سورة الواقعة
Suratul Waƙi’a da fassarar Hausa
Mai aukuwa
- 56
- ayoyi 96
- Makkiya
- Juz’i 27
- Shafuka 534–537
Suratul Waƙi’a (الواقعة) ita ce sura ta 56 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 96. Ma’anar sunanta ita ce “Mai aukuwa”. Sura ce Makkiya, wadda ta sauka a Makka kafin Hijira, kuma tana cikin juz’i na 27.
A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Waƙi’a gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.
Suratul Waƙi’a cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ
-
إِذَا وَقَعَتِ ٱلْوَاقِعَةُ١
Itha waqaʿati alwaqiʿatu
Idan mai aukuwa ta auku.
-
لَيْسَ لِوَقْعَتِهَا كَاذِبَةٌ٢
Laysa liwaqʿatiha kathibatun
Bãbu wani (rai) mai ƙaryatãwa ga aukuwarta.
-
خَافِضَةٌ رَّافِعَةٌ٣
Khafidatun rafiʿatun
(Ita) mai ƙasƙantãwa ce, mai ɗaukakãwa.
-
إِذَا رُجَّتِ ٱلْأَرْضُ رَجًّا٤
Itha rujjati alardu rajjan
Idan aka girgiza ƙasã girgizwa.
-
وَبُسَّتِ ٱلْجِبَالُ بَسًّا٥
Wabussati aljibalu bassan
Kuma aka niƙe duwãtsu, niƙẽwa.
-
فَكَانَتْ هَبَآءً مُّنۢبَثًّا٦
Fakanat habaan munbaththan
Sai suka kasance ƙũra da ake wãtsarwa.
-
وَكُنتُمْ أَزْوَٰجًا ثَلَـٰثَةً٧
Wakuntum azwajan thalathatan
Kuma kun kasance nau'i uku.
-
فَأَصْحَـٰبُ ٱلْمَيْمَنَةِ مَآ أَصْحَـٰبُ ٱلْمَيْمَنَةِ٨
Faashabu almaymanati ma ashabu almaymanati
Watau mazõwa dãma1. Mẽne ne mazõwa dãma?
Bayanai
[1] Mazõwa dãma ko mãsu albarka waɗanda zã a baiwa takardunsu a dãma. Mazõwa hagu ko mãsu shu'umci waɗanda zã a baiwa takardunsu da hagu. -
وَأَصْحَـٰبُ ٱلْمَشْـَٔمَةِ مَآ أَصْحَـٰبُ ٱلْمَشْـَٔمَةِ٩
Waashabu almashamati ma ashabu almashamati
Da mazõwa hagu. Mẽne ne mazõwa hagu?
-
وَٱلسَّـٰبِقُونَ ٱلسَّـٰبِقُونَ١٠
Waalssabiqoona alssabiqoona
Da waɗanda suka tsẽre. Sũ wɗanda suka tsẽren nan,
-
أُو۟لَـٰٓئِكَ ٱلْمُقَرَّبُونَ١١
Olaika almuqarraboona
Waɗancan, sũ ne waɗanda aka kusantar.
-
فِى جَنَّـٰتِ ٱلنَّعِيمِ١٢
Fee jannati alnnaʿeemi
A ckin Aljannar ni'ima.
-
ثُلَّةٌ مِّنَ ٱلْأَوَّلِينَ١٣
Thullatun mina alawwaleena
Jama'a ne daga mutãnen farko.1
Bayanai
[1] Jama'a daga mutãnen farko, sũ ne Annabãwan farko da kaɗan daga cikin mutãnen ƙarshe, shi ne Annabi Muhammadu, sallallãhu alaihi wa sallama. Bã a shiga cikin wannan kashi da aiki sai dai da zãɓin Allah. Kuma an rufe ƙõfarsa. Bãbu sauran wani annabi wanda zai zo da wani addini sãbo a bãyan Annabi Muhammadu, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi. -
وَقَلِيلٌ مِّنَ ٱلْـَٔاخِرِينَ١٤
Waqaleelun mina alakhireena
Da kaɗan daga mutãnen ƙarshe.
-
عَلَىٰ سُرُرٍ مَّوْضُونَةٍ١٥
ʿAla sururin mawdoonatin
(Sunã) a kan wasu gadãje sãƙaƙƙu.
-
مُّتَّكِـِٔينَ عَلَيْهَا مُتَقَـٰبِلِينَ١٦
Muttakieena ʿalayha mutaqabileena
Sunã gincire a kansu, sunã mãsu kallon jũna.
-
يَطُوفُ عَلَيْهِمْ وِلْدَٰنٌ مُّخَلَّدُونَ١٧
Yatoofu ʿalayhim wildanun mukhalladoona
Wasu yara samãri na dindindin gẽwaya a kansu.
-
بِأَكْوَابٍ وَأَبَارِيقَ وَكَأْسٍ مِّن مَّعِينٍ١٨
Biakwabin waabareeqa wakasin min maʿeenin
Da wasu kõfuna da shantula da hinjãlai daga (giya) mai ɓuɓɓuga.
-
لَّا يُصَدَّعُونَ عَنْهَا وَلَا يُنزِفُونَ١٩
La yusaddaʿoona ʿanha wala yunzifoona
Bã a sanya musu cĩwon jirĩ sabõda ita, kuma bã su buguwa.
-
وَفَـٰكِهَةٍ مِّمَّا يَتَخَيَّرُونَ٢٠
Wafakihatin mimma yatakhayyaroona
Da wasu 'ya'yan itãcen marmari daga irin waɗanda suke zãɓe.
-
وَلَحْمِ طَيْرٍ مِّمَّا يَشْتَهُونَ٢١
Walahmi tayrin mimma yashtahoona
Da nãman tsuntsãye daga wanda suke ganin sha'awa.
-
وَحُورٌ عِينٌ٢٢
Wahoorun ʿeenun
Da wasu mãtã mãsu fararen idanu da girmansu.
-
كَأَمْثَـٰلِ ٱللُّؤْلُؤِ ٱلْمَكْنُونِ٢٣
Kaamthali allului almaknooni
Kamar misãlan lu'ulu'u wanda aka ɓõye.
-
جَزَآءًۢ بِمَا كَانُوا۟ يَعْمَلُونَ٢٤
Jazaan bima kanoo yaʿmaloona
A kan sakamakon, dõmin abin da suka kasance sunã aikatãwa.
-
لَا يَسْمَعُونَ فِيهَا لَغْوًا وَلَا تَأْثِيمًا٢٥
La yasmaʿoona feeha laghwan wala tatheeman
Bã su jin wata yãsassar magana a cikinta, kuma bã su jin sun yi laifi.
-
إِلَّا قِيلًا سَلَـٰمًا سَلَـٰمًا٢٦
Illa qeelan salaman salaman
Sai dai wata magana (mai dãɗi): Salãmun, Salãmun.
-
وَأَصْحَـٰبُ ٱلْيَمِينِ مَآ أَصْحَـٰبُ ٱلْيَمِينِ٢٧
Waashabu alyameeni ma ashabu alyameeni
Da mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma?
-
فِى سِدْرٍ مَّخْضُودٍ٢٨
Fee sidrin makhdoodin
(Sunã) a cikin itãcen magarya maras ƙaya.
-
وَطَلْحٍ مَّنضُودٍ٢٩
Watalhin mandoodin
Da wata ayaba mai yawan 'ya'ya.
-
وَظِلٍّ مَّمْدُودٍ٣٠
Wathillin mamdoodin
Da wata inuwa mĩƙaƙƙiya.
-
وَمَآءٍ مَّسْكُوبٍ٣١
Wamain maskoobin
Da wani ruwa mai gudãna.
-
وَفَـٰكِهَةٍ كَثِيرَةٍ٣٢
Wafakihatin katheeratin
Da wasu 'ya'yan itacen marmari mãsu yawa.
-
لَّا مَقْطُوعَةٍ وَلَا مَمْنُوعَةٍ٣٣
La maqtooʿatin wala mamnooʿatin
Bã su yankẽwa kuma bã a hana su.
-
وَفُرُشٍ مَّرْفُوعَةٍ٣٤
Wafurushin marfooʿatin
Da wasu shimfiɗu maɗaukaka.
-
إِنَّآ أَنشَأْنَـٰهُنَّ إِنشَآءً٣٥
Inna anshanahunna inshaan
Lalle Mũ, Mun ƙãga halittarsu ƙãgãwa.
-
فَجَعَلْنَـٰهُنَّ أَبْكَارًا٣٦
Fajaʿalnahunna abkaran
Sa'an nan Muka sanya su budurwai.
-
عُرُبًا أَتْرَابًا٣٧
ʿUruban atraban
Mãsu son mazansu, a cikin tsãrã ɗaya.
-
لِّأَصْحَـٰبِ ٱلْيَمِينِ٣٨
Liashabi alyameeni
Ga mazõwa dãma.
-
ثُلَّةٌ مِّنَ ٱلْأَوَّلِينَ٣٩
Thullatun mina alawwaleena
Wata ƙungiya ce daga mutãnen farko.
-
وَثُلَّةٌ مِّنَ ٱلْـَٔاخِرِينَ٤٠
Wathullatun mina alakhireena
Da wata ƙungiya daga mutãnen ƙarshe.
-
وَأَصْحَـٰبُ ٱلشِّمَالِ مَآ أَصْحَـٰبُ ٱلشِّمَالِ٤١
Waashabu alshshimali ma ashabu alshshimali
Mazõwa hagu, Mẽne ne mazõwa hagu?
-
فِى سَمُومٍ وَحَمِيمٍ٤٢
Fee samoomin wahameemin
Sunã a cikin wata iskar zãfi da wani ruwan zãfi.
-
وَظِلٍّ مِّن يَحْمُومٍ٤٣
Wathillin min yahmoomin
Da wata inuwa ta hayãƙi mai baƙi.
-
لَّا بَارِدٍ وَلَا كَرِيمٍ٤٤
La baridin wala kareemin
Bã mai sanyi ba, kuma bã mai wata ni'ima ba.
-
إِنَّهُمْ كَانُوا۟ قَبْلَ ذَٰلِكَ مُتْرَفِينَ٤٥
Innahum kanoo qabla thalika mutrafeena
Lalle sũ, sun kasance a gabãnin wannan waɗanda aka jiyar dãɗi.
-
وَكَانُوا۟ يُصِرُّونَ عَلَى ٱلْحِنثِ ٱلْعَظِيمِ٤٦
Wakanoo yusirroona ʿala alhinthi alʿatheemi
Kuma sun kasance sunã dõgẽwa a kan mummũnan zunubi mai girma.
-
وَكَانُوا۟ يَقُولُونَ أَئِذَا مِتْنَا وَكُنَّا تُرَابًا وَعِظَـٰمًا أَءِنَّا لَمَبْعُوثُونَ٤٧
Wakanoo yaqooloona aitha mitna wakunna turaban waʿithaman ainna lamabʿoothoona
Kuma sun kasance sunã cẽwa: "Shin idan mun mutukuma muko kasance turɓãya da ƙasũsuwa shin lalle mũ waɗanda zã a kõma rãyarwa ne haƙĩƙatan?"
-
أَوَءَابَآؤُنَا ٱلْأَوَّلُونَ٤٨
Awa abaona alawwaloona
"Shin, kuma da ubanninmu na farko?"
-
قُلْ إِنَّ ٱلْأَوَّلِينَ وَٱلْـَٔاخِرِينَ٤٩
Qul inna alawwaleena waalakhireena
Ka ce: "Lalle mutãnen farko da na ƙarshe."
-
لَمَجْمُوعُونَ إِلَىٰ مِيقَـٰتِ يَوْمٍ مَّعْلُومٍ٥٠
Lamajmooʿoona ila meeqati yawmin maʿloomin
"Tabbas, waɗanda ake tãrãwa ne a cikin wani yini sananne."
-
ثُمَّ إِنَّكُمْ أَيُّهَا ٱلضَّآلُّونَ ٱلْمُكَذِّبُونَ٥١
Thumma innakum ayyuha alddalloona almukaththiboona
"Sa'an nan lalle ku, ya kũ ɓatattu, mãsu ƙaryatãwa!"
-
لَـَٔاكِلُونَ مِن شَجَرٍ مِّن زَقُّومٍ٥٢
Laakiloona min shajarin min zaqqoomin
"Lalle mãsu cĩ ne daga wata itãciya ta zaƙƙum (ɗanyen wutã)."
-
فَمَالِـُٔونَ مِنْهَا ٱلْبُطُونَ٥٣
Famalioona minha albutoona
"Har za ku zama mãsu cika cikunna daga gare ta."
-
فَشَـٰرِبُونَ عَلَيْهِ مِنَ ٱلْحَمِيمِ٥٤
Fashariboona ʿalayhi mina alhameemi
"Sa'an nan kuma mãsu shã ne, a kan wannan abin cin, daga ruwan zãfi."
-
فَشَـٰرِبُونَ شُرْبَ ٱلْهِيمِ٥٥
Fashariboona shurba alheemi
"Ku zama mãsu shã irin shan rãƙuma mãsu ƙishirwa."
-
هَـٰذَا نُزُلُهُمْ يَوْمَ ٱلدِّينِ٥٦
Hatha nuzuluhum yawma alddeeni
Wannan ita ce liyãfarsu a rãnar sakamako.
-
نَحْنُ خَلَقْنَـٰكُمْ فَلَوْلَا تُصَدِّقُونَ٥٧
Nahnu khalaqnakum falawla tusaddiqoona
Mũ ne Muka halitta ku, to, don me bã zã ku gaskata ba?
-
أَفَرَءَيْتُم مَّا تُمْنُونَ٥٨
Afaraaytum ma tumnoona
Shin kuma kun ga abin da kuke fitarwa na maniyyi?
-
ءَأَنتُمْ تَخْلُقُونَهُۥٓ أَمْ نَحْنُ ٱلْخَـٰلِقُونَ٥٩
Aantum takhluqoonahu am nahnu alkhaliqoona
Shin kũ ne kuke halitta shi, kõ kuwa mũ ne Mãsu halittãwa?
-
نَحْنُ قَدَّرْنَا بَيْنَكُمُ ٱلْمَوْتَ وَمَا نَحْنُ بِمَسْبُوقِينَ٦٠
Nahnu qaddarna baynakumu almawta wama nahnu bimasbooqeena
Mũ ne Muka ƙaddara mutuwa a tsakãninku, kuma ba Mu zama Mãsu gajiyãwa1 ba,
Bayanai
[1] Ãyã ta 60 haɗe take da ãya ta 61 watau, bã zã Mu kãsa musanya ku da waɗansu mutãne ba su tsaya matsayinku, sa'an nan kũ kuma Mu mayar da ku wata halitta. -
عَلَىٰٓ أَن نُّبَدِّلَ أَمْثَـٰلَكُمْ وَنُنشِئَكُمْ فِى مَا لَا تَعْلَمُونَ٦١
ʿAla an nubaddila amthalakum wanunshiakum fee ma la taʿlamoona
A kan Mu musanya waɗansu (mutãne) kamarku, kuma Mu mayar da ku a cikin wata halitta da ba ku sani ba.
-
وَلَقَدْ عَلِمْتُمُ ٱلنَّشْأَةَ ٱلْأُولَىٰ فَلَوْلَا تَذَكَّرُونَ٦٢
Walaqad ʿalimtumu alnnashata aloola falawla tathakkaroona
Kuma lalle, ne haƙĩƙa, kun san halittar farko, to, don me ba zã ku yi tunãni ba?
-
أَفَرَءَيْتُم مَّا تَحْرُثُونَ٦٣
Afaraaytum ma tahruthoona
Shin, kuma kun ga abin da kũke nõmãwa?
-
ءَأَنتُمْ تَزْرَعُونَهُۥٓ أَمْ نَحْنُ ٱلزَّٰرِعُونَ٦٤
Aantum tazraʿoonahu am nahnu alzzariʿoona
Shin, kũ ne ke tsirar da shi kõ kuwa Mũ ne Mãsu tsirarwa?
-
لَوْ نَشَآءُ لَجَعَلْنَـٰهُ حُطَـٰمًا فَظَلْتُمْ تَفَكَّهُونَ٦٥
Law nashao lajaʿalnahu hutaman fathaltum tafakkahoona
Dã Munã so lalle, da Mun sanya shi bũsasshiyar ciyãwa, sai ku yini kunã mãmãkin bãƙin ciki.
-
إِنَّا لَمُغْرَمُونَ٦٦
Inna lamughramoona
(Kunã cẽwa) "Lalle haƙĩƙa an azã mana tãra!"
-
بَلْ نَحْنُ مَحْرُومُونَ٦٧
Bal nahnu mahroomoona
"Ã'a, mun dai zama waɗanda aka hanã wa!"
-
أَفَرَءَيْتُمُ ٱلْمَآءَ ٱلَّذِى تَشْرَبُونَ٦٨
Afaraaytumu almaa allathee tashraboona
Shin, kuma kun ga ruwa wannan da kuke sha?
-
ءَأَنتُمْ أَنزَلْتُمُوهُ مِنَ ٱلْمُزْنِ أَمْ نَحْنُ ٱلْمُنزِلُونَ٦٩
Aantum anzaltumoohu mina almuzni am nahnu almunziloona
Shin, kũ ne kuke saukar da shi daga girgije, kõ kuwa Mũne Mãsu saukarwa?
-
لَوْ نَشَآءُ جَعَلْنَـٰهُ أُجَاجًا فَلَوْلَا تَشْكُرُونَ٧٠
Law nashao jaʿalnahu ojajan falawla tashkuroona
Dã Mun so, dã Mun mayar da shi ruwan zartsi. To don me bã ku gõdẽwa?
-
أَفَرَءَيْتُمُ ٱلنَّارَ ٱلَّتِى تُورُونَ٧١
Afaraaytumu alnnara allatee tooroona
Shin, kuma kun ga wutã wannan da kuke ƙyastãwa?
-
ءَأَنتُمْ أَنشَأْتُمْ شَجَرَتَهَآ أَمْ نَحْنُ ٱلْمُنشِـُٔونَ٧٢
Aantum anshatum shajarataha am nahnu almunshioona
Shin, kũ ne kuke ƙagã halittar itãciyarta, kõ kuwa Mũ ne Mãsu ƙãgãwa?
-
نَحْنُ جَعَلْنَـٰهَا تَذْكِرَةً وَمَتَـٰعًا لِّلْمُقْوِينَ٧٣
Nahnu jaʿalnaha tathkiratan wamataʿan lilmuqweena
Mũ ne Muka sanya ta wata abar wa'azi da jin dãɗi ga matafiya a cikin jẽji.
-
فَسَبِّحْ بِٱسْمِ رَبِّكَ ٱلْعَظِيمِ٧٤
Fasabbih biismi rabbika alʿatheemi
Sai ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mai girma.
-
۞ فَلَآ أُقْسِمُ بِمَوَٰقِعِ ٱلنُّجُومِ٧٥
Fala oqsimu bimawaqiʿi alnnujoomi
To, bã sai Na yi rantsuwa ba da lõkutan fãɗuwar taurãri.
-
وَإِنَّهُۥ لَقَسَمٌ لَّوْ تَعْلَمُونَ عَظِيمٌ٧٦
Wainnahu laqasamun law taʿlamoona ʿatheemun
Kuma lalle ne' haƙĩƙa, rantsuwa ce mai girma, dã kun sani.
-
إِنَّهُۥ لَقُرْءَانٌ كَرِيمٌ٧٧
Innahu laquranun kareemun
Lalle shi (wannan littãfi), haƙĩƙa, abin karantãwa ne mai daraja.
-
فِى كِتَـٰبٍ مَّكْنُونٍ٧٨
Fee kitabin maknoonin
A cikin wani littafi tsararre.
-
لَّا يَمَسُّهُۥٓ إِلَّا ٱلْمُطَهَّرُونَ٧٩
La yamassuhu illa almutahharoona
Bãbu mai shãfa shi fãce waɗanda aka tsarkake.
-
تَنزِيلٌ مِّن رَّبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ٨٠
Tanzeelun min rabbi alʿalameena
Wanda aka saukar ne daga Ubangijin halitta.
-
أَفَبِهَـٰذَا ٱلْحَدِيثِ أَنتُم مُّدْهِنُونَ٨١
Afabihatha alhadeethi antum mudhinoona
Shin, to, wannan lãbãrin ne kuke mãsu wulãkantãwa?
-
وَتَجْعَلُونَ رِزْقَكُمْ أَنَّكُمْ تُكَذِّبُونَ٨٢
Watajʿaloona rizqakum annakum tukaththiboona
Kuma kunã sanya arzikinku (game da shi) lalle kũ, ku ƙaryata (shi)?
-
فَلَوْلَآ إِذَا بَلَغَتِ ٱلْحُلْقُومَ٨٣
Falawla itha balaghati alhulqooma
To, don me idan rai ya kai ga maƙõshi? (Kusa da mutuwa).
-
وَأَنتُمْ حِينَئِذٍ تَنظُرُونَ٨٤
Waantum heenaithin tanthuroona
Alhãli kuwa kũ, a lõklcin nan, kunã kallo.
-
وَنَحْنُ أَقْرَبُ إِلَيْهِ مِنكُمْ وَلَـٰكِن لَّا تُبْصِرُونَ٨٥
Wanahnu aqrabu ilayhi minkum walakin la tubsiroona
Kuma Mũ ne mafi kusanta gare shi daga gare ku, to, amma kũ bã ku gani.
-
فَلَوْلَآ إِن كُنتُمْ غَيْرَ مَدِينِينَ٨٦
Falawla in kuntum ghayra madeeneena
To, don me in dai kun kasance bã waɗanda zã a yi wa sakamako ba?
-
تَرْجِعُونَهَآ إِن كُنتُمْ صَـٰدِقِينَ٨٧
Tarjiʿoonaha in kuntum sadiqeena
Ku mayar da shi (cikin jikinsa) har idan kun kasance mãsu gaskiya.1
Bayanai
[1] Idan kun kasance mãsu gaskiya ga da'awar rashin Tãshin Ƙiyãma, to, ku yi ƙõƙarin hana mutuwa ga mutãne dõmin ku hana cikar alkawarin tayarwa a bãyan mutuwa. -
فَأَمَّآ إِن كَانَ مِنَ ٱلْمُقَرَّبِينَ٨٨
Faamma in kana mina almuqarrabeena
To, amma idan (mai mutuwar) ya kasance daga makusanta,
-
فَرَوْحٌ وَرَيْحَانٌ وَجَنَّتُ نَعِيمٍ٨٩
Farawhun warayhanun wajannatu naʿeemin
Sai hũtawa da kyakkyawan abinci da Aljannar ni'ima.
-
وَأَمَّآ إِن كَانَ مِنْ أَصْحَـٰبِ ٱلْيَمِينِ٩٠
Waamma in kana min ashabi alyameeni
Kuma amma idan ya kasance daga mazõwa dãma,
-
فَسَلَـٰمٌ لَّكَ مِنْ أَصْحَـٰبِ ٱلْيَمِينِ٩١
Fasalamun laka min ashabi alyameeni
Sai (a ce masa) aminci ya tabbata a gare ka daga mazõwa dãma.
-
وَأَمَّآ إِن كَانَ مِنَ ٱلْمُكَذِّبِينَ ٱلضَّآلِّينَ٩٢
Waamma in kana mina almukaththibeena alddalleena
Kuma amma idan ya kasance daga mãsu ƙaryatãwar, ɓatattun,
-
فَنُزُلٌ مِّنْ حَمِيمٍ٩٣
Fanuzulun min hameemin
Sai wata liyãfa ta ruwan zãfi.
-
وَتَصْلِيَةُ جَحِيمٍ٩٤
Watasliyatu jaheemin
Da ƙõnuwa da Jahĩm,
-
إِنَّ هَـٰذَا لَهُوَ حَقُّ ٱلْيَقِينِ٩٥
Inna hatha lahuwa haqqu alyaqeeni
Lalle wannan, haƙĩƙa, ita ce gaskiya ta yaƙĩni.
-
فَسَبِّحْ بِٱسْمِ رَبِّكَ ٱلْعَظِيمِ٩٦
Fasabbih biismi rabbika alʿatheemi
Sabõda haka, ka tsarkake1 sũnan Ubangijinka, Mai karimci.
Bayanai
[1] A cikin rukũ'i anã tasbĩhi da cewa: "Subhãna Rabbiyal Azĩm wa Bihamdih." Ma'anarsa Tsarki ya tabbata ga Ubangijina Mai girma game da gõde Masa.
Tambayoyin da ake yawan yi
Mece ce ma’anar sunan Suratul Waƙi’a?
Ma’anar Waƙi’a ita ce “Mai aukuwa”.
Suratul Waƙi’a tana cikin juz’i na nawa?
Suratul Waƙi’a tana cikin juz’i na 27.
Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Waƙi’a?
Suratul Waƙi’a tana da ayoyi 96.
Suratul Waƙi’a Makkiya ce ko Madaniya?
Suratul Waƙi’a sura ce Makkiya.
Suratul Waƙi’a ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?
Ita ce sura ta 56 a cikin Alƙur’ani.
Majiyoyi
- Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
- Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
- Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
- Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
- Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
- Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.
Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.