cikin ƙasa," sukan ce: "Mũ mãsu kyautatawa kawai ne!"

  12. أَلَآ إِنَّهُمْ هُمُ ٱلْمُفْسِدُونَ وَلَـٰكِن لَّا يَشْعُرُونَ۝١٢

    Ala innahum humu almufsidoona walakin la yashʿuroona

    To, lalle ne su, sũne mãsu ɓarna, kuma amma bã su san hakan ba.

  13. وَإِذَا قِيلَ لَهُمْ ءَامِنُوا۟ كَمَآ ءَامَنَ ٱلنَّاسُ قَالُوٓا۟ أَنُؤْمِنُ كَمَآ ءَامَنَ ٱلسُّفَهَآءُ ۗ أَلَآ إِنَّهُمْ هُمُ ٱلسُّفَهَآءُ وَلَـٰكِن لَّا يَعْلَمُونَ۝١٣

    Waitha qeela lahum aminoo kama amana alnnasu qaloo anuminu kama amana alssufahao ala innahum humu alssufahao walakin la yaʿlamoona

    Kuma idan aka ce musu: "ku yi ĩmãni kamar yadda mutãne suka yi ĩmãni," sukan ce: "Zã mu yi ĩmãni ne kamar yadda wãwãye suka yi ĩmãni?" To, lalle ne su, sũ ne wãwãye, kuma amma bã su sani.

  14. وَإِذَا لَقُوا۟ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ قَالُوٓا۟ ءَامَنَّا وَإِذَا خَلَوْا۟ إِلَىٰ شَيَـٰطِينِهِمْ قَالُوٓا۟ إِنَّا مَعَكُمْ إِنَّمَا نَحْنُ مُسْتَهْزِءُونَ۝١٤

    Waitha laqoo allatheena amanoo qaloo amanna waitha khalaw ila shayateenihim qaloo inna maʿakum innama nahnu mustahzioona

    Kuma idan sun haɗu da waɗanda suka yi ĩmãni, sukan ce: "Mun yi ĩmãni. "Kuma idan sun wõfinta zuwa ga shaiɗãnunsu,1 sukan ce: "Lalle ne muna tãre da ku: Mu mãsu izgili, kawai ne."

    Bayanai
    [1] Kashi na hudu su ne Yahudãwa waɗanda suke sun san gaskiyar Annabcin Muhammadu da Manzancinsa, amma hãsada ta hana su su bi shi, sunã ƙõƙãrin ɓãta abin da ya zo da shi ta hanyar jħfa shibhõhi a ciki, dõmin su kange mutãne daga shigarsa. Sabõda haka aka ce musu shaiɗãnu. Duk wanda ya san gaskiya amma kuma ya yi girman kai daga binta, to, shi ne shaiɗan, daga aljannu kõ daga mutane.
  15. ٱللَّهُ يَسْتَهْزِئُ بِهِمْ وَيَمُدُّهُمْ فِى طُغْيَـٰنِهِمْ يَعْمَهُونَ۝١٥

    Allahu yastahzio bihim wayamudduhum fee tughyanihim yaʿmahoona

    Allah Yana yin izgili1 gare su kuma Yana taimakon su a cikin ɓatarsu, suna ɗimuwa.

    Bayanai
    [1] Allah Yanã mayar masu da sakamakon izgilinsu.
  16. أُو۟لَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ ٱشْتَرَوُا۟ ٱلضَّلَـٰلَةَ بِٱلْهُدَىٰ فَمَا رَبِحَت تِّجَـٰرَتُهُمْ وَمَا كَانُوا۟ مُهْتَدِينَ۝١٦

    Olaika allatheena ishtarawoo alddalalata bialhuda fama rabihat tijaratuhum wama kanoo muhtadeena

    Waɗan can su ne waɗanda suka sayi ɓata da shiriya, sai fataucinsu bai yi rĩba ba, kuma ba su kasance masu shiryuwa ba.

  17. مَثَلُهُمْ كَمَثَلِ ٱلَّذِى ٱسْتَوْقَدَ نَارًا فَلَمَّآ أَضَآءَتْ مَا حَوْلَهُۥ ذَهَبَ ٱللَّهُ بِنُورِهِمْ وَتَرَكَهُمْ فِى ظُلُمَـٰتٍ لَّا يُبْصِرُونَ۝١٧

    Mathaluhum kamathali allathee istawqada naran falamma adaat ma hawlahu thahaba Allahu binoorihim watarakahum fee thulumatin la yubsiroona

    Misãlinsu shĩ ne kamar misãlin wanda ya hũra wuta, to, a lõkacin da ta haskake abin da yake gẽfensa (na abin tsõro), Allah Ya tafi da haskensu, kuma Ya bar su a cikin duffai, bã su gani.

  18. صُمٌّۢ بُكْمٌ عُمْىٌ فَهُمْ لَا يَرْجِعُونَ۝١٨

    Summun bukmun ʿumyun fahum la yarjiʿoona

    Kurãme, bẽbãye, makãfi, sabõda haka bã su dawowa.

  19. أَوْ كَصَيِّبٍ مِّنَ ٱلسَّمَآءِ فِيهِ ظُلُمَـٰتٌ وَرَعْدٌ وَبَرْقٌ يَجْعَلُونَ أَصَـٰبِعَهُمْ فِىٓ ءَاذَانِهِم مِّنَ ٱلصَّوَٰعِقِ حَذَرَ ٱلْمَوْتِ ۚ وَٱللَّهُ مُحِيطٌۢ بِٱلْكَـٰفِرِينَ۝١٩

    Aw kasayyibin mina alssamai feehi thulumatun waraʿdun wabarqun yajʿaloona asabiʿahum fee athanihim mina alssawaʿiqi hathara almawti waAllahu muheetun bialkafireena

    Ko kuwa kamar girgije mai zuba daga sama, a cikinsa akwai duffai da tsãwa da walƙiya: suna sanyãwar yãtsunsu a cikin kunnuwansu dãga tsãwarwakin, dõmin tsõron mutuwa. Kuma Allah Mai kẽwayewane gã kãfirai!

  20. يَكَادُ ٱلْبَرْقُ يَخْطَفُ أَبْصَـٰرَهُمْ ۖ كُلَّمَآ أَضَآءَ لَهُم مَّشَوْا۟ فِيهِ وَإِذَآ أَظْلَمَ عَلَيْهِمْ قَامُوا۟ ۚ وَلَوْ شَآءَ ٱللَّهُ لَذَهَبَ بِسَمْعِهِمْ وَأَبْصَـٰرِهِمْ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍ قَدِيرٌ۝٢٠

    Yakadu albarqu yakhtafu absarahum kullama adaa lahum mashaw feehi waitha athlama ʿalayhim qamoo walaw shaa Allahu lathahaba bisamʿihim waabsarihim inna Allaha ʿala kulli shayin qadeerun

    Walƙiyar tana yin kusa ta fizge gannansu, ko da yaushe ta haskakã musu, sai su yi tafiya a cikinta, kuma idan ta yi duhu a kansu, sai su yi tsaye. Kuma dã Allah Yã so, sai Ya tafi da jinsu da gannansu. Lalle ne Allah a kan dukan kõme Mai ĩkon yi ne.

  21. يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ ٱعْبُدُوا۟ رَبَّكُمُ ٱلَّذِى خَلَقَكُمْ وَٱلَّذِينَ مِن قَبْلِكُمْ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ۝٢١

    Ya ayyuha alnnasu oʿbudoo rabbakumu allathee khalaqakum waallatheena min qablikum laʿallakum tattaqoona

    Yã ku mutãne! Ku bauta wa Ubangjinku, Wanda Ya halicce ku, kũ da waɗanda suke daga gabãninku, tsammãninku ku kãre kanku!

  22. ٱلَّذِى جَعَلَ لَكُمُ ٱلْأَرْضَ فِرَٰشًا وَٱلسَّمَآءَ بِنَآءً وَأَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءً فَأَخْرَجَ بِهِۦ مِنَ ٱلثَّمَرَٰتِ رِزْقًا لَّكُمْ ۖ فَلَا تَجْعَلُوا۟ لِلَّهِ أَندَادًا وَأَنتُمْ تَعْلَمُونَ۝٢٢

    Allathee jaʿala lakumu alarda firashan waalssamaa binaan waanzala mina alssamai maan faakhraja bihi mina alththamarati rizqan lakum fala tajʿaloo lillahi andadan waantum taʿlamoona

    Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa, kuma sama gini, kuma Ya saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Ya fitar da abinci daga 'ya'yan itãce game da shi, sabõda ku. Sabõda haka kada ku sanya wa Allah wasu kĩshiyõyi, alhãli kuwa kuna sane.

  23. وَإِن كُنتُمْ فِى رَيْبٍ مِّمَّا نَزَّلْنَا عَلَىٰ عَبْدِنَا فَأْتُوا۟ بِسُورَةٍ مِّن مِّثْلِهِۦ وَٱدْعُوا۟ شُهَدَآءَكُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ إِن كُنتُمْ صَـٰدِقِينَ۝٢٣

    Wain kuntum fee raybin mimma nazzalna ʿala ʿabdina fatoo bisooratin min mithlihi waodʿoo shuhadaakum min dooni Allahi in kuntum sadiqeena

    To idan baku iya yi ba to kuwa bazaku taba iya yin ba to kuji tsoron wutar da makamahinta Mutane ne da Duwatsu kuma an tanadeta ne ga Kafirai.

  24. فَإِن لَّمْ تَفْعَلُوا۟ وَلَن تَفْعَلُوا۟ فَٱتَّقُوا۟ ٱلنَّارَ ٱلَّتِى وَقُودُهَا ٱلنَّاسُ وَٱلْحِجَارَةُ ۖ أُعِدَّتْ لِلْكَـٰفِرِينَ۝٢٤

    Fain lam tafʿaloo walan tafʿaloo faittaqoo alnnara allatee waqooduha alnnasu waalhijaratu oʿiddat lilkafireena

    To, idan ba ku aikata (kãwo sura) ba, to, bã zã ku aikataba, sabõda haka, ku ji tsoron wuta, wadda makãmashinta mutãne da duwãtsu ne, an yi tattalinta dõmin kãfurai.

  25. وَبَشِّرِ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ أَنَّ لَهُمْ جَنَّـٰتٍ تَجْرِى مِن تَحْتِهَا ٱلْأَنْهَـٰرُ ۖ كُلَّمَا رُزِقُوا۟ مِنْهَا مِن ثَمَرَةٍ رِّزْقًا ۙ قَالُوا۟ هَـٰذَا ٱلَّذِى رُزِقْنَا مِن قَبْلُ ۖ وَأُتُوا۟ بِهِۦ مُتَشَـٰبِهًا ۖ وَلَهُمْ فِيهَآ أَزْوَٰجٌ مُّطَهَّرَةٌ ۖ وَهُمْ فِيهَا خَـٰلِدُونَ۝٢٥

    Wabashshiri allatheena amanoo waʿamiloo alssalihati anna lahum jannatin tajree min tahtiha alanharu kullama ruziqoo minha min thamaratin rizqan qaloo hatha allathee ruziqna min qablu waotoo bihi mutashabihan walahum feeha azwajun mutahharatun wahum feeha khalidoona

    Kuma ka bãyar da bishãra ga waɗanda suka yi ĩmãni. kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, cẽwa lallene, suna da gidãjen Aljanna, ƙõramu na gudãna daga ƙarƙashinsu. Ko da yaushe aka azurta su da abinci daga wasu 'ya'yan itãce daga gare su,1 sai su ce: "Wannan shi ne aka azurta mu da shi daga gabãnin haka," Kuma a je musu da shi yana mai kama da juna, Kuma sunã da, a cikin su, mãtan aure mãsu tsarki, kuma su, cikin su madawwama ne.

    Bayanai
    [1] Gõnaki kõ gidãjen Aljanna.
  26. ۞ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَسْتَحْىِۦٓ أَن يَضْرِبَ مَثَلًا مَّا بَعُوضَةً فَمَا فَوْقَهَا ۚ فَأَمَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ فَيَعْلَمُونَ أَنَّهُ ٱلْحَقُّ مِن رَّبِّهِمْ ۖ وَأَمَّا ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ فَيَقُولُونَ مَاذَآ أَرَادَ ٱللَّهُ بِهَـٰذَا مَثَلًا ۘ يُضِلُّ بِهِۦ كَثِيرًا وَيَهْدِى بِهِۦ كَثِيرًا ۚ وَمَا يُضِلُّ بِهِۦٓ إِلَّا ٱلْفَـٰسِقِينَ۝٢٦

    Inna Allaha la yastahyee an yadriba mathalan ma baʿoodatan fama fawqaha faamma allatheena amanoo fayaʿlamoona annahu alhaqqu min rabbihim waamma allatheena kafaroo fayaqooloona matha arada Allahu bihatha mathalan yudillu bihi katheeran wayahdee bihi katheeran wama yudillu bihi illa alfasiqeena

    Lalle ne, Allah bã Ya jin kunyar Ya bayyana wani misãli, kõwane iri ne, sauro da abin da yake bisa gare shi. To, amma waɗanda suka yi ĩmãni, sai su san cewa lalle shi ne gaskiya daga Ubangijin su, kuma amma waɗanda suka kãfirta, sai su ce: "Mẽne ne Allah Ya yi nufi da wannan1 ya zama misãli?" na ɓatar da wasu mãsu yawa da shi, kuma Yana shiryar da wasu mãsu yawada shi, kuma bã Ya ɓatarwa da shi fãce fasiƙai.

    Bayanai
    [1] Misãli da kamar mãtan Aljanna mãsu tsarki. Ba mãtã ba kõ da sauro ko abin da ya fi, kõ ya kãsa sauro, to, akwai hikima a cikin halittarsa, wadda zã ta jãwo hankalin mai hankali ga ĩmãni da Allah sabõda ita.
  27. ٱلَّذِينَ يَنقُضُونَ عَهْدَ ٱللَّهِ مِنۢ بَعْدِ مِيثَـٰقِهِۦ وَيَقْطَعُونَ مَآ أَمَرَ ٱللَّهُ بِهِۦٓ أَن يُوصَلَ وَيُفْسِدُونَ فِى ٱلْأَرْضِ ۚ أُو۟لَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلْخَـٰسِرُونَ۝٢٧

    Allatheena yanqudoona ʿahda Allahi min baʿdi meethaqihi wayaqtaʿoona ma amara Allahu bihi an yoosala wayufsidoona fee alardi olaika humu alkhasiroona

    Waɗanda suke warware alƙawarin Allah daga bãyan ƙulla shi, kuma su yanke abin da Allah Ya yi umurni da shi a sãdar, kuma suna ɓarna a cikin ƙasa, waɗannan sũ ne mãsu hasãra.

  28. كَيْفَ تَكْفُرُونَ بِٱللَّهِ وَكُنتُمْ أَمْوَٰتًا فَأَحْيَـٰكُمْ ۖ ثُمَّ يُمِيتُكُمْ ثُمَّ يُحْيِيكُمْ ثُمَّ إِلَيْهِ تُرْجَعُونَ۝٢٨

    Kayfa takfuroona biAllahi wakuntum amwatan faahyakum thumma yumeetukum thumma yuhyeekum thumma ilayhi turjaʿoona

    Yaya kuke kãficewa da Allah, alhãli kuwa kun kasance matattu sa'an nan Ya rãyar da ku, sa'nnan kuma Ya matar da ku, sa'an nan kuma Ya rãya ku, sa'an nan zuwa gare Shi ake mayar da ku?

  29. هُوَ ٱلَّذِى خَلَقَ لَكُم مَّا فِى ٱلْأَرْضِ جَمِيعًا ثُمَّ ٱسْتَوَىٰٓ إِلَى ٱلسَّمَآءِ فَسَوَّىٰهُنَّ سَبْعَ سَمَـٰوَٰتٍ ۚ وَهُوَ بِكُلِّ شَىْءٍ عَلِيمٌ۝٢٩

    Huwa allathee khalaqa lakum ma fee alardi jameeʿan thumma istawa ila alssamai fasawwahunna sabʿa samawatin wahuwa bikulli shayin ʿaleemun

    Shi ne Wanda Ya halitta muku abin da ke a cikin ƙasa gaba ɗaya, sa'an nan kuma Ya daidaita1 zuwa sama, sa'an nan Y a aikata su sammai bakwai. Kuma Shi ga dukan kõmai Masani ne.

    Bayanai
    [1] Ya daidaita, watau Ya yi nufi; "Sa'an nan" yana amfãnar da jeranta aiki bã jerantar nufi ba, dõmin sifõfn Allah dukansu, bã fãrarru ba ne.
  30. وَإِذْ قَالَ رَبُّكَ لِلْمَلَـٰٓئِكَةِ إِنِّى جَاعِلٌ فِى ٱلْأَرْضِ خَلِيفَةً ۖ قَالُوٓا۟ أَتَجْعَلُ فِيهَا مَن يُفْسِدُ فِيهَا وَيَسْفِكُ ٱلدِّمَآءَ وَنَحْنُ نُسَبِّحُ بِحَمْدِكَ وَنُقَدِّسُ لَكَ ۖ قَالَ إِنِّىٓ أَعْلَمُ مَا لَا تَعْلَمُونَ۝٣٠

    Waith qala rabbuka lilmalaikati innee jaʿilun fee alardi khaleefatan qaloo atajʿalu feeha man yufsidu feeha wayasfiku alddimaa wanahnu nusabbihu bihamdika wanuqaddisu laka qala innee aʿlamu ma la taʿlamoona

    Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya ce ga malã'iku: "Lalle ne, Ni Mai sanya wani halĩfa ne a cikin ƙasa," suka ce: "Ashe, zã Ka sanya a cikinta, wanda zai yi ɓarna a cikinta, kuma mu, muna yi maka tasbihi tare da gõde maka, kuma1 muna tsarkakewa gareka" Ya ce: "Lalle ne, Ni Na san abin da ba ku sani ba."

    Bayanai
    [1] Malã'iku sun yi tambaya ne irin ta mai neman ya rinjãyi mai jãyayya da shi ga neman haliftaka a kan ƙasa. Sun san hãlãyen jinn da bunn waɗanda suka fãra zama a kan ƙasa suka yi ɓarna da zubarda jini.
  31. وَعَلَّمَ ءَادَمَ ٱلْأَسْمَآءَ كُلَّهَا ثُمَّ عَرَضَهُمْ عَلَى ٱلْمَلَـٰٓئِكَةِ فَقَالَ أَنۢبِـُٔونِى بِأَسْمَآءِ هَـٰٓؤُلَآءِ إِن كُنتُمْ صَـٰدِقِينَ۝٣١

    Waʿallama adama alasmaa kullaha thumma ʿaradahum ʿala almalaikati faqala anbioonee biasmai haolai in kuntum sadiqeena

    Kuma Ya sanar da Ãdam sũnãye dukansu, sa'an nan kuma ya gitta su a kan malã'iku, sa'n nan Ya ce: "Ku gaya mini sũnayen waɗannan, idan kun nasance mãsu gaskiya."

  32. قَالُوا۟ سُبْحَـٰنَكَ لَا عِلْمَ لَنَآ إِلَّا مَا عَلَّمْتَنَآ ۖ إِنَّكَ أَنتَ ٱلْعَلِيمُ ٱلْحَكِيمُ۝٣٢

    Qaloo subhanaka la ʿilma lana illa ma ʿallamtana innaka anta alʿaleemu alhakeemu

    Suka ce: "Tsarki ya tabbata a gare Ka! Bãbu sani a gare mu, lalle ne Kai, Kai ne Masani, Mai hikima."

  33. قَالَ يَـٰٓـَٔادَمُ أَنۢبِئْهُم بِأَسْمَآئِهِمْ ۖ فَلَمَّآ أَنۢبَأَهُم بِأَسْمَآئِهِمْ قَالَ أَلَمْ أَقُل لَّكُمْ إِنِّىٓ أَعْلَمُ غَيْبَ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ وَأَعْلَمُ مَا تُبْدُونَ وَمَا كُنتُمْ تَكْتُمُونَ۝٣٣

    Qala ya adamu anbihum biasmaihim falamma anbaahum biasmaihim qala alam aqul lakum innee aʿlamu ghayba alssamawati waalardi waaʿlamu ma tubdoona wama kuntum taktumoona

    Ya ce: "Yã Ãdam! Ka gaya musu sũnãyensu." To, a lokacin da ya gaya musu sũnãyensu, (Allah) Ya ce: "Ashe, ban ce muku1ba, lalle Ni, Inã sane da gaibin sammai da ƙasa, kuma (Inã sane da) abin da kuke bayyanawa da abin da kuka kasance kuna ɓõyewa?"

    Bayanai
    [1] Wannan ƙissa ta nũna cewa shũgabanci da ilmi ake yinsa, bã da yawan ibãda wadda mutum yake keɓanta da yin ta ba. Dõmin an nũna wa mala'iku fĩfĩkon Ãdam a kansu da ilmi,bã da ibãda ba. Kuma da wannan sifa zai zama Halĩfa, kõ dã Iblis bai fitar da shi ba, daga cikin Aljanna, zai fita ta wata hanya dõmin zartar da hukuncin Allah.
  34. وَإِذْ قُلْنَا لِلْمَلَـٰٓئِكَةِ ٱسْجُدُوا۟ لِـَٔادَمَ فَسَجَدُوٓا۟ إِلَّآ إِبْلِيسَ أَبَىٰ وَٱسْتَكْبَرَ وَكَانَ مِنَ ٱلْكَـٰفِرِينَ۝٣٤

    Waith qulna lilmalaikati osjudoo liadama fasajadoo illa ibleesa aba waistakbara wakana mina alkafireena

    Kuma a lõkacin da Muka ce ga malã'iku: "Ku yi sujada ga Ãdam," Sai suka yi sujada, fãce Ibilĩsa ya ƙi, kuma ya yi girman kai, kuma ya kasance daga kãfirai.

  35. وَقُلْنَا يَـٰٓـَٔادَمُ ٱسْكُنْ أَنتَ وَزَوْجُكَ ٱلْجَنَّةَ وَكُلَا مِنْهَا رَغَدًا حَيْثُ شِئْتُمَا وَلَا تَقْرَبَا هَـٰذِهِ ٱلشَّجَرَةَ فَتَكُونَا مِنَ ٱلظَّـٰلِمِينَ۝٣٥

    Waqulna ya adamu oskun anta wazawjuka aljannata wakula minha raghadan haythu shituma wala taqraba hathihi alshshajarata fatakoona mina alththalimeena

    Kuma muka ce: "Ya Ãdam! Ka zauna kai da matarka a gidan Aljanna, kuma ku ci daga gare ta, bisa wadãta, inda kuke so, kuma kada ku kusanci wannan itãciyar, har ku kasance daga azzãlumai."

  36. فَأَزَلَّهُمَا ٱلشَّيْطَـٰنُ عَنْهَا فَأَخْرَجَهُمَا مِمَّا كَانَا فِيهِ ۖ وَقُلْنَا ٱهْبِطُوا۟ بَعْضُكُمْ لِبَعْضٍ عَدُوٌّ ۖ وَلَكُمْ فِى ٱلْأَرْضِ مُسْتَقَرٌّ وَمَتَـٰعٌ إِلَىٰ حِينٍ۝٣٦

    Faazallahuma alshshaytanu ʿanha faakhrajahuma mimma kana feehi waqulna ihbitoo baʿdukum libaʿdin ʿaduwwun walakum fee alardi mustaqarrun wamataʿun ila heenin

    Sai Shaiɗan ya talãlãɓantar da su ga barinta, sai ya fitar da su daga abin da suka kasance a cikinsa. Kuma muka ce: "Sãshenku nã maƙiyi ga sãshe, kuma kuna da a cikin ƙasa matabbata da jin dãɗi zuwa ga wani lõkaci."

  37. فَتَلَقَّىٰٓ ءَادَمُ مِن رَّبِّهِۦ كَلِمَـٰتٍ فَتَابَ عَلَيْهِ ۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلتَّوَّابُ ٱلرَّحِيمُ۝٣٧

    Fatalaqqa adamu min rabbihi kalimatin fataba ʿalayhi innahu huwa alttawwabu alrraheemu

    Sai Ãdam ya karɓi wasu kalmõmi daga Ubangjjinsa, sabõda haka ya karɓi tũba a kansa. Lalle ne Shi, Shĩ ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai.

  38. قُلْنَا ٱهْبِطُوا۟ مِنْهَا جَمِيعًا ۖ فَإِمَّا يَأْتِيَنَّكُم مِّنِّى هُدًى فَمَن تَبِعَ هُدَاىَ فَلَا خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلَا هُمْ يَحْزَنُونَ۝٣٨

    Qulna ihbitoo minha jameeʿan faimma yatiyannakum minnee hudan faman tabiʿa hudaya fala khawfun ʿalayhim wala hum yahzanoona

    Muka ce: "Ku ku sauka daga gare ta gabã ɗaya. To, imma lalle shiriya ta je muku daga gare Ni, to, wanda ya bi shiriya ta to, bãbu tsõro a kansu, kuma bã su yin baƙin ciki."

  39. وَٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ وَكَذَّبُوا۟ بِـَٔايَـٰتِنَآ أُو۟لَـٰٓئِكَ أَصْحَـٰبُ ٱلنَّارِ ۖ هُمْ فِيهَا خَـٰلِدُونَ۝٣٩

    Waallatheena kafaroo wakaththaboo biayatina olaika ashabu alnnari hum feeha khalidoona

    "Kuma waɗan da suka kãfirta, kuma suka ƙaryata game da ãyõyinMu, waɗannan sũ ne abõkan Wuta; sũ a cikinta madawwama ne."

  40. يَـٰبَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ ٱذْكُرُوا۟ نِعْمَتِىَ ٱلَّتِىٓ أَنْعَمْتُ عَلَيْكُمْ وَأَوْفُوا۟ بِعَهْدِىٓ أُوفِ بِعَهْدِكُمْ وَإِيَّـٰىَ فَٱرْهَبُونِ۝٤٠

    Ya banee israeela othkuroo niʿmatiya allatee anʿamtu ʿalaykum waawfoo biʿahdee oofi biʿahdikum waiyyaya fairhabooni

    Yã Banĩ Isrã'Ĩla1! Ku tuna ni'imãTa a kanku, kuma ku cika alƙawariNa, In cika muku da alƙawarinku. kuma Ni, ku ji tsõro Na.

    Bayanai
    [1] Bãyan kiran mutãne gabã ɗaya zuwa ga addinin musulunci, sai kuma ya keɓance Yahũdu da kira zuwa ga addinin, dõmin sun bambanta da sauran kãfirai, sabõda ilminsu ga gaskiyar Musulunci. Yã gabata cewa jama'ar, kashi huɗu ce; mũminai, da kãfiran Lãrabãwan da bã zã su musulunta ba, da munãfukai da Yahũdu. Ya kira Yahũdu da Bani Isrã'ĩla, dõmin Ya tunãtar da su, cewa anã kiransu ne zuwa ga addini irin na ubansu Ya'aƙũbu bawan Allah.
  41. وَءَامِنُوا۟ بِمَآ أَنزَلْتُ مُصَدِّقًا لِّمَا مَعَكُمْ وَلَا تَكُونُوٓا۟ أَوَّلَ كَافِرٍۭ بِهِۦ ۖ وَلَا تَشْتَرُوا۟ بِـَٔايَـٰتِى ثَمَنًا قَلِيلًا وَإِيَّـٰىَ فَٱتَّقُونِ۝٤١

    Waaminoo bima anzaltu musaddiqan lima maʿakum wala takoonoo awwala kafirin bihi wala tashtaroo biayatee thamanan qaleelan waiyyaya faittaqooni

    Kuma, ku yi ĩmãni da abin da na saukar, mai gaskatãwa ga abin da yake tãre da ku, kuma kada ku kasance farkon kãfiri game da shi, Kuma kada ku sayi 'yan kuɗi kaɗan da ãyõyiNa. Kuma ku ji tsõrõNa, Nĩ kaɗai.

  42. وَلَا تَلْبِسُوا۟ ٱلْحَقَّ بِٱلْبَـٰطِلِ وَتَكْتُمُوا۟ ٱلْحَقَّ وَأَنتُمْ تَعْلَمُونَ۝٤٢

    Wala talbisoo alhaqqa bialbatili wataktumoo alhaqqa waantum taʿlamoona

    Kuma kada ku lulluɓe gaskiya da ƙarya, kuma ku ɓõye gaskiya, alhãli kuwa kuna sane.

  43. وَأَقِيمُوا۟ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُوا۟ ٱلزَّكَوٰةَ وَٱرْكَعُوا۟ مَعَ ٱلرَّٰكِعِينَ۝٤٣

    Waaqeemoo alssalata waatoo alzzakata wairkaʿoo maʿa alrrakiʿeena

    Kuma ku tsayar da salla; kuma ku bãyar da zakka; kuma ku yi rukũ'i tãre da mãsu yin rukũ'i.

  44. ۞ أَتَأْمُرُونَ ٱلنَّاسَ بِٱلْبِرِّ وَتَنسَوْنَ أَنفُسَكُمْ وَأَنتُمْ تَتْلُونَ ٱلْكِتَـٰبَ ۚ أَفَلَا تَعْقِلُونَ۝٤٤

    Atamuroona alnnasa bialbirri watansawna anfusakum waantum tatloona alkitaba afala taʿqiloona

    Shin, kuna umurnin mutãne da alhẽri, kuma ku manta da kanku alhãli kuwa kuna karatun littãfi? Shin, bãzã ku hankalta ba?

  45. وَٱسْتَعِينُوا۟ بِٱلصَّبْرِ وَٱلصَّلَوٰةِ ۚ وَإِنَّهَا لَكَبِيرَةٌ إِلَّا عَلَى ٱلْخَـٰشِعِينَ۝٤٥

    Waistaʿeenoo bialssabri waalssalati wainnaha lakabeeratun illa ʿala alkhashiʿeena

    Kuma ku nẽmi taimako da yin haƙuri, da salla. Kuma lalle ne ita, haƙĩƙa, mai girma ce fãce fa a kan mãsu tsõron Allah.

  46. ٱلَّذِينَ يَظُنُّونَ أَنَّهُم مُّلَـٰقُوا۟ رَبِّهِمْ وَأَنَّهُمْ إِلَيْهِ رَٰجِعُونَ۝٤٦

    Allatheena yathunnoona annahum mulaqoo rabbihim waannahum ilayhi rajiʿoona

    Waɗanda suka tabbata cẽwa lalle ne su mãsu haɗuwa da Ubangijinsu, kuma lalle ne sũ a gareshi mãsu kõmãwa ne.

  47. يَـٰبَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ ٱذْكُرُوا۟ نِعْمَتِىَ ٱلَّتِىٓ أَنْعَمْتُ عَلَيْكُمْ وَأَنِّى فَضَّلْتُكُمْ عَلَى ٱلْعَـٰلَمِينَ۝٤٧

    Ya banee israeela othkuroo niʿmatiya allatee anʿamtu ʿalaykum waannee faddaltukum ʿala alʿalameena

    ku Banĩ Isrã'Ĩla! Ku tuna ni'imãTa a kanku, kuma kuma ni na fifita ku akan sauran Talikai .

  48. وَٱتَّقُوا۟ يَوْمًا لَّا تَجْزِى نَفْسٌ عَن نَّفْسٍ شَيْـًٔا وَلَا يُقْبَلُ مِنْهَا شَفَـٰعَةٌ وَلَا يُؤْخَذُ مِنْهَا عَدْلٌ وَلَا هُمْ يُنصَرُونَ۝٤٨

    Waittaqoo yawman la tajzee nafsun ʿan nafsin shayan wala yuqbalu minha shafaʿatun wala yukhathu minha ʿadlun wala hum yunsaroona

    Kuma ku ji tsron wani yini, (a cikinsa) rai bã ya Wadãtar da wani rai da kõme, kuma bã a karɓar cetõ daga gareshi, kuma ba a karɓar fansa daga gare shi, kuma bã su zama ana taimakon su ba.

  49. وَإِذْ نَجَّيْنَـٰكُم مِّنْ ءَالِ فِرْعَوْنَ يَسُومُونَكُمْ سُوٓءَ ٱلْعَذَابِ يُذَبِّحُونَ أَبْنَآءَكُمْ وَيَسْتَحْيُونَ نِسَآءَكُمْ ۚ وَفِى ذَٰلِكُم بَلَآءٌ مِّن رَّبِّكُمْ عَظِيمٌ۝٤٩

    Waith najjaynakum min ali firʿawna yasoomoonakum sooa alʿathabi yuthabbihoona abnaakum wayastahyoona nisaakum wafee thalikum balaon min rabbikum ʿatheemun

    Kuma a lõkacin da muka tsĩrar da ku daga mutãnen Fir'auna, su na taya muku muguntar azãba, su na yayyanke ɗiyanku maza su na rãyar da mãtanku. Kuma a cikin wancan akwai jarabawa mai girma daga Ubangijinku.

  50. وَإِذْ فَرَقْنَا بِكُمُ ٱلْبَحْرَ فَأَنجَيْنَـٰكُمْ وَأَغْرَقْنَآ ءَالَ فِرْعَوْنَ وَأَنتُمْ تَنظُرُونَ۝٥٠

    Waith faraqna bikumu albahra faanjaynakum waaghraqna ala firʿawna waantum tanthuroona

    Kuma a lõkacin da Muka raba tẽku sabõda ku, sai Muka tsĩrar da ku kuma Muka nutsar da mutãnen Fir'auna, alhãli kuwa kũ kuna kallo.

  51. وَإِذْ وَٰعَدْنَا مُوسَىٰٓ أَرْبَعِينَ لَيْلَةً ثُمَّ ٱتَّخَذْتُمُ ٱلْعِجْلَ مِنۢ بَعْدِهِۦ وَأَنتُمْ ظَـٰلِمُونَ۝٥١

    Waith waʿadna moosa arbaʿeena laylatan thumma ittakhathtumu alʿijla min baʿdihi waantum thalimoona

    Kuma a lõkacin da muka yi wa'adi ga Mũsa, dare arba'in, sa'an nan kuma kuka riƙi maraƙi daga bãyansa, alhãli kũ, kuna mãsu zãlunci (da bauta masa).

  52. ثُمَّ عَفَوْنَا عَنكُم مِّنۢ بَعْدِ ذَٰلِكَ لَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ۝٥٢

    Thumma ʿafawna ʿankum min baʿdi thalika laʿallakum tashkuroona

    Sa'an nan kuma muka yãfe muku daga bãyan wancan, tsammãninku, kuna gõdẽwa.

  53. وَإِذْ ءَاتَيْنَا مُوسَى ٱلْكِتَـٰبَ وَٱلْفُرْقَانَ لَعَلَّكُمْ تَهْتَدُونَ۝٥٣

    Waith atayna moosa alkitaba waalfurqana laʿallakum tahtadoona

    Kuma a lõkacin da Muka baiwa Mũsa Littãfi da rarrabẽwa, tsammãninku, kuna shiryuwa.

  54. وَإِذْ قَالَ مُوسَىٰ لِقَوْمِهِۦ يَـٰقَوْمِ إِنَّكُمْ ظَلَمْتُمْ أَنفُسَكُم بِٱتِّخَاذِكُمُ ٱلْعِجْلَ فَتُوبُوٓا۟ إِلَىٰ بَارِئِكُمْ فَٱقْتُلُوٓا۟ أَنفُسَكُمْ ذَٰلِكُمْ خَيْرٌ لَّكُمْ عِندَ بَارِئِكُمْ فَتَابَ عَلَيْكُمْ ۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلتَّوَّابُ ٱلرَّحِيمُ۝٥٤

    Waith qala moosa liqawmihi ya qawmi innakum thalamtum anfusakum biittikhathikumu alʿijla fatooboo ila bariikum faoqtuloo anfusakum thalikum khayrun lakum ʿinda bariikum fataba ʿalaykum innahu huwa alttawwabu alrraheemu

    Kuma a lõkacin da Mũsa ya ce ga mutãnensa: "Ya mutãnena! Lalle ne ku, kun zãlunci kanku game da riƙonku maraƙin, sai ku tũba zuwa ga Mahaliccinku, sai ku kashe kãwunanku. Wancan ne mafii alheri a wajen mahaliccinku. Sa'an nan Ya karɓi tuba a kanku. lalle ne Shi, Shi ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai.

  55. وَإِذْ قُلْتُمْ يَـٰمُوسَىٰ لَن نُّؤْمِنَ لَكَ حَتَّىٰ نَرَى ٱللَّهَ جَهْرَةً فَأَخَذَتْكُمُ ٱلصَّـٰعِقَةُ وَأَنتُمْ تَنظُرُونَ۝٥٥

    Waith qultum ya moosa lan numina laka hatta nara Allaha jahratan faakhathatkumu alssaʿiqatu waantum tanthuroona

    Kuma a lõkacin da kuka ce: "Ya Musa! Bã zã mu yi ĩmãni ba dõminka, sai munga Allah bayyane," sabada haka tsãwar nan ta kamaku, alhãli kuwa kuna kallo.

  56. ثُمَّ بَعَثْنَـٰكُم مِّنۢ بَعْدِ مَوْتِكُمْ لَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ۝٥٦

    Thumma baʿathnakum min baʿdi mawtikum laʿallakum tashkuroona

    Sa'an nan kuma Muka tãyar da ku daga bãyan mutuwarku, tsammãninku, kuna gõdẽwa.

  57. وَظَلَّلْنَا عَلَيْكُمُ ٱلْغَمَامَ وَأَنزَلْنَا عَلَيْكُمُ ٱلْمَنَّ وَٱلسَّلْوَىٰ ۖ كُلُوا۟ مِن طَيِّبَـٰتِ مَا رَزَقْنَـٰكُمْ ۖ وَمَا ظَلَمُونَا وَلَـٰكِن كَانُوٓا۟ أَنفُسَهُمْ يَظْلِمُونَ۝٥٧

    Wathallalna ʿalaykumu alghamama waanzalna ʿalaykumu almanna waalssalwa kuloo min tayyibati ma razaqnakum wama thalamoona walakin kanoo anfusahum yathlimoona

    Kuma Muka sanya girgije ya yi inuwa a kanku, kuma Muka saukar da darɓa da tantabaru a kanku; "Ku ci daga mãsu dãɗin abin da Muka azurta ku." kuma ba su zãlunce Mu ba, kuma amma kansu suka kasance suna zãlunta.

  58. وَإِذْ قُلْنَا ٱدْخُلُوا۟ هَـٰذِهِ ٱلْقَرْيَةَ فَكُلُوا۟ مِنْهَا حَيْثُ شِئْتُمْ رَغَدًا وَٱدْخُلُوا۟ ٱلْبَابَ سُجَّدًا وَقُولُوا۟ حِطَّةٌ نَّغْفِرْ لَكُمْ خَطَـٰيَـٰكُمْ ۚ وَسَنَزِيدُ ٱلْمُحْسِنِينَ۝٥٨

    Waith qulna odkhuloo hathihi alqaryata fakuloo minha haythu shitum raghadan waodkhuloo albaba sujjadan waqooloo hittatun naghfir lakum khatayakum wasanazeedu almuhsineena

    Kuma a lokacin da Muka ce: "Ku shiga wannan alƙarya. San nan ku ci daga gareta, idan kuka so, bisa wadata, kuma ku shiga ƙofa kuna masu tawalu'i, kuma ku ce; "kãyar da zunubai" Mu gãfarta muku laifukanku, kuma zã mu ƙãra wa mãsu kyautatawa."

  59. فَبَدَّلَ ٱلَّذِينَ ظَلَمُوا۟ قَوْلًا غَيْرَ ٱلَّذِى قِيلَ لَهُمْ فَأَنزَلْنَا عَلَى ٱلَّذِينَ ظَلَمُوا۟ رِجْزًا مِّنَ ٱلسَّمَآءِ بِمَا كَانُوا۟ يَفْسُقُونَ۝٥٩

    Fabaddala allatheena thalamoo qawlan ghayra allathee qeela lahum faanzalna ʿala allatheena thalamoo rijzan mina alssamai bima kanoo yafsuqoona

    Sai waɗan da suka yi zalunci suka sake magana watar wannan da aka ce musu, saboda haka muka saukar a kan waɗanda suka yi zãlunci da azãba daga sama sabõda abin da suka kasance suna yi na fãsiƙanci.

  60. ۞ وَإِذِ ٱسْتَسْقَىٰ مُوسَىٰ لِقَوْمِهِۦ فَقُلْنَا ٱضْرِب بِّعَصَاكَ ٱلْحَجَرَ ۖ فَٱنفَجَرَتْ مِنْهُ ٱثْنَتَا عَشْرَةَ عَيْنًا ۖ قَدْ عَلِمَ كُلُّ أُنَاسٍ مَّشْرَبَهُمْ ۖ كُلُوا۟ وَٱشْرَبُوا۟ مِن رِّزْقِ ٱللَّهِ وَلَا تَعْثَوْا۟ فِى ٱلْأَرْضِ مُفْسِدِينَ۝٦٠

    Waithi istasqa moosa liqawmihi faqulna idrib biʿasaka alhajara fainfajarat minhu ithnata ʿashrata ʿaynan qad ʿalima kullu onasin mashrabahum kuloo waishraboo min rizqi Allahi wala taʿthaw fee alardi mufsideena

    Kuma a lokacin da Mũsa ya nemi shãyarwa domin mutãnensa, Muka ce; "Ka dõki dũtsen da sandarka." Sai marmaro gõma sha biyu suka ɓuɓɓugo, haƙĩƙa, kõwaɗanne mutãne sun san wurin shansu. "Ku ci kuma ku sha daga arziƙin Ubangijinku, kuma kada ku yi fasadi, a cikin ƙasa, kuna mãsu ɓarna."

  61. وَإِذْ قُلْتُمْ يَـٰمُوسَىٰ لَن نَّصْبِرَ عَلَىٰ طَعَامٍ وَٰحِدٍ فَٱدْعُ لَنَا رَبَّكَ يُخْرِجْ لَنَا مِمَّا تُنۢبِتُ ٱلْأَرْضُ مِنۢ بَقْلِهَا وَقِثَّآئِهَا وَفُومِهَا وَعَدَسِهَا وَبَصَلِهَا ۖ قَالَ أَتَسْتَبْدِلُونَ ٱلَّذِى هُوَ أَدْنَىٰ بِٱلَّذِى هُوَ خَيْرٌ ۚ ٱهْبِطُوا۟ مِصْرًا فَإِنَّ لَكُم مَّا سَأَلْتُمْ ۗ وَضُرِبَتْ عَلَيْهِمُ ٱلذِّلَّةُ وَٱلْمَسْكَنَةُ وَبَآءُو بِغَضَبٍ مِّنَ ٱللَّهِ ۗ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمْ كَانُوا۟ يَكْفُرُونَ بِـَٔايَـٰتِ ٱللَّهِ وَيَقْتُلُونَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ بِغَيْرِ ٱلْحَقِّ ۗ ذَٰلِكَ بِمَا عَصَوا۟ وَّكَانُوا۟ يَعْتَدُونَ۝٦١

    Waith qultum ya moosa lan nasbira ʿala taʿamin wahidin faodʿu lana rabbaka yukhrij lana mimma tunbitu alardu min baqliha waqiththaiha wafoomiha waʿadasiha wabasaliha qala atastabdiloona allathee huwa adna biallathee huwa khayrun ihbitoo misran fainna lakum ma saaltum waduribat ʿalayhimu alththillatu waalmaskanatu wabaoo bighadabin mina Allahi thalika biannahum kanoo yakfuroona biayati Allahi wayaqtuloona alnnabiyyeena bighayri alhaqqi thalika bima ʿasaw wakanoo yaʿtadoona

    Kuma a lõkacin da kuka ce: "Yã Mũsã! Bã zã mu yi haƙuri ba a kan abinci guda. Sai ka rõƙa mana Ubangijinka Ya fitar mana daga abin da ƙasa take tsirarwa daga ganyenta, dumanta, da alkamarta da albasarta. Ya ce: "Kuna nẽman musanya abin da yake mafi ƙasƙanci da wanda yake mafi alhẽri? Ku sauka wani birni (daga cikin birane), lalle ne, kuna da abin da kuka rõƙa. "Kuma Muka dõka musu walãƙanci da talauci. Kuma suka kõma da wani fushi daga Allah. Wancan sabõda lalle su, sun kasance suna kãfirta da ãyõyin Allah, kuma suna kashe Aannabãwa, bãda hakki ba. Wancan, sabõda sãɓawarsu ne, kuma sun kasance suna ƙẽtarewar haddi.

  62. إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَٱلَّذِينَ هَادُوا۟ وَٱلنَّصَـٰرَىٰ وَٱلصَّـٰبِـِٔينَ مَنْ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَٱلْيَوْمِ ٱلْـَٔاخِرِ وَعَمِلَ صَـٰلِحًا فَلَهُمْ أَجْرُهُمْ عِندَ رَبِّهِمْ وَلَا خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلَا هُمْ يَحْزَنُونَ۝٦٢

    Inna allatheena amanoo waallatheena hadoo waalnnasara waalssabieena man amana biAllahi waalyawmi alakhiri waʿamila salihan falahum ajruhum ʿinda rabbihim wala khawfun ʿalayhim wala hum yahzanoona

    Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, da waɗanda suka tũba1, da Nasãra da Makarkata, wana ya yi ĩmani da Allah da Yinin Lãhira, kuma ya aikata aikin ƙwarai, to, suna da ijãrarsu a wurin Ubangijinsu, kuma bãbu tsõro a kansu, kuma ba su zama suna yin baƙin ciki ba.

    Bayanai
    [1] Waɗanda suka koma, watau Yahũdu, daga maganar Mũsa, "Mun kõma garesu" Sura ta 7 aya ta 156, kuma Makarkata, jama'a ce daga Lãrabãwa suka karkata daga addĩnin ubanninsu zuwa ga bauta wa malã'iku. A farkon Musulunci sunã cewa ga wanda ya musulunta, wai ya yi kama da su.
  63. وَإِذْ أَخَذْنَا مِيثَـٰقَكُمْ وَرَفَعْنَا فَوْقَكُمُ ٱلطُّورَ خُذُوا۟ مَآ ءَاتَيْنَـٰكُم بِقُوَّةٍ وَٱذْكُرُوا۟ مَا فِيهِ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ۝٦٣

    Waith akhathna meethaqakum warafaʿna fawqakumu alttoora khuthoo ma ataynakum biquwwatin waothkuroo ma feehi laʿallakum tattaqoona

    Kuma a lõkacin da Muka riƙi alƙawarinku, kuma Muka ɗaukaka dũtse a bisa gareku: "Ku kãma abin da Muka baku da ƙarfi. Kuma ku ambaci abin da yake a cikin sa, tsammãninku ku kãrekanku.

  64. ثُمَّ تَوَلَّيْتُم مِّنۢ بَعْدِ ذَٰلِكَ ۖ فَلَوْلَا فَضْلُ ٱللَّهِ عَلَيْكُمْ وَرَحْمَتُهُۥ لَكُنتُم مِّنَ ٱلْخَـٰسِرِينَ۝٦٤

    Thumma tawallaytum min baʿdi thalika falawla fadlu Allahi ʿalaykum warahmatuhu lakuntum mina alkhasireena

    Sa'an nan kuma kuka jũya daga bayan wancan, to, bã dõmin falalar Allah ba da rahamarSa a kanku, haƙĩƙa, dã kun kasance daga mãsu hasãra."

  65. وَلَقَدْ عَلِمْتُمُ ٱلَّذِينَ ٱعْتَدَوْا۟ مِنكُمْ فِى ٱلسَّبْتِ فَقُلْنَا لَهُمْ كُونُوا۟ قِرَدَةً خَـٰسِـِٔينَ۝٦٥

    Walaqad ʿalimtumu allatheena iʿtadaw minkum fee alssabti faqulna lahum koonoo qiradatan khasieena

    Kuma lalle ne, haƙĩƙa, kun san waɗanda suka ƙẽtare haddi daga gare ku a cikin Asabar, sai muka ce musu: "ku kasance birai ƙasƙantattu."

  66. فَجَعَلْنَـٰهَا نَكَـٰلًا لِّمَا بَيْنَ يَدَيْهَا وَمَا خَلْفَهَا وَمَوْعِظَةً لِّلْمُتَّقِينَ۝٦٦

    Fajaʿalnaha nakalan lima bayna yadayha wama khalfaha wamawʿithatan lilmuttaqeena

    Muka sanya ta (mas'alar) azãba, dõmin abin da yake gaba gareta, da yake a bãyanta, kuma wa'azi ga mãsu taƙawa.

  67. وَإِذْ قَالَ مُوسَىٰ لِقَوْمِهِۦٓ إِنَّ ٱللَّهَ يَأْمُرُكُمْ أَن تَذْبَحُوا۟ بَقَرَةً ۖ قَالُوٓا۟ أَتَتَّخِذُنَا هُزُوًا ۖ قَالَ أَعُوذُ بِٱللَّهِ أَنْ أَكُونَ مِنَ ٱلْجَـٰهِلِينَ۝٦٧

    Waith qala moosa liqawmihi inna Allaha yamurukum an tathbahoo baqaratan qaloo atattakhithuna huzuwan qala aʿoothu biAllahi an akoona mina aljahileena

    Kuma a lõkacin da Musa yace ga mutanensa: "Lalle ne, Allah Yana umurtar ku da ku yanka wata sãniya." Suka ce: "Shin kana riƙon mu ne da izgili?" Ya ce: "Ina nẽman tsari daga Allah da in kasance daga jãhilai."

  68. قَالُوا۟ ٱدْعُ لَنَا رَبَّكَ يُبَيِّن لَّنَا مَا هِىَ ۚ قَالَ إِنَّهُۥ يَقُولُ إِنَّهَا بَقَرَةٌ لَّا فَارِضٌ وَلَا بِكْرٌ عَوَانٌۢ بَيْنَ ذَٰلِكَ ۖ فَٱفْعَلُوا۟ مَا تُؤْمَرُونَ۝٦٨

    Qaloo odʿu lana rabbaka yubayyin lana ma hiya qala innahu yaqoolu innaha baqaratun la faridun wala bikrun ʿawanun bayna thalika faifʿaloo ma tumaroona

    Suka ce: "Ka rõƙa mana Ubangijinka, Ya bayyana mana, mecẽ ce ita?" Ya ce: "Lalle ne, Shi, Yana cewa: "Lalle ne ita sãniya ce; bã tsõfuwa ba, bã kuma budurwa ba, tsakãtsaki ce a tsakãnin wancan,' sai ku aikata abin da ake umurninku."

  69. قَالُوا۟ ٱدْعُ لَنَا رَبَّكَ يُبَيِّن لَّنَا مَا لَوْنُهَا ۚ قَالَ إِنَّهُۥ يَقُولُ إِنَّهَا بَقَرَةٌ صَفْرَآءُ فَاقِعٌ لَّوْنُهَا تَسُرُّ ٱلنَّـٰظِرِينَ۝٦٩

    Qaloo odʿu lana rabbaka yubayyin lana ma lawnuha qala innahu yaqoolu innaha baqaratun safrao faqiʿun lawnuha tasurru alnnathireena

    Suka ce: "Ka rõƙa mana Ubangijinka Ya bayyana mana abin da yake launinta." Ya ce: "Lalle ne, Shi Yana cewa: "Ita wata saniya ce fatsa-fatsa, mai tsan-tsan launi, tana faranta ran mausu kallonta."

  70. قَالُوا۟ ٱدْعُ لَنَا رَبَّكَ يُبَيِّن لَّنَا مَا هِىَ إِنَّ ٱلْبَقَرَ تَشَـٰبَهَ عَلَيْنَا وَإِنَّآ إِن شَآءَ ٱللَّهُ لَمُهْتَدُونَ۝٧٠

    Qaloo odʿu lana rabbaka yubayyin lana ma hiya inna albaqara tashabaha ʿalayna wainna in shaa Allahu lamuhtadoona

    Suka ce: "Ka rõƙa mana Ubangijinka, Ya bayyana mana abin da yake ita, lalle ne shãnu suna yi mana kamã da jũna, kuma mu, idan Allah Yã so, haƙĩƙa, shiryuwa ne."

  71. قَالَ إِنَّهُۥ يَقُولُ إِنَّهَا بَقَرَةٌ لَّا ذَلُولٌ تُثِيرُ ٱلْأَرْضَ وَلَا تَسْقِى ٱلْحَرْثَ مُسَلَّمَةٌ لَّا شِيَةَ فِيهَا ۚ قَالُوا۟ ٱلْـَٔـٰنَ جِئْتَ بِٱلْحَقِّ ۚ فَذَبَحُوهَا وَمَا كَادُوا۟ يَفْعَلُونَ۝٧١

    Qala innahu yaqoolu innaha baqaratun la thaloolun tutheeru alarda wala tasqee alhartha musallamatun la shiyata feeha qaloo alana jita bialhaqqi fathabahooha wama kadoo yafʿaloona

    Ya ce: "Lalle ne Shi, Yana cẽwa: "Ita wata sãniya ce; ba horarra bã tana noman ƙasa, kuma ba ta shayar da shuka, lãfiyayya ce: bãbu wani sõfane a cikinta." Suka ce: "Yanzu kã zo da gaskiya. Sai suka yanka ta, kamar ba zã su aikata ba.

  72. وَإِذْ قَتَلْتُمْ نَفْسًا فَٱدَّٰرَْٰٔتُمْ فِيهَا ۖ وَٱللَّهُ مُخْرِجٌ مَّا كُنتُمْ تَكْتُمُونَ۝٧٢

    Waith qataltum nafsan faiddaratum feeha waAllahu mukhrijun ma kuntum taktumoona

    Kuma a lõkacin da kuka yi kisan kai, kuka dinga tunkuɗa wa jũna laifĩ a cikinsa,1 kuma Allah Mai fitar da abin da kuka kasance kuna ɓõyẽwa ne.

    Bayanai
    [1] Asalin ƙissar, wani mutum ne mai arziƙi da yawa daga cikin Banĩ Isra'ĩla amma bã shida magaji sai ɗan ɗan'uwan sa. Saboda yayi gãdo, sai ya kashe shi da dare, ya kuma ɗauke shi ya ajiye shi a bakin ƙofar wani mutum, a cikin su. Da safiyã ta wãye, sai suka tãshi dõmin su yi faɗa a tsakãnin dangin wanda aka kashe da dangin wanda aka same shi a ƙofarsu, sa'an nan suka haɗa ra'ayi ga su kai ƙãra ga Manzon Allah, Mũsã. Suka isa gareshi, suka ba shi lãbãrin. Sai yace musu: "Lalle ne, Allah Yã ce: "Ku yanka wata sãniya." Da sun yanke kõwace irin sãniya da buƙãtarsu ta biya musu, amma sai suka yi ta yin tambayoyi ana bã su amsa, kuma yanã ƙãra yi musu wuyã, har suka kai ga a sifantã musu sãniyar yãro mai ɗã'a ga uwarsa wadda aka ce: bã zã a sayar musu da ita ba sai da zĩnãriya cike da fãtarta ko dai dai da nauyinta sau gõma. Bayan sun saye ta suka yanka ta sai Mũsã ya ce musu, su dõki wanda aka kashen nan da wani juzu'i nata. Suka dõke shi da ƙashin ta kõ harshenta, sai ya tãshi ya ce: "Wane ɗan ɗan'uwãna, ya kasheni." Sai suka kãma wanda ya yi kisar suka kashe shi. Tartĩbin Alƙur'ãni ya yi ishara da mas'alar tsaurin kan Banĩ Isra'ila da hikimar bin umurnin Allah, da ĩkon tãyar da matattu da gaskiyar Wahayin Annabawa, da asiran da Allah ke sanyãwa a cikin wasu abũbuwa dõmin su zama sanadi ga aukuwar wasu, da yadda yake azurta mãsu yi masa ɗã'a, da sauran su duk a cikin ƙissa guda, ba da ya ambaci tsarin asalinta ba. Tsarki ya tabbata ga Allah.
  73. فَقُلْنَا ٱضْرِبُوهُ بِبَعْضِهَا ۚ كَذَٰلِكَ يُحْىِ ٱللَّهُ ٱلْمَوْتَىٰ وَيُرِيكُمْ ءَايَـٰتِهِۦ لَعَلَّكُمْ تَعْقِلُونَ۝٧٣

    Faqulna idriboohu bibaʿdiha kathalika yuhyee Allahu almawta wayureekum ayatihi laʿallakum taʿqiloona

    Sai Muka ce: "Ku dõke shi da wani sãshenta." Kamar wancan ne Allah Yake rãyar da matattu, kuma Ya nũna muku ayõyinSa, tsammãninku kuna hankalta.

  74. ثُمَّ قَسَتْ قُلُوبُكُم مِّنۢ بَعْدِ ذَٰلِكَ فَهِىَ كَٱلْحِجَارَةِ أَوْ أَشَدُّ قَسْوَةً ۚ وَإِنَّ مِنَ ٱلْحِجَارَةِ لَمَا يَتَفَجَّرُ مِنْهُ ٱلْأَنْهَـٰرُ ۚ وَإِنَّ مِنْهَا لَمَا يَشَّقَّقُ فَيَخْرُجُ مِنْهُ ٱلْمَآءُ ۚ وَإِنَّ مِنْهَا لَمَا يَهْبِطُ مِنْ خَشْيَةِ ٱللَّهِ ۗ وَمَا ٱللَّهُ بِغَـٰفِلٍ عَمَّا تَعْمَلُونَ۝٧٤

    Thumma qasat quloobukum min baʿdi thalika fahiya kaalhijarati aw ashaddu qaswatan wainna mina alhijarati lama yatafajjaru minhu alanharu wainna minha lama yashshaqqaqu fayakhruju minhu almao wainna minha lama yahbitu min khashyati Allahi wama Allahu bighafilin ʿamma taʿmaloona

    San nan kuma zukãtanku, suka ƙẽƙashe daga bãyan wancan. Sabõda haka suka zamanto kamar duwatsu. Ko mafi tsananin ƙeƙashewa. kuma lalle ne daga duwãtsu, haƙĩka, akwai abin da maremari suke ɓuɓɓuga daga gare shi, kuma lalle ne daga gare su, haƙĩƙa, akwai abin da yake tsatstsagewa har ruwa ya fita daga gare shi, kuma lalle ne, haƙĩƙa, daga gare su, haƙĩƙa, akwai da yake fãɗõwa dõmin tsõron Allah, kuma Allah bai zama gãfili ba daga barin abin da kuke aikatãwa.

  75. ۞ أَفَتَطْمَعُونَ أَن يُؤْمِنُوا۟ لَكُمْ وَقَدْ كَانَ فَرِيقٌ مِّنْهُمْ يَسْمَعُونَ كَلَـٰمَ ٱللَّهِ ثُمَّ يُحَرِّفُونَهُۥ مِنۢ بَعْدِ مَا عَقَلُوهُ وَهُمْ يَعْلَمُونَ۝٧٥

    Afatatmaʿoona an yuminoo lakum waqad kana fareequn minhum yasmaʿoona kalama Allahi thumma yuharrifoonahu min baʿdi ma ʿaqaloohu wahum yaʿlamoona

    Shin kuna tsammãnin zã su yi imãni sabõda ku, alhãli kuwa, haƙĩƙa, wata ƙungiya daga gare su sun kasance suna jin maganar Allah, sa'an nan kuma su karkatar da ita daga bãyan sun gãne ta, alhãli sũ, suna sane?

  76. وَإِذَا لَقُوا۟ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ قَالُوٓا۟ ءَامَنَّا وَإِذَا خَلَا بَعْضُهُمْ إِلَىٰ بَعْضٍ قَالُوٓا۟ أَتُحَدِّثُونَهُم بِمَا فَتَحَ ٱللَّهُ عَلَيْكُمْ لِيُحَآجُّوكُم بِهِۦ عِندَ رَبِّكُمْ ۚ أَفَلَا تَعْقِلُونَ۝٧٦

    Waitha laqoo allatheena amanoo qaloo amanna waitha khala baʿduhum ila baʿdin qaloo atuhaddithoonahum bima fataha Allahu ʿalaykum liyuhajjookum bihi ʿinda rabbikum afala taʿqiloona

    Kuma idan sun haɗu da waɗanda suka yi ĩmãni sukan ce: "Mun yi ĩmãni," kuma idan sãshensu ya wõfinta zuwa ga sãshe, sukan ce: "Shin, kuna yi musu magana da abin da Allah Ya buɗa muku ne dõmin su yi muku hujja da shi a wurin Ubangijinku?" Shin fa, bã ku hankalta?

  77. أَوَلَا يَعْلَمُونَ أَنَّ ٱللَّهَ يَعْلَمُ مَا يُسِرُّونَ وَمَا يُعْلِنُونَ۝٧٧

    Awala yaʿlamoona anna Allaha yaʿlamu ma yusirroona wama yuʿlinoona

    Shin, kuma bã su sanin cẽwa lalle ne Allah Yana sanin abin da suke ɓõyẽwa da abin da suke bayyanãwa?

  78. وَمِنْهُمْ أُمِّيُّونَ لَا يَعْلَمُونَ ٱلْكِتَـٰبَ إِلَّآ أَمَانِىَّ وَإِنْ هُمْ إِلَّا يَظُنُّونَ۝٧٨

    Waminhum ommiyyoona la yaʿlamoona alkitaba illa amaniyya wain hum illa yathunnoona

    Kuma daga cikin su akwai ummiyyai, bã su da sanin Littãfi, fãce tãtsuniyoyi, kuma sũ bã kõme suke yi ba fãce suna yin zato.

  79. فَوَيْلٌ لِّلَّذِينَ يَكْتُبُونَ ٱلْكِتَـٰبَ بِأَيْدِيهِمْ ثُمَّ يَقُولُونَ هَـٰذَا مِنْ عِندِ ٱللَّهِ لِيَشْتَرُوا۟ بِهِۦ ثَمَنًا قَلِيلًا ۖ فَوَيْلٌ لَّهُم مِّمَّا كَتَبَتْ أَيْدِيهِمْ وَوَيْلٌ لَّهُم مِّمَّا يَكْسِبُونَ۝٧٩

    Fawaylun lillatheena yaktuboona alkitaba biaydeehim thumma yaqooloona hatha min ʿindi Allahi liyashtaroo bihi thamanan qaleelan fawaylun lahum mimma katabat aydeehim wawaylun lahum mimma yaksiboona

    To, bone ya tabbata ga waɗanda suke rubũta littãfi da hannuwansu sa'an nan kuma su ce wannan daga wurin Allah yake, dõmin su sayi kuɗi kaɗan da shi, san nan bone ya tabbata a gare su daga abin da hannayensu ke rubũtãwa, kuma bone ya tabbata a gare su daga abin da suke sanã'antãwa.

  80. وَقَالُوا۟ لَن تَمَسَّنَا ٱلنَّارُ إِلَّآ أَيَّامًا مَّعْدُودَةً ۚ قُلْ أَتَّخَذْتُمْ عِندَ ٱللَّهِ عَهْدًا فَلَن يُخْلِفَ ٱللَّهُ عَهْدَهُۥٓ ۖ أَمْ تَقُولُونَ عَلَى ٱللَّهِ مَا لَا تَعْلَمُونَ۝٨٠

    Waqaloo lan tamassana alnnaru illa ayyaman maʿdoodatan qul attakhathtum ʿinda Allahi ʿahdan falan yukhlifa Allahu ʿahdahu am taqooloona ʿala Allahi ma la taʿlamoona

    Kuma suka ce: "Wuta bã zã ta shãfe mu ba, fãce, 'yan kwãnuka ƙidãyayyu."Ka ce: "Ashe kun riƙi wani alkawari a wurin Allah, sa'an nan Allah ba zai sãɓa wa alkawarinSa ba ko kuwa kuna faɗin abin da ba ku sani ba bisa ga Allah?"

  81. بَلَىٰ مَن كَسَبَ سَيِّئَةً وَأَحَـٰطَتْ بِهِۦ خَطِيٓـَٔتُهُۥ فَأُو۟لَـٰٓئِكَ أَصْحَـٰبُ ٱلنَّارِ ۖ هُمْ فِيهَا خَـٰلِدُونَ۝٨١

    Bala man kasaba sayyiatan waahatat bihi khateeatuhu faolaika ashabu alnnari hum feeha khalidoona

    Na'am! Wanda ya yi tsiwur-wurin mũgun abu, kuma laifinsa ya kẽwaye shi, to, waɗannan su ne 'yan Wuta, sũ a cikinta madawwama ne.

  82. وَٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ أُو۟لَـٰٓئِكَ أَصْحَـٰبُ ٱلْجَنَّةِ ۖ هُمْ فِيهَا خَـٰلِدُونَ۝٨٢

    Waallatheena amanoo waʿamiloo alssalihati olaika ashabu aljannati hum feeha khalidoona

    Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, waɗannan, 'yan Aljanna ne, sũ a cikinta madawwama ne.

  83. وَإِذْ أَخَذْنَا مِيثَـٰقَ بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ لَا تَعْبُدُونَ إِلَّا ٱللَّهَ وَبِٱلْوَٰلِدَيْنِ إِحْسَانًا وَذِى ٱلْقُرْبَىٰ وَٱلْيَتَـٰمَىٰ وَٱلْمَسَـٰكِينِ وَقُولُوا۟ لِلنَّاسِ حُسْنًا وَأَقِيمُوا۟ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُوا۟ ٱلزَّكَوٰةَ ثُمَّ تَوَلَّيْتُمْ إِلَّا قَلِيلًا مِّنكُمْ وَأَنتُم مُّعْرِضُونَ۝٨٣

    Waith akhathna meethaqa banee israeela la taʿbudoona illa Allaha wabialwalidayni ihsanan wathee alqurba waalyatama waalmasakeeni waqooloo lilnnasi husnan waaqeemoo alssalata waatoo alzzakata thumma tawallaytum illa qaleelan minkum waantum muʿridoona

    Kuma a lõkacin da Muka karɓi alkawarin Bani-Isrã'ĩla1: "Kada ku bauta wa kõwa fãce Allah, kuma ga mahaifa ku kyautata, da mai zumunta da marãyu da matalauta, kuma ku faɗi magana mai kyau zuwa ga mutãne, kuma ku tsayar da salla, kuma ku bãyar da zakka, sa'an nan kuka jũya bãya, fãce kaɗan daga gare ku, alhãli kuwa kuna mãsu bijirẽwa.

    Bayanai
    [1] Tunãtar da Banĩ Isrã'ĩla alkawurra gõma da Allah Yã yi da Mũsã a cikin Attaura a kansu. Na farko bã zã su bauta wa kõwa ba fãce Allah. Na biyu kyautata wa iyãye da dangi da marãyu da matalauta. Na uku, faɗin magana mai kyau zuwa ga mutãne. Na huɗu, tsayar da salla. Nabiyar, bãyar da zakka. Na shida, bã zã a kashe rai bãbu hakki na sharĩ'a ba. Na bakwai, bã zã a fitar da kõwa daga gidansa ba. Na takwas, bã zã a taimaki azzãlumi a kan zãluncinsa ba. Na tara, idan abõkan gãbã sun kãma wani daga cikinsu, su yi fansarsa. Nagõma, ɗã'a ga kõwane Manzon Allah wanda bai sãɓãwa Attaura ba ga aƙida.
  84. وَإِذْ أَخَذْنَا مِيثَـٰقَكُمْ لَا تَسْفِكُونَ دِمَآءَكُمْ وَلَا تُخْرِجُونَ أَنفُسَكُم مِّن دِيَـٰرِكُمْ ثُمَّ أَقْرَرْتُمْ وَأَنتُمْ تَشْهَدُونَ۝٨٤

    Waith akhathna meethaqakum la tasfikoona dimaakum wala tukhrijoona anfusakum min diyarikum thumma aqrartum waantum tashhadoona

    Lõkacin da Muka riƙi alkawarinku; bã zã ku zubar da jininku ba, kuma bã zã ku fitar da kanku daga gidãjenku ba; sa'an nan kuka tabbatar alhãli kuwa kuna bãyar da shaida (a kanku).

  85. ثُمَّ أَنتُمْ هَـٰٓؤُلَآءِ تَقْتُلُونَ أَنفُسَكُمْ وَتُخْرِجُونَ فَرِيقًا مِّنكُم مِّن دِيَـٰرِهِمْ تَظَـٰهَرُونَ عَلَيْهِم بِٱلْإِثْمِ وَٱلْعُدْوَٰنِ وَإِن يَأْتُوكُمْ أُسَـٰرَىٰ تُفَـٰدُوهُمْ وَهُوَ مُحَرَّمٌ عَلَيْكُمْ إِخْرَاجُهُمْ ۚ أَفَتُؤْمِنُونَ بِبَعْضِ ٱلْكِتَـٰبِ وَتَكْفُرُونَ بِبَعْضٍ ۚ فَمَا جَزَآءُ مَن يَفْعَلُ ذَٰلِكَ مِنكُمْ إِلَّا خِزْىٌ فِى ٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا ۖ وَيَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ يُرَدُّونَ إِلَىٰٓ أَشَدِّ ٱلْعَذَابِ ۗ وَمَا ٱللَّهُ بِغَـٰفِلٍ عَمَّا تَعْمَلُونَ۝٨٥

    Thumma antum haolai taqtuloona anfusakum watukhrijoona fareeqan minkum min diyarihim tathaharoona ʿalayhim bialithmi waalʿudwani wain yatookum osara tufadoohum wahuwa muharramun ʿalaykum ikhrajuhum afatuminoona bibaʿdi alkitabi watakfuroona bibaʿdin fama jazao man yafʿalu thalika minkum illa khizyun fee alhayati alddunya wayawma alqiyamati yuraddoona ila ashaddi alʿathabi wama Allahu bighafilin ʿamma taʿmaloona

    Sa'an nan kuma, gã ku, yã waɗannan! Kuna kashe kanku, kuma kuna fitar da wani ɓangare daga gare ku daga gidãjensu, kuna taimakon jũna a kansu da zunubi da zãlunci kuma idan kãmammu suka je muku kuna fansarsu alhãli kuwa shĩ fitar da su abin da aka haramta muku ne. Shin fa, kuna ĩmãni da sãshen Littãfin ne, kuma ku kãfirta da sãshe? To, mẽne ne sakamakon wanda ke aikata wancan daga gare ku fãce wulãkanci1 a cikin rãyuwar dũniya? Kuma a Rãnar ¡iyãma ana mayar da su zuwa ga mafi tsananin azãba. Kuma Allah bai zama Mai gafala ba daga barin abin da kuke aikatãwa.

    Bayanai
    [1] Aiki da sãshen wasu abũbuwa na addini da barin wasu kãfirci ne mai wajabta wulãƙanci a kan Musulmi.
  86. أُو۟لَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ ٱشْتَرَوُا۟ ٱلْحَيَوٰةَ ٱلدُّنْيَا بِٱلْـَٔاخِرَةِ ۖ فَلَا يُخَفَّفُ عَنْهُمُ ٱلْعَذَابُ وَلَا هُمْ يُنصَرُونَ۝٨٦

    Olaika allatheena ishtarawoo alhayata alddunya bialakhirati fala yukhaffafu ʿanhumu alʿathabu wala hum yunsaroona

    Waɗan nan su ne waɗan da suka sayi rãyuwar dũniya da Lãhira, dõmin haka bã zã a sauƙaƙa azãba ba daga kansu, kuma sũ, bã ataimakonsu.

  87. وَلَقَدْ ءَاتَيْنَا مُوسَى ٱلْكِتَـٰبَ وَقَفَّيْنَا مِنۢ بَعْدِهِۦ بِٱلرُّسُلِ ۖ وَءَاتَيْنَا عِيسَى ٱبْنَ مَرْيَمَ ٱلْبَيِّنَـٰتِ وَأَيَّدْنَـٰهُ بِرُوحِ ٱلْقُدُسِ ۗ أَفَكُلَّمَا جَآءَكُمْ رَسُولٌۢ بِمَا لَا تَهْوَىٰٓ أَنفُسُكُمُ ٱسْتَكْبَرْتُمْ فَفَرِيقًا كَذَّبْتُمْ وَفَرِيقًا تَقْتُلُونَ۝٨٧

    Walaqad atayna moosa alkitaba waqaffayna min baʿdihi bialrrusuli waatayna ʿeesa ibna maryama albayyinati waayyadnahu biroohi alqudusi afakullama jaakum rasoolun bima la tahwa anfusukumu istakbartum fafareeqan kaththabtum wafareeqan taqtuloona

    Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Munbai wa Mũsã Littãfi, kuma Mun biyar daga bãyansa da wasu Manzanni, kuma Muka bai wa Ĩsã ɗan Maryama hujjõji bayyanannu, kuma Muka ƙarfafa shi da Rũhi mai tsarki1. Shinfa, kõ da yaushe wani manzo ya je muku tãre da abin da rãyukanku bã su so, sai ku kangara, wani ɓangare kun ƙaryata, kuma wani ɓangare kuna kashẽwa?

    Bayanai
    [1] Rũhul Kuds; watau ran tsarki kõ rai mai tsarki, shi ne Jibirilu, amincin Allah ya tabbata a gare Shi. Ya zauna tãre da Ĩsã inda duk yake sunã tãre. Ãyõyin da aka bai wa Ĩsã sũ ne rãyar da matattu da warkar da kutãre da makãfi da marasa lãfiya. Wannan ya sanya cewa mãsu da'awar bin sa suka fito da aikin maristan, watau asibiti.
  88. وَقَالُوا۟ قُلُوبُنَا غُلْفٌۢ ۚ بَل لَّعَنَهُمُ ٱللَّهُ بِكُفْرِهِمْ فَقَلِيلًا مَّا يُؤْمِنُونَ۝٨٨

    Waqaloo quloobuna ghulfun bal laʿanahumu Allahu bikufrihim faqaleelan ma yuminoona

    Kuma suka ce: "Zukatanmu suna cikin rufi." A'a, Allah Yã la'ane su, dõmin kafircinsu kadan kwarai suke yin ĩmãni!

  89. وَلَمَّا جَآءَهُمْ كِتَـٰبٌ مِّنْ عِندِ ٱللَّهِ مُصَدِّقٌ لِّمَا مَعَهُمْ وَكَانُوا۟ مِن قَبْلُ يَسْتَفْتِحُونَ عَلَى ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ فَلَمَّا جَآءَهُم مَّا عَرَفُوا۟ كَفَرُوا۟ بِهِۦ ۚ فَلَعْنَةُ ٱللَّهِ عَلَى ٱلْكَـٰفِرِينَ۝٨٩

    Walamma jaahum kitabun min ʿindi Allahi musaddiqun lima maʿahum wakanoo min qablu yastaftihoona ʿala allatheena kafaroo falamma jaahum ma ʿarafoo kafaroo bihi falaʿnatu Allahi ʿala alkafireena

    Kuma a lõkacin da wani Littãfi daga wurin Allah ya je musu, mai gaskatãwa ga abin da yake tãre da su, alhãli kuwa sun kasance daga gabãnin haka suna fãtar taimako1 da shi a kan waɗanda suka kãfirta. To, a lõkacin da abin da suka sani ya je musu, sai suka kãfirta da shi. Sabõda haka la'anar Allah ta tabbata a kan kãfirai.

    Bayanai
    [1] Sunã cewa idan Annabin ƙarshen zãmaninsa ya zo, zã su yãƙi kãfiran Lãrabãwa da shi. Sunã zaton a cikinsu zai ɓullo. Sai ya fito a cikin Lãrabãwan.
  90. بِئْسَمَا ٱشْتَرَوْا۟ بِهِۦٓ أَنفُسَهُمْ أَن يَكْفُرُوا۟ بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ بَغْيًا أَن يُنَزِّلَ ٱللَّهُ مِن فَضْلِهِۦ عَلَىٰ مَن يَشَآءُ مِنْ عِبَادِهِۦ ۖ فَبَآءُو بِغَضَبٍ عَلَىٰ غَضَبٍ ۚ وَلِلْكَـٰفِرِينَ عَذَابٌ مُّهِينٌ۝٩٠

    Bisama ishtaraw bihi anfusahum an yakfuroo bima anzala Allahu baghyan an yunazzila Allahu min fadlihi ʿala man yashao min ʿibadihi fabaoo bighadabin ʿala ghadabin walilkafireena ʿathabun muheenun

    Tir, da abin da suka sayi rãyukansu da shi; watau su kãfirta da abin da Allah Ya saukar sabõda zãlunci;1 kada Allah Ya saukar da falalarsa a kan wanda Yake so daga bãyinsa. Sai suka kõmo da fushi game da wani fushi. Kuma ga kãfirai akwai azãba mai wulãƙantarwa.

    Bayanai
    [1] Bisa ga zãlunci, watau hãsada. Sun yi hãsadar Allah Ya saukar da abin da Yake so na falalarSa a kan wanda Yake so, shi ne Muhammadu, a cikin Lãrabãwa.
  91. وَإِذَا قِيلَ لَهُمْ ءَامِنُوا۟ بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ قَالُوا۟ نُؤْمِنُ بِمَآ أُنزِلَ عَلَيْنَا وَيَكْفُرُونَ بِمَا وَرَآءَهُۥ وَهُوَ ٱلْحَقُّ مُصَدِّقًا لِّمَا مَعَهُمْ ۗ قُلْ فَلِمَ تَقْتُلُونَ أَنۢبِيَآءَ ٱللَّهِ مِن قَبْلُ إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ۝٩١

    Waitha qeela lahum aminoo bima anzala Allahu qaloo numinu bima onzila ʿalayna wayakfuroona bima waraahu wahuwa alhaqqu musaddiqan lima maʿahum qul falima taqtuloona anbiyaa Allahi min qablu in kuntum mumineena

    Kuma idan aka ce musu: "Ku yi ĩmãni da abin da Allah Ya saukar." Sai su ce: "Muna ĩmãni da abin da aka saukar a gare mu," kuma suna kãfircẽwa da abin da ke bãyansa, alhãli kuwa, shi ne gaskiyar (da suka sani) mai gaskatawa ga abin da yake tãre da su (na Attaura) Ka ce: "To, don me kuke kashe annabãwan Allah gabãnin wannan, idan kun kasance mãsu bãyar da gaskiya?"1

    Bayanai
    [1] Waɗannan Annabãwan da kuka kashe ko kuka ƙaryata a cikinku suke kũ ne aka saukar wa da abin da aka bã su, sabõda haka da'awarku ta cewa kunã ĩmãni da abin da aka saukar muku ƙarya ce.
  92. ۞ وَلَقَدْ جَآءَكُم مُّوسَىٰ بِٱلْبَيِّنَـٰتِ ثُمَّ ٱتَّخَذْتُمُ ٱلْعِجْلَ مِنۢ بَعْدِهِۦ وَأَنتُمْ ظَـٰلِمُونَ۝٩٢

    Walaqad jaakum moosa bialbayyinati thumma ittakhathtumu alʿijla min baʿdihi waantum thalimoona

    Kuma lalle ne haƙĩƙa Mũsã ya zo muku da hujjõji bayyanannu, sa'an nan kuka riƙi maraƙi1 (daga bãyansa, alhãli kuwa kuna mãsu zãlunci.

    Bayanai
    [1] Riƙo A nan ma'anarsa bautawa; watau kõmãwa ga maraƙi da ibãda, ku bar Allah, bãyan Musa ya nuna muku ãyõyin Allah, yana ƙãra ƙaryata maganarku, ta cewa kunã yin ĩmãni da abin da aka saukar muku kawai. Dã kunã yin ĩmãni da abin da aka saukar muku, dã waɗannan abubuwa ba su auku ba daga gare ku.
  93. وَإِذْ أَخَذْنَا مِيثَـٰقَكُمْ وَرَفَعْنَا فَوْقَكُمُ ٱلطُّورَ خُذُوا۟ مَآ ءَاتَيْنَـٰكُم بِقُوَّةٍ وَٱسْمَعُوا۟ ۖ قَالُوا۟ سَمِعْنَا وَعَصَيْنَا وَأُشْرِبُوا۟ فِى قُلُوبِهِمُ ٱلْعِجْلَ بِكُفْرِهِمْ ۚ قُلْ بِئْسَمَا يَأْمُرُكُم بِهِۦٓ إِيمَـٰنُكُمْ إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ۝٩٣

    Waith akhathna meethaqakum warafaʿna fawqakumu alttoora khuthoo ma ataynakum biquwwatin waismaʿoo qaloo samiʿna waʿasayna waoshriboo fee quloobihimu alʿijla bikufrihim qul bisama yamurukum bihi eemanukum in kuntum mumineena

    Kuma a lõkacin da Muka riƙi1 alkawarinku kuma Muka ɗaukaka dutse a bisa gare ku, (Muka ce:) "Ku riƙi abin da Muka kãwo muku da ƙarfi kuma ku ji" Suka ce: "Mun ji kuma mun ƙi." Kuma aka zuba son maraƙin a cikin zukatansu sabõda kãfircinsu. Ka ce: "Tir da abin da ĩmãninku yake umurnin ku da shi, har idan kun kasance mãsu ĩmãni!"

    Bayanai
    [1] A lõkacin da aka bã su Attaura sai suka ƙi aiki da ita sai da aka ɓamɓari dutse aka ɗaukaka shi sama a kansu, idan ba su yi aiki da ita ba ya fãɗa kansu. Sai suka karɓa, sa'an nan daga bãya kuma suka warware dõmin haka Ya ce: "Suka ce: Mun jiya kuma mun ƙiya." Hãsali dai Yahũdu sun ƙi aiki da Littãfinsu, Attaura.
  94. قُلْ إِن كَانَتْ لَكُمُ ٱلدَّارُ ٱلْـَٔاخِرَةُ عِندَ ٱللَّهِ خَالِصَةً مِّن دُونِ ٱلنَّاسِ فَتَمَنَّوُا۟ ٱلْمَوْتَ إِن كُنتُمْ صَـٰدِقِينَ۝٩٤

    Qul in kanat lakumu alddaru alakhiratu ʿinda Allahi khalisatan min dooni alnnasi fatamannawoo almawta in kuntum sadiqeena

    Ka ce: "Idan Gidan Lãhira ya kasance sabõda ku ku ne kadai, a wurin Allah babu sauran mutãne, to, ku yi bũrin mutuwa, idan kun kasance mãsu gaskiya1 ."

    Bayanai
    [1] Ya shiga bãyanin ruɗuwar Yahũdu, da alfahari da iyãye, ya sanyã su har suka gina ransu, cewa sũ ne mafifitan mutãne a wurin Allah.
  95. وَلَن يَتَمَنَّوْهُ أَبَدًۢا بِمَا قَدَّمَتْ أَيْدِيهِمْ ۗ وَٱللَّهُ عَلِيمٌۢ بِٱلظَّـٰلِمِينَ۝٩٥

    Walan yatamannawhu abadan bima qaddamat aydeehim waAllahu ʿaleemun bialththalimeena

    Kuma bã zã su yi gũrinta ba har abada sabõda abin da hannayensu, suka gabãtar. Kuma Allah Masani ne ga azzãlumai.

  96. وَلَتَجِدَنَّهُمْ أَحْرَصَ ٱلنَّاسِ عَلَىٰ حَيَوٰةٍ وَمِنَ ٱلَّذِينَ أَشْرَكُوا۟ ۚ يَوَدُّ أَحَدُهُمْ لَوْ يُعَمَّرُ أَلْفَ سَنَةٍ وَمَا هُوَ بِمُزَحْزِحِهِۦ مِنَ ٱلْعَذَابِ أَن يُعَمَّرَ ۗ وَٱللَّهُ بَصِيرٌۢ بِمَا يَعْمَلُونَ۝٩٦

    Walatajidannahum ahrasa alnnasi ʿala hayatin wamina allatheena ashrakoo yawaddu ahaduhum law yuʿammaru alfa sanatin wama huwa bimuzahzihihi mina alʿathabi an yuʿammara waAllahu baseerun bima yaʿmaloona

    Kuma lalle ne, zã ka sãme su mafiya kwaɗayin mutãne a kan rãyuwa, kuma sũ ne mafiya kwaɗayin rãyuwa daga waɗanda suka yi shirka. ¦ayansu yana son dã zã a rãyar da shi shekara dubu, kuma bã ya zama mai nĩsantar da shi daga azãba dõmin an rãyar da shi. Kuma Allah, Mai gani ne ga abin da suke aikatãwa.

  97. قُلْ مَن كَانَ عَدُوًّا لِّجِبْرِيلَ فَإِنَّهُۥ نَزَّلَهُۥ عَلَىٰ قَلْبِكَ بِإِذْنِ ٱللَّهِ مُصَدِّقًا لِّمَا بَيْنَ يَدَيْهِ وَهُدًى وَبُشْرَىٰ لِلْمُؤْمِنِينَ۝٩٧

    Qul man kana ʿaduwwan lijibreela fainnahu nazzalahu ʿala qalbika biithni Allahi musaddiqan lima bayna yadayhi wahudan wabushra lilmumineena

    Ka ce: Wanda ya1 kasance maƙiyi ga Jibirilu, to, lalle ne shi ya saukar da shi a kan zũciyarka da izinin Allah, yana mai gaskatãwa ga abin da yake gaba gare shi, kuma da shiriya da bishãra ga mũminai.

    Bayanai
    [1] Mai ƙin gaskiya kullum yanã neman dalĩlin da zai kãma ya zama wani uzuri a gare shi wajen ƙin aiki da gaskiyar. Yahũdu sunã cewa bã su son Jibirila dõmin shi ne ake aikõwa da azãba, yã halakar da Ãdãwa da Samũdãwa da mutãnen Luɗu, sunã nufin su ƙi abin da ya kãwo wa Annabi na Alƙur'ãni.
  98. مَن كَانَ عَدُوًّا لِّلَّهِ وَمَلَـٰٓئِكَتِهِۦ وَرُسُلِهِۦ وَجِبْرِيلَ وَمِيكَىٰلَ فَإِنَّ ٱللَّهَ عَدُوٌّ لِّلْكَـٰفِرِينَ۝٩٨

    Man kana ʿaduwwan lillahi wamalaikatihi warusulihi wajibreela wameekala fainna Allaha ʿaduwwun lilkafireena

    Wanda ya kasance maƙiyi ga Allah da malã'ikunSa da manzanninSa da Jibirĩla da Mĩkã'ĩla to, lalle ne, Allah Maƙiyi ne ga kãfirai.

  99. وَلَقَدْ أَنزَلْنَآ إِلَيْكَ ءَايَـٰتٍۭ بَيِّنَـٰتٍ ۖ وَمَا يَكْفُرُ بِهَآ إِلَّا ٱلْفَـٰسِقُونَ۝٩٩

    Walaqad anzalna ilayka ayatin bayyinatin wama yakfuru biha illa alfasiqoona

    Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun saukar, zuwa gare ka, ãyõyi bayyanannu, kuma ba wanda yake kãfirta da su fãce fãsikai.1

    Bayanai
    [1] Wannan ãya tana umurnin bin Alkur'ãni da aiki da shi kamar yadda ãyõyin da ke bin ta suke hana barin aiki da shi dõmin a kõma ga son zũciya kamar sihiri da surkulle waɗanda yake bin su kãfirci ne.
  100. أَوَكُلَّمَا عَـٰهَدُوا۟ عَهْدًا نَّبَذَهُۥ فَرِيقٌ مِّنْهُم ۚ بَلْ أَكْثَرُهُمْ لَا يُؤْمِنُونَ۝١٠٠

    Awakullama ʿahadoo ʿahdan nabathahu fareequn minhum bal aktharuhum la yuminoona

    Shin, kuma a kõ da yaushe suka ƙulla wani alkawari sai wani ɓangare daga gare su ya, yi jĩfa da shi? Ã'a, mafi yawansu bã su yin ĩmãni.

  101. وَلَمَّا جَآءَهُمْ رَسُولٌ مِّنْ عِندِ ٱللَّهِ مُصَدِّقٌ لِّمَا مَعَهُمْ نَبَذَ فَرِيقٌ مِّنَ ٱلَّذِينَ أُوتُوا۟ ٱلْكِتَـٰبَ كِتَـٰبَ ٱللَّهِ وَرَآءَ ظُهُورِهِمْ كَأَنَّهُمْ لَا يَعْلَمُونَ۝١٠١

    Walamma jaahum rasoolun min ʿindi Allahi musaddiqun lima maʿahum nabatha fareequn mina allatheena ootoo alkitaba kitaba Allahi waraa thuhoorihim kaannahum la yaʿlamoona

    Kuma a lõkacin da wani manzo (Muhammadu) daga wurin Allah ya je musu, mai gaskatãwa ga abin da yake tãre da su, sai wani ɓangare daga waɗanda aka bai wa Littãfi, suka yar da Littãfin (Alƙur'ãnin) Allah a bãyan bãyansu, kamar dai sũ ba su sani ba.

  102. وَٱتَّبَعُوا۟ مَا تَتْلُوا۟ ٱلشَّيَـٰطِينُ عَلَىٰ مُلْكِ سُلَيْمَـٰنَ ۖ وَمَا كَفَرَ سُلَيْمَـٰنُ وَلَـٰكِنَّ ٱلشَّيَـٰطِينَ كَفَرُوا۟ يُعَلِّمُونَ ٱلنَّاسَ ٱلسِّحْرَ وَمَآ أُنزِلَ عَلَى ٱلْمَلَكَيْنِ بِبَابِلَ هَـٰرُوتَ وَمَـٰرُوتَ ۚ وَمَا يُعَلِّمَانِ مِنْ أَحَدٍ حَتَّىٰ يَقُولَآ إِنَّمَا نَحْنُ فِتْنَةٌ فَلَا تَكْفُرْ ۖ فَيَتَعَلَّمُونَ مِنْهُمَا مَا يُفَرِّقُونَ بِهِۦ بَيْنَ ٱلْمَرْءِ وَزَوْجِهِۦ ۚ وَمَا هُم بِضَآرِّينَ بِهِۦ مِنْ أَحَدٍ إِلَّا بِإِذْنِ ٱللَّهِ ۚ وَيَتَعَلَّمُونَ مَا يَضُرُّهُمْ وَلَا يَنفَعُهُمْ ۚ وَلَقَدْ عَلِمُوا۟ لَمَنِ ٱشْتَرَىٰهُ مَا لَهُۥ فِى ٱلْـَٔاخِرَةِ مِنْ خَلَـٰقٍ ۚ وَلَبِئْسَ مَا شَرَوْا۟ بِهِۦٓ أَنفُسَهُمْ ۚ لَوْ كَانُوا۟ يَعْلَمُونَ۝١٠٢

    Waittabaʿoo ma tatloo alshshayateenu ʿala mulki sulaymana wama kafara sulaymanu walakinna alshshayateena kafaroo yuʿallimoona alnnasa alssihra wama onzila ʿala almalakayni bibabila haroota wamaroota wama yuʿallimani min ahadin hatta yaqoola innama nahnu fitnatun fala takfur fayataʿallamoona minhuma ma yufarriqoona bihi bayna almari wazawjihi wama hum bidarreena bihi min ahadin illa biithni Allahi wayataʿallamoona ma yadurruhum wala yanfaʿuhum walaqad ʿalimoo lamani ishtarahu ma lahu fee alakhirati min khalaqin walabisa ma sharaw bihi anfusahum law kanoo yaʿlamoona

    Kuma suka bi abin da shaiɗãnu1 ke karantawa a kan mulkin Sulaimãnu, kuma Sulaimãnu bai yi kãfirci ba, kuma Shaidãnun, sũ ne suka yi kãfirci, suna karantar da mutãne sihiri. Kuma ba a saukar da shi ba a kan malã'iku biyu a Bãbila, Harũta da Mãrũta. Kuma ba su sanar da kõwa ba balle su ce: "Mũ fitina kawai ne, sabõda haka kada ka kãfirta," balle har su yi ta nẽman ilmin abin da suke rarrabẽwa tsakãnin mutum da mãtarsa da shi daga gare su. Kuma su (mãsu yin sihirin) ba su zama mãsu cũtar da kõwa da shi ba, fãce da iznin Allah. Kuma suna nẽman ilmin abin da yake cũtar da su, kuma bã ya amfaninsu. Kuma lalle ne, haƙiƙa, sun sani, tabbas, wanda ya saye shi, bã ya da wani rabo a cikin Lãhira. Kuma tir da abin da suka sayar da rãyukansu da shi, dã sun kasance suna sani.

    Bayanai
    [1] Shaiɗan shi ne dukan wanda ya san gaskiya kuma ya ƙi yin aiki da ita, mutum ne kõ aljani. Sabõda haka a nan anã nufin miyagun malamai mãsu ɗauke mutãne daga abin da Allah Ya saukar musu na addini zuwa ga abin da suke so dõmin su cũce su. Hanyar ɗauke mutãne daga addinin gaskiya ita ce a wajen jingina magana ga wani mutum sãlihi wanda aka yarda da shi a bãyan yã mutu kamar Sulaimanu, kõ kuma a jingina ta ga wanda bã zã a iya tambayarsa ba kamar malã'iku. A wannan ãyã an jingina asalin sihiri ga Sulaimãnu aka ce da sihiri ya kai ga mulkinsa, kuma aka ce asalin sihirin nan ilmi ne daga Allah Ya saukar da shi ta kan wasu mala'iku biyu waɗanda suke a garin da ake ce wa Bãbila a ƙasar Iraƙ, anã kiransuHãrũta da Mãrũta waɗanda suke, kãfin su gayawa mai neman ilmin sihirin daga gare su abin da yake so, sai sun yi masa gargaɗi da cewa: "Kada ka yi kãfirci," sa'an nan su gaya masa abin dasuke iya raba miji da mãta da shi na sihiri. To, Allah Yã farkar da mu cewa Sulamiãnu bai yi sihiri ba, dõmin yin sihiri kãfirci ne. Sũ mãlaman mãsu faɗin haka, sũ ne suka yi kãfirci. Mai aiki da sihiri bai cũtar kõwa sai da iznin Allah. neman saninsa cũta ne, bãbu wani amfãni.
  103. وَلَوْ أَنَّهُمْ ءَامَنُوا۟ وَٱتَّقَوْا۟ لَمَثُوبَةٌ مِّنْ عِندِ ٱللَّهِ خَيْرٌ ۖ لَّوْ كَانُوا۟ يَعْلَمُونَ۝١٠٣

    Walaw annahum amanoo waittaqaw lamathoobatun min ʿindi Allahi khayrun law kanoo yaʿlamoona

    Kuma dã lalle ne sũ, sun yi ĩmani, kuma sun yi taƙawa, haƙiƙa, da sakamako daga wurin Allah shi ne mafi alhẽri, dã sun kasance suna sani.

  104. يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ لَا تَقُولُوا۟ رَٰعِنَا وَقُولُوا۟ ٱنظُرْنَا وَٱسْمَعُوا۟ ۗ وَلِلْكَـٰفِرِينَ عَذَابٌ أَلِيمٌ۝١٠٤

    Ya ayyuha allatheena amanoo la taqooloo raʿina waqooloo onthurna waismaʿoo walilkafireena ʿathabun aleemun

    Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Kada ku ce: 'Rã'inã'1 kuma ku ce: 'Jinkirtã manã', kuma ku saurara. Kuma kãfirai suna da azãba mai raɗaɗi.

    Bayanai
    [1] 'Rã'ina,' magana ce mai ma'ana iri biyu ta yabo da ta zãgi. Ta farko ita ce a lõkacin; da Annabi ke karantar da Sahabbansa sai su ce, 'ra'inã' watau dãkata mana har mu gane wannan; ta biyu ita ce, ra'inã!, watau yã ruɓaɓɓe! To, idan Sahabbai sun ce, 'ra'ina,' sunã nufin ma'anar farko, sai Yahũdu da mushirikai su jũya musu magana da ma'ana ta biyu.
  105. مَّا يَوَدُّ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ مِنْ أَهْلِ ٱلْكِتَـٰبِ وَلَا ٱلْمُشْرِكِينَ أَن يُنَزَّلَ عَلَيْكُم مِّنْ خَيْرٍ مِّن رَّبِّكُمْ ۗ وَٱللَّهُ يَخْتَصُّ بِرَحْمَتِهِۦ مَن يَشَآءُ ۚ وَٱللَّهُ ذُو ٱلْفَضْلِ ٱلْعَظِيمِ۝١٠٥

    Ma yawaddu allatheena kafaroo min ahli alkitabi wala almushrikeena an yunazzala ʿalaykum min khayrin min rabbikum waAllahu yakhtassu birahmatihi man yashao waAllahu thoo alfadli alʿatheemi

    Waɗanda suka kãfirta daga Ma'abuta Littãfi, bã su son a saukar da wani alhẽri a kanku daga Ubangijinku, kuma mushirikai mã bã su so. Kuma Allah Yana keɓance da wanda Yake so da rahamarSa. Kuma Allah Ma'abũcin falala mai girma ne.

  106. ۞ مَا نَنسَخْ مِنْ ءَايَةٍ أَوْ نُنسِهَا نَأْتِ بِخَيْرٍ مِّنْهَآ أَوْ مِثْلِهَآ ۗ أَلَمْ تَعْلَمْ أَنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍ قَدِيرٌ۝١٠٦

    Ma nansakh min ayatin aw nunsiha nati bikhayrin minha aw mithliha alam taʿlam anna Allaha ʿala kulli shayin qadeerun

    Abin da Muka shãfe1 daga ãya, ko kuwa Muka jinkirtar da ita, zã Mu zo da mafi Alhẽri daga gare ta ko kuwa misãlinta. Ashe, ba ka sani ba, cẽwa lalle ne, Allah a kan dukkan kõme Mai ĩkon yi ne?

    Bayanai
    [1] Wannan ãya da abin da yakea bayanta sunã kõrewar shubuhãtu watau rikice-rikicen addini da maƙiyan addini suke sanyãwa a cikinsa, dõmin su sanya Musulmi a cikin shakka da ruɗu.
  107. أَلَمْ تَعْلَمْ أَنَّ ٱللَّهَ لَهُۥ مُلْكُ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ۗ وَمَا لَكُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ مِن وَلِىٍّ وَلَا نَصِيرٍ۝١٠٧

    Alam taʿlam anna Allaha lahu mulku alssamawati waalardi wama lakum min dooni Allahi min waliyyin wala naseerin

    Shin ba ka sani ba, cẽwa lalle ne Allah, Shĩ ne da mulkin sammai da ƙasa kuma bã ku da, baicin Allah, wani majiɓinci, kuma bã ku da wani mataimaki?

  108. أَمْ تُرِيدُونَ أَن تَسْـَٔلُوا۟ رَسُولَكُمْ كَمَا سُئِلَ مُوسَىٰ مِن قَبْلُ ۗ وَمَن يَتَبَدَّلِ ٱلْكُفْرَ بِٱلْإِيمَـٰنِ فَقَدْ ضَلَّ سَوَآءَ ٱلسَّبِيلِ۝١٠٨

    Am tureedoona an tasaloo rasoolakum kama suila moosa min qablu waman yatabaddali alkufra bialeemani faqad dalla sawaa alssabeeli

    Kõ kuna nufin ku tambayi Manzonku, kamar yadda aka tambayi Mũsã a gabãnin haka? Kuma wanda ya musanya kãfirci da ĩmãni, to, lalle ne yã ɓace tsakar hanya.

  109. وَدَّ كَثِيرٌ مِّنْ أَهْلِ ٱلْكِتَـٰبِ لَوْ يَرُدُّونَكُم مِّنۢ بَعْدِ إِيمَـٰنِكُمْ كُفَّارًا حَسَدًا مِّنْ عِندِ أَنفُسِهِم مِّنۢ بَعْدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُمُ ٱلْحَقُّ ۖ فَٱعْفُوا۟ وَٱصْفَحُوا۟ حَتَّىٰ يَأْتِىَ ٱللَّهُ بِأَمْرِهِۦٓ ۗ إِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍ قَدِيرٌ۝١٠٩

    Wadda katheerun min ahli alkitabi law yaruddoonakum min baʿdi eemanikum kuffaran hasadan min ʿindi anfusihim min baʿdi ma tabayyana lahumu alhaqqu faoʿfoo waisfahoo hatta yatiya Allahu biamrihi inna Allaha ʿala kulli shayin qadeerun

    Mãsu yawa daga Ma'abuta Littãfi sunã gũrin dã sun mayar da ku, daga bãyan ĩmãninku, kãfirai, sabõda hãsada daga wurin rãyukansu, daga bayãn gaskiya tã bayyana a gare su. To, ku yãfe, kuma ku kau da kai, sai Allah Yã zo da umurninSa. Lalle ne Allah a kan dukkan kõme Mai ĩkon yi ne.

  110. وَأَقِيمُوا۟ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُوا۟ ٱلزَّكَوٰةَ ۚ وَمَا تُقَدِّمُوا۟ لِأَنفُسِكُم مِّنْ خَيْرٍ تَجِدُوهُ عِندَ ٱللَّهِ ۗ إِنَّ ٱللَّهَ بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِيرٌ۝١١٠

    Waaqeemoo alssalata waatoo alzzakata wama tuqaddimoo lianfusikum min khayrin tajidoohu ʿinda Allahi inna Allaha bima taʿmaloona baseerun

    Kuma ku tsayar da salla, kuma ku bãyar da zakka. Kuma abin da kuka gabãtar dõmin kanku daga alhẽri, zã ku sãme shi a wurin Allah. Lalle ne Allah, ga abin da kuke aikatãwa Mai gani ne.

  111. وَقَالُوا۟ لَن يَدْخُلَ ٱلْجَنَّةَ إِلَّا مَن كَانَ هُودًا أَوْ نَصَـٰرَىٰ ۗ تِلْكَ أَمَانِيُّهُمْ ۗ قُلْ هَاتُوا۟ بُرْهَـٰنَكُمْ إِن كُنتُمْ صَـٰدِقِينَ۝١١١

    Waqaloo lan yadkhula aljannata illa man kana hoodan aw nasara tilka amaniyyuhum qul hatoo burhanakum in kuntum sadiqeena

    Kuma suka ce: "Bãbu mai shiga Aljanna fãce waɗanda suka zama Yahũdu ko Nasãra." Waɗancan tãtsũniyõyinsu ne. Ka ce: "Ku kãwo dalilinku idan kun kasance mãsu gaskiya."

  112. بَلَىٰ مَنْ أَسْلَمَ وَجْهَهُۥ لِلَّهِ وَهُوَ مُحْسِنٌ فَلَهُۥٓ أَجْرُهُۥ عِندَ رَبِّهِۦ وَلَا خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلَا هُمْ يَحْزَنُونَ۝١١٢

    Bala man aslama wajhahu lillahi wahuwa muhsinun falahu ajruhu ʿinda rabbihi wala khawfun ʿalayhim wala hum yahzanoona

    Na'am! Wanda ya sallama fuskarsa ga Allah, alhãli kuwa yana mai kyautatãwa, to, yana da ijãrarsa, a wurin Ubangijinsa, kuma bãbu tsõro a kansu, kuma ba su zama suna baƙin ciki ba.

  113. وَقَالَتِ ٱلْيَهُودُ لَيْسَتِ ٱلنَّصَـٰرَىٰ عَلَىٰ شَىْءٍ وَقَالَتِ ٱلنَّصَـٰرَىٰ لَيْسَتِ ٱلْيَهُودُ عَلَىٰ شَىْءٍ وَهُمْ يَتْلُونَ ٱلْكِتَـٰبَ ۗ كَذَٰلِكَ قَالَ ٱلَّذِينَ لَا يَعْلَمُونَ مِثْلَ قَوْلِهِمْ ۚ فَٱللَّهُ يَحْكُمُ بَيْنَهُمْ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ فِيمَا كَانُوا۟ فِيهِ يَخْتَلِفُونَ۝١١٣

    Waqalati alyahoodu laysati alnnasara ʿala shayin waqalati alnnasara laysati alyahoodu ʿala shayin wahum yatloona alkitaba kathalika qala allatheena la yaʿlamoona mithla qawlihim faAllahu yahkumu baynahum yawma alqiyamati feema kanoo feehi yakhtalifoona

    Kuma Yahũdãwa suka ce: "Nasãra ba su zamana a kan kõme ba,"1 kuma Nasãra suka ce: "Yahũdãwa ba su zamana a kan kõmeba," alhãli kuwa su, suna karãtun Littãfi. Kamar wancan ne waɗanda ba su sani ba suka faɗa, kamar maganarsu sabõda haka Allah ne ke yin hukunci a tsakãninsu a Rãnar ¡iyãma, a cikin abin da suka kasance suna sãɓawa jũna a cikinsa.

    Bayanai
    [1] Mai gaskiya idan marasa gaskiya sun tãru sunã faɗa da shi, to, rashin jituwar tsakãninsu zai sanya Allah Ya kange shi daga sharrinsu, sũ duka, kamar husumar da ke tsakãnin Yahũdu da Nasãra da kuma tsakãnin sũ mushirikai, su duka mãsu yãƙi da Musulmi ne kuma mãsu sãɓãwa jũnã ne wajen aƙidõjinsu.
  114. وَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّن مَّنَعَ مَسَـٰجِدَ ٱللَّهِ أَن يُذْكَرَ فِيهَا ٱسْمُهُۥ وَسَعَىٰ فِى خَرَابِهَآ ۚ أُو۟لَـٰٓئِكَ مَا كَانَ لَهُمْ أَن يَدْخُلُوهَآ إِلَّا خَآئِفِينَ ۚ لَهُمْ فِى ٱلدُّنْيَا خِزْىٌ وَلَهُمْ فِى ٱلْـَٔاخِرَةِ عَذَابٌ عَظِيمٌ۝١١٤

    Waman athlamu mimman manaʿa masajida Allahi an yuthkara feeha ismuhu wasaʿa fee kharabiha olaika ma kana lahum an yadkhulooha illa khaifeena lahum fee alddunya khizyun walahum fee alakhirati ʿathabun ʿatheemun

    Kuma wãne ne mafi zãlunci1 daga wanda ya hana masallãtan Allah, dõmin kada a ambaci sunanSa a cikinsu, sai kuma ya yi aiki ga rushe su? Waɗannan bã ya kasancẽwa a gare su su shigẽ su fãce suna mãsu tsõro. Suna da, a cikin duniya wani wulãkanci, kuma suna da, a cikin Lãhira, Azãba mai girma.

    Bayanai
    [1] Misãlin sãɓãni tsakãninsu; Nasãra suka taimaki Bukhta Nassara ga ɓata masallacin Baitil Maƙdis da jefa mũshe da shãra a ciki, dõmin ƙin Yahũdu. Wannan ƙiyayya tã bayyana har a cikin takardar alƙawari a tsakãnin Nasãra da Halifa Umar bn Khattãb suka ce kada ya bar Yahũdu su shiga Baitil Maƙdis. Sabõda haka idan wasu sun hana ku isa ga masallacinku kõ kuma suka jũyarda ku daga Alƙibla, to, kada ku ji kõme, sun yi irin aikin danginsu. Gabas da yamma na Allah ɗaya ne, duk inda aka jũyar da ku, to, a can yardar Allah take. A lõkacin Musulmi na dũbin Baitil Maƙdis ga salla a bãyan Hijira daga Makka, bã su son haka.
  115. وَلِلَّهِ ٱلْمَشْرِقُ وَٱلْمَغْرِبُ ۚ فَأَيْنَمَا تُوَلُّوا۟ فَثَمَّ وَجْهُ ٱللَّهِ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ وَٰسِعٌ عَلِيمٌ۝١١٥

    Walillahi almashriqu waalmaghribu faaynama tuwalloo fathamma wajhu Allahi inna Allaha wasiʿun ʿaleemun

    Kuma Allah ɗai yake da gabas da yamma sabõda haka, inda duk aka jũyar da ku, to, a can fuskar Allah take. Lalle ne, Allah Mawadãci ne, Mai ilmi.

  116. وَقَالُوا۟ ٱتَّخَذَ ٱللَّهُ وَلَدًا ۗ سُبْحَـٰنَهُۥ ۖ بَل لَّهُۥ مَا فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ۖ كُلٌّ لَّهُۥ قَـٰنِتُونَ۝١١٦

    Waqaloo itakhatha Allahu waladan subhanahu bal lahu ma fee alssamawati waalardi kullun lahu qanitoona

    Kuma suka ce: "Allah Yã riƙi1 ɗã." Tsarki yã tabbata a gare Shi! A'a, Shi ne da abin da yake a cikin sammai da ƙasa, dukansu, a gare Shi, mãsu ƙanƙan da kai ne.

    Bayanai
    [1] Misãli na biyu Yahũdu na cewa Uzairu ɗãn Allah, kuma Nasãra sunã cewa Ĩsa ɗan Allah, Lãrabãwa na cewa Malã'iku 'ya'yan Allah. Wannan zai hana su jituwa har adãwarsu ga Musulmi ta yi tãsĩri.
  117. بَدِيعُ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ۖ وَإِذَا قَضَىٰٓ أَمْرًا فَإِنَّمَا يَقُولُ لَهُۥ كُن فَيَكُونُ۝١١٧

    Badeeʿu alssamawati waalardi waitha qada amran fainnama yaqoolu lahu kun fayakoonu

    Mai kyautata halittar sammai da ƙasa, kuma idan Ya hukunta wani al'amari, sai kawai Ya ce masa: "Kasance." Sai ya yi ta kasancewa.

  118. وَقَالَ ٱلَّذِينَ لَا يَعْلَمُونَ لَوْلَا يُكَلِّمُنَا ٱللَّهُ أَوْ تَأْتِينَآ ءَايَةٌ ۗ كَذَٰلِكَ قَالَ ٱلَّذِينَ مِن قَبْلِهِم مِّثْلَ قَوْلِهِمْ ۘ تَشَـٰبَهَتْ قُلُوبُهُمْ ۗ قَدْ بَيَّنَّا ٱلْـَٔايَـٰتِ لِقَوْمٍ يُوقِنُونَ۝١١٨

    Waqala allatheena la yaʿlamoona lawla yukallimuna Allahu aw tateena ayatun kathalika qala allatheena min qablihim mithla qawlihim tashabahat quloobuhum qad bayyanna alayati liqawmin yooqinoona

    Kuma waɗanda bã su da sani suka ce: "Don me Allah bã Ya yi mana magana, ko wata ãyã ta zo mana?"1 Kamar wancan ne waɗanda suke a gabãninsu suka faɗa, kamar maganarsu. zukãtansu sun yi kamã da jũna. Lalle ne, Mun bayyana ãyõyi ga mutãne masu sakankancewa.

    Bayanai
    [1] Misãli ne ga irin rikicin mushirikai ga addini kuma da yadda suka yi kamã da Yahũdu, waɗanda suka ce wa Mũsã: "Ka nũna mana Allah bayyane.".
  119. إِنَّآ أَرْسَلْنَـٰكَ بِٱلْحَقِّ بَشِيرًا وَنَذِيرًا ۖ وَلَا تُسْـَٔلُ عَنْ أَصْحَـٰبِ ٱلْجَحِيمِ۝١١٩

    Inna arsalnaka bialhaqqi basheeran wanatheeran wala tusalu Aaan ashabi aljaheemi

    Lalle ne Mun aike ka da gaskiya, kana mai bãyar da bishãra, kuma mai gargaɗi, kuma bã zã a tambaye ka ba, game da abõkan Wuta.

  120. وَلَن تَرْضَىٰ عَنكَ ٱلْيَهُودُ وَلَا ٱلنَّصَـٰرَىٰ حَتَّىٰ تَتَّبِعَ مِلَّتَهُمْ ۗ قُلْ إِنَّ هُدَى ٱللَّهِ هُوَ ٱلْهُدَىٰ ۗ وَلَئِنِ ٱتَّبَعْتَ أَهْوَآءَهُم بَعْدَ ٱلَّذِى جَآءَكَ مِنَ ٱلْعِلْمِ ۙ مَا لَكَ مِنَ ٱللَّهِ مِن وَلِىٍّ وَلَا نَصِيرٍ۝١٢٠

    Walan tarda ʿanka alyahoodu wala alnnasara hatta tattabiʿa millatahum qul inna huda Allahi huwa alhuda walaini ittabaʿta ahwaahum baʿda allathee jaaka mina alʿilmi ma laka mina Allahi min waliyyin wala naseerin

    Kuma Yahũdu bã zã su yarda da kõme daga gare ka ba, kuma Nasãra bã zã su yarda ba, sai kã bi irin aƙidarsu. Ka ce: "Lalle ne, shiriyar Allah ita ce shiriya." Kuma lalle ne idan ka bi son zũciyõyinsu a bãyan abin da ya zo maka na ilmi, bã ka da, daga Allah, wani majiɓinci, kuma bãbu wani mataimaki.

  121. ٱلَّذِينَ ءَاتَيْنَـٰهُمُ ٱلْكِتَـٰبَ يَتْلُونَهُۥ حَقَّ تِلَاوَتِهِۦٓ أُو۟لَـٰٓئِكَ يُؤْمِنُونَ بِهِۦ ۗ وَمَن يَكْفُرْ بِهِۦ فَأُو۟لَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلْخَـٰسِرُونَ۝١٢١

    Allatheena ataynahumu alkitaba yatloonahu haqqa tilawatihi olaika yuminoona bihi waman yakfur bihi faolaika humu alkhasiroona

    Waɗanda Muka bai wa Littãfi suna karãtunsa a kan haƙƙin karãtunsa, waɗannan suna ĩmani da shi (Alƙur'ãni). Kuma wanda ya kãfirta da shi, to, waɗannan sũ ne mãsu hasãra.

  122. يَـٰبَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ ٱذْكُرُوا۟ نِعْمَتِىَ ٱلَّتِىٓ أَنْعَمْتُ عَلَيْكُمْ وَأَنِّى فَضَّلْتُكُمْ عَلَى ٱلْعَـٰلَمِينَ۝١٢٢

    Ya banee israeela othkuroo niʿmatiya allatee anʿamtu ʿalaykum waannee faddaltukum ʿala alʿalameena

    Yã Banĩ Isrã'ĩla! Ku1 tuna ni'imaTa wadda Na ni'imtar da ita a kanku, kuma lalle ne Nĩ, Nã fĩfĩtã ku a kan tãlikai.

    Bayanai
    [1] Kira na ƙarshe zuwa ga Yahũdu dõmin shiga Musulunci. An biyar da gargaɗi gare su da tunãtar da su cewa wannan addinin fa, shi ne addinin kãkansu Ibrãhim, dõmin kada su fanɗare daga addinin ubanninsu na ƙwarai. Kuma sunã da lãbãrin ginin Ɗakin Ka'aba da addu'ar da lbrahim ya yi alõkacin, wadda ta ƙunshi zuwan annabi daga cikin zuriyar Isama'ila a Makka, watau Fãrãna.
  123. وَٱتَّقُوا۟ يَوْمًا لَّا تَجْزِى نَفْسٌ عَن نَّفْسٍ شَيْـًٔا وَلَا يُقْبَلُ مِنْهَا عَدْلٌ وَلَا تَنفَعُهَا شَفَـٰعَةٌ وَلَا هُمْ يُنصَرُونَ۝١٢٣

    Waittaqoo yawman la tajzee nafsun ʿan nafsin shayan wala yuqbalu minha ʿadlun wala tanfaʿuha shafaʿatun wala hum yunsaroona

    Ku ji tsõron wani yini, (a cikinsa) wani rai bã ya tunkuɗe wa wani rai kõme kuma bã a karɓar fansa daga gare shi, kuma wani cẽto bã ya amfanin sa, kuma ba su zama ana taimakon su ba.

  124. ۞ وَإِذِ ٱبْتَلَىٰٓ إِبْرَٰهِـۧمَ رَبُّهُۥ بِكَلِمَـٰتٍ فَأَتَمَّهُنَّ ۖ قَالَ إِنِّى جَاعِلُكَ لِلنَّاسِ إِمَامًا ۖ قَالَ وَمِن ذُرِّيَّتِى ۖ قَالَ لَا يَنَالُ عَهْدِى ٱلظَّـٰلِمِينَ۝١٢٤

    Waithi ibtala ibraheema rabbuhu bikalimatin faatammahunna qala innee jaʿiluka lilnnasi imaman qala wamin thurriyyatee qala la yanalu ʿahdee alththalimeena

    Kuma a lõkacin da Ubangijin Ibrãhim Ya jarrabẽ shi da wasu kalmõmi, sai ya cika su. Ya ce: "Lalle ne Nĩ, Mai sanya ka shugaba dõmin mutãne ne." Ya ce: "Kuma daga zũriyata." Ya ce: "AlkawarĩNa bã zai sãmu azzãlumai ba."

  125. وَإِذْ جَعَلْنَا ٱلْبَيْتَ مَثَابَةً لِّلنَّاسِ وَأَمْنًا وَٱتَّخِذُوا۟ مِن مَّقَامِ إِبْرَٰهِـۧمَ مُصَلًّى ۖ وَعَهِدْنَآ إِلَىٰٓ إِبْرَٰهِـۧمَ وَإِسْمَـٰعِيلَ أَن طَهِّرَا بَيْتِىَ لِلطَّآئِفِينَ وَٱلْعَـٰكِفِينَ وَٱلرُّكَّعِ ٱلسُّجُودِ۝١٢٥

    Waith jaʿalna albayta mathabatan lilnnasi waamnan waittakhithoo min maqami ibraheema musallan waʿahidna ila ibraheema waismaʿeela an tahhira baytiya lilttaifeena waalʿakifeena waalrrukkaʿi alssujoodi

    Kuma a lõkacin da Muka sanya ¦ãkin ya zama makõma ga mutãne, da aminci, kuma ku riƙi wurin salla daga Maƙãmi Ibrãhĩm, kuma Muka yi alƙawari zuwa ga Ibrãhĩm, da Ismã'ila da cẽwa: "Ku tsarkake ¦ãkiNa dõmin mãsu ɗawãfi da mãsu lizimta da mãsu rukũ'i, mãsu sujada."

  126. وَإِذْ قَالَ إِبْرَٰهِـۧمُ رَبِّ ٱجْعَلْ هَـٰذَا بَلَدًا ءَامِنًا وَٱرْزُقْ أَهْلَهُۥ مِنَ ٱلثَّمَرَٰتِ مَنْ ءَامَنَ مِنْهُم بِٱللَّهِ وَٱلْيَوْمِ ٱلْـَٔاخِرِ ۖ قَالَ وَمَن كَفَرَ فَأُمَتِّعُهُۥ قَلِيلًا ثُمَّ أَضْطَرُّهُۥٓ إِلَىٰ عَذَابِ ٱلنَّارِ ۖ وَبِئْسَ ٱلْمَصِيرُ۝١٢٦

    Waith qala ibraheemu rabbi ijʿal hatha baladan aminan waorzuq ahlahu mina alththamarati man amana minhum biAllahi waalyawmi alakhiri qala waman kafara faomattiʿuhu qaleelan thumma adtarruhu ila ʿathabi alnnari wabisa almaseeru

    Kuma a lõkacin da lbrãhĩm ya ce: "Yã Ubangijĩna! Ka sanya wannan gari amintacce, Ka azurta mutãnensa, daga 'ya'yan itãcen, wanda ya yi ĩmãni, daga gare su, da Allah da Ranar Lãhira." Allah Ya ce: "Wanda ya kãfirta ma Ina jiyar da shi dãɗi kaɗan, sa'an nan kuma Ina tĩlastã shi zuwa ga azãbar Wuta. Kuma makõmar, ta munana."

  127. وَإِذْ يَرْفَعُ إِبْرَٰهِـۧمُ ٱلْقَوَاعِدَ مِنَ ٱلْبَيْتِ وَإِسْمَـٰعِيلُ رَبَّنَا تَقَبَّلْ مِنَّآ ۖ إِنَّكَ أَنتَ ٱلسَّمِيعُ ٱلْعَلِيمُ۝١٢٧

    Waith yarfaʿu ibraheemu alqawaʿida mina albayti waismaʿeelu rabbana taqabbal minna innaka anta alssameeʿu alʿaleemu

    Kuma a lõkacin da Ibrãhĩm yake ɗaukaka harsãshin gini ga ¦ãkin, da Ismã'ĩla (suna cẽwa:) "Yã Ubangijnmu! Ka karɓa daga gare mu, lalle ne Kai, Kai ne Mai ji, Mai sani.

  128. رَبَّنَا وَٱجْعَلْنَا مُسْلِمَيْنِ لَكَ وَمِن ذُرِّيَّتِنَآ أُمَّةً مُّسْلِمَةً لَّكَ وَأَرِنَا مَنَاسِكَنَا وَتُبْ عَلَيْنَآ ۖ إِنَّكَ أَنتَ ٱلتَّوَّابُ ٱلرَّحِيمُ۝١٢٨

    Rabbana waijʿalna muslimayni laka wamin thurriyyatina ommatan muslimatan laka waarina manasikana watub ʿalayna innaka anta alttawwabu alrraheemu

    "Ya Ubangijnmu! Ka sanyã mu, mu biyu, waɗanda suka sallama (al'amari) gare Ka, kuma daga zuriyarmu (Ka sanya) al'umma mai sallamãwa zuwa gare Ka, Kuma Ka nũna mana wurãren ibãdar hajjinmu, kuma Ka karɓi tũba a kanmu. Lalle ne Kai, Kai ne Mai karɓar tũba, Mai rahama.

  129. رَبَّنَا وَٱبْعَثْ فِيهِمْ رَسُولًا مِّنْهُمْ يَتْلُوا۟ عَلَيْهِمْ ءَايَـٰتِكَ وَيُعَلِّمُهُمُ ٱلْكِتَـٰبَ وَٱلْحِكْمَةَ وَيُزَكِّيهِمْ ۚ إِنَّكَ أَنتَ ٱلْعَزِيزُ ٱلْحَكِيمُ۝١٢٩

    Rabbana waibʿath feehim rasoolan minhum yatloo ʿalayhim ayatika wayuʿallimuhumu alkitaba waalhikmata wayuzakkeehim innaka anta alʿazeezu alhakeemu

    "Ya Ubangijinmu! Ka aiko, a cikinsu, wani manzo1 daga gare su, yana karanta musu ãyõyinKa, kuma yana karantar da su Littãfin2 da hikimar, kuma yana tsarkake su. Lalle ne Kai, Kai ne Mabuwãyi Mai hikima."

    Bayanai
    [1] Addu'ar an karɓa, ta aiko Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. [2] Littãfin-ya bayyana cewa Alƙur'ãni ne, dõmin bãbu wani sai shi. Hikima kuwa ita ce shari'ar da ke a cikinsa. Zai tsarkake su daga dauɗar shirka idan sun bĩ shi.
  130. وَمَن يَرْغَبُ عَن مِّلَّةِ إِبْرَٰهِـۧمَ إِلَّا مَن سَفِهَ نَفْسَهُۥ ۚ وَلَقَدِ ٱصْطَفَيْنَـٰهُ فِى ٱلدُّنْيَا ۖ وَإِنَّهُۥ فِى ٱلْـَٔاخِرَةِ لَمِنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ۝١٣٠

    Waman yarghabu ʿan millati ibraheema illa man safiha nafsahu walaqadi istafaynahu fee alddunya wainnahu fee alakhirati lamina alssaliheena

    Kuma wãne ne yake gudu daga aƙĩdar Ibrãhĩm, fãce wanda ya jãhilta ga ransa? Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun zãɓe shi, a cikin dũniya, kuma lalle ne shi, a cikin Lãhira, haƙĩƙa, yana daga sãlihai.

  131. إِذْ قَالَ لَهُۥ رَبُّهُۥٓ أَسْلِمْ ۖ قَالَ أَسْلَمْتُ لِرَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ۝١٣١

    Ith qala lahu rabbuhu aslim qala aslamtu lirabbi alʿalameena

    lokacin da Ubangijisa ya ce da shi ka mika wuya sai ya ce na mika wuya ga Ubangijin Talikai

  132. وَوَصَّىٰ بِهَآ إِبْرَٰهِـۧمُ بَنِيهِ وَيَعْقُوبُ يَـٰبَنِىَّ إِنَّ ٱللَّهَ ٱصْطَفَىٰ لَكُمُ ٱلدِّينَ فَلَا تَمُوتُنَّ إِلَّا وَأَنتُم مُّسْلِمُونَ۝١٣٢

    Wawassa biha ibraheemu baneehi wayaʿqoobu ya baniyya inna Allaha istafa lakumu alddeena fala tamootunna illa waantum muslimoona

    Kuma lbrãhĩm ya yi wasiyya da ita ga ɗiyansa, kuma Ya'aƙũbu (ya yi wasiyya, suka ce:) "Yã ɗiyãna! Lalle ne, Allah Ya zãɓã muku addini don haka kada ku mutu, lalle, fãce kuna Musulmi."

  133. أَمْ كُنتُمْ شُهَدَآءَ إِذْ حَضَرَ يَعْقُوبَ ٱلْمَوْتُ إِذْ قَالَ لِبَنِيهِ مَا تَعْبُدُونَ مِنۢ بَعْدِى قَالُوا۟ نَعْبُدُ إِلَـٰهَكَ وَإِلَـٰهَ ءَابَآئِكَ إِبْرَٰهِـۧمَ وَإِسْمَـٰعِيلَ وَإِسْحَـٰقَ إِلَـٰهًا وَٰحِدًا وَنَحْنُ لَهُۥ مُسْلِمُونَ۝١٣٣

    Am kuntum shuhadaa ith hadara yaʿqooba almawtu ith qala libaneehi ma taʿbudoona min baʿdee qaloo naʿbudu ilahaka wailaha abaika ibraheema waismaʿeela waishaqa ilahan wahidan wanahnu lahu muslimoona

    Ko kun1 kasance halarce a lõkacin da mutuwa ta halarci Ya'aƙũbu, a lõkacin da ya ce wa ɗiyansa: "Mẽne ne zã ku bauta wa daga bãyãna?" Suka ce: "Muna bauta wa Abin bautawarka kuma Abin bautawar ubanninka lbrãhĩm da lsmã'ĩla da Is'hãƙa, Ubangiji Guda, kuma mu a gare Shi mãsu miƙa wuya ne."

    Bayanai
    [1] Lamĩrin Yahũdãwan Madĩna ne na zãmanin Annabi, waɗanda ake kira zuwa ga Musulunci anã tunãtar da su abinda kakansu lsrã'ĩla ya yi wasiyya da shi zuwa ga ɗiyansa, kãfin ya mutu; watau wannan aƙĩda da ake kiran suyanzu zuwa gare ta.
  134. تِلْكَ أُمَّةٌ قَدْ خَلَتْ ۖ لَهَا مَا كَسَبَتْ وَلَكُم مَّا كَسَبْتُمْ ۖ وَلَا تُسْـَٔلُونَ عَمَّا كَانُوا۟ يَعْمَلُونَ۝١٣٤

    Tilka ommatun qad khalat laha ma kasabat walakum ma kasabtum wala tusaloona ʿamma kano yaʿmaloona

    Waccan, wata al'umma ce, ta riga ta shige, tana da abin da ta sanã'anta kuma kuna da abin da kuka sanã'anta, Kuma bã zã a tambaye ku ba daga abin da suka kasance suna aikatãwa.

  135. وَقَالُوا۟ كُونُوا۟ هُودًا أَوْ نَصَـٰرَىٰ تَهْتَدُوا۟ ۗ قُلْ بَلْ مِلَّةَ إِبْرَٰهِـۧمَ حَنِيفًا ۖ وَمَا كَانَ مِنَ ٱلْمُشْرِكِينَ۝١٣٥

    Waqaloo koonoo hoodan aw nasara tahtadoo qul bal millata ibraheema haneefan wama kana mina almushrikeena

    Kuma suka ce: "Ku kasance1 Yahũdãwa ko Nasãra, kwã shiryu."Ka ce: "A'a aƙidar Ibrãhĩm dai, maikarkata, zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga mãsu shirki ba."

    Bayanai
    [1] Yahũdu suka ce: "Ku kasance Yahũdawa ku shiryu" Nasãra suka ce: "Ku kasance Nasãraku shiryu". Allah Ya nũna addinin Yahũdu da na Nasãra yã sãɓãwa abin da suke yi, su duka biyu, kuma yã sãɓawa na mushirikai.
  136. قُولُوٓا۟ ءَامَنَّا بِٱللَّهِ وَمَآ أُنزِلَ إِلَيْنَا وَمَآ أُنزِلَ إِلَىٰٓ إِبْرَٰهِـۧمَ وَإِسْمَـٰعِيلَ وَإِسْحَـٰقَ وَيَعْقُوبَ وَٱلْأَسْبَاطِ وَمَآ أُوتِىَ مُوسَىٰ وَعِيسَىٰ وَمَآ أُوتِىَ ٱلنَّبِيُّونَ مِن رَّبِّهِمْ لَا نُفَرِّقُ بَيْنَ أَحَدٍ مِّنْهُمْ وَنَحْنُ لَهُۥ مُسْلِمُونَ۝١٣٦

    Qooloo amanna biAllahi wama onzila ilayna wama onzila ila ibraheema waismaʿeela waishaqa wayaʿqooba waalasbati wama ootiya moosa waʿeesa wama ootiya alnnabiyyoona min rabbihim la nufarriqu bayna ahadin minhum wanahnu lahu muslimoona

    Ku1 ce: "Mun yi ĩmãni da Allah, da abin da aka saukar zuwa gare mu, da abin da aka saukar zuwa ga Ibrãhĩm da Ismã'ĩla da Is'hãka da Ya'aƙũbu da jĩkõki, da abin da aka bai wa Mũsã da Ĩsã, da abin da aka bai wa annabãwa daga Ubangijinsu, bã mu rarrabẽwa a tsakãnin kõwa daga gare su, kuma mu, a gare Shi, mãsu miƙa wuya ne."

    Bayanai
    [1] Musulmi ake yi wa umurni.
  137. فَإِنْ ءَامَنُوا۟ بِمِثْلِ مَآ ءَامَنتُم بِهِۦ فَقَدِ ٱهْتَدَوا۟ ۖ وَّإِن تَوَلَّوْا۟ فَإِنَّمَا هُمْ فِى شِقَاقٍ ۖ فَسَيَكْفِيكَهُمُ ٱللَّهُ ۚ وَهُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلْعَلِيمُ۝١٣٧

    Fain amanoo bimithli ma amantum bihi faqadi ihtadaw wain tawallaw fainnama hum fee shiqaqin fasayakfeekahumu Allahu wahuwa alssameeʿu alʿaleemu

    To, idan sun yi ĩmãni1 da misãlin abin da kuka yi ĩmãni da shi, to, lalle ne sun shiryu, kuma idan sun jũya bãya, to, suna a cikin sãɓãni kawai sabõda haka Allah zai isar maka a gare su, kuma Shi ne Mai ji, Masani.

    Bayanai
    [1] Ĩmãni irin na Musulmi shi ne rinin Allah watau baptisma.
  138. صِبْغَةَ ٱللَّهِ ۖ وَمَنْ أَحْسَنُ مِنَ ٱللَّهِ صِبْغَةً ۖ وَنَحْنُ لَهُۥ عَـٰبِدُونَ۝١٣٨

    Sibghata Allahi waman ahsanu mina Allahi sibghatan wanahnu lahu ʿabidoona

    Rinin Allah! Kuma wãne ne mafi kyau ga rini daga Allah? Kuma mu, a gare Shi, mãsu bautãwa ne.

  139. قُلْ أَتُحَآجُّونَنَا فِى ٱللَّهِ وَهُوَ رَبُّنَا وَرَبُّكُمْ وَلَنَآ أَعْمَـٰلُنَا وَلَكُمْ أَعْمَـٰلُكُمْ وَنَحْنُ لَهُۥ مُخْلِصُونَ۝١٣٩

    Qul atuhajjoonana fee Allahi wahuwa rabbuna warabbukum walana aʿmaluna walakum aʿmalukum wanahnu lahu mukhlisoona

    Ka ce: Shin kuna jãyayyar hujia ne da mu a cikin al'amarin Allah, alhãli kuwa Shi ne Ubangijinmu kuma Ubangijinku, kuma muna da ayyukanmu, kuma kuna da ayyukanku, kuma mũ, a gare Shi, mãsu tsarkakẽwane?

  140. أَمْ تَقُولُونَ إِنَّ إِبْرَٰهِـۧمَ وَإِسْمَـٰعِيلَ وَإِسْحَـٰقَ وَيَعْقُوبَ وَٱلْأَسْبَاطَ كَانُوا۟ هُودًا أَوْ نَصَـٰرَىٰ ۗ قُلْ ءَأَنتُمْ أَعْلَمُ أَمِ ٱللَّهُ ۗ وَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّن كَتَمَ شَهَـٰدَةً عِندَهُۥ مِنَ ٱللَّهِ ۗ وَمَا ٱللَّهُ بِغَـٰفِلٍ عَمَّا تَعْمَلُونَ۝١٤٠

    Am taqooloona inna ibraheema waismaʿeela waishaqa wayaʿqooba waalasbata kanoo hoodan aw nasara qul aantum aʿlamu ami Allahu waman athlamu mimman katama shahadatan ʿindahu mina Allahi wama Allahu bighafilin ʿamma taʿmaloona

    Ko kuna cẽwa: Lalle ne, Ibrãhĩm da Ismã'ĩla da Is'hãƙa da Ya'aƙũbu da Jĩkõki, sun kasance Yahũdãwa kõ kuwa Nasãra? Ka ce: Shin kũ ne kuke mafi sani kõAllah? Kuma wãne ne ya zama mafi zãlunci daga wanda ya bõye shaida a wurinsa daga Allah? Kuma Allah bai zama Mai gafala ba daga abin da kuke aikatãwa!

  141. تِلْكَ أُمَّةٌ قَدْ خَلَتْ ۖ لَهَا مَا كَسَبَتْ وَلَكُم مَّا كَسَبْتُمْ ۖ وَلَا تُسْـَٔلُونَ عَمَّا كَانُوا۟ يَعْمَلُونَ۝١٤١

    Tilka ommatun qad khalat laha ma kasabat walakum ma kasabtum wala tusaloona ʿamma kanoo yaʿmaloona

    Waccan, wata al'umma ce, tã riga ta shige, suna da abin da suka sana'anta kuma kuna da abin da kuka sana'anta kuma bã a tambayar ku daga abin da suka kasance suna aikatãwa.

  142. ۞ سَيَقُولُ ٱلسُّفَهَآءُ مِنَ ٱلنَّاسِ مَا وَلَّىٰهُمْ عَن قِبْلَتِهِمُ ٱلَّتِى كَانُوا۟ عَلَيْهَا ۚ قُل لِّلَّهِ ٱلْمَشْرِقُ وَٱلْمَغْرِبُ ۚ يَهْدِى مَن يَشَآءُ إِلَىٰ صِرَٰطٍ مُّسْتَقِيمٍ۝١٤٢

    Sayaqoolu alssufahao mina alnnasi ma wallahum ʿan qiblatihimu allatee kanoo ʿalayha qul lillahi almashriqu waalmaghribu yahdee man yashao ila siratin mustaqeemin

    Wãwãye daga mutãne zã su ce: Mẽne ne ya jũyar da su daga alƙiblarsu wadda suka kasance a kanta? Ka ce: "Allah ¦ai ne Yake da gabas da yamma, Yana shiryar da wanda Yake so zuwa ga hanya madaidaiciya."

  143. وَكَذَٰلِكَ جَعَلْنَـٰكُمْ أُمَّةً وَسَطًا لِّتَكُونُوا۟ شُهَدَآءَ عَلَى ٱلنَّاسِ وَيَكُونَ ٱلرَّسُولُ عَلَيْكُمْ شَهِيدًا ۗ وَمَا جَعَلْنَا ٱلْقِبْلَةَ ٱلَّتِى كُنتَ عَلَيْهَآ إِلَّا لِنَعْلَمَ مَن يَتَّبِعُ ٱلرَّسُولَ مِمَّن يَنقَلِبُ عَلَىٰ عَقِبَيْهِ ۚ وَإِن كَانَتْ لَكَبِيرَةً إِلَّا عَلَى ٱلَّذِينَ هَدَى ٱللَّهُ ۗ وَمَا كَانَ ٱللَّهُ لِيُضِيعَ إِيمَـٰنَكُمْ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ بِٱلنَّاسِ لَرَءُوفٌ رَّحِيمٌ۝١٤٣

    Wakathalika jaʿalnakum ommatan wasatan litakoonoo shuhadaa ʿala alnnasi wayakoona alrrasoolu ʿalaykum shaheedan wama jaʿalna alqiblata allatee kunta ʿalayha illa linaʿlama man yattabiʿu alrrasoola mimman yanqalibu ʿala ʿaqibayhi wain kanat lakabeeratan illa ʿala allatheena hada Allahu wama kana Allahu liyudeeʿa eemanakum inna Allaha bialnnasi laraoofun raheemun

    Kuma kamar wancan, Muka sanya ku al'umma matsakaiciya1 dõmin ku kasance mãsu bãyar da shaida a kan mutãne. Kuma Manzo ya kasance mai shaida a kanku. Kuma ba Mu sanya Alƙibla2 wadda ka kasance a kanta ba, fãce dõmin Mu san wanda yake biyar Manzo daga wanda yake jũyãwa a kan duga-dugansa. Kuma lalle ne, tã kasance haƙĩƙa, mai girma, sai a kan waɗanda Allah Ya shiryar. Kuma ba ya yiwuwa ga Allah Ya tõzartar da ĩmãninku.3 Lalle ne, Allah, ga mutãne, haƙĩƙa, Mai tausayi ne, Mai jin ƙai.

    Bayanai
    [1] Ãdilai, kõ matsakaita ga kõmai, babu zurewa,babu kãsawa ga addini da rãyuwa da sauran mu'ãmalõli duka. [2] A lõkacin da Annabi ya yi hijira zuwa Madĩna, alhãli a cikin mutãnenta akwai Yahũdu Allah Ya umurce shi da ya fuskanci Baitil Maƙdis. Sai Yahũdu suka ji dãɗi. Sai Manzon Allah ya fuskance ta wata gõma sha wani abu kuma Manzon Allah ya kasance yana son Alƙiblar lbrãhĩm kamar yadda ya gabata ga ãyã ta 115. Kuma ya kasance yana addu'a yanã dũbi zuwa ga sama, har Allah Ya saukar da hukuncin jũyãwa zuwa gare ta. [3] Ĩmãninku watau sallarku da kuka yi wajen Baitil Makdis, dõmin kun yi ta ne a kan umurnin Allah da ĩmãni da Shi.
  144. قَدْ نَرَىٰ تَقَلُّبَ وَجْهِكَ فِى ٱلسَّمَآءِ ۖ فَلَنُوَلِّيَنَّكَ قِبْلَةً تَرْضَىٰهَا ۚ فَوَلِّ وَجْهَكَ شَطْرَ ٱلْمَسْجِدِ ٱلْحَرَامِ ۚ وَحَيْثُ مَا كُنتُمْ فَوَلُّوا۟ وُجُوهَكُمْ شَطْرَهُۥ ۗ وَإِنَّ ٱلَّذِينَ أُوتُوا۟ ٱلْكِتَـٰبَ لَيَعْلَمُونَ أَنَّهُ ٱلْحَقُّ مِن رَّبِّهِمْ ۗ وَمَا ٱللَّهُ بِغَـٰفِلٍ عَمَّا يَعْمَلُونَ۝١٤٤

    Qad nara taqalluba wajhika fee alssamai falanuwalliyannaka qiblatan tardaha fawalli wajhaka shatra almasjidi alharami wahaythu ma kuntum fawalloo wujoohakum shatrahu wainna allatheena ootoo alkitaba layaʿlamoona annahu alhaqqu min rabbihim wama Allahu bighafilin ʿamma yaʿmaloona

    Lalle ne, Muna ganin jujjũyãwar fuskarka a cikin sama. To, lalle ne, Mu jũyar da kai ga Alƙibla wadda kake yardã da ita. Sai ka jũyar da fuskarka wajen Masallãci Tsararre, kuma inda duk kuka kasance, to, ku jũyar da fuskõkinku jiharsa. Kuma lalle ne waɗanda aka bai wa Littãfi, haƙĩƙa su, sunã sanin lalle ne, shĩ ne gaskiya, daga Ubangijinka. Kuma Allah bai zama Mai gafala ba daga abin da suke aikatãwa.

  145. وَلَئِنْ أَتَيْتَ ٱلَّذِينَ أُوتُوا۟ ٱلْكِتَـٰبَ بِكُلِّ ءَايَةٍ مَّا تَبِعُوا۟ قِبْلَتَكَ ۚ وَمَآ أَنتَ بِتَابِعٍ قِبْلَتَهُمْ ۚ وَمَا بَعْضُهُم بِتَابِعٍ قِبْلَةَ بَعْضٍ ۚ وَلَئِنِ ٱتَّبَعْتَ أَهْوَآءَهُم مِّنۢ بَعْدِ مَا جَآءَكَ مِنَ ٱلْعِلْمِ ۙ إِنَّكَ إِذًا لَّمِنَ ٱلظَّـٰلِمِينَ۝١٤٥

    Walain atayta allatheena ootoo alkitaba bikulli ayatin ma tabiʿoo qiblataka wama anta bitabiʿin qiblatahum wama baʿduhum bitabiʿin qiblata baʿdin walaini ittabaʿta ahwaahum min baʿdi ma jaaka mina alʿilmi innaka ithan lamina alththalimeena

    Kuma hakĩka, idan ka je wawaɗanda aka bai wa Littafi da dukan ãyã, bã zã su bi Alƙiblarka ba, kuma kai ba ka zama mai bin Alƙiblarsu ba, kuma sãshensu bã mai bin Alƙiblar1 sãshe ba ne. Kuma haƙĩƙa, idan ka bi son zũciyõyinsu daga bãyan abin da ya zo maka daga ilmi, lalle ne kai, sa'an nan, haƙiƙa, azzãlumi kake.

    Bayanai
    [1] Alƙiblar Yahũdu ita ce falalen dũtsen da ke Baitil Maƙdis. Kuma ita ce Alƙiblar Nasãra a zãmanin Ĩsã. A bãyansa Alƙiblarsu ta kõma ga mafitar rãnã, da ƙãgensu sabõda St. Paul koõ Bulis el Ƙissi, ya ce musu bãyan an ɗauke Ĩsa cewa: "Nã haɗu da Ĩsa yã ce mini lalle ne ranã tauraro ne wanda yake inã sonsa. Yanã kai gaisuwata a cikin kõwane yini sabõda haka ka umurci mutãnena, su fuskanta zuwa gare ta." Da haka ya karkatar da su daga alƙiblarsu. Kuma inã zaton haka abin yake ga girmamãwar Lahadi maimakon Asabar dõmin Rũmãwa, ranã suke bauta wa a rãnar Lahadi wannan kuwa shi ne ma'anar "Sunday" da Tũrancin, watau 'yinin rãna.'.
  146. ٱلَّذِينَ ءَاتَيْنَـٰهُمُ ٱلْكِتَـٰبَ يَعْرِفُونَهُۥ كَمَا يَعْرِفُونَ أَبْنَآءَهُمْ ۖ وَإِنَّ فَرِيقًا مِّنْهُمْ لَيَكْتُمُونَ ٱلْحَقَّ وَهُمْ يَعْلَمُونَ۝١٤٦

    Allatheena ataynahumu alkitaba yaʿrifoonahu kama yaʿrifoona abnaahum wainna fareeqan minhum layaktumoona alhaqqa wahum yaʿlamoona

    Waɗanda Muka bã su Littãfi, suna saninsa kamar yadda suke sanin ɗiyansu. Kuma lalle ne wani ɓangare daga gare su, haƙiƙa, suna ɓõyewar gaskiya alhãli kuwa sũ, suna sane.

  147. ٱلْحَقُّ مِن رَّبِّكَ ۖ فَلَا تَكُونَنَّ مِنَ ٱلْمُمْتَرِينَ۝١٤٧

    Alhaqqu min rabbika fala takoonanna mina almumtareena

    Gaskiya daga Ubangijinka1 take sabõda haka, lalle kada ka kasance daga mãsu shakka.

    Bayanai
    [1] Jũyãwar alƙibla abu ne na gaskiya daga Allah dõmin rarrashin wanda Allah bai yi nufi da tsĩrarsa ba ya ƙãre. Bãyan rarrashi sai yankewa wannan shi ne matakin farko da Musulmi suka fara tsiraita da shi daga maƙiyansu bayyane. Yanzu kuma Musulmi sun zama dabam.
  148. وَلِكُلٍّ وِجْهَةٌ هُوَ مُوَلِّيهَا ۖ فَٱسْتَبِقُوا۟ ٱلْخَيْرَٰتِ ۚ أَيْنَ مَا تَكُونُوا۟ يَأْتِ بِكُمُ ٱللَّهُ جَمِيعًا ۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍ قَدِيرٌ۝١٤٨

    Walikullin wijhatun huwa muwalleeha faistabiqoo alkhayrati ayna ma takoonoo yati bikumu Allahu jameeʿan inna Allaha ʿala kulli shayin qadeerun

    Kuma kõwane ɓangare yana da alƙibla wadda yake shi mai fuskantar ta ne. Sai ku yi tsẽre zuwa ga ayyukan alhẽri, inda kuka kasance duka Allah zai zo da ku gabã ɗaya. Lalle ne Allah, a kan kõme, Mai ĩkon yi ne.

  149. وَمِنْ حَيْثُ خَرَجْتَ فَوَلِّ وَجْهَكَ شَطْرَ ٱلْمَسْجِدِ ٱلْحَرَامِ ۖ وَإِنَّهُۥ لَلْحَقُّ مِن رَّبِّكَ ۗ وَمَا ٱللَّهُ بِغَـٰفِلٍ عَمَّا تَعْمَلُونَ۝١٤٩

    Wamin haythu kharajta fawalli wajhaka shatra almasjidi alharami wainnahu lalhaqqu min rabbika wama Allahu bighafilin ʿamma taʿmaloona

    Kuma daga inda ka fita, to, sai ka jũyar da fuskarka a wajen Masallãci Tsararre kuma lalle tabbas, shi ne gaskiya daga Ubangijinka. Kuma Allah bai zama Mai gafala ba daga abin da kuke aikatãwa ba.

  150. وَمِنْ حَيْثُ خَرَجْتَ فَوَلِّ وَجْهَكَ شَطْرَ ٱلْمَسْجِدِ ٱلْحَرَامِ ۚ وَحَيْثُ مَا كُنتُمْ فَوَلُّوا۟ وُجُوهَكُمْ شَطْرَهُۥ لِئَلَّا يَكُونَ لِلنَّاسِ عَلَيْكُمْ حُجَّةٌ إِلَّا ٱلَّذِينَ ظَلَمُوا۟ مِنْهُمْ فَلَا تَخْشَوْهُمْ وَٱخْشَوْنِى وَلِأُتِمَّ نِعْمَتِى عَلَيْكُمْ وَلَعَلَّكُمْ تَهْتَدُونَ۝١٥٠

    Wamin haythu kharajta fawalli wajhaka shatra almasjidi alharami wahaythu ma kuntum fawalloo wujoohakum shatrahu lialla yakoona lilnnasi ʿalaykum hujjatun illa allatheena thalamoo minhum fala takhshawhum waikhshawnee waliotimma niʿmatee ʿalaykum walaʿallakum tahtadoona

    Kuma daga inda ka fita, to, ka jũyar da fuskarka a wajen Masallãci Tsararre kuma inda kuke duka, to, ku jũyar da fuskõkinku a wajensa, dõmin kada wata hujja ta kasance ga mutãne a kanku, fãce waɗanda suka yi zãlunci daga gare su. Sabõda haka kada ku ji tsõronsu kuma ku ji tsõrõNa kuma dõmin In cika ni'imaTa a kanku, kuma tsammãninku zã ku shiryu.

  151. كَمَآ أَرْسَلْنَا فِيكُمْ رَسُولًا مِّنكُمْ يَتْلُوا۟ عَلَيْكُمْ ءَايَـٰتِنَا وَيُزَكِّيكُمْ وَيُعَلِّمُكُمُ ٱلْكِتَـٰبَ وَٱلْحِكْمَةَ وَيُعَلِّمُكُم مَّا لَمْ تَكُونُوا۟ تَعْلَمُونَ۝١٥١

    Kama arsalna feekum rasoolan minkum yatloo ʿalaykum ayatina wayuzakkeekum wayuʿallimukumu alkitaba waalhikmata wayuʿallimukum ma lam takoonoo taʿlamoona

    Kamar1 yadda Muka aika Manzo a cikinku, daga gare ku, yana karanta ãyõyinMu a gare ku kuma yana tsarkake ku, kuma yana sanar da ku Littãfi da hikima, kuma yana sanar da ku abin da ba ku kasance kuna sani ba.

    Bayanai
    [1] Jũyar da alƙibla da yankewa daga dukkan kãfirai da hani daga tsõronsu kuma Allah Ya farkar da Musulmi ga ni'imõmin da Ya yi musu game da aiko Annabi daga gare su, zuwa gare su, a cikinsu, dõmin ya tsarkake su, bayyane da ɓõye, daga dukan ƙurar kãfirci. Wannan ya nũna cewa sai an yi rarrashin mutãne wajen kira zuwa ga addini da kõwace hanya mai yiwuwa. Bãyan haka a yanke wa wanda ya ƙi bin gaskiya bayyane kuma kada a ji tsõronsa. Kuma aka umurce su da fuskanta zuwa ga Allah kawai da tunãwa gare Shi da gõdiya, da nisantar kafirci.
  152. فَٱذْكُرُونِىٓ أَذْكُرْكُمْ وَٱشْكُرُوا۟ لِى وَلَا تَكْفُرُونِ۝١٥٢

    Faothkuroonee athkurkum waoshkuroo lee wala takfurooni

    Sabõda haka, ku tuna Ni, In tunã ku, kuma ku yi gõdiya gare Ni, kuma kada ku butulce Mini.

  153. يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ ٱسْتَعِينُوا۟ بِٱلصَّبْرِ وَٱلصَّلَوٰةِ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ مَعَ ٱلصَّـٰبِرِينَ۝١٥٣

    Ya ayyuha allatheena amanoo istaʿeenoo bialssabri waalssalati inna Allaha maʿa alssabireena

    Ya ku waɗan da1suka yi ĩmãni! Ku nẽmi taimako da haƙuri game da salla. Lalle ne, Allah na tãre da mãsu haƙuri.

    Bayanai
    [1] Magana kuma ta fuskanta zuwa ga mũminai kawai dõmin a shirya zamansu.
  154. وَلَا تَقُولُوا۟ لِمَن يُقْتَلُ فِى سَبِيلِ ٱللَّهِ أَمْوَٰتٌۢ ۚ بَلْ أَحْيَآءٌ وَلَـٰكِن لَّا تَشْعُرُونَ۝١٥٤

    Wala taqooloo liman yuqtalu fee sabeeli Allahi amwatun bal ahyaon walakin la tashʿuroona

    kada ku ce ga waɗanda ake kashẽwa a cikin hanyar Allah: "Matattu ne." Ã'a, rãyayyu ne, kuma amma bã ku sani ba1 .

    Bayanai
    [1] Wanda ya tsiraita da kansa, to, maƙiyinsa bã zai bar shi ba, sabõda haka an fara ƙulla zukãtan mũminai ga tarbon wahalar tsiraita da dõgara ga kai, bãyan Allah.
  155. وَلَنَبْلُوَنَّكُم بِشَىْءٍ مِّنَ ٱلْخَوْفِ وَٱلْجُوعِ وَنَقْصٍ مِّنَ ٱلْأَمْوَٰلِ وَٱلْأَنفُسِ وَٱلثَّمَرَٰتِ ۗ وَبَشِّرِ ٱلصَّـٰبِرِينَ۝١٥٥

    Walanabluwannakum bishayin mina alkhawfi waaljooʿi wanaqsin mina alamwali waalanfusi waalththamarati wabashshiri alssabireena

    Kuma lalle ne, Muna jarrabar ku da wani abu daga tsõro da yunwa da naƙasa daga dũkiya da rãyuka da 'ya'yan itãce. Kuma ka yi bishãra ga mãsu haƙuri.

  156. ٱلَّذِينَ إِذَآ أَصَـٰبَتْهُم مُّصِيبَةٌ قَالُوٓا۟ إِنَّا لِلَّهِ وَإِنَّآ إِلَيْهِ رَٰجِعُونَ۝١٥٦

    Allatheena itha asabathum museebatun qaloo inna lillahi wainna ilayhi rajiʿoona

    Waɗanda suke idan wata masĩfa ta sãme su, sai su ce: "Lalle ne mũ ga Allah muke, kuma lalle ne mũ, zuwa gare Shi, muke kõmãwa."

  157. أُو۟لَـٰٓئِكَ عَلَيْهِمْ صَلَوَٰتٌ مِّن رَّبِّهِمْ وَرَحْمَةٌ ۖ وَأُو۟لَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلْمُهْتَدُونَ۝١٥٧

    Olaika ʿalayhim salawatun min rabbihim warahmatun waolaika humu almuhtadoona

    Waɗannan akwai albarku a kansu daga Ubangijinsu da wata rahama. Kuma waɗannan sũ ne shiryayyu.

  158. ۞ إِنَّ ٱلصَّفَا وَٱلْمَرْوَةَ مِن شَعَآئِرِ ٱللَّهِ ۖ فَمَنْ حَجَّ ٱلْبَيْتَ أَوِ ٱعْتَمَرَ فَلَا جُنَاحَ عَلَيْهِ أَن يَطَّوَّفَ بِهِمَا ۚ وَمَن تَطَوَّعَ خَيْرًا فَإِنَّ ٱللَّهَ شَاكِرٌ عَلِيمٌ۝١٥٨

    Inna alssafa waalmarwata min shaʿairi Allahi faman hajja albayta awi iʿtamara fala junaha ʿalayhi an yattawwafa bihima waman tatawwaʿa khayran fainna Allaha shakirun ʿaleemun

    Lalle ne Safã da Marwa1 suna daga wurãren ibãdar Allah, to, wanda ya yi hajin ¦ãki kõ kuwa ya yi Umra, to, bãbu laifi a kansa ga ya yi ɗawãfi gare su, su biyu. Kuma wanda ya ƙãra yin wani aikin alhẽri to, lalle ne Allah Mai gõdiya ne, Masani.

    Bayanai
    [1] Al'umma bã ta haɗuwa sai an wanke ta daga al'adun Jãhiliyya, har dai waɗanda suka haɗu da ibãda, sabõda haka aka fãra da Safã da Marwa dõmin a ije cewa ɗawãfi a tsakãninsu aikin Jãhiliyya ne, sũ suna cikin ayyukan ibãda da Allah Ya shar'anta kuma ɗawãfin mutãne da sa'ayi a kansu da tsakãninsu duka daidai suke Baƙuraishe da Balãrabe da Ba'ajame duka daidai suke.
  159. إِنَّ ٱلَّذِينَ يَكْتُمُونَ مَآ أَنزَلْنَا مِنَ ٱلْبَيِّنَـٰتِ وَٱلْهُدَىٰ مِنۢ بَعْدِ مَا بَيَّنَّـٰهُ لِلنَّاسِ فِى ٱلْكِتَـٰبِ ۙ أُو۟لَـٰٓئِكَ يَلْعَنُهُمُ ٱللَّهُ وَيَلْعَنُهُمُ ٱللَّـٰعِنُونَ۝١٥٩

    Inna allatheena yaktumoona ma anzalna mina albayyinati waalhuda min baʿdi ma bayyannahu lilnnasi fee alkitabi olaika yalʿanuhumu Allahu wayalʿanuhumu allaʿinoona

    Lalle ne waɗanda suke ɓõyẽwar abin da Allah Ya saukar da ga hujjõji bayyanannu, da shiriya, daga bãyan Mun bayyana shi ga mutãne, a cikin Littãfi (Alƙur'ãni), waɗannan Allah Yana la'anar su, kuma mãsu la'ana suna la'anar su.

  160. إِلَّا ٱلَّذِينَ تَابُوا۟ وَأَصْلَحُوا۟ وَبَيَّنُوا۟ فَأُو۟لَـٰٓئِكَ أَتُوبُ عَلَيْهِمْ ۚ وَأَنَا ٱلتَّوَّابُ ٱلرَّحِيمُ۝١٦٠

    Illa allatheena taboo waaslahoo wabayyanoo faolaika atoobu ʿalayhim waana alttawwabu alrraheemu

    Sai waɗanda suka tũba, kuma suka gyãra, kuma suka bayyana, to waɗannan Ina karɓar tũba a kansu kuma Nĩ ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai.

  161. إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ وَمَاتُوا۟ وَهُمْ كُفَّارٌ أُو۟لَـٰٓئِكَ عَلَيْهِمْ لَعْنَةُ ٱللَّهِ وَٱلْمَلَـٰٓئِكَةِ وَٱلنَّاسِ أَجْمَعِينَ۝١٦١

    Inna allatheena kafaroo wamatoo wahum kuffarun olaika ʿalayhim laʿnatu Allahi waalmalaikati waalnnasi ajmaʿeena

    Lalle ne, waɗanda suka kãfirta kuma suka mutu alhãli kuwa suna kãfirai, waɗannan akwai, a kansu, la'anar Allah da Malã'iku da mutãne gabã ɗaya.

  162. خَـٰلِدِينَ فِيهَا ۖ لَا يُخَفَّفُ عَنْهُمُ ٱلْعَذَابُ وَلَا هُمْ يُنظَرُونَ۝١٦٢

    Khalideena feeha la yukhaffafu ʿanhumu alʿathabu wala hum yuntharoona

    Suna madawwama a cikin ta, bã a sauƙaƙa Azãba daga barinsu, kuma ba su zama ana jinkirta musu ba.

  163. وَإِلَـٰهُكُمْ إِلَـٰهٌ وَٰحِدٌ ۖ لَّآ إِلَـٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلرَّحْمَـٰنُ ٱلرَّحِيمُ۝١٦٣

    Wailahukum ilahun wahidun la ilaha illa huwa alrrahmanu alrraheemu

    Kuma Ubangijinku Ubangiji1 Guda ne. Bãbu wani Ubangiji fãce Shi, Mai rahama, Mai jin ƙai.

    Bayanai
    [1] Ubangiji Shi ne Mai rãyarwa da matarwa, Mai umurni da hani kuma Mai halattãwa da haramtãwa. Ãyar da ke bin wannan tanã nũna dalilan sãmuwarSa da kaɗaitarSa.
  164. إِنَّ فِى خَلْقِ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ وَٱخْتِلَـٰفِ ٱلَّيْلِ وَٱلنَّهَارِ وَٱلْفُلْكِ ٱلَّتِى تَجْرِى فِى ٱلْبَحْرِ بِمَا يَنفَعُ ٱلنَّاسَ وَمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مِن مَّآءٍ فَأَحْيَا بِهِ ٱلْأَرْضَ بَعْدَ مَوْتِهَا وَبَثَّ فِيهَا مِن كُلِّ دَآبَّةٍ وَتَصْرِيفِ ٱلرِّيَـٰحِ وَٱلسَّحَابِ ٱلْمُسَخَّرِ بَيْنَ ٱلسَّمَآءِ وَٱلْأَرْضِ لَـَٔايَـٰتٍ لِّقَوْمٍ يَعْقِلُونَ۝١٦٤

    Inna fee khalqi alssamawati waalardi waikhtilafi allayli waalnnahari waalfulki allatee tajree fee albahri bima yanfaʿu alnnasa wama anzala Allahu mina alssamai min main faahya bihi alarda baʿda mawtiha wabaththa feeha min kulli dabbatin watasreefi alrriyahi waalssahabi almusakhkhari bayna alssamai waalardi laayatin liqawmin yaʿqiloona

    Lalle ne, a cikin halittar sammai da ƙasa, da sãɓãwar dare da yini, da jirãge wadaɗnda suke gudana a cikin tẽku (ɗauke) da abin da yake amfãnin mutãne, da abin da Allah Ya saukar daga sama daga ruwa, sai Ya rãyar da ƙasa da shi a bãyan mutuwarta, kuma Ya wãtsa, a cikinta, daga dukan dabba, kuma da jũyãwar iskõki da girgije hõrarre a tsakãnin sama da ƙasa; haƙĩƙa, akwaiãyõyi ga mutãne mãsu yin hankali.

  165. وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يَتَّخِذُ مِن دُونِ ٱللَّهِ أَندَادًا يُحِبُّونَهُمْ كَحُبِّ ٱللَّهِ ۖ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓا۟ أَشَدُّ حُبًّا لِّلَّهِ ۗ وَلَوْ يَرَى ٱلَّذِينَ ظَلَمُوٓا۟ إِذْ يَرَوْنَ ٱلْعَذَابَ أَنَّ ٱلْقُوَّةَ لِلَّهِ جَمِيعًا وَأَنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلْعَذَابِ۝١٦٥

    Wamina alnnasi man yattakhithu min dooni Allahi andadan yuhibboonahum kahubbi Allahi waallatheena amanoo ashaddu hubban lillahi walaw yara allatheena thalamoo ith yarawna alʿathaba anna alquwwata lillahi jameeʿan waanna Allaha shadeedu alʿathabi

    Kuma akwai daga mutãne wanda yake riƙon kinãye, baicin Allah, suna son su, kamar son Allah, kuma waɗanda suka yi ĩmãni ne mafiya tsananin so1 ga Allah. Kuma dã waɗanda2 suka yi zãlunci, suna ganin lõkacin da zã su ga azãba, da cewa lalle ne ƙarfi ga Allah yake duka, da cẽwa lalle neAllah Mai tsananin azãba ne.

    Bayanai
    [1] So mai kai ga karɓar umurni daga abin son, wanda ba Allah ba shi ne shirki da kãfirci. Amma so sabõda ihsãnin abin son, kõ dõmin zamansa sãlihi dõmin a yi kõyi da aikinsa na cikin haddõdin sharĩ'a, bã shirki ba ne, dõmin bai kai yadda mũminai ke son Allah ba. [2] Ãyõyi na l65 da l66 da 167 duka ɗinke suke ga ma'anoninsu. Ãyã ta l66 zarafi ce ga ta l65, sa'an nan ta 167 an haɗa rabinta ga ãyã ta 166. Sa'an nan sauran ãyã 167 ta zama ta'aƙĩbi da bayãni gare su duka.
  166. إِذْ تَبَرَّأَ ٱلَّذِينَ ٱتُّبِعُوا۟ مِنَ ٱلَّذِينَ ٱتَّبَعُوا۟ وَرَأَوُا۟ ٱلْعَذَابَ وَتَقَطَّعَتْ بِهِمُ ٱلْأَسْبَابُ۝١٦٦

    Ith tabarraa allatheena ittubiʿoo mina allatheena ittabaʿoo waraawoo alʿathaba wataqattaʿat bihimu alasbabu

    A lõkacin da waɗanda aka bi suka barranta daga waɗanda suka bi, kuma suka ga azãba, kuma sabubba suka yanke da su.

  167. وَقَالَ ٱلَّذِينَ ٱتَّبَعُوا۟ لَوْ أَنَّ لَنَا كَرَّةً فَنَتَبَرَّأَ مِنْهُمْ كَمَا تَبَرَّءُوا۟ مِنَّا ۗ كَذَٰلِكَ يُرِيهِمُ ٱللَّهُ أَعْمَـٰلَهُمْ حَسَرَٰتٍ عَلَيْهِمْ ۖ وَمَا هُم بِخَـٰرِجِينَ مِنَ ٱلنَّارِ۝١٦٧

    Waqala allatheena ittabaʿoo law anna lana karratan fanatabarraa minhum kama tabarraoo minna kathalika yureehimu Allahu aʿmalahum hasaratin ʿalayhim wama hum bikharijeena mina alnnari

    Kuma waɗanda suka bi, suka ce: "Dã lalle ne muna da wata kõmãwa (dũniya) sai mu barranta dagagare su kamar yadda suka barranta daga gare mu (dã ba su riƙi kinãyen ba)." Kamar wancan ne Allah ke nũna musu ayyukansu, suna da nadãmõmi a kansu, kuma ba su zama mãsu fita daga wutar ba.

  168. يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ كُلُوا۟ مِمَّا فِى ٱلْأَرْضِ حَلَـٰلًا طَيِّبًا وَلَا تَتَّبِعُوا۟ خُطُوَٰتِ ٱلشَّيْطَـٰنِ ۚ إِنَّهُۥ لَكُمْ عَدُوٌّ مُّبِينٌ۝١٦٨

    Ya ayyuha alnnasu kuloo mimma fee alardi halalan tayyiban wala tattabiʿoo khutuwati alshshaytani innahu lakum ʿaduwwun mubeenun

    Yã ku mutãne!1 Ku ci daga abin da yake a cikin ƙasa, wanda yake halal, mai dãɗi. Kuma kada ku bi zambiyõyin2 Shaiɗan. Lalle ne shi, gare ku, maƙiyi ne bayyananne.

    Bayanai
    [1] Yã kira mutãne a nan, bai ce mũminai ba, dõmin ba dukan Musulmi yake mũmini ba, sai wanda ya tsĩra daga ãyõyin da ke tafe. A cikinsu akwai abin da zai mai da Musulmi kãfiri kõ mai bidi'a. [2] Hanyõyin Shaiɗan ga halattar da abin da Allah Ya haramta kõ haramtar da abin da Allah Ya halatta dõmin kãga hukuncin da bai zo daga Allah ba, shirka ne tãre da Allah. Yã ce zambiyõyin Shaiɗan, dõmin Shaiɗan bã ya da hanya miƙaƙƙiya.
  169. إِنَّمَا يَأْمُرُكُم بِٱلسُّوٓءِ وَٱلْفَحْشَآءِ وَأَن تَقُولُوا۟ عَلَى ٱللَّهِ مَا لَا تَعْلَمُونَ۝١٦٩

    Innama yamurukum bialssooi waalfahshai waan taqooloo ʿala Allahi ma la taʿlamoona

    Yana umurnin ku ne kawai da mugun aiki da alfãsha, kuma da ku faɗi abin da ba ku sani ba ga Allah.

  170. وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ ٱتَّبِعُوا۟ مَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ قَالُوا۟ بَلْ نَتَّبِعُ مَآ أَلْفَيْنَا عَلَيْهِ ءَابَآءَنَآ ۗ أَوَلَوْ كَانَ ءَابَآؤُهُمْ لَا يَعْقِلُونَ شَيْـًٔا وَلَا يَهْتَدُونَ۝١٧٠

    Waitha qeela lahumu ittabiʿoo ma anzala Allahu qaloo bal nattabiʿu ma alfayna ʿalayhi abaana awalaw kana abaohum la yaʿqiloona shayan wala yahtadoona

    kuma idan aka ce musu, "Ku bi abin da Allah ya saukar," sai su ce: "Ã'a, munã bin abin da muka sãmi ubanninmu sun saba a kansa." ashe koda iyayen su sun zamanto basa iya fahimtar komai ballanta ma su shiriya ga gaskiya?,

  171. وَمَثَلُ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ كَمَثَلِ ٱلَّذِى يَنْعِقُ بِمَا لَا يَسْمَعُ إِلَّا دُعَآءً وَنِدَآءً ۚ صُمٌّۢ بُكْمٌ عُمْىٌ فَهُمْ لَا يَعْقِلُونَ۝١٧١

    Wamathalu allatheena kafaroo kamathali allathee yanʿiqu bima la yasmaʿu illa duʿaan wanidaan summun bukmun ʿumyun fahum la yaʿqiloona

    Kuma misãlin (mai kiran) waɗanda suka kãfirta kamar misãlin wanda ke yin me! me! ga abin da ba ya ji ne, fãce kira da ƙãra, kurãme, bẽbãye, makafi, sabõda haka bã su hankalta.

  172. يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ كُلُوا۟ مِن طَيِّبَـٰتِ مَا رَزَقْنَـٰكُمْ وَٱشْكُرُوا۟ لِلَّهِ إِن كُنتُمْ إِيَّاهُ تَعْبُدُونَ۝١٧٢

    Ya ayyuha allatheena amanoo kuloo min tayyibati ma razaqnakum waoshkuroo lillahi in kuntum iyyahu taʿbudoona

    Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku ci ku sha daga mãsu dãɗin abin da Muka azurta ku. Kuma ku gõde wa Allah, idan kun kasance Shi kuke bauta wa.

  173. إِنَّمَا حَرَّمَ عَلَيْكُمُ ٱلْمَيْتَةَ وَٱلدَّمَ وَلَحْمَ ٱلْخِنزِيرِ وَمَآ أُهِلَّ بِهِۦ لِغَيْرِ ٱللَّهِ ۖ فَمَنِ ٱضْطُرَّ غَيْرَ بَاغٍ وَلَا عَادٍ فَلَآ إِثْمَ عَلَيْهِ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ۝١٧٣

    Innama harrama ʿalaykumu almaytata waalddama walahma alkhinzeeri wama ohilla bihi lighayri Allahi famani idturra ghayra baghin wala ʿadin fala ithma ʿalayhi inna Allaha ghafoorun raheemun

    Kawai abin da Ya haramta a kanku, mũshe da Jini da nãman alade da abin da aka kurũrũta game da shi ga wanin Allah. To, wanda aka matsã, wanin ɗan tãwãye, kuma banda mai zãlunci, to bãbu laifi a kansa. Lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.

  174. إِنَّ ٱلَّذِينَ يَكْتُمُونَ مَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ مِنَ ٱلْكِتَـٰبِ وَيَشْتَرُونَ بِهِۦ ثَمَنًا قَلِيلًا ۙ أُو۟لَـٰٓئِكَ مَا يَأْكُلُونَ فِى بُطُونِهِمْ إِلَّا ٱلنَّارَ وَلَا يُكَلِّمُهُمُ ٱللَّهُ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ وَلَا يُزَكِّيهِمْ وَلَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ۝١٧٤

    Inna allatheena yaktumoona ma anzala Allahu mina alkitabi wayashtaroona bihi thamanan qaleelan olaika ma yakuloona fee butoonihim illa alnnara wala yukallimuhumu Allahu yawma alqiyamati wala yuzakkeehim walahum ʿathabun aleemun

    Lalle ne waɗannan da suke ɓõye abin da Allah Ya saukar daga Littãfi, kuma suna sayen kuɗi kaɗan da shi; waɗannan bã su cin kome a cikin cikkunansu fãce wuta, kuma Allah bã zai yi musu magana ba a Rãnar ¡iyãma, kuma bã zai tsarkake su ba, kuma suna da azãba mai raɗaɗi.

  175. أُو۟لَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ ٱشْتَرَوُا۟ ٱلضَّلَـٰلَةَ بِٱلْهُدَىٰ وَٱلْعَذَابَ بِٱلْمَغْفِرَةِ ۚ فَمَآ أَصْبَرَهُمْ عَلَى ٱلنَّارِ۝١٧٥

    Olaika allatheena ishtarawoo alddalalata bialhuda waalʿathaba bialmaghfirati fama asbarahum ʿala alnnari

    Waɗan nan su ne waɗan da suka sayi ɓata da shiriya, kuma azãba da gãfara. To, me ya yi haƙurin su a kan Wuta!

  176. ذَٰلِكَ بِأَنَّ ٱللَّهَ نَزَّلَ ٱلْكِتَـٰبَ بِٱلْحَقِّ ۗ وَإِنَّ ٱلَّذِينَ ٱخْتَلَفُوا۟ فِى ٱلْكِتَـٰبِ لَفِى شِقَاقٍۭ بَعِيدٍ۝١٧٦

    Thalika bianna Allaha nazzala alkitaba bialhaqqi wainna allatheena ikhtalafoo fee alkitabi lafee shiqaqin baʿeedin

    Wancan dõmin lalle ne Allah Ya saukar da Littafi da gaskiya, kuma lalle ne waɗanda suka sãɓã a cikin Littãfin, haƙĩƙa, suna a cikin sãɓãni mai nĩsa.

  177. ۞ لَّيْسَ ٱلْبِرَّ أَن تُوَلُّوا۟ وُجُوهَكُمْ قِبَلَ ٱلْمَشْرِقِ وَٱلْمَغْرِبِ وَلَـٰكِنَّ ٱلْبِرَّ مَنْ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَٱلْيَوْمِ ٱلْـَٔاخِرِ وَٱلْمَلَـٰٓئِكَةِ وَٱلْكِتَـٰبِ وَٱلنَّبِيِّـۧنَ وَءَاتَى ٱلْمَالَ عَلَىٰ حُبِّهِۦ ذَوِى ٱلْقُرْبَىٰ وَٱلْيَتَـٰمَىٰ وَٱلْمَسَـٰكِينَ وَٱبْنَ ٱلسَّبِيلِ وَٱلسَّآئِلِينَ وَفِى ٱلرِّقَابِ وَأَقَامَ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتَى ٱلزَّكَوٰةَ وَٱلْمُوفُونَ بِعَهْدِهِمْ إِذَا عَـٰهَدُوا۟ ۖ وَٱلصَّـٰبِرِينَ فِى ٱلْبَأْسَآءِ وَٱلضَّرَّآءِ وَحِينَ ٱلْبَأْسِ ۗ أُو۟لَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ صَدَقُوا۟ ۖ وَأُو۟لَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلْمُتَّقُونَ۝١٧٧

    Laysa albirra an tuwalloo wujoohakum qibala almashriqi waalmaghribi walakinna albirra man amana biAllahi waalyawmi alakhiri waalmalaikati waalkitabi waalnnabiyyeena waata almala ʿala hubbihi thawee alqurba waalyatama waalmasakeena waibna alssabeeli waalssaileena wafee alrriqabi waaqama alssalata waata alzzakata waalmoofoona biʿahdihim itha ʿahadoo waalssabireena fee albasai waalddarrai waheena albasi olaika allatheena sadaqoo waolaika humu almuttaqoona

    Bai zama addini1 ba dõmin kun jũyar da fuskõkinku wajen gabas da yamma, kuma amma addini shi ne ga wanda ya yi ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira da malã'iku da Littattafan sama da Annabãwa, kuma ya bãyar da dũkiya, akan yana son ta, ga mai zumunta da marãyu da matalauta da ɗan hanya da mãsu rõƙo, kuma a cikin fansar wuya, kuma ya tsayar da salla, kuma ya bãyar da zakka, da mãsu cika alkawari idan sun ƙulla alkawarin da mãsu haƙuri a cikin tsanani da cũta da lõkacin yãƙi. Waɗannan su ne suka yi gaskiya. Kuma waɗannan su ne mãsu taƙawa.

    Bayanai
    [1] Bayãnin cewa Musulunci bã yin salla ɗai ba ne. A'aha! Musulunci tsarewar rãyuwane kamar yadda Allah Ya ce a tsare ta.
  178. يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ كُتِبَ عَلَيْكُمُ ٱلْقِصَاصُ فِى ٱلْقَتْلَى ۖ ٱلْحُرُّ بِٱلْحُرِّ وَٱلْعَبْدُ بِٱلْعَبْدِ وَٱلْأُنثَىٰ بِٱلْأُنثَىٰ ۚ فَمَنْ عُفِىَ لَهُۥ مِنْ أَخِيهِ شَىْءٌ فَٱتِّبَاعٌۢ بِٱلْمَعْرُوفِ وَأَدَآءٌ إِلَيْهِ بِإِحْسَـٰنٍ ۗ ذَٰلِكَ تَخْفِيفٌ مِّن رَّبِّكُمْ وَرَحْمَةٌ ۗ فَمَنِ ٱعْتَدَىٰ بَعْدَ ذَٰلِكَ فَلَهُۥ عَذَابٌ أَلِيمٌ۝١٧٨

    Ya ayyuha allatheena amanoo kutiba ʿalaykumu alqisasu fee alqatla alhurru bialhurri waalʿabdu bialʿabdi waalontha bialontha faman ʿufiya lahu min akheehi shayon faittibaʿun bialmaʿroofi waadaon ilayhi biihsanin thalika takhfeefun min rabbikum warahmatun famani iʿtada baʿda thalika falahu ʿathabun aleemun

    Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! An wajabta, a kanku, yin ƙisãsi1 a cikin kasassu. ɗa da ɗa kuma bãwa da bãwa, kuma mace da mace, to, wanda aka yi rangwamen wani abu gare shi daga ɗan'uwansa to a bi da alhẽri da biya zuwa gare, shi da kyautatãwa. Wancan sauƙaƙewa ne daga Ubangijinku, kuma rahama ce. To, wanda ya yi zãlunci a bãyan wancan, to, yana da azãba mai raɗaɗi.

    Bayanai
    [1] Bayãnin hukuncin ƙisãsi: Ana kashe namiji sabõda ya kashe mace, bã a kashe ɗa da Musulmi saboda kashin bãwa da kãfiri sai idan ya zama kisan gila ne kõ ƙwãce. Gila shĩ ne kashe mutum dõmin dũkiyarsa kõ mãtarsa.
  179. وَلَكُمْ فِى ٱلْقِصَاصِ حَيَوٰةٌ يَـٰٓأُو۟لِى ٱلْأَلْبَـٰبِ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ۝١٧٩

    Walakum fee alqisasi hayatun ya olee alalbabi laʿallakum tattaqoona

    Kuma kuna da rãyuwa a cikin ƙisãsi, yã ma'abuta hankula; tsammãninku, zã ku yi taƙawa.

  180. كُتِبَ عَلَيْكُمْ إِذَا حَضَرَ أَحَدَكُمُ ٱلْمَوْتُ إِن تَرَكَ خَيْرًا ٱلْوَصِيَّةُ لِلْوَٰلِدَيْنِ وَٱلْأَقْرَبِينَ بِٱلْمَعْرُوفِ ۖ حَقًّا عَلَى ٱلْمُتَّقِينَ۝١٨٠

    Kutiba ʿalaykum itha hadara ahadakumu almawtu in taraka khayran alwasiyyatu lilwalidayni waalaqrabeena bialmaʿroofi haqqan ʿala almuttaqeena

    Kuma an wajabta,1 a kanku idan mutuwa ta halarci ɗayanku, idan ya bar wata dũkiya, wasiyya dõmin mahaifa da dangi bisa ga abin da aka sani; wajabce a kan mãsu taƙawa.

    Bayanai
    [1] Bayãnin hukuncin wasiyya: Sunna ta bayyana cewa bãbu wasiyya ga wanda zai yi gãdo, kuma wasiyya bã zã ta shige sulusin dũkiyar tarika ba.
  181. فَمَنۢ بَدَّلَهُۥ بَعْدَ مَا سَمِعَهُۥ فَإِنَّمَآ إِثْمُهُۥ عَلَى ٱلَّذِينَ يُبَدِّلُونَهُۥٓ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَمِيعٌ عَلِيمٌ۝١٨١

    Faman baddalahu baʿdama samiʿahu fainnama ithmuhu ʿala allatheena yubaddiloonahu inna Allaha sameeʿun ʿaleemun

    To, wanda ya musanya masa a bãyan ya ji shi, to, kawai laifinsa yana a kan waɗanda suke musanya shi. Lalle ne, Allah Mai ji ne, Masani.

  182. فَمَنْ خَافَ مِن مُّوصٍ جَنَفًا أَوْ إِثْمًا فَأَصْلَحَ بَيْنَهُمْ فَلَآ إِثْمَ عَلَيْهِ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ۝١٨٢

    Faman khafa min moosin janafan aw ithman faaslaha baynahum fala ithma ʿalayhi inna Allaha ghafoorun raheemun

    To, wanda ya ji tsõron karkata ko kuwa wani zunubi daga mai wasiyyar, sai ya yi sulhi a tsakãninsu to bãbu laifi a kansa. Lalle ne Allah, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.

  183. يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ كُتِبَ عَلَيْكُمُ ٱلصِّيَامُ كَمَا كُتِبَ عَلَى ٱلَّذِينَ مِن قَبْلِكُمْ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ۝١٨٣

    Ya ayyuha allatheena amanoo kutiba ʿalaykumu alssiyamu kama kutiba ʿala allatheena min qablikum laʿallakum tattaqoona

    Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! An wajabta1 azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan waɗanda suke daga gabãninku, tsammãninku, zã ku yi taƙawa,

    Bayanai
    [1] Bayãnin hukuncin azumi da darajar watan Ramalãna wanda aka saukar da Alƙur'ãni a cikinsa.
  184. أَيَّامًا مَّعْدُودَٰتٍ ۚ فَمَن كَانَ مِنكُم مَّرِيضًا أَوْ عَلَىٰ سَفَرٍ فَعِدَّةٌ مِّنْ أَيَّامٍ أُخَرَ ۚ وَعَلَى ٱلَّذِينَ يُطِيقُونَهُۥ فِدْيَةٌ طَعَامُ مِسْكِينٍ ۖ فَمَن تَطَوَّعَ خَيْرًا فَهُوَ خَيْرٌ لَّهُۥ ۚ وَأَن تَصُومُوا۟ خَيْرٌ لَّكُمْ ۖ إِن كُنتُمْ تَعْلَمُونَ۝١٨٤

    Ayyaman maʿdoodatin faman kana minkum mareedan aw ʿala safarin faʿiddatun min ayyamin okhara waʿala allatheena yuteeqoonahu fidyatun taʿamu miskeenin faman tatawwaʿa khayran fahuwa khayrun lahu waan tasoomoo khayrun lakum in kuntum taʿlamoona

    Kwanuka ƙidãyayyu. To, wanda ya kasance daga gare ku majinyaci ko kuwa yana a kan tafiya, sai (ya biya) adadi daga wasu kwanuka na dabam. Kuma a kan waɗanda suke yin sa da wahala akwai fansa; ciyar da matalauci, sai dai wanda ya ƙãra alhẽri to, shi ne mafi alhẽri a gare shi. Kuma ku yi azumi (da wahalar) ne mafi alhẽri a gare ku idan kun kasance kuna sani.

  185. شَهْرُ رَمَضَانَ ٱلَّذِىٓ أُنزِلَ فِيهِ ٱلْقُرْءَانُ هُدًى لِّلنَّاسِ وَبَيِّنَـٰتٍ مِّنَ ٱلْهُدَىٰ وَٱلْفُرْقَانِ ۚ فَمَن شَهِدَ مِنكُمُ ٱلشَّهْرَ فَلْيَصُمْهُ ۖ وَمَن كَانَ مَرِيضًا أَوْ عَلَىٰ سَفَرٍ فَعِدَّةٌ مِّنْ أَيَّامٍ أُخَرَ ۗ يُرِيدُ ٱللَّهُ بِكُمُ ٱلْيُسْرَ وَلَا يُرِيدُ بِكُمُ ٱلْعُسْرَ وَلِتُكْمِلُوا۟ ٱلْعِدَّةَ وَلِتُكَبِّرُوا۟ ٱللَّهَ عَلَىٰ مَا هَدَىٰكُمْ وَلَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ۝١٨٥

    Shahru ramadana allathee onzila feehi alquranu hudan lilnnasi wabayyinatin mina alhuda waalfurqani faman shahida minkumu alshshahra falyasumhu waman kana mareedan aw ʿala safarin faʿiddatun min ayyamin okhara yureedu Allahu bikumu alyusra wala yureedu bikumu alʿusra walitukmiloo alʿiddata walitukabbiroo Allaha ʿala ma hadakum walaʿallakum tashkuroona

    Watan Ramalãna ne wanda aka saukar da Alƙur'ãni a cikinsa yana shiriya ga mutãne da hujjõji bayyanannu daga shiriya da rarrabẽwa. To, wanda ya halarta daga gare ku a watan, sai ya azumce shi, kuma wanda ya kasance majinyaci ko kuwa a kan tafiya, sai ya biya adadi daga wasu kwanuka na dabam. Allah Yana nufin sauƙi gare ku, kuma ba Ya nufin tsanani gare ku, kuma dõmin ku cika adadin, kuma dõmin ku girmama Allah a kan Yã shiryar da ku, kuma tsammãninku, zã ku gõde.

  186. وَإِذَا سَأَلَكَ عِبَادِى عَنِّى فَإِنِّى قَرِيبٌ ۖ أُجِيبُ دَعْوَةَ ٱلدَّاعِ إِذَا دَعَانِ ۖ فَلْيَسْتَجِيبُوا۟ لِى وَلْيُؤْمِنُوا۟ بِى لَعَلَّهُمْ يَرْشُدُونَ۝١٨٦

    Waitha saalaka ʿibadee ʿannee fainnee qareebun ojeebu daʿwata alddaʿi itha daʿani falyastajeeboo lee walyuminoo bee laʿallahum yarshudoona

    Kuma idan bãyiNa suka tambaye ka daga gare Ni, to, lalle Ni Makusanci ne. Ina karɓa kiran mai kira idan ya kirã Ni.1 Sabõda haka su nẽmi karɓawaTa, kuma su yi ĩmãni da Ni: tsammãninsu, su shiryu.

    Bayanai
    [1] Bayãnin yin addu'a: Anã son addu'a a cikin ramalãna, yadda neman karɓar addu'a da aikin da'a yake bãyan imani. Aikin ƙwarai shine gõɗiyar Addu'a.
  187. أُحِلَّ لَكُمْ لَيْلَةَ ٱلصِّيَامِ ٱلرَّفَثُ إِلَىٰ نِسَآئِكُمْ ۚ هُنَّ لِبَاسٌ لَّكُمْ وَأَنتُمْ لِبَاسٌ لَّهُنَّ ۗ عَلِمَ ٱللَّهُ أَنَّكُمْ كُنتُمْ تَخْتَانُونَ أَنفُسَكُمْ فَتَابَ عَلَيْكُمْ وَعَفَا عَنكُمْ ۖ فَٱلْـَٔـٰنَ بَـٰشِرُوهُنَّ وَٱبْتَغُوا۟ مَا كَتَبَ ٱللَّهُ لَكُمْ ۚ وَكُلُوا۟ وَٱشْرَبُوا۟ حَتَّىٰ يَتَبَيَّنَ لَكُمُ ٱلْخَيْطُ ٱلْأَبْيَضُ مِنَ ٱلْخَيْطِ ٱلْأَسْوَدِ مِنَ ٱلْفَجْرِ ۖ ثُمَّ أَتِمُّوا۟ ٱلصِّيَامَ إِلَى ٱلَّيْلِ ۚ وَلَا تُبَـٰشِرُوهُنَّ وَأَنتُمْ عَـٰكِفُونَ فِى ٱلْمَسَـٰجِدِ ۗ تِلْكَ حُدُودُ ٱللَّهِ فَلَا تَقْرَبُوهَا ۗ كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ ٱللَّهُ ءَايَـٰتِهِۦ لِلنَّاسِ لَعَلَّهُمْ يَتَّقُونَ۝١٨٧

    Ohilla lakum laylata alssiyami alrrafathu ila nisaikum hunna libasun lakum waantum libasun lahunna ʿalima Allahu annakum kuntum takhtanoona anfusakum fataba ʿalaykum waʿafa ʿankum faalana bashiroohunna waibtaghoo ma kataba Allahu lakum wakuloo waishraboo hatta yatabayyana lakumu alkhaytu alabyadu mina alkhayti alaswadi mina alfajri thumma atimmoo alssiyama ila allayli wala tubashiroohunna waantum ʿakifoona fee almasajidi tilka hudoodu Allahi fala taqrabooha kathalika yubayyinu Allahu ayatihi lilnnasi laʿallahum yattaqoona

    An halatta a gare ku, a daren azumi, yin jima'i1 zuwa ga matanku sũ tufa ne a gare ku, kuma kũ tufa ne a gare su, Allah Yã sani lalle ne ku kun kasance kuna yaudarar kanku. Sabõda haka Yã karɓi tũbarku, kuma Yã yãfe muku. To, yanzu ku rungume su kuma ku nẽmi abin da Allah yã rubũta muku. Kuma ku ci kuma ku sha har sĩlĩli fari ya bayyana a gare ku daga sĩlĩli baƙi daga alfijiri, sa'an nan kuma ku cika azumi zuwa ga dare. Kuma kada ku rungume su alhãli kuna mãsu itikãfi a cikin masallãtai. Waɗancan iyãkokin Allah ne: don haka kada ku kusancesu kamar haka ne Allah Yake bayyana ãyõyinSa ga mutãne: tsammãninsu, zã su yi taƙawa.

    Bayanai
    [1] Abũbuwan da aka hana, a cikin azumi, da ranã, an halatta su da dare har zuwa fitar alfijiri wato sĩlĩli fari na hasken sãfiya da sĩlĩli baƙi na duhun dare. Bã a yin jima'i kõ da dare a hãlin itikãfi, kuma bã a yin itikãfi sai a cikin masallãci.
  188. وَلَا تَأْكُلُوٓا۟ أَمْوَٰلَكُم بَيْنَكُم بِٱلْبَـٰطِلِ وَتُدْلُوا۟ بِهَآ إِلَى ٱلْحُكَّامِ لِتَأْكُلُوا۟ فَرِيقًا مِّنْ أَمْوَٰلِ ٱلنَّاسِ بِٱلْإِثْمِ وَأَنتُمْ تَعْلَمُونَ۝١٨٨

    Wala takuloo amwalakum baynakum bialbatili watudloo biha ila alhukkami litakuloo fareeqan min amwali alnnasi bialithmi waantum taʿlamoona

    Kada ku ci dukiyõyinku1 a tsakãninku da ƙarya, kuma ku sãdu da ita zuwa ga mahukunta dõmin ku ci wani yanki daga dũkiyõyin mutãne da zunubi alhãli kuwa kũ, kuna sane.

    Bayanai
    [1] Haramun ne cin dũkiyar mutãne da zãlunci. An haɗa wannan ãyã da ta gabãninta, ta azumi, dõmin haɗin hana ci da ya gama su. Sãduwa da mahukunta da dukiya, shi ne rashawa, Allah Yã la'ani mai bãyar da ita da mai karɓarta.
  189. ۞ يَسْـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلْأَهِلَّةِ ۖ قُلْ هِىَ مَوَٰقِيتُ لِلنَّاسِ وَٱلْحَجِّ ۗ وَلَيْسَ ٱلْبِرُّ بِأَن تَأْتُوا۟ ٱلْبُيُوتَ مِن ظُهُورِهَا وَلَـٰكِنَّ ٱلْبِرَّ مَنِ ٱتَّقَىٰ ۗ وَأْتُوا۟ ٱلْبُيُوتَ مِنْ أَبْوَٰبِهَا ۚ وَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ۝١٨٩

    Yasaloonaka ʿani alahillati qul hiya mawaqeetu lilnnasi waalhajji walaysa albirru bian tatoo albuyoota min thuhooriha walakinna albirra mani ittaqa watoo albuyoota min abwabiha waittaqoo Allaha laʿallakum tuflihoona

    Kuma suna tambayar ka1 daga jirajiran wata. Ka ce: "Su lõkatai ne dõmin mutãne da haji, kuma bã addini ba ne ku je wa gidãje daga bãyansu: kuma amma abin da yake addini shi ne wanda ya yi taƙawa. Kuma ku je wa gidãje daga ƙõfõfinsu, kuma ku bi Allah da taƙawa: tsammãninku, ku ci nasara.

    Bayanai
    [1] Shiga Musulunci yarda ne da barin al'ãdu da hukunce-hukuncen jãhiliyya, sabõda haka ake sãmun tambayõyi da yawa daga sãbon Musulmi kãfin ya kammala da canza tsõfaffin al'ãdunsa da sãbabbi. Allah Yã yi tarbiyar Sahabban Annabi a cikin rãyuwar Annabi, bãyan saukar wahayi.
  190. وَقَـٰتِلُوا۟ فِى سَبِيلِ ٱللَّهِ ٱلَّذِينَ يُقَـٰتِلُونَكُمْ وَلَا تَعْتَدُوٓا۟ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ ٱلْمُعْتَدِينَ۝١٩٠

    Waqatiloo fee sabeeli Allahi allatheena yuqatiloonakum wala taʿtadoo inna Allaha la yuhibbu almuʿtadeena

    Kuma ku yãƙi waɗanda1 suke yãƙinku, a cikin hanyar Allah, kuma kada ku yi tsõkana, lalle ne Allah bã Ya son mãsu tsõkana.

    Bayanai
    [1] An umurci Musulmi da tsare kansu da yãƙi ga duk wanda ya yãƙe su, a kõ'ina yake. Sai dai an hana su tsõkanar wasu, kuma an hana su su yi yãƙi a cikin Hurumin Makka sai fa idan an fãɗa su da yãƙi a cikinsa.
  191. وَٱقْتُلُوهُمْ حَيْثُ ثَقِفْتُمُوهُمْ وَأَخْرِجُوهُم مِّنْ حَيْثُ أَخْرَجُوكُمْ ۚ وَٱلْفِتْنَةُ أَشَدُّ مِنَ ٱلْقَتْلِ ۚ وَلَا تُقَـٰتِلُوهُمْ عِندَ ٱلْمَسْجِدِ ٱلْحَرَامِ حَتَّىٰ يُقَـٰتِلُوكُمْ فِيهِ ۖ فَإِن قَـٰتَلُوكُمْ فَٱقْتُلُوهُمْ ۗ كَذَٰلِكَ جَزَآءُ ٱلْكَـٰفِرِينَ۝١٩١

    Waoqtuloohum haythu thaqiftumoohum waakhrijoohum min haythu akhrajookum waalfitnatu ashaddu mina alqatli wala tuqatiloohum ʿinda almasjidi alharami hatta yuqatilookum feehi fain qatalookum faoqtuloohum kathalika jazao alkafireena

    Kuma ku yãƙe su inda kuka sãme su, kuma ku fitar da su daga inda suka fitar da ku. Kuma fitina ita ce mafi tsanani daga kisa. Kuma kada ku yãƙe su a wurin Masallãci Tsararre (Hurumin Makka) fãce fa idan sun yãƙe ku a cikinsa. To, idan sun yãƙe ku, sai ku yãƙe su. Kamar wancan ne sakamakon kãfirai yake.

  192. فَإِنِ ٱنتَهَوْا۟ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ۝١٩٢

    Faini intahaw fainna Allaha ghafoorun raheemun

    Sa'an nan idan sun hanu, to, lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.

  193. وَقَـٰتِلُوهُمْ حَتَّىٰ لَا تَكُونَ فِتْنَةٌ وَيَكُونَ ٱلدِّينُ لِلَّهِ ۖ فَإِنِ ٱنتَهَوْا۟ فَلَا عُدْوَٰنَ إِلَّا عَلَى ٱلظَّـٰلِمِينَ۝١٩٣

    Waqatiloohum hatta la takoona fitnatun wayakoona alddeenu lillahi faini intahaw fala ʿudwana illa ʿala alththalimeena

    Kuma ku yãƙe1 su har ya zama wata fitina bã zã ta kasance ba, kuma addini ya zama na Allah. Sa'an nan idan sun hanu to bãbu tsõkana fãce a kan azzãlumai.

    Bayanai
    [1] An umurci Musulmi da tsõkana ga kãfiran da suke nũna musu ƙiyayya bayyane, dõmin su hana su yin addininsu da kyau, kamar yadda Allah Ya umurce su, suna fitinar su da wahalõli. Kuma kada ku bar su, su laɓe da wani watan alfarma kõ hurumi, duk yadda hãli ya yi, a yi haka nan, alfarmõmi nã da ƙisãsi.
  194. ٱلشَّهْرُ ٱلْحَرَامُ بِٱلشَّهْرِ ٱلْحَرَامِ وَٱلْحُرُمَـٰتُ قِصَاصٌ ۚ فَمَنِ ٱعْتَدَىٰ عَلَيْكُمْ فَٱعْتَدُوا۟ عَلَيْهِ بِمِثْلِ مَا ٱعْتَدَىٰ عَلَيْكُمْ ۚ وَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَٱعْلَمُوٓا۟ أَنَّ ٱللَّهَ مَعَ ٱلْمُتَّقِينَ۝١٩٤

    Alshshahru alharamu bialshshahri alharami waalhurumatu qisasun famani iʿtada ʿalaykum faiʿtadoo ʿalayhi bimithli ma iʿtada ʿalaykum waittaqoo Allaha waiʿlamoo anna Allaha maʿa almuttaqeena

    Watan alfarma da wani watan alfarma alfarmõmi mãsu dũkar jũna ne. Sabõda haka wanda ya yi tsõkana a kanku, sai ku yi tsokana a kansa da misãlin abin da ya yi tsõkana a kanku. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma ku sani cẽwa lalle ne, Allah Yana tãre da mãsu taƙawa.

  195. وَأَنفِقُوا۟ فِى سَبِيلِ ٱللَّهِ وَلَا تُلْقُوا۟ بِأَيْدِيكُمْ إِلَى ٱلتَّهْلُكَةِ ۛ وَأَحْسِنُوٓا۟ ۛ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلْمُحْسِنِينَ۝١٩٥

    Waanfiqoo fee sabeeli Allahi wala tulqoo biaydeekum ila alttahlukati waahsinoo inna Allaha yuhibbu almuhsineena

    Kuma ku ciyar1 a cikin hanyar Allah. Kuma kada ku jefa kanku da hannayenku, zuwa ga halaka. Kuma ku kyautata; lalle ne, Allah Yana son mãsu kyautatãwa.

    Bayanai
    [1] Bã a iya yãƙi sai da abinci, kuma bã kõwa ke iya zuwa yãƙi ba, kamar yadda yake bã kowa yake da abinci ba. Sabõda haka sai a ciyar da dũkiya, a tãra ta dõmin ɗaukaka kalmar Allah. Rashin bãyar da ita, to, halaka kai ne.
  196. وَأَتِمُّوا۟ ٱلْحَجَّ وَٱلْعُمْرَةَ لِلَّهِ ۚ فَإِنْ أُحْصِرْتُمْ فَمَا ٱسْتَيْسَرَ مِنَ ٱلْهَدْىِ ۖ وَلَا تَحْلِقُوا۟ رُءُوسَكُمْ حَتَّىٰ يَبْلُغَ ٱلْهَدْىُ مَحِلَّهُۥ ۚ فَمَن كَانَ مِنكُم مَّرِيضًا أَوْ بِهِۦٓ أَذًى مِّن رَّأْسِهِۦ فَفِدْيَةٌ مِّن صِيَامٍ أَوْ صَدَقَةٍ أَوْ نُسُكٍ ۚ فَإِذَآ أَمِنتُمْ فَمَن تَمَتَّعَ بِٱلْعُمْرَةِ إِلَى ٱلْحَجِّ فَمَا ٱسْتَيْسَرَ مِنَ ٱلْهَدْىِ ۚ فَمَن لَّمْ يَجِدْ فَصِيَامُ ثَلَـٰثَةِ أَيَّامٍ فِى ٱلْحَجِّ وَسَبْعَةٍ إِذَا رَجَعْتُمْ ۗ تِلْكَ عَشَرَةٌ كَامِلَةٌ ۗ ذَٰلِكَ لِمَن لَّمْ يَكُنْ أَهْلُهُۥ حَاضِرِى ٱلْمَسْجِدِ ٱلْحَرَامِ ۚ وَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَٱعْلَمُوٓا۟ أَنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلْعِقَابِ۝١٩٦

    Waatimmoo alhajja waalʿumrata lillahi fain ohsirtum fama istaysara mina alhadyi wala tahliqoo ruoosakum hatta yablugha alhadyu mahillahu faman kana minkum mareedan aw bihi athan min rasihi fafidyatun min siyamin aw sadaqatin aw nusukin faitha amintum faman tamattaʿa bialʿumrati ila alhajji fama istaysara mina alhadyi faman lam yajid fasiyamu thalathati ayyamin fee alhajji wasabʿatin itha rajaʿtum tilka ʿasharatun kamilatun thalika liman lam yakun ahluhu hadiree almasjidi alharami waittaqoo Allaha waiʿlamoo anna Allaha shadeedu alʿiqabi

    Kuma ku cika1 hajji da umra dõmin Allah. To idan an kange ku, to, ku bãyar da abin da ya sauƙaƙa na hadaya. Kuma kada ku aske kãnunku, sai hadaya ta kai wurinta. To, wanda ya kasance majinyaci daga cikinku, kõ kuwa akwai wata cũta daga kansa (ya yi aski) sai fansa (fidiya) daga azumi ko kuwa sadaka ko kuwa yanka. To, idan kuna cikin aminci to, wanda ya ji dãdi da umra zuwa haji, sai ya biya abin da ya sauƙaƙa daga hadaya, sa'an nan wanda bai sãmu ba, sai azumin yini uku a cikin haji da bakwai idan kun kõma, waɗancan gõma ne cikakku. Wancan yana ga wanda iyãlinsa ba su kasance mazaunan Masallãci Tsararre ba. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma ku sani cewa Allah Mai tsananin uƙũba ne.

    Bayanai
    [1] Hukunce-hukuncen hajji a cikin fitina kõ a cikin rashin lãfiya, idan sun auku a bãyan harama, da hukuncin wanda ya ji dãɗi da umra sa'annan ya yi hajji, kõ kuma ya haɗa su a cikin harama guda, watau ƙirãni, hukuncinsu ɗaya ne.
  197. ٱلْحَجُّ أَشْهُرٌ مَّعْلُومَـٰتٌ ۚ فَمَن فَرَضَ فِيهِنَّ ٱلْحَجَّ فَلَا رَفَثَ وَلَا فُسُوقَ وَلَا جِدَالَ فِى ٱلْحَجِّ ۗ وَمَا تَفْعَلُوا۟ مِنْ خَيْرٍ يَعْلَمْهُ ٱللَّهُ ۗ وَتَزَوَّدُوا۟ فَإِنَّ خَيْرَ ٱلزَّادِ ٱلتَّقْوَىٰ ۚ وَٱتَّقُونِ يَـٰٓأُو۟لِى ٱلْأَلْبَـٰبِ۝١٩٧

    Alhajju ashhurun maʿloomatun faman farada feehinna alhajja fala rafatha wala fusooqa wala jidala fee alhajji wama tafʿaloo min khayrin yaʿlamhu Allahu watazawwadoo fainna khayra alzzadi alttaqwa waittaqooni ya olee alalbabi

    Hajji watanni ne sanannu. To, wanda ya yi niyyar hajji1 a cikinsu to bãbu jimã'i kuma bãbu fãsiƙanci, kuma bãbu jãyayya a cikin hajji. Kuma abin da kuka aikata daga alhẽri, Allah Ya san shi. Kuma ku yi guzuri. To, mafi alhẽrin guzuri yin taƙawa. Kuma ku bi Ni da taƙawa, ya ma'abuta hankula.

    Bayanai
    [1] Bayãnin abũbuwan da aka hana a cikin hajji da waɗanda ake son a yi.
  198. لَيْسَ عَلَيْكُمْ جُنَاحٌ أَن تَبْتَغُوا۟ فَضْلًا مِّن رَّبِّكُمْ ۚ فَإِذَآ أَفَضْتُم مِّنْ عَرَفَـٰتٍ فَٱذْكُرُوا۟ ٱللَّهَ عِندَ ٱلْمَشْعَرِ ٱلْحَرَامِ ۖ وَٱذْكُرُوهُ كَمَا هَدَىٰكُمْ وَإِن كُنتُم مِّن قَبْلِهِۦ لَمِنَ ٱلضَّآلِّينَ۝١٩٨

    Laysa ʿalaykum junahun an tabtaghoo fadlan min rabbikum faitha afadtum min ʿarafatin faothkuroo Allaha ʿinda almashʿari alharami waothkuroohu kama hadakum wain kuntum min qablihi lamina alddalleena

    Bãbu laifi a kanku ga ku nẽmi falala daga Ubangijinku. Sa'an nan idan kun malãlo daga Arafãt, sai ku yi ta ambatar Allah a wurin Mash'aril Harãmi kuma ku tuna Shi kamar shiriyar da Ya yi muku kuma lalle ne kun kasance a gabãninsa, haƙĩƙa, daga ɓatattu.

  199. ثُمَّ أَفِيضُوا۟ مِنْ حَيْثُ أَفَاضَ ٱلنَّاسُ وَٱسْتَغْفِرُوا۟ ٱللَّهَ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ۝١٩٩

    Thumma afeedoo min haythu afada alnnasu waistaghfiroo Allaha inna Allaha ghafoorun raheemun

    Sa'an nan kuma ku malãlo daga inda mutãne suke malalowa. Kuma ku nemi gafara ga Allah. Lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙKai.

  200. فَإِذَا قَضَيْتُم مَّنَـٰسِكَكُمْ فَٱذْكُرُوا۟ ٱللَّهَ كَذِكْرِكُمْ ءَابَآءَكُمْ أَوْ أَشَدَّ ذِكْرًا ۗ فَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يَقُولُ رَبَّنَآ ءَاتِنَا فِى ٱلدُّنْيَا وَمَا لَهُۥ فِى ٱلْـَٔاخِرَةِ مِنْ خَلَـٰقٍ۝٢٠٠

    Faitha qadaytum manasikakum faothkuroo Allaha kathikrikum abaakum aw ashadda thikran famina alnnasi man yaqoolu rabbana atina fee alddunya wama lahu fee alakhirati min khalaqin

    To, idan kun ƙãre ayyukan hajji, sai ku ambaci Allah kamar ambatarku ga ubanninku, kõ kuwa mafi tsanani ga ambato. To, daga cikin mutãne akwai wanda yake cẽwa: "Ya Ubangjinmu! Ka bã mu a cikin dũniya! Kuma bã ya da wanirabo a cikin Lãhira.

  201. وَمِنْهُم مَّن يَقُولُ رَبَّنَآ ءَاتِنَا فِى ٱلدُّنْيَا حَسَنَةً وَفِى ٱلْـَٔاخِرَةِ حَسَنَةً وَقِنَا عَذَابَ ٱلنَّارِ۝٢٠١

    Waminhum man yaqoolu rabbana atina fee alddunya hasanatan wafee alakhirati hasanatan waqina ʿathaba alnnari

    Kuma daga gare su akwai wanda yake cẽwa: "Yã Ubangijinmu! Ka bã mu mai kyau a cikin dũniya da mai kyau a cikin Lãhira, kuma Ka tsare mana azãbar Wuta!"

  202. أُو۟لَـٰٓئِكَ لَهُمْ نَصِيبٌ مِّمَّا كَسَبُوا۟ ۚ وَٱللَّهُ سَرِيعُ ٱلْحِسَابِ۝٢٠٢

    Olaika lahum naseebun mimma kasaboo waAllahu sareeʿu alhisabi

    Waɗannan suna da rabo daga abin da suka sanã'anta; kuma Allah Mai gaggãwar sakamako ne.

  203. ۞ وَٱذْكُرُوا۟ ٱللَّهَ فِىٓ أَيَّامٍ مَّعْدُودَٰتٍ ۚ فَمَن تَعَجَّلَ فِى يَوْمَيْنِ فَلَآ إِثْمَ عَلَيْهِ وَمَن تَأَخَّرَ فَلَآ إِثْمَ عَلَيْهِ ۚ لِمَنِ ٱتَّقَىٰ ۗ وَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَٱعْلَمُوٓا۟ أَنَّكُمْ إِلَيْهِ تُحْشَرُونَ۝٢٠٣

    Waothkuroo Allaha fee ayyamin maʿdoodatin faman taʿajjala fee yawmayni fala ithma ʿalayhi waman taakhkhara fala ithma ʿalayhi limani ittaqa waittaqoo Allaha waiʿlamoo annakum ilayhi tuhsharoona

    Kuma ku ambaci Allah a cikin kwanuka ƙidayayyu.1 To, wanda ya yi gaggawa a cikin kwana biyu, to, bãbu laifi a kansa, kuma wanda ya jinkirta, to, bãbu laifi a kansa, ga wanda ya yi taƙawa. Kuma ku bi Allah da taƙawa, kuma ku sani cewa lalle ne kũ, zuwa gare Shi ake tãrã ku.

    Bayanai
    [1] Bayãnin kabbarõri, bãyan sallõlin farillai gõma sha biyar, anã fãrawa da sallar azahar ta ranar salla a ƙãre da sallar asuba ta rãna ta huɗu daga rãnar salla. Kwãnukan Mina uku ne daga rãnar salla, sai ga wanda ya yi gaggawa ya fita daga Mina bãyan fitar rãnar nan kuma gabãnin fãɗuwar rãna.
  204. وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يُعْجِبُكَ قَوْلُهُۥ فِى ٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا وَيُشْهِدُ ٱللَّهَ عَلَىٰ مَا فِى قَلْبِهِۦ وَهُوَ أَلَدُّ ٱلْخِصَامِ۝٢٠٤

    Wamina alnnasi man yuʿjibuka qawluhu fee alhayati alddunya wayushhidu Allaha ʿala ma fee qalbihi wahuwa aladdu alkhisami

    Kuma akwai daga mutãne1 wanda maganarsa tana bã ka sha'awa a cikin rãyuwar dũniya, alhãli yanã shaidar da Allah a kan abin da yake cikin zuciyarsa, kuma shi mai tsananin husũma ne.

    Bayanai
    [1] Bayãnin munafuki da hãlayensa, a cikin jama'a, a san shi, dõmin kada a dõgara a kansa. Haka mutumin kirki shi ma ana son a san shi dõmin a dogara da shi kamar yadda yayi bayãninsa.
  205. وَإِذَا تَوَلَّىٰ سَعَىٰ فِى ٱلْأَرْضِ لِيُفْسِدَ فِيهَا وَيُهْلِكَ ٱلْحَرْثَ وَٱلنَّسْلَ ۗ وَٱللَّهُ لَا يُحِبُّ ٱلْفَسَادَ۝٢٠٥

    Waitha tawalla saʿa fee alardi liyufsida feeha wayuhlika alhartha waalnnasla waAllahu la yuhibbu alfasada

    Kuma idan ya jũya sai ya yi gaggawa a cikin ƙasa dõmin ya yi ɓarna a cikinta, kuma ya halaka shũka da 'ya'yan dabbõbi. Kuma Allah bã Ya son ɓarna.

  206. وَإِذَا قِيلَ لَهُ ٱتَّقِ ٱللَّهَ أَخَذَتْهُ ٱلْعِزَّةُ بِٱلْإِثْمِ ۚ فَحَسْبُهُۥ جَهَنَّمُ ۚ وَلَبِئْسَ ٱلْمِهَادُ۝٢٠٦

    Waitha qeela lahu ittaqi Allaha akhathathu alʿizzatu bialithmi fahasbuhu jahannamu walabisa almihadu

    Kuma idan an ce masa: "Ka ji tsõron Allah," sai girman kai da yin zunubi ya ɗauke shi To abin da yake mai isarsa Jahannama ce. Kuma haƙĩƙa, shimfiɗa tã munana.

  207. وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يَشْرِى نَفْسَهُ ٱبْتِغَآءَ مَرْضَاتِ ٱللَّهِ ۗ وَٱللَّهُ رَءُوفٌۢ بِٱلْعِبَادِ۝٢٠٧

    Wamina alnnasi man yashree nafsahu ibtighaa mardati Allahi waAllahu raoofun bialʿibadi

    Kuma akwai daga mutãne1 wanda yake sayar da ransa, dõmin nẽman yardar Allah: KumaAllah Mai tausayi ga bãyi ne.

    Bayanai
    [1] Bayãnin mũmini sõsai a cikin Musulmi da halayensa, a sanshi dõmin a dõgara a kansa.
  208. يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ ٱدْخُلُوا۟ فِى ٱلسِّلْمِ كَآفَّةً وَلَا تَتَّبِعُوا۟ خُطُوَٰتِ ٱلشَّيْطَـٰنِ ۚ إِنَّهُۥ لَكُمْ عَدُوٌّ مُّبِينٌ۝٢٠٨

    Ya ayyuha allatheena amanoo odkhuloo fee alssilmi kaffatan wala tattabiʿoo khutuwati alshshaytani innahu lakum ʿaduwwun mubeenun

    Yã ku waɗanda suka yi ĩmani! Ku shiga cikin Musulunci gabã ɗaya; kuma kada ku bi zambiyõyin Shaiɗan; lalle ne shĩ a gare ku maƙiyine, bayyanan ne.

  209. فَإِن زَلَلْتُم مِّنۢ بَعْدِ مَا جَآءَتْكُمُ ٱلْبَيِّنَـٰتُ فَٱعْلَمُوٓا۟ أَنَّ ٱللَّهَ عَزِيزٌ حَكِيمٌ۝٢٠٩

    Fain zalaltum min baʿdi ma jaatkumu albayyinatu faiʿlamoo anna Allaha ʿazeezun hakeemun

    To, idan kun karkace daga bayan hujjõji bayyanannu sun zo muku to ku sani cẽwa lalle ne Allah, Mabuwãyi ne, Mai hikima.

  210. هَلْ يَنظُرُونَ إِلَّآ أَن يَأْتِيَهُمُ ٱللَّهُ فِى ظُلَلٍ مِّنَ ٱلْغَمَامِ وَٱلْمَلَـٰٓئِكَةُ وَقُضِىَ ٱلْأَمْرُ ۚ وَإِلَى ٱللَّهِ تُرْجَعُ ٱلْأُمُورُ۝٢١٠

    Hal yanthuroona illa an yatiyahumu Allahu fee thulalin mina alghamami waalmalaikatu waqudiya alamru waila Allahi turjaʿu alomooru

    Shin suna jira, fãce dai Allah Ya je musu a cikin wasu inuwõyi na girgije, da malã'iku, kuma an hukunta al'amarin? Kuma zuwa ga Allah al'amurra ake mayar da su.

  211. سَلْ بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ كَمْ ءَاتَيْنَـٰهُم مِّنْ ءَايَةٍۭ بَيِّنَةٍ ۗ وَمَن يُبَدِّلْ نِعْمَةَ ٱللَّهِ مِنۢ بَعْدِ مَا جَآءَتْهُ فَإِنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلْعِقَابِ۝٢١١

    Sal banee israeela kam ataynahum min ayatin bayyinatin waman yubaddil niʿmata Allahi min baʿdi ma jaathu fainna Allaha shadeedu alʿiqabi

    Ka tambayi Banĩ Isrã'ila, da yawa Muka bã su daga ãyõyi bayyanannu. Kuma wanda ya musanya ni'imar Allah daga bãyan tã je masa, to, lalle ne Allah Mai tsananin uƙũba ne.

  212. زُيِّنَ لِلَّذِينَ كَفَرُوا۟ ٱلْحَيَوٰةُ ٱلدُّنْيَا وَيَسْخَرُونَ مِنَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ ۘ وَٱلَّذِينَ ٱتَّقَوْا۟ فَوْقَهُمْ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ ۗ وَٱللَّهُ يَرْزُقُ مَن يَشَآءُ بِغَيْرِ حِسَابٍ۝٢١٢

    Zuyyina lillatheena kafaroo alhayatu alddunya wayaskharoona mina allatheena amanoo waallatheena ittaqaw fawqahum yawma alqiyamati waAllahu yarzuqu man yashao bighayri hisabin

    An ƙawata rãyuwar dũniya ga waɗanda suka kãfirta, kuma suna izgili daga waɗanda suka yi ĩmãni, alhãli waɗanda suka yi taƙawa suna bisa gare su, a Rãnar ¡iyãma. Kuma Allah Yana azurta wanda Yake so, bã da lissãfi ba.

  213. كَانَ ٱلنَّاسُ أُمَّةً وَٰحِدَةً فَبَعَثَ ٱللَّهُ ٱلنَّبِيِّـۧنَ مُبَشِّرِينَ وَمُنذِرِينَ وَأَنزَلَ مَعَهُمُ ٱلْكِتَـٰبَ بِٱلْحَقِّ لِيَحْكُمَ بَيْنَ ٱلنَّاسِ فِيمَا ٱخْتَلَفُوا۟ فِيهِ ۚ وَمَا ٱخْتَلَفَ فِيهِ إِلَّا ٱلَّذِينَ أُوتُوهُ مِنۢ بَعْدِ مَا جَآءَتْهُمُ ٱلْبَيِّنَـٰتُ بَغْيًۢا بَيْنَهُمْ ۖ فَهَدَى ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ لِمَا ٱخْتَلَفُوا۟ فِيهِ مِنَ ٱلْحَقِّ بِإِذْنِهِۦ ۗ وَٱللَّهُ يَهْدِى مَن يَشَآءُ إِلَىٰ صِرَٰطٍ مُّسْتَقِيمٍ۝٢١٣

    Kana alnnasu ommatan wahidatan fabaʿatha Allahu alnnabiyyeena mubashshireena wamunthireena waanzala maʿahumu alkitaba bialhaqqi liyahkuma bayna alnnasi feema ikhtalafoo feehi wama ikhtalafa feehi illa allatheena ootoohu min baʿdi ma jaathumu albayyinatu baghyan baynahum fahada Allahu allatheena amanoo lima ikhtalafoo feehi mina alhaqqi biithnihi waAllahu yahdee man yashao ila siratin mustaqeemin

    Mutãne sun kasance al'umma guda. Sai Allah Ya aiki annabãwa suna mãsu bãyar da bishãra kuma mãsu gargaɗi; kuma Ya saukar da Littãfi da gaskiya tãre da su dõmin (Littãfin) ya yi hukunci a tsakãnin mutãnen a cikin abin da suka sãɓã wa jũna a cikinsa. kuma bãbu wanda ya sãɓã, a cikinsa, fãce waɗanda aka bai wa shi daga bãyan hujjõji bayyanannu sun je musu dõmin zãlunci a tsakãninsu. Sai Allah Ya shiryar da waɗanda suka yi ĩmani ga abin da suka sãɓã a cikinsa daga gaskiya da izninSa. Kuma Allah Yana shiryar da wanda Yake so, zuwa ga hanya madaidaiciya.

  214. أَمْ حَسِبْتُمْ أَن تَدْخُلُوا۟ ٱلْجَنَّةَ وَلَمَّا يَأْتِكُم مَّثَلُ ٱلَّذِينَ خَلَوْا۟ مِن قَبْلِكُم ۖ مَّسَّتْهُمُ ٱلْبَأْسَآءُ وَٱلضَّرَّآءُ وَزُلْزِلُوا۟ حَتَّىٰ يَقُولَ ٱلرَّسُولُ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ مَعَهُۥ مَتَىٰ نَصْرُ ٱللَّهِ ۗ أَلَآ إِنَّ نَصْرَ ٱللَّهِ قَرِيبٌ۝٢١٤

    Am hasibtum an tadkhuloo aljannata walamma yatikum mathalu allatheena khalaw min qablikum massathumu albasao waalddarrao wazulziloo hatta yaqoola alrrasoolu waallatheena amanoo maʿahu mata nasru Allahi ala inna nasra Allahi qareebun

    Ko kuna zaton ku shiga Aljanna kuma tun misãlin waɗanda suka shige daga gabãninku bai zo muku ba? Wahalõli da cũta sun shãfe su, kuma aka tsõratar da su har manzonsu da waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi su ce: "Yaushe taimakon Allah zai zo?" To! Lalle ne, taimakon Allah yana kusa!

  215. يَسْـَٔلُونَكَ مَاذَا يُنفِقُونَ ۖ قُلْ مَآ أَنفَقْتُم مِّنْ خَيْرٍ فَلِلْوَٰلِدَيْنِ وَٱلْأَقْرَبِينَ وَٱلْيَتَـٰمَىٰ وَٱلْمَسَـٰكِينِ وَٱبْنِ ٱلسَّبِيلِ ۗ وَمَا تَفْعَلُوا۟ مِنْ خَيْرٍ فَإِنَّ ٱللَّهَ بِهِۦ عَلِيمٌ۝٢١٥

    Yasaloonaka matha yunfiqoona qul ma anfaqtum min khayrin falilwalidayni waalaqrabeena waalyatama waalmasakeeni waibni alssabeeli wama tafʿaloo min khayrin fainna Allaha bihi ʿaleemun

    Suna tambayar ka mẽne nezã su ciyar. Ka ce: Abin da kuka ciyar daga alhẽri sai ga mahaifa1 da mafi kusantar dangantaka da marãyu da matalauta da ɗan hanya. Kuma abin da kuka aikata daga alhẽri, to, lalle ne, Allah gare shi Masani ne.

    Bayanai
    [1] Ciyar da mahaifa matalauta wãjibi ne haka ɗiya da 'ya'ya ƙanãna waɗanda bãsu da dũkiya har yãro ya balaga a kuma aurar da yãrinya ta tãre a gidan mijinta. Amma mãtar aure da bãwan mutum ciyar da su wãjibi ne kõ dã sunã da dũkiya. Liyãfa ga bãƙo har kwãna uku gwargwadon bukãta wãjibi ne, sauran ciyarwa mustahabbi ce bãyan an fitar da zakka idan tã wajaba.
  216. كُتِبَ عَلَيْكُمُ ٱلْقِتَالُ وَهُوَ كُرْهٌ لَّكُمْ ۖ وَعَسَىٰٓ أَن تَكْرَهُوا۟ شَيْـًٔا وَهُوَ خَيْرٌ لَّكُمْ ۖ وَعَسَىٰٓ أَن تُحِبُّوا۟ شَيْـًٔا وَهُوَ شَرٌّ لَّكُمْ ۗ وَٱللَّهُ يَعْلَمُ وَأَنتُمْ لَا تَعْلَمُونَ۝٢١٦

    Kutiba ʿalaykumu alqitalu wahuwa kurhun lakum waʿasa an takrahoo shayan wahuwa khayrun lakum waʿasa an tuhibboo shayan wahuwa sharrun lakum waAllahu yaʿlamu waantum la taʿlamoona

    An wajabta1 yãƙi a kanku, alhãli kuwa shi abin ƙi ne a gare ku, akwai fãtar cẽwa ku ƙi wani abu, alhãli shi ne mafi alhẽri a gare ku, kumaakwai fãtar cẽwa kuna son wani abu alhãli kuwa shi ne mafi sharri a gare ku. Kuma Allah ne Yake sani, kuma kũ ba ku sani ba.

    Bayanai
    [1] Bayãnin hukuncin yãƙi da wuri da lõkacin da aka hana yinsa, da dalilin yinsa.
  217. يَسْـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلشَّهْرِ ٱلْحَرَامِ قِتَالٍ فِيهِ ۖ قُلْ قِتَالٌ فِيهِ كَبِيرٌ ۖ وَصَدٌّ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ وَكُفْرٌۢ بِهِۦ وَٱلْمَسْجِدِ ٱلْحَرَامِ وَإِخْرَاجُ أَهْلِهِۦ مِنْهُ أَكْبَرُ عِندَ ٱللَّهِ ۚ وَٱلْفِتْنَةُ أَكْبَرُ مِنَ ٱلْقَتْلِ ۗ وَلَا يَزَالُونَ يُقَـٰتِلُونَكُمْ حَتَّىٰ يَرُدُّوكُمْ عَن دِينِكُمْ إِنِ ٱسْتَطَـٰعُوا۟ ۚ وَمَن يَرْتَدِدْ مِنكُمْ عَن دِينِهِۦ فَيَمُتْ وَهُوَ كَافِرٌ فَأُو۟لَـٰٓئِكَ حَبِطَتْ أَعْمَـٰلُهُمْ فِى ٱلدُّنْيَا وَٱلْـَٔاخِرَةِ ۖ وَأُو۟لَـٰٓئِكَ أَصْحَـٰبُ ٱلنَّارِ ۖ هُمْ فِيهَا خَـٰلِدُونَ۝٢١٧

    Yasaloonaka ʿani alshshahri alharami qitalin feehi qul qitalun feehi kabeerun wasaddun ʿan sabeeli Allahi wakufrun bihi waalmasjidi alharami waikhraju ahlihi minhu akbaru ʿinda Allahi waalfitnatu akbaru mina alqatli wala yazaloona yuqatiloonakum hatta yaruddookum ʿan deenikum ini istataʿoo waman yartadid minkum ʿan deenihi fayamut wahuwa kafirun faolaika habitat aʿmaluhum fee alddunya waalakhirati waolaika ashabu alnnari hum feeha khalidoona

    Suna tambayar ka game da Watan Alfarma: yin yãki a cikinsa. Ka ce: "Yin yãƙi a cikinsa babban zunubi ne, kuma hani daga hanyar Allah, da kuma kãfirci da Shi, da kuma da Masallaci Tsararre, da Kuma fitar da mutãnensa daga gare shi, shi ne mafi girman zunubi a wurin Allah." Kuma fitina ita ce mafi girma daga kisa. Kuma bã su gushẽwa suna yãƙinku har su mayar da ku daga barin addininku idan za su iya. Kuma wanda ya yi ridda daga gare ku ga barin addininsa har ya mutu alhãli kuwa yana kãfiri, to, waɗannan ayyukansu sun ɓãci a cikin dũniya da Lãhira. Kuma waɗannan abõkan Wuta ne, sũ a cikinta madawwama ne.

  218. إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَٱلَّذِينَ هَاجَرُوا۟ وَجَـٰهَدُوا۟ فِى سَبِيلِ ٱللَّهِ أُو۟لَـٰٓئِكَ يَرْجُونَ رَحْمَتَ ٱللَّهِ ۚ وَٱللَّهُ غَفُورٌ رَّحِيمٌ۝٢١٨

    Inna allatheena amanoo waallatheena hajaroo wajahadoo fee sabeeli Allahi olaika yarjoona rahmata Allahi waAllahu ghafoorun raheemun

    Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, da waɗanda suka yi hijira kuma suka yi jihãdi a cikin hanyar Allah waɗannan suna fãtar (sãmun) rahamar Allah kuma Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.

  219. ۞ يَسْـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلْخَمْرِ وَٱلْمَيْسِرِ ۖ قُلْ فِيهِمَآ إِثْمٌ كَبِيرٌ وَمَنَـٰفِعُ لِلنَّاسِ وَإِثْمُهُمَآ أَكْبَرُ مِن نَّفْعِهِمَا ۗ وَيَسْـَٔلُونَكَ مَاذَا يُنفِقُونَ قُلِ ٱلْعَفْوَ ۗ كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ ٱللَّهُ لَكُمُ ٱلْـَٔايَـٰتِ لَعَلَّكُمْ تَتَفَكَّرُونَ۝٢١٩

    Yasaloonaka ʿani alkhamri waalmaysiri qul feehima ithmun kabeerun wamanafiʿu lilnnasi waithmuhuma akbaru min nafʿihima wayasaloonaka matha yunfiqoona quli alʿafwa kathalika yubayyinu Allahu lakumu alayati laʿallakum tatafakkaroona

    Suna tambayar ka game da giya da cãcã.1 Ka ce: "A cikinsu akwai zunubi mai girma da wasu amfãnõni ga mutãne, kuma zunubinsu ne mafi girma daga amfaninsu." Kuma suna tambayar ka mẽne ne zã su ciyar; ka ce: "Abin da ya rage."2 Kamar wancan ne Allah Yake bayyanawar ãyõyi a gare ku; tsammãninku, kuna tunãni.

    Bayanai
    [1] Bayãnin hukuncin cãca da giya da ciyarwa ta alhħri. Cãca da giya harãmun ne dõmin cũtarsu tã fi amfaninsu yawa, ana hukunci da abin da ya rinjãya. Ayõyin wata sura sun bayyana haramcin. [2] Abin da ya rage daga larũrarku da ta iyãlanku da wanda ciyar da shi yake wãjibi a kanku, saura shi ne afwu. Daga afwu ake sadakar taɗawwu'i.
  220. فِى ٱلدُّنْيَا وَٱلْـَٔاخِرَةِ ۗ وَيَسْـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلْيَتَـٰمَىٰ ۖ قُلْ إِصْلَاحٌ لَّهُمْ خَيْرٌ ۖ وَإِن تُخَالِطُوهُمْ فَإِخْوَٰنُكُمْ ۚ وَٱللَّهُ يَعْلَمُ ٱلْمُفْسِدَ مِنَ ٱلْمُصْلِحِ ۚ وَلَوْ شَآءَ ٱللَّهُ لَأَعْنَتَكُمْ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَزِيزٌ حَكِيمٌ۝٢٢٠

    Fee alddunya waalakhirati wayasaloonaka ʿani alyatama qul islahun lahum khayrun wain tukhalitoohum faikhwanukum waAllahu yaʿlamu almufsida mina almuslihi walaw shaa Allahu laaʿnatakum inna Allaha ʿazeezun hakeemun

    A cikin dũniya da Lãhira. Kuma suna tambayar ka game da marãyu.1 Ka ce: "Kyautatãwa gare su ne mafi alhẽri, kuma idan kun haɗa da su (wajen abinci), to, 'yan'uwanku ne; kuma Allah Yana sanin mai ɓãtãwa daga mai kyautatãwa. Kuma dã Allah Yã so, dã Ya tsananta muku. Lalle ne Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima.

    Bayanai
    [1] Bayãnin gama abinci da yãra marãyu mãsu dũkiyar kansu.
  221. وَلَا تَنكِحُوا۟ ٱلْمُشْرِكَـٰتِ حَتَّىٰ يُؤْمِنَّ ۚ وَلَأَمَةٌ مُّؤْمِنَةٌ خَيْرٌ مِّن مُّشْرِكَةٍ وَلَوْ أَعْجَبَتْكُمْ ۗ وَلَا تُنكِحُوا۟ ٱلْمُشْرِكِينَ حَتَّىٰ يُؤْمِنُوا۟ ۚ وَلَعَبْدٌ مُّؤْمِنٌ خَيْرٌ مِّن مُّشْرِكٍ وَلَوْ أَعْجَبَكُمْ ۗ أُو۟لَـٰٓئِكَ يَدْعُونَ إِلَى ٱلنَّارِ ۖ وَٱللَّهُ يَدْعُوٓا۟ إِلَى ٱلْجَنَّةِ وَٱلْمَغْفِرَةِ بِإِذْنِهِۦ ۖ وَيُبَيِّنُ ءَايَـٰتِهِۦ لِلنَّاسِ لَعَلَّهُمْ يَتَذَكَّرُونَ۝٢٢١

    Wala tankihoo almushrikati hatta yuminna walaamatun muminatun khayrun min mushrikatin walaw aʿjabatkum wala tunkihoo almushrikeena hatta yuminoo walaʿabdun muminun khayrun min mushrikin walaw aʿjabakum olaika yadʿoona ila alnnari waAllahu yadʿoo ila aljannati waalmaghfirati biithnihi wayubayyinu ayatihi lilnnasi laʿallahum yatathakkaroona

    Kuma kada ku auri mãtã1 mushirikai sai sun yi ĩmãni: Kuma lalle ne baiwa mũminaita ce mafi alhẽri daga ɗiya kãfira, kuma kõ da tã bã ku sha'awa. Kuma kada ku aurar wa maza mushirikai sai sun yi ĩmãni, kuma lalle ne bãwa mũmini shi ne mafi alhẽri daga da mushiriki, kuma kõ da yã bã ku sha'awa, waɗannan suna kira ne zuwa ga wuta kuma Allah Yana kira zuwa ga Aljanna da gãfara da izninsa. Kuma Yana bayyana ãyõyinsa ga mutãne; tsammãninsu suna tunãwa.

    Bayanai
    [1] Bayãnin irin maza da mãtan wani addini da bã zã a aure su ba sai sun musulunta, watau mushirikai, banda mãtan Mutãnen Littãfi, sũ kam anã auren 'ya'yansu tãre da kãfircinsu. Bã a auren wanda ya yi ridda daga addinin Musulunci.
  222. وَيَسْـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلْمَحِيضِ ۖ قُلْ هُوَ أَذًى فَٱعْتَزِلُوا۟ ٱلنِّسَآءَ فِى ٱلْمَحِيضِ ۖ وَلَا تَقْرَبُوهُنَّ حَتَّىٰ يَطْهُرْنَ ۖ فَإِذَا تَطَهَّرْنَ فَأْتُوهُنَّ مِنْ حَيْثُ أَمَرَكُمُ ٱللَّهُ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلتَّوَّٰبِينَ وَيُحِبُّ ٱلْمُتَطَهِّرِينَ۝٢٢٢

    Wayasaloonaka ʿani almaheedi qul huwa athan faiʿtaziloo alnnisaa fee almaheedi wala taqraboohunna hatta yathurna faitha tatahharna fatoohunna min haythu amarakumu Allahu inna Allaha yuhibbu alttawwabeena wayuhibbu almutatahhireena

    Kuma suna tambayar ka game da haila1 Ka ce: Shi cũta ne. Sabõda haka ku nĩsanci mãta a cikin wurin haila kuma kada ku kusance su sai sun yi tsarki. To, idan sun yi wanka sai ku je musu daga inda Allah Ya umurce ku. Lalle ne Allah Yana son mãsu tũba kuma Yana son mãsu tsarkakẽwa.

    Bayanai
    [1] Bayãnin hukuncin sãduwa da mãtan aure a lõkacin hailarsu; watau jima'i ya haramta a cikin haila kõ bãyan haila gabãnin ta yi wanka. Kõ da ta yi taimama tã yi salla duk da haka dai sai tã yi wanka sannan farjinta yake halatta ga mijinta. Amma anã iya mubãshara da rungumayya ko a cikin haila bãyan tã ɗaura gyauto, tã rũfe cĩbiya zuwa gwiwa.
  223. نِسَآؤُكُمْ حَرْثٌ لَّكُمْ فَأْتُوا۟ حَرْثَكُمْ أَنَّىٰ شِئْتُمْ ۖ وَقَدِّمُوا۟ لِأَنفُسِكُمْ ۚ وَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَٱعْلَمُوٓا۟ أَنَّكُم مُّلَـٰقُوهُ ۗ وَبَشِّرِ ٱلْمُؤْمِنِينَ۝٢٢٣

    Nisaokum harthun lakum fatoo harthakum anna shitum waqaddimoo lianfusikum waittaqoo Allaha waiʿlamoo annakum mulaqoohu wabashshiri almumineena

    Mãtanku gõnaki ne a gare ku,1 sabõda haka ku je wa gõnakinku yadda kuka so. Kuma ku gabãtar (da alheri) sabõda kanku, ku bi Allah da taƙawa. Kuma ku sani cẽwa lalle nekũ mãsu haɗuwa da Shi ne. Kuma ka bãyar da bishãra ga mũminai.

    Bayanai
    [1] Mutum na iya sãduwa da mãtarsa yadda yake so kuma yadda ya sauƙaƙa a gare shi, daga gaba kõ daga bãya, amma ga farji banda ga dubura. Ma'anar ku gabãtar da alheri dõmin rãyukanku, shi ne ku yi basmala ku nemi tsari daga Shaiɗan sabõda 'ya'yanku. Ba a jimã'i da mace alhãli tanã barci, ana son gabãtarda wãsa.
  224. وَلَا تَجْعَلُوا۟ ٱللَّهَ عُرْضَةً لِّأَيْمَـٰنِكُمْ أَن تَبَرُّوا۟ وَتَتَّقُوا۟ وَتُصْلِحُوا۟ بَيْنَ ٱلنَّاسِ ۗ وَٱللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ۝٢٢٤

    Wala tajʿaloo Allaha ʿurdatan liaymanikum an tabarroo watattaqoo watuslihoo bayna alnnasi waAllahu sameeʿun ʿaleemun

    Kuma kada ku sanya1 Allah kambu ga rantsuwõyinku dõmin kada ku yi wani alhẽri, kuma ku yi taƙawa, kuma ku yi wani gyara tsakãnin mutãne, kuma Allah Mai jĩ ne, Masani.

    Bayanai
    [1] Bãyanin rantsuwa da hukunce-hukuncenta. Kada ku sanya rantsuwa da Allah sababin rashin aikata wani alheri, kõ wani aikin ɗã'a, kõ kuma sanya sulhu a tsakanin mutãne, kamar a rõƙe shi ga wani abu daga cikinsu, sai ya yi rantsuwa ya ce: "Wallãhi bã zan yi ba," dõmin tsare kansa daga aikatãwar abin da aka nema gare shi. Yin irin wannan rantsuwa makarũhi ne kõ haram, gwargwadon nauyin abin da aka yi ta sabõda rashin yin sa. Kambu shi ne wurin gwada harbi.
  225. لَّا يُؤَاخِذُكُمُ ٱللَّهُ بِٱللَّغْوِ فِىٓ أَيْمَـٰنِكُمْ وَلَـٰكِن يُؤَاخِذُكُم بِمَا كَسَبَتْ قُلُوبُكُمْ ۗ وَٱللَّهُ غَفُورٌ حَلِيمٌ۝٢٢٥

    La yuakhithukumu Allahu biallaghwi fee aymanikum walakin yuakhithukum bima kasabat quloobukum waAllahu ghafoorun haleemun

    Allah ba Ya kãmã ku da laifi sabõda yãsasshiya a cikin rantsuwõyinku. Kuma amma Yana kama ku sabõda abin da zukãtanku1 suka sanã'anta. Kuma Allah Mai gãfara ne, Mai haƙuri.

    Bayanai
    [1] Yasasshiyar rantsuwa ita ce, a wurin Mãlik, rantsuwa a kan abin da mutum ke ganin sa tabbatacce ne, sai ya bayyana daga bãya akasin tunãninsa. Kamar ya ce Wallãhi bã ni da kuɗi, ga saninsa kuwa haka ne bã ya da su, bai sani ba ashe wani yã mutu, yã yi gãdo. A Shafi'i ita ce: ã'aha Wallahi, I, wallãhi, a cikin magana bã da nufi ba.
  226. لِّلَّذِينَ يُؤْلُونَ مِن نِّسَآئِهِمْ تَرَبُّصُ أَرْبَعَةِ أَشْهُرٍ ۖ فَإِن فَآءُو فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ۝٢٢٦

    Lillatheena yuloona min nisaihim tarabbusu arbaʿati ashhurin fain faoo fainna Allaha ghafoorun raheemun

    Ga waɗanda suke yin rantsuwa1 daga matansu akwai jinkirin watã huɗu. To, idan sun kõma, to, lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.

    Bayanai
    [1] Hukuncin ĩlã'i, watau rantsuwa a kan barin tãkin matarsa dõmin ya wahalar da ita, a jira shi wata hudu, idan yã ƙi kõmãwa a sake ta daga gare shi.
  227. وَإِنْ عَزَمُوا۟ ٱلطَّلَـٰقَ فَإِنَّ ٱللَّهَ سَمِيعٌ عَلِيمٌ۝٢٢٧

    Wain ʿazamoo alttalaqa fainna Allaha sameeʿun ʿaleemun

    Kuma idan sun yi niyyar saki, to, lalle ne, Allah Mai ji ne, Masani.

  228. وَٱلْمُطَلَّقَـٰتُ يَتَرَبَّصْنَ بِأَنفُسِهِنَّ ثَلَـٰثَةَ قُرُوٓءٍ ۚ وَلَا يَحِلُّ لَهُنَّ أَن يَكْتُمْنَ مَا خَلَقَ ٱللَّهُ فِىٓ أَرْحَامِهِنَّ إِن كُنَّ يُؤْمِنَّ بِٱللَّهِ وَٱلْيَوْمِ ٱلْـَٔاخِرِ ۚ وَبُعُولَتُهُنَّ أَحَقُّ بِرَدِّهِنَّ فِى ذَٰلِكَ إِنْ أَرَادُوٓا۟ إِصْلَـٰحًا ۚ وَلَهُنَّ مِثْلُ ٱلَّذِى عَلَيْهِنَّ بِٱلْمَعْرُوفِ ۚ وَلِلرِّجَالِ عَلَيْهِنَّ دَرَجَةٌ ۗ وَٱللَّهُ عَزِيزٌ حَكِيمٌ۝٢٢٨

    Waalmutallaqatu yatarabbasna bianfusihinna thalathata qurooin wala yahillu lahunna an yaktumna ma khalaqa Allahu fee arhamihinna in kunna yuminna biAllahi waalyawmi alakhiri wabuʿoolatuhunna ahaqqu biraddihinna fee thalika in aradoo islahan walahunna mithlu allathee ʿalayhinna bialmaʿroofi walilrrijali ʿalayhinna darajatun waAllahu ʿazeezun hakeemun

    Kuma mãtã waɗanda1 aka saki aurensu, suna jinkiri da kansu tsarki uku. Kuma bã ya halatta a gare su, su ɓõye abin da Allah Ya halitta a cikin mahaifunsu, idan sun kasance suna yin ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Kuma mazan aurensu su ne mafiya haƙƙi ga mayar da su a cikin wancan, idan sun yi nufin gyãrawa. Kuma sũ mãtan suna da kamar abin da yake a kansu, yadda aka sani. Kuma maza suna da wata daraja a kansu (su mãtan). Kuma Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima.

    Bayanai
    [1] Bayãnin iddar saki da hukunce-hukuncen da suka rãtayu da ita iddar tsarki uku ga mãtar aure ɗiya, baiwa tsarki biyu. Ƙwarƙwara tsarki guda. Istibrã'in zina kõ kuskure kamar idda yake.
  229. ٱلطَّلَـٰقُ مَرَّتَانِ ۖ فَإِمْسَاكٌۢ بِمَعْرُوفٍ أَوْ تَسْرِيحٌۢ بِإِحْسَـٰنٍ ۗ وَلَا يَحِلُّ لَكُمْ أَن تَأْخُذُوا۟ مِمَّآ ءَاتَيْتُمُوهُنَّ شَيْـًٔا إِلَّآ أَن يَخَافَآ أَلَّا يُقِيمَا حُدُودَ ٱللَّهِ ۖ فَإِنْ خِفْتُمْ أَلَّا يُقِيمَا حُدُودَ ٱللَّهِ فَلَا جُنَاحَ عَلَيْهِمَا فِيمَا ٱفْتَدَتْ بِهِۦ ۗ تِلْكَ حُدُودُ ٱللَّهِ فَلَا تَعْتَدُوهَا ۚ وَمَن يَتَعَدَّ حُدُودَ ٱللَّهِ فَأُو۟لَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلظَّـٰلِمُونَ۝٢٢٩

    Alttalaqu marratani faimsakun bimaʿroofin aw tasreehun biihsanin wala yahillu lakum an takhuthoo mimma ataytumoohunna shayan illa an yakhafa alla yuqeema hudooda Allahi fain khiftum alla yuqeema hudooda Allahi fala junaha ʿalayhima feema iftadat bihi tilka hudoodu Allahi fala taʿtadooha waman yataʿadda hudooda Allahi faolaika humu alththalimoona

    Saki sau biyu1 yake, sai a riƙa da alh ẽri, ko kuwa a sallama bisa kyautatãwa. Kuma ba ya halatta a gare ku (maza) ku karɓe wani abu daga abin da kuka bã su, fãce fa idan su (ma'auran) na tsõron bã zã su tsayar da iyãkõkin Allah ba, Idan kun (danginsu) ji tsõron bã zã su tsayar da iyãkõkin Allah ba, to, bãbu laifi a kansu a cikin abin da ta yi fansa da shi. Waɗancan iyãkõkin Allah ne sabõda haka kada ku kẽtare su. Kuma wanda ya ƙẽtare iyãkõkin Allah, to waɗannan su ne Azzãlumai.

    Bayanai
    [1] Sakin aure da hukunce-hukuncen da suka rãtayu da shi. Wanda ya saki matarsa sau ɗaya ko sau biyu, yanã iya mayar da ita kõ dã ba ta so ba matuƙar ba ta kãre idda ba. Wanda ya yi saki uku, bã ya iya kõma aurenta, sai tã yi jimã'i da wani sãbon miji a cikin aure sahĩhi. Sakin bãwa biyu ne.
  230. فَإِن طَلَّقَهَا فَلَا تَحِلُّ لَهُۥ مِنۢ بَعْدُ حَتَّىٰ تَنكِحَ زَوْجًا غَيْرَهُۥ ۗ فَإِن طَلَّقَهَا فَلَا جُنَاحَ عَلَيْهِمَآ أَن يَتَرَاجَعَآ إِن ظَنَّآ أَن يُقِيمَا حُدُودَ ٱللَّهِ ۗ وَتِلْكَ حُدُودُ ٱللَّهِ يُبَيِّنُهَا لِقَوْمٍ يَعْلَمُونَ۝٢٣٠

    Fain tallaqaha fala tahillu lahu min baʿdu hatta tankiha zawjan ghayrahu fain tallaqaha fala junaha ʿalayhima an yatarajaʿa in thanna an yuqeema hudooda Allahi watilka hudoodu Allahi yubayyinuha liqawmin yaʿlamoona

    Sa'an nan idan ya sake ta (na uku), to, bã ta halatta a gare shi, daga bãya, sai tã yi jima'i da wani miji waninsa. Sa'an nan idan (sãbon mijin, watau na biyu) ya sake ta, to, bãbu laifi a kansu ga su kõma wa (auren) jũna, idan sun (mijin farko da matar) yi zaton cẽwa zã su tsayar da iyãkõkin Allah, kuma waɗancan dõkõkin Allah ne Yana bayyana su ga mutãne waɗanda suke sani.

  231. وَإِذَا طَلَّقْتُمُ ٱلنِّسَآءَ فَبَلَغْنَ أَجَلَهُنَّ فَأَمْسِكُوهُنَّ بِمَعْرُوفٍ أَوْ سَرِّحُوهُنَّ بِمَعْرُوفٍ ۚ وَلَا تُمْسِكُوهُنَّ ضِرَارًا لِّتَعْتَدُوا۟ ۚ وَمَن يَفْعَلْ ذَٰلِكَ فَقَدْ ظَلَمَ نَفْسَهُۥ ۚ وَلَا تَتَّخِذُوٓا۟ ءَايَـٰتِ ٱللَّهِ هُزُوًا ۚ وَٱذْكُرُوا۟ نِعْمَتَ ٱللَّهِ عَلَيْكُمْ وَمَآ أَنزَلَ عَلَيْكُم مِّنَ ٱلْكِتَـٰبِ وَٱلْحِكْمَةِ يَعِظُكُم بِهِۦ ۚ وَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَٱعْلَمُوٓا۟ أَنَّ ٱللَّهَ بِكُلِّ شَىْءٍ عَلِيمٌ۝٢٣١

    Waitha tallaqtumu alnnisaa fabalaghna ajalahunna faamsikoohunna bimaʿroofin aw sarrihoohunna bimaʿroofin wala tumsikoohunna diraran litaʿtadoo waman yafʿal thalika faqad thalama nafsahu wala tattakhithoo ayati Allahi huzuwan waothkuroo niʿmata Allahi ʿalaykum wama anzala ʿalaykum mina alkitabi waalhikmati yaʿithukum bihi waittaqoo Allaha waiʿlamoo anna Allaha bikulli shayin ʿaleemun

    Kuma idan kun saki mãta, sa'an nan suka isa ga ajalinsu (iddarsu), sai ku riƙe su da alhẽri ko ku sallame su da alhẽri, kuma kada ku riƙe su a kan cũtarwa dõmin ta tsawaita idda. Kuma wanda ya aikata wancan, to, haƙĩƙa, yã zãlunci kansa. Kuma kada ku riƙi ãyõyin Allah da izgili. Kuma ku tuna ni'imar Allah da abin da Ya saukar a kanku na Littãfi da hikima. Yana yi muku wa'azi da shi. Kuma ku bi Allah da takawa kuma ku sani cewa lalle ne Allah ga dukan kõme Masani ne.

  232. وَإِذَا طَلَّقْتُمُ ٱلنِّسَآءَ فَبَلَغْنَ أَجَلَهُنَّ فَلَا تَعْضُلُوهُنَّ أَن يَنكِحْنَ أَزْوَٰجَهُنَّ إِذَا تَرَٰضَوْا۟ بَيْنَهُم بِٱلْمَعْرُوفِ ۗ ذَٰلِكَ يُوعَظُ بِهِۦ مَن كَانَ مِنكُمْ يُؤْمِنُ بِٱللَّهِ وَٱلْيَوْمِ ٱلْـَٔاخِرِ ۗ ذَٰلِكُمْ أَزْكَىٰ لَكُمْ وَأَطْهَرُ ۗ وَٱللَّهُ يَعْلَمُ وَأَنتُمْ لَا تَعْلَمُونَ۝٢٣٢

    Waitha tallaqtumu alnnisaa fabalaghna ajalahunna fala taʿduloohunna an yankihna azwajahunna itha taradaw baynahum bialmaʿroofi thalika yooʿathu bihi man kana minkum yuminu biAllahi waalyawmi alakhiri thalikum azka lakum waatharu waAllahu yaʿlamu waantum la taʿlamoona

    Kuma idan kuka saki mãta, har suka isa ga ajalinsu (iddarsu), to, kada ku (waliyyansu) hana su, su auri mazansu (da suka sake su) idan sun yarda da jũna a tsakãninsu (tsõhon miji da tsõhuwar mãta) da alhẽri. Wancan ana yin wa'azi da shi ga wanda ya kasance daga gare ku yana ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Wancan ne mafi mutunci a gare ku, kuma mafi tsarki. Kuma Allah Yana sani, kuma kũ ba ku sani ba.

  233. ۞ وَٱلْوَٰلِدَٰتُ يُرْضِعْنَ أَوْلَـٰدَهُنَّ حَوْلَيْنِ كَامِلَيْنِ ۖ لِمَنْ أَرَادَ أَن يُتِمَّ ٱلرَّضَاعَةَ ۚ وَعَلَى ٱلْمَوْلُودِ لَهُۥ رِزْقُهُنَّ وَكِسْوَتُهُنَّ بِٱلْمَعْرُوفِ ۚ لَا تُكَلَّفُ نَفْسٌ إِلَّا وُسْعَهَا ۚ لَا تُضَآرَّ وَٰلِدَةٌۢ بِوَلَدِهَا وَلَا مَوْلُودٌ لَّهُۥ بِوَلَدِهِۦ ۚ وَعَلَى ٱلْوَارِثِ مِثْلُ ذَٰلِكَ ۗ فَإِنْ أَرَادَا فِصَالًا عَن تَرَاضٍ مِّنْهُمَا وَتَشَاوُرٍ فَلَا جُنَاحَ عَلَيْهِمَا ۗ وَإِنْ أَرَدتُّمْ أَن تَسْتَرْضِعُوٓا۟ أَوْلَـٰدَكُمْ فَلَا جُنَاحَ عَلَيْكُمْ إِذَا سَلَّمْتُم مَّآ ءَاتَيْتُم بِٱلْمَعْرُوفِ ۗ وَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَٱعْلَمُوٓا۟ أَنَّ ٱللَّهَ بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِيرٌ۝٢٣٣

    Waalwalidatu yurdiʿna awladahunna hawlayni kamilayni liman arada an yutimma alrradaʿata waʿala almawloodi lahu rizquhunna wakiswatuhunna bialmaʿroofi la tukallafu nafsun illa wusʿaha la tudarra walidatun biwaladiha wala mawloodun lahu biwaladihi waʿala alwarithi mithlu thalika fain arada fisalan ʿan taradin minhuma watashawurin fala junaha ʿalayhima wain aradtum an tastardiʿoo awladakum fala junaha ʿalaykum itha sallamtum ma ataytum bialmaʿroofi waittaqoo Allaha waiʿlamoo anna Allaha bima taʿmaloona baseerun

    Kuma mãsu haifuwa (sakakku)1 suna shãyar da abin haifuwarsu shẽkara biyu cikakku ga wanda ya yi nufin ya cika shãyarwa. Kuma ciyar da su da tufãtar da su yana a kan wanda aka haifar masa da alhẽri. Bã a kallafa wa rai fãce iyãwarsa. Bã a cũtar da uwa game da ɗanta, kuma bã a cũtar da uba game da ɗansa, kuma a kan magãji akwai misãlin wancan. To, idan suka yi nufin yãye, a kan yardatayya daga gare su, da shãwartar jũna, to bãbu laifi a kansu. Kuma idan, kun yi nufin ku bãyar da ɗiyanku shãyarwa, to, bãbu laifi a kanku idan kun mĩƙa abin da kukazo da shi bisa al'ãda. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma ku sani cẽwa lalle ne Allah, ga abin da kuke aikatawa, Mai gani ne.

    Bayanai
    [1] Bayãnin shãyar da mãma ga jinjirin da ubansa ya saki uwarsa a lõkacin shãyarwa ko kuma ta haife shi bãyan sakin yã auku.
  234. وَٱلَّذِينَ يُتَوَفَّوْنَ مِنكُمْ وَيَذَرُونَ أَزْوَٰجًا يَتَرَبَّصْنَ بِأَنفُسِهِنَّ أَرْبَعَةَ أَشْهُرٍ وَعَشْرًا ۖ فَإِذَا بَلَغْنَ أَجَلَهُنَّ فَلَا جُنَاحَ عَلَيْكُمْ فِيمَا فَعَلْنَ فِىٓ أَنفُسِهِنَّ بِٱلْمَعْرُوفِ ۗ وَٱللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرٌ۝٢٣٤

    Waallatheena yutawaffawna minkum wayatharoona azwajan yatarabbasna bianfusihinna arbaʿata ashhurin waʿashran faitha balaghna ajalahunna fala junaha ʿalaykum feema faʿalna fee anfusihinna bialmaʿroofi waAllahu bima taʿmaloona khabeerun

    Kuma waɗanda suke mutuwa1 daga gare ku suna barin mãtan aure, mãtan suna jinkiri da kansu wata huɗu da kwãna goma. To, idan sun isa ga ajalinsu, to, bãbu laifi a kanku a cikin abin da suka aikata game da kansu ga al'ãda. Kuma Allah ga abin da kuke aikatawa Masani ne.

    Bayanai
    [1] Bayãnin iddar mutuwar maza; mace ɗiya za ta zauna wata huɗu da kwana gõma. Baiwa mãtar aure tanã a kan rabi. Wadda ke shakkar ciki sai ta zauna sai shakka tã ɗebe. Ana takaba watau mai iddar mutuwa ta nisanci ƙawa kõwace iri ce, sai tã ƙãre idda.
  235. وَلَا جُنَاحَ عَلَيْكُمْ فِيمَا عَرَّضْتُم بِهِۦ مِنْ خِطْبَةِ ٱلنِّسَآءِ أَوْ أَكْنَنتُمْ فِىٓ أَنفُسِكُمْ ۚ عَلِمَ ٱللَّهُ أَنَّكُمْ سَتَذْكُرُونَهُنَّ وَلَـٰكِن لَّا تُوَاعِدُوهُنَّ سِرًّا إِلَّآ أَن تَقُولُوا۟ قَوْلًا مَّعْرُوفًا ۚ وَلَا تَعْزِمُوا۟ عُقْدَةَ ٱلنِّكَاحِ حَتَّىٰ يَبْلُغَ ٱلْكِتَـٰبُ أَجَلَهُۥ ۚ وَٱعْلَمُوٓا۟ أَنَّ ٱللَّهَ يَعْلَمُ مَا فِىٓ أَنفُسِكُمْ فَٱحْذَرُوهُ ۚ وَٱعْلَمُوٓا۟ أَنَّ ٱللَّهَ غَفُورٌ حَلِيمٌ۝٢٣٥

    Wala junaha ʿalaykum feema ʿarradtum bihi min khitbati alnnisai aw aknantum fee anfusikum ʿalima Allahu annakum satathkuroonahunna walakin la tuwaʿidoohunna sirran illa an taqooloo qawlan maʿroofan wala taʿzimoo ʿuqdata alnnikahi hatta yablugha alkitabu ajalahu waiʿlamoo anna Allaha yaʿlamu ma fee anfusikum faihtharoohu waiʿlamoo anna Allaha ghafoorun haleemun

    Kuma bãbu laifi a kanku a cikin abin da kuka gitta1 da shi daga nẽman auren mãtãko kuwa kuka ɓõye a cikin zukatanku. Allah Ya san cẽwa lalle ne ku za ku ambata musu (shi). Kuma amma kada ku yi wa jũna alkawari da shia ɓõye, fãce dai ku faɗi magana sananniya. Kuma kada ku ƙulla niyyar daurin auren sai littãfin (idda) ya kai ga ajalinsa. Kuma ku sani cẽwa lalle ne Allah Yana sanin abin da yake cikin zukatanku, sabõda haka ku ji tsõronsa. Kuma ku sani cewa Allah Mai gãfara ne, Mai haƙuri.

    Bayanai
    [1] Bayãnin hukuncin neman auren mace a cikin iddarta. An hana sai dai da bananci kamar ya ce mata, "Ina zan sãmi kamarki?".
  236. لَّا جُنَاحَ عَلَيْكُمْ إِن طَلَّقْتُمُ ٱلنِّسَآءَ مَا لَمْ تَمَسُّوهُنَّ أَوْ تَفْرِضُوا۟ لَهُنَّ فَرِيضَةً ۚ وَمَتِّعُوهُنَّ عَلَى ٱلْمُوسِعِ قَدَرُهُۥ وَعَلَى ٱلْمُقْتِرِ قَدَرُهُۥ مَتَـٰعًۢا بِٱلْمَعْرُوفِ ۖ حَقًّا عَلَى ٱلْمُحْسِنِينَ۝٢٣٦

    La junaha ʿalaykum in tallaqtumu alnnisaa ma lam tamassoohunna aw tafridoo lahunna fareedatan wamattiʿoohunna ʿala almoosiʿi qadaruhu waʿala almuqtiri qadaruhu mataʿan bialmaʿroofi haqqan ʿala almuhsineena

    Kuma bãbu laifi1 a kanku idan kun saki mãtã matuƙar ba ku shãfe su ba, kuma ba ku yanka musu sadãki ba. Kuma ku bã su kyautar dãɗaɗãwa, a kan mawadãci gwargwadonsa, kuma a kan maƙuntaci gwargwadonsa; dõmin dãɗaɗrwa, da alhẽri, wãjibi ne a kan mãsu kyautatãwa.

    Bayanai
    [1] Bayãnin sadãkin wadda aka saki gabãnin shãfa da yanka sadaki, watau mijin ya saki tun bai sãdu da ita ba kuma bai yanka sadãki ba. Bãbu sadãki gare ta sai kyautar dãɗaɗãwa kawai.
  237. وَإِن طَلَّقْتُمُوهُنَّ مِن قَبْلِ أَن تَمَسُّوهُنَّ وَقَدْ فَرَضْتُمْ لَهُنَّ فَرِيضَةً فَنِصْفُ مَا فَرَضْتُمْ إِلَّآ أَن يَعْفُونَ أَوْ يَعْفُوَا۟ ٱلَّذِى بِيَدِهِۦ عُقْدَةُ ٱلنِّكَاحِ ۚ وَأَن تَعْفُوٓا۟ أَقْرَبُ لِلتَّقْوَىٰ ۚ وَلَا تَنسَوُا۟ ٱلْفَضْلَ بَيْنَكُمْ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِيرٌ۝٢٣٧

    Wain tallaqtumoohunna min qabli an tamassoohunna waqad faradtum lahunna fareedatan fanisfu ma faradtum illa an yaʿfoona aw yaʿfuwa allathee biyadihi ʿuqdatu alnnikahi waan taʿfoo aqrabu lilttaqwa wala tansawoo alfadla baynakum inna Allaha bima taʿmaloona baseerun

    Kuma idan kuka sake su daga gabãnin ku shãfe su, alhãli kuwa1 kun yanka musu sadãki, to, rabin abin da kuka yanka fãce idan sun yãfe, kõ wanda ɗaurin auren yake ga hannunsa ya yãfe. Kuma ku yãfe ɗin ne mafi kusa da taƙawa. Kuma kada ku manta da falala a tsakãninku. Lalle ne Allah ga abin da kuke aikatãwa Mai gani ne.

    Bayanai
    [1] Bayãnin sadãkin wadda aka yanka wa sadãki amma kuma aka sake ta gabãnin shãfa, to, ita tanã da rabin sadãkinta, sai idan tã zauna a ɗakinsa shekara guda cikakkiya, to, sai a biya ta dukan sadãkinta.
  238. حَـٰفِظُوا۟ عَلَى ٱلصَّلَوَٰتِ وَٱلصَّلَوٰةِ ٱلْوُسْطَىٰ وَقُومُوا۟ لِلَّهِ قَـٰنِتِينَ۝٢٣٨

    Hafithoo ʿala alssalawati waalssalati alwusta waqoomoo lillahi qaniteena

    Ku tsare1 lõkatai a kan sallõli da salla mafificiya. Kuma ku tsayu kuna mãsu ƙanƙan da kai ga Allah.

    Bayanai
    [1] Bayãnin hukuncin tsare lõkutan salla a cikin kõwane hãli: aminci ko tsõro, da bãyar da salla yadda hãli ya bãyar duka; tsaye kõ da tafiya kõ gudãne. Hikimar sanya wannan hukunci a tsakãnin hukunce-hukuncen aure dõmin farkarwa a kan muhimmancin salla, dõmin kada mu'ãmala ta shagaltar da Musulmi daga gare ta.
  239. فَإِنْ خِفْتُمْ فَرِجَالًا أَوْ رُكْبَانًا ۖ فَإِذَآ أَمِنتُمْ فَٱذْكُرُوا۟ ٱللَّهَ كَمَا عَلَّمَكُم مَّا لَمْ تَكُونُوا۟ تَعْلَمُونَ۝٢٣٩

    Fain khiftum farijalan aw rukbanan faitha amintum faothkuroo Allaha kama ʿallamakum ma lam takoonoo taʿlamoona

    To, idan kun ji tsõro, to (ku dai yi salla gwargwadon hali) da tafiya ƙasa kõ kuwa a kan dabbobi. Sa'an nan idan kun amince sai ku ambaci Allah, kamar yadda Ya nũna muku abin da ba ku kasance kuna sani ba.

  240. وَٱلَّذِينَ يُتَوَفَّوْنَ مِنكُمْ وَيَذَرُونَ أَزْوَٰجًا وَصِيَّةً لِّأَزْوَٰجِهِم مَّتَـٰعًا إِلَى ٱلْحَوْلِ غَيْرَ إِخْرَاجٍ ۚ فَإِنْ خَرَجْنَ فَلَا جُنَاحَ عَلَيْكُمْ فِى مَا فَعَلْنَ فِىٓ أَنفُسِهِنَّ مِن مَّعْرُوفٍ ۗ وَٱللَّهُ عَزِيزٌ حَكِيمٌ۝٢٤٠

    Waallatheena yutawaffawna minkum wayatharoona azwajan wasiyyatan liazwajihim mataʿan ila alhawli ghayra ikhrajin fain kharajna fala junaha ʿalaykum fee ma faʿalna fee anfusihinna min maʿroofin waAllahu ʿazeezun hakeemun

    Kuma waɗanda suke mutuwa1 daga gare ku, alhãli suna barin mãtan aure, wasiyya ga mãtan aurensu da dãɗaɗãwa zuwa ga shekara guda bãbu fitarwa, to, idan sun fita to bãbu laifi a kanku a cikin abin da suka aikata game da kansu daga abin da aka sani, kuma Allah Mabuwayi ne, Mai hikima.

    Bayanai
    [1] Al'ãda idan ba ta sãɓã wa rukunin sharĩ'a ba bã a hana ta sai dai bãbu tilastãwa ga yinta. A zamanin Jãhiliyya mãtã suna iddar mutuwar mazansu shekara guda. Wanda ya yi wasiyyar kada matarsa ta fita daga ɗãkinta har shekara ana karɓar masa sai dai bãbu tĩlas a gare ta da ta zauna, dõmin an shãfe hukuncin iddar shekara ta al'ãdar Jãhiliyya.
  241. وَلِلْمُطَلَّقَـٰتِ مَتَـٰعٌۢ بِٱلْمَعْرُوفِ ۖ حَقًّا عَلَى ٱلْمُتَّقِينَ۝٢٤١

    Walilmutallaqati mataʿun bialmaʿroofi haqqan ʿala almuttaqeena

    Kuma waɗanda aka saki suna da dãɗaɗãwa gwargwadon hãli, wajibi ce a kan mãsu jin tsoron Allah1 .

    Bayanai
    [1] Bayãnin hukuncin dãɗaɗãwa ga mãtan da aka saki bãyan an yi zaman aure da su Tamattu'i gare su wãjibi ne a kan mazansu, gwargwadon hãli.
  242. كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ ٱللَّهُ لَكُمْ ءَايَـٰتِهِۦ لَعَلَّكُمْ تَعْقِلُونَ۝٢٤٢

    Kathalika yubayyinu Allahu lakum ayatihi laʿallakum taʿqiloona

    Kamar wancan ne Allah Yake bayyana muku ãyõyinSa; tsammãninku, kuna hankalta.

  243. ۞ أَلَمْ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ خَرَجُوا۟ مِن دِيَـٰرِهِمْ وَهُمْ أُلُوفٌ حَذَرَ ٱلْمَوْتِ فَقَالَ لَهُمُ ٱللَّهُ مُوتُوا۟ ثُمَّ أَحْيَـٰهُمْ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَذُو فَضْلٍ عَلَى ٱلنَّاسِ وَلَـٰكِنَّ أَكْثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَشْكُرُونَ۝٢٤٣

    Alam tara ila allatheena kharajoo min diyarihim wahum oloofun hathara almawti faqala lahumu Allahu mootoo thumma ahyahum inna Allaha lathoo fadlin ʿala alnnasi walakinna akthara alnnasi la yashkuroona

    Shin, ba ka gani ba, zuwa ga waɗanda suka fita1 daga gidãjensu, alhãli kuwa sũ dubbai ne, dõmin tsõron mutuwa? Sai Allah Ya ce musu: "Ku mutu." Sa'an nan kuma Ya rãyar da su, lalle ne Allah, haƙĩƙa Ma'abũcin falala a kan mutãne ne, kuma amma mafi yawan mutãne bã su gõdẽwa.

    Bayanai
    [1] Wasu mutãne ne daga cikin Bani Isrã'ila annõba tã auku a kansu sai suka fita daga gidãjensu dõmin gudun mutuwa sũ dubũ huɗu kõ takwas kõ wanin wannan adadi, sai Allah Ya ce musu; "Ku mutu,"sai suka mutu kwana takwas kõ fiye da haka. Sa'an nan kuma Allah Ya tãyar da su dõmin Ya nũna musu cewa gudun mutuwa, bã ya hana ta, sai abin da Ya so, shi ke aukuwa. Wannan ƙissa tanã amfãnar da ƙarfafa rãyuka dõmin jihãdi, sabõda haka umurni da yãƙi ya bĩ ta; watau ita shimfiɗa ce ga umurnin jihãdi da fita zuwa yãƙi. Kuma sũrar na karantar da tattalin arziki daga nan zuwa ƙarshenta. Watau kafa gari wajibi ne ga tattalin arziki.
  244. وَقَـٰتِلُوا۟ فِى سَبِيلِ ٱللَّهِ وَٱعْلَمُوٓا۟ أَنَّ ٱللَّهَ سَمِيعٌ عَلِيمٌ۝٢٤٤

    Waqatiloo fee sabeeli Allahi waiʿlamoo anna Allaha sameeʿun ʿaleemun

    Kuma ku yi yãƙi a cikin hanyar Allah, kuma ku sani cẽwa lalle ne, Allah Mai jĩ ne, Masani.

  245. مَّن ذَا ٱلَّذِى يُقْرِضُ ٱللَّهَ قَرْضًا حَسَنًا فَيُضَـٰعِفَهُۥ لَهُۥٓ أَضْعَافًا كَثِيرَةً ۚ وَٱللَّهُ يَقْبِضُ وَيَبْصُۜطُ وَإِلَيْهِ تُرْجَعُونَ۝٢٤٥

    Man tha allathee yuqridu Allaha qardan hasanan fayudaʿifahu lahu adʿafan katheeratan waAllahu yaqbidu wayabsutu wailayhi turjaʿoona

    Wãne ne wanda1 zai bai wa Allah rance, rance mai kyau, dõmin Ya riɓanya masa, riɓanyãwa mai yawa? Kuma Allah Shi ne ke damƙewa, kuma yana shimfiɗawa, kuma zuwa a gare Shi ake mayar da ku.

    Bayanai
    [1] Bãyãni ga cewa jihãdi bã ya yiwuwa sai mutãne kõwa ya bãyar da taimakonsa na dũkiya kõ na ma'ana. Kuma duk wanda ya bãyar da taimako, to, rance ne ya bai wa Allah, Wanda yake Shi ne Ya bãyar da asalin dũkiyar, da yawa kõ kaɗan, kuma Mai sakamako ga wanda ya yi aiki da umurninSa da babban sakamako, bãyan an kõma zuwa gareShi. Jihãdi wãjibi ne ga tattalin arziki domin tsaro.
  246. أَلَمْ تَرَ إِلَى ٱلْمَلَإِ مِنۢ بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ مِنۢ بَعْدِ مُوسَىٰٓ إِذْ قَالُوا۟ لِنَبِىٍّ لَّهُمُ ٱبْعَثْ لَنَا مَلِكًا نُّقَـٰتِلْ فِى سَبِيلِ ٱللَّهِ ۖ قَالَ هَلْ عَسَيْتُمْ إِن كُتِبَ عَلَيْكُمُ ٱلْقِتَالُ أَلَّا تُقَـٰتِلُوا۟ ۖ قَالُوا۟ وَمَا لَنَآ أَلَّا نُقَـٰتِلَ فِى سَبِيلِ ٱللَّهِ وَقَدْ أُخْرِجْنَا مِن دِيَـٰرِنَا وَأَبْنَآئِنَا ۖ فَلَمَّا كُتِبَ عَلَيْهِمُ ٱلْقِتَالُ تَوَلَّوْا۟ إِلَّا قَلِيلًا مِّنْهُمْ ۗ وَٱللَّهُ عَلِيمٌۢ بِٱلظَّـٰلِمِينَ۝٢٤٦

    Alam tara ila almalai min banee israeela min baʿdi moosa ith qaloo linabiyyin lahumu ibʿath lana malikan nuqatil fee sabeeli Allahi qala hal ʿasaytum in kutiba ʿalaykumu alqitalu alla tuqatiloo qaloo wama lana alla nuqatila fee sabeeli Allahi waqad okhrijna min diyarina waabnaina falamma kutiba ʿalayhimu alqitalu tawallaw illa qaleelan minhum waAllahu ʿaleemun bialththalimeena

    Shin, ba ka gani ba zuwa ga wasu mashãwarta1 daga Bani Isrã'ĩla daga bãyan Mũsã, a lõkacinda suka ce ga wani annabi nãsu: "Naɗã mana sarki, mu yi yãƙi a cikin hanyar Allah." Ya ce: "Ashe, akwai tsammãninku idan an wajabta yãƙi a kanku cẽwa bã zã ku yi yãƙin ba?" Suka ce: "Kuma mẽne ne a gare mu, ba zã mu yi yãƙi ba, a cikin hanyar Allah, alhãli kuwa, haƙiƙa, an fitar da mu daga gidãjenmu da ɗiyanmu?" To, a lõkacin da aka wajabta yãƙin a kansu, suka jũya, sai kaɗan daga gare su. Kuma Allah Masani ne ga azzãlumai.

    Bayanai
    [1] Wannan ƙissa tana nũna cewa ba a iya yin yãƙi sai da sarki' shũgaba. Kuma ta fadi dalĩlin da ke sanya jama'a su yi yãƙi; watau dõmin tsaron addini da rãyuka da nasaba da mutunci da dũkiya.
  247. وَقَالَ لَهُمْ نَبِيُّهُمْ إِنَّ ٱللَّهَ قَدْ بَعَثَ لَكُمْ طَالُوتَ مَلِكًا ۚ قَالُوٓا۟ أَنَّىٰ يَكُونُ لَهُ ٱلْمُلْكُ عَلَيْنَا وَنَحْنُ أَحَقُّ بِٱلْمُلْكِ مِنْهُ وَلَمْ يُؤْتَ سَعَةً مِّنَ ٱلْمَالِ ۚ قَالَ إِنَّ ٱللَّهَ ٱصْطَفَىٰهُ عَلَيْكُمْ وَزَادَهُۥ بَسْطَةً فِى ٱلْعِلْمِ وَٱلْجِسْمِ ۖ وَٱللَّهُ يُؤْتِى مُلْكَهُۥ مَن يَشَآءُ ۚ وَٱللَّهُ وَٰسِعٌ عَلِيمٌ۝٢٤٧

    Waqala lahum nabiyyuhum inna Allaha qad baʿatha lakum taloota malikan qaloo anna yakoonu lahu almulku ʿalayna wanahnu ahaqqu bialmulki minhu walam yuta saʿatan mina almali qala inna Allaha istafahu ʿalaykum wazadahu bastatan fee alʿilmi waaljismi waAllahu yutee mulkahu man yashao waAllahu wasiʿun ʿaleemun

    Kuma annabinsu1 ya ce musu: "Lalle ne, Allah ya naɗa muku ¦ãlũta2 ya zama sarki." Suka ce: "Yãya ne sarauta zã ta kasance a gare shi, a kanmu, alhãli kuwa mũ ne mafi cancanta da sarauta daga gare shi, kuma ba a bã shi wata wadata ba daga dũkiya?" Ya ce: "Lalle ne, Allah Yã zãɓe shi a kanku, kuma Ya ƙãra masa yalwa a cikin ilmi da jiki. Kuma Allah Yana bãyar da mulkinSa ga wanda Yake so, kuma Allah Mawadaci ne, Masani.

    Bayanai
    [1] Sũnan Annabinsu Shamwĩlu daga Sibt Lãwaya. A bãyan Mũsã Yũsha'u bin Nũn sa'an nan Kãlib, sa'an nan Hizƙĩl, sa'an nan Ilyas sa'an nan Alyasa'u, daga nan Bani Isrã'ila suka rasa mai jan su har Amãliƙa ɗiyan Amlĩƙ bn Ãd waɗanda ke zaune a Falastĩn suka rinjãyi Bani Isrã'ila, suka karkashe su suka kõre su daga gidãjensu suka kãma 'ya'yansu, har a lõkacin da wata mace daga Sibt Lãwaya ta haifi Shamwĩlu Annabi. Ya naɗa musu sarki Ɗãlũta. [2] Ɗãlũta yana a cikin gidan Binyãminu ɗan Ya'aƙũbu talakãwa ne sunã dõgara a kan sanã'a. Zũriyyar Yahũza, sũ ne sarãkuna dõmin haka sunansu ya rinjãya a kan Bani Isra'ila. Zũriyyar Lãwaya sũ ne Annabãwa da mãlamai.
  248. وَقَالَ لَهُمْ نَبِيُّهُمْ إِنَّ ءَايَةَ مُلْكِهِۦٓ أَن يَأْتِيَكُمُ ٱلتَّابُوتُ فِيهِ سَكِينَةٌ مِّن رَّبِّكُمْ وَبَقِيَّةٌ مِّمَّا تَرَكَ ءَالُ مُوسَىٰ وَءَالُ هَـٰرُونَ تَحْمِلُهُ ٱلْمَلَـٰٓئِكَةُ ۚ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً لَّكُمْ إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ۝٢٤٨

    Waqala lahum nabiyyuhum inna ayata mulkihi an yatiyakumu alttabootu feehi sakeenatun min rabbikum wabaqiyyatun mimma taraka alu moosa waalu haroona tahmiluhu almalaikatu inna fee thalika laayatan lakum in kuntum mumineena

    Kuma annabinsu ya ce musu: "Lalle ne alãmar mulkinSa ita ce akwatin1 nan ya zo muku, a cikinsa akwai natsuwa daga Ubangijinku da sauran kaya daga abin da Gidan Mũsã da Gidan Hãrũna suka bari malã'iku suna ɗaukarsa. Lalle ne a cikin wancan akwai alãma a gare ku (ta naɗin ¦ãlũta daga Allah ne) idan kun kasance mãsu ĩmãni."

    Bayanai
    [1] Akwatin Natsuwa, an saukar da shi tãre da Ãdam a cikinsa akwai sũrõrin annabãwa, da gãdon riƙonsa ya kai ga Mũsã yanã sanya Attaura a ciki sabõda haka aka sãmi karyayyun allunan Attaura a ciki da rawanin Harũna da wani abu daga Mannu da Salwa. A lõkacin da Amãliƙa suka rinjãye su, sai suka karɓe wannan akwãti suka ajiye shi inda bai dãce da shi ba, har a lõkacin da malã'iku suka ɗauke shi zuwa ga Ɗãlũta.
  249. فَلَمَّا فَصَلَ طَالُوتُ بِٱلْجُنُودِ قَالَ إِنَّ ٱللَّهَ مُبْتَلِيكُم بِنَهَرٍ فَمَن شَرِبَ مِنْهُ فَلَيْسَ مِنِّى وَمَن لَّمْ يَطْعَمْهُ فَإِنَّهُۥ مِنِّىٓ إِلَّا مَنِ ٱغْتَرَفَ غُرْفَةًۢ بِيَدِهِۦ ۚ فَشَرِبُوا۟ مِنْهُ إِلَّا قَلِيلًا مِّنْهُمْ ۚ فَلَمَّا جَاوَزَهُۥ هُوَ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ مَعَهُۥ قَالُوا۟ لَا طَاقَةَ لَنَا ٱلْيَوْمَ بِجَالُوتَ وَجُنُودِهِۦ ۚ قَالَ ٱلَّذِينَ يَظُنُّونَ أَنَّهُم مُّلَـٰقُوا۟ ٱللَّهِ كَم مِّن فِئَةٍ قَلِيلَةٍ غَلَبَتْ فِئَةً كَثِيرَةًۢ بِإِذْنِ ٱللَّهِ ۗ وَٱللَّهُ مَعَ ٱلصَّـٰبِرِينَ۝٢٤٩

    Falamma fasala talootu bialjunoodi qala inna Allaha mubtaleekum binaharin faman shariba minhu falaysa minnee waman lam yatʿamhu fainnahu minnee illa mani ightarafa ghurfatan biyadihi fashariboo minhu illa qaleelan minhum falamma jawazahu huwa waallatheena amanoo maʿahu qaloo la taqata lana alyawma bijaloota wajunoodihi qala allatheena yathunnoona annahum mulaqoo Allahi kam min fiatin qaleelatin ghalabat fiatan katheeratan biithni Allahi waAllahu maʿa alssabireena

    A lõkacin da ¦ãlũta ya fita1 da rundunõnin, ya ce: "Lalle ne Allah Mai jarrabarku ne da wani kõgi. To, wanda ya sha daga gare shi, to, ba shi daga gare ni, kuma wanda bai ɗanɗane shi ba to lalle ne shi, yana daga gare ni, fãce, wanda ya kamfata, kamfata guda da hannunsa." Sai suka sha daga gare shi, fãce kaɗan daga gare su. To, a lõkacin da (¦ãlũta) ya ƙẽtare shi, shi da waɗanda suka yi ĩmani tãre da shi, (sai waɗanda suka sha) suka ce: "Babu ĩko a gare mu yau game da Jãlũta da rundunõninsa."Waɗanda suka tabbata cẽwa lalle sũ mãsu gamuwa ne da Allah, suka ce: "Da yawa ƙungiya kaɗan ta rinjayi wata ƙungiya mai yawa da iznin Allah, kuma Allah Yana tãre da mãsu haƙuri."

    Bayanai
    [1] Sõja na bukãtar tarbiya, su sãbã da wahala da ƙishirwa da magana mai shiryarwa. Kõgin kuwa shĩ ne kõgin Urdun tsakãnin Urdun da Falastĩn.
  250. وَلَمَّا بَرَزُوا۟ لِجَالُوتَ وَجُنُودِهِۦ قَالُوا۟ رَبَّنَآ أَفْرِغْ عَلَيْنَا صَبْرًا وَثَبِّتْ أَقْدَامَنَا وَٱنصُرْنَا عَلَى ٱلْقَوْمِ ٱلْكَـٰفِرِينَ۝٢٥٠

    Walamma barazoo lijaloota wajunoodihi qaloo rabbana afrigh ʿalayna sabran wathabbit aqdamana waonsurna ʿala alqawmi alkafireena

    Kuma a lõkacin da suka1 bayyana ga Jãlũta da rundunoninsa, suka ce: "Yã Ubangijinmu! Ka zuba haƙuri a kanmu kuma Ka tabbatar da sãwayenmu, kuma Ka taimake mu a kan mutãnen nan kãfirai."

    Bayanai
    [1] Dãwũdu ɗan Ãisha ya gãji annabcin Shamwĩlu da mulkin Ɗãlũta, shĩ ne ya fãra haɗã su a cikin Bani lsrã'ila bãyansa sai ɗansa Sulaimãn ya gãje shi haka nan. Yawan mutãnen Ɗãlũta da suka yi yãƙi kamar adadin mutãnen Badar ne waɗanda suka yi yãƙi tãre da Annabi, tsĩra da aminci su tabbata a gare shi.
  251. فَهَزَمُوهُم بِإِذْنِ ٱللَّهِ وَقَتَلَ دَاوُۥدُ جَالُوتَ وَءَاتَىٰهُ ٱللَّهُ ٱلْمُلْكَ وَٱلْحِكْمَةَ وَعَلَّمَهُۥ مِمَّا يَشَآءُ ۗ وَلَوْلَا دَفْعُ ٱللَّهِ ٱلنَّاسَ بَعْضَهُم بِبَعْضٍ لَّفَسَدَتِ ٱلْأَرْضُ وَلَـٰكِنَّ ٱللَّهَ ذُو فَضْلٍ عَلَى ٱلْعَـٰلَمِينَ۝٢٥١

    Fahazamoohum biithni Allahi waqatala dawoodu jaloota waatahu Allahu almulka waalhikmata waʿallamahu mimma yashao walawla dafʿu Allahi alnnasa baʿdahum bibaʿdin lafasadati alardu walakinna Allaha thoo fadlin ʿala alʿalameena

    Sai suka karya su da iznin Allah. Kuma Dãwudu ya kashe Jãlũta, kuma Allah Ya bã shi mulki da hikima kuma Ya sanar da shi daga abin da Yake so. Kuma bã dõmin tunkuɗẽwar Allah ga mutãne sãshensu da sãshe ba lalle ne dã ƙasa tã ɓãci; kuma amma Allah Ma'abũcin falala ne a kan tãlikai.

  252. تِلْكَ ءَايَـٰتُ ٱللَّهِ نَتْلُوهَا عَلَيْكَ بِٱلْحَقِّ ۚ وَإِنَّكَ لَمِنَ ٱلْمُرْسَلِينَ۝٢٥٢

    Tilka ayatu Allahi natlooha ʿalayka bialhaqqi wainnaka lamina almursaleena

    Waɗancan ayõyin Allah ne: Muna karanta su a kanka da gaskiya: Kuma lalle ne kai, hakĩka, kana daga manzanni.

  253. ۞ تِلْكَ ٱلرُّسُلُ فَضَّلْنَا بَعْضَهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ ۘ مِّنْهُم مَّن كَلَّمَ ٱللَّهُ ۖ وَرَفَعَ بَعْضَهُمْ دَرَجَـٰتٍ ۚ وَءَاتَيْنَا عِيسَى ٱبْنَ مَرْيَمَ ٱلْبَيِّنَـٰتِ وَأَيَّدْنَـٰهُ بِرُوحِ ٱلْقُدُسِ ۗ وَلَوْ شَآءَ ٱللَّهُ مَا ٱقْتَتَلَ ٱلَّذِينَ مِنۢ بَعْدِهِم مِّنۢ بَعْدِ مَا جَآءَتْهُمُ ٱلْبَيِّنَـٰتُ وَلَـٰكِنِ ٱخْتَلَفُوا۟ فَمِنْهُم مَّنْ ءَامَنَ وَمِنْهُم مَّن كَفَرَ ۚ وَلَوْ شَآءَ ٱللَّهُ مَا ٱقْتَتَلُوا۟ وَلَـٰكِنَّ ٱللَّهَ يَفْعَلُ مَا يُرِيدُ۝٢٥٣

    Tilka alrrusulu faddalna baʿdahum ʿala baʿdin minhum man kallama Allahu warafaʿa baʿdahum darajatin waatayna ʿeesa ibna maryama albayyinati waayyadnahu biroohi alqudusi walaw shaa Allahu ma iqtatala allatheena min baʿdihim min baʿdi ma jaathumu albayyinatu walakini ikhtalafoo faminhum man amana waminhum man kafara walaw shaa Allahu ma iqtataloo walakinna Allaha yafʿalu ma yureedu

    Waɗancan manzannin1 Mun fĩfĩta sãshensu a kan sãshe: Daga cikinsu akwai wanda Allah Ya yi masa magana; kuma Ya ɗaukaka sãshensu da darajõji; kuma Muka bai wa Ĩsã dan Maryama hujjõji bayyanannu, kuma Muka ƙarfafã shi da Rũhi mai tsarki. Kuma dã Allah Yã so dã waɗanda suke daga bãyansu, bã zã su yi yãƙi ba, daga bãyan hujjõji bayyanannu sun je musu. Kuma amma sun sãɓa wa jũna, sabõda haka daga cikinsu akwai wanda ya yi ĩmãni, kuma daga cikin su akwai wanda ya kãfirta. Kuma dã Allah Yã so dã bã zã su yãƙi jũna ba, kuma amma Allah Yana aikata abin da Yake nufi.

    Bayanai
    [1] Allah Yanã tunkuɗe ɓarna a cikin ƙasa da wãsiɗar karantar da mãsu alheri, dõmin su yãƙi mãsu sharri. Ya saukar da ilminSa da wãsiɗar manzanninSa waɗanda Ya tabbatar da cewa Muhammadu, tsira da amincinSa su tabbata a gare shi, yana cikinsu kuma shi ne ya fi ɗaukaka daga cikinsu. Daga wannan ãyã zuwa ƙarshen Sũra duka, ƙãrin bãyani ne da shiryarwa ga hukunce-hukuncen da suka gabãta da kuma yadda zã a zartar da aiki da su, kamar yadda tsãrin magana zai nũna in Allah Ya so.
  254. يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓا۟ أَنفِقُوا۟ مِمَّا رَزَقْنَـٰكُم مِّن قَبْلِ أَن يَأْتِىَ يَوْمٌ لَّا بَيْعٌ فِيهِ وَلَا خُلَّةٌ وَلَا شَفَـٰعَةٌ ۗ وَٱلْكَـٰفِرُونَ هُمُ ٱلظَّـٰلِمُونَ۝٢٥٤

    Ya ayyuha allatheena amanoo anfiqoo mimma razaqnakum min qabli an yatiya yawmun la bayʿun feehi wala khullatun wala shafaʿatun waalkafiroona humu alththalimoona

    Ya ku waɗanda1 suka yi ĩmãni! Ku ciyar daga abin da Muka azurta ku daga gabãnin wani yini ya zo bãbu ciniki a cikinsa kuma bãbu abũta, kuma bãbu cẽto, kuma kãfirai sũ ne Azzãlumai.

    Bayanai
    [1] Bãyan tabbatar da manzancin Annabi Muhammadu tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi, sa'an nan ya sãbunta fuskanta da kira zuwa ga waɗanda suka yi ĩmãni da Annabi, kuma ya farkar da su game da zuwan babbar rãna ta Ƙiyãma. Sa'an nan ya faɗi sũnanSa Ta'ãla, Allah Mai sifõfin da ke cikin ãyã ta 255.
  255. ٱللَّهُ لَآ إِلَـٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلْحَىُّ ٱلْقَيُّومُ ۚ لَا تَأْخُذُهُۥ سِنَةٌ وَلَا نَوْمٌ ۚ لَّهُۥ مَا فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَمَا فِى ٱلْأَرْضِ ۗ مَن ذَا ٱلَّذِى يَشْفَعُ عِندَهُۥٓ إِلَّا بِإِذْنِهِۦ ۚ يَعْلَمُ مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ ۖ وَلَا يُحِيطُونَ بِشَىْءٍ مِّنْ عِلْمِهِۦٓ إِلَّا بِمَا شَآءَ ۚ وَسِعَ كُرْسِيُّهُ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضَ ۖ وَلَا يَـُٔودُهُۥ حِفْظُهُمَا ۚ وَهُوَ ٱلْعَلِىُّ ٱلْعَظِيمُ۝٢٥٥

    Allahu la ilaha illa huwa alhayyu alqayyoomu la takhuthuhu sinatun wala nawmun lahu ma fee alssamawati wama fee alardi man tha allathee yashfaʿu ʿindahu illa biithnihi yaʿlamu ma bayna aydeehim wama khalfahum wala yuheetoona bishayin min ʿilmihi illa bima shaa wasiʿa kursiyyuhu alssamawati waalarda wala yaooduhu hifthuhuma wahuwa alʿaliyyu alʿatheemu

    Allah, bãbu wani Ubangiji fãce Shi, Rãyayye, Mai tsayuwa da kõme, gyangyaɗi bã ya kãma Shi, kuma barci bã ya kãma Shi, Shi ne da abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa. Wane ne wanda yake yin cẽto a wurinSa, fãce da izninSa? Yana sanin abin da yake a gaba gare su da abin da yake a bãyansu. Kuma bã su kẽwayẽwa da kõme daga ilminSa, fãce da abin da Ya so. KursiyyunSa ya yalwaci sammai da ƙasa. Kuma tsare su bã ya nauyayarSa. Kuma Shi ne Maɗaukaki, Mai girma.

  256. لَآ إِكْرَاهَ فِى ٱلدِّينِ ۖ قَد تَّبَيَّنَ ٱلرُّشْدُ مِنَ ٱلْغَىِّ ۚ فَمَن يَكْفُرْ بِٱلطَّـٰغُوتِ وَيُؤْمِنۢ بِٱللَّهِ فَقَدِ ٱسْتَمْسَكَ بِٱلْعُرْوَةِ ٱلْوُثْقَىٰ لَا ٱنفِصَامَ لَهَا ۗ وَٱللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ۝٢٥٦

    La ikraha fee alddeeni qad tabayyana alrrushdu mina alghayyi faman yakfur bialttaghooti wayumin biAllahi faqadi istamsaka bialʿurwati alwuthqa la infisama laha waAllahu sameeʿun ʿaleemun

    Bãbu tĩlastãwa1 a cikin addini, haƙĩƙa shiriya tã bayyana daga ɓata; Sabõda haka wanda ya kãfirta da ¦ãgũta kuma ya yi ĩmãni da Allah, to, haƙĩƙa, yã yi riƙo ga igiya amintacciya, bãbu yankẽwa agare ta. Kuma Allah Mai ji ne, Masani.

    Bayanai
    [1] Abũbuwan bautãwa, iri biyu ne; Ubangijin da Yã aiko Muhammadu da wannan gaskiya da shiriya Shĩ ne Allah, da sauran iyãyen giji mãsu dõkõkin kai da na son zũkãta kamar nafsu da Shaiɗan, na aljannu da mutãne, mãsu ƙãga abin da suke so, su ƙira mutane a kansa ana ce musu Ɗãgũtu. Ya yi bayãnin sakamakon mabiyin kõwane irin bautawar. Sa'an nan ya biyar da ƙissõshi uku dõmin bayãnin abin da wannan magana ta ƙunsa; ta farko Namarũzu tãre da Ibrãhĩm, tanã nũna cewa mai mulki anã umurtar sa da bin Allah da taƙawa, idan ya bi son zũciyarsa, to, ya zama Ɗãgũtu. Allah zai halakar da shi. Ta biyu ƙissar Uzairu, tanã nũna cewa bãbu abin da yake da wuya ga Allah. Ta uku ƙissar Ibrãhim da yadda Allah ke rãyar da matattu, tanã nũna cewa bãbu laifi ka roƙi Allah Ya gãnar da kai dukan abin da ya shige maka duhu dõmin ka ƙãrã ĩmãni.
  257. ٱللَّهُ وَلِىُّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ يُخْرِجُهُم مِّنَ ٱلظُّلُمَـٰتِ إِلَى ٱلنُّورِ ۖ وَٱلَّذِينَ كَفَرُوٓا۟ أَوْلِيَآؤُهُمُ ٱلطَّـٰغُوتُ يُخْرِجُونَهُم مِّنَ ٱلنُّورِ إِلَى ٱلظُّلُمَـٰتِ ۗ أُو۟لَـٰٓئِكَ أَصْحَـٰبُ ٱلنَّارِ ۖ هُمْ فِيهَا خَـٰلِدُونَ۝٢٥٧

    Allahu waliyyu allatheena amanoo yukhrijuhum mina alththulumati ila alnnoori waallatheena kafaroo awliyaohumu alttaghootu yukhrijoonahum mina alnnoori ila alththulumati olaika ashabu alnnari hum feeha khalidoona

    Allah Shi ne Masõyin waɗanda suka yi ĩmãni; Yana fitar da su daga duffai zuwa ga haske, kuma waɗanda suka kãfirta, masõyansu ¦ãgũtu ne; suna fitar da su daga haske zuwa ga duffai. Waɗannan abokan Wuta ne, sũ a cikinta madawwama ne.

  258. أَلَمْ تَرَ إِلَى ٱلَّذِى حَآجَّ إِبْرَٰهِـۧمَ فِى رَبِّهِۦٓ أَنْ ءَاتَىٰهُ ٱللَّهُ ٱلْمُلْكَ إِذْ قَالَ إِبْرَٰهِـۧمُ رَبِّىَ ٱلَّذِى يُحْىِۦ وَيُمِيتُ قَالَ أَنَا۠ أُحْىِۦ وَأُمِيتُ ۖ قَالَ إِبْرَٰهِـۧمُ فَإِنَّ ٱللَّهَ يَأْتِى بِٱلشَّمْسِ مِنَ ٱلْمَشْرِقِ فَأْتِ بِهَا مِنَ ٱلْمَغْرِبِ فَبُهِتَ ٱلَّذِى كَفَرَ ۗ وَٱللَّهُ لَا يَهْدِى ٱلْقَوْمَ ٱلظَّـٰلِمِينَ۝٢٥٨

    Alam tara ila allathee hajja ibraheema fee rabbihi an atahu Allahu almulka ith qala ibraheemu rabbiya allathee yuhyee wayumeetu qala ana ohyee waomeetu qala ibraheemu fainna Allaha yatee bialshshamsi mina almashriqi fati biha mina almaghribi fabuhita allathee kafara waAllahu la yahdee alqawma alththalimeena

    Shin, ba ka gani1 ba zuwa ga wanda ya yi hujjatayya da Ibrãhĩm a cikin (al'amarin) Ubangijinsa dõmin Allah Yã bã shi mulki, a lõkacin da Ibrãhĩm ya ce: "Ubangijina Shi ne Wanda Yake rãyawa kuma Yana matarwa." Ya ce: "Nĩ ina rãyarwa kuma ina matarwa." Ibrãhĩm ya ce: "To, lalle ne Allah Yana zuwa da rana daga gabas: To, ka zo da ita daga yamma." Sai aka ɗimautar da wanda yakãfirta. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutãne azzãlumai.

    Bayanai
    [1] Ƙissar farko ta Ibrãhĩm da Namarũzu.
  259. أَوْ كَٱلَّذِى مَرَّ عَلَىٰ قَرْيَةٍ وَهِىَ خَاوِيَةٌ عَلَىٰ عُرُوشِهَا قَالَ أَنَّىٰ يُحْىِۦ هَـٰذِهِ ٱللَّهُ بَعْدَ مَوْتِهَا ۖ فَأَمَاتَهُ ٱللَّهُ مِا۟ئَةَ عَامٍ ثُمَّ بَعَثَهُۥ ۖ قَالَ كَمْ لَبِثْتَ ۖ قَالَ لَبِثْتُ يَوْمًا أَوْ بَعْضَ يَوْمٍ ۖ قَالَ بَل لَّبِثْتَ مِا۟ئَةَ عَامٍ فَٱنظُرْ إِلَىٰ طَعَامِكَ وَشَرَابِكَ لَمْ يَتَسَنَّهْ ۖ وَٱنظُرْ إِلَىٰ حِمَارِكَ وَلِنَجْعَلَكَ ءَايَةً لِّلنَّاسِ ۖ وَٱنظُرْ إِلَى ٱلْعِظَامِ كَيْفَ نُنشِزُهَا ثُمَّ نَكْسُوهَا لَحْمًا ۚ فَلَمَّا تَبَيَّنَ لَهُۥ قَالَ أَعْلَمُ أَنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍ قَدِيرٌ۝٢٥٩

    Aw kaallathee marra ʿala qaryatin wahiya khawiyatun ʿala ʿurooshiha qala anna yuhyee hathihi Allahu baʿda mawtiha faamatahu Allahu miata ʿamin thumma baʿathahu qala kam labithta qala labithtu yawman aw baʿda yawmin qala bal labithta miata ʿamin faonthur ila taʿamika washarabika lam yatasannah waonthur ila himarika walinajʿalaka ayatan lilnnasi waonthur ila alʿithami kayfa nunshizuha thumma naksooha lahman falamma tabayyana lahu qala aʿlamu anna Allaha ʿala kulli shayin qadeerun

    Kõ kuwa1 wanda ya shũɗe a kan wata alƙarya, alhãli kuwa tana wõfintacciya a kan gadãjen rẽsunanta. Ya ce: "Yaya Allah zai rãyar da wannan a bãyan mutuwarta." Sai Allah Ya matar da shi, shẽkara ɗari; sa'an nankuma ya tãyar da shi. Ya ce: "Nawa ka zauna?" Ya ce: "Na zauna yini ɗaya ko kuwa rabin yini." Ya ce: "A'a kã zauna shẽkara ɗari." To, ka dũba zuwa ga abincinka, da abin shanka, (kõwanensu) bai sãke ba, kuma ka dũba zuwa ga jãkinka, kuma dõmin Mu sanya ka wata ãyã ga mutãne. Kuma ka duba zuwa ga ƙasũsuwa yadda Muke mõtsarda su sa'an nan kuma Mu tufãtar da su, da nãma", To, a lõkacin da (abin) ya bayyana a gare shi, ya ce: "Ina sanin cẽwa lalle Allah a kan dukan kõme Mai ĩkõn yi ne."

    Bayanai
    [1] Ƙissa ta biyu Uzairu da alƙarya matacciya, da jãkinsa, da abincinsa bãyan shekara ɗari.
  260. وَإِذْ قَالَ إِبْرَٰهِـۧمُ رَبِّ أَرِنِى كَيْفَ تُحْىِ ٱلْمَوْتَىٰ ۖ قَالَ أَوَلَمْ تُؤْمِن ۖ قَالَ بَلَىٰ وَلَـٰكِن لِّيَطْمَئِنَّ قَلْبِى ۖ قَالَ فَخُذْ أَرْبَعَةً مِّنَ ٱلطَّيْرِ فَصُرْهُنَّ إِلَيْكَ ثُمَّ ٱجْعَلْ عَلَىٰ كُلِّ جَبَلٍ مِّنْهُنَّ جُزْءًا ثُمَّ ٱدْعُهُنَّ يَأْتِينَكَ سَعْيًا ۚ وَٱعْلَمْ أَنَّ ٱللَّهَ عَزِيزٌ حَكِيمٌ۝٢٦٠

    Waith qala ibraheemu rabbi arinee kayfa tuhyee almawta qala awalam tumin qala bala walakin liyatmainna qalbee qala fakhuth arbaʿatan mina alttayri fasurhunna ilayka thumma ijʿal ʿala kulli jabalin minhunna juzan thumma odʿuhunna yateenaka saʿyan waiʿlam anna Allaha ʿazeezun hakeemun

    Kuma a lõkacin da Ibrãhĩm ya ce: "Ya Ubangijina! Ka nũna mini yadda Kake rãyar da matattu." Ya ce: "Shin, kuma ba ka yi ĩmãni ba?" Ya ce: "Na'am! Kuma amma dõmin zũciyãta, ta natsu." Ya ce: "To ka riƙi huɗu daga tsuntsãye, ka karkatar da su zuwa gare ka, ka yanka su, sa'an nan kuma ka sanya juzu'i daga gare su a kan kõwane dũtse, sa'an nan kuma ka kira su zã su zo maka gudãne. Kuma ka sani cẽwa lalle Allah Mabuwãyi ne, Masani."

  261. مَّثَلُ ٱلَّذِينَ يُنفِقُونَ أَمْوَٰلَهُمْ فِى سَبِيلِ ٱللَّهِ كَمَثَلِ حَبَّةٍ أَنۢبَتَتْ سَبْعَ سَنَابِلَ فِى كُلِّ سُنۢبُلَةٍ مِّا۟ئَةُ حَبَّةٍ ۗ وَٱللَّهُ يُضَـٰعِفُ لِمَن يَشَآءُ ۗ وَٱللَّهُ وَٰسِعٌ عَلِيمٌ۝٢٦١

    Mathalu allatheena yunfiqoona amwalahum fee sabeeli Allahi kamathali habbatin anbatat sabʿa sanabila fee kulli sunbulatin miatu habbatin waAllahu yudaʿifu liman yashao waAllahu wasiʿun ʿaleemun

    Sifar waɗanda suke ciyar da dũkiyõyinsu a cikin hanyar Allah, kamar sifar ƙwãyã ce wadda ta tsirar da zangarniya bakwai, a cikin kõwace zangarniya akwai ƙwãya ɗari. Kuma Allah Yana riɓinyawa ga wanda Ya so. Kuma Allah Mawadãci ne, Masani.

  262. ٱلَّذِينَ يُنفِقُونَ أَمْوَٰلَهُمْ فِى سَبِيلِ ٱللَّهِ ثُمَّ لَا يُتْبِعُونَ مَآ أَنفَقُوا۟ مَنًّا وَلَآ أَذًى ۙ لَّهُمْ أَجْرُهُمْ عِندَ رَبِّهِمْ وَلَا خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلَا هُمْ يَحْزَنُونَ۝٢٦٢

    Allatheena yunfiqoona amwalahum fee sabeeli Allahi thumma la yutbiʿoona ma anfaqoo mannan wala athan lahum ajruhum ʿinda rabbihim wala khawfun ʿalayhim wala hum yahzanoona

    Waɗanda suke ciyar da dũkiyõyinsu a cikin hanyar Allah, sa'an nan kuma bã su biyar wa abin da suka ciyar ɗin da gõri, ko cũta, suna da sakamakonsu a wurin ubangijinsu, kuma bãbu tsõro a kansu, kuma ba su zama suna baƙin ciki ba.

  263. ۞ قَوْلٌ مَّعْرُوفٌ وَمَغْفِرَةٌ خَيْرٌ مِّن صَدَقَةٍ يَتْبَعُهَآ أَذًى ۗ وَٱللَّهُ غَنِىٌّ حَلِيمٌ۝٢٦٣

    Qawlun maʿroofun wamaghfiratun khayrun min sadaqatin yatbaʿuha athan waAllahu ghaniyyun haleemun

    Magana mai kyau da gãfartawa su ne mafi alhẽri daga sadaka wadda wata cũtarwa take biyar ta. Kuma Allah Wadatacce ne, Mai haƙuri.

  264. يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ لَا تُبْطِلُوا۟ صَدَقَـٰتِكُم بِٱلْمَنِّ وَٱلْأَذَىٰ كَٱلَّذِى يُنفِقُ مَالَهُۥ رِئَآءَ ٱلنَّاسِ وَلَا يُؤْمِنُ بِٱللَّهِ وَٱلْيَوْمِ ٱلْـَٔاخِرِ ۖ فَمَثَلُهُۥ كَمَثَلِ صَفْوَانٍ عَلَيْهِ تُرَابٌ فَأَصَابَهُۥ وَابِلٌ فَتَرَكَهُۥ صَلْدًا ۖ لَّا يَقْدِرُونَ عَلَىٰ شَىْءٍ مِّمَّا كَسَبُوا۟ ۗ وَٱللَّهُ لَا يَهْدِى ٱلْقَوْمَ ٱلْكَـٰفِرِينَ۝٢٦٤

    Ya ayyuha allatheena amanoo la tubtiloo sadaqatikum bialmanni waalatha kaallathee yunfiqu malahu riaa alnnasi wala yuminu biAllahi waalyawmi alakhiri famathaluhu kamathali safwanin ʿalayhi turabun faasabahu wabilun fatarakahu saldan la yaqdiroona ʿala shayin mimma kasaboo waAllahu la yahdee alqawma alkafireena

    Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku ɓãta sadakõkinku da gõri da cũtarwa, kamar wanda yake ciyar da dũkiyarsa dõmin nũna wa mutãne, kuma bã ya yin ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. To, abin da yake misãlinsa, kamar falalen dũtse ne, a kansa akwai turɓãya, sai wãbilin hadari1 ya sãme shi, sai ya bar shi ƙanƙara. Bã su iya amfani da kõme daga abin da suka sanã'anta. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutãne kãfirai.

    Bayanai
    [1] 'Wabilin hadari' wãtau ruwan sama kamar da bakin ƙwarya.
  265. وَمَثَلُ ٱلَّذِينَ يُنفِقُونَ أَمْوَٰلَهُمُ ٱبْتِغَآءَ مَرْضَاتِ ٱللَّهِ وَتَثْبِيتًا مِّنْ أَنفُسِهِمْ كَمَثَلِ جَنَّةٍۭ بِرَبْوَةٍ أَصَابَهَا وَابِلٌ فَـَٔاتَتْ أُكُلَهَا ضِعْفَيْنِ فَإِن لَّمْ يُصِبْهَا وَابِلٌ فَطَلٌّ ۗ وَٱللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِيرٌ۝٢٦٥

    Wamathalu allatheena yunfiqoona amwalahumu ibtighaa mardati Allahi watathbeetan min anfusihim kamathali jannatin birabwatin asabaha wabilun faatat okulaha diʿfayni fain lam yusibha wabilun fatallun waAllahu bima taʿmaloona baseerun

    Kuma sifar waɗanda suke ciyar da dũkiyarsu dõmin nẽman yardõjin Allah, kuma da tabbatarwa daga kansu, kamar misãlin lambu ne a jigãwa wadda wãbilin hadari ya sãmu, sai ta bãyar da amfãninta ninki biyu To, idan wãbili bai sãme ta ba, sai yayyafi (ya ishe ta). Kuma Allah ga abin da kuke aikatawa Mai gani ne.

  266. أَيَوَدُّ أَحَدُكُمْ أَن تَكُونَ لَهُۥ جَنَّةٌ مِّن نَّخِيلٍ وَأَعْنَابٍ تَجْرِى مِن تَحْتِهَا ٱلْأَنْهَـٰرُ لَهُۥ فِيهَا مِن كُلِّ ٱلثَّمَرَٰتِ وَأَصَابَهُ ٱلْكِبَرُ وَلَهُۥ ذُرِّيَّةٌ ضُعَفَآءُ فَأَصَابَهَآ إِعْصَارٌ فِيهِ نَارٌ فَٱحْتَرَقَتْ ۗ كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ ٱللَّهُ لَكُمُ ٱلْـَٔايَـٰتِ لَعَلَّكُمْ تَتَفَكَّرُونَ۝٢٦٦

    Ayawaddu ahadukum an takoona lahu jannatun min nakheelin waaʿnabin tajree min tahtiha alanharu lahu feeha min kulli alththamarati waasabahu alkibaru walahu thurriyyatun duʿafao faasabaha iʿsarun feehi narun faihtaraqat kathalika yubayyinu Allahu lakumu alayati laʿallakum tatafakkaroona

    Shin ɗayanku nã son cẽwa wani lambu ya kasance a gare shi daga dabĩnai da inabõbi' marẽmari suna gudãna daga ƙarƙashinsa, yana da, a cikinsa daga kõwane 'ya'yan itãce, kuma tsũfa ya sãme shi, alhãli kuwa yana da zũriyya masu rauni sai gũguwa wadda take a cikinta akwai wuta, ta sãme shi, har ta ƙõne? Kamar wancan ne Allah Yana bayyanãwar ãyõyi a gare ku, tsammãninku kuna tunãni.

  267. يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓا۟ أَنفِقُوا۟ مِن طَيِّبَـٰتِ مَا كَسَبْتُمْ وَمِمَّآ أَخْرَجْنَا لَكُم مِّنَ ٱلْأَرْضِ ۖ وَلَا تَيَمَّمُوا۟ ٱلْخَبِيثَ مِنْهُ تُنفِقُونَ وَلَسْتُم بِـَٔاخِذِيهِ إِلَّآ أَن تُغْمِضُوا۟ فِيهِ ۚ وَٱعْلَمُوٓا۟ أَنَّ ٱللَّهَ غَنِىٌّ حَمِيدٌ۝٢٦٧

    Ya ayyuha allatheena amanoo anfiqoo min tayyibati ma kasabtum wamimma akhrajna lakum mina alardi wala tayammamoo alkhabeetha minhu tunfiqoona walastum biakhitheehi illa an tughmidoo feehi waiʿlamoo anna Allaha ghaniyyun hameedun

    Ya ku waɗan da suka yi ĩmãni! Ku ciyar daga mai kyaun abin da kuka sanã'anta, kuma daga abin da Muka fitar sabõda ku daga ƙasa, kuma kada ku yi nufin mummuna ya zama daga gare shi ne kuke ciyarwa, alhãli kuwa ba ku zama mãsu karɓarsa ba fãce kun runtse ido a cikin sa. Kuma ku sani cẽwa lalle ne, Allah Mawadãci ne, Gõdadde.

  268. ٱلشَّيْطَـٰنُ يَعِدُكُمُ ٱلْفَقْرَ وَيَأْمُرُكُم بِٱلْفَحْشَآءِ ۖ وَٱللَّهُ يَعِدُكُم مَّغْفِرَةً مِّنْهُ وَفَضْلًا ۗ وَٱللَّهُ وَٰسِعٌ عَلِيمٌ۝٢٦٨

    Alshshaytanu yaʿidukumu alfaqra wayamurukum bialfahshai waAllahu yaʿidukum maghfiratan minhu wafadlan waAllahu wasiʿun ʿaleemun

    Shaiɗan yana yi muku alƙawarin talauci, kuma yana umurnin ku da alfasha1, kuma Allah Yana yi muku alƙawarin gãfara daga gare shi da ƙãri, kuma Allah Mawadãci ne, Masani.

    Bayanai
    [1] Alfãsha ita ce ayyukan zunubi kamar zina da shan giya, alhãli ɓatar da dũkiya a nan, ya fi tsanani, kuma bãbu wani badali don sakamako, sabõda haka ƙin ciyarwa dõmin gudun talauci da umurninku da alfãsha sun sãɓã wa jũna, ga abin da shi Shaiɗan yake gaya muku; watau kada ku ciyar, dõmin gudun talauci, amma ku sha giya, ku yi zina!.
  269. يُؤْتِى ٱلْحِكْمَةَ مَن يَشَآءُ ۚ وَمَن يُؤْتَ ٱلْحِكْمَةَ فَقَدْ أُوتِىَ خَيْرًا كَثِيرًا ۗ وَمَا يَذَّكَّرُ إِلَّآ أُو۟لُوا۟ ٱلْأَلْبَـٰبِ۝٢٦٩

    Yutee alhikmata man yashao waman yuta alhikmata faqad ootiya khayran katheeran wama yaththakkaru illa oloo alalbabi

    Yana bãyar da hikima (ga fahimtar gaskiyar abubuwa) ga wanda Yake so. Kuma wanda aka bai wa hikima to lalle ne an bã shi alhẽri mai yawa. Kuma bãbu mai tunãni fãce ma'abuta hankula.

  270. وَمَآ أَنفَقْتُم مِّن نَّفَقَةٍ أَوْ نَذَرْتُم مِّن نَّذْرٍ فَإِنَّ ٱللَّهَ يَعْلَمُهُۥ ۗ وَمَا لِلظَّـٰلِمِينَ مِنْ أَنصَارٍ۝٢٧٠

    Wama anfaqtum min nafaqatin aw nathartum min nathrin fainna Allaha yaʿlamuhu wama lilththalimeena min ansarin

    Kuma abin da kuka ciyar daga ciyarwa, kõ kuka cika alwãshi daga wani bãkance, to, lalle ne, Allah Yana sanin sa. Kuma azzãlumai bã su da wasu mataimaka.

  271. إِن تُبْدُوا۟ ٱلصَّدَقَـٰتِ فَنِعِمَّا هِىَ ۖ وَإِن تُخْفُوهَا وَتُؤْتُوهَا ٱلْفُقَرَآءَ فَهُوَ خَيْرٌ لَّكُمْ ۚ وَيُكَفِّرُ عَنكُم مِّن سَيِّـَٔاتِكُمْ ۗ وَٱللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرٌ۝٢٧١

    In tubdoo alssadaqati faniʿimma hiya wain tukhfooha watutooha alfuqaraa fahuwa khayrun lakum wayukaffiru ʿankum min sayyiatikum waAllahu bima taʿmaloona khabeerun

    Idan kun nũna sadakõki to, yana da kyau ƙwarai kuma idan kuka ɓõye su kuma kuka je da su ga matalauta, to shi ne mafi alhẽri a gareku, kuma Yana kankarẽwa, daga barinku, daga miyãgun ayyukanku. Kuma Allah ga abin da kuke aikatawa Masani ne.

  272. ۞ لَّيْسَ عَلَيْكَ هُدَىٰهُمْ وَلَـٰكِنَّ ٱللَّهَ يَهْدِى مَن يَشَآءُ ۗ وَمَا تُنفِقُوا۟ مِنْ خَيْرٍ فَلِأَنفُسِكُمْ ۚ وَمَا تُنفِقُونَ إِلَّا ٱبْتِغَآءَ وَجْهِ ٱللَّهِ ۚ وَمَا تُنفِقُوا۟ مِنْ خَيْرٍ يُوَفَّ إِلَيْكُمْ وَأَنتُمْ لَا تُظْلَمُونَ۝٢٧٢

    Laysa ʿalayka hudahum walakinna Allaha yahdee man yashao wama tunfiqoo min khayrin falianfusikum wama tunfiqoona illa ibtighaa wajhi Allahi wama tunfiqoo min khayrin yuwaffa ilaykum waantum la tuthlamoona

    Shiryar da su bã ya a kanka, kuma amma Allah Shi ne Yake shiryar da wanda Yake so, kuma abin da kuka ciyar daga alhẽri, to, dõmin kanku ne, kuma bã ku ciyarwa, fãce dõmin nẽman yardar Allah, kuma abin da kuke ciyarwa daga alhẽri zã a cika lãdarsa zuwa gare ku, alhãli kuwa kũ bã a zãluntarku.

  273. لِلْفُقَرَآءِ ٱلَّذِينَ أُحْصِرُوا۟ فِى سَبِيلِ ٱللَّهِ لَا يَسْتَطِيعُونَ ضَرْبًا فِى ٱلْأَرْضِ يَحْسَبُهُمُ ٱلْجَاهِلُ أَغْنِيَآءَ مِنَ ٱلتَّعَفُّفِ تَعْرِفُهُم بِسِيمَـٰهُمْ لَا يَسْـَٔلُونَ ٱلنَّاسَ إِلْحَافًا ۗ وَمَا تُنفِقُوا۟ مِنْ خَيْرٍ فَإِنَّ ٱللَّهَ بِهِۦ عَلِيمٌ۝٢٧٣

    Lilfuqarai allatheena ohsiroo fee sabeeli Allahi la yastateeʿoona darban fee alardi yahsabuhumu aljahilu aghniyaa mina alttaʿaffufi taʿrifuhum biseemahum la yasaloona alnnasa ilhafan wama tunfiqoo min khayrin fainna Allaha bihi ʿaleemun

    (Ciyarwar a yĩ ta) ga matalautan1 nan waɗanda aka tsare a cikin hanyar Allah, ba su iya tafiyar fatauci a cikin ƙasa, jãhilin hãlinsu yana zaton su wadãtattu sabõda kãmun kai kana sanin su da alãmarsu, ba su rõƙon mutãne da nãcẽwa. Kuma abin da kuka ciyar daga alhẽri, to, lalle Allah gare shi Masani ne.

    Bayanai
    [1] Matalautan nan 'muhãjiruna'ne waɗanda suka bar dũkiyarsu da iyãlansu dõmin hijira. Kuma ba su sãmi wata matãka ba a Madĩna, sai aka yi musu rumfuna, sunã kwãna a ciki, suka tsare kansu dõmin jihãdi da yãƙi da karãtun Alƙur'ãni da ibãda kamar matsayin sõja a yanzu. Sũ wajen ɗari huɗu ne, shugabansu, shi ne Abdur Rahman bn Sakhar Abu Huraira el Dawsy.
  274. ٱلَّذِينَ يُنفِقُونَ أَمْوَٰلَهُم بِٱلَّيْلِ وَٱلنَّهَارِ سِرًّا وَعَلَانِيَةً فَلَهُمْ أَجْرُهُمْ عِندَ رَبِّهِمْ وَلَا خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلَا هُمْ يَحْزَنُونَ۝٢٧٤

    Allatheena yunfiqoona amwalahum biallayli waalnnahari sirran waʿalaniyatan falahum ajruhum ʿinda rabbihim wala khawfun ʿalayhim wala hum yahzanoona

    Waɗanda suke ciyar da dukiyõyinsu, a dare da yini, ɓõye da bayyane, to suna da sakamakonsu a wurin Ubangijinsu. Kuma bãbu tsõro a kansu, kuma ba su zama suna baƙin ciki ba.

  275. ٱلَّذِينَ يَأْكُلُونَ ٱلرِّبَوٰا۟ لَا يَقُومُونَ إِلَّا كَمَا يَقُومُ ٱلَّذِى يَتَخَبَّطُهُ ٱلشَّيْطَـٰنُ مِنَ ٱلْمَسِّ ۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمْ قَالُوٓا۟ إِنَّمَا ٱلْبَيْعُ مِثْلُ ٱلرِّبَوٰا۟ ۗ وَأَحَلَّ ٱللَّهُ ٱلْبَيْعَ وَحَرَّمَ ٱلرِّبَوٰا۟ ۚ فَمَن جَآءَهُۥ مَوْعِظَةٌ مِّن رَّبِّهِۦ فَٱنتَهَىٰ فَلَهُۥ مَا سَلَفَ وَأَمْرُهُۥٓ إِلَى ٱللَّهِ ۖ وَمَنْ عَادَ فَأُو۟لَـٰٓئِكَ أَصْحَـٰبُ ٱلنَّارِ ۖ هُمْ فِيهَا خَـٰلِدُونَ۝٢٧٥

    Allatheena yakuloona alrriba la yaqoomoona illa kama yaqoomu allathee yatakhabbatuhu alshshaytanu mina almassi thalika biannahum qaloo innama albayʿu mithlu alrriba waahalla Allahu albayʿa waharrama alrriba faman jaahu mawʿithatun min rabbihi faintaha falahu ma salafa waamruhu ila Allahi waman ʿada faolaika ashabu alnnari hum feeha khalidoona

    Wadanda suke cin ribã1 ba su tashi, fãce kamar yadda wanda da Shaiɗan yake ɗimautarwa daga shafa yake tashi. Wancan, dõmin lalle ne sun ce: "Ciniki kamar riba yake."Kuma Allah Ya halatta ciniki kuma Ya haramta riba. To, wanda wa'azi daga Ubangijinsa, ya je masa, sa'an nan ya hanu, to yana da abin da ya shige, kuma al'amarinsa (ana wakkala shi) zuwa ga Allah. Kuma wanda ya kõma, to, waɗannan sũ ne abõkan Wuta, sũ a cikinta madawwama ne.

    Bayanai
    [1] Ribã ita ce ƙãri ga adadi koga lõkaci. Amma ƙãrin adadi shi ne ƙãri a cikin mu'ãmala da zinãri da azurfa da abũbuwan ci ga rayuwa. Yana haramta ga jinsi guda kawai, kuma ana sharɗantawa ga abinci ya zama abinci kõ abin gyaransa, kuma anã iya ajiye shi, ban da 'ya'yan itãcen marmari da duma da ruwa. Amma ga jinkiri an hana riba muɗlaƙan. kõ dã ga 'ya'yan itãcen marmari. Takardun kuɗi kamar sil'õ'i suke dõmin haka ƙimarsu tana hawa kuma tanã sauka. Har yanzu malamai ba su yanke hukunci a kansu ba sõsai. Annabi, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Ka bar abin da yake sanya maka shakka zuwa ga wanda ba ya sanya maka shakka.".
  276. يَمْحَقُ ٱللَّهُ ٱلرِّبَوٰا۟ وَيُرْبِى ٱلصَّدَقَـٰتِ ۗ وَٱللَّهُ لَا يُحِبُّ كُلَّ كَفَّارٍ أَثِيمٍ۝٢٧٦

    Yamhaqu Allahu alrriba wayurbee alssadaqati waAllahu la yuhibbu kulla kaffarin atheemin

    Allah Yana shãfe albarkar riba, kuma Yana ƙãra sadakõki. Kuma Allah bã Ya son dukan mai yawan kãfirci, mai yawan zunubi.

  277. إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ وَأَقَامُوا۟ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتَوُا۟ ٱلزَّكَوٰةَ لَهُمْ أَجْرُهُمْ عِندَ رَبِّهِمْ وَلَا خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلَا هُمْ يَحْزَنُونَ۝٢٧٧

    Inna allatheena amanoo waʿamiloo alssalihati waaqamoo alssalata waatawoo alzzakata lahum ajruhum ʿinda rabbihim wala khawfun ʿalayhim wala hum yahzanoona

    Lalle ne, waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka tsayar da salla, kuma suka bãyar da zakka, suna da sakamakonsu a wurin Ubangijinsu, kuma bãbu tsõro a kansu, kuma ba su zama suna yin baƙin ciki ba.

  278. يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ ٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَذَرُوا۟ مَا بَقِىَ مِنَ ٱلرِّبَوٰٓا۟ إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ۝٢٧٨

    Ya ayyuha allatheena amanoo ittaqoo Allaha watharoo ma baqiya mina alrriba in kuntum mumineena

    Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa kuma ku bar abin da ya rage daga riba, idan kun kasance mãsu ĩmãni.

  279. فَإِن لَّمْ تَفْعَلُوا۟ فَأْذَنُوا۟ بِحَرْبٍ مِّنَ ٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ ۖ وَإِن تُبْتُمْ فَلَكُمْ رُءُوسُ أَمْوَٰلِكُمْ لَا تَظْلِمُونَ وَلَا تُظْلَمُونَ۝٢٧٩

    Fain lam tafʿaloo fathanoo biharbin mina Allahi warasoolihi wain tubtum falakum ruoosu amwalikum la tathlimoona wala tuthlamoona

    To, idan ba ku aikata ba to, ku sani fa da akwai yãƙi daga Allah da ManzonSa. Kuma idan kun tũba to kuna da asalin dũkiyõyinku, bã ku zãlunta, kuma bã a zãluntar ku.

  280. وَإِن كَانَ ذُو عُسْرَةٍ فَنَظِرَةٌ إِلَىٰ مَيْسَرَةٍ ۚ وَأَن تَصَدَّقُوا۟ خَيْرٌ لَّكُمْ ۖ إِن كُنتُمْ تَعْلَمُونَ۝٢٨٠

    Wain kana thoo ʿusratin fanathiratun ila maysaratin waan tasaddaqoo khayrun lakum in kuntum taʿlamoona

    Kuma idan ma'abucin wahala ya kasance (mawahalci) to, jinkirtãwa ake yi zuwa ga sauƙin al'amarinsa, kuma dã kun yi sadaka, shi ne mafi alhẽri a gare ku, idan kun kasance kuna sani.

  281. وَٱتَّقُوا۟ يَوْمًا تُرْجَعُونَ فِيهِ إِلَى ٱللَّهِ ۖ ثُمَّ تُوَفَّىٰ كُلُّ نَفْسٍ مَّا كَسَبَتْ وَهُمْ لَا يُظْلَمُونَ۝٢٨١

    Waittaqoo yawman turjaʿoona feehi ila Allahi thumma tuwaffa kullu nafsin ma kasabat wahum la yuthlamoona

    Kuma ku ji tsõron wani yini wanda ake mayar da ku a cikinsa zuwa ga Allah, sa'an nan kuma a cika wa kõwane rai abin da ya sanã'anta, kuma sũ bã a zãluntar su.

  282. يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓا۟ إِذَا تَدَايَنتُم بِدَيْنٍ إِلَىٰٓ أَجَلٍ مُّسَمًّى فَٱكْتُبُوهُ ۚ وَلْيَكْتُب بَّيْنَكُمْ كَاتِبٌۢ بِٱلْعَدْلِ ۚ وَلَا يَأْبَ كَاتِبٌ أَن يَكْتُبَ كَمَا عَلَّمَهُ ٱللَّهُ ۚ فَلْيَكْتُبْ وَلْيُمْلِلِ ٱلَّذِى عَلَيْهِ ٱلْحَقُّ وَلْيَتَّقِ ٱللَّهَ رَبَّهُۥ وَلَا يَبْخَسْ مِنْهُ شَيْـًٔا ۚ فَإِن كَانَ ٱلَّذِى عَلَيْهِ ٱلْحَقُّ سَفِيهًا أَوْ ضَعِيفًا أَوْ لَا يَسْتَطِيعُ أَن يُمِلَّ هُوَ فَلْيُمْلِلْ وَلِيُّهُۥ بِٱلْعَدْلِ ۚ وَٱسْتَشْهِدُوا۟ شَهِيدَيْنِ مِن رِّجَالِكُمْ ۖ فَإِن لَّمْ يَكُونَا رَجُلَيْنِ فَرَجُلٌ وَٱمْرَأَتَانِ مِمَّن تَرْضَوْنَ مِنَ ٱلشُّهَدَآءِ أَن تَضِلَّ إِحْدَىٰهُمَا فَتُذَكِّرَ إِحْدَىٰهُمَا ٱلْأُخْرَىٰ ۚ وَلَا يَأْبَ ٱلشُّهَدَآءُ إِذَا مَا دُعُوا۟ ۚ وَلَا تَسْـَٔمُوٓا۟ أَن تَكْتُبُوهُ صَغِيرًا أَوْ كَبِيرًا إِلَىٰٓ أَجَلِهِۦ ۚ ذَٰلِكُمْ أَقْسَطُ عِندَ ٱللَّهِ وَأَقْوَمُ لِلشَّهَـٰدَةِ وَأَدْنَىٰٓ أَلَّا تَرْتَابُوٓا۟ ۖ إِلَّآ أَن تَكُونَ تِجَـٰرَةً حَاضِرَةً تُدِيرُونَهَا بَيْنَكُمْ فَلَيْسَ عَلَيْكُمْ جُنَاحٌ أَلَّا تَكْتُبُوهَا ۗ وَأَشْهِدُوٓا۟ إِذَا تَبَايَعْتُمْ ۚ وَلَا يُضَآرَّ كَاتِبٌ وَلَا شَهِيدٌ ۚ وَإِن تَفْعَلُوا۟ فَإِنَّهُۥ فُسُوقٌۢ بِكُمْ ۗ وَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ ۖ وَيُعَلِّمُكُمُ ٱللَّهُ ۗ وَٱللَّهُ بِكُلِّ شَىْءٍ عَلِيمٌ۝٢٨٢

    Ya ayyuha allatheena amanoo itha tadayantum bidaynin ila ajalin musamman faoktuboohu walyaktub baynakum katibun bialʿadli wala yaba katibun an yaktuba kama ʿallamahu Allahu falyaktub walyumlili allathee ʿalayhi alhaqqu walyattaqi Allaha rabbahu wala yabkhas minhu shayan fain kana allathee ʿalayhi alhaqqu safeehan aw daʿeefan aw la yastateeʿu an yumilla huwa falyumlil waliyyuhu bialʿadli waistashhidoo shaheedayni min rijalikum fain lam yakoona rajulayni farajulun waimraatani mimman tardawna mina alshshuhadai an tadilla ihdahuma fatuthakkira ihdahuma alokhra wala yaba alshshuhadao itha ma duʿoo wala tasamoo an taktuboohu sagheeran aw kabeeran ila ajalihi thalikum aqsatu ʿinda Allahi waaqwamu lilshshahadati waadna alla tartaboo illa an takoona tijaratan hadiratan tudeeroonaha baynakum falaysa ʿalaykum junahun alla taktubooha waashhidoo itha tabayaʿtum wala yudarra katibun wala shaheedun wain tafʿaloo fainnahu fusooqun bikum waittaqoo Allaha wayuʿallimukumu Allahu waAllahu bikulli shayin ʿaleemun

    Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun yi mu'ãmalar bãyar da bãshi zuwa ga wani ajali ambatacce, sai ku rubũta shi. Kuma wani marubuci ya yi rubũtu a tsakaninku da ãdalci. Kuma kada marubũci ya ki rubũtãwa, kamar yadda Allah Ya sanar da shi, sai ya rubũta. Kuma wanda bãshin yake a kansa sai ya yi shibta, kuma ya ji tsõron Allah, Ubangijinsa, da taƙawa, kuma kada ya rage wani abu daga gare shi. To, idan wanda bãshin yake a kansa yã kasance wãwã ne kõ kuwa rarrauna, kõ kuwa shi bã ya iya shibta, to, sai waliyyinsa ya yi shibtar da ãdalci. Kuma ku shaidar da shaidu biyu daga mazanku, to, idan ba su zama maza biyu ba, to, namiji guda da mãtã biyu, daga waɗanda kuke yarda da su daga shaidun dõmin mantuwar ɗayansu, sai gudarsu ta mazãkũtar1 da ɗayar. Kuma kada shaidun su ƙi, idan an kira su. Kuma kada ku ƙõsa ga rubũta shi, ƙarami ya kasance kõ babba, zuwa ajalinsa. Wancan ne mafi ãdalci a wurin Allah kuma mafi tsayuwa ga shaida, kuma mafi kusa ga rashin shakkarku. Sai idan ya kasance fatauci ne halartacce wanda kuke gẽwayarwa da shi hannu da hannu a tsakãninku to bãbu laifi a kanku, ya zama ba ku rubũta shi ba. Kuma ku shaidar idan kun yi sayayya. Kuma kada a wahalarda marubuci, kuma kada a wahalar da shaidu kuma idan kun aikata to, lalle ne, shi fãsiƙanci ne game da ku. Kumaku bi Allah da takƙawa, kuma Allah Ya sanar da ku. Kuma Allah ga dukan kõme Masani ne.

    Bayanai
    [1] Watau mãta biyu su zama kamar namiji guda ga bãyar da shaida. Kuma ana fassara shi da "ta tunãtar da ɗayar".
  283. ۞ وَإِن كُنتُمْ عَلَىٰ سَفَرٍ وَلَمْ تَجِدُوا۟ كَاتِبًا فَرِهَـٰنٌ مَّقْبُوضَةٌ ۖ فَإِنْ أَمِنَ بَعْضُكُم بَعْضًا فَلْيُؤَدِّ ٱلَّذِى ٱؤْتُمِنَ أَمَـٰنَتَهُۥ وَلْيَتَّقِ ٱللَّهَ رَبَّهُۥ ۗ وَلَا تَكْتُمُوا۟ ٱلشَّهَـٰدَةَ ۚ وَمَن يَكْتُمْهَا فَإِنَّهُۥٓ ءَاثِمٌ قَلْبُهُۥ ۗ وَٱللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ عَلِيمٌ۝٢٨٣

    Wain kuntum ʿala safarin walam tajidoo katiban farihanun maqboodatun fain amina baʿdukum baʿdan falyuaddi allathee itumina amanatahu walyattaqi Allaha rabbahu wala taktumoo alshshahadata waman yaktumha fainnahu athimun qalbuhu waAllahu bima taʿmaloona ʿaleemun

    Kuma idan kun kasance a kan tafiya, kuma ba ku sami marubũci ba, to, a bãyar da jingina karɓaɓɓiya (ga hannu). To, idan sãshenku ya amince wa sãshe, to, wanda aka amincẽ wannan sai ya bãyar da amãnarsa, kuma ya bi Allah, Ubangijinsa, da taƙawa. Kuma kada ku ɓõye shaida, kuma wanda ya ɓõye ta, to, shi mai zunubin zũciyarsa ne. KumaAllah ga abin da kuke aikatãwa Masani ne.

  284. لِّلَّهِ مَا فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَمَا فِى ٱلْأَرْضِ ۗ وَإِن تُبْدُوا۟ مَا فِىٓ أَنفُسِكُمْ أَوْ تُخْفُوهُ يُحَاسِبْكُم بِهِ ٱللَّهُ ۖ فَيَغْفِرُ لِمَن يَشَآءُ وَيُعَذِّبُ مَن يَشَآءُ ۗ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍ قَدِيرٌ۝٢٨٤

    Lillahi ma fee alssamawati wama fee alardi wain tubdoo ma fee anfusikum aw tukhfoohu yuhasibkum bihi Allahu fayaghfiru liman yashao wayuʿaththibu man yashao waAllahu ʿala kulli shayin qadeerun

    Allah ne, da abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa, kuma idan kun bayyana abin da yake a cikin zukatanku (na shaida), ko kuka ɓõye shi, Allah zai bincike ku da shi, sa'an nan Ya yi gãfara ga wanda Yake so, kuma Ya azabta wanda Yake so. Kuma Allah a kan dukan kõme Mai ĩkon yi ne.1

    Bayanai
    [1] Wannan ãyã ita ce ƙarshen bayãni a kan bãyar da shaida. A kan shaidar da mutum ya bayyana kõ ya ɓõye a cikin rai, Allah Yake yi masa bincike dõmin hakkin wani da ya rãtaya a kan wannan bayyanawar kõ ɓõyewar. Ita ayar da biyu na bayanta sun ƙunshi ilmin Baƙara dukanta.
  285. ءَامَنَ ٱلرَّسُولُ بِمَآ أُنزِلَ إِلَيْهِ مِن رَّبِّهِۦ وَٱلْمُؤْمِنُونَ ۚ كُلٌّ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَمَلَـٰٓئِكَتِهِۦ وَكُتُبِهِۦ وَرُسُلِهِۦ لَا نُفَرِّقُ بَيْنَ أَحَدٍ مِّن رُّسُلِهِۦ ۚ وَقَالُوا۟ سَمِعْنَا وَأَطَعْنَا ۖ غُفْرَانَكَ رَبَّنَا وَإِلَيْكَ ٱلْمَصِيرُ۝٢٨٥

    Amana alrrasoolu bima onzila ilayhi min rabbihi waalmuminoona kullun amana biAllahi wamalaikatihi wakutubihi warusulihi la nufarriqu bayna ahadin min rusulihi waqaloo samiʿna waataʿna ghufranaka rabbana wailayka almaseeru

    Manzon Allah yã yi ĩmãni da abin da aka saukar zuwa gare shi daga Ubangijinsa, da mũminai. Kõwanensu yã yi ĩmãni da Allah, da mala'ikunSa, da littattafanSa, da manzanninSa. Bã mu rarrabẽwa a tsakãnin daya daga manzanninSa. Kuma (mũminai) suka ce: "Mun ji kuma mun yi dã'a; (Muna nẽman) gãfararKa, yã Ubangijinmu, kuma zuwa a gare Ka makõma take1 "

    Bayanai
    [1] Aya ta 285 da ta 286 sun ƙunshi aikin Annabi da waɗanda suka bi shi daga aƙida da magana da aiki da kyautatãwa da mayar da al'amari ga Allah, da addu'ar tsari da nema daga Ubangijinsu. Aya ta 286 ita ce mafi kyaun addu'a. Kuma ta nũna Musulmi sun sãɓa wa Yahũdãwa mãsu cewa 'Mun ji, munƙi!'.
  286. لَا يُكَلِّفُ ٱللَّهُ نَفْسًا إِلَّا وُسْعَهَا ۚ لَهَا مَا كَسَبَتْ وَعَلَيْهَا مَا ٱكْتَسَبَتْ ۗ رَبَّنَا لَا تُؤَاخِذْنَآ إِن نَّسِينَآ أَوْ أَخْطَأْنَا ۚ رَبَّنَا وَلَا تَحْمِلْ عَلَيْنَآ إِصْرًا كَمَا حَمَلْتَهُۥ عَلَى ٱلَّذِينَ مِن قَبْلِنَا ۚ رَبَّنَا وَلَا تُحَمِّلْنَا مَا لَا طَاقَةَ لَنَا بِهِۦ ۖ وَٱعْفُ عَنَّا وَٱغْفِرْ لَنَا وَٱرْحَمْنَآ ۚ أَنتَ مَوْلَىٰنَا فَٱنصُرْنَا عَلَى ٱلْقَوْمِ ٱلْكَـٰفِرِينَ۝٢٨٦

    La yukallifu Allahu nafsan illa wusʿaha laha ma kasabat waʿalayha ma iktasabat rabbana la tuakhithna in naseena aw akhtana rabbana wala tahmil ʿalayna isran kama hamaltahu ʿala allatheena min qablina rabbana wala tuhammilna ma la taqata lana bihi waoʿfu ʿanna waighfir lana wairhamna anta mawlana faonsurna ʿala alqawmi alkafireena

    Allah ba Ya kallafa wa rai fãce ikon yinsa, yana da lãdar abin da ya tsirfanta, kuma a kansa akwai zunubin abin da ya yi ta aikatãwa: "Yã Ubangijinmu! Kada Ka kãmã mu, idan mun yi mantuwa, ko kuma mun yi kuskure. Yã Ubangijinmu! Kuma kada Ka aza nauyi a kanmu, kamar yadda Ka aza shi a kan waɗanda suke a gabãninmu. Yã Ubangijinmu! Kada Ka sanya mu ɗaukar abin da bãbu ĩko gare mu da shi. Kuma Ka yãfe daga gare mu, kuma Ka gãfarta mana, kuma Ka yi jin ƙai gare mu. Kai ne Majibincinmu, sabõda haka Ka taimake mu a kan mutãnen nan kãfirai."

Tambayoyin da ake yawan yi

Mece ce ma’anar sunan Suratul Baƙara?

Ma’anar Baƙara ita ce “Saniya”.

Suratul Baƙara tana cikin juz’i na nawa?

Suratul Baƙara tana cikin juz’i na 1, 2 da 3.

Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Baƙara?

Suratul Baƙara tana da ayoyi 286.

Suratul Baƙara Makkiya ce ko Madaniya?

Suratul Baƙara sura ce Madaniya.

Suratul Baƙara ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?

Ita ce sura ta 2 a cikin Alƙur’ani.

Majiyoyi

  • Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
  • Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
  • Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
  • Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
  • Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
  • Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.

Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.

Saitunan karatu

Rubutun Alƙur’ani
Girman Larabci
100%
Girman fassara
100%
Kamanni

Ƙara zuwa Allon Gida

ReadSurahBuɗe ReadSurah daga allon gida, a cikakken allo. Surorin da kuka karanta suna buɗewa ko da babu intanet.

  1. A cikin Safari, taɓa maɓallin “Share”. A sababbin iPhone yana cikin menu na •••.
  2. Taɓa “Add to Home Screen”. Gungura ƙasa idan ba ku gan shi ba.
  3. Taɓa “Add”.