سورة التحريم
Suratul Tahrim da fassarar Hausa
Haramtawa
- 66
- ayoyi 12
- Madaniya
- Juz’i 28
- Shafuka 560–561
Suratul Tahrim (التحريم) ita ce sura ta 66 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 12. Ma’anar sunanta ita ce “Haramtawa”. Sura ce Madaniya, wadda ta sauka a Madina bayan Hijira, kuma tana cikin juz’i na 28.
A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Tahrim gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.
Suratul Tahrim cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ
-
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِىُّ لِمَ تُحَرِّمُ مَآ أَحَلَّ ٱللَّهُ لَكَ ۖ تَبْتَغِى مَرْضَاتَ أَزْوَٰجِكَ ۚ وَٱللَّهُ غَفُورٌ رَّحِيمٌ١
Ya ayyuha alnnabiyyu lima tuharrimu ma ahalla Allahu laka tabtaghee mardata azwajika waAllahu ghafoorun raheemun
Yã kai Annabi! Don me kake haramta abin da Allah Ya halatta maka,1 kanã nẽman yardar mãtanka, alhãli kuwa Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
Bayanai
[1] A cikin littãfin Buhãri an ruwaito daga A'isha, mãtar Annabi, cewa Annabi, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gareshi, yakan yi jinkiri a wajen Zainab bint Jahsh dõmin ya shã zuma a wurinta. Ta ce: "Sai na shirya, nĩ da Hafsah: Duk wadda Manzon Allah ya shiga gurinta daga garemu, ta ce masa, 'Ina jin wãrin tsimi daga gareka! Kã ci tsimi! To, sai Annabi ya shiga ga ɗayansu, ta ce masa: "Kã ci tsimi." Ya ce: "A'isha! Nã shã zuma dai a wurin Zainab bint Jahsh, kuma ba zan kõma gareshi ba." Asalin abin, Annabi tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi,yã kasance yanã zagayãwa a gidãjen mãtansa a bãyan sallar la'asar dõmin ya gaishe su. To, sai ya sh ga ga Hafsah bãyan ya shiga ga Zainab, ta gaya masa haka. Kuma ya gaya mata nĩsantarsa ga zuma, kuma ya gaya mata lãbãrin cewa Abubakar da Umar, Allah Ya yarda da su, za su zama halĩfai a bãyansa. To, sai ta faɗi waɗannan lãbãru ga maƙwabciyarta A'isha. Wannan Ƙissa tana koyar da sauƙin halin Annabi a game da iyãlansa, da girmamawarsa a gare su. -
قَدْ فَرَضَ ٱللَّهُ لَكُمْ تَحِلَّةَ أَيْمَـٰنِكُمْ ۚ وَٱللَّهُ مَوْلَىٰكُمْ ۖ وَهُوَ ٱلْعَلِيمُ ٱلْحَكِيمُ٢
Qad farada Allahu lakum tahillata aymanikum waAllahu mawlakum wahuwa alʿaleemu alhakeemu
Haƙĩƙa Allah ya faralta muku warware1 rantsuwõyinku, kuma Allah ne Mataimakinku kuma shĩ ne Masani, Mai hikima.
Bayanai
[1] An rubũta yadda ake warware rantsuwa da kaffãra wadda aka ambata a cikin sũra ta 5, ãyã ta 89. Anã kaffãrar rantsuwa da ciyar da miskĩnai gõma daga matsakaicin abinci, mũdu biyu ga kõwane, kõ tufãtar da su tufar da za ta ishe su salla, idan bai sãmu ba, ya yi azumin kwãna uku. -
وَإِذْ أَسَرَّ ٱلنَّبِىُّ إِلَىٰ بَعْضِ أَزْوَٰجِهِۦ حَدِيثًا فَلَمَّا نَبَّأَتْ بِهِۦ وَأَظْهَرَهُ ٱللَّهُ عَلَيْهِ عَرَّفَ بَعْضَهُۥ وَأَعْرَضَ عَنۢ بَعْضٍ ۖ فَلَمَّا نَبَّأَهَا بِهِۦ قَالَتْ مَنْ أَنۢبَأَكَ هَـٰذَا ۖ قَالَ نَبَّأَنِىَ ٱلْعَلِيمُ ٱلْخَبِيرُ٣
Waith asarra alnnabiyyu ila baʿdi azwajihi hadeethan falamma nabbaat bihi waathharahu Allahu ʿalayhi ʿarrafa baʿdahu waaʿrada ʿan baʿdin falamma nabbaaha bihi qalat man anbaaka hatha qala nabbaaniya alʿaleemu alkhabeeru
Kuma a sã'ilin da Annabi ya asirta wani lãbãri zuwa ga sãshen mãtansa, to, a lõkacin da ta bã da lãbari da shi. Kuma Allah Ya bayyana shi a gare shi, ya sanar da sãshensa kuma ya kau da kai daga wani sãshe. To, a lõkacin da ya bã ta lãbãri da shi, ta ce: "Wãne ne ya gaya maka wannan?" Ya ce: "Masani, Mai labartãwa, Ya gaya mini."
-
إِن تَتُوبَآ إِلَى ٱللَّهِ فَقَدْ صَغَتْ قُلُوبُكُمَا ۖ وَإِن تَظَـٰهَرَا عَلَيْهِ فَإِنَّ ٱللَّهَ هُوَ مَوْلَىٰهُ وَجِبْرِيلُ وَصَـٰلِحُ ٱلْمُؤْمِنِينَ ۖ وَٱلْمَلَـٰٓئِكَةُ بَعْدَ ذَٰلِكَ ظَهِيرٌ٤
In tatooba ila Allahi faqad saghat quloobukuma wain tathahara ʿalayhi fainna Allaha huwa mawlahu wajibreelu wasalihu almumineena waalmalaikatu baʿda thalika thaheerun
Idan kũ biyu kuka tũba zuwa ga Allah, to, haƙĩƙa zukãtanku sun karkata. Kuma idan kun taimaki jũna a kansa to, lalle Allah Shĩ ne Mataimakinsa, da Jibrĩlu da sãlihan mũminai. Kuma malã'iku a bãyan wancan, mataimaka ne.
-
عَسَىٰ رَبُّهُۥٓ إِن طَلَّقَكُنَّ أَن يُبْدِلَهُۥٓ أَزْوَٰجًا خَيْرًا مِّنكُنَّ مُسْلِمَـٰتٍ مُّؤْمِنَـٰتٍ قَـٰنِتَـٰتٍ تَـٰٓئِبَـٰتٍ عَـٰبِدَٰتٍ سَـٰٓئِحَـٰتٍ ثَيِّبَـٰتٍ وَأَبْكَارًا٥
ʿAsa rabbuhu in tallaqakunna an yubdilahu azwajan khayran minkunna muslimatin muminatin qanitatin taibatin ʿabidatin saihatin thayyibatin waabkaran
Mai yiwuwa ne Ubangijinsa, idan ya sake ku, Ya musanya masa waɗansu mãtan aure mafiya alhẽri daga gare ku, Musulmai mũminai mãsu tawãli'u, mãsu tũba, mãsu ibãda, mãsu, azumi, zawarõri da 'yammãta.
-
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ قُوٓا۟ أَنفُسَكُمْ وَأَهْلِيكُمْ نَارًا وَقُودُهَا ٱلنَّاسُ وَٱلْحِجَارَةُ عَلَيْهَا مَلَـٰٓئِكَةٌ غِلَاظٌ شِدَادٌ لَّا يَعْصُونَ ٱللَّهَ مَآ أَمَرَهُمْ وَيَفْعَلُونَ مَا يُؤْمَرُونَ٦
Ya ayyuha allatheena amanoo qoo anfusakum waahleekum naran waqooduha alnnasu waalhijaratu ʿalayha malaikatun ghilathun shidadun la yaʿsoona Allaha ma amarahum wayafʿaloona ma yumaroona
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kãre wa kanku1 (da iyãlinku wata wuta makãmashinta mutãne da duwãtsu ne. A kanta akwai waɗansu malã'iku mãsu kauri, mãsu ƙarfi. Bã su sãɓã wa Allah ga abin da Ya umarce su, kuma sunã aikata abin da ake umarnin su.
Bayanai
[1] Tsare kai da iyãli daga wuta yanã sãmuwa da shiryar da su da karãtu da nasiha a kan addini. Wannan yanã a cikin kyawun zamantakewa wanda sũrar ke karantarwa. -
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ لَا تَعْتَذِرُوا۟ ٱلْيَوْمَ ۖ إِنَّمَا تُجْزَوْنَ مَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ٧
Ya ayyuha allatheena kafaroo la taʿtathiroo alyawma innama tujzawna ma kuntum taʿmaloona
Yã kũ waɗanda suka kãfirta!1 Kada ku kãwo wani uzuri a yau. Anã yi muku sakamakon abin da kuka kasance kunã aikatãwa kawai ne.
Bayanai
[1] Kãfirai a nan, kafircinsu sabõda ƙin bin umurnin Allah game da kyawun zamantakewa da iyali yake. Laifinsu yã fi sauran laifuffuka dõmin yanã sabbaba yãmutsi a gida, har abin ya shãfi zurriya da ƙasã gabã ɗaya. -
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ تُوبُوٓا۟ إِلَى ٱللَّهِ تَوْبَةً نَّصُوحًا عَسَىٰ رَبُّكُمْ أَن يُكَفِّرَ عَنكُمْ سَيِّـَٔاتِكُمْ وَيُدْخِلَكُمْ جَنَّـٰتٍ تَجْرِى مِن تَحْتِهَا ٱلْأَنْهَـٰرُ يَوْمَ لَا يُخْزِى ٱللَّهُ ٱلنَّبِىَّ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ مَعَهُۥ ۖ نُورُهُمْ يَسْعَىٰ بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَبِأَيْمَـٰنِهِمْ يَقُولُونَ رَبَّنَآ أَتْمِمْ لَنَا نُورَنَا وَٱغْفِرْ لَنَآ ۖ إِنَّكَ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍ قَدِيرٌ٨
Ya ayyuha allatheena amanoo tooboo ila Allahi tawbatan nasoohan ʿasa rabbukum an yukaffira ʿankum sayyiatikum wayudkhilakum jannatin tajree min tahtiha alanharu yawma la yukhzee Allahu alnnabiyya waallatheena amanoo maʿahu nooruhum yasʿa bayna aydeehim wabiaymanihim yaqooloona rabbana atmim lana noorana waighfir lana innaka ʿala kulli shayin qadeerun
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kõma zuwa ga Allah kõmawar gaskiya. Mai yiwuwa Ubangjinku Ya kankare muku miyãgun ayyukanku kuma Ya shigar da ku a gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu a rãnar da Allah bã Ya kunyatar da Annabi1da wadanda suka yi ĩmãni tãre da shi. Haskensu yanã tafiya a gaba gare su da jihõhin dãmansu, sunã cẽwa, "Yã Ubangijiumu! Ka cika mana haskenmu, kuma Ka yi mana gãfara. Lalle Kai, a kan dukkan kõme, Yã kai Mai ikon yi ne."
Bayanai
[1] Allah Yã yi alkawarin bã zai kunyatar da AnnabinSa ba, haka kuma waɗanda sukayi ĩmãni tãre da shi, watau sahabbansa a Rãnar Kiyãma. Wannan shĩ ne dalĩlin da ya sa Allah Ya tsare Annabi da Sahabbansa daga bauta musu kamar yadda aka bautã wa waɗansu Annabãwa da Sãlihai waɗanda Allah zai tambaye su kõ sũ ne suka yi umurni da a yi musu bautar, sũ kuma su faɗi barrantarsu daga waɗanda suka bauta musu. -
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِىُّ جَـٰهِدِ ٱلْكُفَّارَ وَٱلْمُنَـٰفِقِينَ وَٱغْلُظْ عَلَيْهِمْ ۚ وَمَأْوَىٰهُمْ جَهَنَّمُ ۖ وَبِئْسَ ٱلْمَصِيرُ٩
Ya ayyuha alnnabiyyu jahidi alkuffara waalmunafiqeena waoghluth ʿalayhim wamawahum jahannamu wabisa almaseeru
Yã kai Annabi! Ka yãki kãfirai da munãfwkai. Kuma ka tsananta a kansu. Kuma matattararsu Jahannama ce, kuma tir da makoma, ita.
-
ضَرَبَ ٱللَّهُ مَثَلًا لِّلَّذِينَ كَفَرُوا۟ ٱمْرَأَتَ نُوحٍ وَٱمْرَأَتَ لُوطٍ ۖ كَانَتَا تَحْتَ عَبْدَيْنِ مِنْ عِبَادِنَا صَـٰلِحَيْنِ فَخَانَتَاهُمَا فَلَمْ يُغْنِيَا عَنْهُمَا مِنَ ٱللَّهِ شَيْـًٔا وَقِيلَ ٱدْخُلَا ٱلنَّارَ مَعَ ٱلدَّٰخِلِينَ١٠
Daraba Allahu mathalan lillatheena kafaroo imraata noohin waimraata lootin kanata tahta ʿabdayni min ʿibadina salihayni fakhanatahuma falam yughniya ʿanhuma mina Allahi shayan waqeela odkhula alnnara maʿa alddakhileena
Allah Ya buga wani misãli dõmin waɗanda suka kãfirta1: mãtar Nũhu da mãtar Lũɗu, sun kasance a ƙarƙashin wasu bãyi biyu daga bãyin Mu sãlihai, sai suka yaudare su, sabõda haka ba su wadãtar musu da kõme daga Allah ba. Kuma aka ce: "Ku shiga, kũ biyu, wutã tãre da mãsu shiga."
Bayanai
[1] Waɗannan misãlai biyu,mãtar Nũhu da mãtar Lũɗu sunã nũna kusanci ga sãlihai bã ya isa ga addini sai kõwa ya yi abin da Allah Ya yi umurni da shi. Kuma anã kallafa wa mãtã da su kiyãye kyawun zamantakewa da mazansu. Kuma anã yi musu azãba sabõda sãɓa wa Allah ga barin haka kamar yadda ake ga mazansu. -
وَضَرَبَ ٱللَّهُ مَثَلًا لِّلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ ٱمْرَأَتَ فِرْعَوْنَ إِذْ قَالَتْ رَبِّ ٱبْنِ لِى عِندَكَ بَيْتًا فِى ٱلْجَنَّةِ وَنَجِّنِى مِن فِرْعَوْنَ وَعَمَلِهِۦ وَنَجِّنِى مِنَ ٱلْقَوْمِ ٱلظَّـٰلِمِينَ١١
Wadaraba Allahu mathalan lillatheena amanoo imraata firʿawna ith qalat rabbi ibni lee ʿindaka baytan fee aljannati wanajjinee min firʿawna waʿamalihi wanajjinee mina alqawmi alththalimeena
Kuma Allah Ya buga wani misãli dõmin waɗanda suka yi ĩmãni; matar Fir'auna,1 sa'ad da ta ce "Ya Ubangiji! Ka gina mini wani gida a wurin Ka a cikin Aljanna. Kuma Ka tsĩrar da ni daga Fir'auna da aikinsa. Kuma Ka tsĩrar da ni daga mutãnen nan azzãlumai."
Bayanai
[1] Wannan yanã nũna cewa kusantar kãfiri bã zai cũci mũminai ba. Sai dai Allah Yã hana aure a tsakãnin Musulma da kãfiri. -
وَمَرْيَمَ ٱبْنَتَ عِمْرَٰنَ ٱلَّتِىٓ أَحْصَنَتْ فَرْجَهَا فَنَفَخْنَا فِيهِ مِن رُّوحِنَا وَصَدَّقَتْ بِكَلِمَـٰتِ رَبِّهَا وَكُتُبِهِۦ وَكَانَتْ مِنَ ٱلْقَـٰنِتِينَ١٢
Wamaryama ibnata ʿimrana allatee ahsanat farjaha fanafakhna feehi min roohina wasaddaqat bikalimati rabbiha wakutubihi wakanat mina alqaniteena
Da Maryama1 ɗiyar Imrãna wadda ta tsare farjinta, sai Muka hũra a cikinsa daga rũhinMu. Kuma ta gaskata game da ãyõyin Ubangijinta da Littattafan Sa alhãli kuwa ta kasance daga mãsu tawãli'u.
Bayanai
[1] Wannan yanã nũna cewa rashin aure ga mãtar da ke iya tsare farjinta daga alfãsha kuma ta tsare addininta da taƙawa, bã zai cũce ta ba ga sãmun rahamar Allah a dũniya da lãhira.
Tambayoyin da ake yawan yi
Mece ce ma’anar sunan Suratul Tahrim?
Ma’anar Tahrim ita ce “Haramtawa”.
Suratul Tahrim tana cikin juz’i na nawa?
Suratul Tahrim tana cikin juz’i na 28.
Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Tahrim?
Suratul Tahrim tana da ayoyi 12.
Suratul Tahrim Makkiya ce ko Madaniya?
Suratul Tahrim sura ce Madaniya.
Suratul Tahrim ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?
Ita ce sura ta 66 a cikin Alƙur’ani.
Majiyoyi
- Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
- Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
- Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
- Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
- Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
- Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.
Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.