سورة الإسراء
Suratul Isra’i da fassarar Hausa
Tafiyar dare
- 17
- ayoyi 111
- Makkiya
- Juz’i 15
- Shafuka 282–293
Suratul Isra’i (الإسراء) ita ce sura ta 17 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 111. Ma’anar sunanta ita ce “Tafiyar dare”. Sura ce Makkiya, wadda ta sauka a Makka kafin Hijira, kuma tana cikin juz’i na 15.
A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Isra’i gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.
Suratul Isra’i cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ
-
سُبْحَـٰنَ ٱلَّذِىٓ أَسْرَىٰ بِعَبْدِهِۦ لَيْلًا مِّنَ ٱلْمَسْجِدِ ٱلْحَرَامِ إِلَى ٱلْمَسْجِدِ ٱلْأَقْصَا ٱلَّذِى بَـٰرَكْنَا حَوْلَهُۥ لِنُرِيَهُۥ مِنْ ءَايَـٰتِنَآ ۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلْبَصِيرُ١
Subhana allathee asra biʿabdihi laylan mina almasjidi alharami ila almasjidi alaqsa allathee barakna hawlahu linuriyahu min ayatina innahu huwa alssameeʿu albaseeru
Tsarki ya tabbata ga wanda Ya yi tafiyar dare1 da bãwanSa da dare daga Masallaci mai alfarma zuwa ga Masallaci mafi nĩsa2 wanda Muka sanya albarka a gefensa dõmin Mu nũna masa daga ãyõyinMu. Lalle ne Shi shĩ ne Mai ji, Mai gani.
Bayanai
[1] Isrã'i, shi ne tafiyar dare da Allah Ya yi da Annabi daga Makka zuwa Baitil Maƙadis. Sa'an nan Mi'iraji zuwa sama inda aka ba shi sallõli. [2] Muƙarana a tsakãnin Masjidil Harãm watau tsararre daga a yãki mutãnensa da Masjidil Aƙsã wanda ba tsararre ba. Isrã'i da Mi'irãji sun fi Miƙãtin Mũsã da gãnãwarsa da Ubangiji a Ɗũr-Sĩna'a. -
وَءَاتَيْنَا مُوسَى ٱلْكِتَـٰبَ وَجَعَلْنَـٰهُ هُدًى لِّبَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ أَلَّا تَتَّخِذُوا۟ مِن دُونِى وَكِيلًا٢
Waatayna moosa alkitaba wajaʿalnahu hudan libanee israeela alla tattakhithoo min doonee wakeelan
Kuma Mun bai wa Mũsã1 littafi, kuma Mun sanya shi shiriya ga Banĩ Isrã'ila, cẽwa kada ku riƙi wani wakĩli baici Na.
Bayanai
[1] Tsakãnin Bãwan Allah Muhammadu da Mũsã, kuma an aiko Mũsã ga Banĩ Isrã'ila kawai, kuma Nũhu an ce masa bãwa amma ba a jingina shi kamar yadda aka jingina bawanSa ba. Sa'an nan kuma Jingina Yahũdu ga Nũhu ya daidaita su da sauran mutãne wajen da'awar ɗaukaka da nasaba. -
ذُرِّيَّةَ مَنْ حَمَلْنَا مَعَ نُوحٍ ۚ إِنَّهُۥ كَانَ عَبْدًا شَكُورًا٣
Thurriyyata man hamalna maʿa noohin innahu kana ʿabdan shakooran
Zuriyar waɗanda Muka ɗauka tãre da Nũhu. Lalle ne shi ya kasance wani bãwa mai gõdiya.
-
وَقَضَيْنَآ إِلَىٰ بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ فِى ٱلْكِتَـٰبِ لَتُفْسِدُنَّ فِى ٱلْأَرْضِ مَرَّتَيْنِ وَلَتَعْلُنَّ عُلُوًّا كَبِيرًا٤
Waqadayna ila banee israeela fee alkitabi latufsidunna fee alardi marratayni walataʿlunna ʿuluwwan kabeeran
Kuma Mun hukunta zuwa ga Bani Isrã'ĩla a cikin Littãfi, cewa lalle ne, kunã yin ɓarna a cikin ƙasa sau biyu, kuma lalle ne kunã zãlunci, zãlunci mai girma.
-
فَإِذَا جَآءَ وَعْدُ أُولَىٰهُمَا بَعَثْنَا عَلَيْكُمْ عِبَادًا لَّنَآ أُو۟لِى بَأْسٍ شَدِيدٍ فَجَاسُوا۟ خِلَـٰلَ ٱلدِّيَارِ ۚ وَكَانَ وَعْدًا مَّفْعُولًا٥
Faitha jaa waʿdu oolahuma baʿathna ʿalaykum ʿibadan lana olee basin shadeedin fajasoo khilala alddiyari wakana waʿdan mafʿoolan
To idan wa'adin na farkonsu yajẽ, za Mu aika, a kanku waɗansu bãyi1 Nãmu, ma'abũta yãƙi mafĩ tsanani, har su yi yãwo a tsakãnin gidãjenku, kuma yã zama wa'adi abin aikatawa.
Bayanai
[1] Sun yi fasãdi da barin aiki da Taurãti, sabõda haka aka aika Jãlũta a kansu. Ya kashe su kuma ya kãma zuriyarsu. -
ثُمَّ رَدَدْنَا لَكُمُ ٱلْكَرَّةَ عَلَيْهِمْ وَأَمْدَدْنَـٰكُم بِأَمْوَٰلٍ وَبَنِينَ وَجَعَلْنَـٰكُمْ أَكْثَرَ نَفِيرًا٦
Thumma radadna lakumu alkarrata ʿalayhim waamdadnakum biamwalin wabaneena wajaʿalnakum akthara nafeeran
Sa'an nan kuma Mu nwayar da ɗauki a gare ku a kansu, kuma Mu taimake ku da dũkiyõyi da ɗiya kuma Mu sanya ku mafiya yawan mãsu fita yãƙi.
-
إِنْ أَحْسَنتُمْ أَحْسَنتُمْ لِأَنفُسِكُمْ ۖ وَإِنْ أَسَأْتُمْ فَلَهَا ۚ فَإِذَا جَآءَ وَعْدُ ٱلْـَٔاخِرَةِ لِيَسُـۥٓـُٔوا۟ وُجُوهَكُمْ وَلِيَدْخُلُوا۟ ٱلْمَسْجِدَ كَمَا دَخَلُوهُ أَوَّلَ مَرَّةٍ وَلِيُتَبِّرُوا۟ مَا عَلَوْا۟ تَتْبِيرًا٧
In ahsantum ahsantum lianfusikum wain asatum falaha faitha jaa waʿdu alakhirati liyasoooo wujoohakum waliyadkhuloo almasjida kama dakhaloohu awwala marratin waliyutabbiroo ma ʿalaw tatbeeran
Idan kun kyautata, kun kyautata dõmin kanku, kuma idan kun mũnana to dõmĩnsu. Sa'an nan idan wa'adin na ƙarshe1 ya jẽ, (za su je) dõmin su baƙanta fuskokinku, kuma su shiga masallaci kamar yadda suka shige shi a farkon lõkaci, kuma dõmin su halakar da abin da suka rinjaya a kansa, halakarwa.
Bayanai
[1] Suka yi fasãdi marra ta biyu da kashe Zakariyya da Yahaya, sai aka aika musu da Bukht Nasar daga Bãbila ya karkashe su, kuma ya kãma zuriyarsu, kuma ya rũshe Baitil Maƙadis. Waɗannan lãbaru biyu na ɓarnar Banĩ Isrã'ila sunã cikin bãyar da lãbaru ga gaibi. Idan an daidaita su da lãbarun gaibi waɗanda Alƙur'ãni ya faɗã, waɗansu suka auku kuma waɗansu sunã ta aukuwa zã a san falalar Alƙur'ãni a kan Taurãti kamar yadda ya bayyana cewa Attaura ta yi kira zuwa ga tauhidi da shiriya, sa'an nan ya bayyana abũbuwan da Alƙur'ãnĩ yake karantarwa daga ãyã ta 9 zuwa ga ãyã ta 38 inda ya tãra hãlãyen ƙwarai kuma ya kõre mũnãna. -
عَسَىٰ رَبُّكُمْ أَن يَرْحَمَكُمْ ۚ وَإِنْ عُدتُّمْ عُدْنَا ۘ وَجَعَلْنَا جَهَنَّمَ لِلْكَـٰفِرِينَ حَصِيرًا٨
ʿAsa rabbukum an yarhamakum wain ʿudtum ʿudna wajaʿalna jahannama lilkafireena haseeran
Akwai tsammãnin Ubangijinku Ya yi muku rahama. Kuma idan kun sãke Mu sãke. Kuma Mun sanya Jahannama matsara ga kãfirai.
-
إِنَّ هَـٰذَا ٱلْقُرْءَانَ يَهْدِى لِلَّتِى هِىَ أَقْوَمُ وَيُبَشِّرُ ٱلْمُؤْمِنِينَ ٱلَّذِينَ يَعْمَلُونَ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ أَنَّ لَهُمْ أَجْرًا كَبِيرًا٩
Inna hatha alqurana yahdee lillatee hiya aqwamu wayubashshiru almumineena allatheena yaʿmaloona alssalihati anna lahum ajran kabeeran
Lalle ne wannan Alƙur'ãni yanã shiryarwa ga (hãlayen) waɗanda suke mafi daidaita1 kuma yanã bãyar da bushãra ga mũminai waɗanda suke aikata ayyuka na ƙwarai (cẽwa) "Lalle ne sunã da wata ijãra. mai girma."
Bayanai
[1] Bãyan ya faɗi abũbuwan da Attaura ta karantar, ya ce: "Alƙur'ãni yanã shiryarwa zuwa ga hãlãyen da suka fi daidaita daga abin da Attaura ta karantar." Sa'an nan ya ci gaba da bayãnin abũbuwan da Alƙur'ãni yake karantarwa. -
وَأَنَّ ٱلَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِٱلْـَٔاخِرَةِ أَعْتَدْنَا لَهُمْ عَذَابًا أَلِيمًا١٠
Waanna allatheena la yuminoona bialakhirati aʿtadna lahum ʿathaban aleeman
Kuma lalle ne, waɗanda ba su yin ĩmãni da Lãhira, Mun yimusu tattalin wata azãba mai raɗaɗi.
-
وَيَدْعُ ٱلْإِنسَـٰنُ بِٱلشَّرِّ دُعَآءَهُۥ بِٱلْخَيْرِ ۖ وَكَانَ ٱلْإِنسَـٰنُ عَجُولًا١١
Wayadʿu alinsanu bialshsharri duʿaahu bialkhayri wakana alinsanu ʿajoolan
Kuma mutum yanã1 yin addu'a da sharri kamar addu'arsa da alhẽri, kuma mutum ya kasance mai gaggãwa.
Bayanai
[1] Alƙur'ani yanã shiryar da mutum har ga yadda yake yin addu'a dõmin kada ya yi wa kansa addu'a ta sharri alhãli kuwa yanã nufin ya yi alhħri dõmin an halicci mutum da son gaggãwa. -
وَجَعَلْنَا ٱلَّيْلَ وَٱلنَّهَارَ ءَايَتَيْنِ ۖ فَمَحَوْنَآ ءَايَةَ ٱلَّيْلِ وَجَعَلْنَآ ءَايَةَ ٱلنَّهَارِ مُبْصِرَةً لِّتَبْتَغُوا۟ فَضْلًا مِّن رَّبِّكُمْ وَلِتَعْلَمُوا۟ عَدَدَ ٱلسِّنِينَ وَٱلْحِسَابَ ۚ وَكُلَّ شَىْءٍ فَصَّلْنَـٰهُ تَفْصِيلًا١٢
Wajaʿalna allayla waalnnahara ayatayni famahawna ayata allayli wajaʿalna ayata alnnahari mubsiratan litabtaghoo fadlan min rabbikum walitaʿlamoo ʿadada alssineena waalhisaba wakulla shayin fassalnahu tafseelan
Kuma Mun sanya dare da rãna, ãyõyi biyu, sa'an nan Muka shãfe ãyar dare, kuma Muka sanya ãyar rãna mai sanyãwa a yi gani, dõmin ku nẽmi falala daga Ubangijinku, kuma dõmin ku san ƙidãyar shẽkara da lissafi. Kuma dukan kõme Mun bayyana shi daki-dakin bayyanãwa.
-
وَكُلَّ إِنسَـٰنٍ أَلْزَمْنَـٰهُ طَـٰٓئِرَهُۥ فِى عُنُقِهِۦ ۖ وَنُخْرِجُ لَهُۥ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ كِتَـٰبًا يَلْقَىٰهُ مَنشُورًا١٣
Wakulla insanin alzamnahu tairahu fee ʿunuqihi wanukhriju lahu yawma alqiyamati kitaban yalqahu manshooran
Kuma kõwane mutum Mun lazimta masa abin rekõdinsa a cikin wuyansa, kuma Mu fitar masa a Rãnar ¡iyãma da littãfi wanda zai haɗu da shi buɗaɗɗe.
-
ٱقْرَأْ كِتَـٰبَكَ كَفَىٰ بِنَفْسِكَ ٱلْيَوْمَ عَلَيْكَ حَسِيبًا١٤
Iqra kitabaka kafa binafsika alyawma ʿalayka haseeban
"Karanta Littãfinka. Ranka ya isa ya zama mai hisãbi a kanka a yau."
-
مَّنِ ٱهْتَدَىٰ فَإِنَّمَا يَهْتَدِى لِنَفْسِهِۦ ۖ وَمَن ضَلَّ فَإِنَّمَا يَضِلُّ عَلَيْهَا ۚ وَلَا تَزِرُ وَازِرَةٌ وِزْرَ أُخْرَىٰ ۗ وَمَا كُنَّا مُعَذِّبِينَ حَتَّىٰ نَبْعَثَ رَسُولًا١٥
Mani ihtada fainnama yahtadee linafsihi waman dalla fainnama yadillu ʿalayha wala taziru waziratun wizra okhra wama kunna muʿaththibeena hatta nabʿatha rasoolan
Wanda ya nẽmi shiryuwa, to, ya nẽmi shiryuwa ne dõminkansa kawai kuma wanda ya ɓace, to, ya ɓace ne a kansa kawai kuma rai mai ɗaukar nauyi bã ya ɗaukar nauyin wani ran, kuma ba Mu zama mãsu yin azãba ba, sai Mun aika wani Manzo.
-
وَإِذَآ أَرَدْنَآ أَن نُّهْلِكَ قَرْيَةً أَمَرْنَا مُتْرَفِيهَا فَفَسَقُوا۟ فِيهَا فَحَقَّ عَلَيْهَا ٱلْقَوْلُ فَدَمَّرْنَـٰهَا تَدْمِيرًا١٦
Waitha aradna an nuhlika qaryatan amarna mutrafeeha fafasaqoo feeha fahaqqa ʿalayha alqawlu fadammarnaha tadmeeran
Kuma idan Mun yi nufin Mu halakar da wata alƙarya, sai Mu umurci mawadãtanta, har su yi fasadi a cikinta, sa'an nan maganar azãba ta wajaba a kanta, sa'an nan Mu darkãke ta, darkãkẽwa.
-
وَكَمْ أَهْلَكْنَا مِنَ ٱلْقُرُونِ مِنۢ بَعْدِ نُوحٍ ۗ وَكَفَىٰ بِرَبِّكَ بِذُنُوبِ عِبَادِهِۦ خَبِيرًۢا بَصِيرًا١٧
Wakam ahlakna mina alqurooni min baʿdi noohin wakafa birabbika bithunoobi ʿibadihi khabeeran baseeran
Kuma da yawa Muka halakar da al'ummomi a bãyan Nũhu. Kuma Ubangijinka Ya isa ya zama Mai ƙididdigewa ga zunubban bãyinSa, Mai gani.
-
مَّن كَانَ يُرِيدُ ٱلْعَاجِلَةَ عَجَّلْنَا لَهُۥ فِيهَا مَا نَشَآءُ لِمَن نُّرِيدُ ثُمَّ جَعَلْنَا لَهُۥ جَهَنَّمَ يَصْلَىٰهَا مَذْمُومًا مَّدْحُورًا١٨
Man kana yureedu alʿajilata ʿajjalna lahu feeha ma nashao liman nureedu thumma jaʿalna lahu jahannama yaslaha mathmooman madhooran
Wanda ya kasance yanã nufin mai gaggãwa, sai Mu gaggauta masa a cikinta, abin da Muke so ga wanda Muke nufi, sa'an nan kuma Mu sanya masa Jahannama, ya ƙõnu da ita, yanã abin zargi kuma abin tunkuɗewa.
-
وَمَنْ أَرَادَ ٱلْـَٔاخِرَةَ وَسَعَىٰ لَهَا سَعْيَهَا وَهُوَ مُؤْمِنٌ فَأُو۟لَـٰٓئِكَ كَانَ سَعْيُهُم مَّشْكُورًا١٩
Waman arada alakhirata wasaʿa laha saʿyaha wahuwa muminun faolaika kana saʿyuhum mashkooran
Kuma wanda ya nufi Lãhira, kuma ya yi aiki sabõda ita irin aikinta alhãli kuwa yanã mũmĩni, to, waɗannan aikinsu ya kasance gõdadde.
-
كُلًّا نُّمِدُّ هَـٰٓؤُلَآءِ وَهَـٰٓؤُلَآءِ مِنْ عَطَآءِ رَبِّكَ ۚ وَمَا كَانَ عَطَآءُ رَبِّكَ مَحْظُورًا٢٠
Kullan numiddu haolai wahaolai min ʿatai rabbika wama kana ʿatao rabbika mahthooran
Dukkansu Munã taimakon waɗannan da waɗancan daga kyautar Ubangijinka, kuma kyautar Ubangijinka ba ta kasance hananna ba.
-
ٱنظُرْ كَيْفَ فَضَّلْنَا بَعْضَهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ ۚ وَلَلْـَٔاخِرَةُ أَكْبَرُ دَرَجَـٰتٍ وَأَكْبَرُ تَفْضِيلًا٢١
Onthur kayfa faddalna baʿdahum ʿala baʿdin walalakhiratu akbaru darajatin waakbaru tafdeelan
Ka duba yadda Muka fĩfĩtar da sãshensu a kan sãshe! Kuma lalle ne Lãhira ce mafi girman darajõji, kuma mafi girman fĩfĩtãwa.
-
لَّا تَجْعَلْ مَعَ ٱللَّهِ إِلَـٰهًا ءَاخَرَ فَتَقْعُدَ مَذْمُومًا مَّخْذُولًا٢٢
La tajʿal maʿa Allahi ilahan akhara fataqʿuda mathmooman makhthoolan
Kada ka sanya wani abin bautawa na daban tãre da Allah har ka zauna kana abin zargi, yarɓaɓɓe.
-
۞ وَقَضَىٰ رَبُّكَ أَلَّا تَعْبُدُوٓا۟ إِلَّآ إِيَّاهُ وَبِٱلْوَٰلِدَيْنِ إِحْسَـٰنًا ۚ إِمَّا يَبْلُغَنَّ عِندَكَ ٱلْكِبَرَ أَحَدُهُمَآ أَوْ كِلَاهُمَا فَلَا تَقُل لَّهُمَآ أُفٍّ وَلَا تَنْهَرْهُمَا وَقُل لَّهُمَا قَوْلًا كَرِيمًا٢٣
Waqada rabbuka alla taʿbudoo illa iyyahu wabialwalidayni ihsanan imma yablughanna ʿindaka alkibara ahaduhuma aw kilahuma fala taqul lahuma offin wala tanharhuma waqul lahuma qawlan kareeman
Kuma Ubangijinka Ya hukunta kada ku bauta wa kõwa fãce Shi, kum game da mahaifa biyu ku kyautata kyautatawa, ko dai ɗayansu ya kai ga tsũfa a wurinka ko dukansu biyu, to, kada ka ce musu 'tir' kuma kada ka tsãwace su kuma ka faɗa musu magana mai karimci.
-
وَٱخْفِضْ لَهُمَا جَنَاحَ ٱلذُّلِّ مِنَ ٱلرَّحْمَةِ وَقُل رَّبِّ ٱرْحَمْهُمَا كَمَا رَبَّيَانِى صَغِيرًا٢٤
Waikhfid lahuma janaha alththulli mina alrrahmati waqul rabbi irhamhuma kama rabbayanee sagheeran
Kuma ka sassauta musu fikãfikan tausasãwa na rahama. Kuma ka ce: "Ya Ubangijina! Ka yi musu rahama, kamar yadda suka yi rẽnõna, ina ƙarami."
-
رَّبُّكُمْ أَعْلَمُ بِمَا فِى نُفُوسِكُمْ ۚ إِن تَكُونُوا۟ صَـٰلِحِينَ فَإِنَّهُۥ كَانَ لِلْأَوَّٰبِينَ غَفُورًا٢٥
Rabbukum aʿlamu bima fee nufoosikum in takoonoo saliheena fainnahu kana lilawwabeena ghafooran
Ubangijin ku ne Mafi sani ga abin da yake a cikin rãyukanku. Idan kun kasan ce sãlihai to lalle ne shĩ Ya kasance ga mãsu kõmawa gare Shi, Mai gãfara.
-
وَءَاتِ ذَا ٱلْقُرْبَىٰ حَقَّهُۥ وَٱلْمِسْكِينَ وَٱبْنَ ٱلسَّبِيلِ وَلَا تُبَذِّرْ تَبْذِيرًا٢٦
Waati tha alqurba haqqahu waalmiskeena waibna alssabeeli wala tubaththir tabtheeran
Kuma ka bai wa ma'abũcin zumunta hakkinsa1 da miskĩna da ɗan hanya. Kuma kada ka bazzara dũkiyar ka, bazzarãwa.
Bayanai
[1] Hakkin zumunta shi ne alheri da sãdar da zumunta. Hakkin miskini da ɗan hanya zakka da sadakar taɗawwa'i da liyãfar kwana uku ga bãƙo bisa al'ada da alheri, bã bisa ɓarna da kallafãwa ba. -
إِنَّ ٱلْمُبَذِّرِينَ كَانُوٓا۟ إِخْوَٰنَ ٱلشَّيَـٰطِينِ ۖ وَكَانَ ٱلشَّيْطَـٰنُ لِرَبِّهِۦ كَفُورًا٢٧
Inna almubaththireena kanoo ikhwana alshshayateeni wakana alshshaytanu lirabbihi kafooran
Lalle ne mubazzarai sun kasance 'yan'uwan shaiɗanu. Kuma Shaiɗan ya kasance ga Ubangijinsa, mai yawan kãfirci.
-
وَإِمَّا تُعْرِضَنَّ عَنْهُمُ ٱبْتِغَآءَ رَحْمَةٍ مِّن رَّبِّكَ تَرْجُوهَا فَقُل لَّهُمْ قَوْلًا مَّيْسُورًا٢٨
Waimma tuʿridanna ʿanhumu ibtighaa rahmatin min rabbika tarjooha faqul lahum qawlan maysooran
Ko dai ka kau da kai daga gare su dõmin nẽman rahama daga Ubangijinka, wadda kake fãtanta, to sai ka gaya musu magana mai laushi.
-
وَلَا تَجْعَلْ يَدَكَ مَغْلُولَةً إِلَىٰ عُنُقِكَ وَلَا تَبْسُطْهَا كُلَّ ٱلْبَسْطِ فَتَقْعُدَ مَلُومًا مَّحْسُورًا٢٩
Wala tajʿal yadaka maghloolatan ila ʿunuqika wala tabsutha kulla albasti fataqʿuda malooman mahsooran
Kuma kada ka sanya hannunka ƙuƙuntacce zuwa ga wuyanka, kuma kada ka shimfiɗa shi dukan shimfiɗãwa har ka zama abin zargi, wanda ake yanke wa.1
Bayanai
[1] Kada ka zama marõwaci a zarge ka, kuma kada ka zama almubazzari ka rasa mutãne, su yanke daga gare ka. -
إِنَّ رَبَّكَ يَبْسُطُ ٱلرِّزْقَ لِمَن يَشَآءُ وَيَقْدِرُ ۚ إِنَّهُۥ كَانَ بِعِبَادِهِۦ خَبِيرًۢا بَصِيرًا٣٠
Inna rabbaka yabsutu alrrizqa liman yashao wayaqdiru innahu kana biʿibadihi khabeeran baseeran
Lalle ne Ubangijinka Yanã shimfiɗa arzĩki ga wanda Yake so, kuma Yanã ƙuƙuntãwa. Lalle Shi, Yã kasance Mai sani ga bãyinSa, Mai gani.
-
وَلَا تَقْتُلُوٓا۟ أَوْلَـٰدَكُمْ خَشْيَةَ إِمْلَـٰقٍ ۖ نَّحْنُ نَرْزُقُهُمْ وَإِيَّاكُمْ ۚ إِنَّ قَتْلَهُمْ كَانَ خِطْـًٔا كَبِيرًا٣١
Wala taqtuloo awladakum khashyata imlaqin nahnu narzuquhum waiyyakum inna qatlahum kana khitan kabeeran
Kuma kada ku kashe 'yã'yanku dõmin tsõron talauci. Mu ne ke arzũta su, su da ku. Lalle ne kashe su yã kasance kuskure babba.
-
وَلَا تَقْرَبُوا۟ ٱلزِّنَىٰٓ ۖ إِنَّهُۥ كَانَ فَـٰحِشَةً وَسَآءَ سَبِيلًا٣٢
Wala taqraboo alzzina innahu kana fahishatan wasaa sabeelan
Kuma kada ku kusanci zina. Lalle ne ita ta kasance alfãsha ce kuma tã mũnãna ga zama hanya.
-
وَلَا تَقْتُلُوا۟ ٱلنَّفْسَ ٱلَّتِى حَرَّمَ ٱللَّهُ إِلَّا بِٱلْحَقِّ ۗ وَمَن قُتِلَ مَظْلُومًا فَقَدْ جَعَلْنَا لِوَلِيِّهِۦ سُلْطَـٰنًا فَلَا يُسْرِف فِّى ٱلْقَتْلِ ۖ إِنَّهُۥ كَانَ مَنصُورًا٣٣
Wala taqtuloo alnnafsa allatee harrama Allahu illa bialhaqqi waman qutila mathlooman faqad jaʿalna liwaliyyihi sultanan fala yusrif fee alqatli innahu kana mansooran
Kuma kada ku kashe rai wanda Allah Ya haramta fãce da haƙƙi, kuma wanda aka kashe, yanã wanda aka zãlunta to, haƙĩƙa Mun sanya hujja ga waliyyinsa, sai dai kada ya ƙẽtare haddi a cikin kashẽwar. Lalle shĩ ya kasance wanda ake taimako.
-
وَلَا تَقْرَبُوا۟ مَالَ ٱلْيَتِيمِ إِلَّا بِٱلَّتِى هِىَ أَحْسَنُ حَتَّىٰ يَبْلُغَ أَشُدَّهُۥ ۚ وَأَوْفُوا۟ بِٱلْعَهْدِ ۖ إِنَّ ٱلْعَهْدَ كَانَ مَسْـُٔولًا٣٤
Wala taqraboo mala alyateemi illa biallatee hiya ahsanu hatta yablugha ashuddahu waawfoo bialʿahdi inna alʿahda kana masoolan
Kuma kada ku kusanci dũkiyar marãya fãce dai da sifa wadda take ita ce mafi kyau, har ya isa ga mafi ƙarfinsa. Kuma ku cika alkawari. Lalle alkawari yã kasance abin tambayãwa ne.
-
وَأَوْفُوا۟ ٱلْكَيْلَ إِذَا كِلْتُمْ وَزِنُوا۟ بِٱلْقِسْطَاسِ ٱلْمُسْتَقِيمِ ۚ ذَٰلِكَ خَيْرٌ وَأَحْسَنُ تَأْوِيلًا٣٥
Waawfoo alkayla itha kiltum wazinoo bialqistasi almustaqeemi thalika khayrun waahsanu taweelan
Kuma ku cika mũdu idan kun yi awo, kuma ku auna nauyi da sikẽli madaidaici. Wancan ne mafi alhẽri, kuma mafi kyau ga fassara.
-
وَلَا تَقْفُ مَا لَيْسَ لَكَ بِهِۦ عِلْمٌ ۚ إِنَّ ٱلسَّمْعَ وَٱلْبَصَرَ وَٱلْفُؤَادَ كُلُّ أُو۟لَـٰٓئِكَ كَانَ عَنْهُ مَسْـُٔولًا٣٦
Wala taqfu ma laysa laka bihi ʿilmun inna alssamʿa waalbasara waalfuada kullu olaika kana ʿanhu masoolan
Kuma kada ka bi abin da bã ka da ilmi game da shi. Lalle ne jĩ da gani da zũciya, dukan waɗancan (mutum) yã kasance daga gare shi wanda ake tambaya.
-
وَلَا تَمْشِ فِى ٱلْأَرْضِ مَرَحًا ۖ إِنَّكَ لَن تَخْرِقَ ٱلْأَرْضَ وَلَن تَبْلُغَ ٱلْجِبَالَ طُولًا٣٧
Wala tamshi fee alardi marahan innaka lan takhriqa alarda walan tablugha aljibala toolan
Kuma kada ka yi tafiya a cikin ƙasa da alfahari. Lalle kai bã zã ka hũda ƙasa ba kuma bã zã ka kai a duwãtsu ba ga tsawo.
-
كُلُّ ذَٰلِكَ كَانَ سَيِّئُهُۥ عِندَ رَبِّكَ مَكْرُوهًا٣٨
Kullu thalika kana sayyiohu ʿinda rabbika makroohan
Dukan wancan mli mũninsa yã kasance abin ƙyãma a wurin Ubangijin ka.
-
ذَٰلِكَ مِمَّآ أَوْحَىٰٓ إِلَيْكَ رَبُّكَ مِنَ ٱلْحِكْمَةِ ۗ وَلَا تَجْعَلْ مَعَ ٱللَّهِ إِلَـٰهًا ءَاخَرَ فَتُلْقَىٰ فِى جَهَنَّمَ مَلُومًا مَّدْحُورًا٣٩
Thalika mimma awha ilayka rabbuka mina alhikmati wala tajʿal maʿa Allahi ilahan akhara fatulqa fee jahannama malooman madhooran
Wancan yãnã daga abin da Ubangijinka Ya yi wahayi zuwa gare ka na hikima. Kuma kada ka sanya wani abin bautãwa na daban tãre da Allah har a jẽfa ka a cikin Jahannama kanã wanda ake zargi, wanda ake tunkuɗẽwa1
Bayanai
[1] Wannan shĩ ne ƙarshen muƙãrana tsakãnin shiryarwar da Alƙur'ãni ya kãwo wa dũniya da abin da Attaura ta kãwo wa Banĩ Isrã'ĩla. Kuma akwai daidatãwa a cikinsu a tsakãnin hãlãye mãsu kyau da kĩshiyõyinsu, watau hãlãye mãsu mũni. -
أَفَأَصْفَىٰكُمْ رَبُّكُم بِٱلْبَنِينَ وَٱتَّخَذَ مِنَ ٱلْمَلَـٰٓئِكَةِ إِنَـٰثًا ۚ إِنَّكُمْ لَتَقُولُونَ قَوْلًا عَظِيمًا٤٠
Afaasfakum rabbukum bialbaneena waittakhatha mina almalaikati inathan innakum lataqooloona qawlan ʿatheeman
Shin fa, Ubangijinku Ya zãɓe ku da ɗiya maza ne, kuma Ya riƙi 'ya'ya mãta daga malã'iku?1 Lalle ne kũ, haƙĩƙa, kunã faɗar magana mai girma!
Bayanai
[1] Farkon muƙãrana a tsakãnin al'ãdun mushirikai da shiryarwar Alƙur'ãni dõmin gyãra tunãninsu ga karɓar ĩmãnin tauhĩdi. -
وَلَقَدْ صَرَّفْنَا فِى هَـٰذَا ٱلْقُرْءَانِ لِيَذَّكَّرُوا۟ وَمَا يَزِيدُهُمْ إِلَّا نُفُورًا٤١
Walaqad sarrafna fee hatha alqurani liyaththakkaroo wama yazeeduhum illa nufooran
Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun sarrafa bayãni a cikin wannan Alƙur'ãni dõmin su yi tunãni, kuma bã ya ƙãra musu kõme fãce gudu.
-
قُل لَّوْ كَانَ مَعَهُۥٓ ءَالِهَةٌ كَمَا يَقُولُونَ إِذًا لَّٱبْتَغَوْا۟ إِلَىٰ ذِى ٱلْعَرْشِ سَبِيلًا٤٢
Qul law kana maʿahu alihatun kama yaqooloona ithan laibtaghaw ila thee alʿarshi sabeelan
Ka ce: "Dã akwai waɗansu abũbuwan bautãwa tãre da shi, kamar yadda suka faɗa, a lõkacin, dã (abũbuwan bautãwar) sun nẽmi wata hanya1 zuwa ga Ma'abũcin Al'arshi."
Bayanai
[1] Dã su abõkan tãrayyar sun nemi hanya zuwa ga Allah dõmin su yãƙe shi sabõda Ya ce Al'arshi Tãsa ce, Shi kaɗai, dõmin su sãmi nãsu rabon, sabõda Al'arshi tã haɗiye kõme, har da su. -
سُبْحَـٰنَهُۥ وَتَعَـٰلَىٰ عَمَّا يَقُولُونَ عُلُوًّا كَبِيرًا٤٣
Subhanahu wataʿala ʿamma yaqooloona ʿuluwwan kabeeran
TsarkinSa yã tabbata kuma Ya ɗaukaka daga abin da suke faɗã, ɗaukaka mai girma.
-
تُسَبِّحُ لَهُ ٱلسَّمَـٰوَٰتُ ٱلسَّبْعُ وَٱلْأَرْضُ وَمَن فِيهِنَّ ۚ وَإِن مِّن شَىْءٍ إِلَّا يُسَبِّحُ بِحَمْدِهِۦ وَلَـٰكِن لَّا تَفْقَهُونَ تَسْبِيحَهُمْ ۗ إِنَّهُۥ كَانَ حَلِيمًا غَفُورًا٤٤
Tusabbihu lahu alssamawatu alssabʿu waalardu waman feehinna wain min shayin illa yusabbihu bihamdihi walakin la tafqahoona tasbeehahum innahu kana haleeman ghafooran
Sammai bakwai da ƙasa da wanda yake a cikinsu sunã yi Masa tasbĩhi. Kuma bãbu wani abu fãce yanã tasbĩhi game da gõde Masa, kuma amma ba ku fahimtar tasbĩhinsu. Lalle ne shĩ, Ya kasance Mai haƙuri ne, Mai gãfara.
-
وَإِذَا قَرَأْتَ ٱلْقُرْءَانَ جَعَلْنَا بَيْنَكَ وَبَيْنَ ٱلَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِٱلْـَٔاخِرَةِ حِجَابًا مَّسْتُورًا٤٥
Waitha qarata alqurana jaʿalna baynaka wabayna allatheena la yuminoona bialakhirati hijaban mastooran
Kuma idan ka karanta Alƙur'ani,1 sai Mu sanya a tsakãninka da tsakanin waɗanda bã su yin ĩmãni da Lãhira wani shãmaki mai suturcẽwa.
Bayanai
[1] Mushirikai jahilai ne, ba su iya ɗaukar jãyayyar magana, sabõda sun fi kusanta zuwa ga dabbõbi ga tunãninsu, bisa gare su zuwa ga mutãne, kõ da yake sauran jikinsu na mutãne ne. Sabõda haka a kõ yaushe sunã kusa ga faɗan tãyar da hankali da dõke-dõke. Sabõda haka Allah Ya sanya tsari ga AnnabinSa da wanda ya bi hanyar Annabin, wajen shiryar da mutãne game da karanta Alƙur'ãni. Bã zã su iya fãɗa mai karanta Alƙur'ãni da dũka ba, kuma tsõronsa suke ji dõmin kwarjinin Alƙur'ãni. -
وَجَعَلْنَا عَلَىٰ قُلُوبِهِمْ أَكِنَّةً أَن يَفْقَهُوهُ وَفِىٓ ءَاذَانِهِمْ وَقْرًا ۚ وَإِذَا ذَكَرْتَ رَبَّكَ فِى ٱلْقُرْءَانِ وَحْدَهُۥ وَلَّوْا۟ عَلَىٰٓ أَدْبَـٰرِهِمْ نُفُورًا٤٦
Wajaʿalna ʿala quloobihim akinnatan an yafqahoohu wafee athanihim waqran waitha thakarta rabbaka fee alqurani wahdahu wallaw ʿala adbarihim nufooran
Kuma Mu sanya marufai a kan zukãtansu dõmin kada su fahimce shi, da, wani nauyi a cikin kunnuwansu, kuma idan ka ambaci Ubangijinka, a cikin Alƙur'ãni shĩ kaɗai, sai su jũya a kan bayayyakinsu dõmin gudu.
-
نَّحْنُ أَعْلَمُ بِمَا يَسْتَمِعُونَ بِهِۦٓ إِذْ يَسْتَمِعُونَ إِلَيْكَ وَإِذْ هُمْ نَجْوَىٰٓ إِذْ يَقُولُ ٱلظَّـٰلِمُونَ إِن تَتَّبِعُونَ إِلَّا رَجُلًا مَّسْحُورًا٤٧
Nahnu aʿlamu bima yastamiʿoona bihi ith yastamiʿoona ilayka waith hum najwa ith yaqoolu alththalimoona in tattabiʿoona illa rajulan mashooran
Mũ ne Mafi sani game da abin da suke saurãre da shi a lõkacin da suke yin saurãren zuwa gare ka, kuma a lõkacin da suke mãsu gãnãwa a tsakãninsu a lõkacin da azzãlumai suke cẽwa, "Bã ku biyar kõwa fãce wani namiji sihirtacce."
-
ٱنظُرْ كَيْفَ ضَرَبُوا۟ لَكَ ٱلْأَمْثَالَ فَضَلُّوا۟ فَلَا يَسْتَطِيعُونَ سَبِيلًا٤٨
Onthur kayfa daraboo laka alamthala fadalloo fala yastateeʿoona sabeelan
Ka dũba yadda suka buga maka misãlai, sai suka ɓace bã su iya sãmun hanya.
-
وَقَالُوٓا۟ أَءِذَا كُنَّا عِظَـٰمًا وَرُفَـٰتًا أَءِنَّا لَمَبْعُوثُونَ خَلْقًا جَدِيدًا٤٩
Waqaloo aitha kunna ʿithaman warufatan ainna lamabʿoothoona khalqan jadeedan
Kuma suka ce: "Shin, idan mun kasance ƙasũsuwa da, niƙaƙƙun gaɓãɓuwa ashe, lalle ne mũ haƙĩƙa, waɗanda ake tãyarwa ne a wata halitta sãbuwa?"
-
۞ قُلْ كُونُوا۟ حِجَارَةً أَوْ حَدِيدًا٥٠
Qul koonoo hijaratan aw hadeedan
Ka ce: "Ku kasance duwãtsu ko kuwa baƙin ƙarfe."
-
أَوْ خَلْقًا مِّمَّا يَكْبُرُ فِى صُدُورِكُمْ ۚ فَسَيَقُولُونَ مَن يُعِيدُنَا ۖ قُلِ ٱلَّذِى فَطَرَكُمْ أَوَّلَ مَرَّةٍ ۚ فَسَيُنْغِضُونَ إِلَيْكَ رُءُوسَهُمْ وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هُوَ ۖ قُلْ عَسَىٰٓ أَن يَكُونَ قَرِيبًا٥١
Aw khalqan mimma yakburu fee sudoorikum fasayaqooloona man yuʿeeduna quli allathee fatarakum awwala marratin fasayunghidoona ilayka ruoosahum wayaqooloona mata huwa qul ʿasa an yakoona qareeban
"Kõ kuwa wata halitta daga abin da yake da girma a cikin ƙirazanku." To zã su ce "Wãne ne zai mayar da mu?" Ka ce: "Wanda Ya ƙaga halittarku a fabkon lõkaci." To, zã su gyaɗa kansu zuwa gare ka, kuma sunã cẽwa, "A yaushene shi?" Ka ce: "Akwai tsammãninsa ya kasance kusa."
-
يَوْمَ يَدْعُوكُمْ فَتَسْتَجِيبُونَ بِحَمْدِهِۦ وَتَظُنُّونَ إِن لَّبِثْتُمْ إِلَّا قَلِيلًا٥٢
Yawma yadʿookum fatastajeeboona bihamdihi watathunnoona in labithtum illa qaleelan
"A rãnar da Yake kiran ku, sa'an nan ku riƙa karɓãwa game dã gõde Masa, kuma kunã zaton ba ku zauna ba fãce kaɗan."
-
وَقُل لِّعِبَادِى يَقُولُوا۟ ٱلَّتِى هِىَ أَحْسَنُ ۚ إِنَّ ٱلشَّيْطَـٰنَ يَنزَغُ بَيْنَهُمْ ۚ إِنَّ ٱلشَّيْطَـٰنَ كَانَ لِلْإِنسَـٰنِ عَدُوًّا مُّبِينًا٥٣
Waqul liʿibadee yaqooloo allatee hiya ahsanu inna alshshaytana yanzaghu baynahum inna alshshaytana kana lilinsani ʿaduwwan mubeenan
Kuma ka cẽ wa bãyiNa, su faɗi kalma1 wadda take mafi kyau. Lalle ne Shaiɗan yanã sanya ɓarna a tsakãninsu. Lalle ne Shaiɗan ya kasance ga mutum, maƙiyi bayyanan ne.
Bayanai
[1] Ka ce wa bãyĩNa, mutãne, idan sunã magana su auna kalmõmin da suke zance da su, sa'an nan su riƙa amfãni da kalma mafi kyãwo dõmin kada shaiɗan ya sãmi mashiga daga maganarsu zuwa ga zukãtansu, ya sanya ɓarna a tsakãninsu. -
رَّبُّكُمْ أَعْلَمُ بِكُمْ ۖ إِن يَشَأْ يَرْحَمْكُمْ أَوْ إِن يَشَأْ يُعَذِّبْكُمْ ۚ وَمَآ أَرْسَلْنَـٰكَ عَلَيْهِمْ وَكِيلًا٥٤
Rabbukum aʿlamu bikum in yasha yarhamkum aw in yasha yuʿaththibkum wama arsalnaka ʿalayhim wakeelan
Ubangijinku ne Mafi sani game da ku. Idan Ya so, zai yi muku rahama, kõ kuwa idan Yã so zai azabtãku. Kuma ba Mu aika ka kanã wakĩli a kansu ba.
-
وَرَبُّكَ أَعْلَمُ بِمَن فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ۗ وَلَقَدْ فَضَّلْنَا بَعْضَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ عَلَىٰ بَعْضٍ ۖ وَءَاتَيْنَا دَاوُۥدَ زَبُورًا٥٥
Warabbuka aʿlamu biman fee alssamawati waalardi walaqad faddalna baʿda alnnabiyyeena ʿala baʿdin waatayna dawooda zabooran
Kuma Ubangijinka ne Mafi sani game da wanda yake a cikin sammai da ƙasa. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun fĩfĩta sãshen Annabãwa a kan sãshe kuma Mun bai wa Dãwũda zabũra.1
Bayanai
[1] Muƙãrana a tsakãnin Annabãwa. Allah Yã fĩfĩta waɗansu a kan waɗansu. Falalar Dãwũda a kan waɗansu Annabãwa da Zabũra ne to inã fĩfĩkon wanda aka bai wa Alƙur'ãni mafĩfĩcin littafi da sauran Annabãwa?. -
قُلِ ٱدْعُوا۟ ٱلَّذِينَ زَعَمْتُم مِّن دُونِهِۦ فَلَا يَمْلِكُونَ كَشْفَ ٱلضُّرِّ عَنكُمْ وَلَا تَحْوِيلًا٥٦
Quli odʿu allatheena zaʿamtum min doonihi fala yamlikoona kashfa alddurri ʿankum wala tahweelan
Ka ce: "Ku kirãyi waɗanda kuka riya, baicinSa." To, ba su mallakar kuranyẽwar cũta daga gare ku, kuma haka jũyarwa."1
Bayanai
[1] Bã zã su iya jũyar da cũta daga gare ku zuwa ga wani ko kuwa daga wani zuwa gare ku ba. -
أُو۟لَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ يَدْعُونَ يَبْتَغُونَ إِلَىٰ رَبِّهِمُ ٱلْوَسِيلَةَ أَيُّهُمْ أَقْرَبُ وَيَرْجُونَ رَحْمَتَهُۥ وَيَخَافُونَ عَذَابَهُۥٓ ۚ إِنَّ عَذَابَ رَبِّكَ كَانَ مَحْذُورًا٥٧
Olaika allatheena yadʿoona yabtaghoona ila rabbihimu alwaseelata ayyuhum aqrabu wayarjoona rahmatahu wayakhafoona ʿathabahu inna ʿathaba rabbika kana mahthooran
Waɗancan, waɗanda suke kiran1, sunã nẽman tsãni zuwa ga Ubangijinsu. Waɗanne ne suke mafĩfĩta a kusanta? Kuma sunã fãtan sãmun rahamarSa, kuma sunã tsõron azãbarSa. Lalle ne azãbar Ubangijinka ta kasance abar tsõro ce.
Bayanai
[1] Waɗanda kãfirai ke neman tawassuli da su zuwa ga Allah, sũ ma sunã neman abin da zai sãdar da su zuwa ga Allah, sabõda haka bãbu bambanci a tsakãnin mai tawassuli da wanda ake tawassulin da shi ga kusanta zuwa ga Allah. Bãbu mai kusanta zuwa ga Allah sai da taƙawa ga ibãdarSa kawai. -
وَإِن مِّن قَرْيَةٍ إِلَّا نَحْنُ مُهْلِكُوهَا قَبْلَ يَوْمِ ٱلْقِيَـٰمَةِ أَوْ مُعَذِّبُوهَا عَذَابًا شَدِيدًا ۚ كَانَ ذَٰلِكَ فِى ٱلْكِتَـٰبِ مَسْطُورًا٥٨
Wain min qaryatin illa nahnu muhlikooha qabla yawmi alqiyamati aw muʿaththibooha ʿathaban shadeedan kana thalika fee alkitabi mastooran
Kuma bãbu wata alƙarya fãce, Mu ne mãsu halaka ta a gabãnin Rãnar ¡iyãma kõ kuwa Mũ mãsu azãbta ta ne da azãba mai tsanani. Wancan ya kasance a cikin littãfi rubũtacce.
-
وَمَا مَنَعَنَآ أَن نُّرْسِلَ بِٱلْـَٔايَـٰتِ إِلَّآ أَن كَذَّبَ بِهَا ٱلْأَوَّلُونَ ۚ وَءَاتَيْنَا ثَمُودَ ٱلنَّاقَةَ مُبْصِرَةً فَظَلَمُوا۟ بِهَا ۚ وَمَا نُرْسِلُ بِٱلْـَٔايَـٰتِ إِلَّا تَخْوِيفًا٥٩
Wama manaʿana an nursila bialayati illa an kaththaba biha alawwaloona waatayna thamooda alnnaqata mubsiratan fathalamoo biha wama nursilu bialayati illa takhweefan
Kuma bãbu abin da ya hana Mu, Mu aika da ãyõyi fãce sabõda mutãnen farko sun ƙaryata game da su. Kuma Mun bai wa Samũdãwa tãguwa, ãyã bayyananna, sai suka yi zãlunci game da ita. Kuma bã Mu aikãwa da ãyõyi fãce dõmin tsõratarwa.
-
وَإِذْ قُلْنَا لَكَ إِنَّ رَبَّكَ أَحَاطَ بِٱلنَّاسِ ۚ وَمَا جَعَلْنَا ٱلرُّءْيَا ٱلَّتِىٓ أَرَيْنَـٰكَ إِلَّا فِتْنَةً لِّلنَّاسِ وَٱلشَّجَرَةَ ٱلْمَلْعُونَةَ فِى ٱلْقُرْءَانِ ۚ وَنُخَوِّفُهُمْ فَمَا يَزِيدُهُمْ إِلَّا طُغْيَـٰنًا كَبِيرًا٦٠
Waith qulna laka inna rabbaka ahata bialnnasi wama jaʿalna alrruya allatee araynaka illa fitnatan lilnnasi waalshshajarata almalʿoonata fee alqurani wanukhawwifuhum fama yazeeduhum illa tughyanan kabeeran
Kuma a lõkacin da Muka ce maka, "Lalle ne Ubangijinka Yã kẽwaye mutãne." Kuma ba Mu sanya abin da ya gani wanda1 Muka nũna maka ba, fãce dõmin fitina ga mutãne, da itãciya wadda aka la'anta a cikin Alƙur'ani. Kuma Munã tsõratar da su, sa'an nan (tsõratarwar) bã ta ƙãra su fãce da kangara mai girma.
Bayanai
[1] Abũbuwan da Annabi ya gani a daren Isrã'i da Mi'irãji, watau tafiyarsa zuwa sama wadda aka yi ishãrã da ita a farkon sũrar. Itãciyar da aka la'anta ita ce Zaƙƙũm abincin mutãnen Wuta. Akwai muƙãrana, a cikin wannan,cħwa ãyõyin da aka bai wa wani Annabi sun fi waɗanda aka bai wa wasu Annabãwa girma. -
وَإِذْ قُلْنَا لِلْمَلَـٰٓئِكَةِ ٱسْجُدُوا۟ لِـَٔادَمَ فَسَجَدُوٓا۟ إِلَّآ إِبْلِيسَ قَالَ ءَأَسْجُدُ لِمَنْ خَلَقْتَ طِينًا٦١
Waith qulna lilmalaikati osjudoo liadama fasajadoo illa ibleesa qala aasjudu liman khalaqta teenan
Kuma a lõkacin1 da Muka cẽ wa malã'iku, "Ku yi sujada ga Ãdamu," sai suka yi sujada, fãce Ibilĩsa, ya ce: "shin, zan yi sujada ga wanda ka2 halitta shi yanã lãka?"
Bayanai
[1] Muƙãrana a tsakãnin jinsin mutum da malã'iku da aljannu. An fĩfĩtar da jinsin mutum da sanya wa sauran jinsõshi biyu su yi masa sujada, sa'an nan aka ɗaukaka jinsin malã'ika sabõda ɗã'a, kuma aka la'anci jinsin Iblĩsa da sãɓo. [2] Rubũta "ka" da ƙaramin "ka" ne kõ da yake lamĩrin Allah ne, dõmin ya nuna hãlin maganar Shaiɗan zuwa ga Allah Mai girma. Yanã yin maganar da hushi, ba da girmamawa ba. -
قَالَ أَرَءَيْتَكَ هَـٰذَا ٱلَّذِى كَرَّمْتَ عَلَىَّ لَئِنْ أَخَّرْتَنِ إِلَىٰ يَوْمِ ٱلْقِيَـٰمَةِ لَأَحْتَنِكَنَّ ذُرِّيَّتَهُۥٓ إِلَّا قَلِيلًا٦٢
Qala araaytaka hatha allathee karramta ʿalayya lain akhkhartani ila yawmi alqiyamati laahtanikanna thurriyyatahu illa qaleelan
Ya ce: "Shin, kã gan ka1! Wannan wanda ka girmama a kaina, lalle ne idan ka jinkirtã mini zuwa ga Rãnar ¡iyãma lalle ne, zan tumɓuke zuriyarsa, fãce kaɗan."
Bayanai
[1] Mai sãɓõ sabõda hassada bã ya ganin girman Ubangijinsa. A cikin maganar Iblĩs akwai rashin ladabi da nũna ƙiyayya ga Ãdamu, har zuwa ga zuriyarsa, wadda ba a haifã ba tukuna. -
قَالَ ٱذْهَبْ فَمَن تَبِعَكَ مِنْهُمْ فَإِنَّ جَهَنَّمَ جَزَآؤُكُمْ جَزَآءً مَّوْفُورًا٦٣
Qala ithhab faman tabiʿaka minhum fainna jahannama jazaokum jazaan mawfooran
Ya ce: "Ka tafi. Sa'an nan wanda ya bĩ ka daga gare su, to, Jahannama ce sakamakonku, (Mu ba ku shi) sakamako cikakke."
-
وَٱسْتَفْزِزْ مَنِ ٱسْتَطَعْتَ مِنْهُم بِصَوْتِكَ وَأَجْلِبْ عَلَيْهِم بِخَيْلِكَ وَرَجِلِكَ وَشَارِكْهُمْ فِى ٱلْأَمْوَٰلِ وَٱلْأَوْلَـٰدِ وَعِدْهُمْ ۚ وَمَا يَعِدُهُمُ ٱلشَّيْطَـٰنُ إِلَّا غُرُورًا٦٤
Waistafziz mani istataʿta minhum bisawtika waajlib ʿalayhim bikhaylika warajlika washarikhum fee alamwali waalawladi waʿidhum wama yaʿiduhumu alshshaytanu illa ghurooran
"Kuma ka rikitar da wanda ka sãmi ĩko a kansa, daga gare su, da sautinka, kuma ka yi hari a kansu da dawãkinka da dãkãrunka kuma ka yi tãrẽwa da su a cikin dũkiyõyi da ɗiyã, kumaka yi musu wa'adi. Alhãli kuwa Shaiɗan bã ya yi musu wa'adin kõme fãce da ruɗi."
-
إِنَّ عِبَادِى لَيْسَ لَكَ عَلَيْهِمْ سُلْطَـٰنٌ ۚ وَكَفَىٰ بِرَبِّكَ وَكِيلًا٦٥
Inna ʿibadee laysa laka ʿalayhim sultanun wakafa birabbika wakeelan
"Lalle ne bãyiNa, bã ka da wani ƙarfi a kansu. Kuma Ubangijinka Ya isa Ya zama wakĩli."
-
رَّبُّكُمُ ٱلَّذِى يُزْجِى لَكُمُ ٱلْفُلْكَ فِى ٱلْبَحْرِ لِتَبْتَغُوا۟ مِن فَضْلِهِۦٓ ۚ إِنَّهُۥ كَانَ بِكُمْ رَحِيمًا٦٦
Rabbukumu allathee yuzjee lakumu alfulka fee albahri litabtaghoo min fadlihi innahu kana bikum raheeman
Ubangijinku ne Yake gudãnar da jirgi a cikin tẽku, dõmin ku nema daga falalarSa. Lalle ne Shĩ, Yã kasance a gare ku Mai jin ƙai.
-
وَإِذَا مَسَّكُمُ ٱلضُّرُّ فِى ٱلْبَحْرِ ضَلَّ مَن تَدْعُونَ إِلَّآ إِيَّاهُ ۖ فَلَمَّا نَجَّىٰكُمْ إِلَى ٱلْبَرِّ أَعْرَضْتُمْ ۚ وَكَانَ ٱلْإِنسَـٰنُ كَفُورًا٦٧
Waitha massakumu alddurru fee albahri dalla man tadʿoona illa iyyahu falamma najjakum ila albarri aʿradtum wakana alinsanu kafooran
Kuma idan cũta ta shãfe ku, a cikin tẽku, sai wanda kuke kira ya ɓace fãce Shi. To, a lõkacin da Ya tsira da ku zuwa, ga tudu sai kuka bijire. Kuma mutum ya kasance mai yawan butulci.
-
أَفَأَمِنتُمْ أَن يَخْسِفَ بِكُمْ جَانِبَ ٱلْبَرِّ أَوْ يُرْسِلَ عَلَيْكُمْ حَاصِبًا ثُمَّ لَا تَجِدُوا۟ لَكُمْ وَكِيلًا٦٨
Afaamintum an yakhsifa bikum janiba albarri aw yursila ʿalaykum hasiban thumma la tajidoo lakum wakeelan
Shin fa kun amince cẽwa (Allah) bã Ya shãfe gẽfen ƙasa game da ku kõ kuwa Ya aika da iska mai tsakuwa a kanku, sa'an nan kuma bã zã ku sãmi wani wakĩli ba dõminku?
-
أَمْ أَمِنتُمْ أَن يُعِيدَكُمْ فِيهِ تَارَةً أُخْرَىٰ فَيُرْسِلَ عَلَيْكُمْ قَاصِفًا مِّنَ ٱلرِّيحِ فَيُغْرِقَكُم بِمَا كَفَرْتُمْ ۙ ثُمَّ لَا تَجِدُوا۟ لَكُمْ عَلَيْنَا بِهِۦ تَبِيعًا٦٩
Am amintum an yuʿeedakum feehi taratan okhra fayursila ʿalaykum qasifan mina alrreehi fayughriqakum bima kafartum thumma la tajidoo lakum ʿalayna bihi tabeeʿan
Ko kun amince ga Ya mayar da ku a cikin tẽkun a wani lõkaci na dabam, sa'an na Ya aika wata gũguwa mai karya abũbuwa daga iska, har ya nutsar da ku sabõda abin da kuka yi na kãfirci? Sa'an nan kuma bã ku sãmun mai bin hakki sabõda ku, a kanMu, game da Shi.
-
۞ وَلَقَدْ كَرَّمْنَا بَنِىٓ ءَادَمَ وَحَمَلْنَـٰهُمْ فِى ٱلْبَرِّ وَٱلْبَحْرِ وَرَزَقْنَـٰهُم مِّنَ ٱلطَّيِّبَـٰتِ وَفَضَّلْنَـٰهُمْ عَلَىٰ كَثِيرٍ مِّمَّنْ خَلَقْنَا تَفْضِيلًا٧٠
Walaqad karramna banee adama wahamalnahum fee albarri waalbahri warazaqnahum mina alttayyibati wafaddalnahum ʿala katheerin mimman khalaqna tafdeelan
Kuma lalle ne Mun girmama 'yan Adam1, kuma Muka ɗauke su a cikin ƙasa da tẽku kuma Muka azurta su daga abũbuwa mãsu dãɗi kuma Muka fĩfĩta su a kan mãsu yawa daga waɗanda Muka halitta, fĩfĩtãwa.
Bayanai
[1] Muƙãrana a tsakãnin jinsin mutum da sauran halittar Allah. -
يَوْمَ نَدْعُوا۟ كُلَّ أُنَاسٍۭ بِإِمَـٰمِهِمْ ۖ فَمَنْ أُوتِىَ كِتَـٰبَهُۥ بِيَمِينِهِۦ فَأُو۟لَـٰٓئِكَ يَقْرَءُونَ كِتَـٰبَهُمْ وَلَا يُظْلَمُونَ فَتِيلًا٧١
Yawma nadʿoo kulla onasin biimamihim faman ootiya kitabahu biyameenihi faolaika yaqraoona kitabahum wala yuthlamoona fateelan
A rãnar da Muke kiran1 kõwane mutãne da lĩmãminsu to, wanda aka bai wa littafinsa a dã, mansa, to, waɗannan sunã karãtun littãfinsu, kuma bã a zãluntar su da zaren bãkin gurtsin dabĩno.
Bayanai
[1] Muƙãrana a Lãhira a tsakãnin al'ummõmi kuma da tsakãnin mũminai da kãfirai,. -
وَمَن كَانَ فِى هَـٰذِهِۦٓ أَعْمَىٰ فَهُوَ فِى ٱلْـَٔاخِرَةِ أَعْمَىٰ وَأَضَلُّ سَبِيلًا٧٢
Waman kana fee hathihi aʿma fahuwa fee alakhirati aʿma waadallu sabeelan
Kuma wanda ya kasance makãho1 a cikin wannan sabõda haka shi a Lãhira makãho ne kuma mafi ɓata ga hanya.
Bayanai
[1] Muƙarana a tsakãnin makantar basĩra da makantar ganin ido. -
وَإِن كَادُوا۟ لَيَفْتِنُونَكَ عَنِ ٱلَّذِىٓ أَوْحَيْنَآ إِلَيْكَ لِتَفْتَرِىَ عَلَيْنَا غَيْرَهُۥ ۖ وَإِذًا لَّٱتَّخَذُوكَ خَلِيلًا٧٣
Wain kadoo layaftinoonaka ʿani allathee awhayna ilayka litaftariya ʿalayna ghayrahu waithan laittakhathooka khaleelan
Kuma lalle ne sun yi kusa haƙĩƙa, su fitinẽ ka daga abin da Muka yi wahayi zuwa gare ka, dõmin ka ƙirƙira waninsa a gare Mu, a lõkacin, haƙĩƙa, dã sun riƙe ka masoyi.
-
وَلَوْلَآ أَن ثَبَّتْنَـٰكَ لَقَدْ كِدتَّ تَرْكَنُ إِلَيْهِمْ شَيْـًٔا قَلِيلًا٧٤
Walawla an thabbatnaka laqad kidta tarkanu ilayhim shayan qaleelan
Kuma bã dõmin1 Mun tabbatar da kai ba, lalle ne, haƙĩƙa, dã kã yi kusa ka karkata zuwa gare su ta wani abu kaɗan.
Bayanai
[1] Muƙãrana a tsakãnin sarauta da Manzancin Allah. Sarkin dũniya yanã canja manufarsa dõmin neman yardar mutãnensa. Amman Manzon Allah bã ya sãke abin da Allah Ya umurce shi da shi dõmin neman yardar Mutãne. -
إِذًا لَّأَذَقْنَـٰكَ ضِعْفَ ٱلْحَيَوٰةِ وَضِعْفَ ٱلْمَمَاتِ ثُمَّ لَا تَجِدُ لَكَ عَلَيْنَا نَصِيرًا٧٥
Ithan laathaqnaka diʿfa alhayati wadiʿfa almamati thumma la tajidu laka ʿalayna naseeran
A lõkacin, lalle ne, dã Mun ɗanɗana maka ninkin azãbar rãyuwa da ninkin azãbar mutuwa, sa'an nan kuma bã zã ka sãmi mataimaki ba a kanMu.
-
وَإِن كَادُوا۟ لَيَسْتَفِزُّونَكَ مِنَ ٱلْأَرْضِ لِيُخْرِجُوكَ مِنْهَا ۖ وَإِذًا لَّا يَلْبَثُونَ خِلَـٰفَكَ إِلَّا قَلِيلًا٧٦
Wain kadoo layastafizzoonaka mina alardi liyukhrijooka minha waithan la yalbathoona khilafaka illa qaleelan
Kuma lalle ne, sun1 yi kusa, haƙĩƙa, su tãyar da hankalinka daga ƙasar, dõmin su fitar da kai daga gare ta. Kuma a lõkacin, bã zã su zauna ba a kan sãɓãninka fãce kaɗan.
Bayanai
[1] Muƙãrana a tsakãnin mai aiki dõmin Allah, bã a iya jũyar da shi daga aikinsa dõmin neman wata kamãla, amma mai aikin dũniya anã iya canja shi dõmin haka. Kuma bambancin hijira da kõra waɗanda suka kõri Annabinsu sai a halaka su, amma waɗanda Annabinsu ya yi hijira gabãnin azãba, to, bã zã a halaka su ba. -
سُنَّةَ مَن قَدْ أَرْسَلْنَا قَبْلَكَ مِن رُّسُلِنَا ۖ وَلَا تَجِدُ لِسُنَّتِنَا تَحْوِيلًا٧٧
Sunnata man qad arsalna qablaka min rusulina wala tajidu lisunnatina tahweelan
Hanyar waɗanda, haƙĩƙa, Muka aika a gabãninka, daga ManzanninMu, kuma bã zã ka sãmi jũyarwa ba ga hanyar Mu.
-
أَقِمِ ٱلصَّلَوٰةَ لِدُلُوكِ ٱلشَّمْسِ إِلَىٰ غَسَقِ ٱلَّيْلِ وَقُرْءَانَ ٱلْفَجْرِ ۖ إِنَّ قُرْءَانَ ٱلْفَجْرِ كَانَ مَشْهُودًا٧٨
Aqimi alssalata lidulooki alshshamsi ila ghasaqi allayli waqurana alfajri inna qurana alfajri kana mashhoodan
Ka tsayar da salla1 a karkatar rãnã zuwa ga duhun dare da lõkacin fitar alfijir2 lalle ne karãtun fitar alfijir ya kasance wanda ake halarta.
Bayanai
[1] Tsayar da salla a cikin lõkutanta, shi ne yake hana a yaudari mutum da magana har a sanya shi ya yi abin da bai kamãta ba, ko kuma ya yi abin da sharĩ'a ta hana. [2] Karãtun fitar alfijir, ana nufin sallar asuba. Sabõda haka anã son dõgon karãtu a cikinta, gwargwadon fãrã ta a duhun dare a bayan fitar Alfijir. -
وَمِنَ ٱلَّيْلِ فَتَهَجَّدْ بِهِۦ نَافِلَةً لَّكَ عَسَىٰٓ أَن يَبْعَثَكَ رَبُّكَ مَقَامًا مَّحْمُودًا٧٩
Wamina allayli fatahajjad bihi nafilatan laka ʿasa an yabʿathaka rabbuka maqaman mahmoodan
Kuma da dare, sai ka yi hĩra1 da shi (Alƙur'ãni) akan ƙãri gare ka. Akwai tsammãnin Ubangijin ka Ya tãyar da kai a wani matsayi gõdadde.
Bayanai
[1] Hĩra da Alƙur'ãni, watau a yi sallõlin nãfila na dare, shafa'i bibbiyu, a ƙãre da wutri. Ga Annabi tahajjudi da wutrin wãjibi ne ƙãri a kan abin da aka ɗõra wa sauran mutãne, a lõkacin da yake zaune a gida. Ga sauran mutãne wutri sunna ce, kamar sallõlin ĩdi da rõkon ruwa da husũfin rãnã da na wata. A nan akwai bambanci a tsakãnin Annabi da jama'arsa a wajen wutri. -
وَقُل رَّبِّ أَدْخِلْنِى مُدْخَلَ صِدْقٍ وَأَخْرِجْنِى مُخْرَجَ صِدْقٍ وَٱجْعَل لِّى مِن لَّدُنكَ سُلْطَـٰنًا نَّصِيرًا٨٠
Waqul rabbi adkhilnee mudkhala sidqin waakhrijnee mukhraja sidqin waijʿal lee min ladunka sultanan naseeran
Kuma ka ce: "Yã Ubangijĩna1! Ka shigar, da ni shigar gaskiya, kuma Ka fitar da ni fitar gaskiya. Kuma Ka sanya mini, daga gun Ka, wani ƙarfi mai taimako."
Bayanai
[1] Kuma ka yi addu'a a cikin sallarka da bãyanta da wannan addu'a dõmin ta nũna sallamãwarka ga Ubangijinka Allah. -
وَقُلْ جَآءَ ٱلْحَقُّ وَزَهَقَ ٱلْبَـٰطِلُ ۚ إِنَّ ٱلْبَـٰطِلَ كَانَ زَهُوقًا٨١
Waqul jaa alhaqqu wazahaqa albatilu inna albatila kana zahooqan
Kuma ka ce: "Gaskiya tã zo, kuma ƙarya ta lãlãce. Lalle ne ƙarya ta kasance lãlãtacciya."
-
وَنُنَزِّلُ مِنَ ٱلْقُرْءَانِ مَا هُوَ شِفَآءٌ وَرَحْمَةٌ لِّلْمُؤْمِنِينَ ۙ وَلَا يَزِيدُ ٱلظَّـٰلِمِينَ إِلَّا خَسَارًا٨٢
Wanunazzilu mina alqurani ma huwa shifaon warahmatun lilmumineena wala yazeedu alththalimeena illa khasaran
Kuma Munã sassaukarwa daga Alƙur'ãni, abin da yake waraka ne da rahama ga mũminai. Kuma bã ya ƙãra wa azzãlumai (kõme) fãce hasãra.
-
وَإِذَآ أَنْعَمْنَا عَلَى ٱلْإِنسَـٰنِ أَعْرَضَ وَنَـَٔا بِجَانِبِهِۦ ۖ وَإِذَا مَسَّهُ ٱلشَّرُّ كَانَ يَـُٔوسًا٨٣
Waitha anʿamna ʿala alinsani aʿrada wanaa bijanibihi waitha massahu alshsharru kana yaoosan
Kuma idan Muka yi ni'ima a kan mutum,1 sai ya hinjire, kuma ya nĩsanta da gefensa, kuma idan sharri ya shãfe shi, sai ya kasance mai yanke ƙauna.
Bayanai
[1] Muƙãrana a tsakãnin hãlãye biyu na mutum, hãlin tsanani da hãlin cũta. -
قُلْ كُلٌّ يَعْمَلُ عَلَىٰ شَاكِلَتِهِۦ فَرَبُّكُمْ أَعْلَمُ بِمَنْ هُوَ أَهْدَىٰ سَبِيلًا٨٤
Qul kullun yaʿmalu ʿala shakilatihi farabbukum aʿlamu biman huwa ahda sabeelan
Ka ce: "Kõwa ya yi aiki a kan hanyarsa. Sa'an nan Ubangijinka ne Mafi sani ga wanda yake mafi shiryuwa ga Hanya."
-
وَيَسْـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلرُّوحِ ۖ قُلِ ٱلرُّوحُ مِنْ أَمْرِ رَبِّى وَمَآ أُوتِيتُم مِّنَ ٱلْعِلْمِ إِلَّا قَلِيلًا٨٥
Wayasaloonaka ʿani alrroohi quli alrroohu min amri rabbee wama ooteetum mina alʿilmi illa qaleelan
Sunã tambayar ka ga rũhi. Ka ce: "Rũhi daga al'amarin Ubangijina ne, kuma ba a bã ku (kõme) ba daga ilmi fãce kaɗan."
-
وَلَئِن شِئْنَا لَنَذْهَبَنَّ بِٱلَّذِىٓ أَوْحَيْنَآ إِلَيْكَ ثُمَّ لَا تَجِدُ لَكَ بِهِۦ عَلَيْنَا وَكِيلًا٨٦
Walain shina lanathhabanna biallathee awhayna ilayka thumma la tajidu laka bihi ʿalayna wakeelan
Kuma lalle ne idan Mun so, haƙĩƙa, Munã tafiya da abinda Muka yi wahayi zuwa gare ka. Sa'an nan kuma bã za ka sãmi wani wakĩli ba dõminka game da shi a kanMu.
-
إِلَّا رَحْمَةً مِّن رَّبِّكَ ۚ إِنَّ فَضْلَهُۥ كَانَ عَلَيْكَ كَبِيرًا٨٧
Illa rahmatan min rabbika inna fadlahu kana ʿalayka kabeeran
Fãce da rahama daga Ubangijinka. Lalle ne falalarSa ta kasance mai girma a kanka.
-
قُل لَّئِنِ ٱجْتَمَعَتِ ٱلْإِنسُ وَٱلْجِنُّ عَلَىٰٓ أَن يَأْتُوا۟ بِمِثْلِ هَـٰذَا ٱلْقُرْءَانِ لَا يَأْتُونَ بِمِثْلِهِۦ وَلَوْ كَانَ بَعْضُهُمْ لِبَعْضٍ ظَهِيرًا٨٨
Qul laini ijtamaʿati alinsu waaljinnu ʿala an yatoo bimithli hatha alqurani la yatoona bimithlihi walaw kana baʿduhum libaʿdin thaheeran
Ka ce: "Lalle ne idan mutãne da aljannu sun tãru a kan su zo da misãlin wannan Alƙur'ãni bã zã su zo da misãlinsa ba, kuma kõ dã sãshinsu yã kasance, mataimaki ga sãshi."
-
وَلَقَدْ صَرَّفْنَا لِلنَّاسِ فِى هَـٰذَا ٱلْقُرْءَانِ مِن كُلِّ مَثَلٍ فَأَبَىٰٓ أَكْثَرُ ٱلنَّاسِ إِلَّا كُفُورًا٨٩
Walaqad sarrafna lilnnasi fee hatha alqurani min kulli mathalin faaba aktharu alnnasi illa kufooran
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun caccanza dõmin mutãne, a cikin wannan Alƙur'ãni, daga kõwane misãli sai mafi yawan mutãne suka ƙi (kõme) fãce kãfirci,
-
وَقَالُوا۟ لَن نُّؤْمِنَ لَكَ حَتَّىٰ تَفْجُرَ لَنَا مِنَ ٱلْأَرْضِ يَنۢبُوعًا٩٠
Waqaloo lan numina laka hatta tafjura lana mina alardi yanbooʿan
Kuma suka ce: "Bã zã mu yi ĩmãni ba dõminka sai kã ɓuɓɓugar1 da idan ruwa daga ƙasa.
Bayanai
[1] Kãfiri bã ya iya hangen abinda bã a iya taɓa shi da gaɓoɓin ji na jiki, dõmin haka suka nemi ɗayan waɗannan abũbuwa ya auku kãmin su yi ĩmãni. Mũmini yanã kange da ganin basĩra, dõmin haka ya wadãtu da zaman Alƙur'ani ãyã mai isa ga ya yi ĩmãni da shi. -
أَوْ تَكُونَ لَكَ جَنَّةٌ مِّن نَّخِيلٍ وَعِنَبٍ فَتُفَجِّرَ ٱلْأَنْهَـٰرَ خِلَـٰلَهَا تَفْجِيرًا٩١
Aw takoona laka jannatun min nakheelin waʿinabin fatufajjira alanhara khilalaha tafjeeran
"Kõ kuma wata gõna daga dabĩnai da inabi ta kasance a gare ka. Sa'an nan ka ɓuɓɓugar da ƙõramu a tsakãninta ɓuɓɓugarwa."
-
أَوْ تُسْقِطَ ٱلسَّمَآءَ كَمَا زَعَمْتَ عَلَيْنَا كِسَفًا أَوْ تَأْتِىَ بِٱللَّهِ وَٱلْمَلَـٰٓئِكَةِ قَبِيلًا٩٢
Aw tusqita alssamaa kama zaʿamta ʿalayna kisafan aw tatiya biAllahi waalmalaikati qabeelan
"Kõ kuwa ka kãyar da sama a kanmu kaɓukka kõ kuwa ka zo da Allah, da malã'iku banga-banga."
-
أَوْ يَكُونَ لَكَ بَيْتٌ مِّن زُخْرُفٍ أَوْ تَرْقَىٰ فِى ٱلسَّمَآءِ وَلَن نُّؤْمِنَ لِرُقِيِّكَ حَتَّىٰ تُنَزِّلَ عَلَيْنَا كِتَـٰبًا نَّقْرَؤُهُۥ ۗ قُلْ سُبْحَانَ رَبِّى هَلْ كُنتُ إِلَّا بَشَرًا رَّسُولًا٩٣
Aw yakoona laka baytun min zukhrufin aw tarqa fee alssamai walan numina liruqiyyika hatta tunazzila ʿalayna kitaban naqraohu qul subhana rabbee hal kuntu illa basharan rasoolan
"Kõ kuwa wani gida na zĩnãriya ya kasance a gare ka, kõ kuwa ka tãka a cikin sama. Kuma bã zã mu yi ĩmãni ba ga tãkawarka, sai ka sassaukõ da wani littãfi a kanmu, munã karantã shi." Ka ce: "Tsarki ya tabbata ga Ubangijĩna! Ban kasance ba fãce mutum, Manzo."
-
وَمَا مَنَعَ ٱلنَّاسَ أَن يُؤْمِنُوٓا۟ إِذْ جَآءَهُمُ ٱلْهُدَىٰٓ إِلَّآ أَن قَالُوٓا۟ أَبَعَثَ ٱللَّهُ بَشَرًا رَّسُولًا٩٤
Wama manaʿa alnnasa an yuminoo ith jaahumu alhuda illa an qaloo abaʿatha Allahu basharan rasoolan
Kuma bãbu abin da ya hana mutãne su yi ĩmãni, a lõkacin da shiriya ta jẽ musu, fãce sunce, "Shin, Allah zai aiko mutum ya zamo yana Manzo."
-
قُل لَّوْ كَانَ فِى ٱلْأَرْضِ مَلَـٰٓئِكَةٌ يَمْشُونَ مُطْمَئِنِّينَ لَنَزَّلْنَا عَلَيْهِم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ مَلَكًا رَّسُولًا٩٥
Qul law kana fee alardi malaikatun yamshoona mutmainneena lanazzalna ʿalayhim mina alssamai malakan rasoolan
Ka ce: "Dã malã'iku sun kasance a cikin ƙasa, kuma sunã tafiya, sunã masu natsuwa, lalle ne dã mun saukar da malã'ika daga sama ya zama manzo a kansu."
-
قُلْ كَفَىٰ بِٱللَّهِ شَهِيدًۢا بَيْنِى وَبَيْنَكُمْ ۚ إِنَّهُۥ كَانَ بِعِبَادِهِۦ خَبِيرًۢا بَصِيرًا٩٦
Qul kafa biAllahi shaheedan baynee wabaynakum innahu kana biʿibadihi khabeeran baseeran
Ka ce: "Allah Yã isa zama shaida a tsakãnina da ku. Lalle Shi Ya kasance ga bãyinsa, mai ƙididdigewa ne Mai gani."
-
وَمَن يَهْدِ ٱللَّهُ فَهُوَ ٱلْمُهْتَدِ ۖ وَمَن يُضْلِلْ فَلَن تَجِدَ لَهُمْ أَوْلِيَآءَ مِن دُونِهِۦ ۖ وَنَحْشُرُهُمْ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ عَلَىٰ وُجُوهِهِمْ عُمْيًا وَبُكْمًا وَصُمًّا ۖ مَّأْوَىٰهُمْ جَهَنَّمُ ۖ كُلَّمَا خَبَتْ زِدْنَـٰهُمْ سَعِيرًا٩٧
Waman yahdi Allahu fahuwa almuhtadi waman yudlil falan tajida lahum awliyaa min doonihi wanahshuruhum yawma alqiyamati ʿala wujoohihim ʿumyan wabukman wasumman mawahum jahannamu kullama khabat zidnahum saʿeeran
Kuma wanda Allah Ya shiryar, to, shĩ ne shiryayye, kuma wanda Ya ɓatar to bã zã ka sãmi waɗansu masõya gare su ba baicinSa. Kuma Munã tãra su a Rãnar ¡iyãma a kan fuskõkinsu, sunã makãfi, kuma bẽbãye da kurãme. Matattararsu Jahannama ce, kõ da yaushe ta bice, sai Mu ƙãra musu wata wuta mai tsanani.
-
ذَٰلِكَ جَزَآؤُهُم بِأَنَّهُمْ كَفَرُوا۟ بِـَٔايَـٰتِنَا وَقَالُوٓا۟ أَءِذَا كُنَّا عِظَـٰمًا وَرُفَـٰتًا أَءِنَّا لَمَبْعُوثُونَ خَلْقًا جَدِيدًا٩٨
Thalika jazaohum biannahum kafaroo biayatina waqaloo aitha kunna ʿithaman warufatan ainna lamabʿoothoona khalqan jadeedan
Wancan ne sãkamakonsu sabõda lalle sũ, sun kãfirta da ãyõ yinMu, kuma suka ce: "Shin idan muka kasance ƙasũsuwa da nĩƙaƙƙun gaɓũɓuwa, shin lalle mũ, haƙĩ ka, waɗanda ake tãyarwa ne a cikin wata halitta sãbuwa?"
-
۞ أَوَلَمْ يَرَوْا۟ أَنَّ ٱللَّهَ ٱلَّذِى خَلَقَ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضَ قَادِرٌ عَلَىٰٓ أَن يَخْلُقَ مِثْلَهُمْ وَجَعَلَ لَهُمْ أَجَلًا لَّا رَيْبَ فِيهِ فَأَبَى ٱلظَّـٰلِمُونَ إِلَّا كُفُورًا٩٩
Awalam yaraw anna Allaha allathee khalaqa alssamawati waalarda qadirun ʿala an yakhluqa mithlahum wajaʿala lahum ajalan la rayba feehi faaba alththalimoona illa kufooran
Shin, kuma ba su ganĩ1 ba (cẽwa) lalle ne Allah, wandaYa halicci sammai da ƙasa, Mai ikon yi ne a kan Ya halicci misãlinsu? Kuma Ya sanya wani ajali wanda bãbu kõkwanto a cikinsa? Sai azzãlumai suka ƙi fãce kãfirci.
Bayanai
[1] Muƙãrana a tsakãnin farkon halitta da mayarwa da ita, idan fãrãwa ba ta buwãya ba, mayarwa bã zã ta buwãya ba. -
قُل لَّوْ أَنتُمْ تَمْلِكُونَ خَزَآئِنَ رَحْمَةِ رَبِّىٓ إِذًا لَّأَمْسَكْتُمْ خَشْيَةَ ٱلْإِنفَاقِ ۚ وَكَانَ ٱلْإِنسَـٰنُ قَتُورًا١٠٠
Qul law antum tamlikoona khazaina rahmati rabbee ithan laamsaktum khashyata alinfaqi wakana alinsanu qatooran
Ka ce: "Dã dai kũ, kunã mallakar1 taskõkin rahamar Ubangijĩna, a lõkacin, haƙĩƙa dã kun kãme dõmin tsõron ƙãrẽwar taskõkin. Kuma mutum yã kasance mai ƙwauro ne."
Bayanai
[1] Muƙãrana a tsakãnin kyautar mutum da rõwarsa ga dũkiyar da ya mallaka. -
وَلَقَدْ ءَاتَيْنَا مُوسَىٰ تِسْعَ ءَايَـٰتٍۭ بَيِّنَـٰتٍ ۖ فَسْـَٔلْ بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ إِذْ جَآءَهُمْ فَقَالَ لَهُۥ فِرْعَوْنُ إِنِّى لَأَظُنُّكَ يَـٰمُوسَىٰ مَسْحُورًا١٠١
Walaqad atayna moosa tisʿa ayatin bayyinatin faisal banee israeela ith jaahum faqala lahu firʿawnu innee laathunnuka ya moosa mashooran
Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun bai wa Mũsã ãyõyi1 guda tara bayyanannu, sai ka tambayi Banĩ Isrã'ila, a lõkacin da ya jẽ musu, sai Fir'auna ya ce masa, "Lalle nĩ, inã zaton ka, ya Mũsã, sihirtacce."
Bayanai
[1] Muƙãrana a tsakãnin maganar makangari Fir'auna da Manzon Allah, Mũsã dõmin nũna ãyar Annabãwa ba su tsõron kõwa wajen iyar da Manzancin Allah, kuma bã su ganin wani ƙarfi a gabansu fãce na Allah. -
قَالَ لَقَدْ عَلِمْتَ مَآ أَنزَلَ هَـٰٓؤُلَآءِ إِلَّا رَبُّ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ بَصَآئِرَ وَإِنِّى لَأَظُنُّكَ يَـٰفِرْعَوْنُ مَثْبُورًا١٠٢
Qala laqad ʿalimta ma anzala haolai illa rabbu alssamawati waalardi basaira wainnee laathunnuka ya firʿawnu mathbooran
Ya ce: "lalle ne haƙĩƙa ka sani bãbu wanda ya saukar da waɗannan, fãce Ubangijin sammai da ƙasa dõmĩn su zama abũbuwan lũra. Kuma lalle ne ni, haƙĩƙa, ina zaton ka, yã Fir'auna, halakakke."
-
فَأَرَادَ أَن يَسْتَفِزَّهُم مِّنَ ٱلْأَرْضِ فَأَغْرَقْنَـٰهُ وَمَن مَّعَهُۥ جَمِيعًا١٠٣
Faarada an yastafizzahum mina alardi faaghraqnahu waman maʿahu jameeʿan
Sai ya yi nufin fitar da su daga ƙasar, sai Muka nutsar da shi, shi da wanda yake tãre da shi gabã ɗaya.
-
وَقُلْنَا مِنۢ بَعْدِهِۦ لِبَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ ٱسْكُنُوا۟ ٱلْأَرْضَ فَإِذَا جَآءَ وَعْدُ ٱلْـَٔاخِرَةِ جِئْنَا بِكُمْ لَفِيفًا١٠٤
Waqulna min baʿdihi libanee israeela oskunoo alarda faitha jaa waʿdu alakhirati jina bikum lafeefan
Kuma Muka ce: daga bãyansa ga Banĩ Isrã'ĩla, "Ku zauni ƙasar. Sa'an nan idan wa'adin ƙarshe ya zo, zã Mu jẽ da ku jama'a-jama'a."1
Bayanai
[1] Wannan magana tanã kamã da da'awar Yahũdu cewa yanã rubuce a cikin littãfinsu za su kõma haɗuwa bãyan rarraba a nan dũniya kuma Hadĩsin kõmawar Yahũdu a Falasɗĩnu, har Musulmi su yi yãƙi da su, sunã a kan gãɓar gabas kuma su Yahũdãwa suna a kan gãɓar yamma daga Kõgin Urdun yanã ƙarfafa wannan ra'ayi. Kuma an ruwaito cewa daga cikin alãmõmin Tãshin Ƙiyãma akwai kõmãwar Yahũdu a Falasɗinu. Allah ne Mafi sani. -
وَبِٱلْحَقِّ أَنزَلْنَـٰهُ وَبِٱلْحَقِّ نَزَلَ ۗ وَمَآ أَرْسَلْنَـٰكَ إِلَّا مُبَشِّرًا وَنَذِيرًا١٠٥
Wabialhaqqi anzalnahu wabialhaqqi nazala wama arsalnaka illa mubashshiran wanatheeran
Kuma da gaskiya Muka saukar da shi, kuma da gaskiya ya sauka. Kuma ba Mu aike ka ba fãce kanã mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi.
-
وَقُرْءَانًا فَرَقْنَـٰهُ لِتَقْرَأَهُۥ عَلَى ٱلنَّاسِ عَلَىٰ مُكْثٍ وَنَزَّلْنَـٰهُ تَنزِيلًا١٠٦
Waquranan faraqnahu litaqraahu ʿala alnnasi ʿala mukthin wanazzalnahu tanzeelan
Kuma yanã abin karãtu Mun rarraba shi dõmin ka karanta shi ga mutane a kan jinkiri kuma Mun sassaukar da shi sassaukarwa.1
Bayanai
[1] Saukar da Alƙur'ãni a cikin shekaru ashirin ko ashirin da uku ya yi kama da saukar ãyõyin Mũsã tãre a lõkacin da yake kiran Fir'auna zuwa ga addini. -
قُلْ ءَامِنُوا۟ بِهِۦٓ أَوْ لَا تُؤْمِنُوٓا۟ ۚ إِنَّ ٱلَّذِينَ أُوتُوا۟ ٱلْعِلْمَ مِن قَبْلِهِۦٓ إِذَا يُتْلَىٰ عَلَيْهِمْ يَخِرُّونَ لِلْأَذْقَانِ سُجَّدًا١٠٧
Qul aminoo bihi aw la tuminoo inna allatheena ootoo alʿilma min qablihi itha yutla ʿalayhim yakhirroona lilathqani sujjadan
Ka ce: "Ku yi ĩmãni1 da Shi, ko kuwa kada ku yi ĩmãni, lalle ne waɗanda aka bai wa ilmi daga gabãninsa, idan anã karãtunsa a kansu, sunã fãɗuwa ga haɓõɓinsu, sunã mãsu sujada."
Bayanai
[1] Muƙãranar yin ĩmãni da rashin ĩmãnin mutãne ga Alƙur'ãni ba zai rage gaskiyarsa da kõme ba, sai dai waɗanda suka ƙi ĩmãnin ne zã su cũtu, sa'an nan da bambanci a tsakãnin mai ilmi da jãhili. Mai ilmi yanã da sauƙin jãwuwa zuwa ga gaskiya har ya rasa abin da zai aikata fãce ya fãɗi rikice, a kan haɓarsa, yanã mayar da al'amari ga Allah kuma yanã tawali'u. -
وَيَقُولُونَ سُبْحَـٰنَ رَبِّنَآ إِن كَانَ وَعْدُ رَبِّنَا لَمَفْعُولًا١٠٨
Wayaqooloona subhana rabbina in kana waʿdu rabbina lamafʿoolan
"Kuma sunã cẽwa: Tsarki ya tabbata ga Ubangijinmu! Lalle ne wa'adin Ubangijinmu ya kasance, haƙĩƙa, abin aikatãwa."
-
وَيَخِرُّونَ لِلْأَذْقَانِ يَبْكُونَ وَيَزِيدُهُمْ خُشُوعًا ۩١٠٩
Wayakhirroona lilathqani yabkoona wayazeeduhum khushooʿan
Kuma sunã fãɗuwa ga haɓõɓinsu sunã kũka, kuma yanã ƙara musu tsõro.
-
قُلِ ٱدْعُوا۟ ٱللَّهَ أَوِ ٱدْعُوا۟ ٱلرَّحْمَـٰنَ ۖ أَيًّا مَّا تَدْعُوا۟ فَلَهُ ٱلْأَسْمَآءُ ٱلْحُسْنَىٰ ۚ وَلَا تَجْهَرْ بِصَلَاتِكَ وَلَا تُخَافِتْ بِهَا وَٱبْتَغِ بَيْنَ ذَٰلِكَ سَبِيلًا١١٠
Quli odʿoo Allaha awi odʿoo alrrahmana ayyan ma tadʿoo falahu alasmao alhusna wala tajhar bisalatika wala tukhafit biha waibtaghi bayna thalika sabeelan
Ka ce: "Ku kirayi Allah1 kõ kuwa ku kirãyi Mai rahama. Kõwane kuka kira to Yanã da sũnãye mafi kyau. Kuma, kada ka bayyana2 ga sallarka, kuma kada ka ɓõye ta. Ka nẽmi hanya a tsakãnin wancan."
Bayanai
[1] Muƙarana a tsakãnin sũnayen Allah waɗanda ake kiran sa da su wajen rõƙo da waɗanda bã a yin roko da su. Sũnãyen mafiya kyau da ake kiran Allah da su Hadĩsi ya kãwo su sai a nħma daga Jalãlaini. [2] Kuma tsakaitãwa wajen karãtun salla ko addu'a kamar yadda aikin Annabi ya nũna yadda ake yi, kada a bayyana kada a ɓõye. Sai dai tsaka. -
وَقُلِ ٱلْحَمْدُ لِلَّهِ ٱلَّذِى لَمْ يَتَّخِذْ وَلَدًا وَلَمْ يَكُن لَّهُۥ شَرِيكٌ فِى ٱلْمُلْكِ وَلَمْ يَكُن لَّهُۥ وَلِىٌّ مِّنَ ٱلذُّلِّ ۖ وَكَبِّرْهُ تَكْبِيرًۢا١١١
Waquli alhamdu lillahi allathee lam yattakhith waladan walam yakun lahu shareekun fee almulki walam yakun lahu waliyyun mina alththulli wakabbirhu takbeeran
Kuma ka ce: "Gõdiyã1 ta tabbata ga Allah wanda bai riƙi ɗã ba kuma abõkin tãrayya bai kasance a gare Shi ba a cikin mulkinSa, kuma wani masõyi sabõda wulãkancin bai kasance a gare Shi ba." Kuma ka girmama Shi, girmamãwa.
Bayanai
[1] Ka ce: "Allah ba Shi da abõkin muƙãrana a kõwace jiha. Shi kaɗai Ya cancanci girmamãwa." Sabõda haka ka girmama Shi, girmãmãwar da ta dãce da Shi.
Tambayoyin da ake yawan yi
Mece ce ma’anar sunan Suratul Isra’i?
Ma’anar Isra’i ita ce “Tafiyar dare”.
Suratul Isra’i tana cikin juz’i na nawa?
Suratul Isra’i tana cikin juz’i na 15.
Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Isra’i?
Suratul Isra’i tana da ayoyi 111.
Suratul Isra’i Makkiya ce ko Madaniya?
Suratul Isra’i sura ce Makkiya.
Suratul Isra’i ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?
Ita ce sura ta 17 a cikin Alƙur’ani.
Majiyoyi
- Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
- Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
- Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
- Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
- Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
- Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.
Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.