Suratul Rum (الروم) ita ce sura ta 30 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 60. Ma’anar sunanta ita ce “Rumawa”. Sura ce Makkiya, wadda ta sauka a Makka kafin Hijira, kuma tana cikin juz’i na 21.
A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Rum gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.
Suratul Rum cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ
-
الٓمٓ١
Aliflammeem
A. L̃. M̃.
-
غُلِبَتِ ٱلرُّومُ٢
Ghulibati alrroomu
An rinjãyi Rũmawa.1
Bayanai
[1] Rũmãwa Kiristoci ne mãsu aiki da littãfi, sunã faɗa da Fãrisãwa mãsu bautã wa wutã. Fãrisawa suka rinjãyi Rumãwa, sabõda haka Ƙuraishãwa suka ji dãɗi sabõda alfãnun cewa zã su rinjãyi Musulmi idan sun yi faɗa. A bãyan saukar surar, sai Musulmi suka yi farin ciki sabõda alfãnun cewa sũ kuma zã su rinjãyi Ƙuraishãwa. Wannan ya sanya Abũbakar ya yi ƙuri'a da Ubaiyu bn Halaf a kan rãƙuma gõma a cikin shekaru uku. Sai Annabi ya ce wa Abũbakar ya ƙãra rãkuma da ajãli zuwa shekaru tara. A bãyan shekaru bakwai sai Rũmawa suka ci nasara a kan Fãrisãwa, kuma wannan ya yi daidai da Badar,watau rãnar da Musulmi suka ci nasara a kan Ƙuraishãwa. Abũbakar ya ci rãƙumansa daga magãdan Ubaiyu. Amma sai ya yi sadaka da su da umurnin Annabi, dõmin Allah Yã hana Musulmi su yi cãca a lõkacin. -
فِىٓ أَدْنَى ٱلْأَرْضِ وَهُم مِّنۢ بَعْدِ غَلَبِهِمْ سَيَغْلِبُونَ٣
Fee adna alardi wahum min baʿdi ghalabihim sayaghliboona
A cikin mafi kusantar ƙasarsu, kuma sũ, a bãyan rinjãyarsu, zã sn rinjãya.
-
فِى بِضْعِ سِنِينَ ۗ لِلَّهِ ٱلْأَمْرُ مِن قَبْلُ وَمِنۢ بَعْدُ ۚ وَيَوْمَئِذٍ يَفْرَحُ ٱلْمُؤْمِنُونَ٤
Fee bidʿi sineena lillahi alamru min qablu wamin baʿdu wayawmaithin yafrahu almuminoona
A cikin'yan shẽkaru. Al'amari na Allah ne a gabãnin kõme da bãyansa, kuma a rãnar nan mũminai zã su yi farin ciki.
-
بِنَصْرِ ٱللَّهِ ۚ يَنصُرُ مَن يَشَآءُ ۖ وَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ٥
Binasri Allahi yansuru man yashao wahuwa alʿazeezu alrraheemu
Da taimakon Allah Yanã taimakon wanda Yake so. Kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
-
وَعْدَ ٱللَّهِ ۖ لَا يُخْلِفُ ٱللَّهُ وَعْدَهُۥ وَلَـٰكِنَّ أَكْثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعْلَمُونَ٦
Waʿda Allahi la yukhlifu Allahu waʿdahu walakinna akthara alnnasi la yaʿlamoona
Wa'adin Allah, Allah bã ya sãɓãwa ga wa'adinsa, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba.
-
يَعْلَمُونَ ظَـٰهِرًا مِّنَ ٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا وَهُمْ عَنِ ٱلْـَٔاخِرَةِ هُمْ غَـٰفِلُونَ٧
Yaʿlamoona thahiran mina alhayati alddunya wahum ʿani alakhirati hum ghafiloona
Sunã sanin bayyanannar rãyuwar dũniya, alhãli kuwa sũ shagalallu ne daga rãyuwar Lãhira.1
Bayanai
[1] Dangantakar rashin sanin ĩkon Allah da sanin sha'anin dũniya da kuma jãhiltar al'amarin Lãhira,. -
أَوَلَمْ يَتَفَكَّرُوا۟ فِىٓ أَنفُسِهِم ۗ مَّا خَلَقَ ٱللَّهُ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَآ إِلَّا بِٱلْحَقِّ وَأَجَلٍ مُّسَمًّى ۗ وَإِنَّ كَثِيرًا مِّنَ ٱلنَّاسِ بِلِقَآئِ رَبِّهِمْ لَكَـٰفِرُونَ٨
Awalam yatafakkaroo fee anfusihim ma khalaqa Allahu alssamawati waalarda wama baynahuma illa bialhaqqi waajalin musamman wainna katheeran mina alnnasi biliqai rabbihim lakafiroona
Shin, ba su yi tunãni ba a cikin zukãtansu cẽwa Allah bai halitta sammai da ƙasa ba da abin da ke tsakãninsu, fãce da gaskiya1 da ajali ambatacce? Kuma lalle mãsu yawa daga mutãne kãfirai ne ga gamuwa da Ubangijinsu?
Bayanai
[1] Gaskiya ita ce tsãri tabbatacce wanda bã ya canzãwa. -
أَوَلَمْ يَسِيرُوا۟ فِى ٱلْأَرْضِ فَيَنظُرُوا۟ كَيْفَ كَانَ عَـٰقِبَةُ ٱلَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ ۚ كَانُوٓا۟ أَشَدَّ مِنْهُمْ قُوَّةً وَأَثَارُوا۟ ٱلْأَرْضَ وَعَمَرُوهَآ أَكْثَرَ مِمَّا عَمَرُوهَا وَجَآءَتْهُمْ رُسُلُهُم بِٱلْبَيِّنَـٰتِ ۖ فَمَا كَانَ ٱللَّهُ لِيَظْلِمَهُمْ وَلَـٰكِن كَانُوٓا۟ أَنفُسَهُمْ يَظْلِمُونَ٩
Awalam yaseeroo fee alardi fayanthuroo kayfa kana ʿaqibatu allatheena min qablihim kanoo ashadda minhum quwwatan waatharoo alarda waʿamarooha akthara mimma ʿamarooha wajaathum rusuluhum bialbayyinati fama kana Allahu liyathlimahum walakin kanoo anfusahum yathlimoona
Shin, kuma ba su yi tafiya ba, a cikin ƙasã dõmin su gani yadda aƙibar waɗanda ke a gabãninsu ta kasance? Sun kasance mafiya ƙarfi daga gare su kuma suka nõmi ƙasa suka rãya ta fiye da yadda suka raya ta, kuma manzanninsu suka je musu da hujjoji bayyanannu. Sabo da haka Allah ba Ya yiwuwa Ya zãlunce su, amma kansu suka kasance sunã zãlunta.
-
ثُمَّ كَانَ عَـٰقِبَةَ ٱلَّذِينَ أَسَـٰٓـُٔوا۟ ٱلسُّوٓأَىٰٓ أَن كَذَّبُوا۟ بِـَٔايَـٰتِ ٱللَّهِ وَكَانُوا۟ بِهَا يَسْتَهْزِءُونَ١٠
Thumma kana ʿaqibata allatheena asaoo alssooa an kaththaboo biayati Allahi wakanoo biha yastahzioona
Sa'an nan ãƙibar waɗannan da suka aikata mũgun aiki ta kasance mafi muni, wãtau sun ƙaryata game da ãyõyin Allah, kuma suka kasance sunã izgili da su.
-
ٱللَّهُ يَبْدَؤُا۟ ٱلْخَلْقَ ثُمَّ يُعِيدُهُۥ ثُمَّ إِلَيْهِ تُرْجَعُونَ١١
Allahu yabdao alkhalqa thumma yuʿeeduhu thumma ilayhi turjaʿoona
Allah ne ke fãra yin halitta, sa'an nan Ya sãke ta sa'an nan zuwa gare Shi ake mayar da ku.
-
وَيَوْمَ تَقُومُ ٱلسَّاعَةُ يُبْلِسُ ٱلْمُجْرِمُونَ١٢
Wayawma taqoomu alssaʿatu yublisu almujrimoona
Kuma a rãnar da sa'a ke tsayuwa, mãsu laifi zã su kãsa magana.
-
وَلَمْ يَكُن لَّهُم مِّن شُرَكَآئِهِمْ شُفَعَـٰٓؤُا۟ وَكَانُوا۟ بِشُرَكَآئِهِمْ كَـٰفِرِينَ١٣
Walam yakun lahum min shurakaihim shufaʿao wakanoo bishurakaihim kafireena
Kuma bã su da mãsu cẽto daga abũbuwan shirkinsu, kuma snn kasance mãsu kãfircẽwa daga abũbuwan shirkinsu.
-
وَيَوْمَ تَقُومُ ٱلسَّاعَةُ يَوْمَئِذٍ يَتَفَرَّقُونَ١٤
Wayawma taqoomu alssaʿatu yawmaithin yatafarraqoona
kuma a rãnar tashin Alkiyama ranar ne suke rarrabuwa.
-
فَأَمَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ فَهُمْ فِى رَوْضَةٍ يُحْبَرُونَ١٥
Faamma allatheena amanoo waʿamiloo alssalihati fahum fee rawdatin yuhbaroona
To, amma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai to sũ anã faranta musu rãyuka, a cikin wani lambu.
-
وَأَمَّا ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ وَكَذَّبُوا۟ بِـَٔايَـٰتِنَا وَلِقَآئِ ٱلْـَٔاخِرَةِ فَأُو۟لَـٰٓئِكَ فِى ٱلْعَذَابِ مُحْضَرُونَ١٦
Waamma allatheena kafaroo wakaththaboo biayatina waliqai alakhirati faolaika fee alʿathabi muhdaroona
Kuma waɗanda suka kãfirta, kuma suka ƙaryata, game da ãyõyinMu da kuma haɗuwa da Rãnar Lãhira, to, waɗancan anã halartar da su a cikin azãba.
-
فَسُبْحَـٰنَ ٱللَّهِ حِينَ تُمْسُونَ وَحِينَ تُصْبِحُونَ١٧
Fasubhana Allahi heena tumsoona waheena tusbihoona
Sabõda haka tsarkakẽwa ta tabbata ga Allah a lõkacin da kuke shiga maraice, da lõkacin da kuke shiga sãfiya.1
Bayanai
[1] Akwai dangantaka a tsakãnin tasbĩhi, watau ibãda da rãyuwa, da tsakãnin fitar hantsi da sãfiya kamar yadda yake akwai dangantaka a tsakãnin mutuwa da maraice, da yamma da kãfirci. -
وَلَهُ ٱلْحَمْدُ فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ وَعَشِيًّا وَحِينَ تُظْهِرُونَ١٨
Walahu alhamdu fee alssamawati waalardi waʿashiyyan waheena tuthhiroona
Kuma Shĩ ne da gõdiya, a cikin sammai da ƙasã kuma da lõkacin yamma da lõkacin zawãli.
-
يُخْرِجُ ٱلْحَىَّ مِنَ ٱلْمَيِّتِ وَيُخْرِجُ ٱلْمَيِّتَ مِنَ ٱلْحَىِّ وَيُحْىِ ٱلْأَرْضَ بَعْدَ مَوْتِهَا ۚ وَكَذَٰلِكَ تُخْرَجُونَ١٩
Yukhriju alhayya mina almayyiti wayukhriju almayyita mina alhayyi wayuhyee alarda baʿda mawtiha wakathalika tukhrajoona
Yanã fitar da mai rai daga matacce kuma Yanã fitar da matacce daga mai rai, kuma Yanã rãyar da ƙasa a bãyan mutuwarta. Kuma haka ake fitar da ku.
-
وَمِنْ ءَايَـٰتِهِۦٓ أَنْ خَلَقَكُم مِّن تُرَابٍ ثُمَّ إِذَآ أَنتُم بَشَرٌ تَنتَشِرُونَ٢٠
Wamin ayatihi an khalaqakum min turabin thumma itha antum basharun tantashiroona
Kuma akwai daga ãyõyin Sa, Ya halitta ku daga turɓãya, sai gã ku kun zama mutum, kunã wãtsuwa.
-
وَمِنْ ءَايَـٰتِهِۦٓ أَنْ خَلَقَ لَكُم مِّنْ أَنفُسِكُمْ أَزْوَٰجًا لِّتَسْكُنُوٓا۟ إِلَيْهَا وَجَعَلَ بَيْنَكُم مَّوَدَّةً وَرَحْمَةً ۚ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَـٰتٍ لِّقَوْمٍ يَتَفَكَّرُونَ٢١
Wamin ayatihi an khalaqa lakum min anfusikum azwajan litaskunoo ilayha wajaʿala baynakum mawaddatan warahmatan inna fee thalika laayatin liqawmin yatafakkaroona
Kuma akwai daga ãyõyinsa, Ya halitta muku mãtan aure daga kanku, dõmin ku natsu zuwa gare ta, kuma Ya sanya sõyayya da rahama a tsakãninku.1 Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu yin tunãni.
Bayanai
[1] Akwai dangantaka a tsakãnin halittar namiji da mace daga yumɓu da kuma natsuwar da suke sãmu daga junã da sõyayya da rahamar da ke a ciki. -
وَمِنْ ءَايَـٰتِهِۦ خَلْقُ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ وَٱخْتِلَـٰفُ أَلْسِنَتِكُمْ وَأَلْوَٰنِكُمْ ۚ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَـٰتٍ لِّلْعَـٰلِمِينَ٢٢
Wamin ayatihi khalqu alssamawati waalardi waikhtilafu alsinatikum waalwanikum inna fee thalika laayatin lilʿalimeena
Kuma akwai daga ãyõyin Sa halittar sammai da ƙasã da sãɓã, war harsunanku, da launukanku. Lalle a cikin wannan akwai ãyõyi ga mãsu ilmi.
-
وَمِنْ ءَايَـٰتِهِۦ مَنَامُكُم بِٱلَّيْلِ وَٱلنَّهَارِ وَٱبْتِغَآؤُكُم مِّن فَضْلِهِۦٓ ۚ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَـٰتٍ لِّقَوْمٍ يَسْمَعُونَ٢٣
Wamin ayatihi manamukum biallayli waalnnahari waibtighaokum min fadlihi inna fee thalika laayatin liqawmin yasmaʿoona
Kuma akwai daga cikin ãyõyin Sa, barcinku a cikin dare da rãna, da nẽmanku ga falalarsa. Lalle a cikin wannan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu saurãrãwa.
-
وَمِنْ ءَايَـٰتِهِۦ يُرِيكُمُ ٱلْبَرْقَ خَوْفًا وَطَمَعًا وَيُنَزِّلُ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءً فَيُحْىِۦ بِهِ ٱلْأَرْضَ بَعْدَ مَوْتِهَآ ۚ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَـٰتٍ لِّقَوْمٍ يَعْقِلُونَ٢٤
Wamin ayatihi yureekumu albarqa khawfan watamaʿan wayunazzilu mina alssamai maan fayuhyee bihi alarda baʿda mawtiha inna fee thalika laayatin liqawmin yaʿqiloona
Kuma akwai daga cikin ãyõyin Sa, Ya nũna muku walƙiya a kan tsõro da ɗammãni kuma Ya dinga saukar da ruwa daga sama Sa'an nan Ya rãyar da ƙasã game da shi a bãyan mutuwarta. Lalle a cikin wannan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu hankaltawa.
-
وَمِنْ ءَايَـٰتِهِۦٓ أَن تَقُومَ ٱلسَّمَآءُ وَٱلْأَرْضُ بِأَمْرِهِۦ ۚ ثُمَّ إِذَا دَعَاكُمْ دَعْوَةً مِّنَ ٱلْأَرْضِ إِذَآ أَنتُمْ تَخْرُجُونَ٢٥
Wamin ayatihi an taqooma alssamao waalardu biamrihi thumma itha daʿakum daʿwatan mina alardi itha antum takhrujoona
Kuma akwai daga ãyõyinsa, tsayuwar sama da asƙã bisa umurninsa, sa'an nan idan Ya kira ku, kira ɗaya, daga ƙasã, sai gã ku kunã fita.
-
وَلَهُۥ مَن فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ۖ كُلٌّ لَّهُۥ قَـٰنِتُونَ٢٦
Walahu man fee alssamawati waalardi kullun lahu qanitoona
Kuma wanda ke cikin sammai da ƙasã Nãsa ne shi kaɗai. Dukansu mãsu tawãli'u ne a gare Shi.
-
وَهُوَ ٱلَّذِى يَبْدَؤُا۟ ٱلْخَلْقَ ثُمَّ يُعِيدُهُۥ وَهُوَ أَهْوَنُ عَلَيْهِ ۚ وَلَهُ ٱلْمَثَلُ ٱلْأَعْلَىٰ فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ۚ وَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلْحَكِيمُ٢٧
Wahuwa allathee yabdao alkhalqa thumma yuʿeeduhu wahuwa ahwanu ʿalayhi walahu almathalu alaʿla fee alssamawati waalardi wahuwa alʿazeezu alhakeemu
Kuma Shĩ ne Wanda Ya fãra halitta, sa'an nan Ya sãke ta kuma sakẽwarta tã fi sauƙi a gare shi. Kuma Yanã da misãli wanda ya fi ɗaukaka a cikin sammai da ƙasã kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
-
ضَرَبَ لَكُم مَّثَلًا مِّنْ أَنفُسِكُمْ ۖ هَل لَّكُم مِّن مَّا مَلَكَتْ أَيْمَـٰنُكُم مِّن شُرَكَآءَ فِى مَا رَزَقْنَـٰكُمْ فَأَنتُمْ فِيهِ سَوَآءٌ تَخَافُونَهُمْ كَخِيفَتِكُمْ أَنفُسَكُمْ ۚ كَذَٰلِكَ نُفَصِّلُ ٱلْـَٔايَـٰتِ لِقَوْمٍ يَعْقِلُونَ٢٨
Daraba lakum mathalan min anfusikum hal lakum mi mma malakat aymanukum min shurakaa fee ma razaqnakum faantum feehi sawaon takhafoonahum kakheefatikum anfusakum kathalika nufassilu alayati liqawmin yaʿqiloona
Ya bũga muku wani misãli daga kanku. Kõ kunã da abõkan tarẽwa, daga cikin bãyin da hannãyenku na dãma suka mallaka, a cikin arzikinku, watau ku zama daidai a ciki kunã tsõron su kamar tSõronku ga kanku? Haka dai Muke bayyana ãyõyi, daki-daki, ga mutãne mãsu hankaltuwa.
-
بَلِ ٱتَّبَعَ ٱلَّذِينَ ظَلَمُوٓا۟ أَهْوَآءَهُم بِغَيْرِ عِلْمٍ ۖ فَمَن يَهْدِى مَنْ أَضَلَّ ٱللَّهُ ۖ وَمَا لَهُم مِّن نَّـٰصِرِينَ٢٩
Bali ittabaʿa allatheena thalamoo ahwaahum bighayri ʿilmin faman yahdee man adalla Allahu wama lahum min nasireena
Ã'aha! waɗanda suka yi zãunci sun bi son zũciyõyinsu, bã tãre da wani ilmi ba. To wãne ne zai shiryar da wanda Allah Ya ɓatar, kuma bã su da waɗansu mataimaka?
-
فَأَقِمْ وَجْهَكَ لِلدِّينِ حَنِيفًا ۚ فِطْرَتَ ٱللَّهِ ٱلَّتِى فَطَرَ ٱلنَّاسَ عَلَيْهَا ۚ لَا تَبْدِيلَ لِخَلْقِ ٱللَّهِ ۚ ذَٰلِكَ ٱلدِّينُ ٱلْقَيِّمُ وَلَـٰكِنَّ أَكْثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعْلَمُونَ٣٠
Faaqim wajhaka lilddeeni haneefan fitrata Allahi allatee fatara alnnasa ʿalayha la tabdeela likhalqi Allahi thalika alddeenu alqayyimu walakinna akthara alnnasi la yaʿlamoona
Sabõda haka, ka tsayar da fuskarka ga addini,1 kanã mai karkata zuwa ga gaskiya, halittar Allah da Ya halitta mutãne a kanta. Bãbu musanyãwa ga halittar Allah, wannan shĩ ne addini madaidaici kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba.
Bayanai
[1] Yin addini ɗabĩ'a ce wadda Allah Ya halicci mutum akanta. Idan mutum ya bi abin da Allah Ya umurce shi da yi kõ bari, to yã yi addinin gaskiya, idan kuwa bai yi haka ba, ya zama mushiriki game da wanda yake karɓar umurni daga gare shi. -
۞ مُنِيبِينَ إِلَيْهِ وَٱتَّقُوهُ وَأَقِيمُوا۟ ٱلصَّلَوٰةَ وَلَا تَكُونُوا۟ مِنَ ٱلْمُشْرِكِينَ٣١
Muneebeena ilayhi waittaqoohu waaqeemoo alssalata wala takoonoo mina almushrikeena
Kunã mãsu mai da al'amari gare Shi, kuma ku bĩ Shi dataƙawa, kuma ku tsayar da salla, kuma kada ku kasance daga mushirikai.1
Bayanai
[1] Ya fassara mushirikai da ãyã ta 32. Wannan ya nũna ta yi nũni ga hana dukkan ɗarĩƙun sũfãye dõmin sunã rarraba mutãne ƙungiya-ƙungiya, kuma kõwa nã ganin abin da yake yi ko kuma wanda yake bi yã fi na wani. Kumawanda ke cikin wata ƙungiya bã zai iya haɗuwa da wata ba a lõkacin wurudinsu, a bãyan abũbuwan da suke ƙunsãwa a cikin ayyukansu na bidi'õ'i da aƙĩdõdi da suka sãɓa wa Musulunci. -
مِنَ ٱلَّذِينَ فَرَّقُوا۟ دِينَهُمْ وَكَانُوا۟ شِيَعًا ۖ كُلُّ حِزْبٍۭ بِمَا لَدَيْهِمْ فَرِحُونَ٣٢
Mina allatheena farraqoo deenahum wakanoo shiyaʿan kullu hizbin bima ladayhim farihoona
Wãtau waɗanda suka rarrabe addininsu kuma suka kasance ƙungiya-ƙungiya, kõwace ƙungiya tanã mai farin ciki da abin da ke a gare ta kawai.
-
وَإِذَا مَسَّ ٱلنَّاسَ ضُرٌّ دَعَوْا۟ رَبَّهُم مُّنِيبِينَ إِلَيْهِ ثُمَّ إِذَآ أَذَاقَهُم مِّنْهُ رَحْمَةً إِذَا فَرِيقٌ مِّنْهُم بِرَبِّهِمْ يُشْرِكُونَ٣٣
Waitha massa alnnasa durrun daʿaw rabbahum muneebeena ilayhi thumma itha athaqahum minhu rahmatan itha fareequn minhum birabbihim yushrikoona
Kuma idan cũta ta shãfi mutãne, sai su kirãyi Ubangijinsu, sunã mãsu mai da al'amari gare Shi, sa'an nan idan Ya ɗanɗana musu wata rahama daga gare Shi, sai gã wani ɓangare daga gare su sunã shirki da Ubangijinsu.
-
لِيَكْفُرُوا۟ بِمَآ ءَاتَيْنَـٰهُمْ ۚ فَتَمَتَّعُوا۟ فَسَوْفَ تَعْلَمُونَ٣٤
Liyakfuroo bima ataynahum fatamattaʿoo fasawfa taʿlamoona
Dõmin su kãfirta dl abin da Muka bã su. To ku ji dãɗi kaɗan Sa'an nan zã ku, sani.
-
أَمْ أَنزَلْنَا عَلَيْهِمْ سُلْطَـٰنًا فَهُوَ يَتَكَلَّمُ بِمَا كَانُوا۟ بِهِۦ يُشْرِكُونَ٣٥
Am anzalna ʿalayhim sultanan fahuwa yatakallamu bima kanoo bihi yushrikoona
Kõ Mun saukar da wani dalĩ li a gare su? Shi kuwa yanã magana da abin da suka kasance sunã shirkin da shi?
-
وَإِذَآ أَذَقْنَا ٱلنَّاسَ رَحْمَةً فَرِحُوا۟ بِهَا ۖ وَإِن تُصِبْهُمْ سَيِّئَةٌۢ بِمَا قَدَّمَتْ أَيْدِيهِمْ إِذَا هُمْ يَقْنَطُونَ٣٦
Waitha athaqna alnnasa rahmatan farihoo biha wain tusibhum sayyiatun bima qaddamat aydeehim itha hum yaqnatoona
Kuma idan Muka ɗanɗana wa mutãne wata rahama, sai su yi farin ciki da ita kuma idan cũta ta sãme su, sabõda abin da hannayensu suka gabãtar, sai gã su sunã yanke ƙauna,
-
أَوَلَمْ يَرَوْا۟ أَنَّ ٱللَّهَ يَبْسُطُ ٱلرِّزْقَ لِمَن يَشَآءُ وَيَقْدِرُ ۚ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَـٰتٍ لِّقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ٣٧
Awalam yaraw anna Allaha yabsutu alrrizqa liman yashao wayaqdiru inna fee thalika laayatin liqawmin yuminoona
Shin, kuma ba su gani ba cẽwa Allah na shimfida arziki ga wanda Yake so kuma Yanã ƙuntatãwa? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu yin ĩmãni.
-
فَـَٔاتِ ذَا ٱلْقُرْبَىٰ حَقَّهُۥ وَٱلْمِسْكِينَ وَٱبْنَ ٱلسَّبِيلِ ۚ ذَٰلِكَ خَيْرٌ لِّلَّذِينَ يُرِيدُونَ وَجْهَ ٱللَّهِ ۖ وَأُو۟لَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلْمُفْلِحُونَ٣٨
Faati tha alqurba haqqahu waalmiskeena waibna alssabeeli thalika khayrun lillatheena yureedoona wajha Allahi waolaika humu almuflihoona
Sabõda haka ka bai wa zumu hakkinsa da miskĩnai da ɗan hanya, wannan shĩ ne alhẽri ga waɗanda ke nufin yardar Allah kuma waɗancan sũ ne mãsu sãmun babban rabo.
-
وَمَآ ءَاتَيْتُم مِّن رِّبًا لِّيَرْبُوَا۟ فِىٓ أَمْوَٰلِ ٱلنَّاسِ فَلَا يَرْبُوا۟ عِندَ ٱللَّهِ ۖ وَمَآ ءَاتَيْتُم مِّن زَكَوٰةٍ تُرِيدُونَ وَجْهَ ٱللَّهِ فَأُو۟لَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلْمُضْعِفُونَ٣٩
Wama ataytum min riban liyarbuwa fee amwali alnnasi fala yarboo ʿinda Allahi wama ataytum min zakatin tureedoona wajha Allahi faolaika humu almudʿifoona
Kuma abin da kuka bãyar na riba dõmin ya ƙãru a cikin dũkiyar mutãne to, bã zai ƙãru ba, a wurin Allah. Kuma abin da kuka bãyar na zakka, kanã nufin yardar Allah to (mãsu yin haka) waɗancan sũ ne mãsu ninkãwa (ga dũkiyarsu).
-
ٱللَّهُ ٱلَّذِى خَلَقَكُمْ ثُمَّ رَزَقَكُمْ ثُمَّ يُمِيتُكُمْ ثُمَّ يُحْيِيكُمْ ۖ هَلْ مِن شُرَكَآئِكُم مَّن يَفْعَلُ مِن ذَٰلِكُم مِّن شَىْءٍ ۚ سُبْحَـٰنَهُۥ وَتَعَـٰلَىٰ عَمَّا يُشْرِكُونَ٤٠
Allahu allathee khalaqakum thumma razaqakum thumma yumeetukum thumma yuhyeekum hal min shurakaikum man yafʿalu min thalikum min shayin subhanahu wataʿala ʿamma yushrikoona
Allah ne Wanda Ya halicce ku, sa'an nan Ya azurta ku, sa'an nan Ya matar da ku, sa'an nan Ya rãyar da ku. Ashe, daga cikin abũbuwan shirkinku akwai wanda ke aikata wani abu daga waɗannan ahũbuwa? Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma Ya ɗaukaka bisa ga abin da suke yi na shirki.
-
ظَهَرَ ٱلْفَسَادُ فِى ٱلْبَرِّ وَٱلْبَحْرِ بِمَا كَسَبَتْ أَيْدِى ٱلنَّاسِ لِيُذِيقَهُم بَعْضَ ٱلَّذِى عَمِلُوا۟ لَعَلَّهُمْ يَرْجِعُونَ٤١
Thahara alfasadu fee albarri waalbahri bima kasabat aydee alnnasi liyutheeqahum baʿda allathee ʿamiloo laʿallahum yarjiʿoona
¥arnã tã bayyana a cikin ƙasa da tẽku, sabõda abin da hannãyen mutãne suka aikata. Dõmin Allah Ya ɗanɗana musu sãshin abin da suka aikata, ɗammãninsu zã su kõmo.
-
قُلْ سِيرُوا۟ فِى ٱلْأَرْضِ فَٱنظُرُوا۟ كَيْفَ كَانَ عَـٰقِبَةُ ٱلَّذِينَ مِن قَبْلُ ۚ كَانَ أَكْثَرُهُم مُّشْرِكِينَ٤٢
Qul seeroo fee alardi faonthuroo kayfa kana ʿaqibatu allatheena min qablu kana aktharuhum mushrikeena
Ka ce: "Ku tafi a cikin ƙasã sa'an nan ku dũbi yadda ãƙibar waɗanda suka kasance a gabãninku ta kasance. Mafi yawansu sun kasance mãsu yin shirka."
-
فَأَقِمْ وَجْهَكَ لِلدِّينِ ٱلْقَيِّمِ مِن قَبْلِ أَن يَأْتِىَ يَوْمٌ لَّا مَرَدَّ لَهُۥ مِنَ ٱللَّهِ ۖ يَوْمَئِذٍ يَصَّدَّعُونَ٤٣
Faaqim wajhaka lilddeeni alqayyimi min qabli an yatiya yawmun la maradda lahu mina Allahi yawmaithin yassaddaʿoona
Sabõda haka, ka tsayar da fuskarka ga addini madaidaici a gabãnin wani yini ya zo, bãbu makawa gare Shi daga Allah, a rãnar nan mutãne sunã tsãgẽwa (su rabu biyu).
-
مَن كَفَرَ فَعَلَيْهِ كُفْرُهُۥ ۖ وَمَنْ عَمِلَ صَـٰلِحًا فَلِأَنفُسِهِمْ يَمْهَدُونَ٤٤
Man kafara faʿalayhi kufruhu waman ʿamila salihan falianfusihim yamhadoona
Wanda ya kãfirta, to, kãfircinsa na kansa, kuma wanda ya aikata aikin ƙwarai, to, sabõda kansu suke yin shimfiɗa.
-
لِيَجْزِىَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ مِن فَضْلِهِۦٓ ۚ إِنَّهُۥ لَا يُحِبُّ ٱلْكَـٰفِرِينَ٤٥
Liyajziya allatheena amanoo waʿamiloo alssalihati min fadlihi innahu la yuhibbu alkafireena
Dõmin Ya sãkã wa waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, daga falalarSa. Lalle Allah bã Ya son kafirai.
-
وَمِنْ ءَايَـٰتِهِۦٓ أَن يُرْسِلَ ٱلرِّيَاحَ مُبَشِّرَٰتٍ وَلِيُذِيقَكُم مِّن رَّحْمَتِهِۦ وَلِتَجْرِىَ ٱلْفُلْكُ بِأَمْرِهِۦ وَلِتَبْتَغُوا۟ مِن فَضْلِهِۦ وَلَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ٤٦
Wamin ayatihi an yursila alrriyaha mubashshiratin waliyutheeqakum min rahmatihi walitajriya alfulku biamrihi walitabtaghoo min fadlihi walaʿallakum tashkuroona
Kuma akwai daga ãyõyinSa, ya aika iskõki mãsu bãyar da bushãra kuma dõmin Ya ɗanɗana muku daga rahamarSa, kuma dõmin jirãgen ruwa su gudãna da umurninSa, kuma dõmin ku nẽma daga falalar Sa, fãtanku zã ku gode.
-
وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا مِن قَبْلِكَ رُسُلًا إِلَىٰ قَوْمِهِمْ فَجَآءُوهُم بِٱلْبَيِّنَـٰتِ فَٱنتَقَمْنَا مِنَ ٱلَّذِينَ أَجْرَمُوا۟ ۖ وَكَانَ حَقًّا عَلَيْنَا نَصْرُ ٱلْمُؤْمِنِينَ٤٧
Walaqad arsalna min qablika rusulan ila qawmihim fajaoohum bialbayyinati faintaqamna mina allatheena ajramoo wakana haqqan ʿalayna nasru almumineena
Kuma lalle Mun aiki waɗansu Manzanni a gabãninka, zuwa ga mutãnensu sai suka je musu da hujjõji, bayyanannu, sa'an nan Muka azabtar da waɗanda suka yi laifi, kuma ya kasance tabbatacce taimakon mũminai wajibi ne a kan mu.
-
ٱللَّهُ ٱلَّذِى يُرْسِلُ ٱلرِّيَـٰحَ فَتُثِيرُ سَحَابًا فَيَبْسُطُهُۥ فِى ٱلسَّمَآءِ كَيْفَ يَشَآءُ وَيَجْعَلُهُۥ كِسَفًا فَتَرَى ٱلْوَدْقَ يَخْرُجُ مِنْ خِلَـٰلِهِۦ ۖ فَإِذَآ أَصَابَ بِهِۦ مَن يَشَآءُ مِنْ عِبَادِهِۦٓ إِذَا هُمْ يَسْتَبْشِرُونَ٤٨
Allahu allathee yursilu alrriyaha fatutheeru sahaban fayabsutuhu fee alssamai kayfa yashao wayajʿaluhu kisafan fatara alwadqa yakhruju min khilalihi faitha asaba bihi man yashao min ʿibadihi itha hum yastabshiroona
Allah ne Wanda ke aika iskõki, sai su mõtsar da girgije, sa'an nan Ya shimfiɗa shi a cikin sama yadda Yake so, kuma Ya sanya shi wani ɓaɓɓake, sa'an nan ka ga ruwa na fita daga tsakãninsa. Sa'an nan idan Allah Ya sãmi waɗanda Ya so daga bãyinsa, Sai gã su suna bushãra da shi.
-
وَإِن كَانُوا۟ مِن قَبْلِ أَن يُنَزَّلَ عَلَيْهِم مِّن قَبْلِهِۦ لَمُبْلِسِينَ٤٩
Wain kanoo min qabli an yunazzala ʿalayhim min qablihi lamubliseena
Kuma kõ da sun kasance a gabãnin a saukar da shi a kansu, kusa-kusa, sunã baƙin ciki hai bã su iya magana.
-
فَٱنظُرْ إِلَىٰٓ ءَاثَـٰرِ رَحْمَتِ ٱللَّهِ كَيْفَ يُحْىِ ٱلْأَرْضَ بَعْدَ مَوْتِهَآ ۚ إِنَّ ذَٰلِكَ لَمُحْىِ ٱلْمَوْتَىٰ ۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍ قَدِيرٌ٥٠
Faonthur ila athari rahmati Allahi kayfa yuhyee alarda baʿda mawtiha inna thalika lamuhyee almawta wahuwa ʿala kulli shayin qadeerun
Sai ka dũbi alãmõmin rahamar Allah yadda Yake rãyar da ƙasã a bãyan mutuwarta. Lalle wannan (Mai wannan aiki), tabbas, Mai rãyar da halitta ne, kuma Shi Mai ikon yi ne a kan kõme.
-
وَلَئِنْ أَرْسَلْنَا رِيحًا فَرَأَوْهُ مُصْفَرًّا لَّظَلُّوا۟ مِنۢ بَعْدِهِۦ يَكْفُرُونَ٥١
Walain arsalna reehan faraawhu musfarran lathalloo min baʿdihi yakfuroona
Kuma lalle idan Mun aika wata iska, suka ganta fatsifatsi, lalle zã su yini a bãyansa sunã kãfirta.
-
فَإِنَّكَ لَا تُسْمِعُ ٱلْمَوْتَىٰ وَلَا تُسْمِعُ ٱلصُّمَّ ٱلدُّعَآءَ إِذَا وَلَّوْا۟ مُدْبِرِينَ٥٢
Fainnaka la tusmiʿu almawta wala tusmiʿu alssumma aldduʿaa itha wallaw mudbireena
Sabõda haka, kai, bã ka jiyar da matattu kira, kuma bã ka jiyar da kurãme kira idan sun jũya bãya sunã gudu.
-
وَمَآ أَنتَ بِهَـٰدِ ٱلْعُمْىِ عَن ضَلَـٰلَتِهِمْ ۖ إِن تُسْمِعُ إِلَّا مَن يُؤْمِنُ بِـَٔايَـٰتِنَا فَهُم مُّسْلِمُونَ٥٣
Wama anta bihadi alʿumyi ʿan dalalatihim in tusmiʿu illa man yuminu biayatina fahum muslimoona
Kuma ba ka zamo mai shiryar da makãfi ba daga ɓatarsu, bã ka jiyarwa fãce wanda ke yin ĩmãni da ãyõyin Mu, watau sũ ne mãsu mĩƙa wuya, su sallama.
-
۞ ٱللَّهُ ٱلَّذِى خَلَقَكُم مِّن ضَعْفٍ ثُمَّ جَعَلَ مِنۢ بَعْدِ ضَعْفٍ قُوَّةً ثُمَّ جَعَلَ مِنۢ بَعْدِ قُوَّةٍ ضَعْفًا وَشَيْبَةً ۚ يَخْلُقُ مَا يَشَآءُ ۖ وَهُوَ ٱلْعَلِيمُ ٱلْقَدِيرُ٥٤
Allahu allathee khalaqakum min daʿfin thumma jaʿala min baʿdi daʿfin quwwatan thumma jaʿala min baʿdi quwwatin daʿfan washaybatan yakhluqu ma yashao wahuwa alʿaleemu alqadeeru
Allah ne Ya halitta ku daga rauni,1 sa'an nan Ya sanya wani ƙarfi a bayan wani rauni, sa'an nan Ya sanya wani rauni da furfura a bãyan wani ƙarfi, Allah na halitta abin da Ya so, kuma Shĩ ne Mai ilmi, Mai ĩkon yi,
Bayanai
[1] Raunin farko, shĩ ne maniyyi, na biyu jãruntaka da ƙarfin ƙurũciya, rauni na uku, shi ne tsũfa bãyan ƙarfin hankalin kamãla ta dattãko. -
وَيَوْمَ تَقُومُ ٱلسَّاعَةُ يُقْسِمُ ٱلْمُجْرِمُونَ مَا لَبِثُوا۟ غَيْرَ سَاعَةٍ ۚ كَذَٰلِكَ كَانُوا۟ يُؤْفَكُونَ٥٥
Wayawma taqoomu alssaʿatu yuqsimu almujrimoona ma labithoo ghayra saʿatin kathalika kanoo yufakoona
Kuma a rãnar da Sa'a1 ke tsayuwa, mãsu laifi na rantsuwã: Ba su zauna a cikin kabari ba fãce sã'a guda. Kamar haka suka kasance anã karkatar da su.
Bayanai
[1] Sa'a ta farko Rãnar Ƙiyãma,ta biyu ɗan lõkaci, watau ɗan lõkacin da suka sãmi hutun azãbar kabari a tsakãnin bũsar farko da ta biyu. Akwai munãsabar ƙaryarsu ta dũniya da ta Lãhira. Akwai munasabar dangantakar lafazin kalmomi. -
وَقَالَ ٱلَّذِينَ أُوتُوا۟ ٱلْعِلْمَ وَٱلْإِيمَـٰنَ لَقَدْ لَبِثْتُمْ فِى كِتَـٰبِ ٱللَّهِ إِلَىٰ يَوْمِ ٱلْبَعْثِ ۖ فَهَـٰذَا يَوْمُ ٱلْبَعْثِ وَلَـٰكِنَّكُمْ كُنتُمْ لَا تَعْلَمُونَ٥٦
Waqala allatheena ootoo alʿilma waaleemana laqad labithtum fee kitabi Allahi ila yawmi albaʿthi fahatha yawmu albaʿthi walakinnakum kuntum la taʿlamoona
Kuma waɗanda aka bai wa ilmi da ĩmãni suka ce: "Lalle, haƙĩƙa kun zauna a cikin Littãfin Allah, har zuwa rãnar tãyarwa, to, kuma wannan ita ce rãnar tãyarwar, kuma amma kũ, kun kasance1 ba ku sani ba."
Bayanai
[1] Rashin aiki da littãfin Allah a dũniya yakan sanya ɗĩmuwa a rãnar Lãhira. -
فَيَوْمَئِذٍ لَّا يَنفَعُ ٱلَّذِينَ ظَلَمُوا۟ مَعْذِرَتُهُمْ وَلَا هُمْ يُسْتَعْتَبُونَ٥٧
Fayawmaithin la yanfaʿu allatheena thalamoo maʿthiratuhum wala hum yustaʿtaboona
To, a rãnar da uzurin waɗanda suka yi zãlunci bã ya amfaninsu, kuma bã a neman yardarsu.
-
وَلَقَدْ ضَرَبْنَا لِلنَّاسِ فِى هَـٰذَا ٱلْقُرْءَانِ مِن كُلِّ مَثَلٍ ۚ وَلَئِن جِئْتَهُم بِـَٔايَةٍ لَّيَقُولَنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓا۟ إِنْ أَنتُمْ إِلَّا مُبْطِلُونَ٥٨
Walaqad darabna lilnnasi fee hatha alqurani min kulli mathalin walain jitahum biayatin layaqoolanna allatheena kafaroo in antum illa mubtiloona
Kuma lalle tabbas Mun buga kõwane irin misãli ga mutãne a cikin wannan Alƙur'ãni, kuma lalle idan kã je musu da kõwace ãyã, lalle, waɗanda suka kãfirta zã su ce "Kũ, bã kõme kuke ba fãce mãsu barua."
-
كَذَٰلِكَ يَطْبَعُ ٱللَّهُ عَلَىٰ قُلُوبِ ٱلَّذِينَ لَا يَعْلَمُونَ٥٩
Kathalika yatbaʿu Allahu ʿala quloobi allatheena la yaʿlamoona
Kamar haka Allah Yake shãfe haske a kan zukãtan waɗanda ba su sani ba.
-
فَٱصْبِرْ إِنَّ وَعْدَ ٱللَّهِ حَقٌّ ۖ وَلَا يَسْتَخِفَّنَّكَ ٱلَّذِينَ لَا يُوقِنُونَ٦٠
Faisbir inna waʿda Allahi haqqun wala yastakhiffannaka allatheena la yooqinoona
Sabõda haka ka yi haƙuri lalle wa'adin Allah gaskiya ne, kuma kada waɗanda bã su da yaƙĩni su sassance maka hankali.
Tambayoyin da ake yawan yi
Mece ce ma’anar sunan Suratul Rum?
Ma’anar Rum ita ce “Rumawa”.
Suratul Rum tana cikin juz’i na nawa?
Suratul Rum tana cikin juz’i na 21.
Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Rum?
Suratul Rum tana da ayoyi 60.
Suratul Rum Makkiya ce ko Madaniya?
Suratul Rum sura ce Makkiya.
Suratul Rum ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?
Ita ce sura ta 30 a cikin Alƙur’ani.
Majiyoyi
- Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
- Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
- Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
- Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
- Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
- Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.
Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.