سورة القلم

Suratul Ƙalam da fassarar Hausa

Alƙalami

Mushafi

Mishary Rashid AlafasySauke MP3Sauke PDF

Suratul Ƙalam (القلم) ita ce sura ta 68 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 52. Ma’anar sunanta ita ce “Alƙalami”. Sura ce Makkiya, wadda ta sauka a Makka kafin Hijira, kuma tana cikin juz’i na 29.

A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Ƙalam gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.

Suratul Ƙalam cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. نٓ ۚ وَٱلْقَلَمِ وَمَا يَسْطُرُونَ۝١

    Noon waalqalami wama yasturoona

    Ñ. Na rantse da alƙalami da abin da (marubũta) suke rubũtãwa.

  2. مَآ أَنتَ بِنِعْمَةِ رَبِّكَ بِمَجْنُونٍ۝٢

    Ma anta biniʿmati rabbika bimajnoonin

    Kai, sabõda ni'imar Ubangijinka, bã mahaukaci kake ba.

  3. وَإِنَّ لَكَ لَأَجْرًا غَيْرَ مَمْنُونٍ۝٣

    Wainna laka laajran ghayra mamnoonin

    Kuma, lalle, haƙĩƙa kanã da lãdar da bã ta yankewa.

  4. وَإِنَّكَ لَعَلَىٰ خُلُقٍ عَظِيمٍ۝٤

    Wainnaka laʿala khuluqin ʿatheemin

    Kuma, lalle haƙiƙa kana a kan hãlãyen kirki, manya.

  5. فَسَتُبْصِرُ وَيُبْصِرُونَ۝٥

    Fasatubsiru wayubsiroona

    Don haka, zã ka gani, sũ kuma zã su gani.

  6. بِأَييِّكُمُ ٱلْمَفْتُونُ۝٦

    Biayyikumu almaftoonu

    Ga wanenku haukã take.

  7. إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعْلَمُ بِمَن ضَلَّ عَن سَبِيلِهِۦ وَهُوَ أَعْلَمُ بِٱلْمُهْتَدِينَ۝٧

    Inna rabbaka huwa aʿlamu biman dalla ʿan sabeelihi wahuwa aʿlamu bialmuhtadeena

    Lalle Ubangijinka Shi ne Mafi sani ga wanda ya ɓace daga tafarkin Sa. Kuma Shi ne Mafi sani ga mãsu shiryuwa.

  8. فَلَا تُطِعِ ٱلْمُكَذِّبِينَ۝٨

    Fala tutiʿi almukaththibeena

    Saboda haka kada ka bi mãsu ƙaryatãwa.

  9. وَدُّوا۟ لَوْ تُدْهِنُ فَيُدْهِنُونَ۝٩

    Waddoo law tudhinu fayudhinoona

    Sunã fatar ka sassauta, su kuma sũ sassauta.

  10. وَلَا تُطِعْ كُلَّ حَلَّافٍ مَّهِينٍ۝١٠

    Wala tutiʿ kulla hallafin maheenin

    Kada ka bi dukkan mai yawan rantsuwa, walãkantacce.

  11. هَمَّازٍ مَّشَّآءٍۭ بِنَمِيمٍ۝١١

    Hammazin mashshain binameemin

    Mai zunɗe, mai yãwo da gulma.

  12. مَّنَّاعٍ لِّلْخَيْرِ مُعْتَدٍ أَثِيمٍ۝١٢

    Mannaʿin lilkhayri muʿtadin atheemin

    Mai hana alhẽri mai zãlunci, mai zunubi.

  13. عُتُلٍّۭ بَعْدَ ذَٰلِكَ زَنِيمٍ۝١٣

    ʿUtullin baʿda thalika zaneemin

    Mai girman kai, bãyan haka kuma la'ĩmi (bã ya son alhẽri).

  14. أَن كَانَ ذَا مَالٍ وَبَنِينَ۝١٤

    An kana tha malin wabaneena

    Sabõda yã kasance mai dũkiya da ɗiya.

  15. إِذَا تُتْلَىٰ عَلَيْهِ ءَايَـٰتُنَا قَالَ أَسَـٰطِيرُ ٱلْأَوَّلِينَ۝١٥

    Itha tutla ʿalayhi ayatuna qala asateeru alawwaleena

    Idan ana karanta masa ãyõyin Mu, sai ya ce: "Tatsũniyõyin mutãnen farko ne."

  16. سَنَسِمُهُۥ عَلَى ٱلْخُرْطُومِ۝١٦

    Sanasimuhu ʿala alkhurtoomi

    Zã Mu yi masa alãma a kan hanci.

  17. إِنَّا بَلَوْنَـٰهُمْ كَمَا بَلَوْنَآ أَصْحَـٰبَ ٱلْجَنَّةِ إِذْ أَقْسَمُوا۟ لَيَصْرِمُنَّهَا مُصْبِحِينَ۝١٧

    Inna balawnahum kama balawna ashaba aljannati ith aqsamoo layasrimunnaha musbiheena

    Lalle Mun jarrabe su kamar yadda Muka jarrabi mãsu gonar lambu, a lokacin da suka yi rantsuwa, wai lalle zã su girbe amfãninta, suna mãsu asubanci.

  18. وَلَا يَسْتَثْنُونَ۝١٨

    Wala yastathnoona

    Kuma (suka yi niyya), bã su kõ tõgẽwa.

  19. فَطَافَ عَلَيْهَا طَآئِفٌ مِّن رَّبِّكَ وَهُمْ نَآئِمُونَ۝١٩

    Fatafa ʿalayha taifun min rabbika wahum naimoona

    Wani mai kẽwayãwa daga Ubangijinka ya kẽwayã a kanta, (ya ƙone ta,) alhãli sunã barci.

  20. فَأَصْبَحَتْ كَٱلصَّرِيمِ۝٢٠

    Faasbahat kaalssareemi

    Sai ta wãyi gari (baƙa ƙirin) kamar dare.

  21. فَتَنَادَوْا۟ مُصْبِحِينَ۝٢١

    Fatanadaw musbiheena

    Sai suka kirãyi jũna, sunã mãsu yin asubanci.

  22. أَنِ ٱغْدُوا۟ عَلَىٰ حَرْثِكُمْ إِن كُنتُمْ صَـٰرِمِينَ۝٢٢

    Ani ighdoo ʿala harthikum in kuntum sarimeena

    Cẽwa ku yi sammakõ ga amfãnin gõnarku, idan kun kasance mãsu girbewa.

  23. فَٱنطَلَقُوا۟ وَهُمْ يَتَخَـٰفَتُونَ۝٢٣

    Faintalaqoo wahum yatakhafatoona

    Sai suka tafi sunã shãwara a ɓõye (sunã cẽwa).

  24. أَن لَّا يَدْخُلَنَّهَا ٱلْيَوْمَ عَلَيْكُم مِّسْكِينٌ۝٢٤

    An la yadkhulannaha alyawma ʿalaykum miskeenun

    "Lalle kada wani miskĩni ya shigar muku ita a yau!"

  25. وَغَدَوْا۟ عَلَىٰ حَرْدٍ قَـٰدِرِينَ۝٢٥

    Waghadaw ʿala hardin qadireena

    Kuma suka yi sammako akan (niyyar) rõwa, matuƙar iyãwarsu.

  26. فَلَمَّا رَأَوْهَا قَالُوٓا۟ إِنَّا لَضَآلُّونَ۝٢٦

    Falamma raawha qaloo inna ladalloona

    Lõkacin da suka gan ta, sai suka ce: "Lalle, mun saki hanya (mun ɓace)!"

  27. بَلْ نَحْنُ مَحْرُومُونَ۝٢٧

    Bal nahnu mahroomoona

    "Ba haka ba, mũ dai, an hana mu ne."

  28. قَالَ أَوْسَطُهُمْ أَلَمْ أَقُل لَّكُمْ لَوْلَا تُسَبِّحُونَ۝٢٨

    Qala awsatuhum alam aqul lakum lawla tusabbihoona

    Mafificinsu (hankali) ya ce: "Ban gaya muku ba, yã kamata ku tsarkake Allah?"

  29. قَالُوا۟ سُبْحَـٰنَ رَبِّنَآ إِنَّا كُنَّا ظَـٰلِمِينَ۝٢٩

    Qaloo subhana rabbina inna kunna thalimeena

    Suka ce: "Tsarki ya tabbata ga Ubangijinmu! Lalle, mu mun kasance azzãlumai."

  30. فَأَقْبَلَ بَعْضُهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ يَتَلَـٰوَمُونَ۝٣٠

    Faaqbala baʿduhum ʿala baʿdin yatalawamoona

    Sai suka fuskanci jũna, sunã zargin kansu.

  31. قَالُوا۟ يَـٰوَيْلَنَآ إِنَّا كُنَّا طَـٰغِينَ۝٣١

    Qaloo ya waylana inna kunna tagheena

    Suka ce: "Kaitonmu! Lalle, mũ ne muka kasance mãsu ƙẽtare iyãka."

  32. عَسَىٰ رَبُّنَآ أَن يُبْدِلَنَا خَيْرًا مِّنْهَآ إِنَّآ إِلَىٰ رَبِّنَا رَٰغِبُونَ۝٣٢

    ʿAsa rabbuna an yubdilana khayran minha inna ila rabbina raghiboona

    "Mai yiwuwa ne Ubangijinmu Ya musanya mana da wani abu da yã fi ta. Lalle, mũ (ba mu yanke ƙauna ba) zuwa ga Ubangijinmu, mãsu kwaɗayi ne."

  33. كَذَٰلِكَ ٱلْعَذَابُ ۖ وَلَعَذَابُ ٱلْـَٔاخِرَةِ أَكْبَرُ ۚ لَوْ كَانُوا۟ يَعْلَمُونَ۝٣٣

    Kathalika alʿathabu walaʿathabu alakhirati akbaru law kanoo yaʿlamoona

    Haka dai azãbar1 take, kuma lalle ne azãbar Lãhira ta fi girma, in da sun kasance zã su iya gãnẽwã.

    Bayanai
    [1] Irin wannan azãba ce za a yi wa Ƙuraishãwa, dangin Annabi, kamar yadda aka yi wa mãsu gonar lambu, wãto da suka tũba aka musanya musu da abin da ya fi abin da suka sãba sãmu. Wato an gayã wa Annabi ne lõkacin da danginsa suka kangare, suka ƙi shiga Musulunci, aka yi musu azãbar fari, da rashin ruwa shekara bakwai, Allah Ya gaya masa cewa, zã su musulunta, alheri ya kõma musu. Ya kuwa kõma, kamar yadda Allah Ya yi alkawari
  34. إِنَّ لِلْمُتَّقِينَ عِندَ رَبِّهِمْ جَنَّـٰتِ ٱلنَّعِيمِ۝٣٤

    Inna lilmuttaqeena ʿinda rabbihim jannati alnnaʿeemi

    Lalle ne mãsu taƙawa nã da a wurin Ubangijinsu, gidãjen Aljanna na ni'ima.

  35. أَفَنَجْعَلُ ٱلْمُسْلِمِينَ كَٱلْمُجْرِمِينَ۝٣٥

    Afanajʿalu almuslimeena kaalmujrimeena

    Shin ko zã Mu sanya waɗanda ke bi da ɗa'a kamar mãsu laifi?

  36. مَا لَكُمْ كَيْفَ تَحْكُمُونَ۝٣٦

    Ma lakum kayfa tahkumoona

    Me ya sãme ku, yãya kuke yin hukunci (da haka)?

  37. أَمْ لَكُمْ كِتَـٰبٌ فِيهِ تَدْرُسُونَ۝٣٧

    Am lakum kitabun feehi tadrusoona

    Ko kuna da wani littafi, wanda a cikinsa, kuke karantãwa?

  38. إِنَّ لَكُمْ فِيهِ لَمَا تَخَيَّرُونَ۝٣٨

    Inna lakum feehi lama takhayyaroona

    Cẽwã kunã da, a cikinsa lalle (duk) abin da rãyukanku suka zãɓa?

  39. أَمْ لَكُمْ أَيْمَـٰنٌ عَلَيْنَا بَـٰلِغَةٌ إِلَىٰ يَوْمِ ٱلْقِيَـٰمَةِ ۙ إِنَّ لَكُمْ لَمَا تَحْكُمُونَ۝٣٩

    Am lakum aymanun ʿalayna balighatun ila yawmi alqiyamati inna lakum lama tahkumoona

    Kõ kunã (riƙe) da wasu rantsuwõyin alkawari a kan Mu, har ya zuwa Rãnar ¡iyãma, cẽwa lalle ne kunã da abin da kuke hukuntã wa kanku?

  40. سَلْهُمْ أَيُّهُم بِذَٰلِكَ زَعِيمٌ۝٤٠

    Salhum ayyuhum bithalika zaʿeemun

    Ka tambaye su, wãne, a cikinsu, ke lãmuncewã ga sãmun wannan (hukuncin)?

  41. أَمْ لَهُمْ شُرَكَآءُ فَلْيَأْتُوا۟ بِشُرَكَآئِهِمْ إِن كَانُوا۟ صَـٰدِقِينَ۝٤١

    Am lahum shurakao falyatoo bishurakaihim in kanoo sadiqeena

    Kõ sunã da abõkan tãrẽwa (ga wannan ra'ayi)? To, sai su kãwo abõkan tãrayyarsu, idan sun kasance mãsu gaskiya.

  42. يَوْمَ يُكْشَفُ عَن سَاقٍ وَيُدْعَوْنَ إِلَى ٱلسُّجُودِ فَلَا يَسْتَطِيعُونَ۝٤٢

    Yawma yukshafu ʿan saqin wayudʿawna ila alssujoodi fala yastateeʿoona

    Ranar da zã a kuranye ƙwabri, kuma a kira su zuwa ga yin sujada, sai bã zã su iyãwa ba.

  43. خَـٰشِعَةً أَبْصَـٰرُهُمْ تَرْهَقُهُمْ ذِلَّةٌ ۖ وَقَدْ كَانُوا۟ يُدْعَوْنَ إِلَى ٱلسُّجُودِ وَهُمْ سَـٰلِمُونَ۝٤٣

    Khashiʿatan absaruhum tarhaquhum thillatun waqad kanoo yudʿawna ila alssujoodi wahum salimoona

    Su fito da idãnu ƙasƙantattu, wulãkanci yana rufe su. Lalle ne a dã sun kasance anã kiran su zuwa, yin sujũdar, alhãli kuwa sunã lãfiya lau, (suka ƙi yi).

  44. فَذَرْنِى وَمَن يُكَذِّبُ بِهَـٰذَا ٱلْحَدِيثِ ۖ سَنَسْتَدْرِجُهُم مِّنْ حَيْثُ لَا يَعْلَمُونَ۝٤٤

    Fatharnee waman yukaththibu bihatha alhadeethi sanastadrijuhum min haythu la yaʿlamoona

    Sabõda haka ka bar Ni da mai ƙaryata wanna lãbãri (Alƙur'ãni). Zã Mu yi musu istidrãji daga inda ba su sani ba.

  45. وَأُمْلِى لَهُمْ ۚ إِنَّ كَيْدِى مَتِينٌ۝٤٥

    Waomlee lahum inna kaydee mateenun

    Ina jinkirtã musu, lalle kaidi Na mai ƙarfi ne.

  46. أَمْ تَسْـَٔلُهُمْ أَجْرًا فَهُم مِّن مَّغْرَمٍ مُّثْقَلُونَ۝٤٦

    Am tasaluhum ajran fahum min maghramin muthqaloona

    Kõ kana tambayar su wata la'ada ne, sabõda haka sũ, daga wannan tãrar, suke jin an nauyaya musu?

  47. أَمْ عِندَهُمُ ٱلْغَيْبُ فَهُمْ يَكْتُبُونَ۝٤٧

    Am ʿindahumu alghaybu fahum yaktuboona

    Ko kuma sunã da ilmin gaibu ne, wãto sunã yin rubũtun (abin da suke faɗã daga gare shi) ne?

  48. فَٱصْبِرْ لِحُكْمِ رَبِّكَ وَلَا تَكُن كَصَاحِبِ ٱلْحُوتِ إِذْ نَادَىٰ وَهُوَ مَكْظُومٌ۝٤٨

    Faisbir lihukmi rabbika wala takun kasahibi alhooti ith nada wahuwa makthoomun

    Sabõda haka, ka yi haƙuri da hukuncin Ubangijinka, kada ka zama kamar Ma'abũcin kĩfi, alõkacin da ya yi kira, alhãli yana cike da hushi.

  49. لَّوْلَآ أَن تَدَٰرَكَهُۥ نِعْمَةٌ مِّن رَّبِّهِۦ لَنُبِذَ بِٱلْعَرَآءِ وَهُوَ مَذْمُومٌ۝٤٩

    Lawla an tadarakahu niʿmatun min rabbihi lanubitha bialʿarai wahuwa mathmoomun

    Ba dõmin ni'ima daga wajen Ubangijinsa tã riske shi ba, lalle ne da an jẽfa shi a cikin wõfintacciyar ƙasa, alhãli yanã abin zargi.

  50. فَٱجْتَبَـٰهُ رَبُّهُۥ فَجَعَلَهُۥ مِنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ۝٥٠

    Faijtabahu rabbuhu fajaʿalahu mina alssaliheena

    Sai Ubangijinsa Ya zãɓe shi, sa'an nan Ya sanya shi a cikin mutãnen kirki.

  51. وَإِن يَكَادُ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ لَيُزْلِقُونَكَ بِأَبْصَـٰرِهِمْ لَمَّا سَمِعُوا۟ ٱلذِّكْرَ وَيَقُولُونَ إِنَّهُۥ لَمَجْنُونٌ۝٥١

    Wain yakadu allatheena kafaroo layuzliqoonaka biabsarihim lamma samiʿoo alththikra wayaqooloona innahu lamajnoonun

    Kuma lalle, ne waɗanda suka kãfirta sunã yin kamar su kãyar da kai sabõ da kallonsu (kallon mãmãki), a lokacin da suke jin karãtun Alƙur'ãni, kuma sunã cẽwa, "Lalle ne shi mahaukaci ne!"

  52. وَمَا هُوَ إِلَّا ذِكْرٌ لِّلْعَـٰلَمِينَ۝٥٢

    Wama huwa illa thikrun lilʿalameena

    Shi (Alƙur'ãni) bai kasance ba, fãce abin tunãtarwa ne ga duka dũniya.

Tambayoyin da ake yawan yi

Mece ce ma’anar sunan Suratul Ƙalam?

Ma’anar Ƙalam ita ce “Alƙalami”.

Suratul Ƙalam tana cikin juz’i na nawa?

Suratul Ƙalam tana cikin juz’i na 29.

Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Ƙalam?

Suratul Ƙalam tana da ayoyi 52.

Suratul Ƙalam Makkiya ce ko Madaniya?

Suratul Ƙalam sura ce Makkiya.

Suratul Ƙalam ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?

Ita ce sura ta 68 a cikin Alƙur’ani.

Majiyoyi

  • Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
  • Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
  • Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
  • Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
  • Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
  • Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.

Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.

Saitunan karatu

Rubutun Alƙur’ani
Girman Larabci
100%
Girman fassara
100%
Kamanni

Ƙara zuwa Allon Gida

ReadSurahBuɗe ReadSurah daga allon gida, a cikakken allo. Surorin da kuka karanta suna buɗewa ko da babu intanet.

  1. A cikin Safari, taɓa maɓallin “Share”. A sababbin iPhone yana cikin menu na •••.
  2. Taɓa “Add to Home Screen”. Gungura ƙasa idan ba ku gan shi ba.
  3. Taɓa “Add”.