سورة المجادلة
Suratul Mujadila da fassarar Hausa
Mai jayayya
- 58
- ayoyi 22
- Madaniya
- Juz’i 28
- Shafuka 542–545
Suratul Mujadila (المجادلة) ita ce sura ta 58 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 22. Ma’anar sunanta ita ce “Mai jayayya”. Sura ce Madaniya, wadda ta sauka a Madina bayan Hijira, kuma tana cikin juz’i na 28.
A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Mujadila gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.
Suratul Mujadila cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ
-
قَدْ سَمِعَ ٱللَّهُ قَوْلَ ٱلَّتِى تُجَـٰدِلُكَ فِى زَوْجِهَا وَتَشْتَكِىٓ إِلَى ٱللَّهِ وَٱللَّهُ يَسْمَعُ تَحَاوُرَكُمَآ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَمِيعٌۢ بَصِيرٌ١
Qad samiʿa Allahu qawla allatee tujadiluka fee zawjiha watashtakee ila Allahi waAllahu yasmaʿu tahawurakuma inna Allaha sameeʿun baseerun
Lalle Alla Ya ji maganar1 wadda ke yi maka jãyayya game da mijinta, tanã kai ƙãra ga Allah, kuma Allah nã jin muhawararku. Lalle Allah Mai ji ne, Mai gani.
Bayanai
[1] Wannan ƙissa tanã nũna cewa a Majalisar Annabi kõwa na da 'yancin shiga, namiji da mace, kuma ya faɗi abin da yake so, kõ da ya sãɓãwa abin da Annabi ya gani ƙãfin wani wahayi ya sauka. Gã wannan mace sunanta Khaulatu bnt Sa'alabah ta kai ƙãrar mijinta Ausu bn Samit wanda ya yi zihãri game da ita, watau ya ce idan ya kusance ta kamar ya kwãna da uwarsa ne. Ga al'adar lãrabãwa wannan bã saki bã ne, kuma ba ya iya kwana da ita har abada. Wannan shi ne takai ƙarã wurin Annabi har ta yi mahãwar da shi a kansa. Kuma wannan ƙissa tanã nũna gaskiyar Annabi, bai yi jawãbi ba ga abin da bai sãmi wahayi ba a kansa. -
ٱلَّذِينَ يُظَـٰهِرُونَ مِنكُم مِّن نِّسَآئِهِم مَّا هُنَّ أُمَّهَـٰتِهِمْ ۖ إِنْ أُمَّهَـٰتُهُمْ إِلَّا ٱلَّـٰٓـِٔى وَلَدْنَهُمْ ۚ وَإِنَّهُمْ لَيَقُولُونَ مُنكَرًا مِّنَ ٱلْقَوْلِ وَزُورًا ۚ وَإِنَّ ٱللَّهَ لَعَفُوٌّ غَفُورٌ٢
Allatheena yuthahiroona minkum min nisaihim ma hunna ommahatihim in ommahatuhum illa allaee waladnahum wainnahum layaqooloona munkaran mina alqawli wazooran wainna Allaha laʿafuwwun ghafoorun
Waɗanda ke yin zihãri daga cikinku game da mãtansu, sũmãtan nan bã uwãyensu ba ne, bãbu uwayensu fãce waɗanda suka haife su. Lalle sũ, sunã faɗar abin ƙyãmã na magana da ƙarya, kuma lalle Allah haƙĩƙa Mai yãfẽwa ne, Mai gãfara.
-
وَٱلَّذِينَ يُظَـٰهِرُونَ مِن نِّسَآئِهِمْ ثُمَّ يَعُودُونَ لِمَا قَالُوا۟ فَتَحْرِيرُ رَقَبَةٍ مِّن قَبْلِ أَن يَتَمَآسَّا ۚ ذَٰلِكُمْ تُوعَظُونَ بِهِۦ ۚ وَٱللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرٌ٣
Waallatheena yuthahiroona min nisaihim thumma yaʿoodoona lima qaloo fatahreeru raqabatin min qabli an yatamassa thalikum tooʿathoona bihi waAllahu bima taʿmaloona khabeerun
Waɗanda ke yin zihãri game da mãtansu, sa'an nan su kõma wa abin da suka faɗa, to, akwai 'yanta wuya a gabãnin su shãfi jũna. Wannan anã yi muku wa'azi da shi. Kuma Allah Mai ƙididdigewa ne ga abin da kuke aikatãwa.
-
فَمَن لَّمْ يَجِدْ فَصِيَامُ شَهْرَيْنِ مُتَتَابِعَيْنِ مِن قَبْلِ أَن يَتَمَآسَّا ۖ فَمَن لَّمْ يَسْتَطِعْ فَإِطْعَامُ سِتِّينَ مِسْكِينًا ۚ ذَٰلِكَ لِتُؤْمِنُوا۟ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ ۚ وَتِلْكَ حُدُودُ ٱللَّهِ ۗ وَلِلْكَـٰفِرِينَ عَذَابٌ أَلِيمٌ٤
Faman lam yajid fasiyamu shahrayni mutatabiʿayni min qabli an yatamassa faman lam yastatiʿ faitʿamu sitteena miskeenan thalika lituminoo biAllahi warasoolihi watilka hudoodu Allahi walilkafireena ʿathabun aleemun
To, wanda bai sãmu ba, sai azumin wata biyu jẽre a gabãnin su shãfi jũna, sa'an nan wanda bai sãmi ĩkon yi ba, to, sai ciyar da miskĩnai sittin. Wannan dõmin ku yĩ ĩmãni da Allah da Manzonsa. Kuma waɗannan hukunce-hukunce haddõdin Allah ne. Kuma kãfirai, sunã da azãba mai raɗadi.
-
إِنَّ ٱلَّذِينَ يُحَآدُّونَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ كُبِتُوا۟ كَمَا كُبِتَ ٱلَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ ۚ وَقَدْ أَنزَلْنَآ ءَايَـٰتٍۭ بَيِّنَـٰتٍ ۚ وَلِلْكَـٰفِرِينَ عَذَابٌ مُّهِينٌ٥
Inna allatheena yuhaddoona Allaha warasoolahu kubitoo kama kubita allatheena min qablihim waqad anzalna ayatin bayyinatin walilkafireena ʿathabun muheenun
Lalle waɗanda ke sãɓã wa Allah da ManzonSa, an wulãkanta su kamar yadda aka wulãkantar da waɗanda ke a gabãninsu, kuma lalle Mun saukar da ãyõyi bayyanannu, kuma kãfirai nã da azãba mai wulãkantãwa.
-
يَوْمَ يَبْعَثُهُمُ ٱللَّهُ جَمِيعًا فَيُنَبِّئُهُم بِمَا عَمِلُوٓا۟ ۚ أَحْصَىٰهُ ٱللَّهُ وَنَسُوهُ ۚ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍ شَهِيدٌ٦
Yawma yabʿathuhumu Allahu jameeʿan fayunabbiohum bima ʿamiloo ahsahu Allahu wanasoohu waAllahu ʿala kulli shayin shaheedun
Rãnar da Allah zai tãyar da su gabã ɗaya, sa'an nan Ya bã su lãbãri game da abin da suka aikata, Allah Yã lissafa shi, alhãli kuwa sũ, sun manta da shi, kuma a kan kõme Allah Halartacce ne.
-
أَلَمْ تَرَ أَنَّ ٱللَّهَ يَعْلَمُ مَا فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَمَا فِى ٱلْأَرْضِ ۖ مَا يَكُونُ مِن نَّجْوَىٰ ثَلَـٰثَةٍ إِلَّا هُوَ رَابِعُهُمْ وَلَا خَمْسَةٍ إِلَّا هُوَ سَادِسُهُمْ وَلَآ أَدْنَىٰ مِن ذَٰلِكَ وَلَآ أَكْثَرَ إِلَّا هُوَ مَعَهُمْ أَيْنَ مَا كَانُوا۟ ۖ ثُمَّ يُنَبِّئُهُم بِمَا عَمِلُوا۟ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ بِكُلِّ شَىْءٍ عَلِيمٌ٧
Alam tara anna Allaha yaʿlamu ma fee alssamawati wama fee alardi ma yakoonu min najwa thalathatin illa huwa rabiʿuhum wala khamsatin illa huwa sadisuhum wala adna min thalika wala akthara illa huwa maʿahum ayna ma kanoo thumma yunabbiohum bima ʿamiloo yawma alqiyamati inna Allaha bikulli shayin ʿaleemun
Ashe, ba ka ga cẽwa lalle Allah Yanã sane da abin da yake a cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa ba? Wata gãnãwa1 ta mutum uku bã zã ta kasance ba fãce Allah Shĩ ne na huɗu ɗinta, kuma bãbu ta mutum biyar fãce Shĩ ne na shida ɗinta, kuma babu abin da ya kãsa wannan kuma babu abin da yake mafi yawa fãce Shĩ Yanã tãre da su duk inda suka kasance, sa'an nan Ya bã su lãbãri game da abin da suka aikata a Rãnar ¡iyãma. Lalle Allah Masani ne ga dukkan kõme.
Bayanai
[1] A bãyan ƙissar zihãri, ya shiga maganar mãsu gãnãwa a cikin majalisa. Kuma ya nuna cewa ba a sifanta Annabi kõ a jingina wani abu zuwa gare shi sai idan abin nan yã fito daga Allah a cikin harshen Manzon Sa. -
أَلَمْ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ نُهُوا۟ عَنِ ٱلنَّجْوَىٰ ثُمَّ يَعُودُونَ لِمَا نُهُوا۟ عَنْهُ وَيَتَنَـٰجَوْنَ بِٱلْإِثْمِ وَٱلْعُدْوَٰنِ وَمَعْصِيَتِ ٱلرَّسُولِ وَإِذَا جَآءُوكَ حَيَّوْكَ بِمَا لَمْ يُحَيِّكَ بِهِ ٱللَّهُ وَيَقُولُونَ فِىٓ أَنفُسِهِمْ لَوْلَا يُعَذِّبُنَا ٱللَّهُ بِمَا نَقُولُ ۚ حَسْبُهُمْ جَهَنَّمُ يَصْلَوْنَهَا ۖ فَبِئْسَ ٱلْمَصِيرُ٨
Alam tara ila allatheena nuhoo ʿani alnnajwa thumma yaʿoodoona lima nuhoo ʿanhu wayatanajawna bialithmi waalʿudwani wamaʿsiyati alrrasooli waitha jaooka hayyawka bima lam yuhayyika bihi Allahu wayaqooloona fee anfusihim lawla yuʿaththibuna Allahu bima naqoolu hasbuhum jahannamu yaslawnaha fabisa almaseeru
Ashe, ba ka ga waɗanda aka hane su ba daga ganãwar, sa'an nan sunã kõmã wa abin da aka hane su daga gare shi, kuma sunã gãnãwa game da zunubi da zãlunci da sãɓã wa Manzon Allah, kuma idan sun zo maka sai su gasihe ka da abin da Allah bai gaishe ka da shi ba, kuma sunã cẽwa a cikin zukatansu: "Don me Allah ba Ya yi mana azãba sabõda abin da muke faɗi?" Jahannama ita ce mai isarsu, zã su shigeta. Sabõda haka makõmarsu ta mũnana.
-
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓا۟ إِذَا تَنَـٰجَيْتُمْ فَلَا تَتَنَـٰجَوْا۟ بِٱلْإِثْمِ وَٱلْعُدْوَٰنِ وَمَعْصِيَتِ ٱلرَّسُولِ وَتَنَـٰجَوْا۟ بِٱلْبِرِّ وَٱلتَّقْوَىٰ ۖ وَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ ٱلَّذِىٓ إِلَيْهِ تُحْشَرُونَ٩
Ya ayyuha allatheena amanoo itha tanajaytum fala tatanajaw bialithmi waalʿudwani wamaʿsiyati alrrasooli watanajaw bialbirri waalttaqwa waittaqoo Allaha allathee ilayhi tuhsharoona
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan za ku yi gãnãwa, to, kada ku gãna game da zunubi da zãlunci da sãɓã wa Manzon Allah, kuma ku yi gãnãwa game da alhẽri da taƙawa. Ku bi Allah da taƙawa wanda zã a tattara ku zuwa gare, shi.
-
إِنَّمَا ٱلنَّجْوَىٰ مِنَ ٱلشَّيْطَـٰنِ لِيَحْزُنَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَلَيْسَ بِضَآرِّهِمْ شَيْـًٔا إِلَّا بِإِذْنِ ٱللَّهِ ۚ وَعَلَى ٱللَّهِ فَلْيَتَوَكَّلِ ٱلْمُؤْمِنُونَ١٠
Innama alnnajwa mina alshshaytani liyahzuna allatheena amanoo walaysa bidarrihim shayan illa biithni Allahi waʿala Allahi falyatawakkali almuminoona
Gãnãwar daga Shaiɗan take kawai dõmin ya mũnanã wa waɗanda suka yi ĩmãni, alhãli kuwa bã zai iya cũtar su da kõme ba fãce da iznin Allah. Kuma sai mũminai su dogara ga Allah.
-
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓا۟ إِذَا قِيلَ لَكُمْ تَفَسَّحُوا۟ فِى ٱلْمَجَـٰلِسِ فَٱفْسَحُوا۟ يَفْسَحِ ٱللَّهُ لَكُمْ ۖ وَإِذَا قِيلَ ٱنشُزُوا۟ فَٱنشُزُوا۟ يَرْفَعِ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ مِنكُمْ وَٱلَّذِينَ أُوتُوا۟ ٱلْعِلْمَ دَرَجَـٰتٍ ۚ وَٱللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرٌ١١
Ya ayyuha allatheena amanoo itha qeela lakum tafassahoo fee almajalisi faifsahoo yafsahi Allahu lakum waitha qeela onshuzoo faonshuzoo yarfaʿi Allahu allatheena amanoo minkum waallatheena ootoo alʿilma darajatin waAllahu bima taʿmaloona khabeerun
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan an ce muka,1"Ku yalwatã a cikin majalisai," to, ku yalwatã, sai Allah Ya yalwatã muku, kuma idan an ce muku, "Ku tãshi" to, ku tãshi. Allah nã ɗaukaka waɗanda suka yi ĩmãni daga cikinku da waɗanda aka bai wa ilim wasu darajõji mãsu yawa, kuma, Allah Mai ƙididdigewa ne ga dukan kõme.
Bayanai
[1] Bãyan ƙissar hukuncin gãnãwa cikin majalisa, sai kuma hukuncin zaunãwa kõ tãshi dõmin wani ya zauna. Kuma ana fifita mãsu ilmi da zama ga wurin da ya fi dãcewa da su. -
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓا۟ إِذَا نَـٰجَيْتُمُ ٱلرَّسُولَ فَقَدِّمُوا۟ بَيْنَ يَدَىْ نَجْوَىٰكُمْ صَدَقَةً ۚ ذَٰلِكَ خَيْرٌ لَّكُمْ وَأَطْهَرُ ۚ فَإِن لَّمْ تَجِدُوا۟ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ١٢
Ya ayyuha allatheena amanoo itha najaytumu alrrasoola faqaddimoo bayna yaday najwakum sadaqatan thalika khayrun lakum waatharu fain lam tajidoo fainna Allaha ghafoorun raheemun
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan zã ku gãnãwa da Manzon Allah, to, ku gabãtar da 'yar sadaka1 a gabãnin gãnãwarku, wannan ne mafi alhẽri a gare ku, kuma mafi tsarki. Sai idan ba ku sãmi (abin sadakar ba), to, lalle, Allah, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
Bayanai
[1] Hukuncin tãyar da mutãne dõmin a gãna da Manzon Allah, bã ya halatta sai a kan larũra mai tsanani sabõda haka aka sanya gabãtar da sadaka, sa'an nan aka sõke shi da umurni da tsaron salla dõmin wa'azin da ke cikinta da kuma bayar da zakka. -
ءَأَشْفَقْتُمْ أَن تُقَدِّمُوا۟ بَيْنَ يَدَىْ نَجْوَىٰكُمْ صَدَقَـٰتٍ ۚ فَإِذْ لَمْ تَفْعَلُوا۟ وَتَابَ ٱللَّهُ عَلَيْكُمْ فَأَقِيمُوا۟ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُوا۟ ٱلزَّكَوٰةَ وَأَطِيعُوا۟ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ ۚ وَٱللَّهُ خَبِيرٌۢ بِمَا تَعْمَلُونَ١٣
Aashfaqtum an tuqaddimoo bayna yaday najwakum sadaqatin faith lam tafʿaloo wataba Allahu ʿalaykum faaqeemoo alssalata waatoo alzzakata waateeʿoo Allaha warasoolahu waAllahu khabeerun bima taʿmaloona
Ashe, kun ji tsõron ku gabãtar da sadakõki a gabãnin gãnãwarku? To, idan ba ku aikata ba, kuma Allah Ya kõmo da ku zuwa ga sauƙi, sai ku tsai da salla, kuma ku bãyar da zakka, kuma ku yi ɗã'ã ga Allah da Manzon Sa. Kuma Allah ne Mai ƙididdigewa ga abin da kuke aikatãwa.
-
۞ أَلَمْ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ تَوَلَّوْا۟ قَوْمًا غَضِبَ ٱللَّهُ عَلَيْهِم مَّا هُم مِّنكُمْ وَلَا مِنْهُمْ وَيَحْلِفُونَ عَلَى ٱلْكَذِبِ وَهُمْ يَعْلَمُونَ١٤
Alam tara ila allatheena tawallaw qawman ghadiba Allahu ʿalayhim ma hum minkum wala minhum wayahlifoona ʿala alkathibi wahum yaʿlamoona
Ashe, baka ga waɗanda1 suka jiɓinci waɗansu mutãne da Allah Ya yi hushi a kansu ba, bã su cikinku, kuma bã su a cikinsu kuma sunã rantsuwa a kan ƙarya, alhãli kuwa sunã sane?
Bayanai
[1] Bãyan maganar mãsu tãyar da mutãne dõmin gãnãwa a cikin majalisa, sai kuma munãfikai mãsu mu'ãmala da kãfirai, kuma su je su zauna cikin majalisar Musulmi dõmin su ɗauki rahõtonsu zuwa ga maƙiyansu. -
أَعَدَّ ٱللَّهُ لَهُمْ عَذَابًا شَدِيدًا ۖ إِنَّهُمْ سَآءَ مَا كَانُوا۟ يَعْمَلُونَ١٥
aʿadda Allahu lahum ʿathaban shadeedan innahum saa ma kanoo yaʿmaloona
Allah Ya yi musu tattalin azãba mai tsanani. Lalle sũ abin da suka kasance sunã aikatãwa ya mũnana.
-
ٱتَّخَذُوٓا۟ أَيْمَـٰنَهُمْ جُنَّةً فَصَدُّوا۟ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ فَلَهُمْ عَذَابٌ مُّهِينٌ١٦
Ittakhathoo aymanahum junnatan fasaddoo ʿan sabeeli Allahi falahum ʿathabun muheenun
Sun riƙi rantsuwõwinsu garkuwa, sabõda haka suka kange (mũminai) daga jihãdin ɗaukaka tafarkin Allah. To, sunã da azãba mai wulãkantãwa.
-
لَّن تُغْنِىَ عَنْهُمْ أَمْوَٰلُهُمْ وَلَآ أَوْلَـٰدُهُم مِّنَ ٱللَّهِ شَيْـًٔا ۚ أُو۟لَـٰٓئِكَ أَصْحَـٰبُ ٱلنَّارِ ۖ هُمْ فِيهَا خَـٰلِدُونَ١٧
Lan tughniya ʿanhum amwaluhum wala awladuhum mina Allahi shayan olaika ashabu alnnari hum feeha khalidoona
Dũkiyõyinsu ba su wadãtar musu kõme ba daga Allah, haka kuma ɗiyansu. Waɗannan 'yan wutã ne. Sũ, mãsu dawwama ne a cikinta.
-
يَوْمَ يَبْعَثُهُمُ ٱللَّهُ جَمِيعًا فَيَحْلِفُونَ لَهُۥ كَمَا يَحْلِفُونَ لَكُمْ ۖ وَيَحْسَبُونَ أَنَّهُمْ عَلَىٰ شَىْءٍ ۚ أَلَآ إِنَّهُمْ هُمُ ٱلْكَـٰذِبُونَ١٨
Yawma yabʿathuhumu Allahu jameeʿan fayahlifoona lahu kama yahlifoona lakum wayahsaboona annahum ʿala shayin ala innahum humu alkathiboona
Rãnar da Allah ke tãyar da su gabã ɗaya, sai su yi Masa rantsuwa kamar yadda suke yi muku rantsuwa (a nan dũniya) kuma sunã zaton cẽwa sũ a kan wani abu suke! To, lalle sũ, sũ ne maƙaryata.
-
ٱسْتَحْوَذَ عَلَيْهِمُ ٱلشَّيْطَـٰنُ فَأَنسَىٰهُمْ ذِكْرَ ٱللَّهِ ۚ أُو۟لَـٰٓئِكَ حِزْبُ ٱلشَّيْطَـٰنِ ۚ أَلَآ إِنَّ حِزْبَ ٱلشَّيْطَـٰنِ هُمُ ٱلْخَـٰسِرُونَ١٩
Istahwatha ʿalayhimu alshshaytanu faansahum thikra Allahi olaika hizbu alshshaytani ala inna hizba alshshaytani humu alkhasiroona
Shaiɗan ya rinjaya a kansu, sai ya mantar da su ambaton Allah, waɗannan ƙungiyar Shaiɗan ne. To, lalle ƙungiyar Shaiɗan, sũ ne mãsu hasãra.
-
إِنَّ ٱلَّذِينَ يُحَآدُّونَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥٓ أُو۟لَـٰٓئِكَ فِى ٱلْأَذَلِّينَ٢٠
Inna allatheena yuhaddoona Allaha warasoolahu olaika fee alathalleena
Lalle, waɗanda ke sãɓã wa Allah da ManzonSa waɗannan sunã a cikin (mutãne) mafi ƙasƙanci.
-
كَتَبَ ٱللَّهُ لَأَغْلِبَنَّ أَنَا۠ وَرُسُلِىٓ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ قَوِىٌّ عَزِيزٌ٢١
Kataba Allahu laaghlibanna ana warusulee inna Allaha qawiyyun ʿazeezun
Allah Ya rubũta cẽwa," Lalle zan rinjãya, Nĩ da Manzanni Na." Lalle Allah Mai ƙarfi ne, Mabuwãyi.
-
لَّا تَجِدُ قَوْمًا يُؤْمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلْيَوْمِ ٱلْـَٔاخِرِ يُوَآدُّونَ مَنْ حَآدَّ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ وَلَوْ كَانُوٓا۟ ءَابَآءَهُمْ أَوْ أَبْنَآءَهُمْ أَوْ إِخْوَٰنَهُمْ أَوْ عَشِيرَتَهُمْ ۚ أُو۟لَـٰٓئِكَ كَتَبَ فِى قُلُوبِهِمُ ٱلْإِيمَـٰنَ وَأَيَّدَهُم بِرُوحٍ مِّنْهُ ۖ وَيُدْخِلُهُمْ جَنَّـٰتٍ تَجْرِى مِن تَحْتِهَا ٱلْأَنْهَـٰرُ خَـٰلِدِينَ فِيهَا ۚ رَضِىَ ٱللَّهُ عَنْهُمْ وَرَضُوا۟ عَنْهُ ۚ أُو۟لَـٰٓئِكَ حِزْبُ ٱللَّهِ ۚ أَلَآ إِنَّ حِزْبَ ٱللَّهِ هُمُ ٱلْمُفْلِحُونَ٢٢
La tajidu qawman yuminoona biAllahi waalyawmi alakhiri yuwaddoona man hadda Allaha warasoolahu walaw kanoo abaahum aw abnaahum aw ikhwanahum aw ʿasheeratahum olaika kataba fee quloobihimu aleemana waayyadahum biroohin minhu wayudkhiluhum jannatin tajree min tahtiha alanharu khalideena feeha radiya Allahu ʿanhum waradoo ʿanhu olaika hizbu Allahi ala inna hizba Allahi humu almuflihoona
Bã zã ka sãmi mutãne mãsu yin ĩmãni da Allah da RãnarLãhira sunã sõyayya da wanda ya sãɓã wa Allah da ManzonSa ba, kõ dã sun kasance ubanninsu ne, kõ ɗiyansu kõ 'yan'uwansu, ko danginsu. waɗannan Allah Yã rubuta ĩmãni a cikin zukãtansu, kuma Yã ƙarfafa su da wani rũhi1 daga gare Shi, kuma zai shigar da su a gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna ƙarƙashinsu sunã mãsu dawwama a cikinsu. Allah Yã yarda da su, kuma sun yarda da Shi. Waɗannan ƙungiyar Allah ne. To, lalle ƙungiyar Allah sũ ne mãsu babban rabo.
Bayanai
[1] Waɗanda suka tsare dõkokin Allah, Allah zai ba su ƙarfin rai ga zartar da al'amuransu da kyau, kuma zai wadãta su a dũniya da Lãhira. Asalin rũhi shine rai. Anã nufin rãyuwar ĩmãni da ƙarfin halin fuskantar gaskiya.
Tambayoyin da ake yawan yi
Mece ce ma’anar sunan Suratul Mujadila?
Ma’anar Mujadila ita ce “Mai jayayya”.
Suratul Mujadila tana cikin juz’i na nawa?
Suratul Mujadila tana cikin juz’i na 28.
Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Mujadila?
Suratul Mujadila tana da ayoyi 22.
Suratul Mujadila Makkiya ce ko Madaniya?
Suratul Mujadila sura ce Madaniya.
Suratul Mujadila ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?
Ita ce sura ta 58 a cikin Alƙur’ani.
Majiyoyi
- Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
- Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
- Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
- Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
- Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
- Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.
Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.