سورة النمل

Suratul Naml da fassarar Hausa

Tururuwa

Mushafi

Mishary Rashid AlafasySauke MP3Sauke PDF

Suratul Naml (النمل) ita ce sura ta 27 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 93. Ma’anar sunanta ita ce “Tururuwa”. Sura ce Makkiya, wadda ta sauka a Makka kafin Hijira, kuma tana cikin juz’i na 19 da 20.

A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Naml gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.

Suratul Naml cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. طسٓ ۚ تِلْكَ ءَايَـٰتُ ٱلْقُرْءَانِ وَكِتَابٍ مُّبِينٍ۝١

    Taseen tilka ayatu alqurani wakitabin mubeenin

    T. S̃. Waɗancan ãyõyin Alƙur'ãni ne da Littãfi mai bayyanawa.

  2. هُدًى وَبُشْرَىٰ لِلْمُؤْمِنِينَ۝٢

    Hudan wabushra lilmumineena

    Shiriya ce da bushãra ga mũminai.

  3. ٱلَّذِينَ يُقِيمُونَ ٱلصَّلَوٰةَ وَيُؤْتُونَ ٱلزَّكَوٰةَ وَهُم بِٱلْـَٔاخِرَةِ هُمْ يُوقِنُونَ۝٣

    Allatheena yuqeemoona alssalata wayutoona alzzakata wahum bialakhirati hum yooqinoona

    Waɗanda suke tsayar da salla kuma su bãyar da zakka, alhãli kuwa sũ, game da Lãhira, to, sũ, sunã yin yaƙĩni.

  4. إِنَّ ٱلَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِٱلْـَٔاخِرَةِ زَيَّنَّا لَهُمْ أَعْمَـٰلَهُمْ فَهُمْ يَعْمَهُونَ۝٤

    Inna allatheena la yuminoona bialakhirati zayyanna lahum aʿmalahum fahum yaʿmahoona

    Lalle ne waɗanda suke bã su yin ĩmãni da Lãhira, Mun ƙawãta musu ayyukansu, sabõda haka sunã ɗimuwa.

  5. أُو۟لَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ لَهُمْ سُوٓءُ ٱلْعَذَابِ وَهُمْ فِى ٱلْـَٔاخِرَةِ هُمُ ٱلْأَخْسَرُونَ۝٥

    Olaika allatheena lahum sooo alʿathabi wahum fee alakhirati humu alakhsaroona

    Waɗannan ne waɗanda suke sunã da mugunyar azãba (a dũniya), kuma sũ, a Lãhira, sũ ne mafiya hasãra.

  6. وَإِنَّكَ لَتُلَقَّى ٱلْقُرْءَانَ مِن لَّدُنْ حَكِيمٍ عَلِيمٍ۝٦

    Wainnaka latulaqqa alqurana min ladun hakeemin ʿaleemin

    Kuma lalle ne haƙĩƙa, anã haɗa1 ka da Alƙur'ãni daga gun Mai hikima, Masani.

    Bayanai
    [1] Lãhira da ĩmãni da ita sunã a cikin ashĩran Allah. Haka karɓar Alƙur'ãni daga Allah yanã a cikin asĩran Allah da Ya bayyana a Littafi. Ganin Mũsa ga wutã da abubuwan da suka auku a wurin game da maganar Allah a gare shi da jũyãwar sanda macijiya da kõmawarta sanda da jũyãwar hannunsa fari ƙal da jũyãwarsa zuwa ga asalinsa, duka sunã a cikin asĩran Allah da Ya bayyana su ga wani mutum.
  7. إِذْ قَالَ مُوسَىٰ لِأَهْلِهِۦٓ إِنِّىٓ ءَانَسْتُ نَارًا سَـَٔاتِيكُم مِّنْهَا بِخَبَرٍ أَوْ ءَاتِيكُم بِشِهَابٍ قَبَسٍ لَّعَلَّكُمْ تَصْطَلُونَ۝٧

    Ith qala moosa liahlihi innee anastu naran saateekum minha bikhabarin aw ateekum bishihabin qabasin laʿallakum tastaloona

    A lõkacin da Mũsã ya ce wa iyãlinsa "Lalle ni, na tsinkãyi wata wuta, ni mai zo muku daga gare ta ne, da wani lãbari, ko kuwa mai zo muku ne da Yũla, makãmashi, tsammãninku, ku ji ɗimi."

  8. فَلَمَّا جَآءَهَا نُودِىَ أَنۢ بُورِكَ مَن فِى ٱلنَّارِ وَمَنْ حَوْلَهَا وَسُبْحَـٰنَ ٱللَّهِ رَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ۝٨

    Falamma jaaha noodiya an boorika man fee alnnari waman hawlaha wasubhana Allahi rabbi alʿalameena

    To, a lõkacin da ya jẽ mata, sai aka kira shi cẽwa, "An tsarkake wanda yake cikin (wurin) wutar da yanda yake a gẽfenta kuma tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin halittu."

  9. يَـٰمُوسَىٰٓ إِنَّهُۥٓ أَنَا ٱللَّهُ ٱلْعَزِيزُ ٱلْحَكِيمُ۝٩

    Ya moosa innahu ana Allahu alʿazeezu alhakeemu

    "Yã Mũsã lalle ne shi, Nĩ ne Allah, Mabuwãyi, Mai hikima."

  10. وَأَلْقِ عَصَاكَ ۚ فَلَمَّا رَءَاهَا تَهْتَزُّ كَأَنَّهَا جَآنٌّ وَلَّىٰ مُدْبِرًا وَلَمْ يُعَقِّبْ ۚ يَـٰمُوسَىٰ لَا تَخَفْ إِنِّى لَا يَخَافُ لَدَىَّ ٱلْمُرْسَلُونَ۝١٠

    Waalqi ʿasaka falamma raaha tahtazzu kaannaha jannun walla mudbiran walam yuʿaqqib ya moosa la takhaf innee la yakhafu ladayya almursaloona

    "Kuma ka jẽfa sandarka." To, a lõkacin da ya gan ta tanã girgiza kamar dai ita ƙaramin macĩji ne, sai ya jũya yanã mai bãyar da bãya, kuma bai kõma ba, "Yã Musã! Kada ka ji tsõro lalle Ni, Manzanni bã sujin tsõro a wuri Na."

  11. إِلَّا مَن ظَلَمَ ثُمَّ بَدَّلَ حُسْنًۢا بَعْدَ سُوٓءٍ فَإِنِّى غَفُورٌ رَّحِيمٌ۝١١

    Illa man thalama thumma baddala husnan baʿda sooin fainnee ghafoorun raheemun

    "Sai wanda ya yi zãlunci, sa'an nan ya musanya kyau a bãyan cũta, to, lalle Nĩ, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai."

  12. وَأَدْخِلْ يَدَكَ فِى جَيْبِكَ تَخْرُجْ بَيْضَآءَ مِنْ غَيْرِ سُوٓءٍ ۖ فِى تِسْعِ ءَايَـٰتٍ إِلَىٰ فِرْعَوْنَ وَقَوْمِهِۦٓ ۚ إِنَّهُمْ كَانُوا۟ قَوْمًا فَـٰسِقِينَ۝١٢

    Waadkhil yadaka fee jaybika takhruj baydaa min ghayri sooin fee tisʿi ayatin ila firʿawna waqawmihi innahum kanoo qawman fasiqeena

    "Kuma ka shigar da hannunka a cikin wuyan rĩgarka, ya fita fari, bãbu wata cũta, a cikinwasu ãyõyi tara zuwa ga Fir'auna da mutãnensa. Lalle ne sũ, sun kasance mutãne ne fãsiƙai."

  13. فَلَمَّا جَآءَتْهُمْ ءَايَـٰتُنَا مُبْصِرَةً قَالُوا۟ هَـٰذَا سِحْرٌ مُّبِينٌ۝١٣

    Falamma jaathum ayatuna mubsiratan qaloo hatha sihrun mubeenun

    To, a lõkacin da ãyõyin Mu suka jẽ musu, sunã mãsu wãyar da kai suka ce wannan sihiri ne bayyananne.

  14. وَجَحَدُوا۟ بِهَا وَٱسْتَيْقَنَتْهَآ أَنفُسُهُمْ ظُلْمًا وَعُلُوًّا ۚ فَٱنظُرْ كَيْفَ كَانَ عَـٰقِبَةُ ٱلْمُفْسِدِينَ۝١٤

    Wajahadoo biha waistayqanatha anfusuhum thulman waʿuluwwan faonthur kayfa kana ʿaqibatu almufsideena

    Kuma suka yi musunsu, alhãli zukãtansu sun natsu da su dõmin zãlunci da girman kai. To, ka dũbi yadda ãƙibar maɓarnata ta kasance.

  15. وَلَقَدْ ءَاتَيْنَا دَاوُۥدَ وَسُلَيْمَـٰنَ عِلْمًا ۖ وَقَالَا ٱلْحَمْدُ لِلَّهِ ٱلَّذِى فَضَّلَنَا عَلَىٰ كَثِيرٍ مِّنْ عِبَادِهِ ٱلْمُؤْمِنِينَ۝١٥

    Walaqad atayna dawooda wasulaymana ʿilman waqala alhamdu lillahi allathee faddalana ʿala katheerin min ʿibadihi almumineena

    Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bai wa Dãwũda da Sulaimãn ilmi kuma suka ce: "Gõdiya1 ta tabbata ga Allah, Wanda Ya fĩfĩta mu a kan mãsu yawa daga bãyin Sa mũminai."

    Bayanai
    [1] Abin da ke hakkin ni'imar Allah a kan mutum, ya gõde Masa. Dãwũda da Sulaiman Allah Yã bã su ilmi na Annabci sun tsayu da gõdiyarsa a kan aiki da shi, da kuma iƙrãri da cewa nĩ'ima ce daga Allah, bã da wani aiki nãsu ba. Annabci da ilmi da sanin maganar tsuntsu da ta aljannu da taturũruwa duka sunã cikin ashĩrin Allah da Yake nũnãwa ta hanyar waɗansu bãyinsa Annabãwa.
  16. وَوَرِثَ سُلَيْمَـٰنُ دَاوُۥدَ ۖ وَقَالَ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ عُلِّمْنَا مَنطِقَ ٱلطَّيْرِ وَأُوتِينَا مِن كُلِّ شَىْءٍ ۖ إِنَّ هَـٰذَا لَهُوَ ٱلْفَضْلُ ٱلْمُبِينُ۝١٦

    Wawaritha sulaymanu dawooda waqala ya ayyuha alnnasu ʿullimna mantiqa alttayri waooteena min kulli shayin inna hatha lahuwa alfadlu almubeenu

    Kuma sulaimãn ya gãji Dãwũda ya ce: "Yã ku mutãne! An sanar da mu maganar tsuntsãye, kuma an bã mu daga kõwane abu. Lalle ne wannan haƙĩƙa shi ne falalar (Allah) bayyananna."

  17. وَحُشِرَ لِسُلَيْمَـٰنَ جُنُودُهُۥ مِنَ ٱلْجِنِّ وَٱلْإِنسِ وَٱلطَّيْرِ فَهُمْ يُوزَعُونَ۝١٧

    Wahushira lisulaymana junooduhu mina aljinni waalinsi waalttayri fahum yoozaʿoona

    Kuma aka tattara, dõmin Sulaimãn, rundunõninsa, daga aljannu da mutãne da tsuntsãye, to, sũ anã kange su (ga tafiya).

  18. حَتَّىٰٓ إِذَآ أَتَوْا۟ عَلَىٰ وَادِ ٱلنَّمْلِ قَالَتْ نَمْلَةٌ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّمْلُ ٱدْخُلُوا۟ مَسَـٰكِنَكُمْ لَا يَحْطِمَنَّكُمْ سُلَيْمَـٰنُ وَجُنُودُهُۥ وَهُمْ لَا يَشْعُرُونَ۝١٨

    Hatta itha ataw ʿala wadi alnnamli qalat namlatun ya ayyuha alnnamlu odkhuloo masakinakum la yahtimannakum sulaymanu wajunooduhu wahum la yashʿuroona

    Har a lõkacin da suka je a kan rãfin turũruwa wata turũruwa ta ce, "Yã kũ jama'ar turũruwa! Ku shiga gidãjenku, kada Sulaimãn da rundunõninsa su kakkarya ku, alhãli kuwa sũ, ba su sani ba."

  19. فَتَبَسَّمَ ضَاحِكًا مِّن قَوْلِهَا وَقَالَ رَبِّ أَوْزِعْنِىٓ أَنْ أَشْكُرَ نِعْمَتَكَ ٱلَّتِىٓ أَنْعَمْتَ عَلَىَّ وَعَلَىٰ وَٰلِدَىَّ وَأَنْ أَعْمَلَ صَـٰلِحًا تَرْضَىٰهُ وَأَدْخِلْنِى بِرَحْمَتِكَ فِى عِبَادِكَ ٱلصَّـٰلِحِينَ۝١٩

    Fatabassama dahikan min qawliha waqala rabbi awziʿnee an ashkura niʿmataka allatee anʿamta ʿalayya waʿala walidayya waan aʿmala salihan tardahu waadkhilnee birahmatika fee ʿibadika alssaliheena

    Sai ya yi murmushi yanã mai dãriya daga maganarta, kuma ya ce, "Yã Ubangijĩna! Ka cũsa mini in gõde wa ni'imarKa wadda Ka ni'imta ta a gare ni da kuma ga mahaifãna biyu, kuma in aikata aiki na ƙwarai, wanda Kake yarda da shi, kuma Ka shigar da ni, sabõda rahamarKa, a cikin bãyinKa sãlihai."

  20. وَتَفَقَّدَ ٱلطَّيْرَ فَقَالَ مَا لِىَ لَآ أَرَى ٱلْهُدْهُدَ أَمْ كَانَ مِنَ ٱلْغَآئِبِينَ۝٢٠

    Watafaqqada alttayra faqala ma liya la ara alhudhuda am kana mina alghaibeena

    Kuma ya binciki1 tsuntsãye, sai ya ce: "Me ya kãre ni bã ni ganin hudhudu, kõ ya kasance daga mãsu fakuwa ne?"

    Bayanai
    [1] Wannan ya nũna tsayuwar sulaimãn da binciken kõme da kõwa a cikin daularsa. Kuma da yadda yake yin tsanani a cikin sauƙi. Wannan ita ce hanyar mulki mai kyau.
  21. لَأُعَذِّبَنَّهُۥ عَذَابًا شَدِيدًا أَوْ لَأَا۟ذْبَحَنَّهُۥٓ أَوْ لَيَأْتِيَنِّى بِسُلْطَـٰنٍ مُّبِينٍ۝٢١

    Laoʿaththibannahu ʿathaban shadeedan aw laathbahannahu aw layatiyannee bisultanin mubeenin

    "Lalle ne zã ni azabta shi azãba mai tsanani kõ kuwa lalle in yanka shi, kõ kuwa lalle ya zo mini da dalĩli bayyananne."

  22. فَمَكَثَ غَيْرَ بَعِيدٍ فَقَالَ أَحَطتُ بِمَا لَمْ تُحِطْ بِهِۦ وَجِئْتُكَ مِن سَبَإٍۭ بِنَبَإٍ يَقِينٍ۝٢٢

    Famakatha ghayra baʿeedin faqala ahattu bima lam tuhit bihi wajituka min sabain binabain yaqeenin

    Sai ya zauna bã nẽsa ba, sa'an nan ya ce: "Nã san abin da ba ka sani ba, kuma na zo maka daga Saba da wani lãbari tabbatacce."

  23. إِنِّى وَجَدتُّ ٱمْرَأَةً تَمْلِكُهُمْ وَأُوتِيَتْ مِن كُلِّ شَىْءٍ وَلَهَا عَرْشٌ عَظِيمٌ۝٢٣

    Innee wajadtu imraatan tamlikuhum waootiyat min kulli shayin walaha ʿarshun ʿatheemun

    "Lalle ni nã sãmi wata mace wadda tanã mulkinsu kuma an bã ta daga dukkan kõme, kuma tanã da gadon sarauta mai girma.

  24. وَجَدتُّهَا وَقَوْمَهَا يَسْجُدُونَ لِلشَّمْسِ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَزَيَّنَ لَهُمُ ٱلشَّيْطَـٰنُ أَعْمَـٰلَهُمْ فَصَدَّهُمْ عَنِ ٱلسَّبِيلِ فَهُمْ لَا يَهْتَدُونَ۝٢٤

    Wajadtuha waqawmaha yasjudoona lilshshamsi min dooni Allahi wazayyana lahumu alshshaytanu aʿmalahum fasaddahum ʿani alssabeeli fahum la yahtadoona

    "Na sãme ta ita da mutãnenta, sunã yin sujada ga rãnã, baicin Allah, kuma Shaiɗan ya ƙawãce musu ayyukansu, sabõda haka ya karkatar da su daga hanya, sa'an nan sũ, ba su shiryuwa."

  25. أَلَّا يَسْجُدُوا۟ لِلَّهِ ٱلَّذِى يُخْرِجُ ٱلْخَبْءَ فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ وَيَعْلَمُ مَا تُخْفُونَ وَمَا تُعْلِنُونَ۝٢٥

    Alla yasjudoo lillahi allathee yukhriju alkhabaa fee alssamawati waalardi wayaʿlamu ma tukhfoona wama tuʿlinoona

    "Ga1 su yi sujada ga Allah Wanda Yake fitar da abin da yake a ɓõye, a cikin sammai da ƙasa, kuma Yã san abin da kuke ɓõyẽwada abin da kuke bayyanãwa."

    Bayanai
    [1] An kãyar da harafin kõrewa dõmin barinsa, da Hausa, yanã ɓãta ma'ana, dõmin shaiɗan bai kange su daga rashin yin sujada ba.
  26. ٱللَّهُ لَآ إِلَـٰهَ إِلَّا هُوَ رَبُّ ٱلْعَرْشِ ٱلْعَظِيمِ ۩۝٢٦

    Allahu la ilaha illa huwa rabbu alʿarshi alʿatheemi

    "Allah bãbu abin bautãwa fãce shĩ Ubangijin1 Al'arshi, mai girma."

    Bayanai
    [1] Ya siffanta Allah da cewa bãbu abin bautãwa fãce Shi, dõmin ya kõre cancantar rãnã ga ibãda, da Ubangijin Al'arshi dõmin ya ɗebe girman gadon Bilkisu daga zukãta.
  27. ۞ قَالَ سَنَنظُرُ أَصَدَقْتَ أَمْ كُنتَ مِنَ ٱلْكَـٰذِبِينَ۝٢٧

    Qala sananthuru asadaqta am kunta mina alkathibeena

    Ya ce: "Za mu dũba shin kã yi gaskiya ne, kõ kuwa kã kasance daga maƙaryata?"

  28. ٱذْهَب بِّكِتَـٰبِى هَـٰذَا فَأَلْقِهْ إِلَيْهِمْ ثُمَّ تَوَلَّ عَنْهُمْ فَٱنظُرْ مَاذَا يَرْجِعُونَ۝٢٨

    Ithhab bikitabee hatha faalqih ilayhim thumma tawalla ʿanhum faonthur matha yarjiʿoona

    "Ka tafi da takardata wannan, sa'an nan ka jẽfa ta zuwa gare su, sa'an nan kuma ka jũya daga barinsu, sa'an nan ka ga mẽne ne suke mayarwa."

  29. قَالَتْ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلْمَلَؤُا۟ إِنِّىٓ أُلْقِىَ إِلَىَّ كِتَـٰبٌ كَرِيمٌ۝٢٩

    Qalat ya ayyuha almalao innee olqiya ilayya kitabun kareemun

    Ta ce: "Yã kũ mashawarta! Lalle ne, an jẽfo, zuwa gareni, wata takarda mai girma."

  30. إِنَّهُۥ مِن سُلَيْمَـٰنَ وَإِنَّهُۥ بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ۝٣٠

    Innahu min sulaymana wainnahu bismi Allahi alrrahmani alrraheemi

    "Lalle ita daga Sulaiman take, kuma lalle ita da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai ne."

  31. أَلَّا تَعْلُوا۟ عَلَىَّ وَأْتُونِى مُسْلِمِينَ۝٣١

    Alla taʿloo ʿalayya watoonee muslimeena

    "Kada ku yi girman kai a gare ni, kuma ku zo mini kunã mãsu sallamãwa."

  32. قَالَتْ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلْمَلَؤُا۟ أَفْتُونِى فِىٓ أَمْرِى مَا كُنتُ قَاطِعَةً أَمْرًا حَتَّىٰ تَشْهَدُونِ۝٣٢

    Qalat ya ayyuha almalao aftoonee fee amree ma kuntu qatiʿatan amran hatta tashhadoona

    Ta ce: "Yã ku mashawarta1! Ku yi Mini fatawa ga al'amarĩna, ban kasance mai yanke wani al'amari ba, sai kun halarta."

    Bayanai
    [1] Allah bai keɓance hikima ga maza kawai ba har mãtã akwai mãsu hikima a cikinsu. Sai dai Musulunci yã hana shugabancin mãtã, sabõda galibinsu ãdifarsu tã rinjãyi hankalinsu, sabõda kyautata tarbiyyar yãra. Anã fahimtar cewa iya mulki shi ne rashin fallewa da ra'ayi ga shũgaba, sai a bãyan ya shãwarci mutãnensa, kamar yadda sarauniyar Saba' ta yi da Majalisarta.
  33. قَالُوا۟ نَحْنُ أُو۟لُوا۟ قُوَّةٍ وَأُو۟لُوا۟ بَأْسٍ شَدِيدٍ وَٱلْأَمْرُ إِلَيْكِ فَٱنظُرِى مَاذَا تَأْمُرِينَ۝٣٣

    Qaloo nahnu oloo quwwatin waoloo basin shadeedin waalamru ilayki faonthuree matha tamureena

    Suka ce: "Mũ ma'abũta ƙarfi ne, kuma ma'abbũta yãƙi mai tsanani ne, kuma al'amari yã kõma zuwa gare ki, sabõda haka ki dũbamẽne ne zã ki yi umarni (da shi)?"

  34. قَالَتْ إِنَّ ٱلْمُلُوكَ إِذَا دَخَلُوا۟ قَرْيَةً أَفْسَدُوهَا وَجَعَلُوٓا۟ أَعِزَّةَ أَهْلِهَآ أَذِلَّةً ۖ وَكَذَٰلِكَ يَفْعَلُونَ۝٣٤

    Qalat inna almulooka itha dakhaloo qaryatan afsadooha wajaʿaloo aʿizzata ahliha athillatan wakathalika yafʿaloona

    Ta ce: "Lalle sarakuna idan sun shiga wata alƙarya, sai su ɓãta ta, kuma su sanya mãsu darajar mutãnenta ƙasƙantattu. Kuma kamar wancan ne suke likatãwa."

  35. وَإِنِّى مُرْسِلَةٌ إِلَيْهِم بِهَدِيَّةٍ فَنَاظِرَةٌۢ بِمَ يَرْجِعُ ٱلْمُرْسَلُونَ۝٣٥

    Wainnee mursilatun ilayhim bihadiyyatin fanathiratun bima yarjiʿu almursaloona

    "Kuma lalle nĩ mai aikãwa ce zuwa gare su da kyauta, sa'an nan mai dũbawa ce: Da me manzannin zã su kõmo."

  36. فَلَمَّا جَآءَ سُلَيْمَـٰنَ قَالَ أَتُمِدُّونَنِ بِمَالٍ فَمَآ ءَاتَىٰنِۦَ ٱللَّهُ خَيْرٌ مِّمَّآ ءَاتَىٰكُم بَلْ أَنتُم بِهَدِيَّتِكُمْ تَفْرَحُونَ۝٣٦

    Falamma jaa sulaymana qala atumiddoonani bimalin fama ataniya Allahu khayrun mimma atakum bal antum bihadiyyatikum tafrahoona

    To, a lõkacin da ya jẽ wa Sulaiman ya ce: "Shin, za ku ƙãra ni da dũkiya ne? To, abin daAllah Ya bã ni, shi ne mafi alhẽridaga abin da Ya bã ku. A'a, kũ nekuke yin farin ciki da kyautarku."

  37. ٱرْجِعْ إِلَيْهِمْ فَلَنَأْتِيَنَّهُم بِجُنُودٍ لَّا قِبَلَ لَهُم بِهَا وَلَنُخْرِجَنَّهُم مِّنْهَآ أَذِلَّةً وَهُمْ صَـٰغِرُونَ۝٣٧

    Irjiʿ ilayhim falanatiyannahum bijunoodin la qibala lahum biha walanukhrijannahum minha athillatan wahum saghiroona

    "Ka kõma zuwa gare su. Sa'an nan lalle munã je musu da rundunõni, bãbu wata tãɓukawa gare su game da su, kuma lalle munã fitar da su daga gare ta, sunã mafi wulãkantuwa, kuma sunã ƙasƙantattu."

  38. قَالَ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلْمَلَؤُا۟ أَيُّكُمْ يَأْتِينِى بِعَرْشِهَا قَبْلَ أَن يَأْتُونِى مُسْلِمِينَ۝٣٨

    Qala ya ayyuha almalao ayyukum yateenee biʿarshiha qabla an yatoonee muslimeena

    Ya ce: "Yã ku mashãwarta! Wannenku zai zo mini da gadonta a gabãnin su zo, sunã mãsu sallamãwa?"

  39. قَالَ عِفْرِيتٌ مِّنَ ٱلْجِنِّ أَنَا۠ ءَاتِيكَ بِهِۦ قَبْلَ أَن تَقُومَ مِن مَّقَامِكَ ۖ وَإِنِّى عَلَيْهِ لَقَوِىٌّ أَمِينٌ۝٣٩

    Qala ʿifreetun mina aljinni ana ateeka bihi qabla an taqooma min maqamika wainne ʿalayhi laqawiyyun ameenun

    Wani mai ƙarfi daga aljannu ya ce: "Nĩ inã zo maka da shi a gabãnin ka tãshi daga matsayinka. Kuma llale nĩ a gare shi, haƙĩƙa, mai ƙarfi ne amintacce."

  40. قَالَ ٱلَّذِى عِندَهُۥ عِلْمٌ مِّنَ ٱلْكِتَـٰبِ أَنَا۠ ءَاتِيكَ بِهِۦ قَبْلَ أَن يَرْتَدَّ إِلَيْكَ طَرْفُكَ ۚ فَلَمَّا رَءَاهُ مُسْتَقِرًّا عِندَهُۥ قَالَ هَـٰذَا مِن فَضْلِ رَبِّى لِيَبْلُوَنِىٓ ءَأَشْكُرُ أَمْ أَكْفُرُ ۖ وَمَن شَكَرَ فَإِنَّمَا يَشْكُرُ لِنَفْسِهِۦ ۖ وَمَن كَفَرَ فَإِنَّ رَبِّى غَنِىٌّ كَرِيمٌ۝٤٠

    Qala allathee ʿindahu ʿilmun mina alkitabi ana ateeka bihi qabla an yartadda ilayka tarfuka falamma raahu mustaqirran ʿindahu qala hatha min fadli rabbee liyabluwanee aashkuru am akfuru waman shakara fainnama yashkuru linafsihi waman kafara fainna rabbee ghaniyyun kareemun

    Wanda yake a wurinsa akwai1 wani ilmi daga Littafin ya ce: "Ni inã zo maka da shi a gabãnin ƙyaftãwar ganinka ta kõma gare ka." To, a lõkacin da ya gan shi matabbaci a wurinsa, ya ce: "Wannan daga falalar Ubangijĩna yake, dõmin Ya jarraba ni: Shin, zan gõde ne, kõ kuwa zan butulce! Kuma wanda ya gõde, to, yanã gõdẽwa ne dõmin kansa, kuma wanda ya kãfirta, to, lalle Ubangijina Wadãtacce ne, Karĩmi."

    Bayanai
    [1] Allah na bãyar da asirai daga littattafai, kõ da wahayi zuwa ga Annabãwa, kõ da ilhãma daga abin da aka bai wa Annabãwa. Waɗansu sun ce ilmin nan sũnan Allah ne Mafi girma. Allah ne Mafi sani. Sai dai sharaɗin aiki da ilmi ga ĩbãda, ya kasance daga Annabãwa kawai, a cikin lõkacin aiwatar da shari'arsu.Bã a iya amfãni da wani sũnan Allah wanda wani Annabi bai zo da shi ba a gabãnin Musulunci, kuma a bãyan Musulunci.
  41. قَالَ نَكِّرُوا۟ لَهَا عَرْشَهَا نَنظُرْ أَتَهْتَدِىٓ أَمْ تَكُونُ مِنَ ٱلَّذِينَ لَا يَهْتَدُونَ۝٤١

    Qala nakkiroo laha ʿarshaha nanthur atahtadee am takoonu mina allatheena la yahtadoona

    Ya ce: "Ku canza kamar gadonta gare ta, mu gani, shin zã ta shiryu, kõ kuwa tanã kasancẽwa daga waɗanda bã su shiryuwa."

  42. فَلَمَّا جَآءَتْ قِيلَ أَهَـٰكَذَا عَرْشُكِ ۖ قَالَتْ كَأَنَّهُۥ هُوَ ۚ وَأُوتِينَا ٱلْعِلْمَ مِن قَبْلِهَا وَكُنَّا مُسْلِمِينَ۝٤٢

    Falamma jaat qeela ahakatha ʿarshuki qalat kaannahu huwa waooteena alʿilma min qabliha wakunna muslimeena

    To a lõkacin da ta jẽ aka ce "Shin, kamar wannan gadon sarautarki yake?" Ta ce: "Kamar dai shĩne. Kuma an bã mu ilmi daga gabãninta kuma mun kasance mãsu sallamãwar (al'amari ga Allah)."

  43. وَصَدَّهَا مَا كَانَت تَّعْبُدُ مِن دُونِ ٱللَّهِ ۖ إِنَّهَا كَانَتْ مِن قَوْمٍ كَـٰفِرِينَ۝٤٣

    Wasaddaha ma kanat taʿbudu min dooni Allahi innaha kanat min qawmin kafireena

    Kuma abin da ta kasance tanã bautãwa, baicin Allah, ya kange ta. Lalle ita, tã kasance daga mutãne kãfirai.

  44. قِيلَ لَهَا ٱدْخُلِى ٱلصَّرْحَ ۖ فَلَمَّا رَأَتْهُ حَسِبَتْهُ لُجَّةً وَكَشَفَتْ عَن سَاقَيْهَا ۚ قَالَ إِنَّهُۥ صَرْحٌ مُّمَرَّدٌ مِّن قَوَارِيرَ ۗ قَالَتْ رَبِّ إِنِّى ظَلَمْتُ نَفْسِى وَأَسْلَمْتُ مَعَ سُلَيْمَـٰنَ لِلَّهِ رَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ۝٤٤

    Qeela laha odkhulee alssarha falamma raathu hasibathu lujjatan wakashafat ʿan saqayha qala innahu sarhun mumarradun min qawareera qalat rabbi innee thalamtu nafsee waaslamtu maʿa sulaymana lillahi rabbi alʿalameena

    Aka ce mata, "Ki shiga a gidan sarauta." To, a lõkacin da ta gan shi, ta yi zatona wai gurbi ne, kuma ta kuranye1 daga ƙwaurinta. Ya ce: "Lalle ne shi, gidan sarauta ne mai santsi daga madũbai." Ta ce: "Yã Ubangijĩna! Bã a rõƙon Allah sai da sunãyensa mãsu kyau, tis'in da taran nan, sai dai a dunƙule kamar a ce, "Inã rõƙon Allah da sunãyenSa da na sani da waɗanda ban sani ba." Lalle nĩ, na zãlunci kaina, kuma nã sallama al'amari tãre da Sulaiman ga Allah, Ubangijin halittu."

    Bayanai
    [1] Idan ĩmãni ya shiga a cikin zũciya, sai girman kai ya fita daga gare ta sarauniya Bilkisu tanã kuranye ƙafãfunta da niyyarta ta shiga a cikin ruwa dõmin ta nũna ɗã'arta ga umurnin Annabin Allah Sulaimãn kuma ta yarda da shiga gulbin da ba ta san tsawon zurfinsa ba, kõ da za ta mutu awurin ɗã'ã da taƙawa. Mace da sarauta iyakar girman kai ke nan, bãbu abin da zai gusar da shi sai ĩmãnin gaskiya.
  45. وَلَقَدْ أَرْسَلْنَآ إِلَىٰ ثَمُودَ أَخَاهُمْ صَـٰلِحًا أَنِ ٱعْبُدُوا۟ ٱللَّهَ فَإِذَا هُمْ فَرِيقَانِ يَخْتَصِمُونَ۝٤٥

    Walaqad arsalna ila thamooda akhahum salihan ani oʿbudoo Allaha faitha hum fareeqani yakhtasimoona

    Kuma lalle ne, haƙĩƙa, mun aika zuwa Samũdãwa da ɗan'uwansu, Salihu (ya ce), "Ku bauta wa Allah." Sai gã su ƙungiyõyi biyu sunã ta husũma.

  46. قَالَ يَـٰقَوْمِ لِمَ تَسْتَعْجِلُونَ بِٱلسَّيِّئَةِ قَبْلَ ٱلْحَسَنَةِ ۖ لَوْلَا تَسْتَغْفِرُونَ ٱللَّهَ لَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ۝٤٦

    Qala ya qawmi lima tastaʿjiloona bialssayyiati qabla alhasanati lawla tastaghfiroona Allaha laʿallakum turhamoona

    Ya ce: "Yã mutãnẽna! Don me kuke nẽman gaggãwa game da mũnanãwa, a gabãnin kyautatãwa. Don me bã ku nẽman Allah gãfara, tsammãninku, zã a yi muku rahama?"

  47. قَالُوا۟ ٱطَّيَّرْنَا بِكَ وَبِمَن مَّعَكَ ۚ قَالَ طَـٰٓئِرُكُمْ عِندَ ٱللَّهِ ۖ بَلْ أَنتُمْ قَوْمٌ تُفْتَنُونَ۝٤٧

    Qaloo ittayyarna bika wabiman maʿaka qala tairukum ʿinda Allahi bal antum qawmun tuftanoona

    Suka ce: "Munã shu'umci da kai, kuma da wanda ke tãre da kai." Ya ce: "Shu'umcinku a wurin Allah yake. Ã'a, kũ mutãne ne, anã fitinar ku."

  48. وَكَانَ فِى ٱلْمَدِينَةِ تِسْعَةُ رَهْطٍ يُفْسِدُونَ فِى ٱلْأَرْضِ وَلَا يُصْلِحُونَ۝٤٨

    Wakana fee almadeenati tisʿatu rahtin yufsidoona fee alardi wala yuslihoona

    Kuma waɗansu jama'a tara1 sun kasance a cikin birnin, sunã yin ɓarna, kuma bã su kyautatãwa. Suka ce: "Ku yi rantsuwa da Allah, lalle zã mu kwãnan masa,2 shi da mutãnensa sa'an nan mu ce wa waliyyinsa. 'Ba mu halarci halakar mutãnensa ba kuma mũ, haƙĩ ƙa, mãsu gaskiya ne'."

    Bayanai
    [1] Yawan mãsu ɓarnã bã ya hana gaskiya bayyana. Kuma mai mãkirci dõmin ya halakar da mai gargaɗin addinin Allah, yanã yi wa kansa sanadin halaka kawai ne. Waɗannan mutãne tara sun yi niyyar kashe Sãlihu ne, bã da sanin danginsa ba, a wurin dayake kwãna yanã salla a masallacinsa, a bãyan gari. A can Allah ya halakar da su. Wannan shĩ ne sakamakon mãkircin da suka ƙulla. [2] Zã mu kwãnan masa, ai zãmu kwãna da niyyar kashe shi a cikin dare, a ɓõye.
  49. قَالُوا۟ تَقَاسَمُوا۟ بِٱللَّهِ لَنُبَيِّتَنَّهُۥ وَأَهْلَهُۥ ثُمَّ لَنَقُولَنَّ لِوَلِيِّهِۦ مَا شَهِدْنَا مَهْلِكَ أَهْلِهِۦ وَإِنَّا لَصَـٰدِقُونَ۝٤٩

    Qaloo taqasamoo biAllahi lanubayyitannahu waahlahu thumma lanaqoolanna liwaliyyihi ma shahidna mahlika ahlihi wainna lasadiqoona

    Kuma suka ƙulla mãkirci, kuma Muka ƙulla sakamakon mãkirci, alhãli sũ ba su sani ba.

  50. وَمَكَرُوا۟ مَكْرًا وَمَكَرْنَا مَكْرًا وَهُمْ لَا يَشْعُرُونَ۝٥٠

    Wamakaroo makran wamakarna makran wahum la yashʿuroona

    Ka dũba yadda ãƙibar mãkircinsu ta kasance lalle Mũ Mun darkãke su da mutãnensu, gabã ɗaya.

  51. فَٱنظُرْ كَيْفَ كَانَ عَـٰقِبَةُ مَكْرِهِمْ أَنَّا دَمَّرْنَـٰهُمْ وَقَوْمَهُمْ أَجْمَعِينَ۝٥١

    Faonthur kayfa kana ʿaqibatu makrihim anna dammarnahum waqawmahum ajmaʿeena

    Waɗancan, gidãjensu ne, wõfintattu sabõda zãluncin da suka yi, lalle ne a wancan akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke sani.

  52. فَتِلْكَ بُيُوتُهُمْ خَاوِيَةًۢ بِمَا ظَلَمُوٓا۟ ۗ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً لِّقَوْمٍ يَعْلَمُونَ۝٥٢

    Fatilka buyootuhum khawiyatan bima thalamoo inna fee thalika laayatan liqawmin yaʿlamoona

    Muka tsĩrar da waɗanda suka yi ĩmãni, kuma sun kasance sunã taƙawa.

  53. وَأَنجَيْنَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَكَانُوا۟ يَتَّقُونَ۝٥٣

    Waanjayna allatheena amanoo wakanoo yattaqoona

    Da Lũdu, a lõkacin da ya ce wa mutãnensa, "Shin kunã jẽ wa alfasha ne, alhãli, kuwa kunã gani?"

  54. وَلُوطًا إِذْ قَالَ لِقَوْمِهِۦٓ أَتَأْتُونَ ٱلْفَـٰحِشَةَ وَأَنتُمْ تُبْصِرُونَ۝٥٤

    Walootan ith qala liqawmihi atatoona alfahishata waantum tubsiroona

    "Shin lalle kũ haƙĩƙa kunã je wa maza da sha'awa baicin mãtã? Ã'a, kũ wasu irin mutãne ne kuna aikin jãhilci."1

    Bayanai
    [1] Alfãshar mutãnen Lũɗu, ita ce luwãɗi, namji yabi namiji a duburarsa wannan alfãsha, kõ dabbõbi bã su yin ta. Ga mutãnen Lũɗuta fãra bayyana. Allah Ya halakar da su kamar yadda Ya ambata. Sa'an nan kuma ba a ƙãra ganinta ba, sai ga wannan al'umma asĩirin da ke ciki, shĩ ne yadda Allah Yake jũyar da ɗabĩ'ar mutum ta zama bã ta mãsu hankali ba, tãre da dõgewar halittar jikinsa kamar yadda take ga zãhiri.
  55. أَئِنَّكُمْ لَتَأْتُونَ ٱلرِّجَالَ شَهْوَةً مِّن دُونِ ٱلنِّسَآءِ ۚ بَلْ أَنتُمْ قَوْمٌ تَجْهَلُونَ۝٥٥

    Ainnakum latatoona alrrijala shahwatan min dooni alnnisai bal antum qawmun tajhaloona

    Lalle ne ku, haƙĩƙa kunã jẽ wa maza da sha'awa, baicin mata; Ã'a, kũ mutãne ne maɓarnata.

  56. ۞ فَمَا كَانَ جَوَابَ قَوْمِهِۦٓ إِلَّآ أَن قَالُوٓا۟ أَخْرِجُوٓا۟ ءَالَ لُوطٍ مِّن قَرْيَتِكُمْ ۖ إِنَّهُمْ أُنَاسٌ يَتَطَهَّرُونَ۝٥٦

    Fama kana jawaba qawmihi illa an qaloo akhrijoo ala lootin min qaryatikum innahum onasun yatatahharoona

    Bãbu abin da ya kasance jawãbin mutãnensa fãce suka ce "Ku fitar da mutãnen Lũɗu daga alƙaryarku, lalle sũ, wasu irin mutãne ne mãsu da'awar sunã da tsarki."

  57. فَأَنجَيْنَـٰهُ وَأَهْلَهُۥٓ إِلَّا ٱمْرَأَتَهُۥ قَدَّرْنَـٰهَا مِنَ ٱلْغَـٰبِرِينَ۝٥٧

    Faanjaynahu waahlahu illa imraatahu qaddarnaha mina alghabireena

    Sai Muka tsĩrar da shi, shi da mutãnensa,1 fãce mãtarsa, Mun ƙaddara ta a cikin mãsu wanzuwa.

    Bayanai
    [1] Mutãnensa mũminai. Ĩmãni da gaskiya idan gaskiya ta bayyana asĩri ne daga asĩran Allah sai wanda Ya bai wa. Kusanci ga wani Annabi da aure kõ zumunta, bã ya bãyar da shi. Ruwan azãba, shĩ ma asĩri ne na Allah.
  58. وَأَمْطَرْنَا عَلَيْهِم مَّطَرًا ۖ فَسَآءَ مَطَرُ ٱلْمُنذَرِينَ۝٥٨

    Waamtarna ʿalayhim mataran fasaa mataru almunthareena

    Kuma Muka yi ruwa a kansu da wani irin ruwa. To, ruwan waɗanda ake yi wa gargaɗi ya mũnana.

  59. قُلِ ٱلْحَمْدُ لِلَّهِ وَسَلَـٰمٌ عَلَىٰ عِبَادِهِ ٱلَّذِينَ ٱصْطَفَىٰٓ ۗ ءَآللَّهُ خَيْرٌ أَمَّا يُشْرِكُونَ۝٥٩

    Quli alhamdu lillahi wasalamun ʿala ʿibadihi allatheena istafa allahu khayrun amma yushrikoona

    Ka ce: "Godiya ta tabbata ga Alah, kuma aminci ya tabbata bisa ga bãyin Sa, waɗanda Ya zãɓa." Shin Allah ne Mafi alhẽri koabin da suke yin shirki da Shi?1

    Bayanai
    [1] Daga wannan ãyã ta 59 zuwa ƙarshen Sũra, duka tambĩhi ne ga abũbuwan fake na ilmin Allah, wanda ya shãfi jikunanmu, amma ba mu san yadda suke aukuwa a gare mu ba. Sa'an nan kuma da tambĩhi ga abũbuwan gaibi da suke zuwa dõmin mu yi ĩmãni da su.
  60. أَمَّنْ خَلَقَ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضَ وَأَنزَلَ لَكُم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءً فَأَنۢبَتْنَا بِهِۦ حَدَآئِقَ ذَاتَ بَهْجَةٍ مَّا كَانَ لَكُمْ أَن تُنۢبِتُوا۟ شَجَرَهَآ ۗ أَءِلَـٰهٌ مَّعَ ٱللَّهِ ۚ بَلْ هُمْ قَوْمٌ يَعْدِلُونَ۝٦٠

    Amman khalaqa alssamawati waalarda waanzala lakum mina alssamai maan faanbatna bihi hadaiqa thata bahjatin ma kana lakum an tunbitoo shajaraha ailahun maʿa Allahi bal hum qawmun yaʿdiloona

    Kõ wãne ne Ya halitta sammai da ƙasa kuma Ya saukar muku, daga, sama, wani ruwa, Muka tsirar, game da shi, gõnaki mãsu sha'awa, ba ya kasancẽwa gare ku, ku tsirar da itãcensu? Shin, akwai abin bautãwa tãre da Allah? Ã'a, sũ mutãne ne suna daidaitãwa (Allah da wani).

  61. أَمَّن جَعَلَ ٱلْأَرْضَ قَرَارًا وَجَعَلَ خِلَـٰلَهَآ أَنْهَـٰرًا وَجَعَلَ لَهَا رَوَٰسِىَ وَجَعَلَ بَيْنَ ٱلْبَحْرَيْنِ حَاجِزًا ۗ أَءِلَـٰهٌ مَّعَ ٱللَّهِ ۚ بَلْ أَكْثَرُهُمْ لَا يَعْلَمُونَ۝٦١

    Amman jaʿala alarda qararan wajaʿala khilalaha anharan wajaʿala laha rawasiya wajaʿala bayna albahrayni hajizan ailahun maʿa Allahi bal aktharuhum la yaʿlamoona

    Kõ kuwa wãne ne Ya sanya ƙasa tabbatacciya, kuma Ya sanya kõguna a tsakãninta kuma Ya sanya mata manyan duwãtsu tabatattu, kuma Ya sanya wani shãmaki a tsakãnin tẽkuna biyu? Shin akwai wani abin bautãwa tãre da Allah. Ã'a, mafi yawansu ba su sanĩ ba.

  62. أَمَّن يُجِيبُ ٱلْمُضْطَرَّ إِذَا دَعَاهُ وَيَكْشِفُ ٱلسُّوٓءَ وَيَجْعَلُكُمْ خُلَفَآءَ ٱلْأَرْضِ ۗ أَءِلَـٰهٌ مَّعَ ٱللَّهِ ۚ قَلِيلًا مَّا تَذَكَّرُونَ۝٦٢

    Amman yujeebu almudtarra itha daʿahu wayakshifu alssooa wayajʿalukum khulafaa alardi ailahun maʿa Allahi qaleelan ma tathakkaroona

    Kõ wãne ne yake karɓã, kuma ya sanya ku mamãyan ƙasa? Shin akwai wani abin bautawa tãre da Allah? Kaɗan ƙwarai kuke yin tunãni.

  63. أَمَّن يَهْدِيكُمْ فِى ظُلُمَـٰتِ ٱلْبَرِّ وَٱلْبَحْرِ وَمَن يُرْسِلُ ٱلرِّيَـٰحَ بُشْرًۢا بَيْنَ يَدَىْ رَحْمَتِهِۦٓ ۗ أَءِلَـٰهٌ مَّعَ ٱللَّهِ ۚ تَعَـٰلَى ٱللَّهُ عَمَّا يُشْرِكُونَ۝٦٣

    Amman yahdeekum fee thulumati albarri waalbahri waman yursilu alrriyaha bushran bayna yaday rahmatihi ailahun maʿa Allahi taʿala Allahu ʿamma yushrikoona

    Kõ wãne ne yake shiryarwa a cikin duffan ƙasa da tẽku, kuma wãne ne Yake aikõwar iskõki dõmin bãyar da bushãra a gaba ga rahamar Sa? Ashe akwai wani abin bautãwa tãre da Allah? tsarki yã tabbata ga Allah daga barin abin da suke shirki da Shi.

  64. أَمَّن يَبْدَؤُا۟ ٱلْخَلْقَ ثُمَّ يُعِيدُهُۥ وَمَن يَرْزُقُكُم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ وَٱلْأَرْضِ ۗ أَءِلَـٰهٌ مَّعَ ٱللَّهِ ۚ قُلْ هَاتُوا۟ بُرْهَـٰنَكُمْ إِن كُنتُمْ صَـٰدِقِينَ۝٦٤

    Amman yabdao alkhalqa thumma yuʿeeduhu waman yarzuqukum mina alssamai waalardi ailahun maʿa Allahi qul hatoo burhanakum in kuntum sadiqeena

    Kõ wãne ne yake fã ra halitta sa'an nan kuma ya mayar da ita, kuma Wãne ne Ya azurta ku daga sama da ƙasa? Ashe, akwai wani abin bautãwa tãre da Allah? Ka ce: "Ku kãwo dalĩlinku idan kun kasance mãsu gaskiya."

  65. قُل لَّا يَعْلَمُ مَن فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ٱلْغَيْبَ إِلَّا ٱللَّهُ ۚ وَمَا يَشْعُرُونَ أَيَّانَ يُبْعَثُونَ۝٦٥

    Qul la yaʿlamu man fee alssamawati waalardi alghayba illa Allahu wama yashʿuroona ayyana yubʿathoona

    Ka ce: "Bãbu wanda ya san gaibi a cikin sammai da ƙasa fãce Allah. Kuma bã su sansancẽwar a yaushe ne zã a tãyar da su."

  66. بَلِ ٱدَّٰرَكَ عِلْمُهُمْ فِى ٱلْـَٔاخِرَةِ ۚ بَلْ هُمْ فِى شَكٍّ مِّنْهَا ۖ بَلْ هُم مِّنْهَا عَمُونَ۝٦٦

    Bali iddaraka ʿilmuhum fee alakhirati bal hum fee shakkin minha bal hum minha ʿamoona

    Ã'a, saninsu ya kai a cikin Lãhira Ã'a, sunã cikin shakka daga gare ta. Ã'a, sũ da gare ta makãfin zũci ne.

  67. وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓا۟ أَءِذَا كُنَّا تُرَٰبًا وَءَابَآؤُنَآ أَئِنَّا لَمُخْرَجُونَ۝٦٧

    Waqala allatheena kafaroo aitha kunna turaban waabaona ainna lamukhrajoona

    Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Shin idan mun kasance turɓaya, mu da ubanninmu, shin, haƙĩƙa, waɗanda ake fitarwa ne?"

  68. لَقَدْ وُعِدْنَا هَـٰذَا نَحْنُ وَءَابَآؤُنَا مِن قَبْلُ إِنْ هَـٰذَآ إِلَّآ أَسَـٰطِيرُ ٱلْأَوَّلِينَ۝٦٨

    Laqad wuʿidna hatha nahnu waabaona min qablu in hatha illa asateeru alawwaleena

    "Lalle ne, haƙĩƙa, an yi mana wa'adi ga wannan, mũ da ubanninmu, daga gabãnin haka. Wannan bã kõme ba ne fãce tãtsũniyõyin farko."

  69. قُلْ سِيرُوا۟ فِى ٱلْأَرْضِ فَٱنظُرُوا۟ كَيْفَ كَانَ عَـٰقِبَةُ ٱلْمُجْرِمِينَ۝٦٩

    Qul seeroo fee alardi faonthuroo kayfa kana ʿaqibatu almujrimeena

    Ka ce: "Ku yi tafiya a cikin ƙasa, sa'an nan ku dũba, yãya ãƙibar mãsu laifi take?"

  70. وَلَا تَحْزَنْ عَلَيْهِمْ وَلَا تَكُن فِى ضَيْقٍ مِّمَّا يَمْكُرُونَ۝٧٠

    Wala tahzan ʿalayhim wala takun fee dayqin mimma yamkuroona

    Kuma kada ka yi baƙin ciki a kansu, kuma kada ka kasance a cikin ƙuncin rai daga abin da suke ƙullãwa na mãkirci.

  71. وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هَـٰذَا ٱلْوَعْدُ إِن كُنتُمْ صَـٰدِقِينَ۝٧١

    Wayaqooloona mata hatha alwaʿdu in kuntum sadiqeena

    Kuma sunã cẽwa, "A yaushe wannan wa'adi (zai auku), idan kun kasance mãsu gaskiya?"

  72. قُلْ عَسَىٰٓ أَن يَكُونَ رَدِفَ لَكُم بَعْضُ ٱلَّذِى تَسْتَعْجِلُونَ۝٧٢

    Qul ʿasa an yakoona radifa lakum baʿdu allathee tastaʿjiloona

    Ka ce: "Akwai fatan sãshen abin da kuke, nẽman gaggãwarsa, ya kasance yã kuturta1 a gare ku."

    Bayanai
    [1] Kuturi, shi ne a bãyan wani ya hau dabba ya kuma aza wani a kanta daga bãya gare shi. Kinaya ce na cewa abin yanã kusa gare su ƙwarai, kamar tsakãnin ɗan kuturi da mahayin dabba.
  73. وَإِنَّ رَبَّكَ لَذُو فَضْلٍ عَلَى ٱلنَّاسِ وَلَـٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَشْكُرُونَ۝٧٣

    Wainna rabbaka lathoo fadlin ʿala alnnasi walakinna aktharahum la yashkuroona

    Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa Mai falala ne a kanmutãne kuma amma mafi yawansu, bã su gõdẽwa.

  74. وَإِنَّ رَبَّكَ لَيَعْلَمُ مَا تُكِنُّ صُدُورُهُمْ وَمَا يُعْلِنُونَ۝٧٤

    Wainna rabbaka layaʿlamu ma tukinnu sudooruhum wama yuʿlinoona

    Kuma lalle Ubangijinka, haƙĩƙa Yanã sanin abin da ƙirãzansu suke, ɓõyẽwa, da abin da suke hayyanãwa.

  75. وَمَا مِنْ غَآئِبَةٍ فِى ٱلسَّمَآءِ وَٱلْأَرْضِ إِلَّا فِى كِتَـٰبٍ مُّبِينٍ۝٧٥

    Wama min ghaibatin fee alssamai waalardi illa fee kitabin mubeenin

    Kuma bãbu wata (mas'ala) mai bõyuwa, a cikin sama da ƙasa fãce tanã a cikin littafi bayyananne.

  76. إِنَّ هَـٰذَا ٱلْقُرْءَانَ يَقُصُّ عَلَىٰ بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ أَكْثَرَ ٱلَّذِى هُمْ فِيهِ يَخْتَلِفُونَ۝٧٦

    Inna hatha alqurana yaqussu ʿala banee israeela akthara allathee hum feehi yakhtalifoona

    Lalle ne wannan Alƙur'ãni1 yanã gaya wa Banĩ Isrãĩla mafi yawan abin da sũ suke sãɓa wa jũnansu a ciki.

    Bayanai
    [1] Idan wannan Alƙur'ani ya ƙunsã ilmin asĩrai da yake iya gaya wa Banĩ Israĩla mafi yawan abin da sũ da kansu, suke sãɓã wa jũna a kansu, tãre da shahararsu da ilmi, da yawan Annabãwan da suka wuce a cikinsu, to, ga Lãrabãwa jãhilai hiyãka ke nan. Bãbu abin da ya wajaba a gare su, sai sallamawa ga abin da yake kiran zuwa gare shi. In abin da yake faɗa ba gaskiya ba ne, dã Banĩ Isrãĩla ne farkon mãsu nũna ƙaryarsa. Ammã ba su yi ba. Sabõda haka duka gaskiya ne. Sai kõwa ya bĩ shi ya tsĩra.
  77. وَإِنَّهُۥ لَهُدًى وَرَحْمَةٌ لِّلْمُؤْمِنِينَ۝٧٧

    Wainnahu lahudan warahmatun lilmumineena

    Kuma lalle shi haƙĩƙa shiriya ce da rahama ga mũminai.

  78. إِنَّ رَبَّكَ يَقْضِى بَيْنَهُم بِحُكْمِهِۦ ۚ وَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلْعَلِيمُ۝٧٨

    Inna rabbaka yaqdee baynahum bihukmihi wahuwa alʿazeezu alʿaleemu

    "Lalle Ubangijinka Yanã yin hukunci a tsakãninsu da hukuncinsa, kuma Shi ne Mabuwãyi, Masani."

  79. فَتَوَكَّلْ عَلَى ٱللَّهِ ۖ إِنَّكَ عَلَى ٱلْحَقِّ ٱلْمُبِينِ۝٧٩

    Fatawakkal ʿala Allahi innaka ʿala alhaqqi almubeeni

    Sabõda haka, ka dõgara ga Allah, lalle ne, kai ne a kan gaskiya bayyananniya.

  80. إِنَّكَ لَا تُسْمِعُ ٱلْمَوْتَىٰ وَلَا تُسْمِعُ ٱلصُّمَّ ٱلدُّعَآءَ إِذَا وَلَّوْا۟ مُدْبِرِينَ۝٨٠

    Innaka la tusmiʿu almawta wala tusmiʿu alssumma aldduʿaa itha wallaw mudbireena

    Lalle ne kai, bã ka jiyar da matattu, kuma bã ka sa kurãme su ji kiranka, idan sun jũya sunã mãsu bãyar da bãya.

  81. وَمَآ أَنتَ بِهَـٰدِى ٱلْعُمْىِ عَن ضَلَـٰلَتِهِمْ ۖ إِن تُسْمِعُ إِلَّا مَن يُؤْمِنُ بِـَٔايَـٰتِنَا فَهُم مُّسْلِمُونَ۝٨١

    Wama anta bihadee alʿumyi ʿan dalalatihim in tusmiʿu illa man yuminu biayatina fahum muslimoona

    Kuma kai ba ka zama mai shiryar da ɗimammu daga ɓata ba. Bã ka jiyarwa fãce wanda yake yin ĩmãni da ãyõyin Mu. To, sũ ne mãsu sallamãwa (al'amari zuwa ga Allah).

  82. ۞ وَإِذَا وَقَعَ ٱلْقَوْلُ عَلَيْهِمْ أَخْرَجْنَا لَهُمْ دَآبَّةً مِّنَ ٱلْأَرْضِ تُكَلِّمُهُمْ أَنَّ ٱلنَّاسَ كَانُوا۟ بِـَٔايَـٰتِنَا لَا يُوقِنُونَ۝٨٢

    Waitha waqaʿa alqawlu ʿalayhim akhrajna lahum dabbatan mina alardi tukallimuhum anna alnnasa kanoo biayatina la yooqinoona

    Kuma idan magana ta auku a kansu, Munã fitar musu da wata dabba1 daga ƙasa, tanã yi musu magana, cẽwa "Lalle mutãne sun kasance game da ayoyin Mu, ba su yin ĩmãnin yaƙĩni."

    Bayanai
    [1] Wata dabba ce anã kiranta Jassãsa an ce 'yar rãƙumar Sãlihu ce a lõkacin da aka kashe uwarta, ta gudu, ta shiga cikin dũtse' dũtsen ya rufe da ita. Tanã fitõwa daga dũtsen Safa a Makka da hantsi. Bãyan fitõwarta, bãbu sauran wa'azi. Mũmini ya tabbata mũmini kãfiri kuma ya tabbata haka. Tanã riƙe da sandar Mũsã da Hãtimin Sulaimãn. Tana fitõwa a bãyan fitõwar rãnã daga yamma. Allah ɗai Ya san gaskiyar yadda take.
  83. وَيَوْمَ نَحْشُرُ مِن كُلِّ أُمَّةٍ فَوْجًا مِّمَّن يُكَذِّبُ بِـَٔايَـٰتِنَا فَهُمْ يُوزَعُونَ۝٨٣

    Wayawma nahshuru min kulli ommatin fawjan mimman yukaththibu biayatina fahum yoozaʿoona

    Kuma a rãnar da Muke tãrãwa daga kõwace al'umma, wata ƙungiya daga waɗanda suke ƙaryata ãyõyin Mu, sai ga su anã kangesu. (ga kõra)

  84. حَتَّىٰٓ إِذَا جَآءُو قَالَ أَكَذَّبْتُم بِـَٔايَـٰتِى وَلَمْ تُحِيطُوا۟ بِهَا عِلْمًا أَمَّاذَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ۝٨٤

    Hatta itha jaoo qala akaththabtum biayatee walam tuheetoo biha ʿilman ammatha kuntum taʿmaloona

    Har idan sun zo, (Allah) zai ce, "Ashe kun ƙaryata ãyõyinNa, kuma ba ku kẽwaye su da sani ba? To, mẽne ne kuka kasance kunã aikatãwa?"

  85. وَوَقَعَ ٱلْقَوْلُ عَلَيْهِم بِمَا ظَلَمُوا۟ فَهُمْ لَا يَنطِقُونَ۝٨٥

    Wawaqaʿa alqawlu ʿalayhim bima thalamoo fahum la yantiqoona

    Kuma magana ta auku a kansu, sabõda zãluncin da suka yi. To, sũ bã su da ta cẽwa.

  86. أَلَمْ يَرَوْا۟ أَنَّا جَعَلْنَا ٱلَّيْلَ لِيَسْكُنُوا۟ فِيهِ وَٱلنَّهَارَ مُبْصِرًا ۚ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَـٰتٍ لِّقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ۝٨٦

    Alam yaraw anna jaʿalna allayla liyaskunoo feehi waalnnahara mubsiran inna fee thalika laayatin liqawmin yuminoona

    Shin, ba su gani ba, cẽwa, lalle Mũ, Mun sanya dare dõmin su natsu a cikinsa, kuma da yini mai sanya gani? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi! Dõmin mutãne waɗanda suka yi ĩmãni.

  87. وَيَوْمَ يُنفَخُ فِى ٱلصُّورِ فَفَزِعَ مَن فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَمَن فِى ٱلْأَرْضِ إِلَّا مَن شَآءَ ٱللَّهُ ۚ وَكُلٌّ أَتَوْهُ دَٰخِرِينَ۝٨٧

    Wayawma yunfakhu fee alssoori fafaziʿa man fee alssamawati waman fee alardi illa man shaa Allahu wakullun atawhu dakhireena

    Kuma da rãnar1 da ake hũsa a cikin ƙaho, sai wandayake a cikin sammai da waɗanda suke a cikin ƙasa su firgita, fãce wanda Allah Ya so, kuma dukansu, su je Masa sunã ƙasƙantattu.

    Bayanai
    [1] Bãyan fitõwar dabba, kuma sai bũsar ƙahõ na farkõ, sa'an nan na biyu sa'an nan Ƙiyãma.
  88. وَتَرَى ٱلْجِبَالَ تَحْسَبُهَا جَامِدَةً وَهِىَ تَمُرُّ مَرَّ ٱلسَّحَابِ ۚ صُنْعَ ٱللَّهِ ٱلَّذِىٓ أَتْقَنَ كُلَّ شَىْءٍ ۚ إِنَّهُۥ خَبِيرٌۢ بِمَا تَفْعَلُونَ۝٨٨

    Watara aljibala tahsabuha jamidatan wahiya tamurru marra alssahabi sunʿa Allahi allathee atqana kulla shayin innahu khabeerun bima tafʿaloona

    Kuma kanã ganin duwãtsu, kanã zaton su sandararru, alhãli kuwa sũ sunã shũɗẽwa shũɗewar girgije, bisa sanã'ar Allah wanda Ya kyautata kõwane abu. Lalle Shi, Mai lãbartãwa ne game da abin da kuke aikatãwa.

  89. مَن جَآءَ بِٱلْحَسَنَةِ فَلَهُۥ خَيْرٌ مِّنْهَا وَهُم مِّن فَزَعٍ يَوْمَئِذٍ ءَامِنُونَ۝٨٩

    Man jaa bialhasanati falahu khayrun minha wahum min fazaʿin yawmaithin aminoona

    Wanda ya zo da kyakkyawan aiki guda, to, yanã da mafi alhẽri daga gare shi. Kuma sũ daga wata firgita,1 a yinin nan, amintattu ne.

    Bayanai
    [1] Firgita daga azãbar Lãhira, wannan firgita ba irin ta farko ba ce wadda aka ambata a cikin ãyã ta 87, dõmin wancan firgitar kwarjini ce a bãyan tãshi daga kaburbura.
  90. وَمَن جَآءَ بِٱلسَّيِّئَةِ فَكُبَّتْ وُجُوهُهُمْ فِى ٱلنَّارِ هَلْ تُجْزَوْنَ إِلَّا مَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ۝٩٠

    Waman jaa bialssayyiati fakubbat wujoohuhum fee alnnari hal tujzawna illa ma kuntum taʿmaloona

    Kuma wanda ya zo da mugun aiki, to, an kife fuskõkinsu a cikin wuta. Ko zã a sãka muku fãce da abin da kuka kasance kũnã aikatãwa?

  91. إِنَّمَآ أُمِرْتُ أَنْ أَعْبُدَ رَبَّ هَـٰذِهِ ٱلْبَلْدَةِ ٱلَّذِى حَرَّمَهَا وَلَهُۥ كُلُّ شَىْءٍ ۖ وَأُمِرْتُ أَنْ أَكُونَ مِنَ ٱلْمُسْلِمِينَ۝٩١

    Innama omirtu an aʿbuda rabba hathihi albaldati allathee harramaha walahu kullu shayin waomirtu an akoona mina almuslimeena

    (Ka ce): "An umurce ni, in bauta wa Ubangijin wannan Gari,1 Wanda Ya mayar da shi Hurumi, kuma Yanã da dukan kõme. Kuma an umurce ni da in kasance daga mãsu sallamãwa."

    Bayanai
    [1] Wannan Gari shĩ ne Makka. Sanya Makka hurumi ba a iya shiga cikinsa da yãki yanã a cikin ashĩrai na Allah. Shiryuwa da ɓata duka asĩrai ne na Allah. Tsãrin Alƙur'ani da abubuwan da ya ƙunsa duka asĩran Allah ne.
  92. وَأَنْ أَتْلُوَا۟ ٱلْقُرْءَانَ ۖ فَمَنِ ٱهْتَدَىٰ فَإِنَّمَا يَهْتَدِى لِنَفْسِهِۦ ۖ وَمَن ضَلَّ فَقُلْ إِنَّمَآ أَنَا۠ مِنَ ٱلْمُنذِرِينَ۝٩٢

    Waan atluwa alqurana famani ihtada fainnama yahtadee linafsihi waman dalla faqul innama ana mina almunthireena

    "Kuma inã karanta Alƙur'ãni." To, wanda ya shiryu, yã shiryu ne dõmin kansa kawai. Kuma wanda ya ɓãce, to, ka ce: "Ni daga mãsu gargaɗi kawai nake."

  93. وَقُلِ ٱلْحَمْدُ لِلَّهِ سَيُرِيكُمْ ءَايَـٰتِهِۦ فَتَعْرِفُونَهَا ۚ وَمَا رَبُّكَ بِغَـٰفِلٍ عَمَّا تَعْمَلُونَ۝٩٣

    Waquli alhamdu lillahi sayureekum ayatihi fataʿrifoonaha wama rabbuka bighafilin ʿamma taʿmaloona

    Kuma ka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah. Zai nũna muku ãyõyin Sa, har ku sansu." Kuma Ubangijinka bai zama Mai shagala daga barin abin da kuke aikatãwa ba.

Tambayoyin da ake yawan yi

Mece ce ma’anar sunan Suratul Naml?

Ma’anar Naml ita ce “Tururuwa”.

Suratul Naml tana cikin juz’i na nawa?

Suratul Naml tana cikin juz’i na 19 da 20.

Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Naml?

Suratul Naml tana da ayoyi 93.

Suratul Naml Makkiya ce ko Madaniya?

Suratul Naml sura ce Makkiya.

Suratul Naml ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?

Ita ce sura ta 27 a cikin Alƙur’ani.

Majiyoyi

  • Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
  • Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
  • Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
  • Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
  • Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
  • Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.

Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.

Saitunan karatu

Rubutun Alƙur’ani
Girman Larabci
100%
Girman fassara
100%
Kamanni

Ƙara zuwa Allon Gida

ReadSurahBuɗe ReadSurah daga allon gida, a cikakken allo. Surorin da kuka karanta suna buɗewa ko da babu intanet.

  1. A cikin Safari, taɓa maɓallin “Share”. A sababbin iPhone yana cikin menu na •••.
  2. Taɓa “Add to Home Screen”. Gungura ƙasa idan ba ku gan shi ba.
  3. Taɓa “Add”.