سورة الشعراء
Suratul Shu’ara’i da fassarar Hausa
Mawaƙa
- 26
- ayoyi 227
- Makkiya
- Juz’i 19
- Shafuka 367–376
Suratul Shu’ara’i (الشعراء) ita ce sura ta 26 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 227. Ma’anar sunanta ita ce “Mawaƙa”. Sura ce Makkiya, wadda ta sauka a Makka kafin Hijira, kuma tana cikin juz’i na 19.
A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Shu’ara’i gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.
Suratul Shu’ara’i cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ
-
طسٓمٓ١
Taseenmeem
T. S̃. M̃.
-
تِلْكَ ءَايَـٰتُ ٱلْكِتَـٰبِ ٱلْمُبِينِ٢
Tilka ayatu alkitabi almubeeni
Waɗancan ãyõyin Littãfi ne bayyananne.
-
لَعَلَّكَ بَـٰخِعٌ نَّفْسَكَ أَلَّا يَكُونُوا۟ مُؤْمِنِينَ٣
Laʿallaka bakhiʿun nafsaka alla yakoonoo mumineena
Tsammãninka kai mai zaka halakar da ranka ne, dõn ba su zamanto mũminai ba!1
Bayanai
[1] Wannan yã nũna cewa Annabi Muhammadu yanã jin tsõron rashin ĩmãnin mutãnensa, kada ya zama shĩ ne ya gajarta daga abin da Allah Ya ɗõra a kansa, na iyar da manzanci. Haka mũmini yake, kullum girman Ubangijinsa yake dũbi, sabõda haka kõme ya yi na ɗã'a, sai ya ga kãsãwar kansa ga tsayuwa da hakkin Ubangijinsa, a kansa, ya ƙãra jin tsõro da tawãli'u. -
إِن نَّشَأْ نُنَزِّلْ عَلَيْهِم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ ءَايَةً فَظَلَّتْ أَعْنَـٰقُهُمْ لَهَا خَـٰضِعِينَ٤
In nasha nunazzil ʿalayhim mina alssamai ayatan fathallat aʿnaquhum laha khadiʿeena
Idan Mun so zã Mu saukar, a kansu, da wata ãyã daga sama, sai wuyõyinsu su yini sabõda ita sunã mãsu ƙasƙantar da kai.
-
وَمَا يَأْتِيهِم مِّن ذِكْرٍ مِّنَ ٱلرَّحْمَـٰنِ مُحْدَثٍ إِلَّا كَانُوا۟ عَنْهُ مُعْرِضِينَ٥
Wama yateehim min thikrin mina alrrahmani muhdathin illa kanoo ʿanhu muʿrideena
Kuma wata tunãtarwa ba ta jẽ musu ba, daga Mai rahama, sãbuwa, fãce sun kasance daga barinta sunã mãsu bijirẽwa.
-
فَقَدْ كَذَّبُوا۟ فَسَيَأْتِيهِمْ أَنۢبَـٰٓؤُا۟ مَا كَانُوا۟ بِهِۦ يَسْتَهْزِءُونَ٦
Faqad kaththaboo fasayateehim anbao ma kanoo bihi yastahzioona
To, lalle ne, sun ƙaryata, to, lãbãran abin da suka kasance sunã yi na izgili da shi zã ya je musu.
-
أَوَلَمْ يَرَوْا۟ إِلَى ٱلْأَرْضِ كَمْ أَنۢبَتْنَا فِيهَا مِن كُلِّ زَوْجٍ كَرِيمٍ٧
Awalam yaraw ila alardi kam anbatna feeha min kulli zawjin kareemin
Shin, ba su dũba ba zuwa ga ƙasa, da yawa Muka tsirar a cikinta, daga dukan nau'i mai kyau?
-
إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً ۖ وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ٨
Inna fee thalika laayatan wama kana aktharuhum mumineena
Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mũminai ba.
-
وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ٩
Wainna rabbaka lahuwa alʿazeezu alrraheemu
Kuma lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai rahama.
-
وَإِذْ نَادَىٰ رَبُّكَ مُوسَىٰٓ أَنِ ٱئْتِ ٱلْقَوْمَ ٱلظَّـٰلِمِينَ١٠
Waith nada rabbuka moosa ani iti alqawma alththalimeena
Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya kirãyi Mũsã, "Ka je wa mutãnen nan azzãlumai.
-
قَوْمَ فِرْعَوْنَ ۚ أَلَا يَتَّقُونَ١١
Qawma firʿawna ala yattaqoona
"Mutãnen Fir'auna bã zã su yi taƙawa ba?"
-
قَالَ رَبِّ إِنِّىٓ أَخَافُ أَن يُكَذِّبُونِ١٢
Qala rabbi innee akhafu an yukaththibooni
Ya ce: "Ya Ubangijĩna, nĩ inã tsõron su ƙaryata ni.
-
وَيَضِيقُ صَدْرِى وَلَا يَنطَلِقُ لِسَانِى فَأَرْسِلْ إِلَىٰ هَـٰرُونَ١٣
Wayadeequ sadree wala yantaliqu lisanee faarsil ila haroona
"Kuma ƙirjĩna ya yi ƙunci1 kuma harshẽna bã zai saku ba sabõda haka ka aika zuwa ga Harũna.
Bayanai
[1] Mũsa yanã nũna cewa, shi yanã jin tsõro kada ya zama ya gajarta wajen iyar da manzanci, dõmin shi mai saurin fushine, yanã neman a taimake shi ɗan'uwansa Hãrũna.Wannan ya yi kama da farkon sũrar inda Annabi, tshĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya nũna tsõron taƙaitãwa ga iyar da manzancin Allah zuwa ga mutãnensa dõmin haka ba su yi ĩmãni ba. Hãlin Annabawa duka ɗaya ne ga tsõron taƙaita aikin Ubangijinsu. -
وَلَهُمْ عَلَىَّ ذَنۢبٌ فَأَخَافُ أَن يَقْتُلُونِ١٤
Walahum ʿalayya thanbun faakhafu an yaqtulooni
"Kuma sunã da wani laifi a kaina, sabõda haka inã tsõron kada su kashe ni."
-
قَالَ كَلَّا ۖ فَٱذْهَبَا بِـَٔايَـٰتِنَآ ۖ إِنَّا مَعَكُم مُّسْتَمِعُونَ١٥
Qala kalla faithhaba biayatina inna maʿakum mustamiʿoona
Ya ce: "Kayya! Ku tafi, kũ biyu, da ÃyõyinMu. Lalle ne, Munã tãre da ku Munã Mãsu saurãre."
-
فَأْتِيَا فِرْعَوْنَ فَقُولَآ إِنَّا رَسُولُ رَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ١٦
Fatiya firʿawna faqoola inna rasoolu rabbi alʿalameena
"Sai ku je wa Fir'auna, sa'an nan ku ce, Lalle ne, mu, Manzannin Ubangijin halitta ne."
-
أَنْ أَرْسِلْ مَعَنَا بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ١٧
An arsil maʿana banee israeela
"Ka saki Banĩ Isrã'ila tãre da mu."
-
قَالَ أَلَمْ نُرَبِّكَ فِينَا وَلِيدًا وَلَبِثْتَ فِينَا مِنْ عُمُرِكَ سِنِينَ١٨
Qala alam nurabbika feena waleedan walabithta feena min ʿumurika sineena
Ya ce: "Shin, ba mu yi rẽnonka ba a cikinmu kanã jãrĩri, kuma ka zauna a cikinmu shẽkarudaga lõkacin rãyuwarka?"
-
وَفَعَلْتَ فَعْلَتَكَ ٱلَّتِى فَعَلْتَ وَأَنتَ مِنَ ٱلْكَـٰفِرِينَ١٩
Wafaʿalta faʿlataka allatee faʿalta waanta mina alkafireena
"Kuma ka aikata aikinka wanda ka aikata alhãli kai kanã daga butulai?"
-
قَالَ فَعَلْتُهَآ إِذًا وَأَنَا۠ مِنَ ٱلضَّآلِّينَ٢٠
Qala faʿaltuha ithan waana mina alddalleena
Ya ce: "Na aikata shi a lõkacin inã daga mãsu jãhilcin fushi."
-
فَفَرَرْتُ مِنكُمْ لَمَّا خِفْتُكُمْ فَوَهَبَ لِى رَبِّى حُكْمًا وَجَعَلَنِى مِنَ ٱلْمُرْسَلِينَ٢١
Fafarartu minkum lamma khiftukum fawahaba lee rabbee hukman wajaʿalanee mina almursaleena
"Sabõda haka na gudu daga gãre ku a lõkacin da na ji tsõronku, sai Ubangijĩna Ya bã ni hukunci, kuma Ya sanya ni daga Manzanni."
-
وَتِلْكَ نِعْمَةٌ تَمُنُّهَا عَلَىَّ أَنْ عَبَّدتَّ بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ٢٢
Watilka niʿmatun tamunnuha ʿalayya an ʿabbadta banee israeela
"Kuma waccan ni'ima ce, kanã gõrint a kaina, dõmin kã bautar da Banĩ Isrã'ĩla."
-
قَالَ فِرْعَوْنُ وَمَا رَبُّ ٱلْعَـٰلَمِينَ٢٣
Qala firʿawnu wama rabbu alʿalameena
Fir'auna ya ce: "Kuma mene ne Ubangijin halittu?"
-
قَالَ رَبُّ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَآ ۖ إِن كُنتُم مُّوقِنِينَ٢٤
Qala rabbu alssamawati waalardi wama baynahuma in kuntum mooqineena
Ya ce: "Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu ƙarfin ĩmãni."
-
قَالَ لِمَنْ حَوْلَهُۥٓ أَلَا تَسْتَمِعُونَ٢٥
Qala liman hawlahu ala tastamiʿoona
Ya ce wa waɗanda suke a gẽfensa, "Bã za ku saurãra ba?"
-
قَالَ رَبُّكُمْ وَرَبُّ ءَابَآئِكُمُ ٱلْأَوَّلِينَ٢٦
Qala rabbukum warabbu abaikumu alawwaleena
Ya ce: "Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko."
-
قَالَ إِنَّ رَسُولَكُمُ ٱلَّذِىٓ أُرْسِلَ إِلَيْكُمْ لَمَجْنُونٌ٢٧
Qala inna rasoolakumu allathee orsila ilaykum lamajnoonun
Ya ce: "Lalle ne Manzonku, wanda aka aiko zuwa gare ku, haƙi ƙa, mahaukaci ne."
-
قَالَ رَبُّ ٱلْمَشْرِقِ وَٱلْمَغْرِبِ وَمَا بَيْنَهُمَآ ۖ إِن كُنتُمْ تَعْقِلُونَ٢٨
Qala rabbu almashriqi waalmaghribi wama baynahuma in kuntum taʿqiloona
Ya ce: "Ubangijin mafitar rãnã da maɓũyarta da abin dayake a tsakaninsu, idan kun kasance kunã hankalta."
-
قَالَ لَئِنِ ٱتَّخَذْتَ إِلَـٰهًا غَيْرِى لَأَجْعَلَنَّكَ مِنَ ٱلْمَسْجُونِينَ٢٩
Qala laini ittakhathta ilahan ghayree laajʿalannaka mina almasjooneena
Ya ce: "Lalle ne idan ka riƙi wani abin bautãwa wanĩna haƙĩƙa, inã sanyã ka daga ɗaurarru."
-
قَالَ أَوَلَوْ جِئْتُكَ بِشَىْءٍ مُّبِينٍ٣٠
Qala awalaw jituka bishayin mubeenin
Ya ce: "Ashe, kuma kõ dã nã zõ maka da wani, abu mai bayyanãwa?"
-
قَالَ فَأْتِ بِهِۦٓ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّـٰدِقِينَ٣١
Qala fati bihi in kunta mina alssadiqeena
Ya ce: "To, ka zõ da shi idan ka kasance daga, mãsu gaskiya."
-
فَأَلْقَىٰ عَصَاهُ فَإِذَا هِىَ ثُعْبَانٌ مُّبِينٌ٣٢
Faalqa ʿasahu faitha hiya thuʿbanun mubeenun
Sai ya jẽfa sandarsa, sai ga ta kumurci bayyananne.
-
وَنَزَعَ يَدَهُۥ فَإِذَا هِىَ بَيْضَآءُ لِلنَّـٰظِرِينَ٣٣
Wanazaʿa yadahu faitha hiya baydao lilnnathireena
Kuma ya fizge hannunsa, sai ga shi fari ga mãsu kallo.
-
قَالَ لِلْمَلَإِ حَوْلَهُۥٓ إِنَّ هَـٰذَا لَسَـٰحِرٌ عَلِيمٌ٣٤
Qala lilmalai hawlahu inna hatha lasahirun ʿaleemun
(Fir'auna) ya ce ga mashãwarta a gẽfensa, "Lalle ne, wannan haƙĩƙa, masihirci ne, mai ilmi!
-
يُرِيدُ أَن يُخْرِجَكُم مِّنْ أَرْضِكُم بِسِحْرِهِۦ فَمَاذَا تَأْمُرُونَ٣٥
Yureedu an yukhrijakum min ardikum bisihrihi famatha tamuroona
"Yanã son ya fitar da ku daga ƙasarku game da sihirinSa. To mẽne ne kuke shãwartãwa?"
-
قَالُوٓا۟ أَرْجِهْ وَأَخَاهُ وَٱبْعَثْ فِى ٱلْمَدَآئِنِ حَـٰشِرِينَ٣٦
Qaloo arjih waakhahu waibʿath fee almadaini hashireena
Suka ce: "Ka jinkirtar da shi, shĩ da ɗan'uwansa, kuma ka aika mãsu gayya a cikin birãne."
-
يَأْتُوكَ بِكُلِّ سَحَّارٍ عَلِيمٍ٣٧
Yatooka bikulli sahharin ʿaleemin
"Zã su zõ maka da dukkan mai yawan sihiri masani."
-
فَجُمِعَ ٱلسَّحَرَةُ لِمِيقَـٰتِ يَوْمٍ مَّعْلُومٍ٣٨
Fajumiʿa alssaharatu limeeqati yawmin maʿloomin
Sai aka tãra masihirta dõmin ajalin yini sananne.
-
وَقِيلَ لِلنَّاسِ هَلْ أَنتُم مُّجْتَمِعُونَ٣٩
Waqeela lilnnasi hal antum mujtamiʿoona
Kuma aka ce wa mutãne "Kõ kũ mãsu tãruwã ne?
-
لَعَلَّنَا نَتَّبِعُ ٱلسَّحَرَةَ إِن كَانُوا۟ هُمُ ٱلْغَـٰلِبِينَ٤٠
Laʿallana nattabiʿu alssaharata in kanoo humu alghalibeena
"Tsammãninmu mu bi masihirta, idan sun kasance sũ ne marinjãya."
-
فَلَمَّا جَآءَ ٱلسَّحَرَةُ قَالُوا۟ لِفِرْعَوْنَ أَئِنَّ لَنَا لَأَجْرًا إِن كُنَّا نَحْنُ ٱلْغَـٰلِبِينَ٤١
Falamma jaa alssaharatu qaloo lifirʿawna ainna lana laajran in kunna nahnu alghalibeena
To, a lõkacin da masihirta suka jẽ suka ce wa Fir'auna,"Shin, lalle ne, haƙĩƙa munã da ijãra idan mun kasance mũ ne marinjãya?"
-
قَالَ نَعَمْ وَإِنَّكُمْ إِذًا لَّمِنَ ٱلْمُقَرَّبِينَ٤٢
Qala naʿam wainnakum ithan lamina almuqarrabeena
Ya ce: "Na'am! Kuma lalle ne, kũ ne a lõkacin haƙĩƙa muƙarrabai."
-
قَالَ لَهُم مُّوسَىٰٓ أَلْقُوا۟ مَآ أَنتُم مُّلْقُونَ٤٣
Qala lahum moosa alqoo ma antum mulqoona
Mũsã ya ce musu, "Ku jẽfa abin da kuke mãsu jẽfãwa."
-
فَأَلْقَوْا۟ حِبَالَهُمْ وَعِصِيَّهُمْ وَقَالُوا۟ بِعِزَّةِ فِرْعَوْنَ إِنَّا لَنَحْنُ ٱلْغَـٰلِبُونَ٤٤
Faalqaw hibalahum waʿisiyyahum waqaloo biʿizzati firʿawna inna lanahnu alghaliboona
Sai suka jẽfa igiyõyinsu, da sandunansu, kuma suka ce: "Da ƙarfin Fir'auna lalle ne mũ, haƙĩƙa, mũ ne marinjãya."
-
فَأَلْقَىٰ مُوسَىٰ عَصَاهُ فَإِذَا هِىَ تَلْقَفُ مَا يَأْفِكُونَ٤٥
Faalqa moosa ʿasahu faitha hiya talqafu ma yafikoona
Sai Mũsa ya jẽfa sandarsa, sai ga ta tanã harhaɗe abin da suke yi na ƙarya.
-
فَأُلْقِىَ ٱلسَّحَرَةُ سَـٰجِدِينَ٤٦
Faolqiya alssaharatu sajideena
Sai aka jẽfar da masihirta sunã mãsu sujada.
-
قَالُوٓا۟ ءَامَنَّا بِرَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ٤٧
Qaloo amanna birabbi alʿalameena
Suka ce: "Mun yi ĩmãni da Ubangijin halitta."
-
رَبِّ مُوسَىٰ وَهَـٰرُونَ٤٨
Rabbi moosa waharoona
"Ubangijin Mũsa da Hãrũna."
-
قَالَ ءَامَنتُمْ لَهُۥ قَبْلَ أَنْ ءَاذَنَ لَكُمْ ۖ إِنَّهُۥ لَكَبِيرُكُمُ ٱلَّذِى عَلَّمَكُمُ ٱلسِّحْرَ فَلَسَوْفَ تَعْلَمُونَ ۚ لَأُقَطِّعَنَّ أَيْدِيَكُمْ وَأَرْجُلَكُم مِّنْ خِلَـٰفٍ وَلَأُصَلِّبَنَّكُمْ أَجْمَعِينَ٤٩
Qala amantum lahu qabla an athana lakum innahu lakabeerukumu allathee ʿallamakumu alssihra falasawfa taʿlamoona laoqattiʿanna aydiyakum waarjulakum min khilafin walaosallibannakum ajmaʿeena
Ya ce: "Ashe, kun yi ĩmãni sabõda shĩ, a gabãnin in yi muku izni? Lalle ne shi, haƙĩƙa babbanku ne wanda ya kõya muku sihirin, to, zã ku sani. Lalle ne haƙĩƙa, zan kakkãtse hannuwanku da kafãfunku a tarnaƙi, kuma haƙĩƙa, zan tsĩrẽ ku gabã ɗaya."
-
قَالُوا۟ لَا ضَيْرَ ۖ إِنَّآ إِلَىٰ رَبِّنَا مُنقَلِبُونَ٥٠
Qaloo la dayra inna ila rabbina munqaliboona
Suka ce: "Bãbu wata cũta! Lalle ne mũ mãsu jũyãwa ne zuwa ga Ubangijinmu."
-
إِنَّا نَطْمَعُ أَن يَغْفِرَ لَنَا رَبُّنَا خَطَـٰيَـٰنَآ أَن كُنَّآ أَوَّلَ ٱلْمُؤْمِنِينَ٥١
Inna natmaʿu an yaghfira lana rabbuna khatayana an kunna awwala almumineena
"Lalle ne mu munã kwaɗayin Ubangijinmu, Ya gãfarta mana kurakuranmu dõmin mun kasance farkon mãsu ĩmãni."
-
۞ وَأَوْحَيْنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰٓ أَنْ أَسْرِ بِعِبَادِىٓ إِنَّكُم مُّتَّبَعُونَ٥٢
Waawhayna ila moosa an asri biʿibadee innakum muttabaʿoona
Kuma Muka aika zuwa ga Mũsã cẽwa ka yi tafiyar dare da bãyiNa, lalle ne kũ waɗanda ake biyã1 ne.
Bayanai
[1] Mũsa yanã nũna cewa, shi yanã jin tsõro kada ya zama ya gajarta wajen iyar da manzanci, dõmin shi mai saurin fushine, yanã neman a taimake shi ɗan'uwansa Hãrũna.Wannan ya yi kama da farkon sũrar inda Annabi, tshĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya nũna tsõron taƙaitãwa ga iyar da manzancin Allah zuwa ga mutãnensa dõmin haka ba su yi ĩmãni ba. Hãlin Annabawa duka ɗaya ne ga tsõron taƙaita aikin Ubangijinsu. -
فَأَرْسَلَ فِرْعَوْنُ فِى ٱلْمَدَآئِنِ حَـٰشِرِينَ٥٣
Faarsala firʿawnu fee almadaini hashireena
Sai Fir'auna ya aika mãsu gayya a cikin birãne.
-
إِنَّ هَـٰٓؤُلَآءِ لَشِرْذِمَةٌ قَلِيلُونَ٥٤
Inna haolai lashirthimatun qaleeloona
"Lalle ne, waɗannan, haƙĩƙa, ƙungiya ce kaɗan."
-
وَإِنَّهُمْ لَنَا لَغَآئِظُونَ٥٥
Wainnahum lana laghaithoona
"Kuma lalle ne sũ, a gare Mu, Mãsu fusãtarwa ne."
-
وَإِنَّا لَجَمِيعٌ حَـٰذِرُونَ٥٦
Wainna lajameeʿun hathiroona
"Kuma lalle ne mũ haƙĩƙa gabã ɗaya mãsu sauna ne."
-
فَأَخْرَجْنَـٰهُم مِّن جَنَّـٰتٍ وَعُيُونٍ٥٧
Faakhrajnahum min jannatin waʿuyoonin
Sai Muka fitar da su daga gonaki da marẽmari.
-
وَكُنُوزٍ وَمَقَامٍ كَرِيمٍ٥٨
Wakunoozin wamaqamin kareemin
Da taskõki da mazauni mai kyau.
-
كَذَٰلِكَ وَأَوْرَثْنَـٰهَا بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ٥٩
Kathalika waawrathnaha banee israeela
Kamar haka! Kuma Muka gãdar da su ga Banĩ Isrãĩla.
-
فَأَتْبَعُوهُم مُّشْرِقِينَ٦٠
Faatbaʿoohum mushriqeena
Sai suka bĩ su sunã mãsu fita a lõkacin hũdõwar rãnã.
-
فَلَمَّا تَرَٰٓءَا ٱلْجَمْعَانِ قَالَ أَصْحَـٰبُ مُوسَىٰٓ إِنَّا لَمُدْرَكُونَ٦١
Falamma taraa aljamʿani qala ashabu moosa inna lamudrakoona
Sa'an nan a lõkacin da jama'a biyu suka ga jũna, sai abõkan Mũsã suka ce: "Lalle ne mũ haƙĩ ƙa, waɗanda ake riska ne."
-
قَالَ كَلَّآ ۖ إِنَّ مَعِىَ رَبِّى سَيَهْدِينِ٦٢
Qala kalla inna maʿiya rabbee sayahdeeni
Ya ce: "Kayya! Lalle ne Ubangijina Yanã tare da ni, zai shiryar da ni."
-
فَأَوْحَيْنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰٓ أَنِ ٱضْرِب بِّعَصَاكَ ٱلْبَحْرَ ۖ فَٱنفَلَقَ فَكَانَ كُلُّ فِرْقٍ كَٱلطَّوْدِ ٱلْعَظِيمِ٦٣
Faawhayna ila moosa ani idrib biʿasaka albahra fainfalaqa fakana kullu firqin kaalttawdi alʿatheemi
Sai Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa "Ka dõki tẽku da sandarka." Sai tẽku ta tsãge,1 kõwane tsãgi ya kasance kamar falalen dũtse mai girma.
Bayanai
[1] Teku ta tsãge hanya gõma sha biyu a kan adadin danginBanĩ Isrãĩla. Suka bi suka wuce, sa'ilin nan aka nutsar daFir'auna, shi da jama'arsa, a cikin hanyõyin ruwan,. -
وَأَزْلَفْنَا ثَمَّ ٱلْـَٔاخَرِينَ٦٤
Waazlafna thamma alakhareena
Kuma Muka kusantar da waɗansu mutãne a can.
-
وَأَنجَيْنَا مُوسَىٰ وَمَن مَّعَهُۥٓ أَجْمَعِينَ٦٥
Waanjayna moosa waman maʿahu ajmaʿeena
Kuma Muka tsĩrar da Mũsã da waɗanda suke tãre da shi gabã ɗaya.
-
ثُمَّ أَغْرَقْنَا ٱلْـَٔاخَرِينَ٦٦
Thumma aghraqna alakhareena
Sa'an nan kuma Muka nutsar da waɗansu mutãnen.
-
إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً ۖ وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ٦٧
Inna fee thalika laayatan wama kana aktharuhum mumineena
Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba.
-
وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ٦٨
Wainna rabbaka lahuwa alʿazeezu alrraheemu
Kuma lalle ne Ubangijinka, kaƙĩƙa, Shĩ ne Mabũwayi, Mai jin ƙai.
-
وَٱتْلُ عَلَيْهِمْ نَبَأَ إِبْرَٰهِيمَ٦٩
Waotlu ʿalayhim nabaa ibraheema
Kuma ka karanta, a kansu, lãbãrin Ibrãhĩm.
-
إِذْ قَالَ لِأَبِيهِ وَقَوْمِهِۦ مَا تَعْبُدُونَ٧٠
Ith qala liabeehi waqawmihi ma taʿbudoona
A sã'ilin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mẽne ne kuke bauta wa?"
-
قَالُوا۟ نَعْبُدُ أَصْنَامًا فَنَظَلُّ لَهَا عَـٰكِفِينَ٧١
Qaloo naʿbudu asnaman fanathallu laha ʿakifeena
Suka ce: "Munã bauta wa gumãka, sabõda haka munã yini mãsu lazimta a gare su."
-
قَالَ هَلْ يَسْمَعُونَكُمْ إِذْ تَدْعُونَ٧٢
Qala hal yasmaʿoonakum ith tadʿoona
Ya ce: "Shin, sunã jin ku, a lõkacin da kuke kira?"
-
أَوْ يَنفَعُونَكُمْ أَوْ يَضُرُّونَ٧٣
Aw yanfaʿoonakum aw yadurroona
"Kõ kuwa sunã amfãnin ku, kõ sunã cũtar ku?"
-
قَالُوا۟ بَلْ وَجَدْنَآ ءَابَآءَنَا كَذَٰلِكَ يَفْعَلُونَ٧٤
Qaloo bal wajadna abaana kathalika yafʿaloona
Suka ce: "Ã'a mun sãmĩ ubanninmu, kamar haka ne suke aikatãwa."
-
قَالَ أَفَرَءَيْتُم مَّا كُنتُمْ تَعْبُدُونَ٧٥
Qala afaraaytum ma kuntum taʿbudoona
Ya ce: "Shin to, kun ga abin da kuka kasance kunã bautã wa?"
-
أَنتُمْ وَءَابَآؤُكُمُ ٱلْأَقْدَمُونَ٧٦
Antum waabaokumu alaqdamoona
"Kũ da ubanninku mafi daɗẽwa?"
-
فَإِنَّهُمْ عَدُوٌّ لِّىٓ إِلَّا رَبَّ ٱلْعَـٰلَمِينَ٧٧
Fainnahum ʿaduwwun lee illa rabba alʿalameena
"To lalle ne, sũ maƙiya ne a gare ni, fãce Ubangijin halittu."
-
ٱلَّذِى خَلَقَنِى فَهُوَ يَهْدِينِ٧٨
Allathee khalaqanee fahuwa yahdeeni
"Wanda Ya halitta ni, sa'an nan Yanã shiryar da ni."
-
وَٱلَّذِى هُوَ يُطْعِمُنِى وَيَسْقِينِ٧٩
Waallathee huwa yutʿimunee wayasqeeni
"Kuma Wanda Yake Shĩ ne Yake ciyar da ni, kuma Yanã shãyar da ni."
-
وَإِذَا مَرِضْتُ فَهُوَ يَشْفِينِ٨٠
Waitha maridtu fahuwa yashfeeni
"Kuma idan na yi jiyya, to, Shĩ ne Yake warkar da ni."
-
وَٱلَّذِى يُمِيتُنِى ثُمَّ يُحْيِينِ٨١
Waallathee yumeetunee thumma yuhyeeni
"Kuma wanda Yake matar da ni, sa'an nan Ya rãyar da ni."
-
وَٱلَّذِىٓ أَطْمَعُ أَن يَغْفِرَ لِى خَطِيٓـَٔتِى يَوْمَ ٱلدِّينِ٨٢
Waallathee atmaʿu an yaghfira lee khateeatee yawma alddeeni
"Kuma wanda Yake inã kwaɗayin Ya gãfarta mini kurãkuraina, a rãnar sãkamako."
-
رَبِّ هَبْ لِى حُكْمًا وَأَلْحِقْنِى بِٱلصَّـٰلِحِينَ٨٣
Rabbi hab lee hukman waalhiqnee bialssaliheena
"Ya Ubangijĩna! Ka ba ni hukunci, kuma Ka riskar da ni ga sãlihai."
-
وَٱجْعَل لِّى لِسَانَ صِدْقٍ فِى ٱلْـَٔاخِرِينَ٨٤
Waijʿal lee lisana sidqin fee alakhireena
"Kuma Ka sanya mini harshen gaskiya1 a cikin mutãnen ƙarshe."
Bayanai
[1] Harshen gaskiya shĩ ne yabõ mai kyau. Mutãnen ƙarshe sũ ne Musulmi al'ummar Annabi Muhammadu, mãsu shaida ga annabawa da iyar da manzanci -
وَٱجْعَلْنِى مِن وَرَثَةِ جَنَّةِ ٱلنَّعِيمِ٨٥
Waijʿalnee min warathati jannati alnnaʿeemi
"Kuma Ka sanya ni daga magãdan Aljannar ni'ima."
-
وَٱغْفِرْ لِأَبِىٓ إِنَّهُۥ كَانَ مِنَ ٱلضَّآلِّينَ٨٦
Waighfir liabee innahu kana mina alddalleena
"Kuma Ka gãfarta wa ubãna, lalle ne shi, ya kasance daga ɓatattu."
-
وَلَا تُخْزِنِى يَوْمَ يُبْعَثُونَ٨٧
Wala tukhzinee yawma yubʿathoona
"Kuma kada Ka kunyata ni a rãnar da ake tãyar da su."
-
يَوْمَ لَا يَنفَعُ مَالٌ وَلَا بَنُونَ٨٨
Yawma la yanfaʿu malun wala banoona
"A rãnar da dũkiya bã ta amfãni, kuma ɗiya bã su yi."
-
إِلَّا مَنْ أَتَى ٱللَّهَ بِقَلْبٍ سَلِيمٍ٨٩
Illa man ata Allaha biqalbin saleemin
"Fãce wanda ya jẽ wa Allah da zũciya mai tsarki."
-
وَأُزْلِفَتِ ٱلْجَنَّةُ لِلْمُتَّقِينَ٩٠
Waozlifati aljannatu lilmuttaqeena
Kuma aka kusantar da Aljanna ga mãsu taƙawa.
-
وَبُرِّزَتِ ٱلْجَحِيمُ لِلْغَاوِينَ٩١
Waburrizati aljaheemu lilghaweena
Kuma aka fitar da wutã babba dõmin halakakku.
-
وَقِيلَ لَهُمْ أَيْنَ مَا كُنتُمْ تَعْبُدُونَ٩٢
Waqeela lahum ayna ma kuntum taʿbudoona
Kuma aka ce musu, "Inã abin da kuka kasance kunã bautawa?"
-
مِن دُونِ ٱللَّهِ هَلْ يَنصُرُونَكُمْ أَوْ يَنتَصِرُونَ٩٣
Min dooni Allahi hal yansuroonakum aw yantasiroona
"Baicin Allah? Shin sunã tamakon ku kõ kuwa sunã tsare kansu?"
-
فَكُبْكِبُوا۟ فِيهَا هُمْ وَٱلْغَاوُۥنَ٩٤
Fakubkiboo feeha hum waalghawoona
Sai aka kikkife su1 a cikinta, su da halakakkun.
Bayanai
[1] Gumãkan, sũ da halakakku mabiyansu. Dukkan mai ɓatarda wani shĩ ne gunki ga mai bin sa halakakke. -
وَجُنُودُ إِبْلِيسَ أَجْمَعُونَ٩٥
Wajunoodu ibleesa ajmaʿoona
Da rundunar Ibilĩsa gabã ɗaya.
-
قَالُوا۟ وَهُمْ فِيهَا يَخْتَصِمُونَ٩٦
Qaloo wahum feeha yakhtasimoona
Suka ce: alhãli sunã a cikinta sunã yin husũma,
-
تَٱللَّهِ إِن كُنَّا لَفِى ضَلَـٰلٍ مُّبِينٍ٩٧
TaAllahi in kunna lafee dalalin mubeenin
"Rantsuwa da Allah! Lalle ne mun kasance, haƙĩƙa, a cikin ɓata bayyananna."
-
إِذْ نُسَوِّيكُم بِرَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ٩٨
Ith nusawweekum birabbi alʿalameena
"A lõkacin da muke daidaita ku da Ubangijin halittu.
-
وَمَآ أَضَلَّنَآ إِلَّا ٱلْمُجْرِمُونَ٩٩
Wama adallana illa almujrimoona
"Kuma bãbu abin da ya ɓatar da mu fãce mãsu laifi."
-
فَمَا لَنَا مِن شَـٰفِعِينَ١٠٠
Fama lana min shafiʿeena
"Sabõda haka bã mu da waɗansu macẽta."
-
وَلَا صَدِيقٍ حَمِيمٍ١٠١
Wala sadeeqin hameemin
"Kuma bã mu da abõki, masõyi."
-
فَلَوْ أَنَّ لَنَا كَرَّةً فَنَكُونَ مِنَ ٱلْمُؤْمِنِينَ١٠٢
Falaw anna lana karratan fanakoona mina almumineena
"Sabõda haka dã lalle munã da (dãmar) kõmawa, dõmin mu kasance daga mũminai!"
-
إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً ۖ وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ١٠٣
Inna fee thalika laayatan wama kana aktharuhum mumineena
Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, bã su kasance mũminai ba.
-
وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ١٠٤
Wainna rabbaka lahuwa alʿazeezu alrraheemu
Kuma lalle ne, Ubangijinka, Shi ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
-
كَذَّبَتْ قَوْمُ نُوحٍ ٱلْمُرْسَلِينَ١٠٥
Kaththabat qawmu noohin almursaleena
Mutãnen Nũhu sun ƙaryata Manzanni.
-
إِذْ قَالَ لَهُمْ أَخُوهُمْ نُوحٌ أَلَا تَتَّقُونَ١٠٦
Ith qala lahum akhoohum noohun ala tattaqoona
A lõkacin da Dan uwansu Nuhu ya ce musu, "Bã zã ku ji tsoron Allah ba?"
-
إِنِّى لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ١٠٧
Innee lakum rasoolun ameenun
"Lalle ne, zuwa gare ku, ni Manzo ne amintacce."
-
فَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ١٠٨
Faittaqoo Allaha waateeʿooni
"To, ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."
-
وَمَآ أَسْـَٔلُكُمْ عَلَيْهِ مِنْ أَجْرٍ ۖ إِنْ أَجْرِىَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ١٠٩
Wama asalukum ʿalayhi min ajrin in ajriya illa ʿala rabbi alʿalameena
"Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrãtã ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu."
-
فَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ١١٠
Faittaqoo Allaha waateeʿooni
"Sabõda haka, ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."
-
۞ قَالُوٓا۟ أَنُؤْمِنُ لَكَ وَٱتَّبَعَكَ ٱلْأَرْذَلُونَ١١١
Qaloo anuminu laka waittabaʿaka alarthaloona
Suka ce: "Ashe, zã mu yi ĩmãni sabõda kai alhãli kuwa mafiya ƙasƙanci sun bi ka?"
-
قَالَ وَمَا عِلْمِى بِمَا كَانُوا۟ يَعْمَلُونَ١١٢
Qala wama ʿilmee bima kanoo yaʿmaloona
Ya ce: "Kuma bã ni da sani ga abin da suka kasance sanã aikatãwa."
-
إِنْ حِسَابُهُمْ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّى ۖ لَوْ تَشْعُرُونَ١١٣
In hisabuhum illa ʿala rabbee law tashʿuroona
"Hisãbinsu bai zama ba fãce ga Ubangijina, dã kunã sansancẽwa."
-
وَمَآ أَنَا۠ بِطَارِدِ ٱلْمُؤْمِنِينَ١١٤
Wama ana bitaridi almumineena
"Ban zama mai kõre mũminai ba."
-
إِنْ أَنَا۠ إِلَّا نَذِيرٌ مُّبِينٌ١١٥
In ana illa natheerun mubeenun
"Nĩ ba kõwa ba ne sai mai gargaɗi mai bayyanãwa."
-
قَالُوا۟ لَئِن لَّمْ تَنتَهِ يَـٰنُوحُ لَتَكُونَنَّ مِنَ ٱلْمَرْجُومِينَ١١٦
Qaloo lain lam tantahi ya noohu latakoonanna mina almarjoomeena
Suka ce: "Lalle ne, idan ba ka hanu ba, yã Nũhu, (daga maganarka,) haƙĩƙa, kanã kasancẽwa daga waɗanda ake jẽfewa"
-
قَالَ رَبِّ إِنَّ قَوْمِى كَذَّبُونِ١١٧
Qala rabbi inna qawmee kaththabooni
Ya ce: "Yã Ubangijĩna! Lalle ne mutãnena sun ƙaryatã ni."
-
فَٱفْتَحْ بَيْنِى وَبَيْنَهُمْ فَتْحًا وَنَجِّنِى وَمَن مَّعِىَ مِنَ ٱلْمُؤْمِنِينَ١١٨
Faiftah baynee wabaynahum fathan wanajjinee waman maʿiya mina almumineena
"Sai ka yi hukunci, a tsakãnĩna da tsakãninsu tabbataccen hukanci, kuma ka tsĩrar da ni, da waɗanda suke tãre da ni daga mũminai."
-
فَأَنجَيْنَـٰهُ وَمَن مَّعَهُۥ فِى ٱلْفُلْكِ ٱلْمَشْحُونِ١١٩
Faanjaynahu waman maʿahu fee alfulki almashhooni
Sai Muka tsĩrar da shi, shi da waɗanda suke tãre da shi, a cikin jirgi wanda aka yi wa lõdi.
-
ثُمَّ أَغْرَقْنَا بَعْدُ ٱلْبَاقِينَ١٢٠
Thumma aghraqna baʿdu albaqeena
Sa'an nan Muka nutsar a bãyan haka, da sauran.
-
إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً ۖ وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ١٢١
Inna fee thalika laayatan wama kana aktharuhum mumineena
Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, ba su kasance mãsu ĩmãni ba.
-
وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ١٢٢
Wainna rabbaka lahuwa alʿazeezu alrraheemu
Kuma Lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai Rahama.
-
كَذَّبَتْ عَادٌ ٱلْمُرْسَلِينَ١٢٣
Kaththabat ʿadun almursaleena
Ãdãwa sun ƙaryata Manzanni.
-
إِذْ قَالَ لَهُمْ أَخُوهُمْ هُودٌ أَلَا تَتَّقُونَ١٢٤
Ith qala lahum akhoohum hoodun ala tattaqoona
A lõkacin da ɗan'uwansu, Hũdu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba?"
-
إِنِّى لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ١٢٥
Innee lakum rasoolun ameenun
"Lalle ne ni, zuwa gare ku, haƙĩƙa, Manzo ne, amintacce."
-
فَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ١٢٦
Faittaqoo Allaha waateeʿooni
"Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."
-
وَمَآ أَسْـَٔلُكُمْ عَلَيْهِ مِنْ أَجْرٍ ۖ إِنْ أَجْرِىَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ١٢٧
Wama asalukum ʿalayhi min ajrin in ajriya illa ʿala rabbi alʿalameena
"Kuma bã ni tambayar wata ijãra a kansa. Ijãrãta ba ta zama ba, fãce daga Ubangijin halittu."
-
أَتَبْنُونَ بِكُلِّ رِيعٍ ءَايَةً تَعْبَثُونَ١٢٨
Atabnoona bikulli reeʿin ayatan taʿbathoona
"Shin, kunã yin ginin sitadiyo1 a kõwane tsauni ne, kunã yin wãsa?"
Bayanai
[1] Sitãdiyo shi ne gidan wasanni da Turanci, alãmã da Lãrabci. -
وَتَتَّخِذُونَ مَصَانِعَ لَعَلَّكُمْ تَخْلُدُونَ١٢٩
Watattakhithoona masaniʿa laʿallakum takhludoona
"Kuma kunã riƙon matsãrar ruwa, tsammãninku, ku dawwama?1"
Bayanai
[1] Kõ kuma wurãren sanã'õ'i kamar masãƙoƙi irin na zãmanin nan. -
وَإِذَا بَطَشْتُم بَطَشْتُمْ جَبَّارِينَ١٣٠
Waitha batashtum batashtum jabbareena
"Kuma idan kun yi damƙa, sai ku yi damƙar kunã mãsu tanƙwasãwa."
-
فَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ١٣١
Faittaqoo Allaha waateeʿooni
"To ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."
-
وَٱتَّقُوا۟ ٱلَّذِىٓ أَمَدَّكُم بِمَا تَعْلَمُونَ١٣٢
Waittaqoo allathee amaddakum bima taʿlamoona
"Ku ji tsõron wanda Ya taimake ku da abin da kuka sani."
-
أَمَدَّكُم بِأَنْعَـٰمٍ وَبَنِينَ١٣٣
Amaddakum bianʿamin wabaneena
"Ya taimake ku da dabbõbin ni'ima da ɗiya."
-
وَجَنَّـٰتٍ وَعُيُونٍ١٣٤
Wajannatin waʿuyoonin
"Da gõnaki da marẽmari."
-
إِنِّىٓ أَخَافُ عَلَيْكُمْ عَذَابَ يَوْمٍ عَظِيمٍ١٣٥
Innee akhafu ʿalaykum ʿathaba yawmin ʿatheemin
"Lalle ne nĩ, inã ji muku tsõron azãbar wani yini mai girma."
-
قَالُوا۟ سَوَآءٌ عَلَيْنَآ أَوَعَظْتَ أَمْ لَمْ تَكُن مِّنَ ٱلْوَٰعِظِينَ١٣٦
Qaloo sawaon ʿalayna awaʿathta am lam takun mina alwaʿitheena
Suka ce: "Daidai ne a kanmu: Kã yi wa'azi kõ ba ka kasance daga mãsu wa'azi ba."
-
إِنْ هَـٰذَآ إِلَّا خُلُقُ ٱلْأَوَّلِينَ١٣٧
In hatha illa khuluqu alawwaleena
"Wannan abu bai zamõ ba fãce hãlãyen1 mutãnen farko."
Bayanai
[1] Wãtau lãbarun mutãne waɗanda ba su ci gaba ba bã su son a yi rawa da nishãɗi. Anã karantawar ma'anar ƙaryar ta farko, watau wai tãtsũniya ce: a ce wai a hana ãyã akan tsaunuka dõmin wasanni. Suna nufi da ãya ko alãma gidãjen rawa da na nashãdi watau stadiyam da kasĩno. -
وَمَا نَحْنُ بِمُعَذَّبِينَ١٣٨
Wama nahnu bimuʿaththabeena
"Kuma mũ ba mu zama waɗanda ake yi wa azãba ba."
-
فَكَذَّبُوهُ فَأَهْلَكْنَـٰهُمْ ۗ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً ۖ وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ١٣٩
Fakaththaboohu faahlaknahum inna fee thalika laayatan wama kana aktharuhum mumineena
Sabõda haka suka ƙaryata shi, sai Muka halakar da sũ. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba.
-
وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ١٤٠
Wainna rabbaka lahuwa alʿazeezu alrraheemu
Kuma lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shi ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
-
كَذَّبَتْ ثَمُودُ ٱلْمُرْسَلِينَ١٤١
Kaththabat thamoodu almursaleena
Samũdãwa sun ƙaryata Manzanni.
-
إِذْ قَالَ لَهُمْ أَخُوهُمْ صَـٰلِحٌ أَلَا تَتَّقُونَ١٤٢
Ith qala lahum akhoohum salihun ala tattaqoona
A lõkacin da ɗan'uwansu Sãlihu ya ce: "Shin, bã zã ku bi Allah da taƙawa ba?"
-
إِنِّى لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ١٤٣
Innee lakum rasoolun ameenun
"Lalle ne nĩ zuwã gare ku, Manzo ne, amintacce."
-
فَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ١٤٤
Faittaqoo Allaha waateeʿooni
"Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã.
-
وَمَآ أَسْـَٔلُكُمْ عَلَيْهِ مِنْ أَجْرٍ ۖ إِنْ أَجْرِىَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ١٤٥
Wama asalukum ʿalayhi min ajrin in ajriya illa ʿala rabbi alʿalameena
"Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrãta ba ta zama ba fãce da a Ubangijin halittu."
-
أَتُتْرَكُونَ فِى مَا هَـٰهُنَآ ءَامِنِينَ١٤٦
Atutrakoona fee ma hahuna amineena
"Shin, anã barin ku1 a cikin abin da yake a nan, kunã amintattu?"
Bayanai
[1] Kuna zaton zã a bar ku a irin wannan ni'ima' Allah bã zai karɓi rãyukanku ba kuma Ya yi muku hisãbi a kanta? Kayya! Zã a yi muku hisãbi a bãyan kun mutu an tsayar da ku, dõmin hisãbin ayyukan da kuka yi. -
فِى جَنَّـٰتٍ وَعُيُونٍ١٤٧
Fee jannatin waʿuyoonin
"A cikin gõnaki da marẽmari."
-
وَزُرُوعٍ وَنَخْلٍ طَلْعُهَا هَضِيمٌ١٤٨
Wazurooʿin wanakhlin talʿuha hadeemun
"Da shuke-shuke da dabĩ nai, 'ya'yan itãcensu hirtsi1 mãsu narkẽwa a ciki?"
Bayanai
[1] Hirtsi shi ne 'ya'yan itãce sãbabbi tun ba su nuna ba. Wãtau hirtsin gonakinsu idan an ci shi narkewã ya ke yi a cikin ciki, balle kuma 'ya'yan itãce nunannu. -
وَتَنْحِتُونَ مِنَ ٱلْجِبَالِ بُيُوتًا فَـٰرِهِينَ١٤٩
Watanhitoona mina aljibali buyootan fariheena
"Kuma kunã sassaƙa gidãje daga duwãtsu, kunã mãsu alfãhari?"
-
فَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ١٥٠
Faittaqoo Allaha waateeʿooni
"Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."
-
وَلَا تُطِيعُوٓا۟ أَمْرَ ٱلْمُسْرِفِينَ١٥١
Wala tuteeʿoo amra almusrifeena
"Kada ku yi ɗã'ã ga umurnin maɓarnata."
-
ٱلَّذِينَ يُفْسِدُونَ فِى ٱلْأَرْضِ وَلَا يُصْلِحُونَ١٥٢
Allatheena yufsidoona fee alardi wala yuslihoona
"Waɗanda suke yin ɓarna a cikin ƙasa, kuma bã su kyautatãwa."
-
قَالُوٓا۟ إِنَّمَآ أَنتَ مِنَ ٱلْمُسَحَّرِينَ١٥٣
Qaloo innama anta mina almusahhareena
Suka ce: "Kai daga mãsu sihiri kurum kake."
-
مَآ أَنتَ إِلَّا بَشَرٌ مِّثْلُنَا فَأْتِ بِـَٔايَةٍ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّـٰدِقِينَ١٥٤
Ma anta illa basharun mithluna fati biayatin in kunta mina alssadiqeena
"Bã kõwa kake ba, fãce mutum kamarmu. To, kã zo da wata ãyã idan kã kasance daga mãsu gaskiya."
-
قَالَ هَـٰذِهِۦ نَاقَةٌ لَّهَا شِرْبٌ وَلَكُمْ شِرْبُ يَوْمٍ مَّعْلُومٍ١٥٥
Qala hathihi naqatun laha shirbun walakum shirbu yawmin maʿloomin
Ya ce: "Wannan rãkuma ce tanã da shan1 yini, kuma kunã da shan yini sasanne."
Bayanai
[1] Kuna zaton zã a bar ku a irin wannan ni'ima' Allah bã zai karɓi rãyukanku ba kuma Ya yi muku hisãbi a kanta? Kayya! Zã a yi muku hisãbi a bãyan kun mutu an tsayar da ku, dõmin hisãbin ayyukan da kuka yi. -
وَلَا تَمَسُّوهَا بِسُوٓءٍ فَيَأْخُذَكُمْ عَذَابُ يَوْمٍ عَظِيمٍ١٥٦
Wala tamassooha bisooin fayakhuthakum ʿathabu yawmin ʿatheemin
"Kada ku shãfe ta da cũta har azãbar yini mai girmã ta shãfe ku."
-
فَعَقَرُوهَا فَأَصْبَحُوا۟ نَـٰدِمِينَ١٥٧
Faʿaqarooha faasbahoo nadimeena
Sai suka sõke ta sa'an nan suka wãyi gari sunã mãsu nadãma.
-
فَأَخَذَهُمُ ٱلْعَذَابُ ۗ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً ۖ وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ١٥٨
Faakhathahumu alʿathabu inna fee thalika laayatan wama kana aktharuhum mumineena
Sabõda haka azãba ta kãma su. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, ba su kasance mãsu ĩmãni ba.
-
وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ١٥٩
Wainna rabbaka lahuwa alʿazeezu alrraheemu
Lalle ne Ubangijinka, haƙĩ ƙa, Shĩ ne Mabuwayi, Mai jin ƙai.
-
كَذَّبَتْ قَوْمُ لُوطٍ ٱلْمُرْسَلِينَ١٦٠
Kaththabat qawmu lootin almursaleena
Mutãnen Lũɗu sun ƙaryata Manzanni.
-
إِذْ قَالَ لَهُمْ أَخُوهُمْ لُوطٌ أَلَا تَتَّقُونَ١٦١
Ith qala lahum akhoohum lootun ala tattaqoona
A lõkacin da ɗan'uwansu,1 Lũɗu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba?"
Bayanai
[1] Lũɗu ɗan'uwansu ne na zaman gari da aure kawai. Asalinsa ɗan baffan Ibrãhĩm ne, sun tãso daga gabas, ƙasar Bãbila suka yi hijira, har ibrahĩm ya sauka Habrũna a ƙasar Shãm, Lũɗu kuwa ya sauka a sadũm da alƙaryunta. -
إِنِّى لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ١٦٢
Innee lakum rasoolun ameenun
"Lalle ne nĩ, zuwa gare ku, Manzõ ne, amintacce."
-
فَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ١٦٣
Faittaqoo Allaha waateeʿooni
"Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."
-
وَمَآ أَسْـَٔلُكُمْ عَلَيْهِ مِنْ أَجْرٍ ۖ إِنْ أَجْرِىَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ١٦٤
Wama asalukum ʿalayhi min ajrin in ajriya illa ʿala rabbi alʿalameena
"Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra, Ijãrãta ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu."
-
أَتَأْتُونَ ٱلذُّكْرَانَ مِنَ ٱلْعَـٰلَمِينَ١٦٥
Atatoona alththukrana mina alʿalameena
"Shin kunã jẽ wa maza daga cikin talikai?"
-
وَتَذَرُونَ مَا خَلَقَ لَكُمْ رَبُّكُم مِّنْ أَزْوَٰجِكُم ۚ بَلْ أَنتُمْ قَوْمٌ عَادُونَ١٦٦
Watatharoona ma khalaqa lakum rabbukum min azwajikum bal antum qawmun ʿadoona
"Kuma kunã barin abin da Ubangijinku Ya halitta muku daga mãtanku? Ã'a, ku mutãne ne mãsu ƙẽtarẽwa!"
-
قَالُوا۟ لَئِن لَّمْ تَنتَهِ يَـٰلُوطُ لَتَكُونَنَّ مِنَ ٱلْمُخْرَجِينَ١٦٧
Qaloo lain lam tantahi ya lootu latakoonanna mina almukhrajeena
Suka ce: "Lalle ne haƙĩƙa idan ba ka hanu ba, yã Lũɗu! Tĩlas ne kanã kasancẽwa daga waɗanda ake fitarwa (daga gari)."
-
قَالَ إِنِّى لِعَمَلِكُم مِّنَ ٱلْقَالِينَ١٦٨
Qala innee liʿamalikum mina alqaleena
Ya ce: "Lalle ne ga aikinku, haƙĩƙa, inã daga mãsu ƙinsa."
-
رَبِّ نَجِّنِى وَأَهْلِى مِمَّا يَعْمَلُونَ١٦٩
Rabbi najjinee waahlee mimma yaʿmaloona
"Ya Ubangijina! Ka tsĩrar da ni da iyãlĩna daga abin da suke aikatãwa."
-
فَنَجَّيْنَـٰهُ وَأَهْلَهُۥٓ أَجْمَعِينَ١٧٠
Fanajjaynahu waahlahu ajmaʿeena
Sabõda haka Muka tsĩrar da shi, Shi da mutãnensa gabã ɗaya.
-
إِلَّا عَجُوزًا فِى ٱلْغَـٰبِرِينَ١٧١
Illa ʿajoozan fee alghabireena
Fãce wata tsõhuwa a cikin mãsu wanzuwa.
-
ثُمَّ دَمَّرْنَا ٱلْـَٔاخَرِينَ١٧٢
Thumma dammarna alakhareena
Sa'an nan kuma Muka hallaka wasu.
-
وَأَمْطَرْنَا عَلَيْهِم مَّطَرًا ۖ فَسَآءَ مَطَرُ ٱلْمُنذَرِينَ١٧٣
Waamtarna ʿalayhim mataran fasaa mataru almunthareena
Kuma Muka yi ruwan sama a kansu ruwa, sai dai ruwan waɗanda ake yi wa gargaɗi ya mũnana.
-
إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً ۖ وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ١٧٤
Inna fee thalika laayatan wama kana aktharuhum mumineena
Lalle ne ga wannan, akwai ãyã, kuma mafi yawansu bã su kasance mãsu ĩmãni ba.
-
وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ١٧٥
Wainna rabbaka lahuwa alʿazeezu alrraheemu
Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
-
كَذَّبَ أَصْحَـٰبُ لْـَٔيْكَةِ ٱلْمُرْسَلِينَ١٧٦
Kaththaba ashabu alaykati almursaleena
Ma'abũta ƙunci sun ƙaryata Manzanni.
-
إِذْ قَالَ لَهُمْ شُعَيْبٌ أَلَا تَتَّقُونَ١٧٧
Ith qala lahum shuʿaybun ala tattaqoona
A lõkacin da Shu'aibu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba?"
-
إِنِّى لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ١٧٨
Innee lakum rasoolun ameenun
"Lalle ne ni, zuwa gare ku, Manzo ne, amintacce."
-
فَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ١٧٩
Faittaqoo Allaha waateeʿooni
"Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa kuma ku yi mini ɗã'ã."
-
وَمَآ أَسْـَٔلُكُمْ عَلَيْهِ مِنْ أَجْرٍ ۖ إِنْ أَجْرِىَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ١٨٠
Wama asalukum ʿalayhi min ajrin in ajriya illa ʿala rabbi alʿalameena
"Kuma ba ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrata ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu."
-
۞ أَوْفُوا۟ ٱلْكَيْلَ وَلَا تَكُونُوا۟ مِنَ ٱلْمُخْسِرِينَ١٨١
Awfoo alkayla wala takoonoo mina almukhsireena
"Ku cika mũdu, kuma kada ku kasance daga mãsu sanyãwar hasãra (ga mutãne)."
-
وَزِنُوا۟ بِٱلْقِسْطَاسِ ٱلْمُسْتَقِيمِ١٨٢
Wazinoo bialqistasi almustaqeemi
"Kuma ku yi awo da sikẽli daidaitacce."
-
وَلَا تَبْخَسُوا۟ ٱلنَّاسَ أَشْيَآءَهُمْ وَلَا تَعْثَوْا۟ فِى ٱلْأَرْضِ مُفْسِدِينَ١٨٣
Wala tabkhasoo alnnasa ashyaahum wala taʿthaw fee alardi mufsideena
"Kuma kada ku nakasa wa mutãne abũbuwansu kuma kada ku yi fasãdi a cikin ƙasa kuna mãsu ɓarna."
-
وَٱتَّقُوا۟ ٱلَّذِى خَلَقَكُمْ وَٱلْجِبِلَّةَ ٱلْأَوَّلِينَ١٨٤
Waittaqoo allathee khalaqakum waaljibillata alawwaleena
"Kuma ku ji tsõron Allah wanda Ya halitta ku, kũ da jama'ar farko."
-
قَالُوٓا۟ إِنَّمَآ أَنتَ مِنَ ٱلْمُسَحَّرِينَ١٨٥
Qaloo innama anta mina almusahhareena
Suka ce: "Kai dai daga waɗanda suke sihirtattu kawai ne."
-
وَمَآ أَنتَ إِلَّا بَشَرٌ مِّثْلُنَا وَإِن نَّظُنُّكَ لَمِنَ ٱلْكَـٰذِبِينَ١٨٦
Wama anta illa basharun mithluna wain nathunnuka lamina alkathibeena
"Kuma bã kõwa kake ba, fãce mutum kamarmu kuma lalle ne munã zaton ka, haƙĩƙa, daga maƙaryata."
-
فَأَسْقِطْ عَلَيْنَا كِسَفًا مِّنَ ٱلسَّمَآءِ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّـٰدِقِينَ١٨٧
Faasqit ʿalayna kisafan mina alssamai in kunta mina alssadiqeena
"To ka jẽfo wani ɓaɓɓake daga sama a kanmu, idan ka kasance daga mãsu gaskiya."
-
قَالَ رَبِّىٓ أَعْلَمُ بِمَا تَعْمَلُونَ١٨٨
Qala rabbee aʿlamu bima taʿmaloona
Ya ce: "Ubangijĩna ne Mafi sani ga abin da kuke aikatãwa."
-
فَكَذَّبُوهُ فَأَخَذَهُمْ عَذَابُ يَوْمِ ٱلظُّلَّةِ ۚ إِنَّهُۥ كَانَ عَذَابَ يَوْمٍ عَظِيمٍ١٨٩
Fakaththaboohu faakhathahum ʿathabu yawmi alththullati innahu kana ʿathaba yawmin ʿatheemin
Sai suka ƙaiyatã shi, sabõda haka, azãbar rãnar girgije1 ta kãma su. Lalle ne ita, tã kasance azãbar yini mai girma.
Bayanai
[1] An ruwaito cewa Allah Ya bũɗe musu ƙõfar Jahannama, zãfi ya hana su zama akõ'ina cikin gidãjensu, sa'an nan aka sanya girgije ya yi musu inuwa mai sanyi-sanyi har suka tãru a ciki, sa'an nan aka sanya girgijen ya kãma da wuta a kansu suka ƙõne kurmus kamar an gasa fãra. Suka kõma tõka kamar yadda suka nema daga Shu'aibu da a jefa musu ɓaɓɓake daga sama idan ya zama daga mãsu gaskiya. -
إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً ۖ وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ١٩٠
Inna fee thalika laayatan wama kana aktharuhum mumineena
Lalle a cikin wancan haƙĩka akwai ãya, amma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba.
-
وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ١٩١
Wainna rabbaka lahuwa alʿazeezu alrraheemu
Kuma lalle Ubangijĩnka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
-
وَإِنَّهُۥ لَتَنزِيلُ رَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ١٩٢
Wainnahu latanzeelu rabbi alʿalameena
Kuma lalle shi (Alƙur'ãni), haƙĩƙa, saukarwar Ubangijinhalittu ne.
-
نَزَلَ بِهِ ٱلرُّوحُ ٱلْأَمِينُ١٩٣
Nazala bihi alrroohu alameenu
Rũhi1 amintacce ne ya sauka da shi.
Bayanai
[1] Rũhul Ƙudus, shi ne Jibirĩl, amincin Allah ya tabbata a gare shi. -
عَلَىٰ قَلْبِكَ لِتَكُونَ مِنَ ٱلْمُنذِرِينَ١٩٤
ʿAla qalbika litakoona mina almunthireena
A kan zũciyarka, dõmin ka kasance daga mãsu gargaɗi.
-
بِلِسَانٍ عَرَبِىٍّ مُّبِينٍ١٩٥
Bilisanin ʿarabiyyin mubeenin
Da harshe na Larabci mai bayãni.
-
وَإِنَّهُۥ لَفِى زُبُرِ ٱلْأَوَّلِينَ١٩٦
Wainnahu lafee zuburi alawwaleena
Kuma lalle shin, haƙĩƙa, yanã a cikin litattafan (Manzannin) farko.
-
أَوَلَمْ يَكُن لَّهُمْ ءَايَةً أَن يَعْلَمَهُۥ عُلَمَـٰٓؤُا۟ بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ١٩٧
Awalam yakun lahum ayatan an yaʿlamahu ʿulamao banee israeela
Ashe, bai kasance ãyã ba a gare su, ya zama Mãlaman Banĩ Isrã'ĩla sun san shi?
-
وَلَوْ نَزَّلْنَـٰهُ عَلَىٰ بَعْضِ ٱلْأَعْجَمِينَ١٩٨
Walaw nazzalnahu ʿala baʿdi alaʿjameena
Kuma dã mun saukar da shi a kan sãshen Ajamãwa,
-
فَقَرَأَهُۥ عَلَيْهِم مَّا كَانُوا۟ بِهِۦ مُؤْمِنِينَ١٩٩
Faqaraahu ʿalayhim ma kanoo bihi mumineena
Ya karanta shi a kansu, ba su kasance sabõda shi mãsu ĩmãni ba.
-
كَذَٰلِكَ سَلَكْنَـٰهُ فِى قُلُوبِ ٱلْمُجْرِمِينَ٢٠٠
Kathalika salaknahu fee quloobi almujrimeena
Kamar wancan ne! Muka shigar da shi a cikin zukãtan mãsu laifi.
-
لَا يُؤْمِنُونَ بِهِۦ حَتَّىٰ يَرَوُا۟ ٱلْعَذَابَ ٱلْأَلِيمَ٢٠١
La yuminoona bihi hatta yarawoo alʿathaba alaleema
Bã zã su yi ĩmãni da shĩ ba sai sun ga azãbar nan mai raɗadi.
-
فَيَأْتِيَهُم بَغْتَةً وَهُمْ لَا يَشْعُرُونَ٢٠٢
Fayatiyahum baghtatan wahum la yashʿuroona
Sai ta taho musu kwatsam, alhãli kuwa sũ, ba su sansance ba.
-
فَيَقُولُوا۟ هَلْ نَحْنُ مُنظَرُونَ٢٠٣
Fayaqooloo hal nahnu muntharoona
Sai su ce: "Shin, mu waɗanda ake yi wa jinkiri ne?"
-
أَفَبِعَذَابِنَا يَسْتَعْجِلُونَ٢٠٤
Afabiʿathabina yastaʿjiloona
Ashe, to, da azãbar Mu suke nẽman gaggãwa?
-
أَفَرَءَيْتَ إِن مَّتَّعْنَـٰهُمْ سِنِينَ٢٠٥
Afaraayta in mattaʿnahum sineena
Ashe, to, kã gani, idan Muka jĩshe su daɗi a shẽkaru,
-
ثُمَّ جَآءَهُم مَّا كَانُوا۟ يُوعَدُونَ٢٠٦
Thumma jaahum ma kanoo yooʿadoona
Sa'an nan abin da suka kasance anã yi musu wa'adi (da shi) ya jẽ musu,
-
مَآ أَغْنَىٰ عَنْهُم مَّا كَانُوا۟ يُمَتَّعُونَ٢٠٧
Ma aghna ʿanhum ma kanoo yumattaʿoona
Abin da suka kasance anã jĩshe su dãɗin bã zai tunkuɗe azãba ba daga gare1 su.
Bayanai
[1] Dã an bã su lõkaci mai tsawo sunã jin dãɗi da rãyuwar dũniya a cikinsa, to, rãnar da mutuwa kõ azãbar Allah ta je gare su, wannan lõkacin bã zai tunkuɗe mutuwar kõ azabar ba daga gare su. -
وَمَآ أَهْلَكْنَا مِن قَرْيَةٍ إِلَّا لَهَا مُنذِرُونَ٢٠٨
Wama ahlakna min qaryatin illa laha munthiroona
Kuma bã Mu halakar da wata alƙarya ba fãce tanã da mãsu gargaɗi.
-
ذِكْرَىٰ وَمَا كُنَّا ظَـٰلِمِينَ٢٠٩
Thikra wama kunna thalimeena
Dõmin tunãtarwa, kuma ba Mu kasance Mãsu zãlunci ba.
-
وَمَا تَنَزَّلَتْ بِهِ ٱلشَّيَـٰطِينُ٢١٠
Wama tanazzalat bihi alshshayateenu
Kuma (Alƙur'ãni) Shaiɗãnu ba su ɗõra sauka da shĩba.
-
وَمَا يَنۢبَغِى لَهُمْ وَمَا يَسْتَطِيعُونَ٢١١
Wama yanbaghee lahum wama yastateeʿoona
Kuma bã ya kamãta a gare su (su Shaiɗãnu su sauka da shi), kuma ba su iyãwa.
-
إِنَّهُمْ عَنِ ٱلسَّمْعِ لَمَعْزُولُونَ٢١٢
Innahum ʿani alssamʿi lamaʿzooloona
Lalle ne sũ, daga saurãre, haƙĩƙa, waɗanda aka nĩsantar ne.
-
فَلَا تَدْعُ مَعَ ٱللَّهِ إِلَـٰهًا ءَاخَرَ فَتَكُونَ مِنَ ٱلْمُعَذَّبِينَ٢١٣
Fala tadʿu maʿa Allahi ilahan akhara fatakoona mina almuʿaththabeena
Sabõda haka, kada ka kira wani abin bautãwa na dabam tãre da Allah, sai ka kasance daga waɗanda ake yi wa azãba.
-
وَأَنذِرْ عَشِيرَتَكَ ٱلْأَقْرَبِينَ٢١٤
Waanthir ʿasheerataka alaqrabeena
Kuma ka yi gargaɗi ga danginka mafiya kusanci.
-
وَٱخْفِضْ جَنَاحَكَ لِمَنِ ٱتَّبَعَكَ مِنَ ٱلْمُؤْمِنِينَ٢١٥
Waikhfid janahaka limani ittabaʿaka mina almumineena
Kuma ka sassauta fikãfikanka1 ga wanda ya bĩ ka daga mũminai.
Bayanai
[1] Ka zama mai tausayi ga mũminai waɗanda suka bĩ ka, ka yi musu kamar yadda kãzã take yi wa 'ya'yanta ƙanana a lõkacin sanyi, kõ kuwa idan zã su yi barci dõmin ta kãre su daga cũta. -
فَإِنْ عَصَوْكَ فَقُلْ إِنِّى بَرِىٓءٌ مِّمَّا تَعْمَلُونَ٢١٦
Fain ʿasawka faqul innee bareeon mimma taʿmaloona
Sa'an nan idan suka sãɓã maka to ka ce: "Lalle nĩ, barrantacce ne daga abin da kuko aikatãwa."
-
وَتَوَكَّلْ عَلَى ٱلْعَزِيزِ ٱلرَّحِيمِ٢١٧
Watawakkal ʿala alʿazeezi alrraheemi
Kuma ka dõgara ga Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
-
ٱلَّذِى يَرَىٰكَ حِينَ تَقُومُ٢١٨
Allathee yaraka heena taqoomu
Wanda Yake ganin ka a lõkacin da kake tãshi tsaye.
-
وَتَقَلُّبَكَ فِى ٱلسَّـٰجِدِينَ٢١٩
Wataqallubaka fee alssajideena
Da jujjuyãwarka a cikin mãsu yin sujada.
-
إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلْعَلِيمُ٢٢٠
Innahu huwa alssameeʿu alʿaleemu
Lalle Shi, Shi1 ne Mai ji, Masani.
Bayanai
[1] Allah Shi ne Mai ji, ji na gaskiya, kuma Masani, sani na gaskiya. -
هَلْ أُنَبِّئُكُمْ عَلَىٰ مَن تَنَزَّلُ ٱلشَّيَـٰطِينُ٢٢١
Hal onabbiokum ʿala man tanazzalu alshshayateenu
Shin, (kunã so) in gaya1 muku a kan wanda Shaiɗãnnu kan sauka?
Bayanai
[1] Wannan dõmin raddi ne gamãsu cewa aljannu ke gayawa Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, Alƙur'ãni. Aljannu bã su saukã sai ga maƙaryaci, mai zunubi' Muhammadu kuwa bã haka yake ba. Sabõda haka shi bã mahaukaci ba, kuma ba wanda aljannu suke gaya wa ba. Dukan abin da ya faɗa, to, wahayi ne daga Allah. -
تَنَزَّلُ عَلَىٰ كُلِّ أَفَّاكٍ أَثِيمٍ٢٢٢
Tanazzalu ʿala kulli affakin atheemin
Sukan sauka a kan dukkan maƙaryaci, mai zunubi.
-
يُلْقُونَ ٱلسَّمْعَ وَأَكْثَرُهُمْ كَـٰذِبُونَ٢٢٣
Yulqoona alssamʿa waaktharuhum kathiboona
Sunã jẽfa (abin da suka) ji, alhãli kuwa mafi yawansu maƙaryata ne.
-
وَٱلشُّعَرَآءُ يَتَّبِعُهُمُ ٱلْغَاوُۥنَ٢٢٤
Waalshshuʿarao yattabiʿuhumu alghawoona
Kuma mawãƙa1 halakakku ne ke bin su.
Bayanai
[1] Siffõfin mawãƙa sun nũna cewa Annabi Muhammadu bã mawãƙi ba ne, dõmin bã shi da ɗaya daga cikin siffõfin mawãƙa. Kuma mabiyansa ba halakakku ba ne. -
أَلَمْ تَرَ أَنَّهُمْ فِى كُلِّ وَادٍ يَهِيمُونَ٢٢٥
Alam tara annahum fee kulli wadin yaheemoona
Shin, ba ku cẽwa, lalle ne sũ, cikin kõwane rango sunã yin ɗimuwa (su ƙẽtare haddi) ba?
-
وَأَنَّهُمْ يَقُولُونَ مَا لَا يَفْعَلُونَ٢٢٦
Waannahum yaqooloona ma la yafʿaloona
Kuma lalle ne, sũ, sunã faɗin abin da bã su aikatãwa?
-
إِلَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ وَذَكَرُوا۟ ٱللَّهَ كَثِيرًا وَٱنتَصَرُوا۟ مِنۢ بَعْدِ مَا ظُلِمُوا۟ ۗ وَسَيَعْلَمُ ٱلَّذِينَ ظَلَمُوٓا۟ أَىَّ مُنقَلَبٍ يَنقَلِبُونَ٢٢٧
Illa allatheena amanoo waʿamiloo alssalihati wathakaroo Allaha katheeran waintasaroo min baʿdi ma thulimoo wasayaʿlamu allatheena thalamoo ayya munqalabin yanqaliboona
Fãce waɗanda suka yi ĩmãni suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka ambaci Allah da yawa, kuma suka rãma zãlunci, daga bãyan an zãlunce su. Kuma waɗanda suka yi zãlunci, zã su sani a wace majũya suke jũyãwa.
Tambayoyin da ake yawan yi
Mece ce ma’anar sunan Suratul Shu’ara’i?
Ma’anar Shu’ara’i ita ce “Mawaƙa”.
Suratul Shu’ara’i tana cikin juz’i na nawa?
Suratul Shu’ara’i tana cikin juz’i na 19.
Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Shu’ara’i?
Suratul Shu’ara’i tana da ayoyi 227.
Suratul Shu’ara’i Makkiya ce ko Madaniya?
Suratul Shu’ara’i sura ce Makkiya.
Suratul Shu’ara’i ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?
Ita ce sura ta 26 a cikin Alƙur’ani.
Majiyoyi
- Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
- Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
- Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
- Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
- Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
- Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.
Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.