سورة المعارج
Suratul Ma’arij da fassarar Hausa
Matakan hawa
- 70
- ayoyi 44
- Makkiya
- Juz’i 29
- Shafuka 568–570
Suratul Ma’arij (المعارج) ita ce sura ta 70 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 44. Ma’anar sunanta ita ce “Matakan hawa”. Sura ce Makkiya, wadda ta sauka a Makka kafin Hijira, kuma tana cikin juz’i na 29.
A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Ma’arij gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.
Suratul Ma’arij cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ
-
سَأَلَ سَآئِلٌۢ بِعَذَابٍ وَاقِعٍ١
Saala sailun biʿathabin waqiʿin
Wani mai tambaya yã yi tambaya game da azãba, mai aukuwa.
-
لِّلْكَـٰفِرِينَ لَيْسَ لَهُۥ دَافِعٌ٢
Lilkafireena laysa lahu dafiʿun
Ga kãfirai, bã ta da mai tunkuɗẽwa.
-
مِّنَ ٱللَّهِ ذِى ٱلْمَعَارِجِ٣
Mina Allahi thee almaʿariji
Daga Allah Mai matãkala.
-
تَعْرُجُ ٱلْمَلَـٰٓئِكَةُ وَٱلرُّوحُ إِلَيْهِ فِى يَوْمٍ كَانَ مِقْدَارُهُۥ خَمْسِينَ أَلْفَ سَنَةٍ٤
Taʿruju almalaikatu waalrroohu ilayhi fee yawmin kana miqdaruhu khamseena alfa sanatin
Malã'iku da Ruhi (Jibrila) sunã tãkãwa zuwa gare Shi, a cikin yini wanda gwargwadonsa, shẽkara dubu hamsin ne.
-
فَٱصْبِرْ صَبْرًا جَمِيلًا٥
Faisbir sabran jameelan
Sabõda haka, ka yi haƙuri, haƙuri mai kyãwo.
-
إِنَّهُمْ يَرَوْنَهُۥ بَعِيدًا٦
Innahum yarawnahu baʿeedan
Lalle ne su, sunã ganin ta mai nĩsa.
-
وَنَرَىٰهُ قَرِيبًا٧
Wanarahu qareeban
Kuma Mu, Muna ganin ta a kusa.
-
يَوْمَ تَكُونُ ٱلسَّمَآءُ كَٱلْمُهْلِ٨
Yawma takoonu alssamao kaalmuhli
Rãnar da sama zã ta kasance kamar narkakkar azurfa.
-
وَتَكُونُ ٱلْجِبَالُ كَٱلْعِهْنِ٩
Watakoonu aljibalu kaalʿihni
Kuma duwãtsu su zama kamar saɓin sũfi.
-
وَلَا يَسْـَٔلُ حَمِيمٌ حَمِيمًا١٠
Wala yasalu hameemun hameeman
Kuma abõki bã ya tambayar inda wani abõki yake.
-
يُبَصَّرُونَهُمْ ۚ يَوَدُّ ٱلْمُجْرِمُ لَوْ يَفْتَدِى مِنْ عَذَابِ يَوْمِئِذٍۭ بِبَنِيهِ١١
Yubassaroonahum yawaddu almujrimu law yaftadee min ʿathabi yawmiithin bibaneehi
Ana sanya su, su gajũna, mai laifi na gũrin dã zai iya yin fansa, daga azãbar rãnar nan, da ɗiyansa,
-
وَصَـٰحِبَتِهِۦ وَأَخِيهِ١٢
Wasahibatihi waakheehi
Da matarsa da ɗan'uwansa.
-
وَفَصِيلَتِهِ ٱلَّتِى تُـْٔوِيهِ١٣
Wafaseelatihi allatee tuweehi
Da danginsa, mãsu tattarã shi.
-
وَمَن فِى ٱلْأَرْضِ جَمِيعًا ثُمَّ يُنجِيهِ١٤
Waman fee alardi jameeʿan thumma yunjeehi
Da wanda ke a cikin dũniya duka gabã ɗaya, sa'an nan fansar, ta tsĩrar da shi.
-
كَلَّآ ۖ إِنَّهَا لَظَىٰ١٥
Kalla innaha latha
A'aha! Lalle ne fa, ita ce Lazã,
-
نَزَّاعَةً لِّلشَّوَىٰ١٦
Nazzaʿatan lilshshawa
Mai twãle fãtar goshi.
-
تَدْعُوا۟ مَنْ أَدْبَرَ وَتَوَلَّىٰ١٧
Tadʿoo man adbara watawalla
Tanã kiran wanda ya jũya bãya (daga addini) kuma ya kau da kai.
-
وَجَمَعَ فَأَوْعَىٰٓ١٨
Wajamaʿa faawʿa
Ya tãra (dũkiya), kuma ya sanya ta a cikin jaka.
-
۞ إِنَّ ٱلْإِنسَـٰنَ خُلِقَ هَلُوعًا١٩
Inna alinsana khuliqa halooʿan
Lalle ne mutum an halitta shi mai ciwon kwaɗayi.
-
إِذَا مَسَّهُ ٱلشَّرُّ جَزُوعًا٢٠
Itha massahu alshsharru jazooʿan
Idan sharri ya shãfe shi, ya kãsa haƙuri.
-
وَإِذَا مَسَّهُ ٱلْخَيْرُ مَنُوعًا٢١
Waitha massahu alkhayru manooʿan
Kuma idan alhẽri ya shãfe shi, ya yi rõwa.
-
إِلَّا ٱلْمُصَلِّينَ٢٢
Illa almusalleena
Sai mãsu yin salla,
-
ٱلَّذِينَ هُمْ عَلَىٰ صَلَاتِهِمْ دَآئِمُونَ٢٣
Allatheena hum ʿala salatihim daimoona
Waɗanda suke, a kan sallarsu, su, mãsu dawwama ne.
-
وَٱلَّذِينَ فِىٓ أَمْوَٰلِهِمْ حَقٌّ مَّعْلُومٌ٢٤
Waallatheena fee amwalihim haqqun maʿloomun
Kuma waɗanda a cikin dũkiyarsu, akwai wani haƙƙi sananne.
-
لِّلسَّآئِلِ وَٱلْمَحْرُومِ٢٥
Lilssaili waalmahroomi
Ga (matalauci) mai rõƙo da wanda aka hanã wa roƙon.
-
وَٱلَّذِينَ يُصَدِّقُونَ بِيَوْمِ ٱلدِّينِ٢٦
Waallatheena yusaddiqoona biyawmi alddeeni
Da waɗannan da ke gaskata rãnar sakamako.
-
وَٱلَّذِينَ هُم مِّنْ عَذَابِ رَبِّهِم مُّشْفِقُونَ٢٧
Waallatheena hum min ʿathabi rabbihim mushfiqoona
Da waɗannan sabõda azãbar Ubangijinsu, suna jin tsõro.
-
إِنَّ عَذَابَ رَبِّهِمْ غَيْرُ مَأْمُونٍ٢٨
Inna ʿathaba rabbihim ghayru mamoonin
Lalle ne, azãbar Ubangijinsu bã wadda ake iya amincẽwaba ce.
-
وَٱلَّذِينَ هُمْ لِفُرُوجِهِمْ حَـٰفِظُونَ٢٩
Waallatheena hum lifuroojihim hafithoona
Da waɗanda suke, ga farjojinsu, mãsu tsarewa ne.
-
إِلَّا عَلَىٰٓ أَزْوَٰجِهِمْ أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَـٰنُهُمْ فَإِنَّهُمْ غَيْرُ مَلُومِينَ٣٠
Illa ʿala azwajihim aw ma malakat aymanuhum fainnahum ghayru maloomeena
Sai fa a kan matan aurensu da abin da hannayensu na dãma suka mallaka. To lalle ne sũkam ba waɗanda ake zargi ba ne.
-
فَمَنِ ٱبْتَغَىٰ وَرَآءَ ذَٰلِكَ فَأُو۟لَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلْعَادُونَ٣١
Famani ibtagha waraa thalika faolaika humu alʿadoona
To, duk wanda ya nẽmi abin da yake a bayan wannan, to, waɗancan sũ ne mãsu ƙetare iyãka.
-
وَٱلَّذِينَ هُمْ لِأَمَـٰنَـٰتِهِمْ وَعَهْدِهِمْ رَٰعُونَ٣٢
Waallatheena hum liamanatihim waʿahdihim raʿoona
Kuma da waɗannan da suke ga amãnõninsu da alkawarinsu mãsu tsarẽwa ne.
-
وَٱلَّذِينَ هُم بِشَهَـٰدَٰتِهِمْ قَآئِمُونَ٣٣
Waallatheena hum bishahadatihim qaimoona
Kuma da waɗanda suke, ga shaidarsu, mãsu dãgẽwa ne.
-
وَٱلَّذِينَ هُمْ عَلَىٰ صَلَاتِهِمْ يُحَافِظُونَ٣٤
Waallatheena hum ʿala salatihim yuhafithoona
Kuma waɗanda suke, a kan sallarsu, mãsu tsarẽwa ne.
-
أُو۟لَـٰٓئِكَ فِى جَنَّـٰتٍ مُّكْرَمُونَ٣٥
Olaika fee jannatin mukramoona
Waɗannan, a cikin gidãjen Aljanna, waɗanda ake girmamãwa ne
-
فَمَالِ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ قِبَلَكَ مُهْطِعِينَ٣٦
Famali allatheena kafaroo qibalaka muhtiʿeena
Mẽ yã sãmi waɗanda suka kãfirta, a wajenka, sunã gaugãwar (gudu).
-
عَنِ ٱلْيَمِينِ وَعَنِ ٱلشِّمَالِ عِزِينَ٣٧
ʿAni alyameeni waʿani alshshimali ʿizeena
Daga jihar dãma, kuma daga jihar hagu, jama'a-jama'a!
-
أَيَطْمَعُ كُلُّ ٱمْرِئٍ مِّنْهُمْ أَن يُدْخَلَ جَنَّةَ نَعِيمٍ٣٨
Ayatmaʿu kullu imriin minhum an yudkhala jannata naʿeemin
Shin kõwane mutum daga cikinsu yana nẽman a shigar da shi a Aljannar ni'ima ne (ba da wani aiki ba)?
-
كَلَّآ ۖ إِنَّا خَلَقْنَـٰهُم مِّمَّا يَعْلَمُونَ٣٩
Kalla inna khalaqnahum mimma yaʿlamoona
A'aha! Lalle Mũ, Mun halitta su, daga abin da suka sani.
-
فَلَآ أُقْسِمُ بِرَبِّ ٱلْمَشَـٰرِقِ وَٱلْمَغَـٰرِبِ إِنَّا لَقَـٰدِرُونَ٤٠
Fala oqsimu birabbi almashariqi waalmagharibi inna laqadiroona
Sabõda haka ba sai Na yi rantsuwa da Ubangijin wurãren ɓullõwar rãna da wurãren fãɗuwarta ba, lalle Mũ, Mãsu iyãwa ne.
-
عَلَىٰٓ أَن نُّبَدِّلَ خَيْرًا مِّنْهُمْ وَمَا نَحْنُ بِمَسْبُوقِينَ٤١
ʿAla an nubaddila khayran minhum wama nahnu bimasbooqeena
Ga Mu musanya waɗanda suke mafi alhẽri, daga gare su. Kuma ba Mu kasance waɗanda ake rinjãya ba.
-
فَذَرْهُمْ يَخُوضُوا۟ وَيَلْعَبُوا۟ حَتَّىٰ يُلَـٰقُوا۟ يَوْمَهُمُ ٱلَّذِى يُوعَدُونَ٤٢
Fatharhum yakhoodoo wayalʿaboo hatta yulaqoo yawmahumu allathee yooʿadoona
Sabõda haka ka bar su, su dulmuya, kuma su yi wãsã, har su haɗu da rãnarsu wadda ake yi musu alkawari (da ita).
-
يَوْمَ يَخْرُجُونَ مِنَ ٱلْأَجْدَاثِ سِرَاعًا كَأَنَّهُمْ إِلَىٰ نُصُبٍ يُوفِضُونَ٤٣
Yawma yakhrujoona mina alajdathi siraʿan kaannahum ila nusubin yoofidoona
Rãnar da suke fitowa daga kaburbura da gaugãwa, kamar sũ, zuwa ga wata kafaffiyar (tuta), suke yin gaugãwa.
-
خَـٰشِعَةً أَبْصَـٰرُهُمْ تَرْهَقُهُمْ ذِلَّةٌ ۚ ذَٰلِكَ ٱلْيَوْمُ ٱلَّذِى كَانُوا۟ يُوعَدُونَ٤٤
Khashiʿatan absaruhum tarhaquhum thillatun thalika alyawmu allathee kanoo yooʿadoona
Maƙaskanta ga idanunsu, wani walakanci yana rufe su. wannan shi ne yinin da suka kasance ana yi musa alkawari (a kansa.)
Tambayoyin da ake yawan yi
Mece ce ma’anar sunan Suratul Ma’arij?
Ma’anar Ma’arij ita ce “Matakan hawa”.
Suratul Ma’arij tana cikin juz’i na nawa?
Suratul Ma’arij tana cikin juz’i na 29.
Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Ma’arij?
Suratul Ma’arij tana da ayoyi 44.
Suratul Ma’arij Makkiya ce ko Madaniya?
Suratul Ma’arij sura ce Makkiya.
Suratul Ma’arij ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?
Ita ce sura ta 70 a cikin Alƙur’ani.
Majiyoyi
- Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
- Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
- Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
- Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
- Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
- Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.
Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.