Suratul Ƙasas (القصص) ita ce sura ta 28 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 88. Ma’anar sunanta ita ce “Labarai”. Sura ce Makkiya, wadda ta sauka a Makka kafin Hijira, kuma tana cikin juz’i na 20.
A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Ƙasas gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.
Suratul Ƙasas cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ
-
طسٓمٓ١
Taseenmeem
T. S̃. M̃.
-
تِلْكَ ءَايَـٰتُ ٱلْكِتَـٰبِ ٱلْمُبِينِ٢
Tilka ayatu alkitabi almubeeni
Waɗancan ãyõyin Littãfi ne bayyananne.
-
نَتْلُوا۟ عَلَيْكَ مِن نَّبَإِ مُوسَىٰ وَفِرْعَوْنَ بِٱلْحَقِّ لِقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ٣
Natloo ʿalayka min nabai moosa wafirʿawna bialhaqqi liqawmin yuminoona
Munã karantãwa a kanka daga lãbarin Mũsã da Fir'auna da gaskiya dõmin mutãne waɗanda suke yin ĩmãni.
-
إِنَّ فِرْعَوْنَ عَلَا فِى ٱلْأَرْضِ وَجَعَلَ أَهْلَهَا شِيَعًا يَسْتَضْعِفُ طَآئِفَةً مِّنْهُمْ يُذَبِّحُ أَبْنَآءَهُمْ وَيَسْتَحْىِۦ نِسَآءَهُمْ ۚ إِنَّهُۥ كَانَ مِنَ ٱلْمُفْسِدِينَ٤
Inna firʿawna ʿala fee alardi wajaʿala ahlaha shiyaʿan yastadʿifu taifatan minhum yuthabbihu abnaahum wayastahyee nisaahum innahu kana mina almufsideena
Lalle ne Fir'auna ya ɗaukaka a cikin ƙasa, kuma ya sanya mutãnenta ƙungiya-ƙungiya, yanã raunanar da wata jama'a daga gare su; yanã yanyanka ɗiyansu maza kuma yanã rãyar da mãtan. Lalle shĩ ya kasance daga mãsu ɓarna.
-
وَنُرِيدُ أَن نَّمُنَّ عَلَى ٱلَّذِينَ ٱسْتُضْعِفُوا۟ فِى ٱلْأَرْضِ وَنَجْعَلَهُمْ أَئِمَّةً وَنَجْعَلَهُمُ ٱلْوَٰرِثِينَ٥
Wanureedu an namunna ʿala allatheena istudʿifoo fee alardi wanajʿalahum aimmatan wanajʿalahumu alwaritheena
Kuma Munã nufin Mu yi falala ga waɗanda aka raunanar a cikin ƙasar, kuma Mu sanya su shugabanni, kuma Mu sanya su magãda.
-
وَنُمَكِّنَ لَهُمْ فِى ٱلْأَرْضِ وَنُرِىَ فِرْعَوْنَ وَهَـٰمَـٰنَ وَجُنُودَهُمَا مِنْهُم مَّا كَانُوا۟ يَحْذَرُونَ٦
Wanumakkina lahum fee alardi wanuriya firʿawna wahamana wajunoodahuma minhum ma kanoo yahtharoona
Kuma Mu tabbatar da su a cikin ƙasar, kuma Mu nũna wa Fir'auna da Hãmãna da rundunõninsu abin da suka kasance sunã sauna daga gare su.
-
وَأَوْحَيْنَآ إِلَىٰٓ أُمِّ مُوسَىٰٓ أَنْ أَرْضِعِيهِ ۖ فَإِذَا خِفْتِ عَلَيْهِ فَأَلْقِيهِ فِى ٱلْيَمِّ وَلَا تَخَافِى وَلَا تَحْزَنِىٓ ۖ إِنَّا رَآدُّوهُ إِلَيْكِ وَجَاعِلُوهُ مِنَ ٱلْمُرْسَلِينَ٧
Waawhayna ila ommi moosa an ardiʿeehi faitha khifti ʿalayhi faalqeehi fee alyammi wala takhafee wala tahzanee inna raddoohu ilayki wajaʿiloohu mina almursaleena
Kuma Muka yi wahayi zuwa ga uwar Mũsa, cẽwa ki shãyar da shi, sai idan kin ji tsõro game da shi, to, ki jẽfa shi a cikin kõgi, kuma kada ki ji tsõro, kuma kada ki yi baƙin ciki. Lalle ne Mũ, Mãsu mayar da shi ne zuwa gare ki, kuma Mãsu sanya shi ne a cikin Manzanni
-
فَٱلْتَقَطَهُۥٓ ءَالُ فِرْعَوْنَ لِيَكُونَ لَهُمْ عَدُوًّا وَحَزَنًا ۗ إِنَّ فِرْعَوْنَ وَهَـٰمَـٰنَ وَجُنُودَهُمَا كَانُوا۟ خَـٰطِـِٔينَ٨
Failtaqatahu alu firʿawna liyakoona lahum ʿaduwwan wahazanan inna firʿawna wahamana wajunoodahuma kanoo khatieena
Sai mutãnen Fir'auna suka tsince shi, dõmin ya kasance maƙiyi da baƙin ciki a gare su. Lalle ne Fir'auna da Hãmãna da rundunõninsu, sun kasance mãsu aikin ganganci.
-
وَقَالَتِ ٱمْرَأَتُ فِرْعَوْنَ قُرَّتُ عَيْنٍ لِّى وَلَكَ ۖ لَا تَقْتُلُوهُ عَسَىٰٓ أَن يَنفَعَنَآ أَوْ نَتَّخِذَهُۥ وَلَدًا وَهُمْ لَا يَشْعُرُونَ٩
Waqalati imraatu firʿawna qurratu ʿaynin lee walaka la taqtuloohu ʿasa an yanfaʿana aw nattakhithahu waladan wahum la yashʿuroona
Kuma matar1 Fir'auna ta ce ("Ka bar shi yanã) sanyin ido a gare ni da gare ka! Kada ka kashe shi, akwai fatan ya amfane mu, kõ mu riƙe Shi ɗã," alhãli kuwa sũ ba su sansance ba.
Bayanai
[1] Sunan mãtar Fir'auna Ãsiya, tanã da zumunta da Mũsã. Tace ka yi masa sũna 'Mũshã,' ma'anarsa an same shi tsakãnin "mũ," wãtau ruwa da "shã" watau itãce, sa'an nan ya zama Mũsã. Allah Yanã tsare mutum gaba ga maƙiyinsa. -
وَأَصْبَحَ فُؤَادُ أُمِّ مُوسَىٰ فَـٰرِغًا ۖ إِن كَادَتْ لَتُبْدِى بِهِۦ لَوْلَآ أَن رَّبَطْنَا عَلَىٰ قَلْبِهَا لِتَكُونَ مِنَ ٱلْمُؤْمِنِينَ١٠
Waasbaha fuadu ommi moosa farighan in kadat latubdee bihi lawla an rabatna ʿala qalbiha litakoona mina almumineena
Kuma zuciyar uwar Mũsã ta wãyi gari yõfintatta.1 Lalle ne, haƙĩƙa, ta yi kusa ta bayyanar da shi, bã dõmin Mun ɗaure zũciyarta ba, dõmin ta kasance daga mũminai.
Bayanai
[1] Zũciya yõfintatta, ita ce wadda bã ta da wani tunãni sabõda abin da ya shagaltar da ita na tunãnin ɗanta a hannun maƙiyinsa. -
وَقَالَتْ لِأُخْتِهِۦ قُصِّيهِ ۖ فَبَصُرَتْ بِهِۦ عَن جُنُبٍ وَهُمْ لَا يَشْعُرُونَ١١
Waqalat liokhtihi qusseehi fabasurat bihi ʿan junubin wahum la yashʿuroona
Kuma ta ce wa 'yar'uwarsa,1 "Ki bĩ shi." Sabõda haka sai ta lẽƙe shi daga gẽfe, alhãli sũ ba Su sani ba.
Bayanai
[1] Sũnan 'yar'uwar Mũsã Maryamu ko Kalsuma ko Kalsumu. Sũnan uwarsu Yũhãniz ɗiyar Hãmid ɗan Lãwaya ɗan Yãƙũbu. -
۞ وَحَرَّمْنَا عَلَيْهِ ٱلْمَرَاضِعَ مِن قَبْلُ فَقَالَتْ هَلْ أَدُلُّكُمْ عَلَىٰٓ أَهْلِ بَيْتٍ يَكْفُلُونَهُۥ لَكُمْ وَهُمْ لَهُۥ نَـٰصِحُونَ١٢
Waharramna ʿalayhi almaradiʿa min qablu faqalat hal adullukum ʿala ahli baytin yakfuloonahu lakum wahum lahu nasihoona
Kuma Muka hana masa mãsu shãyai da mãma, a gabãnin haka sai ta ce: "Kõ in nũnamuku mutãnen wani gida, su yi muku renonsa alhãli kuwa su mãsu nasĩha ne a, gare shi?"
-
فَرَدَدْنَـٰهُ إِلَىٰٓ أُمِّهِۦ كَىْ تَقَرَّ عَيْنُهَا وَلَا تَحْزَنَ وَلِتَعْلَمَ أَنَّ وَعْدَ ٱللَّهِ حَقٌّ وَلَـٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَ١٣
Faradadnahu ila ommihi kay taqarra ʿaynuha wala tahzana walitaʿlama anna waʿda Allahi haqqun walakinna aktharahum la yaʿlamoona
Sai Muka mayar da shi zuwa ga uwarsa dõmin idanunta su yi sanyi, kuma bã zã ta yi baƙin ciki ba, kuma dõmin ta san cẽwa lalle wa'adin Allah gaskiya ne, amma kuma mafi yawansu ba su sani ba.
-
وَلَمَّا بَلَغَ أَشُدَّهُۥ وَٱسْتَوَىٰٓ ءَاتَيْنَـٰهُ حُكْمًا وَعِلْمًا ۚ وَكَذَٰلِكَ نَجْزِى ٱلْمُحْسِنِينَ١٤
Walamma balagha ashuddahu waistawa ataynahu hukman waʿilman wakathalika najzee almuhsineena
Kuma a lõkacin da ya kai ƙarfinsa, kuma ya daidaita, Mun bã shi hukunci1 da ilmi kuma kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
Bayanai
[1] Wannan ya nũna, cewa Mũsã an bã shi Annabci a gabãnin ya yi hijira zuwa Madyana. Kuma yanã ƙãra ƙarfafa wannan magana abin da ke cikin ãyã ta 16 inda ya rõƙi Allah gãfara, Ya gãfarta masa, da ãyã ta l7 wadda ta nũna ya san an yi masa gãfarar har yanã neman tsari dõmin kada ya kõma yin haka a gaba. Annabãwa sunã wahami ga abin da bã wahayi ba, sa'an nan Allah Ya gyãra kuskuren, Ya tabbatar da gaskiya. -
وَدَخَلَ ٱلْمَدِينَةَ عَلَىٰ حِينِ غَفْلَةٍ مِّنْ أَهْلِهَا فَوَجَدَ فِيهَا رَجُلَيْنِ يَقْتَتِلَانِ هَـٰذَا مِن شِيعَتِهِۦ وَهَـٰذَا مِنْ عَدُوِّهِۦ ۖ فَٱسْتَغَـٰثَهُ ٱلَّذِى مِن شِيعَتِهِۦ عَلَى ٱلَّذِى مِنْ عَدُوِّهِۦ فَوَكَزَهُۥ مُوسَىٰ فَقَضَىٰ عَلَيْهِ ۖ قَالَ هَـٰذَا مِنْ عَمَلِ ٱلشَّيْطَـٰنِ ۖ إِنَّهُۥ عَدُوٌّ مُّضِلٌّ مُّبِينٌ١٥
Wadakhala almadeenata ʿala heeni ghaflatin min ahliha fawajada feeha rajulayni yaqtatilani hatha min sheeʿatihi wahatha min ʿaduwwihi faistaghathahu allathee min sheeʿatihi ʿala allathee min ʿaduwwihi fawakazahu moosa faqada ʿalayhi qala hatha min ʿamali alshshaytani innahu ʿaduwwun mudillun mubeenun
Kuma sai ya shiga garin a lõkacin da mutãnen garin suka shagala, sai ya sãmu, a cikin garin, waɗansu maza biyu sunã faɗa, wannan daga ƙungiyarsa, kuma ɗayan daga maƙiyansa, sai wannann da yake daga ƙungiyarsa ya nẽmi ãgajinsa, sai Mũsã ya yi masa ƙulli, ya kashe shi. Ya ce: "Wannan aikin Shaiɗan ne, dõmin shi maƙiyi ne mai ɓatarwa, bayyananne!"
-
قَالَ رَبِّ إِنِّى ظَلَمْتُ نَفْسِى فَٱغْفِرْ لِى فَغَفَرَ لَهُۥٓ ۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلْغَفُورُ ٱلرَّحِيمُ١٦
Qala rabbi innee thalamtu nafsee faighfir lee faghafara lahu innahu huwa alghafooru alrraheemu
Ya ce: "Ya Ubangijĩna! Lalle na zãlunci kaina, sai Ka yi mini gãfara." Sai Ya gãfarta masa, dõmin Shĩ ne Mai yawan gãfara, Mai jin ƙai.
-
قَالَ رَبِّ بِمَآ أَنْعَمْتَ عَلَىَّ فَلَنْ أَكُونَ ظَهِيرًا لِّلْمُجْرِمِينَ١٧
Qala rabbi bima anʿamta ʿalayya falan akoona thaheeran lilmujrimeena
Ya ce: "Yã Ubangijĩna! Dõmin abin da Ka ni'imta shi a kaina, sahõda haka bã zan kasance mai taimako ga mãsu laifi ba."
-
فَأَصْبَحَ فِى ٱلْمَدِينَةِ خَآئِفًا يَتَرَقَّبُ فَإِذَا ٱلَّذِى ٱسْتَنصَرَهُۥ بِٱلْأَمْسِ يَسْتَصْرِخُهُۥ ۚ قَالَ لَهُۥ مُوسَىٰٓ إِنَّكَ لَغَوِىٌّ مُّبِينٌ١٨
Faasbaha fee almadeenati khaifan yataraqqabu faitha allathee istansarahu bialamsi yastasrikhuhu qala lahu moosa innaka laghawiyyun mubeenun
Sai ya wãyi gari a cikin birnin yanã mai tsõro, yanã sauna. Sai ga wanda ya nẽmi taimako daga gare shi a jiya, yanã nẽman ãgajinsa. Mũsã ya ce masa, "Lalle kai ɓatacce ne, bayyananne."
-
فَلَمَّآ أَنْ أَرَادَ أَن يَبْطِشَ بِٱلَّذِى هُوَ عَدُوٌّ لَّهُمَا قَالَ يَـٰمُوسَىٰٓ أَتُرِيدُ أَن تَقْتُلَنِى كَمَا قَتَلْتَ نَفْسًۢا بِٱلْأَمْسِ ۖ إِن تُرِيدُ إِلَّآ أَن تَكُونَ جَبَّارًا فِى ٱلْأَرْضِ وَمَا تُرِيدُ أَن تَكُونَ مِنَ ٱلْمُصْلِحِينَ١٩
Falamma an arada an yabtisha biallathee huwa ʿaduwwun lahuma qala ya moosa atureedu an taqtulanee kama qatalta nafsan bialamsi in tureedu illa an takoona jabbaran fee alardi wama tureedu an takoona mina almusliheena
To, a lõkacin da Mũsã ya yi nufin ya damƙi wanda yake maƙiyi ne a gare su, (mai nẽman ãgajin) ya ce,1 "Ya Mũsã! Shin kanãnufin ka kashe ni ne kamar yadda ka kashe wani rai jiya? Ba ka son kõme fãce ka kasance mai tanƙwasawa2 a cikin ƙasa kuma bã ka nufin ka kasance daga mãsu kyautatãwa."
Bayanai
[1] Ya faɗi haka zaton Mũsã zai kashe shi ne sabõda gargaɗin da ya gabãtar a gareshi, Maganar ta nũna Mũsã ya shahara da son gyãran abũbuwa dõmin islãhi, haka ne ga al'adar mutãne wanda ya tãshi yanã gyãra sai sun tuhumce shi da neman girma. [2] Tanƙwasa ce sanya mutãne su yi abin da bã Su son yi. Kyautatãwar islãhi bã ta sãmuwa sai da tanƙwasãwa dõmin gãlibi mutãne sun fi son ɓarna a kan kyautatãwa tãre da saninsu ga cewar kyautatãwar ita ce daidai. -
وَجَآءَ رَجُلٌ مِّنْ أَقْصَا ٱلْمَدِينَةِ يَسْعَىٰ قَالَ يَـٰمُوسَىٰٓ إِنَّ ٱلْمَلَأَ يَأْتَمِرُونَ بِكَ لِيَقْتُلُوكَ فَٱخْرُجْ إِنِّى لَكَ مِنَ ٱلنَّـٰصِحِينَ٢٠
Wajaa rajulun min aqsa almadeenati yasʿa qala ya moosa inna almalaa yatamiroona bika liyaqtulooka faokhruj innee laka mina alnnasiheena
Kuma wani mutum ya zo daga mafi nĩsan birnin yanã taliya da gaggãwa, ya ce: "Ya Mũsã! Lalle mashãwarta sunã shãwara game da kai dõmin su kashe ka sabõda haka ka fita. Lalle nĩ, mai nasĩha ne a gare ka."
-
فَخَرَجَ مِنْهَا خَآئِفًا يَتَرَقَّبُ ۖ قَالَ رَبِّ نَجِّنِى مِنَ ٱلْقَوْمِ ٱلظَّـٰلِمِينَ٢١
Fakharaja minha khaifan yataraqqabu qala rabbi najjinee mina alqawmi alththalimeena
Sai ya fita daga gare ta,1 yanã mai jin tsõro yanã sauna. Ya ce: "Ya Ubangijĩna! Kã tsẽrar da ni daga mutãne azzãlumai."
Bayanai
[1] Ya fita daga alƙaryar. -
وَلَمَّا تَوَجَّهَ تِلْقَآءَ مَدْيَنَ قَالَ عَسَىٰ رَبِّىٓ أَن يَهْدِيَنِى سَوَآءَ ٱلسَّبِيلِ٢٢
Walamma tawajjaha tilqaa madyana qala ʿasa rabbee an yahdiyanee sawaa alssabeeli
Kuma a lõkacin da ya fuskanci wajen Madyana, ya ce: "Inã fatan Ubangijĩna Ya shiryar da ni a kan madaidaiciyar hanya."
-
وَلَمَّا وَرَدَ مَآءَ مَدْيَنَ وَجَدَ عَلَيْهِ أُمَّةً مِّنَ ٱلنَّاسِ يَسْقُونَ وَوَجَدَ مِن دُونِهِمُ ٱمْرَأَتَيْنِ تَذُودَانِ ۖ قَالَ مَا خَطْبُكُمَا ۖ قَالَتَا لَا نَسْقِى حَتَّىٰ يُصْدِرَ ٱلرِّعَآءُ ۖ وَأَبُونَا شَيْخٌ كَبِيرٌ٢٣
Walamma warada maa madyana wajada ʿalayhi ommatan mina alnnasi yasqoona wawajada min doonihimu imraatayni tathoodani qala ma khatbukuma qalata la nasqee hatta yusdira alrriʿao waaboona shaykhun kabeerun
Kuma a lõkacin da ya isa mashãyar Madyana, ya sãmi wata jam'ar mutãne sunã shãyarwa, kuma a bãyansu ya sãmi waɗansu mãtã biyu sunã kõrar (tumãkinsu). Ya ce: "Mẽne ne shã'aninku?" Suka ce, "Bã zã mu iya shãyãrwa ba sai makiyãya sun fita, kuma ubanmu tsõho1 ne mai daraja."
Bayanai
[1] Sabõda girma bã ya zuwa ya shãyar da tumakinsa, sai ya sanya mu, mu 'ya'yansa, kõ da muke mãtã. Wannan ya nũna mace tanã yin aikin maza sabõda larũra. Kuma sabõda darajar ubansu ba su shiga a cikin makiyãya ba dõmin tsaron mutuncinsu don haka ake son asali mai kyau. NĩSantarsu daga maza nau'in ƙauracewa ne na sharĩ'a. -
فَسَقَىٰ لَهُمَا ثُمَّ تَوَلَّىٰٓ إِلَى ٱلظِّلِّ فَقَالَ رَبِّ إِنِّى لِمَآ أَنزَلْتَ إِلَىَّ مِنْ خَيْرٍ فَقِيرٌ٢٤
Fasaqa lahuma thumma tawalla ila alththilli faqala rabbi innee lima anzalta ilayya min khayrin faqeerun
Sai ya shãyar musu, sa'an nan kuma ya jũya zuwa ga inuwa, sa'an nan ya ce: "Yã Ubangijĩna! Lalle ne, ga abin da Ka saukar zuwa gare ni na alhẽri ni mai bukãta ne."
-
فَجَآءَتْهُ إِحْدَىٰهُمَا تَمْشِى عَلَى ٱسْتِحْيَآءٍ قَالَتْ إِنَّ أَبِى يَدْعُوكَ لِيَجْزِيَكَ أَجْرَ مَا سَقَيْتَ لَنَا ۚ فَلَمَّا جَآءَهُۥ وَقَصَّ عَلَيْهِ ٱلْقَصَصَ قَالَ لَا تَخَفْ ۖ نَجَوْتَ مِنَ ٱلْقَوْمِ ٱلظَّـٰلِمِينَ٢٥
Fajaathu ihdahuma tamshee ʿala istihyain qalat inna abee yadʿooka liyajziyaka ajra ma saqayta lana falamma jaahu waqassa ʿalayhi alqasasa qala la takhaf najawta mina alqawmi alththalimeena
Sai ɗayansu ta je masa, tanã tafiya a kan jin kunya, ta ce, "Ubãna yanã kiran ka, dõmin ya sãka maka ijãrar abin da ka shãyar sabõda mu." To, a lõkacin da ya je masa, ya gaya masa lãbãrinsa, ya ce: "Kada ka ji tsõro, kã tsĩra daga mutãne azzãlumai."
-
قَالَتْ إِحْدَىٰهُمَا يَـٰٓأَبَتِ ٱسْتَـْٔجِرْهُ ۖ إِنَّ خَيْرَ مَنِ ٱسْتَـْٔجَرْتَ ٱلْقَوِىُّ ٱلْأَمِينُ٢٦
Qalat ihdahuma ya abati istajirhu inna khayra mani istajarta alqawiyyu alameenu
¦ayarsu ta ce, "Yã Bãba! Ka bã shi aikin ijãra, lalle ne mafi alhẽrin wanda ka bai wa aikin ijãra shi ne mai ƙarfi1 amintacce."
Bayanai
[1] Watau tanã iShãra ga ubantada cewa Mũsa ya tãra siffõfin nan biyu na ƙarfi da amãna dõmin abin da ta jarraba daga gare shi kafin ya iso ga ubanta. -
قَالَ إِنِّىٓ أُرِيدُ أَنْ أُنكِحَكَ إِحْدَى ٱبْنَتَىَّ هَـٰتَيْنِ عَلَىٰٓ أَن تَأْجُرَنِى ثَمَـٰنِىَ حِجَجٍ ۖ فَإِنْ أَتْمَمْتَ عَشْرًا فَمِنْ عِندِكَ ۖ وَمَآ أُرِيدُ أَنْ أَشُقَّ عَلَيْكَ ۚ سَتَجِدُنِىٓ إِن شَآءَ ٱللَّهُ مِنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ٢٧
Qala innee oreedu an onkihaka ihda ibnatayya hatayni ʿala an tajuranee thamaniya hijajin fain atmamta ʿashran famin ʿindika wama oreedu an ashuqqa ʿalayka satajidunee in shaa Allahu mina alssaliheena
Ya ce: "Lalle ne inã nufin in aurar da kai ɗayan 'yã'yãna biyu, waɗannan, a kan ka yi mini aikin ijãra shẽkara takwas to, idan ka cika gõma, to, daga, gare ka yake. Ba ni so in tsanantã maka, zã ka sãme ni, in Allah Ya so, daga sãlihai."
-
قَالَ ذَٰلِكَ بَيْنِى وَبَيْنَكَ ۖ أَيَّمَا ٱلْأَجَلَيْنِ قَضَيْتُ فَلَا عُدْوَٰنَ عَلَىَّ ۖ وَٱللَّهُ عَلَىٰ مَا نَقُولُ وَكِيلٌ٢٨
Qala thalika baynee wabaynaka ayyama alajalayni qadaytu fala ʿudwana ʿalayya waAllahu ʿala ma naqoolu wakeelun
Ya ce: "Wannan yanã a tsakanina da tsakãninka kõwane ɗayan adadin biyun na ƙãre, to, bãbu wani zãlunci a kaina. Kuma Allah ne Wakili ga abin da muke faɗa."
-
۞ فَلَمَّا قَضَىٰ مُوسَى ٱلْأَجَلَ وَسَارَ بِأَهْلِهِۦٓ ءَانَسَ مِن جَانِبِ ٱلطُّورِ نَارًا قَالَ لِأَهْلِهِ ٱمْكُثُوٓا۟ إِنِّىٓ ءَانَسْتُ نَارًا لَّعَلِّىٓ ءَاتِيكُم مِّنْهَا بِخَبَرٍ أَوْ جَذْوَةٍ مِّنَ ٱلنَّارِ لَعَلَّكُمْ تَصْطَلُونَ٢٩
Falamma qada moosaalajala wasara biahlihi anasa min janibi alttoori naran qala liahlihi omkuthoo innee anastu naran laʿallee ateekum minha bikhabarin aw jathwatin mina alnnari laʿallakum tastaloona
To, a lokacin da Mũsã ya ƙãre adadin kuma yanã tafiya da iyãlinsa, sai ya tsinkãyi wata Wutã daga gẽfen dũtse (¦ũr). Ya cewa iyãlinsa, "Ku dãkata, lalle ne nĩ, na tsinkãyi wata wutã, tsammãnĩna ni, mai zo muku ne daga gare ta da wani lãbãrĩ, kõ kuwa da guntun makãmashi daga Wutar don kõ ku ji ɗimi."
-
فَلَمَّآ أَتَىٰهَا نُودِىَ مِن شَـٰطِئِ ٱلْوَادِ ٱلْأَيْمَنِ فِى ٱلْبُقْعَةِ ٱلْمُبَـٰرَكَةِ مِنَ ٱلشَّجَرَةِ أَن يَـٰمُوسَىٰٓ إِنِّىٓ أَنَا ٱللَّهُ رَبُّ ٱلْعَـٰلَمِينَ٣٠
Falamma ataha noodiya min shatii alwadi alaymani fee albuqʿati almubarakati mina alshshajarati an ya moosa innee ana Allahu rabbu alʿalameena
To, a lõkacin da ya jẽ wurinta (Wutar) aka kirã shi, daga gẽfen rãfin na dãma, a cikin wurin nan mai albarka, daga itãciyar (cẽwa) "Ya Mũsã! Lalle Nĩ ne Allah Ubangijin halittu."
-
وَأَنْ أَلْقِ عَصَاكَ ۖ فَلَمَّا رَءَاهَا تَهْتَزُّ كَأَنَّهَا جَآنٌّ وَلَّىٰ مُدْبِرًا وَلَمْ يُعَقِّبْ ۚ يَـٰمُوسَىٰٓ أَقْبِلْ وَلَا تَخَفْ ۖ إِنَّكَ مِنَ ٱلْـَٔامِنِينَ٣١
Waan alqi ʿasaka falamma raaha tahtazzu kaannaha jannun walla mudbiran walam yuʿaqqib ya moosa aqbil wala takhaf innaka mina alamineena
"Kuma ka jẽfa sandarka." To, a lõkacin da ya gan ta, tanã girgiza kamar ƙaramar macijiya, ya jũya yanã mai bãyar da bãya, bai kõma ba. "Ya Mũsã! Ka fuskanto, kuma kada ka ji tsõro lalle ne kanã daga waɗanda ke amintattu."
-
ٱسْلُكْ يَدَكَ فِى جَيْبِكَ تَخْرُجْ بَيْضَآءَ مِنْ غَيْرِ سُوٓءٍ وَٱضْمُمْ إِلَيْكَ جَنَاحَكَ مِنَ ٱلرَّهْبِ ۖ فَذَٰنِكَ بُرْهَـٰنَانِ مِن رَّبِّكَ إِلَىٰ فِرْعَوْنَ وَمَلَإِي۟هِۦٓ ۚ إِنَّهُمْ كَانُوا۟ قَوْمًا فَـٰسِقِينَ٣٢
Osluk yadaka fee jaybika takhruj baydaa min ghayri sooin waodmum ilayka janahaka mina alrrahbi fathanika burhanani min rabbika ila firʿawna wamalaihi innahum kanoo qawman fasiqeena
"Ka shigar da hannunka a cikin wuyan rĩgarka, ya fita fari, ba da wata cũta ba, kuma ka haɗa hannuwanka ga kãfaɗunka, dõmin tsõro (ya gushe daga gare ka). To, waɗannan abũbuwa dalĩlai biyu ne daga Ubangijinka zuwa ga Fir'auna da 'yan Majalisarsa. Lalle sun kasance mutãne ne fãsiƙai."
-
قَالَ رَبِّ إِنِّى قَتَلْتُ مِنْهُمْ نَفْسًا فَأَخَافُ أَن يَقْتُلُونِ٣٣
Qala rabbi innee qataltu minhum nafsan faakhafu an yaqtulooni
Ya ce: "Yã Ubangijĩna! Lalle nã kashe wani rai daga gare su, dõmin haka inã tsõron kada su kashe ni."
-
وَأَخِى هَـٰرُونُ هُوَ أَفْصَحُ مِنِّى لِسَانًا فَأَرْسِلْهُ مَعِىَ رِدْءًا يُصَدِّقُنِىٓ ۖ إِنِّىٓ أَخَافُ أَن يُكَذِّبُونِ٣٤
Waakhee haroonu huwa afsahu minnee lisanan faarsilhu maʿiya ridan yusaddiqunee innee akhafu an yukaththibooni
"Kuma ɗan'uwana Hãrũna shĩ ne mafi fasãha daga gareni, ga harshe, sabõda haka Ka aika shi tãre da ni, yanã mai taimako, yanã gaskata ni, lalle ne inã tsõron su ƙaryata ni."
-
قَالَ سَنَشُدُّ عَضُدَكَ بِأَخِيكَ وَنَجْعَلُ لَكُمَا سُلْطَـٰنًا فَلَا يَصِلُونَ إِلَيْكُمَا ۚ بِـَٔايَـٰتِنَآ أَنتُمَا وَمَنِ ٱتَّبَعَكُمَا ٱلْغَـٰلِبُونَ٣٥
Qala sanashuddu ʿadudaka biakheeka wanajʿalu lakuma sultanan fala yasiloona ilaykuma biayatina antuma wamani ittabaʿakuma alghaliboona
Ya ce: "Zã Mu ƙarfafa damtsenka game da ɗan'uwanka kuma Mu sanya muku wani dalĩli, sabõda haka bã zã su sãdu zuwa gareku ba, tãre da ãyõyinMu, kũ da waɗanda suka bĩ ku ne marinjãya."
-
فَلَمَّا جَآءَهُم مُّوسَىٰ بِـَٔايَـٰتِنَا بَيِّنَـٰتٍ قَالُوا۟ مَا هَـٰذَآ إِلَّا سِحْرٌ مُّفْتَرًى وَمَا سَمِعْنَا بِهَـٰذَا فِىٓ ءَابَآئِنَا ٱلْأَوَّلِينَ٣٦
Falamma jaahum moosa biayatina bayyinatin qaloo ma hatha illa sihrun muftaran wama samiʿna bihatha fee abaina alawwaleena
To, a lõkacin da Mũsã ya jẽ musu da ãyõyinMu bayyanannu, suka ce: "Wannan ba kõme ba sai sihiri, wanda aka ƙãga, kuma ba mu ji wannan ba daga wajen ubanninmu na farko."
-
وَقَالَ مُوسَىٰ رَبِّىٓ أَعْلَمُ بِمَن جَآءَ بِٱلْهُدَىٰ مِنْ عِندِهِۦ وَمَن تَكُونُ لَهُۥ عَـٰقِبَةُ ٱلدَّارِ ۖ إِنَّهُۥ لَا يُفْلِحُ ٱلظَّـٰلِمُونَ٣٧
Waqala moosa rabbee aʿlamu biman jaa bialhuda min ʿindihi waman takoonu lahu ʿaqibatu alddari innahu la yuflihu alththalimoona
Kuma Mũsã ya ce: "Ubangijĩna ne Mafi sanin wanda ya zo da shiriya daga gare Shi, da wanda ãƙibar gida take kasancẽwa agare shi. Lalle ne mãsu zãlunci bã su cin nasara."
-
وَقَالَ فِرْعَوْنُ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلْمَلَأُ مَا عَلِمْتُ لَكُم مِّنْ إِلَـٰهٍ غَيْرِى فَأَوْقِدْ لِى يَـٰهَـٰمَـٰنُ عَلَى ٱلطِّينِ فَٱجْعَل لِّى صَرْحًا لَّعَلِّىٓ أَطَّلِعُ إِلَىٰٓ إِلَـٰهِ مُوسَىٰ وَإِنِّى لَأَظُنُّهُۥ مِنَ ٱلْكَـٰذِبِينَ٣٨
Waqala firʿawnu ya ayyuha almalao ma ʿalimtu lakum min ilahin ghayree faawqid lee ya hamanu ʿala altteeni faijʿal lee sarhan laʿallee attaliʿu ila ilahi moosa wainnee laathunnuhu mina alkathibeena
Kuma Fir'auna ya ce: "Yã ku mashãwarta! Ban san kunã da wani abin bautãwa baicina ba, sabõda haka ka hũra mini wuta, ya Hãmãnu! a kan lãka1 (dõmin a yi tũbali), sa'an nan ka sanya mini bẽne tsammãnĩna zan ninƙãya zuwa ga Ubangijin Mũsã kuma lalle ne ni, haƙĩƙa, inã zaton sa daga maƙaryata."
Bayanai
[1] Fir'auna ya fãra yin gasasshen tũbali da ake cewa ajurru, aka gina masa dõgon bene, ya hau samansa, ya harba kibiya ta tafi ama, ta kõmo da jini. Saĩ ya ce: "yã kashe Ubangijin Mũsa." Bayan haka sai benen ya karye guntu uku' guntu ɗaya ya fãɗa wa sõjansa, da yawa daga cikinsu suka mutu, guntu ɗaya kuma ya fãɗa a cikin ruwa, sauran guntu ɗaya ya fãɗa wa magina, suka mutu. Kuma cewar Fir'auna, "Lalle ne nĩ, inã zuton Mũsã daga maƙaryata," ya nũna girman kansa kawai ne ya hana shi ĩmãni, ba rashin gãnewa ba, sai dai kuma sun ga kamar bãbu Tãshin Ƙiyãma. -
وَٱسْتَكْبَرَ هُوَ وَجُنُودُهُۥ فِى ٱلْأَرْضِ بِغَيْرِ ٱلْحَقِّ وَظَنُّوٓا۟ أَنَّهُمْ إِلَيْنَا لَا يُرْجَعُونَ٣٩
Waistakbara huwa wajunooduhu fee alardi bighayri alhaqqi wathannoo annahum ilayna la yurjaʿoona
Kuma ya kangare, shi da rundunõninsa a cikin ƙasa, bã da haƙƙi ba kuma suka zaci cẽwa sũ, bã zã a mayar da su zuwa gare Mu ba.
-
فَأَخَذْنَـٰهُ وَجُنُودَهُۥ فَنَبَذْنَـٰهُمْ فِى ٱلْيَمِّ ۖ فَٱنظُرْ كَيْفَ كَانَ عَـٰقِبَةُ ٱلظَّـٰلِمِينَ٤٠
Faakhathnahu wajunoodahu fanabathnahum fee alyammi faonthur kayfa kana ʿaqibatu alththalimeena
Sai Muka kãma shi, shĩ da rundunõninsa sai Muka jẽfa su a cikin kõgi. Sai ka dũbi yaddaãƙibar azzãlumai ta kasance.
-
وَجَعَلْنَـٰهُمْ أَئِمَّةً يَدْعُونَ إِلَى ٱلنَّارِ ۖ وَيَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ لَا يُنصَرُونَ٤١
Wajaʿalnahum aimmatan yadʿoona ila alnnari wayawma alqiyamati la yunsaroona
Kuma Muka sanya su shũgabanni, sunã kira zuwa ga wuta, kuma a Rãnar ¡iyãma bã zã a taimake su ba.
-
وَأَتْبَعْنَـٰهُمْ فِى هَـٰذِهِ ٱلدُّنْيَا لَعْنَةً ۖ وَيَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ هُم مِّنَ ٱلْمَقْبُوحِينَ٤٢
Waatbaʿnahum fee hathihi alddunya laʿnatan wayawma alqiyamati hum mina almaqbooheena
Kuma Muka biyar musu da la'ana a cikin wannan dũniyakuma a Rãnar ¡iyãma sunã daga waɗanda aka mũnana halittarsu.
-
وَلَقَدْ ءَاتَيْنَا مُوسَى ٱلْكِتَـٰبَ مِنۢ بَعْدِ مَآ أَهْلَكْنَا ٱلْقُرُونَ ٱلْأُولَىٰ بَصَآئِرَ لِلنَّاسِ وَهُدًى وَرَحْمَةً لَّعَلَّهُمْ يَتَذَكَّرُونَ٤٣
Walaqad atayna moosa alkitaba min baʿdi ma ahlakna alquroona aloola basaira lilnnasi wahudan warahmatan laʿallahum yatathakkaroona
Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã Littãfi daga bãyan Mun halakar da ƙarnõnin farko, dõmin su zama abũbuwan kula ga mutãne, da shiriya da rahama, tsammãninsu sunã tunãwa.
-
وَمَا كُنتَ بِجَانِبِ ٱلْغَرْبِىِّ إِذْ قَضَيْنَآ إِلَىٰ مُوسَى ٱلْأَمْرَ وَمَا كُنتَ مِنَ ٱلشَّـٰهِدِينَ٤٤
Wama kunta bijanibi algharbiyyi ith qadayna ila moosa alamra wama kunta mina alshshahideena
Kuma ba ka kasance ba ga gẽfen rãfi na yamma a lõkacin da Muka hukunta al'amaru zuwa ga Mũsã, kuma ba ka kasance daga halartattu ba.
-
وَلَـٰكِنَّآ أَنشَأْنَا قُرُونًا فَتَطَاوَلَ عَلَيْهِمُ ٱلْعُمُرُ ۚ وَمَا كُنتَ ثَاوِيًا فِىٓ أَهْلِ مَدْيَنَ تَتْلُوا۟ عَلَيْهِمْ ءَايَـٰتِنَا وَلَـٰكِنَّا كُنَّا مُرْسِلِينَ٤٥
Walakinna anshana quroonan fatatawala ʿalayhimu alʿumuru wama kunta thawiyan fee ahli madyana tatloo ʿalayhim ayatina walakinna kunna mursileena
Kuma amma Mũ, Mun ƙãga halittawar wasu ƙarnõni har lõkatan rãyuwa suka yi tsawo a kansu. Kuma ba ka kasance mazauni ba a cikin mutãnen Madyana, kanã karanta musu ãyõyinMu, amma Mũ Mun kasãnce mãsu aikãwa (da kai game1 da waɗancan lãbarai).
Bayanai
[1] Sanin waɗannan abũbuwa duka ga Ummiyyi a wuri mai nĩsa daga wurin da abin ya auku a ciki, da kuma nĩsa daga waɗanda abin ya fi shãfuwa, ya nũna gaskiyar abin da kake da'awa. Kuma yanã natsar da zũciyarka da zũciyar waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi hijira tãre da ku, cewa sunã cikin tsaron Allah. -
وَمَا كُنتَ بِجَانِبِ ٱلطُّورِ إِذْ نَادَيْنَا وَلَـٰكِن رَّحْمَةً مِّن رَّبِّكَ لِتُنذِرَ قَوْمًا مَّآ أَتَىٰهُم مِّن نَّذِيرٍ مِّن قَبْلِكَ لَعَلَّهُمْ يَتَذَكَّرُونَ٤٦
Wama kunta bijanibi alttoori ith nadayna walakin rahmatan min rabbika litunthira qawman ma atahum min natheerin min qablika laʿallahum yatathakkaroona
Kuma ba ka kasance ga gẽfen dũtse ba a lõkacin da Muka yi kira, kuma amma dõmin rahama daga Ubangijinka, dõmin ka yi gargaɗi ga mutãne waɗanda suke wani mai gargaɗi a gabãninka bai je musu ba, tsammãninsu sunã tunãwa.
-
وَلَوْلَآ أَن تُصِيبَهُم مُّصِيبَةٌۢ بِمَا قَدَّمَتْ أَيْدِيهِمْ فَيَقُولُوا۟ رَبَّنَا لَوْلَآ أَرْسَلْتَ إِلَيْنَا رَسُولًا فَنَتَّبِعَ ءَايَـٰتِكَ وَنَكُونَ مِنَ ٱلْمُؤْمِنِينَ٤٧
Walawla an tuseebahum museebatun bima qaddamat aydeehim fayaqooloo rabbana lawla arsalta ilayna rasoolan fanattabiʿa ayatika wanakoona mina almumineena
Kuma bã dõmin wata masĩfa ta sãme su ba sabõda abin da hannayensu suka gabãtar, su ce: "Yã Ubangijinmu! Don me ba Ka aiko wani Manzo zuwa gare mu ba, har mu dinga bĩn ãyõyinKa, kuma mu kasance daga mũminai?"
-
فَلَمَّا جَآءَهُمُ ٱلْحَقُّ مِنْ عِندِنَا قَالُوا۟ لَوْلَآ أُوتِىَ مِثْلَ مَآ أُوتِىَ مُوسَىٰٓ ۚ أَوَلَمْ يَكْفُرُوا۟ بِمَآ أُوتِىَ مُوسَىٰ مِن قَبْلُ ۖ قَالُوا۟ سِحْرَانِ تَظَـٰهَرَا وَقَالُوٓا۟ إِنَّا بِكُلٍّ كَـٰفِرُونَ٤٨
Falamma jaahumu alhaqqu min ʿindina qaloo lawla ootiya mithla ma ootiya moosa awalam yakfuroo bima ootiya moosa min qablu qaloo sihrani tathahara waqaloo inna bikullin kafiroona
Sa'an nan a lõkacin da gaskiya ta jẽ musu daga wurin Mu, suka ce: "Don me ba a bã shi kamar abin da aka bai wa Mũsã ba?" Shin kuma ba su kãfirta ba da abin da aka bai wa Mũsã a gabãnin (wannan)? suka ce: "Sihirõri biyu ne suka taimaki jũna," kuma suka ce: "Lalle ne mũ, mãsu kãfirta ne ga dukansu?"
-
قُلْ فَأْتُوا۟ بِكِتَـٰبٍ مِّنْ عِندِ ٱللَّهِ هُوَ أَهْدَىٰ مِنْهُمَآ أَتَّبِعْهُ إِن كُنتُمْ صَـٰدِقِينَ٤٩
Qul fatoo bikitabin min ʿindi Allahi huwa ahda minhuma attabiʿhu in kuntum sadiqeena
Ka ce: "To ku zo da wani littãfi daga, wurin Allah, wanda yake shi ne mafi shiryarwa daga gare su, in bĩ shi, idan kunkasance mãsu gaskiya."
-
فَإِن لَّمْ يَسْتَجِيبُوا۟ لَكَ فَٱعْلَمْ أَنَّمَا يَتَّبِعُونَ أَهْوَآءَهُمْ ۚ وَمَنْ أَضَلُّ مِمَّنِ ٱتَّبَعَ هَوَىٰهُ بِغَيْرِ هُدًى مِّنَ ٱللَّهِ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهْدِى ٱلْقَوْمَ ٱلظَّـٰلِمِينَ٥٠
Fain lam yastajeeboo laka faiʿlam annama yattabiʿoona ahwaahum waman adallu mimmani ittabaʿa hawahu bighayri hudan mina Allahi inna Allaha la yahdee alqawma alththalimeena
To, idan ba su karɓa maka ba to sai ka sani sunã bin son zuciyarsu ne kawai, kuma wãne ne mafi ɓata daga wanda ya bi son zuciyarsa, bã tãre da wata shiriya daga Allah ba? Lalle ne, Allah bã ya shiryar da mutãne azzãlumai.
-
۞ وَلَقَدْ وَصَّلْنَا لَهُمُ ٱلْقَوْلَ لَعَلَّهُمْ يَتَذَكَّرُونَ٥١
Walaqad wassalna lahumu alqawla laʿallahum yatathakkaroona
Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun sãdar1 da magana sabõda su, tsammãninsu, suna tunãni.
Bayanai
[1] Attaura da Alƙur'ãni. Ayyukan Annabawa sãshen Su sun sãdu da sãshe. -
ٱلَّذِينَ ءَاتَيْنَـٰهُمُ ٱلْكِتَـٰبَ مِن قَبْلِهِۦ هُم بِهِۦ يُؤْمِنُونَ٥٢
Allatheena ataynahumu alkitaba min qablihi hum bihi yuminoona
Waɗanda Muka bã su littãfi daga gabãninsa (Alƙur'ãni), su mãsu ĩmãni ne da shi.1
Bayanai
[1] Mun sãdar da ilmin Taurãta da ilmin Alƙur'ãni, kowãne ya gaskata wani, ko kuwa Mun sãdar da maganar Alƙur'ani, wata ta bi wata, babu bambanci ga fasãha da abũbuwan ban mãmaki a cikinsu. -
وَإِذَا يُتْلَىٰ عَلَيْهِمْ قَالُوٓا۟ ءَامَنَّا بِهِۦٓ إِنَّهُ ٱلْحَقُّ مِن رَّبِّنَآ إِنَّا كُنَّا مِن قَبْلِهِۦ مُسْلِمِينَ٥٣
Waitha yutla ʿalayhim qaloo amanna bihi innahu alhaqqu min rabbina inna kunna min qablihi muslimeena
Kuma idan anã karanta shi a kansu, sai su ce: "Mun yi ĩmãni da shi, lalle shi ne gaskiya daga Ubangijinmu. Lalle mũ, mun kasance a gabãninsa masu sallamãwa."
-
أُو۟لَـٰٓئِكَ يُؤْتَوْنَ أَجْرَهُم مَّرَّتَيْنِ بِمَا صَبَرُوا۟ وَيَدْرَءُونَ بِٱلْحَسَنَةِ ٱلسَّيِّئَةَ وَمِمَّا رَزَقْنَـٰهُمْ يُنفِقُونَ٥٤
Olaika yutawna ajrahum marratayni bima sabaroo wayadraoona bialhasanati alssayyiata wamimma razaqnahum yunfiqoona
Waɗancan anã ba su lãdansu sau biyu, sabõda haƙurin da suka yi, kuma da kyautatãwa suna tunkuɗewar mũnanãwa kuma daga abin da Muka azũrtã susunã ciyarwa.
-
وَإِذَا سَمِعُوا۟ ٱللَّغْوَ أَعْرَضُوا۟ عَنْهُ وَقَالُوا۟ لَنَآ أَعْمَـٰلُنَا وَلَكُمْ أَعْمَـٰلُكُمْ سَلَـٰمٌ عَلَيْكُمْ لَا نَبْتَغِى ٱلْجَـٰهِلِينَ٥٥
Waitha samiʿoo allaghwa aʿradoo ʿanhu waqaloo lana aʿmaluna walakum aʿmalukum salamun ʿalaykum la nabtaghee aljahileena
Kuma idan sun ji yãsassar magana sukan kau da kai daga barinta, kuma sukan ce, "Ayyukanmu sunã a gare mu, kuma ayyukanku sunã a gare ku, aminci ya tabbata a kanmu bã mu nẽman jãhilai (da husũma)."1
Bayanai
[1] Waɗanda aka bai wa littafi a gabãnĩn Alƙur'ãni, sũ ne Yahũdu da Nasãra,waɗansu daga cikin Malamansu sun musulunta, kamar Abdullahi bn salãmi daga Yahũdu, da Nasãran Najrãna daga Nasãra, sun musulunta. Idan ba'ali ya musulunta sai a ce dukansu ke nan sun musulunta, sai wanda ya yi girman kai ya ƙigaskiya. Bã zã a kula da shi ba. -
إِنَّكَ لَا تَهْدِى مَنْ أَحْبَبْتَ وَلَـٰكِنَّ ٱللَّهَ يَهْدِى مَن يَشَآءُ ۚ وَهُوَ أَعْلَمُ بِٱلْمُهْتَدِينَ٥٦
Innaka la tahdee man ahbabta walakinna Allaha yahdee man yashao wahuwa aʿlamu bialmuhtadeena
Lalle ne kai bã ka shiryar1 da wanda ka so, amma kuma Allah Yanã shiryar da wanda Yake so, kuma Shi ne Mafi sani daga mãsu shiryuwa.
Bayanai
[1] Annabi, tsĩra da aminci su tabbata a gare shi, ya kasance yanã son mutãnensa Ƙuraishãwa su shiryu har dai Amminsa Abu Talib, sai Allah Ya gaya masa cewa shiriya ga hannunsa take, shi kaɗai, kuma sai wanda Ya so, shi ne zai shiryu, amma kuma akwai daga cikin dalĩlai bayyanannu maganar hijira kamar yadda ãyar da ke tafe ta bayyana. -
وَقَالُوٓا۟ إِن نَّتَّبِعِ ٱلْهُدَىٰ مَعَكَ نُتَخَطَّفْ مِنْ أَرْضِنَآ ۚ أَوَلَمْ نُمَكِّن لَّهُمْ حَرَمًا ءَامِنًا يُجْبَىٰٓ إِلَيْهِ ثَمَرَٰتُ كُلِّ شَىْءٍ رِّزْقًا مِّن لَّدُنَّا وَلَـٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَ٥٧
Waqaloo in nattabiʿi alhuda maʿaka nutakhattaf min ardina awalam numakkin lahum haraman aminan yujba ilayhi thamaratu kulli shayin rizqan min ladunna walakinna aktharahum la yaʿlamoona
Kuma suka ce: "Idan mun bi shiriya tãre da kai anã fizge mu1 daga ƙasamiu." Shin, ba Mu tabbatar musu da mallakar Hurumi ba, ya zama amintacce, anã jãwõwa zuwa gare shi, 'ya'yan itãcen kõwane iri, bisa ga azurtãwa daga gare Mu? Amma kuma mafi yawansu ba su sani ba.
Bayanai
[1] Wanda ya makkana musu Hurumi ya zama amintacce, yanã iya tsare bãwanSa kuma Yabã shi arziki a kõ'ina yake a cikin ƙasa, sabõda haka tsõron fita daga Hurumi da tsõron wuyar abinci a wurin baƙunci, bã zai hana mũmini ya yi hijira da addininsa ba zuwa wurin yardar Allah. -
وَكَمْ أَهْلَكْنَا مِن قَرْيَةٍۭ بَطِرَتْ مَعِيشَتَهَا ۖ فَتِلْكَ مَسَـٰكِنُهُمْ لَمْ تُسْكَن مِّنۢ بَعْدِهِمْ إِلَّا قَلِيلًا ۖ وَكُنَّا نَحْنُ ٱلْوَٰرِثِينَ٥٨
Wakam ahlakna min qaryatin batirat maʿeeshataha fatilka masakinuhum lam tuskan min baʿdihim illa qaleelan wakunna nahnu alwaritheena
Kuma da yawa Muka halakar da wata alƙarya wadda ta yi butulci ga rãyuwarta. To, waɗancan gidãjensu ne, ba a zaune su ba, a bãyansu, fãce kaɗan. Kuma mun kasance Mũ ne Magãda.
-
وَمَا كَانَ رَبُّكَ مُهْلِكَ ٱلْقُرَىٰ حَتَّىٰ يَبْعَثَ فِىٓ أُمِّهَا رَسُولًا يَتْلُوا۟ عَلَيْهِمْ ءَايَـٰتِنَا ۚ وَمَا كُنَّا مُهْلِكِى ٱلْقُرَىٰٓ إِلَّا وَأَهْلُهَا ظَـٰلِمُونَ٥٩
Wama kana rabbuka muhlika alqura hatta yabʿatha fee ommiha rasoolan yatloo ʿalayhim ayatina wama kunna muhlikee alqura illa waahluha thalimoona
Kuma Ubangijinka bai kasance Mai halaka alƙaryu ba, sai Ya aika a cikin hedkwatarsu da wani Manzo yanã karanta ãyõyinMu a kansu. Kuma ba Mu kasance Mãsu halaka alƙaryu ba, fãce mutanensu sun kasance mãsu zãlunci.
-
وَمَآ أُوتِيتُم مِّن شَىْءٍ فَمَتَـٰعُ ٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا وَزِينَتُهَا ۚ وَمَا عِندَ ٱللَّهِ خَيْرٌ وَأَبْقَىٰٓ ۚ أَفَلَا تَعْقِلُونَ٦٠
Wama ooteetum min shayin famataʿu alhayati alddunya wazeenatuha wama ʿinda Allahi khayrun waabqa afala taʿqiloona
Kuma abin da aka bã su daga kõme, to, jin dãɗin rayuwar dũniya ne da ƙawarta. Kuma abin da ke wurin Allah, shĩ ne mafi alhẽri, knma mafi wanzuwa. Shin bã ku hankalta?
-
أَفَمَن وَعَدْنَـٰهُ وَعْدًا حَسَنًا فَهُوَ لَـٰقِيهِ كَمَن مَّتَّعْنَـٰهُ مَتَـٰعَ ٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا ثُمَّ هُوَ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ مِنَ ٱلْمُحْضَرِينَ٦١
Afaman waʿadnahu waʿdan hasanan fahuwa laqeehi kaman mattaʿnahu mataʿa alhayati alddunya thumma huwa yawma alqiyamati mina almuhdareena
Shin fa, wanda Muka yi wa wa'adi, wa'adi mai kyau, sa'an nan shĩ mai haɗuwa da shi ne, yanã zama kamar wanda Muka jiyar da shi ɗan dãɗi, dãɗin rãyuwar dũniya, sa'an nan shi a Rãnar ¡iyãma yanã daga mãsu shiga wuta?
-
وَيَوْمَ يُنَادِيهِمْ فَيَقُولُ أَيْنَ شُرَكَآءِىَ ٱلَّذِينَ كُنتُمْ تَزْعُمُونَ٦٢
Wayawma yunadeehim fayaqoolu ayna shurakaiya allatheena kuntum tazʿumoona
Kuma rãnar da (Allah) Yake kiran su sa'an nan Ya ce: "Inã abõkan tãrayyaTa, waɗanda kuka kasance kunã rayãwa?"
-
قَالَ ٱلَّذِينَ حَقَّ عَلَيْهِمُ ٱلْقَوْلُ رَبَّنَا هَـٰٓؤُلَآءِ ٱلَّذِينَ أَغْوَيْنَآ أَغْوَيْنَـٰهُمْ كَمَا غَوَيْنَا ۖ تَبَرَّأْنَآ إِلَيْكَ ۖ مَا كَانُوٓا۟ إِيَّانَا يَعْبُدُونَ٦٣
Qala allatheena haqqa ʿalayhimu alqawlu rabbana haolai allatheena aghwayna aghwaynahum kama ghawayna tabarrana ilayka ma kanoo iyyana yaʿbudoona
Waɗanda magana ta wajaba a kansu, su ce: "Yã Ubangijinmu! Waɗannan sũ ne waɗanda muka halakar mun halakar da su kamar yadda muka halaka. Mun barranta zuwa gare Ka, ba su kasance mũ suke bautã wa ba."
-
وَقِيلَ ٱدْعُوا۟ شُرَكَآءَكُمْ فَدَعَوْهُمْ فَلَمْ يَسْتَجِيبُوا۟ لَهُمْ وَرَأَوُا۟ ٱلْعَذَابَ ۚ لَوْ أَنَّهُمْ كَانُوا۟ يَهْتَدُونَ٦٤
Waqeela odʿoo shurakaakum fadaʿawhum falam yastajeeboo lahum waraawoo alʿathaba law annahum kanoo yahtadoona
Kuma a ce ku kirãwo abõkan tãrayyar ɗinku, sai su kira su, sai ba su amsa ba, kuma su ga azãbar. Dã dai lalle su sun kasance snnã shiryuwa1!
Bayanai
[1] An shãfe jawãbi. ƘaddarawarSa ita ce: "Dã Sun kaSance sunã shiryuwa a dũniya, dã ba su gan ta ba a Lãhira.". -
وَيَوْمَ يُنَادِيهِمْ فَيَقُولُ مَاذَآ أَجَبْتُمُ ٱلْمُرْسَلِينَ٦٥
Wayawma yunadeehim fayaqoolu matha ajabtumu almursaleena
Kuma rãnar da Yake kiran su, sa'an nan Ya ce: "Mẽne nekuka karɓa wa Mananni?"
-
فَعَمِيَتْ عَلَيْهِمُ ٱلْأَنۢبَآءُ يَوْمَئِذٍ فَهُمْ لَا يَتَسَآءَلُونَ٦٦
Faʿamiyat ʿalayhimu alanbao yawmaithin fahum la yatasaaloona
Sai lãbãru su ɓace musu a rãnar nan sa'an nan bã zã su tambayi jũnansu ba.
-
فَأَمَّا مَن تَابَ وَءَامَنَ وَعَمِلَ صَـٰلِحًا فَعَسَىٰٓ أَن يَكُونَ مِنَ ٱلْمُفْلِحِينَ٦٧
Faamma man taba waamana waʿamila salihan faʿasa an yakoona mina almufliheena
To, amma wanda ya tũba, kuma ya yi ĩmãni' ya aikata aiki na ƙwarai, to, akwai fãtan su kasance daga mãsu cin nasara.
-
وَرَبُّكَ يَخْلُقُ مَا يَشَآءُ وَيَخْتَارُ ۗ مَا كَانَ لَهُمُ ٱلْخِيَرَةُ ۚ سُبْحَـٰنَ ٱللَّهِ وَتَعَـٰلَىٰ عَمَّا يُشْرِكُونَ٦٨
Warabbuka yakhluqu ma yashao wayakhtaru ma kana lahumu alkhiyaratu subhana Allahi wataʿala ʿamma yushrikoona
Kuma Ubangijinka Yanã halitta abin da Yake so kuma Yake zãɓi. Zãɓi bai kasance a gare su ba. Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma (Allah) Ya ɗaukaka daga barin abin da suke yi na shirka.
-
وَرَبُّكَ يَعْلَمُ مَا تُكِنُّ صُدُورُهُمْ وَمَا يُعْلِنُونَ٦٩
Warabbuka yaʿlamu ma tukinnu sudooruhum wama yuʿlinoona
Kuma Ubangijinka Yanã sanin abin da zukãtansu ke ɓõyẽwa, da abin da suke bayyanãwa.
-
وَهُوَ ٱللَّهُ لَآ إِلَـٰهَ إِلَّا هُوَ ۖ لَهُ ٱلْحَمْدُ فِى ٱلْأُولَىٰ وَٱلْـَٔاخِرَةِ ۖ وَلَهُ ٱلْحُكْمُ وَإِلَيْهِ تُرْجَعُونَ٧٠
Wahuwa Allahu la ilaha illa huwa lahu alhamdu fee aloola waalakhirati walahu alhukmu wailayhi turjaʿoona
Kuma Shĩ ne Allah, bãbu abin bautãwa fãce Shi. Kuma Shi ne abin gõdiya a cikin ta farko (dũniya), da ta ƙarshe (Lãhira). Kuma Shi ne da hukunci, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku.
-
قُلْ أَرَءَيْتُمْ إِن جَعَلَ ٱللَّهُ عَلَيْكُمُ ٱلَّيْلَ سَرْمَدًا إِلَىٰ يَوْمِ ٱلْقِيَـٰمَةِ مَنْ إِلَـٰهٌ غَيْرُ ٱللَّهِ يَأْتِيكُم بِضِيَآءٍ ۖ أَفَلَا تَسْمَعُونَ٧١
Qul araaytum in jaʿala Allahu ʿalaykumu allayla sarmadan ila yawmi alqiyamati man ilahun ghayru Allahi yateekum bidiyain afala tasmaʿoona
Ka ce: "Shin, kun gani, idan Allah Ya sanya dare tutur a kanku har zuwa Rãnar ¡iyãma, wane abin bautãwa wanin Allah zai zo muku da haske? Shin, bã ku ji?"
-
قُلْ أَرَءَيْتُمْ إِن جَعَلَ ٱللَّهُ عَلَيْكُمُ ٱلنَّهَارَ سَرْمَدًا إِلَىٰ يَوْمِ ٱلْقِيَـٰمَةِ مَنْ إِلَـٰهٌ غَيْرُ ٱللَّهِ يَأْتِيكُم بِلَيْلٍ تَسْكُنُونَ فِيهِ ۖ أَفَلَا تُبْصِرُونَ٧٢
Qul araaytum in jaʿala Allahu ʿalaykumu alnnahara sarmadan ila yawmi alqiyamati man ilahun ghayru Allahi yateekum bilaylin taskunoona feehi afala tubsiroona
Ka ce: "Shin, kun gani, idan Allah Ya sanya yini a kanku tutur zuwa Rãnar ¡iyãma, wane abin bautãwa, wanin Allah, zai zo muku da dare wanda kunã natsuwa a cikinsa? Shin fa, bã ku gani?"
-
وَمِن رَّحْمَتِهِۦ جَعَلَ لَكُمُ ٱلَّيْلَ وَٱلنَّهَارَ لِتَسْكُنُوا۟ فِيهِ وَلِتَبْتَغُوا۟ مِن فَضْلِهِۦ وَلَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ٧٣
Wamin rahmatihi jaʿala lakumu allayla waalnnahara litaskunoo feehi walitabtaghoo min fadlihi walaʿallakum tashkuroona
"Kuma daga rahamarSa Ya sanya muku dare da yini dõmin ku natsu a cikinsa, kuma dõmin ku nẽma daga falalar Sa, kuma tsammãninku zã ku gõde."
-
وَيَوْمَ يُنَادِيهِمْ فَيَقُولُ أَيْنَ شُرَكَآءِىَ ٱلَّذِينَ كُنتُمْ تَزْعُمُونَ٧٤
Wayawma yunadeehim fayaqoolu ayna shurakaiya allatheena kuntum tazʿumoona
Kuma a rãnar da Yake kiran su ya ce: "Inã abõkan tarayya Ta, waɗanda kuka kasance kunã riyãwa"1
Bayanai
[1] Bãyan Allah Ya tunãtar da Musulmi rahamarSa da kaɗaita ga bãyar da ni'ima kõ hana ta da siffõfi mãsu kwaɗaitar da mũmini ga ɗã'a ga Allah da ManzonSa, daga cikin ɗã'ã akwai yin hijira wanda yake shĩ ne kan lãbãrin sũrar, sai kuma Ya tsõratar da mai bin wanin Allah ga rashin yin hijira. Duka abin da ya hana mũminai hijira idan shi abin nan ba uzuri ne na shari'a ba, to, ya zama gunki, abin bautãwa, wanin Allah. Umurnin da ya sãɓa wa umurnin Allah duka, umurnin abõkin tãrayya ne ga Allah ga wanda ya bĩ shi. -
وَنَزَعْنَا مِن كُلِّ أُمَّةٍ شَهِيدًا فَقُلْنَا هَاتُوا۟ بُرْهَـٰنَكُمْ فَعَلِمُوٓا۟ أَنَّ ٱلْحَقَّ لِلَّهِ وَضَلَّ عَنْهُم مَّا كَانُوا۟ يَفْتَرُونَ٧٥
Wanazaʿna min kulli ommatin shaheedan faqulna hatoo burhanakum faʿalimoo anna alhaqqa lillahi wadalla ʿanhum ma kanoo yaftaroona
Kuma Muka zãre mai shaida daga kõwace al'umma, sa'an nan Muka ce: "Ku kãwo dalilinku." Sai suka san cẽwa lalle gaskiya ga Allah take. Kuma abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa na ƙarya ya ɓace daga barinsu.
-
۞ إِنَّ قَـٰرُونَ كَانَ مِن قَوْمِ مُوسَىٰ فَبَغَىٰ عَلَيْهِمْ ۖ وَءَاتَيْنَـٰهُ مِنَ ٱلْكُنُوزِ مَآ إِنَّ مَفَاتِحَهُۥ لَتَنُوٓأُ بِٱلْعُصْبَةِ أُو۟لِى ٱلْقُوَّةِ إِذْ قَالَ لَهُۥ قَوْمُهُۥ لَا تَفْرَحْ ۖ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ ٱلْفَرِحِينَ٧٦
Inna qaroona kana min qawmi moosa fabagha ʿalayhim waataynahu mina alkunoozi ma inna mafatihahu latanooo bialʿusbati olee alquwwati ith qala lahu qawmuhu la tafrah inna Allaha la yuhibbu alfariheena
Lalle ne ¡ãrũna ya kasance daga mutãnen Mũsã, sai ya fita1 daga tsãrinsu alhãli Mun bã shi taskõkin abin da yake mabũɗansa sunã nauyi ga jama'a2 ma'abũta ƙarfi a lõkacin da mutãnensa suka ce masa, "Kada ka yi annashuwa, lalle ne Allah bã Ya son mãsu annashuwa."
Bayanai
[1] Asalin baghy zãlunci, amma ga izɗilãhi, shi ne fita daga ɗã'ar shugaban Musulmi. [2] Yawan su saba'in, an ce arba'in, kuma an ce gõma. -
وَٱبْتَغِ فِيمَآ ءَاتَىٰكَ ٱللَّهُ ٱلدَّارَ ٱلْـَٔاخِرَةَ ۖ وَلَا تَنسَ نَصِيبَكَ مِنَ ٱلدُّنْيَا ۖ وَأَحْسِن كَمَآ أَحْسَنَ ٱللَّهُ إِلَيْكَ ۖ وَلَا تَبْغِ ٱلْفَسَادَ فِى ٱلْأَرْضِ ۖ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ ٱلْمُفْسِدِينَ٧٧
Waibtaghi feema ataka Allahu alddara alakhirata wala tansa naseebaka mina alddunya waahsin kama ahsana Allahu ilayka wala tabghi alfasada fee alardi inna Allaha la yuhibbu almufsideena
"Kuma ka biɗã a cikin abin da Allah Ya bã ka, gidan Lãhira, kuma kada ka manta da rabonka daga dũniya. Kuma ka kyautata, kamar yadda Allah Ya kyautata zuwa gare ka, kuma kada ka nẽmi ɓarna a cikin ƙasa,1 lalle ne Allah bã Ya son mãsu barna."
Bayanai
[1] Ɓarna a cikin ƙasa, shi ne fita daga tsarin jama'a, da rabasu ƙungiya-ƙungiya, ko barin hijira a bãyan an yi umurni da yin ta. -
قَالَ إِنَّمَآ أُوتِيتُهُۥ عَلَىٰ عِلْمٍ عِندِىٓ ۚ أَوَلَمْ يَعْلَمْ أَنَّ ٱللَّهَ قَدْ أَهْلَكَ مِن قَبْلِهِۦ مِنَ ٱلْقُرُونِ مَنْ هُوَ أَشَدُّ مِنْهُ قُوَّةً وَأَكْثَرُ جَمْعًا ۚ وَلَا يُسْـَٔلُ عَن ذُنُوبِهِمُ ٱلْمُجْرِمُونَ٧٨
Qala innama ooteetuhu ʿala ʿilmin ʿindee awalam yaʿlam anna Allaha qad ahlaka min qablihi mina alqurooni man huwa ashaddu minhu quwwatan waaktharu jamʿan wala yusalu ʿan thunoobihimu almujrimoona
Ya ce: "An bã ni shi a kan wani ilmi wanda yake gare ni ne kawai." Shin, kuma bai sani ba cẽwa lalle Allah haƙiƙa Ya halakar a gabaninsa, daga ƙarnõni, wanda yake Shi ne mafi tsananin ƙarfi daga gare shi, kuma mafi yawan tãrawar dũkiya, kuma bã zã a tambayi mãsu laifi daga zunubansu ba?1
Bayanai
[1] Yanã ganin dũkiyar da ya samu, ya sãme ta ne sabõda ya san ilmin fatauci da sana'a kuma yanã da ƙarfin neman dũkiyar, sabõda raddin irin tunãninsa Allah Ya ce Ya halaka wanda ya fi shi tsananin ƙarfi da ƙõƙarin tãra dũkiya, kuma idan Ya tãshi halaka mai laifi bã Ya tsayãwa tambayarsa dalĩlin da ya sa ya yi laifin kãfin Ya halakar da shi. Waɗannan abũbuwa uku sun isa ga mai dũkiya ya yi tunãni, dõmin kada annashuwa ta shige shi ya ƙi gõde waAllah. -
فَخَرَجَ عَلَىٰ قَوْمِهِۦ فِى زِينَتِهِۦ ۖ قَالَ ٱلَّذِينَ يُرِيدُونَ ٱلْحَيَوٰةَ ٱلدُّنْيَا يَـٰلَيْتَ لَنَا مِثْلَ مَآ أُوتِىَ قَـٰرُونُ إِنَّهُۥ لَذُو حَظٍّ عَظِيمٍ٧٩
Fakharaja ʿala qawmihi fee zeenatihi qala allatheena yureedoona alhayata alddunya ya layta lana mithla ma ootiya qaroonu innahu lathoo haththin ʿatheemin
Sai (¡ãrũna) ya fita a kan mutãnensa a cikin adonsa. Waɗanda suke nufin rãyuwar dũniya suka ce: "Inã dai munã da kwatancin abin da aka bai wa ¡ãrũna! Lalle shĩ haƙĩƙa ma'abũcin rabo babba ne."
-
وَقَالَ ٱلَّذِينَ أُوتُوا۟ ٱلْعِلْمَ وَيْلَكُمْ ثَوَابُ ٱللَّهِ خَيْرٌ لِّمَنْ ءَامَنَ وَعَمِلَ صَـٰلِحًا وَلَا يُلَقَّىٰهَآ إِلَّا ٱلصَّـٰبِرُونَ٨٠
Waqala allatheena ootoo alʿilma waylakum thawabu Allahi khayrun liman amana waʿamila salihan wala yulaqqaha illa alssabiroona
Kuma waɗanda aka bai wa ilmi suka ce: "Kaitonku! sakamakon Allah ne mafi alhẽri a wanda ya yi tunãni, kuma ya aikata aikin ƙwarai,1 kuma bãbu wanda ake haɗãwa da ita fãce mai haƙuri."
Bayanai
[1] ĩmãni da aikin ƙwarai wanda Allah Ya yi umurni da a yi shi, kuma yinsa kamar yadda ManzonSa ya nũna. Akwai daga cikin aikin ƙwarai yin hijira da barin kula da dũkiya. Bã a sãmun sakamakon Allah sai da haƙuri. -
فَخَسَفْنَا بِهِۦ وَبِدَارِهِ ٱلْأَرْضَ فَمَا كَانَ لَهُۥ مِن فِئَةٍ يَنصُرُونَهُۥ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَمَا كَانَ مِنَ ٱلْمُنتَصِرِينَ٨١
Fakhasafna bihi wabidarihi alarda fama kana lahu min fiatin yansuroonahu min dooni Allahi wama kana mina almuntasireena
Sai Muka shãfe ƙasa1 da shi da kuma gidansa. To, waɗansu jama'a ba su kasance gare shi ba, waɗanda suke taimakon sa, baicin Allah, kuma shi bai kasance daga mãsu taimakon kansu ba.
Bayanai
[1] An ce a bãyan Ƙãrũna ya yanke kansa da nasa mutãne daga Mũsã, sai ya shirya da wata kãruwa dõmin ta yi wa Mũsã ƙazafin cewa ya yi zina da ita, a kan ya aure ta. Sai Mũsãya tãshi yanã wa'azi a cikin Banĩ Isrã'ĩla ya ce: "Yã Banĩ Isrã'ĩla wanda ya yi sãta zã mu yanke hannunsa, wanda yayi ƙazafi mu yi masa bũlãla tamãnin, wanda ya yi zina, bã ya da mãtã, mu yi masa bũlãla ɗãri, wanda ya yi zina yanã da mãtã, mu jefe Shi sai yã mutu." Sai Ƙãruna ya ce: "Kõ dã kai ne?" Ya ce: "Kõ da ni ne." Sai Kãrũna ya ce: "An ce kã yi fãjirci tãre da wance, kãruwa." Sai Mũsã ya ce: "A kirã ta" Da ta zo, ya gama ta da Allah, ta faɗi gaskiya, sai ta ce Ƙãrũna ne ya yi tsãda da ita, ta faɗi hakanan. Sai Mũsã ya yi addu'a a kansa, ƙasa ta haɗiye shi, shi da gidansa duka. -
وَأَصْبَحَ ٱلَّذِينَ تَمَنَّوْا۟ مَكَانَهُۥ بِٱلْأَمْسِ يَقُولُونَ وَيْكَأَنَّ ٱللَّهَ يَبْسُطُ ٱلرِّزْقَ لِمَن يَشَآءُ مِنْ عِبَادِهِۦ وَيَقْدِرُ ۖ لَوْلَآ أَن مَّنَّ ٱللَّهُ عَلَيْنَا لَخَسَفَ بِنَا ۖ وَيْكَأَنَّهُۥ لَا يُفْلِحُ ٱلْكَـٰفِرُونَ٨٢
Waasbaha allatheena tamannaw makanahu bialamsi yaqooloona waykaanna Allaha yabsutu alrrizqa liman yashao min ʿibadihi wayaqdiru lawla an manna Allahu ʿalayna lakhasafa bina waykaannahu la yuflihu alkafiroona
Kuma waɗanda suka yi bũrin matsayinsa a jiya suka wãyi gari sunã cẽwa, "Wai! Allah Yanã shimfiɗa arziki, ga wanda Yake so daga bãyinsa, kuma Yanã ƙuntatãwa. Bã dõmin Allah Ya yi mana falala ba dã Yã shãfe ƙasa da mu. Wai! lalle ne shi, kãfirai bã su cin nasara."
-
تِلْكَ ٱلدَّارُ ٱلْـَٔاخِرَةُ نَجْعَلُهَا لِلَّذِينَ لَا يُرِيدُونَ عُلُوًّا فِى ٱلْأَرْضِ وَلَا فَسَادًا ۚ وَٱلْعَـٰقِبَةُ لِلْمُتَّقِينَ٨٣
Tilka alddaru alakhiratu najʿaluha lillatheena la yureedoona ʿuluwwan fee alardi wala fasadan waalʿaqibatu lilmuttaqeena
Wancan gidan Lãhira Munã sanya shi ga waɗanda suke bã su nufin ɗaukaka a cikin rãyuwar dũniya kuma bã su son ɓarna. Kuma ãkiba ga mãsu taƙawa take.
-
مَن جَآءَ بِٱلْحَسَنَةِ فَلَهُۥ خَيْرٌ مِّنْهَا ۖ وَمَن جَآءَ بِٱلسَّيِّئَةِ فَلَا يُجْزَى ٱلَّذِينَ عَمِلُوا۟ ٱلسَّيِّـَٔاتِ إِلَّا مَا كَانُوا۟ يَعْمَلُونَ٨٤
Man jaa bialhasanati falahu khayrun minha waman jaa bialssayyiati fala yujza allatheena ʿamiloo alssayyiati illa ma kanoo yaʿmaloona
Wanda ya zo da abu mai kyau, to, yana da mafi alhẽri daga gare shi, kuma wanda ya zo da mũgun abu, to, bã zã a sãkawa waɗanda suka aikata miyãgun ayyuka ba, fãce da abin da suka kasance sunã aikatãwa.
-
إِنَّ ٱلَّذِى فَرَضَ عَلَيْكَ ٱلْقُرْءَانَ لَرَآدُّكَ إِلَىٰ مَعَادٍ ۚ قُل رَّبِّىٓ أَعْلَمُ مَن جَآءَ بِٱلْهُدَىٰ وَمَنْ هُوَ فِى ضَلَـٰلٍ مُّبِينٍ٨٥
Inna allathee farada ʿalayka alqurana laradduka ila maʿadin qul rabbee aʿlamu man jaa bialhuda waman huwa fee dalalin mubeenin
Lalle ne wanda Ya faralta Alƙur'ãni a kanka, haƙĩƙa, Mai Mayar da kai ne zuwa ga makõma. ka ce: "Ubangijĩna ne Mafi sani ga wanda ya zo da shiriya, da kuma wanda yake a cikin ɓata bayyananne"
-
وَمَا كُنتَ تَرْجُوٓا۟ أَن يُلْقَىٰٓ إِلَيْكَ ٱلْكِتَـٰبُ إِلَّا رَحْمَةً مِّن رَّبِّكَ ۖ فَلَا تَكُونَنَّ ظَهِيرًا لِّلْكَـٰفِرِينَ٨٦
Wama kunta tarjoo an yulqa ilayka alkitabu illa rahmatan min rabbika fala takoonanna thaheeran lilkafireena
Kuma ba ka kasance kanã fãtan a jẽfa Littafin nan zuwa gare ka ba, fãce dai dõmin rahama daga Ubangijinka. Sabõda haka kada ka zama mai taimako1 ga kãfirai.
Bayanai
[1] Taimakon, shi ne ka yi bũrin musuluntarsu har ka wahala dõmin a sauƙaƙe ma hukuncin hijira wadda Allah Ya yi umurni da a yi ta a bãyan musulunta sai ka iyar da Manzanci, shiryarwa kuwa ga hannun Allah take. Wannan ãyã tanã nunãwa bayyana ƙaryar mãsu da'awar cewa wani mutum yanã bai wa wani ĩmãni ko ya karɓe shi daga gare shi. Kõwa a cikin tsõro yake, sai wanda Allah Ya sanya shi cikin aminci. Allah Ya sanya mu cikin amincinSa dõmin rahamarsa. -
وَلَا يَصُدُّنَّكَ عَنْ ءَايَـٰتِ ٱللَّهِ بَعْدَ إِذْ أُنزِلَتْ إِلَيْكَ ۖ وَٱدْعُ إِلَىٰ رَبِّكَ ۖ وَلَا تَكُونَنَّ مِنَ ٱلْمُشْرِكِينَ٨٧
Wala yasuddunnaka ʿan ayati Allahi baʿda ith onzilat ilayka waodʿu ila rabbika wala takoonanna mina almushrikeena
Kuma kada lalle su karkatar da kai daga barin ãyõyin Allah, a bãyãn har an saukar da su uwa gare ka. Ka yi kira zuwa ga Ubangijinka, kuma kada lalle ka kasance daga mãsu shirka.
-
وَلَا تَدْعُ مَعَ ٱللَّهِ إِلَـٰهًا ءَاخَرَ ۘ لَآ إِلَـٰهَ إِلَّا هُوَ ۚ كُلُّ شَىْءٍ هَالِكٌ إِلَّا وَجْهَهُۥ ۚ لَهُ ٱلْحُكْمُ وَإِلَيْهِ تُرْجَعُونَ٨٨
Wala tadʿu maʿa Allahi ilahan akhara la ilaha illa huwa kullu shayin halikun illa wajhahu lahu alhukmu wailayhi turjaʿoona
Kada ka kira wani abin bautãwa na dabam tãre da Allah. Bãbu abin bautãwa fãce Shi. Kõwane abu mai halaka ne fãce fuskar Sa. Shi ne da hukunci kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku.1
Bayanai
[1] Wannan ãyã ta ƙarshen sũrar, ta tãra ilmin da sũrar ta karantar a cikin abũbuwa biyar da ta zãna
Tambayoyin da ake yawan yi
Mece ce ma’anar sunan Suratul Ƙasas?
Ma’anar Ƙasas ita ce “Labarai”.
Suratul Ƙasas tana cikin juz’i na nawa?
Suratul Ƙasas tana cikin juz’i na 20.
Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Ƙasas?
Suratul Ƙasas tana da ayoyi 88.
Suratul Ƙasas Makkiya ce ko Madaniya?
Suratul Ƙasas sura ce Makkiya.
Suratul Ƙasas ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?
Ita ce sura ta 28 a cikin Alƙur’ani.
Majiyoyi
- Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
- Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
- Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
- Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
- Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
- Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.
Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.