Suratul Nuhu (نوح) ita ce sura ta 71 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 28. Sura ce Makkiya, wadda ta sauka a Makka kafin Hijira, kuma tana cikin juz’i na 29.
A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Nuhu gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.
Suratul Nuhu cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ
-
إِنَّآ أَرْسَلْنَا نُوحًا إِلَىٰ قَوْمِهِۦٓ أَنْ أَنذِرْ قَوْمَكَ مِن قَبْلِ أَن يَأْتِيَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ١
Inna arsalna noohan ila qawmihi an anthir qawmaka min qabli an yatiyahum ʿathabun aleemun
Lalle ne Mun aiki Nũhu zuwa ga mutãnensa, cẽwa ka yi gargaɗi ga mutãnenka gabãnin wata azãba mai raɗaɗi ta zo musu.
-
قَالَ يَـٰقَوْمِ إِنِّى لَكُمْ نَذِيرٌ مُّبِينٌ٢
Qala ya qawmi innee lakum natheerun mubeenun
Ya ce: "Ya mutãnena ni, a gare ku, mai gargaɗi ne, mai bayyanãwa."
-
أَنِ ٱعْبُدُوا۟ ٱللَّهَ وَٱتَّقُوهُ وَأَطِيعُونِ٣
Ani oʿbudoo Allaha waittaqoohu waateeʿooni
"Cewa ku bauta wa Allah, ku ji tsõron Sa, kuma ku bĩ ni."
-
يَغْفِرْ لَكُم مِّن ذُنُوبِكُمْ وَيُؤَخِّرْكُمْ إِلَىٰٓ أَجَلٍ مُّسَمًّى ۚ إِنَّ أَجَلَ ٱللَّهِ إِذَا جَآءَ لَا يُؤَخَّرُ ۖ لَوْ كُنتُمْ تَعْلَمُونَ٤
Yaghfir lakum min thunoobikum wayuakhkhirkum ila ajalin musamman inna ajala Allahi itha jaa la yuakhkharu law kuntum taʿlamoona
"Allah zai gãfarta muku daga zunubanku kuma Ya jinkirta muku zuwa ga ajalin da aka ambata. Lalle ne ajalin Allah idan ya zo, ba za a jinkirta Shi ba, dã kun kasance masana (ga abin da nake faɗã dã, kun bar kãfirci)."
-
قَالَ رَبِّ إِنِّى دَعَوْتُ قَوْمِى لَيْلًا وَنَهَارًا٥
Qala rabbi innee daʿawtu qawmee laylan wanaharan
Nũhu) ya ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne, na kirãyi mutãnena, a cikin dare da yini."
-
فَلَمْ يَزِدْهُمْ دُعَآءِىٓ إِلَّا فِرَارًا٦
Falam yazidhum duʿaee illa firaran
"To, amma kirana bai ƙãre su ba sai da, gudu (daga gare ni)."
-
وَإِنِّى كُلَّمَا دَعَوْتُهُمْ لِتَغْفِرَ لَهُمْ جَعَلُوٓا۟ أَصَـٰبِعَهُمْ فِىٓ ءَاذَانِهِمْ وَٱسْتَغْشَوْا۟ ثِيَابَهُمْ وَأَصَرُّوا۟ وَٱسْتَكْبَرُوا۟ ٱسْتِكْبَارًا٧
Wainnee kullama daʿawtuhum litaghfira lahum jaʿaloo asabiʿahum fee athanihim waistaghshaw thiyabahum waasarroo waistakbaroo istikbaran
"Kuma lalle ne ni, kõ da yaushe na kirãye su dõmin Ka gãfarta musu, sai su sanya yatsunsu a cikin kunnuwansu, su lulluɓe da tufãfinsu, su dõge ga yin laifi. Sun yi girman kai iyãkar girman kai."
-
ثُمَّ إِنِّى دَعَوْتُهُمْ جِهَارًا٨
Thumma innee daʿawtuhum jiharan
"Sa'an nan lalle ne ni, na kira su, a bayyane."
-
ثُمَّ إِنِّىٓ أَعْلَنتُ لَهُمْ وَأَسْرَرْتُ لَهُمْ إِسْرَارًا٩
Thumma innee aʿlantu lahum waasrartu lahum israran
"Sa'an nan lalle ne, na yi yẽkuwa sabõda su, kuma na gãna da su a cikin asĩri."
-
فَقُلْتُ ٱسْتَغْفِرُوا۟ رَبَّكُمْ إِنَّهُۥ كَانَ غَفَّارًا١٠
Faqultu istaghfiroo rabbakum innahu kana ghaffaran
"Shi na ce, 'Ku nẽmi gãfara daga Ubangijinku, lalle ne shi Ya kasance Mai gãfara ne."
-
يُرْسِلِ ٱلسَّمَآءَ عَلَيْكُم مِّدْرَارًا١١
Yursili alssamaa ʿalaykum midraran
"Ya sako (girgijen) sama a kanku da ruwa mai ɓuɓɓuga."
-
وَيُمْدِدْكُم بِأَمْوَٰلٍ وَبَنِينَ وَيَجْعَل لَّكُمْ جَنَّـٰتٍ وَيَجْعَل لَّكُمْ أَنْهَـٰرًا١٢
Wayumdidkum biamwalin wabaneena wayajʿal lakum jannatin wayajʿal lakum anharan
"Kuma ya yalwata muku game da dũkiya da ɗiya, Ya sanya muku (albarka) ga gõnaki, kuma Ya sanya muku koguna."
-
مَّا لَكُمْ لَا تَرْجُونَ لِلَّهِ وَقَارًا١٣
Ma lakum la tarjoona lillahi waqaran
"Me ya sãme ku, bã ku fãtar sãmun natsuwa daga Allah,"
-
وَقَدْ خَلَقَكُمْ أَطْوَارًا١٤
Waqad khalaqakum atwaran
"Alhãli kuwa, lalle ne, Ya halitta. ku, a cikin hãlãye?"
-
أَلَمْ تَرَوْا۟ كَيْفَ خَلَقَ ٱللَّهُ سَبْعَ سَمَـٰوَٰتٍ طِبَاقًا١٥
Alam taraw kayfa khalaqa Allahu sabʿa samawatin tibaqan
"Ba ku ga yadda Allah Ya halitta wasu sammai bakwai ɗabaƙõƙĩ a kan jũna ba?"
-
وَجَعَلَ ٱلْقَمَرَ فِيهِنَّ نُورًا وَجَعَلَ ٱلشَّمْسَ سِرَاجًا١٦
Wajaʿala alqamara feehinna nooran wajaʿala alshshamsa sirajan
"Ya sanya watã a cikinsu, yana mai haske, Ya sanya rãnã babbar fitila?"
-
وَٱللَّهُ أَنۢبَتَكُم مِّنَ ٱلْأَرْضِ نَبَاتًا١٧
WaAllahu anbatakum mina alardi nabatan
"Kuma Allah Ya tsirar da ku daga ƙasa (kamar ganye) tsirarwa."
-
ثُمَّ يُعِيدُكُمْ فِيهَا وَيُخْرِجُكُمْ إِخْرَاجًا١٨
Thumma yuʿeedukum feeha wayukhrijukum ikhrajan
"Sa'an nan Ya mayar da ku a cikinta, kuma Ya fitar da ku fitarwa."
-
وَٱللَّهُ جَعَلَ لَكُمُ ٱلْأَرْضَ بِسَاطًا١٩
WaAllahu jaʿala lakumu alarda bisatan
"Kuma Allah Ya sanya muku ƙasa shimfidaɗɗiya."
-
لِّتَسْلُكُوا۟ مِنْهَا سُبُلًا فِجَاجًا٢٠
Litaslukoo minha subulan fijajan
"Dõmin ku shiga a cikinta, hanyõyi mãsu fãɗi."
-
قَالَ نُوحٌ رَّبِّ إِنَّهُمْ عَصَوْنِى وَٱتَّبَعُوا۟ مَن لَّمْ يَزِدْهُ مَالُهُۥ وَوَلَدُهُۥٓ إِلَّا خَسَارًا٢١
Qala noohun rabbi innahum ʿasawnee waittabaʿoo man lam yazidhu maluhu wawaladuhu illa khasaran
Nũhu ya ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne sũ sun saɓa mini sun bi wanda dukiyarsa da ɗiyansa ba su ƙãre shi da kõme ba sai da hasãra."
-
وَمَكَرُوا۟ مَكْرًا كُبَّارًا٢٢
Wamakaroo makran kubbaran
"Kuma sun yi wani mãkirci, mãkirci babba."
-
وَقَالُوا۟ لَا تَذَرُنَّ ءَالِهَتَكُمْ وَلَا تَذَرُنَّ وَدًّا وَلَا سُوَاعًا وَلَا يَغُوثَ وَيَعُوقَ وَنَسْرًا٢٣
Waqaloo la tatharunna alihatakum wala tatharunna waddan wala suwaʿan wala yaghootha wayaʿooqa wanasran
"Kuma suka ce: Faufau kada ku bar gumãkanku, kuma faufau, kada ku bar wadda, kuma kada ku bar suwã kuma kada ku bar Yagũsa da Yans uƙa da Nasra."
-
وَقَدْ أَضَلُّوا۟ كَثِيرًا ۖ وَلَا تَزِدِ ٱلظَّـٰلِمِينَ إِلَّا ضَلَـٰلًا٢٤
Waqad adalloo katheeran wala tazidi alththalimeena illa dalalan
"Kuma lalle ne sun ɓatar da (mutãne) mãsu yawa, kuma kada Ka ƙãrã wa azzãlumai (kõme) sai ɓata."
-
مِّمَّا خَطِيٓـَٔـٰتِهِمْ أُغْرِقُوا۟ فَأُدْخِلُوا۟ نَارًا فَلَمْ يَجِدُوا۟ لَهُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ أَنصَارًا٢٥
Mimma khateeatihim oghriqoo faodkhiloo naran falam yajidoo lahum min dooni Allahi ansaran
Sabõda laifukansu na ganganci aka nutsar da su, sa'an nan aka sanya su a wuta. Saboda haka ba su sãmã wa kansu wani mataimaki wanin Allah ba.
-
وَقَالَ نُوحٌ رَّبِّ لَا تَذَرْ عَلَى ٱلْأَرْضِ مِنَ ٱلْكَـٰفِرِينَ دَيَّارًا٢٦
Waqala noohun rabbi la tathar ʿala alardi mina alkafireena dayyaran
Kuma Nũhu ya ce: "Ya Ublngijina! Kada Ka bari, a kan ƙasa, daga cikin kãfirai, wanda ke zama a cikin gida."
-
إِنَّكَ إِن تَذَرْهُمْ يُضِلُّوا۟ عِبَادَكَ وَلَا يَلِدُوٓا۟ إِلَّا فَاجِرًا كَفَّارًا٢٧
Innaka in tatharhum yudilloo ʿibadaka wala yalidoo illa fajiran kaffaran
"Lalle ne, Kai idan Ka bar su, zã su ɓatar da bãyin Ka, kuma bã zã su haifi kowa ba fãce fãjiri mai yawan kãfirci"
-
رَّبِّ ٱغْفِرْ لِى وَلِوَٰلِدَىَّ وَلِمَن دَخَلَ بَيْتِىَ مُؤْمِنًا وَلِلْمُؤْمِنِينَ وَٱلْمُؤْمِنَـٰتِ وَلَا تَزِدِ ٱلظَّـٰلِمِينَ إِلَّا تَبَارًۢا٢٨
Rabbi ighfir lee waliwalidayya waliman dakhala baytiya muminan walilmumineena waalmuminati wala tazidi alththalimeena illa tabaran
"Ya Ubanginjina! Ka yi mini gãfara (ni) da mahaifana biyu, da wanda ya shiga gidana, yana mai ĩmãni, da mũminai maza da mũminai mãtã, kuma kada Ka ƙãrã wa azzãlumai kõme sai halaka."
Tambayoyin da ake yawan yi
Suratul Nuhu tana cikin juz’i na nawa?
Suratul Nuhu tana cikin juz’i na 29.
Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Nuhu?
Suratul Nuhu tana da ayoyi 28.
Suratul Nuhu Makkiya ce ko Madaniya?
Suratul Nuhu sura ce Makkiya.
Suratul Nuhu ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?
Ita ce sura ta 71 a cikin Alƙur’ani.
Majiyoyi
- Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
- Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
- Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
- Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
- Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
- Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.
Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.