سورة المنافقون

Suratul Munafiƙun da fassarar Hausa

Munafukai

Mushafi

Mishary Rashid AlafasySauke MP3Sauke PDF

Suratul Munafiƙun (المنافقون) ita ce sura ta 63 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 11. Ma’anar sunanta ita ce “Munafukai”. Sura ce Madaniya, wadda ta sauka a Madina bayan Hijira, kuma tana cikin juz’i na 28.

A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Munafiƙun gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.

Suratul Munafiƙun cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. إِذَا جَآءَكَ ٱلْمُنَـٰفِقُونَ قَالُوا۟ نَشْهَدُ إِنَّكَ لَرَسُولُ ٱللَّهِ ۗ وَٱللَّهُ يَعْلَمُ إِنَّكَ لَرَسُولُهُۥ وَٱللَّهُ يَشْهَدُ إِنَّ ٱلْمُنَـٰفِقِينَ لَكَـٰذِبُونَ۝١

    Itha jaaka almunafiqoona qaloo nashhadu innaka larasoolu Allahi waAllahu yaʿlamu innaka larasooluhu waAllahu yashhadu inna almunafiqeena lakathiboona

    Idan munãfukai1 suka jẽ maka suka ce: "Munẽ shaidar lalle kai haƙĩƙa Manzon Allah ne," Kuma Allah Yanã sane da lalle Kai, haƙĩƙa Manzon Sa ne, kuma Allah Yanã shaida lalle munafukan haƙĩƙa, maƙaryata ne.

    Bayanai
    [1] Munãfuki, a zãmanin Annabi, shine wanda ya bayyana Musulunci, amma kuma a ɓõye Shĩ kãfiri ne. A bãyan Annabi anã cewa munãfuki zindĩƙi.
  2. ٱتَّخَذُوٓا۟ أَيْمَـٰنَهُمْ جُنَّةً فَصَدُّوا۟ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ ۚ إِنَّهُمْ سَآءَ مَا كَانُوا۟ يَعْمَلُونَ۝٢

    Ittakhathoo aymanahum junnatan fasaddoo ʿan sabeeli Allahi innahum saa ma kanoo yaʿmaloona

    Sun riƙi rantsuwõwinsu garkuwa, sai suka taushe daga tafarkin Allah. Lalle sũ abin da suka kasance sunã aikatãwa ya mũnana.

  3. ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمْ ءَامَنُوا۟ ثُمَّ كَفَرُوا۟ فَطُبِعَ عَلَىٰ قُلُوبِهِمْ فَهُمْ لَا يَفْقَهُونَ۝٣

    Thalika biannahum amanoo thumma kafaroo fatubiʿa ʿala quloobihim fahum la yafqahoona

    Wancan, dõmin lalle sũ, sun yi ĩmãni, sa'an nan kuma suka kãfirta, sai aka yunƙe a kan zukãtansu. Sabõda sũ, bã su fahimta.

  4. ۞ وَإِذَا رَأَيْتَهُمْ تُعْجِبُكَ أَجْسَامُهُمْ ۖ وَإِن يَقُولُوا۟ تَسْمَعْ لِقَوْلِهِمْ ۖ كَأَنَّهُمْ خُشُبٌ مُّسَنَّدَةٌ ۖ يَحْسَبُونَ كُلَّ صَيْحَةٍ عَلَيْهِمْ ۚ هُمُ ٱلْعَدُوُّ فَٱحْذَرْهُمْ ۚ قَـٰتَلَهُمُ ٱللَّهُ ۖ أَنَّىٰ يُؤْفَكُونَ۝٤

    Waitha raaytahum tuʿjibuka ajsamuhum wain yaqooloo tasmaʿ liqawlihim kaannahum khushubun musannadatun yahsaboona kulla sayhatin ʿalayhim humu alʿaduwwu faihtharhum qatalahumu Allahu anna yufakoona

    Kuma idan kã gan su, sai jikunansu su bã ka sha'awa kuma idan sun faɗa,1 zã ka saurãra ga maganarsu. Kamar dai sũ ƙyami ne wanda aka jingine. Sunã zaton kõwace tsãwa a kansu take. Sũ ne maƙiyan, sai ka yi saunarsu. Allah Yã la'ane su. Yãya ake karkatar da su?

    Bayanai
    [1] Munãfukai sunã da kyawun sũrar jiki kuma sun iya magana da fasaha amma fa bã su da hankali sabõda ƙaryar da suke a kanta, sabõda haka sunã tsõron kõwane irin mõtsi ya zama a kansu.
  5. وَإِذَا قِيلَ لَهُمْ تَعَالَوْا۟ يَسْتَغْفِرْ لَكُمْ رَسُولُ ٱللَّهِ لَوَّوْا۟ رُءُوسَهُمْ وَرَأَيْتَهُمْ يَصُدُّونَ وَهُم مُّسْتَكْبِرُونَ۝٥

    Waitha qeela lahum taʿalaw yastaghfir lakum rasoolu Allahi lawwaw ruoosahum waraaytahum yasuddoona wahum mustakbiroona

    Kuma idan aka ce musu "Ku zo Manzon Allah ya nẽma maku gãfara," Sai su gyãɗa kãwunansu, kuma ka gan su sunã kangẽwa, alhãli kuwa sunã mãsu girman kai.

  6. سَوَآءٌ عَلَيْهِمْ أَسْتَغْفَرْتَ لَهُمْ أَمْ لَمْ تَسْتَغْفِرْ لَهُمْ لَن يَغْفِرَ ٱللَّهُ لَهُمْ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهْدِى ٱلْقَوْمَ ٱلْفَـٰسِقِينَ۝٦

    Sawaon ʿalayhim astaghfarta lahum am lam tastaghfir lahum lan yaghfira Allahu lahum inna Allaha la yahdee alqawma alfasiqeena

    Daidai ne a kansu, kã nẽma musu gãfara kõ ba ka nẽmamusu ba. faufau Allah bã zai gãfarta musu ba. Lalle Allah, bã zai shiryar da mutãne fãsiƙai ba.

  7. هُمُ ٱلَّذِينَ يَقُولُونَ لَا تُنفِقُوا۟ عَلَىٰ مَنْ عِندَ رَسُولِ ٱللَّهِ حَتَّىٰ يَنفَضُّوا۟ ۗ وَلِلَّهِ خَزَآئِنُ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ وَلَـٰكِنَّ ٱلْمُنَـٰفِقِينَ لَا يَفْقَهُونَ۝٧

    Humu allatheena yaqooloona la tunfiqoo ʿala man ʿinda rasooli Allahi hatta yanfaddoo walillahi khazainu alssamawati waalardi walakinna almunafiqeena la yafqahoona

    Sũ ne waɗanda ke cẽwa "Kada ku ciyar a kan wanda ke wurin Manzon Allah har su wãtse," alhali kuwa taskõkin sammai da ƙasa ga Allah suke kuma amma munãfukai bã su fahimta.

  8. يَقُولُونَ لَئِن رَّجَعْنَآ إِلَى ٱلْمَدِينَةِ لَيُخْرِجَنَّ ٱلْأَعَزُّ مِنْهَا ٱلْأَذَلَّ ۚ وَلِلَّهِ ٱلْعِزَّةُ وَلِرَسُولِهِۦ وَلِلْمُؤْمِنِينَ وَلَـٰكِنَّ ٱلْمُنَـٰفِقِينَ لَا يَعْلَمُونَ۝٨

    Yaqooloona lain rajaʿna ila almadeenati layukhrijanna alaʿazzu minha alathalla walillahi alʿizzatu walirasoolihi walilmumineena walakinna almunafiqeena la yaʿlamoona

    Sunã cẽwa "Lalle ne idan mun kõma1 zuwa Madĩnar, haƙĩƙa mafi rinjaya zai fitar da mafi ƙasƙanta daga gare ta, alhãli kuwa rinjãyar ga Allah take kuma da ManzonSa, kuma da mũminai, kuma amma munãfikai ba su sani ba."

    Bayanai
    [1] Abdullah bn Ubayyi bn Salũl ya faɗi cewa "Wallahi idan mun kõma Madĩna wanda ya fi ƙarfi, lalle zai fitar da wanda ya fi ƙasƙanci." Yanã nufin Ansãrai mutãnen Madĩna zã su kõri Muhãjirai. Yã faɗi haka a cikin wata tafiya ta jihãdi. Aka gaya wa Annabi, sai ya yi musu. Allah Ya kunyata shi.
  9. يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ لَا تُلْهِكُمْ أَمْوَٰلُكُمْ وَلَآ أَوْلَـٰدُكُمْ عَن ذِكْرِ ٱللَّهِ ۚ وَمَن يَفْعَلْ ذَٰلِكَ فَأُو۟لَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلْخَـٰسِرُونَ۝٩

    Ya ayyuha allatheena amanoo la tulhikum amwalukum wala awladukum ʿan thikri Allahi waman yafʿal thalika faolaika humu alkhasiroona

    Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada dũkiyõyinku da ɗiyanku su shagaltar da ku daga ambaton Allah. Kuma wanda ya yi haka, to, waɗannan sũ ne mãsu hasãra.

  10. وَأَنفِقُوا۟ مِن مَّا رَزَقْنَـٰكُم مِّن قَبْلِ أَن يَأْتِىَ أَحَدَكُمُ ٱلْمَوْتُ فَيَقُولَ رَبِّ لَوْلَآ أَخَّرْتَنِىٓ إِلَىٰٓ أَجَلٍ قَرِيبٍ فَأَصَّدَّقَ وَأَكُن مِّنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ۝١٠

    Waanfiqoo min ma razaqnakum min qabli an yatiya ahadakumu almawtu fayaqoola rabbi lawla akhkhartanee ila ajalin qareebin faassaddaqa waakun mina alssaliheena

    Kuma ku ciyar daga abin da Muka azurta ku daga gãbanin mutuwa ta je wa ɗayanku har ya ce: "Yã Ubangijina! Don me ba Ka yi mini jinkiri ba zuwa ga wani ajali makusanci dõmin in gaskata kuma in kasance daga sãlihai?"

  11. وَلَن يُؤَخِّرَ ٱللَّهُ نَفْسًا إِذَا جَآءَ أَجَلُهَا ۚ وَٱللَّهُ خَبِيرٌۢ بِمَا تَعْمَلُونَ۝١١

    Walan yuakhkhira Allahu nafsan itha jaa ajaluha waAllahu khabeerun bima taʿmaloona

    Kuma Allah bã zai jinkirta wa wani rai ba idan ajalinsa ya je. Kuma Allah Masani ne ga abin da suke aikatãwa.

Tambayoyin da ake yawan yi

Mece ce ma’anar sunan Suratul Munafiƙun?

Ma’anar Munafiƙun ita ce “Munafukai”.

Suratul Munafiƙun tana cikin juz’i na nawa?

Suratul Munafiƙun tana cikin juz’i na 28.

Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Munafiƙun?

Suratul Munafiƙun tana da ayoyi 11.

Suratul Munafiƙun Makkiya ce ko Madaniya?

Suratul Munafiƙun sura ce Madaniya.

Suratul Munafiƙun ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?

Ita ce sura ta 63 a cikin Alƙur’ani.

Majiyoyi

  • Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
  • Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
  • Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
  • Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
  • Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
  • Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.

Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.

Saitunan karatu

Rubutun Alƙur’ani
Girman Larabci
100%
Girman fassara
100%
Kamanni

Ƙara zuwa Allon Gida

ReadSurahBuɗe ReadSurah daga allon gida, a cikakken allo. Surorin da kuka karanta suna buɗewa ko da babu intanet.

  1. A cikin Safari, taɓa maɓallin “Share”. A sababbin iPhone yana cikin menu na •••.
  2. Taɓa “Add to Home Screen”. Gungura ƙasa idan ba ku gan shi ba.
  3. Taɓa “Add”.