سورة المزمل

Suratul Muzzammil da fassarar Hausa

Mai lulluɓewa

Mushafi

Mishary Rashid AlafasySauke MP3Sauke PDF

Suratul Muzzammil (المزمل) ita ce sura ta 73 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 20. Ma’anar sunanta ita ce “Mai lulluɓewa”. Sura ce Makkiya, wadda ta sauka a Makka kafin Hijira, kuma tana cikin juz’i na 29.

A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Muzzammil gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.

Suratul Muzzammil cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. يَـٰٓأَيُّهَا ٱلْمُزَّمِّلُ۝١

    Ya ayyuha almuzzammilu

    Yã wanda ya lulluɓe!

  2. قُمِ ٱلَّيْلَ إِلَّا قَلِيلًا۝٢

    Qumi allayla illa qaleelan

    Ka tsayu domin yin salla a cikin dare (duka) fãce kaɗan.

  3. نِّصْفَهُۥٓ أَوِ ٱنقُصْ مِنْهُ قَلِيلًا۝٣

    Nisfahu awi onqus minhu qaleelan

    Rabinsa, ko ka rage abu kaɗan daga gare shi.

  4. أَوْ زِدْ عَلَيْهِ وَرَتِّلِ ٱلْقُرْءَانَ تَرْتِيلًا۝٤

    Aw zid ʿalayhi warattili alqurana tarteelan

    Ko ka ƙara kansa kuma ka kyautata karanta Alƙu'ãni, daki daki.

  5. إِنَّا سَنُلْقِى عَلَيْكَ قَوْلًا ثَقِيلًا۝٥

    Inna sanulqee ʿalayka qawlan thaqeelan

    Lalle ne, Mũ, zã Mu jẽfa maka magana mai nauyi.

  6. إِنَّ نَاشِئَةَ ٱلَّيْلِ هِىَ أَشَدُّ وَطْـًٔا وَأَقْوَمُ قِيلًا۝٦

    Inna nashiata allayli hiya ashaddu watan waaqwamu qeelan

    Lalle ne, tashin dare shi ne mafi tsananin natsuwa, kuma mafi daidaituwa ga magana.

  7. إِنَّ لَكَ فِى ٱلنَّهَارِ سَبْحًا طَوِيلًا۝٧

    Inna laka fee alnnahari sabhan taweelan

    Lalle ne, kanã da, a cikin yini, wani tasĩhi mai tsawo.

  8. وَٱذْكُرِ ٱسْمَ رَبِّكَ وَتَبَتَّلْ إِلَيْهِ تَبْتِيلًا۝٨

    Waothkuri isma rabbika watabattal ilayhi tabteelan

    Kuma ka ambaci sũnan Ubangijinka, kuma ka yanke (ƙauna daga kowa ka koma) zuwa gare Shi, yankewa.

  9. رَّبُّ ٱلْمَشْرِقِ وَٱلْمَغْرِبِ لَآ إِلَـٰهَ إِلَّا هُوَ فَٱتَّخِذْهُ وَكِيلًا۝٩

    Rabbu almashriqi waalmaghribi la ilaha illa huwa faittakhithhu wakeelan

    Shi ne Ubangijin mafitar rãnã da mafãɗarta, bãbu abin bautawa fãce Shi. Sabõda haka ka riƙe Shi wakili.

  10. وَٱصْبِرْ عَلَىٰ مَا يَقُولُونَ وَٱهْجُرْهُمْ هَجْرًا جَمِيلًا۝١٠

    Waisbir ʿala ma yaqooloona waohjurhum hajran jameelan

    Kuma ka yi haƙuri ga abin da suke faɗã, kuma ka ƙaurace musu, ƙauracẽwa mai kyãwo.

  11. وَذَرْنِى وَٱلْمُكَذِّبِينَ أُو۟لِى ٱلنَّعْمَةِ وَمَهِّلْهُمْ قَلِيلًا۝١١

    Watharnee waalmukaththibeena olee alnnaʿmati wamahhilhum qaleelan

    Kuma ka bar Ni da mãsu ƙaryatãwa, mawadãta, kuma ka jinkirta musu kaɗan.

  12. إِنَّ لَدَيْنَآ أَنكَالًا وَجَحِيمًا۝١٢

    Inna ladayna ankalan wajaheeman

    Lalle ne, a wurin Mu, akwai wasu marũruwa mãsu nauyi da Jahĩm.

  13. وَطَعَامًا ذَا غُصَّةٍ وَعَذَابًا أَلِيمًا۝١٣

    Wataʿaman tha ghussatin waʿathaban aleeman

    Da wani abinci mai mãƙara da azãba mai raɗaɗi.

  14. يَوْمَ تَرْجُفُ ٱلْأَرْضُ وَٱلْجِبَالُ وَكَانَتِ ٱلْجِبَالُ كَثِيبًا مَّهِيلًا۝١٤

    Yawma tarjufu alardu waaljibalu wakanati aljibalu katheeban maheelan

    Rãnar da ƙasa ke raurawa, da duwãtsu kuma duwãtsu su kasance tudun rairayi mai malãlã.

  15. إِنَّآ أَرْسَلْنَآ إِلَيْكُمْ رَسُولًا شَـٰهِدًا عَلَيْكُمْ كَمَآ أَرْسَلْنَآ إِلَىٰ فِرْعَوْنَ رَسُولًا۝١٥

    Inna arsalna ilaykum rasoolan shahidan ʿalaykum kama arsalna ila firʿawna rasoolan

    Lalle ne, Mũ. Mun aika zuwa gare ku, wani Manzo1 mai shaida a kanku, kamar yadda Muka aika wani Manzo2 zuwaga Fir'auna,

    Bayanai
    [1] Wato Annabi Muhammad, tsĩra da aminci su tabbata a gare shi. [2] Wato Annabi Mũsã, aminci ya tabbata a gare shi.
  16. فَعَصَىٰ فِرْعَوْنُ ٱلرَّسُولَ فَأَخَذْنَـٰهُ أَخْذًا وَبِيلًا۝١٦

    Faʿasa firʿawnu alrrasoola faakhathnahu akhthan wabeelan

    Sai Fir'auna ya saɓa wa Manzon, saboda haka Muka kãma shi kãmu mai tsanani.

  17. فَكَيْفَ تَتَّقُونَ إِن كَفَرْتُمْ يَوْمًا يَجْعَلُ ٱلْوِلْدَٰنَ شِيبًا۝١٧

    Fakayfa tattaqoona in kafartum yawman yajʿalu alwildana sheeban

    To, yãya, idan kun kãfirta, zã ku kãre (azabar) wani yini mai mayar da yãra (tsofaffi) mãsu hurhura.

  18. ٱلسَّمَآءُ مُنفَطِرٌۢ بِهِۦ ۚ كَانَ وَعْدُهُۥ مَفْعُولًا۝١٨

    Alssamao munfatirun bihi kana waʿduhu mafʿoolan

    Sama za ta tsãge a cikinsa, wa'adinsa yã kasance mai aukuwa.

  19. إِنَّ هَـٰذِهِۦ تَذْكِرَةٌ ۖ فَمَن شَآءَ ٱتَّخَذَ إِلَىٰ رَبِّهِۦ سَبِيلًا۝١٩

    Inna hathihi tathkiratun faman shaa ittakhatha ila rabbihi sabeelan

    Lalle ne, wannan wata tunãtarwa ce, sai dai wanda ya so, ya kãma hanyar ƙwarai zuwa ga Ubangijinsa.

  20. ۞ إِنَّ رَبَّكَ يَعْلَمُ أَنَّكَ تَقُومُ أَدْنَىٰ مِن ثُلُثَىِ ٱلَّيْلِ وَنِصْفَهُۥ وَثُلُثَهُۥ وَطَآئِفَةٌ مِّنَ ٱلَّذِينَ مَعَكَ ۚ وَٱللَّهُ يُقَدِّرُ ٱلَّيْلَ وَٱلنَّهَارَ ۚ عَلِمَ أَن لَّن تُحْصُوهُ فَتَابَ عَلَيْكُمْ ۖ فَٱقْرَءُوا۟ مَا تَيَسَّرَ مِنَ ٱلْقُرْءَانِ ۚ عَلِمَ أَن سَيَكُونُ مِنكُم مَّرْضَىٰ ۙ وَءَاخَرُونَ يَضْرِبُونَ فِى ٱلْأَرْضِ يَبْتَغُونَ مِن فَضْلِ ٱللَّهِ ۙ وَءَاخَرُونَ يُقَـٰتِلُونَ فِى سَبِيلِ ٱللَّهِ ۖ فَٱقْرَءُوا۟ مَا تَيَسَّرَ مِنْهُ ۚ وَأَقِيمُوا۟ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُوا۟ ٱلزَّكَوٰةَ وَأَقْرِضُوا۟ ٱللَّهَ قَرْضًا حَسَنًا ۚ وَمَا تُقَدِّمُوا۟ لِأَنفُسِكُم مِّنْ خَيْرٍ تَجِدُوهُ عِندَ ٱللَّهِ هُوَ خَيْرًا وَأَعْظَمَ أَجْرًا ۚ وَٱسْتَغْفِرُوا۟ ٱللَّهَ ۖ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌۢ۝٢٠

    Inna rabbaka yaʿlamu annaka taqoomu adna min thuluthayi allayli wanisfahu wathuluthahu wataifatun mina allatheena maʿaka waAllahu yuqaddiru allayla waalnnahara ʿalima an lan tuhsoohu fataba ʿalaykum faiqraoo ma tayassara mina alqurani ʿalima an sayakoonu minkum marda waakharoona yadriboona fee alardi yabtaghoona min fadli Allahi waakharoona yuqatiloona fee sabeeli Allahi faiqraoo ma tayassara minhu waaqeemoo alssalata waatoo alzzakata waaqridoo Allaha qardan hasanan wama tuqaddimoo lianfusikum min khayrin tajidoohu ʿinda Allahi huwa khayran waaʿthama ajran waistaghfiroo Allaha inna Allaha ghafoorun raheemun

    Lalle ne, Ubangijinka Yã sani cẽwa, kai kana tsayuwa a kusan kashi biyu daga uku na dare, da rabinsa, da sulusinsa, tãre da wani ɓangare na waɗanda ke tãre da kai. Allah Yake iya ƙaddara dare da yini, Ya san bã zã ku iya lissafa shi ba, sabõda haka Ya karɓi tubarku sai, ku karanta abin da ya sauƙaƙa na Alƙur'ãni. Ya san wasu daga cikinku, zã su yi cĩwo, kuma wasu zã su yi tafiya cikin ƙasa suna nẽman falalar Allah da fatauci, kuma wasu zã su yi yãƙi a cikin banyar Allah. Sabõda haka ku karanta abin da ya sauƙaƙa daga gare shi, kuma ku tsai da salla kuma ku bãyar da zakka, kumaa ku bai wa Allah rance, rance mai kyãwo. Kuma abin da kuka gabatar dõmin kanku, na alhẽri, zã ku sãme shi a wurin Allah zai kasance mafifici (daga wanda kuka ajiye) kuma zai fi girma ga sakamako, kuma ku rõƙi Allah gãfara; lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.

Tambayoyin da ake yawan yi

Mece ce ma’anar sunan Suratul Muzzammil?

Ma’anar Muzzammil ita ce “Mai lulluɓewa”.

Suratul Muzzammil tana cikin juz’i na nawa?

Suratul Muzzammil tana cikin juz’i na 29.

Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Muzzammil?

Suratul Muzzammil tana da ayoyi 20.

Suratul Muzzammil Makkiya ce ko Madaniya?

Suratul Muzzammil sura ce Makkiya.

Suratul Muzzammil ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?

Ita ce sura ta 73 a cikin Alƙur’ani.

Majiyoyi

  • Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
  • Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
  • Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
  • Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
  • Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
  • Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.

Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.

Saitunan karatu

Rubutun Alƙur’ani
Girman Larabci
100%
Girman fassara
100%
Kamanni

Ƙara zuwa Allon Gida

ReadSurahBuɗe ReadSurah daga allon gida, a cikakken allo. Surorin da kuka karanta suna buɗewa ko da babu intanet.

  1. A cikin Safari, taɓa maɓallin “Share”. A sababbin iPhone yana cikin menu na •••.
  2. Taɓa “Add to Home Screen”. Gungura ƙasa idan ba ku gan shi ba.
  3. Taɓa “Add”.