سورة الملك

Suratul Mulk da fassarar Hausa

Mulki

Mushafi

Mishary Rashid AlafasySauke MP3Sauke PDF

Suratul Mulk (الملك) ita ce sura ta 67 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 30. Ma’anar sunanta ita ce “Mulki”. Sura ce Makkiya, wadda ta sauka a Makka kafin Hijira, kuma tana cikin juz’i na 29.

A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Mulk gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.

Suratul Mulk cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. تَبَـٰرَكَ ٱلَّذِى بِيَدِهِ ٱلْمُلْكُ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍ قَدِيرٌ۝١

    Tabaraka allathee biyadihi almulku wahuwa ʿala kulli shayin qadeerun

    (Allah), Wanda gudãnar da mulki yake ga hannun Sa, Ya tsarkaka, kuma Shi Mai ĩko ne a kan kome.

  2. ٱلَّذِى خَلَقَ ٱلْمَوْتَ وَٱلْحَيَوٰةَ لِيَبْلُوَكُمْ أَيُّكُمْ أَحْسَنُ عَمَلًا ۚ وَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلْغَفُورُ۝٢

    Allathee khalaqa almawta waalhayata liyabluwakum ayyukum ahsanu ʿamalan wahuwa alʿazeezu alghafooru

    Shi ne Wanda Ya halitta mutuwa da rãyuwa domin Ya jarraba ku, Ya nũna wãye daga cikinku ya fi kyãwon aiki, Shi ne Mabuwãyi, Mai gafara.

  3. ٱلَّذِى خَلَقَ سَبْعَ سَمَـٰوَٰتٍ طِبَاقًا ۖ مَّا تَرَىٰ فِى خَلْقِ ٱلرَّحْمَـٰنِ مِن تَفَـٰوُتٍ ۖ فَٱرْجِعِ ٱلْبَصَرَ هَلْ تَرَىٰ مِن فُطُورٍ۝٣

    Allathee khalaqa sabʿa samawatin tibaqan ma tara fee khalqi alrrahmani min tafawutin fairjiʿi albasara hal tara min futoorin

    Shi ne wanda Ya halitta sammai bakawi, ɗabaƙõƙi a kan jũna, bã za ka ga goggociya ba a cikin halittar (Allah) Mai rahama. Ka sãke dũbawa, ko za ka ga wata ɓaraka?

  4. ثُمَّ ٱرْجِعِ ٱلْبَصَرَ كَرَّتَيْنِ يَنقَلِبْ إِلَيْكَ ٱلْبَصَرُ خَاسِئًا وَهُوَ حَسِيرٌ۝٤

    Thumma irjiʿi albasara karratayni yanqalib ilayka albasaru khasian wahuwa haseerun

    Sa'an nan ka sake maimaita, dũbãwa, ganinka zai komo maka, gajiyayye, ba da ganin wata naƙasa bã.

  5. وَلَقَدْ زَيَّنَّا ٱلسَّمَآءَ ٱلدُّنْيَا بِمَصَـٰبِيحَ وَجَعَلْنَـٰهَا رُجُومًا لِّلشَّيَـٰطِينِ ۖ وَأَعْتَدْنَا لَهُمْ عَذَابَ ٱلسَّعِيرِ۝٥

    Walaqad zayyanna alssamaa alddunya bimasabeeha wajaʿalnaha rujooman lilshshayateeni waaʿtadna lahum ʿathaba alssaʿeeri

    Kuma lalle Mun ƙawãta samar farko da fitillu, kuma Muka sanya su abin jifa ga shaiɗanu, kuma Muka yi musu tattalin azãbar Sa'ĩr.

  6. وَلِلَّذِينَ كَفَرُوا۟ بِرَبِّهِمْ عَذَابُ جَهَنَّمَ ۖ وَبِئْسَ ٱلْمَصِيرُ۝٦

    Walillatheena kafaroo birabbihim ʿathabu jahannama wabisa almaseeru

    Kuma waɗanda suka kafirce wa Ubangjinsu na da azãbar Jahannama, tã munana ga zamanta makõmarsu.

  7. إِذَآ أُلْقُوا۟ فِيهَا سَمِعُوا۟ لَهَا شَهِيقًا وَهِىَ تَفُورُ۝٧

    Itha olqoo feeha samiʿoo laha shaheeqan wahiya tafooru

    Idan an jẽfa su a cikinta, sai su ji daga gare ta wata ƙãra, tana tafasa.

  8. تَكَادُ تَمَيَّزُ مِنَ ٱلْغَيْظِ ۖ كُلَّمَآ أُلْقِىَ فِيهَا فَوْجٌ سَأَلَهُمْ خَزَنَتُهَآ أَلَمْ يَأْتِكُمْ نَذِيرٌ۝٨

    Takadu tamayyazu mina alghaythi kullama olqiya feeha fawjun saalahum khazanatuha alam yatikum natheerun

    Tana kusa ta tsãge domin hushi, ko da yaushe aka jẽfa wani ɓangaren jama'a a cikinta, matsaranta na tambayar su da cewa, "Wani mai gargaɗi bai je muku ba?"

  9. قَالُوا۟ بَلَىٰ قَدْ جَآءَنَا نَذِيرٌ فَكَذَّبْنَا وَقُلْنَا مَا نَزَّلَ ٱللَّهُ مِن شَىْءٍ إِنْ أَنتُمْ إِلَّا فِى ضَلَـٰلٍ كَبِيرٍ۝٩

    Qaloo bala qad jaana natheerun fakaththabna waqulna ma nazzala Allahu min shayin in antum illa fee dalalin kabeerin

    Sai su ce: "I, lalle wani mai gargaɗi ya je mana, sai muka ƙaryata shi, muka ce, 'Allah bai saukar da kome ba, bã ku cikin kõme sai ɓata babba.'"

  10. وَقَالُوا۟ لَوْ كُنَّا نَسْمَعُ أَوْ نَعْقِلُ مَا كُنَّا فِىٓ أَصْحَـٰبِ ٱلسَّعِيرِ۝١٠

    Waqaloo law kunna nasmaʿu aw naʿqilu ma kunna fee ashabi alssaʿeeri

    Kuma suka ce: "Dã mun zamo muna saurãre, kõ muna da hankali, dã ba mu kasance a cikin 'yan sa'ĩr ba."

  11. فَٱعْتَرَفُوا۟ بِذَنۢبِهِمْ فَسُحْقًا لِّأَصْحَـٰبِ ٱلسَّعِيرِ۝١١

    Faiʿtarafoo bithanbihim fasuhqan liashabi alssaʿeeri

    Wato su yi iƙrãri da laifinsu. Allah Ya la'ani'yan sa'ĩr!

  12. إِنَّ ٱلَّذِينَ يَخْشَوْنَ رَبَّهُم بِٱلْغَيْبِ لَهُم مَّغْفِرَةٌ وَأَجْرٌ كَبِيرٌ۝١٢

    Inna allatheena yakhshawna rabbahum bialghaybi lahum maghfiratun waajrun kabeerun

    Lalle waɗanda ke tsõron Ubangjinsu, a ɓoye, suna da wata gãfara da wani sakamako mai girma.

  13. وَأَسِرُّوا۟ قَوْلَكُمْ أَوِ ٱجْهَرُوا۟ بِهِۦٓ ۖ إِنَّهُۥ عَلِيمٌۢ بِذَاتِ ٱلصُّدُورِ۝١٣

    Waasirroo qawlakum awi ijharoo bihi innahu ʿaleemun bithati alssudoori

    Kuma ku asirta maganarku ko ku bayyana ta, lalle shi, (Allah), Masani ne ga abin da ke cikin ƙirãza.

  14. أَلَا يَعْلَمُ مَنْ خَلَقَ وَهُوَ ٱللَّطِيفُ ٱلْخَبِيرُ۝١٤

    Ala yaʿlamu man khalaqa wahuwa allateefu alkhabeeru

    Ashe, wanda Ya yi halitta bã zai iya saninta ba, alhãli kuwa shi Mai tausasãwa ne, kuma Mai labartawa?

  15. هُوَ ٱلَّذِى جَعَلَ لَكُمُ ٱلْأَرْضَ ذَلُولًا فَٱمْشُوا۟ فِى مَنَاكِبِهَا وَكُلُوا۟ مِن رِّزْقِهِۦ ۖ وَإِلَيْهِ ٱلنُّشُورُ۝١٥

    Huwa allathee jaʿala lakumu alarda thaloolan faimshoo fee manakibiha wakuloo min rizqihi wailayhi alnnushooru

    Shi, (Allah), Yã sanya muku ƙasa hõrarriya, sai ku tafi cikin sãsanninta, kuma ku ci daga arzikin Sa, kuma zuwa gare shi ne tãshin yake.

  16. ءَأَمِنتُم مَّن فِى ٱلسَّمَآءِ أَن يَخْسِفَ بِكُمُ ٱلْأَرْضَ فَإِذَا هِىَ تَمُورُ۝١٦

    Aamintum man fee alssamai an yakhsifa bikumu alarda faitha hiya tamooru

    Shin kõ kun amince cewa wanda ke cikin sama, bã zai iya shãfe ƙasa tãre da ku ba, sai ga ta tana mai girgiza?

  17. أَمْ أَمِنتُم مَّن فِى ٱلسَّمَآءِ أَن يُرْسِلَ عَلَيْكُمْ حَاصِبًا ۖ فَسَتَعْلَمُونَ كَيْفَ نَذِيرِ۝١٧

    Am amintum man fee alssamai an yursila ʿalaykum hasiban fasataʿlamoona kayfa natheeri

    Kõ kun amincẽ cewa wanda ke cikin sama bã zai iya sako muku iskar gũguwa ba? To, zã ku san yadda (ãƙibar) gargaɗi Na take.

  18. وَلَقَدْ كَذَّبَ ٱلَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ فَكَيْفَ كَانَ نَكِيرِ۝١٨

    Walaqad kaththaba allatheena min qablihim fakayfa kana nakeeri

    Lalle, waɗanda ke gabansu sun ƙaryata (manzanni). To, yãya (ãƙibar) gargaɗi Na ta kasance?

  19. أَوَلَمْ يَرَوْا۟ إِلَى ٱلطَّيْرِ فَوْقَهُمْ صَـٰٓفَّـٰتٍ وَيَقْبِضْنَ ۚ مَا يُمْسِكُهُنَّ إِلَّا ٱلرَّحْمَـٰنُ ۚ إِنَّهُۥ بِكُلِّ شَىْءٍۭ بَصِيرٌ۝١٩

    Awalam yaraw ila alttayri fawqahum saffatin wayaqbidna ma yumsikuhunna illa alrrahmanu innahu bikulli shayin baseerun

    Bã zã su yi dũbi ba zuwa ga tsuntsãye a kansu, mãsu sanwã, kuma suna fiffikãwa, bãbu mai riƙe da su sai (Allah), Mairahama? Lalle shi Mai gani ne ga dukan kõme.

  20. أَمَّنْ هَـٰذَا ٱلَّذِى هُوَ جُندٌ لَّكُمْ يَنصُرُكُم مِّن دُونِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ۚ إِنِ ٱلْكَـٰفِرُونَ إِلَّا فِى غُرُورٍ۝٢٠

    Amman hatha allathee huwa jundun lakum yansurukum min dooni alrrahmani ini alkafiroona illa fee ghuroorin

    Wãne ne wanda zai zame muku mayãƙin da zai taimake ku, wanda bã (Allah) ba, Mai rahama? Kãfirai ba su a cikin kõme fãce rũɗu.

  21. أَمَّنْ هَـٰذَا ٱلَّذِى يَرْزُقُكُمْ إِنْ أَمْسَكَ رِزْقَهُۥ ۚ بَل لَّجُّوا۟ فِى عُتُوٍّ وَنُفُورٍ۝٢١

    Amman hatha allathee yarzuqukum in amsaka rizqahu bal lajjoo fee ʿutuwwin wanufoorin

    Wãne ne wanda zai ciyar da ku, idan (Allah) Ya riƙe arzikin Sa? A'aha, sun yi zurfi cikin girman kai da tãshin hankali.

  22. أَفَمَن يَمْشِى مُكِبًّا عَلَىٰ وَجْهِهِۦٓ أَهْدَىٰٓ أَمَّن يَمْشِى سَوِيًّا عَلَىٰ صِرَٰطٍ مُّسْتَقِيمٍ۝٢٢

    Afaman yamshee mukibban ʿala wajhihi ahda amman yamshee sawiyyan ʿala siratin mustaqeemin

    Shin, wanda ke tafiya a kife a kan fuskarsa yã fi zama a kan shiryuwa, ko kuwa wanda ke tafiya miƙe a kan hanya madaidaiciya?

  23. قُلْ هُوَ ٱلَّذِىٓ أَنشَأَكُمْ وَجَعَلَ لَكُمُ ٱلسَّمْعَ وَٱلْأَبْصَـٰرَ وَٱلْأَفْـِٔدَةَ ۖ قَلِيلًا مَّا تَشْكُرُونَ۝٢٣

    Qul huwa allathee anshaakum wajaʿala lakumu alssamʿa waalabsara waalafidata qaleelan ma tashkuroona

    Ka ce: "(Allah) Shine Wanda Ya ƙaga halittarku, Ya sanya muku ji da gani da tunãni, amman kaɗan ce ƙwarai godiyarku!"

  24. قُلْ هُوَ ٱلَّذِى ذَرَأَكُمْ فِى ٱلْأَرْضِ وَإِلَيْهِ تُحْشَرُونَ۝٢٤

    Qul huwa allathee tharaakum fee alardi wailayhi tuhsharoona

    Kuma kace "Shi ne Ya halitta ku daga ƙasã, kuma zuwa gare Shi ne ake tãshin ku."

  25. وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هَـٰذَا ٱلْوَعْدُ إِن كُنتُمْ صَـٰدِقِينَ۝٢٥

    Wayaqooloona mata hatha alwaʿdu in kuntum sadiqeena

    Kuma sunã cewa, "Yaushe ne wannan alkawarin zai tabbata in dai kun kasance mãsu gaskiya ne kũ?"

  26. قُلْ إِنَّمَا ٱلْعِلْمُ عِندَ ٱللَّهِ وَإِنَّمَآ أَنَا۠ نَذِيرٌ مُّبِينٌ۝٢٦

    Qul innama alʿilmu ʿinda Allahi wainnama ana natheerun mubeenun

    Ka ce: "Ilmin a wurin Allah kawai yake, kuma ni mai gargaɗi kawai ne, mai bayyana (gargaɗin)."

  27. فَلَمَّا رَأَوْهُ زُلْفَةً سِيٓـَٔتْ وُجُوهُ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ وَقِيلَ هَـٰذَا ٱلَّذِى كُنتُم بِهِۦ تَدَّعُونَ۝٢٧

    Falamma raawhu zulfatan seeat wujoohu allatheena kafaroo waqeela hatha allathee kuntum bihi taddaʿoona

    To, lokacin da suka gan ta (azãbar) a kusa, fuskokin waɗanda suka kãfirta suka mũnana, kuma aka ce (musu) wannan shi ne abin da kuka zamo kuna ƙaryatãwa.

  28. قُلْ أَرَءَيْتُمْ إِنْ أَهْلَكَنِىَ ٱللَّهُ وَمَن مَّعِىَ أَوْ رَحِمَنَا فَمَن يُجِيرُ ٱلْكَـٰفِرِينَ مِنْ عَذَابٍ أَلِيمٍ۝٢٨

    Qul araaytum in ahlakaniya Allahu waman maʿiya aw rahimana faman yujeeru alkafireena min ʿathabin aleemin

    Ka ce musu "Idan Allah Ya halaka ni nĩ da wanda ke tãre da ni, ko kuma, Yã yi mana rahama, to, wãne ne zai tserar da kafirai daga wata azãba mai raɗaɗi?"

  29. قُلْ هُوَ ٱلرَّحْمَـٰنُ ءَامَنَّا بِهِۦ وَعَلَيْهِ تَوَكَّلْنَا ۖ فَسَتَعْلَمُونَ مَنْ هُوَ فِى ضَلَـٰلٍ مُّبِينٍ۝٢٩

    Qul huwa alrrahmanu amanna bihi waʿalayhi tawakkalna fasataʿlamoona man huwa fee dalalin mubeenin

    Ka ce: "Shĩ ne Mai rahama mun yi ĩmãni da Shi, gare Shi muka dogara, saboda haka zã ku san wanda yake a cikin ɓata bayyananniya."

  30. قُلْ أَرَءَيْتُمْ إِنْ أَصْبَحَ مَآؤُكُمْ غَوْرًا فَمَن يَأْتِيكُم بِمَآءٍ مَّعِينٍۭ۝٣٠

    Qul araaytum in asbaha maokum ghawran faman yateekum bimain maʿeenin

    Ka ce: "Ko kun gani, idan ruwanku ya wãyi gari faƙaƙƙe, to, wãne ne zai zo muku da ruwa wani mai ɓuɓɓuga?"1

    Bayanai
    [1] Ana so idan mai karatu ya kai ƙarshen wannan sũra ya ce: الله رب العالمين wato Allah Ubagijin halitta. An karanta wannan ãya a gaban wani kãfiri, sai ya ce zã mu fito da ruwan game da amfãni da dundurũsai da farħtani, sai ruwan idãnunsa ya faƙe.

Tambayoyin da ake yawan yi

Mece ce ma’anar sunan Suratul Mulk?

Ma’anar Mulk ita ce “Mulki”.

Suratul Mulk tana cikin juz’i na nawa?

Suratul Mulk tana cikin juz’i na 29.

Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Mulk?

Suratul Mulk tana da ayoyi 30.

Suratul Mulk Makkiya ce ko Madaniya?

Suratul Mulk sura ce Makkiya.

Suratul Mulk ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?

Ita ce sura ta 67 a cikin Alƙur’ani.

Majiyoyi

  • Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
  • Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
  • Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
  • Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
  • Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
  • Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.

Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.

Saitunan karatu

Rubutun Alƙur’ani
Girman Larabci
100%
Girman fassara
100%
Kamanni

Ƙara zuwa Allon Gida

ReadSurahBuɗe ReadSurah daga allon gida, a cikakken allo. Surorin da kuka karanta suna buɗewa ko da babu intanet.

  1. A cikin Safari, taɓa maɓallin “Share”. A sababbin iPhone yana cikin menu na •••.
  2. Taɓa “Add to Home Screen”. Gungura ƙasa idan ba ku gan shi ba.
  3. Taɓa “Add”.