Suratul Maryam (مريم) ita ce sura ta 19 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 98. Sura ce Makkiya, wadda ta sauka a Makka kafin Hijira, kuma tana cikin juz’i na 16.
A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Maryam gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.
Suratul Maryam cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ
-
كٓهيعٓصٓ١
Kafhayaʿaynsad
K̃.H. Y.I. Ṣ̃.
-
ذِكْرُ رَحْمَتِ رَبِّكَ عَبْدَهُۥ زَكَرِيَّآ٢
Thikru rahmati rabbika ʿabdahu zakariyya
Ambaton rahamar Ubangijinka ne ga BawanSa Zakariyya.
-
إِذْ نَادَىٰ رَبَّهُۥ نِدَآءً خَفِيًّا٣
Ith nada rabbahu nidaan khafiyyan
A lõkacin da ya kirãyi Ubangijinsa, kira ɓõyayye.
-
قَالَ رَبِّ إِنِّى وَهَنَ ٱلْعَظْمُ مِنِّى وَٱشْتَعَلَ ٱلرَّأْسُ شَيْبًا وَلَمْ أَكُنۢ بِدُعَآئِكَ رَبِّ شَقِيًّا٤
Qala rabbi innee wahana alʿathmu minnee waishtaʿala alrrasu shayban walam akun biduʿaika rabbi shaqiyyan
Ya ce: "Yã Ubangijina! Lalle ne nĩ, ƙashi na daga gare ni ya yi rauni, kuma kaina ya kunnu da furfura, kuma ban kasance marashin arziki ba game da kiranKa, yã Ubangiji!"
-
وَإِنِّى خِفْتُ ٱلْمَوَٰلِىَ مِن وَرَآءِى وَكَانَتِ ٱمْرَأَتِى عَاقِرًا فَهَبْ لِى مِن لَّدُنكَ وَلِيًّا٥
Wainnee khiftu almawaliya min waraee wakanati imraatee ʿaqiran fahab lee min ladunka waliyyan
"Kuma lalle nĩ, na ji tsõron1 dangi a bãyãna, kuma mãtãta ta kasance bakarãriya! Sai ka bã ni wani mataimaki daga wajenKa."
Bayanai
[1] Amfãnin sãmu ɗã ga mutumin kirki shi ne dõmin ya gãji kirkin kuma ya taimaki sauran danginsa, ya rãyar da gida. Kuma wanda ba mutumin kirki ba yana yiwuwa ya sãmi ɗan kirki mai shiryar da shi zuwa ga hanyar ƙwarai. -
يَرِثُنِى وَيَرِثُ مِنْ ءَالِ يَعْقُوبَ ۖ وَٱجْعَلْهُ رَبِّ رَضِيًّا٦
Yarithunee wayarithu min ali yaʿqooba waijʿalhu rabbi radiyyan
"Ya gãjẽ ni, kuma ya yi gãdo daga gidan Yãƙũba. Kuma Ka sanya shi yardajje, yã Ubangiji!"
-
يَـٰزَكَرِيَّآ إِنَّا نُبَشِّرُكَ بِغُلَـٰمٍ ٱسْمُهُۥ يَحْيَىٰ لَمْ نَجْعَل لَّهُۥ مِن قَبْلُ سَمِيًّا٧
Ya zakariyya inna nubashshiruka bighulamin ismuhu yahya lam najʿal lahu min qablu samiyyan
(Allah Ya karɓa) "Yã zakariyya! Lalle ne Mũ, Munã yi maka bushãra da wani yãro, sunansa Yahaya. Ba Mu sanya masa wani takwara ba a gabãni."
-
قَالَ رَبِّ أَنَّىٰ يَكُونُ لِى غُلَـٰمٌ وَكَانَتِ ٱمْرَأَتِى عَاقِرًا وَقَدْ بَلَغْتُ مِنَ ٱلْكِبَرِ عِتِيًّا٨
Qala rabbi anna yakoonu lee ghulamun wakanati imraatee ʿaqiran waqad balaghtu mina alkibari ʿitiyyan
Ya ce: "Yã Ubangijĩna! Yãya wani yãro zai kasance a gare ni, alhãli kuwa mãtãta ta kasance bakarãriya, kuma gã shi nã kai ga matuƙa ta tsũfa?"
-
قَالَ كَذَٰلِكَ قَالَ رَبُّكَ هُوَ عَلَىَّ هَيِّنٌ وَقَدْ خَلَقْتُكَ مِن قَبْلُ وَلَمْ تَكُ شَيْـًٔا٩
Qala kathalika qala rabbuka huwa ʿalayya hayyinun waqad khalaqtuka min qablu walam taku shayan
Ya ce: "Kamar wancan Ubangijinka Ya ce. Shĩ, a gare Ni mai sauƙi ne, kuma haƙĩƙa Na halitta ka a gabãnin haka, alhãli ba ka kasance kõme ba."
-
قَالَ رَبِّ ٱجْعَل لِّىٓ ءَايَةً ۚ قَالَ ءَايَتُكَ أَلَّا تُكَلِّمَ ٱلنَّاسَ ثَلَـٰثَ لَيَالٍ سَوِيًّا١٠
Qala rabbi ijʿal lee ayatan qala ayatuka alla tukallima alnnasa thalatha layalin sawiyyan
Ya ce: "Yã Ubangijina! Ka sanya mini alãma." Ya ce: "Alamarka ita ce ka kãsa yi wa mutãne magana a darũruwa uku daidai."
-
فَخَرَجَ عَلَىٰ قَوْمِهِۦ مِنَ ٱلْمِحْرَابِ فَأَوْحَىٰٓ إِلَيْهِمْ أَن سَبِّحُوا۟ بُكْرَةً وَعَشِيًّا١١
Fakharaja ʿala qawmihi mina almihrabi faawha ilayhim an sabbihoo bukratan waʿashiyyan
Sai ya fita ga mutãnensa daga masallãci, sa'an nan ya yi ishãra zuwa gare su da cẽwa, "Ku yi tasbĩhi sãfe da yamma."
-
يَـٰيَحْيَىٰ خُذِ ٱلْكِتَـٰبَ بِقُوَّةٍ ۖ وَءَاتَيْنَـٰهُ ٱلْحُكْمَ صَبِيًّا١٢
Ya yahya khuthi alkitaba biquwwatin waataynahu alhukma sabiyyan
Yã kai Yahaya! Ka kãma littãfi da ƙarfi. Kuma Muka bã shi hukunci yanã yãro.1
Bayanai
[1] Yahaya dan zakariyya, shi ne Annabi da aka bai wa hukunci tun yanã yãro. Kuma Shĩ ne mai bãyar da bushãra da Ĩsa, amincin Allah ya tabbata agare su. -
وَحَنَانًا مِّن لَّدُنَّا وَزَكَوٰةً ۖ وَكَانَ تَقِيًّا١٣
Wahananan min ladunna wazakatan wakana taqiyyan
Kuma (Muka sanya shi) abin girmamãwa daga gun Mu, kuma mai albarka, kuma ya kasance mai ɗã'ã da taƙawa.
-
وَبَرًّۢا بِوَٰلِدَيْهِ وَلَمْ يَكُن جَبَّارًا عَصِيًّا١٤
Wabarran biwalidayhi walam yakun jabbaran ʿasiyyan
Kuma mai biyayya ga mahaifan sa biyu, kuma bai kasance mai girman kai mai sãɓo ba.
-
وَسَلَـٰمٌ عَلَيْهِ يَوْمَ وُلِدَ وَيَوْمَ يَمُوتُ وَيَوْمَ يُبْعَثُ حَيًّا١٥
Wasalamun ʿalayhi yawma wulida wayawma yamootu wayawma yubʿathu hayyan
Kuma aminci ya tabbata a gare shi a rãnar da aka haife shi da rãnar da yake mutuwa da rãnar da ake tãyar da shi yanã mai rai.
-
وَٱذْكُرْ فِى ٱلْكِتَـٰبِ مَرْيَمَ إِذِ ٱنتَبَذَتْ مِنْ أَهْلِهَا مَكَانًا شَرْقِيًّا١٦
Waothkur fee alkitabi maryama ithi intabathat min ahliha makanan sharqiyyan
Kuma ka ambaci Maryamu1 a cikin Littãfi, a lõkacin da ta tsallake daga mutãnenta a wani wuri, a gẽfen gabas.
Bayanai
[1] An fãra da ƙissar Maryamu dõmin a nũna sakamakon da aka yi mata da sãmun ɗan kirki sabõda kasancewarta mutumiyar kirki, kuma da nũna cewa Annabi Ĩsa bã ɗan Allah ba ne. -
فَٱتَّخَذَتْ مِن دُونِهِمْ حِجَابًا فَأَرْسَلْنَآ إِلَيْهَا رُوحَنَا فَتَمَثَّلَ لَهَا بَشَرًا سَوِيًّا١٧
Faittakhathat min doonihim hijaban faarsalna ilayha roohana fatamaththala laha basharan sawiyyan
Sa'an nan ta riƙi wani shãmaki daga barinsu. Sai Muka aika rũhinMu zuwa gare ta. Sai ya bayyana a gare ta da siffar mutum madaidaci.
-
قَالَتْ إِنِّىٓ أَعُوذُ بِٱلرَّحْمَـٰنِ مِنكَ إِن كُنتَ تَقِيًّا١٨
Qalat innee aʿoothu bialrrahmani minka in kunta taqiyyan
Ta ce: "Lalle nĩ inã nẽman tsari ga Mai, rahama daga gare ka, idan ka kasance mai tsaron addini!"
-
قَالَ إِنَّمَآ أَنَا۠ رَسُولُ رَبِّكِ لِأَهَبَ لَكِ غُلَـٰمًا زَكِيًّا١٩
Qala innama ana rasoolu rabbiki liahaba laki ghulaman zakiyyan
Ya ce: "Abin sani kawai, ni Manzon Ubangijinki ne dõmin in bãyar da wani yãro tsarkakke gare ki."
-
قَالَتْ أَنَّىٰ يَكُونُ لِى غُلَـٰمٌ وَلَمْ يَمْسَسْنِى بَشَرٌ وَلَمْ أَكُ بَغِيًّا٢٠
Qalat anna yakoonu lee ghulamun walam yamsasnee basharun walam aku baghiyyan
Ta ce: "A inã yãro zai kasance a gare ni alhãli kuwa wani mutum bai shãfe ni ba, kuma ban kasance kãruwa ba?"
-
قَالَ كَذَٰلِكِ قَالَ رَبُّكِ هُوَ عَلَىَّ هَيِّنٌ ۖ وَلِنَجْعَلَهُۥٓ ءَايَةً لِّلنَّاسِ وَرَحْمَةً مِّنَّا ۚ وَكَانَ أَمْرًا مَّقْضِيًّا٢١
Qala kathaliki qala rabbuki huwa ʿalayya hayyinun walinajʿalahu ayatan lilnnasi warahmatan minna wakana amran maqdiyyan
Ya ce: "Kamar wancan Ubangijinki Ya ce. Shĩ, a gare Ni mai sauƙi1 ne. Kuma dõmin Mu sanya shi wata alãma ga mutãne, kuma wata rahama ce daga gare Mu.' Kuma abin yã kasance wani al'amari hukuntacce."
Bayanai
[1] Malã'ikin da ya je ga Maryama a cikin sũrar mutum jibrĩlu ne Yã hũra a cikin wuyan rĩgarta, sai ta yi ciki da Ĩsa. -
۞ فَحَمَلَتْهُ فَٱنتَبَذَتْ بِهِۦ مَكَانًا قَصِيًّا٢٢
Fahamalathu faintabathat bihi makanan qasiyyan
Sai ta yi cikinsa, sai ta tsallake da shi ga wani wuri mai nĩsa.
-
فَأَجَآءَهَا ٱلْمَخَاضُ إِلَىٰ جِذْعِ ٱلنَّخْلَةِ قَالَتْ يَـٰلَيْتَنِى مِتُّ قَبْلَ هَـٰذَا وَكُنتُ نَسْيًا مَّنسِيًّا٢٣
Faajaaha almakhadu ila jithʿi alnnakhlati qalat ya laytanee mittu qabla hatha wakuntu nasyan mansiyyan
Sai nãƙuda ta kai ta zuwa ga wani kututturen dabĩniya, ta ce "Kaitona, dã dai na mutu a gabãnin wannan kuma na kasance wani abu wulakantacce wanda aka manta!"
-
فَنَادَىٰهَا مِن تَحْتِهَآ أَلَّا تَحْزَنِى قَدْ جَعَلَ رَبُّكِ تَحْتَكِ سَرِيًّا٢٤
Fanadaha min tahtiha alla tahzanee qad jaʿala rabbuki tahtaki sariyyan
Sai (yãron da ta haifa) ya1 kira ta daga ƙarƙashinta, "Kada ki yi baƙin ciki! Haƙĩƙa Ubangijinki Ya sanya wani marmaro a ƙarƙashinki.
Bayanai
[1] Annabi Ĩsã, amincin Allah ya tabbata a gare shi, ya fãra magana ga uwarsa tun a lõkacin da aka haife shi yanã a ƙarƙashin uwarsa. Gudãnar ruwan marmaro a ƙarƙashinta da fitar da 'ya'yan dabĩno dagakututturen dabĩno, alãmu ne mãsu nũna cħwa Allah nã iya halitta jãrĩri bã da uba ba, kuma Yanã tãyar da matattu daga kabarinsu bã da wata wahala ba. -
وَهُزِّىٓ إِلَيْكِ بِجِذْعِ ٱلنَّخْلَةِ تُسَـٰقِطْ عَلَيْكِ رُطَبًا جَنِيًّا٢٥
Wahuzzee ilayki bijithʿi alnnakhlati tusaqit ʿalayki rutaban janiyyan
"Kuma ki girgiza zuwa gare ki game da kututturen dabĩnon ya zuba a kanki yanã 'ya'yan dabĩno, ruɗabi nunannu."
-
فَكُلِى وَٱشْرَبِى وَقَرِّى عَيْنًا ۖ فَإِمَّا تَرَيِنَّ مِنَ ٱلْبَشَرِ أَحَدًا فَقُولِىٓ إِنِّى نَذَرْتُ لِلرَّحْمَـٰنِ صَوْمًا فَلَنْ أُكَلِّمَ ٱلْيَوْمَ إِنسِيًّا٢٦
Fakulee waishrabee waqarree ʿaynan faimma tarayinna mina albashari ahadan faqoolee innee nathartu lilrrahmani sawman falan okallima alyawma insiyyan
"Sai ki ci kuma ki sha kuma ki ji sanyi ga idãnunki1. To, idan kin ga wani aya daga mutãne, sai ki ce, 'Lalle nĩ, na yi alwãshin azumi dõmin Mai rahama sabõda haka bã zan yi wa wani mutum magana ba."
Bayanai
[1] Jin sanyi ga idãnu shĩ ne farin cikin sabõda sãmun haihuwa. Ga ibãdar Banĩ lsrã'ĩla, mai azumi bã ya yin magana, amma ga Musulunci Allah Ya shãfe wannan hukunci. Mai azumi yanã magana sai dai anã son ya kãma bãkinsa daga maganar da bã ta ibãda ba. -
فَأَتَتْ بِهِۦ قَوْمَهَا تَحْمِلُهُۥ ۖ قَالُوا۟ يَـٰمَرْيَمُ لَقَدْ جِئْتِ شَيْـًٔا فَرِيًّا٢٧
Faatat bihi qawmaha tahmiluhu qaloo ya maryamu laqad jiti shayan fariyyan
Sai ta je wa mutãnenta tanã auke da shi. Suka ce: "Yã Maryamu! Lalle ne, haƙĩƙa kin zo da wani abu mai girma!
-
يَـٰٓأُخْتَ هَـٰرُونَ مَا كَانَ أَبُوكِ ٱمْرَأَ سَوْءٍ وَمَا كَانَتْ أُمُّكِ بَغِيًّا٢٨
Ya okhta haroona ma kana abooki imraa sawin wama kanat ommuki baghiyyan
"Yã 'yar'uwar Hãrũna! Ubanki bai kasance mutumin alfãsha ba, kuma uwarki ba ta kasance kãruwa ba."
-
فَأَشَارَتْ إِلَيْهِ ۖ قَالُوا۟ كَيْفَ نُكَلِّمُ مَن كَانَ فِى ٱلْمَهْدِ صَبِيًّا٢٩
Faasharat ilayhi qaloo kayfa nukallimu man kana fee almahdi sabiyyan
Sai ta yi ishãra zuwa gare shi, suka ce: "Yãya zã mu yi magana da wanda ya kasance a cikin shimfiar tsumma yanã jãrĩri?"
-
قَالَ إِنِّى عَبْدُ ٱللَّهِ ءَاتَىٰنِىَ ٱلْكِتَـٰبَ وَجَعَلَنِى نَبِيًّا٣٠
Qala innee ʿabdu Allahi ataniya alkitaba wajaʿalanee nabiyyan
Ya ce: "Lalle ne, nĩ bãwan Allah ne Allah Yã bã ni Littãfi kuma Ya sanya ni Annabi."1
Bayanai
[1] Wannan ita ce maganar da Ĩsa ya yi wa mutãnen uwarsa dõmin ya barrantar da ita daga tuhuma, kuma ya nũna matsayinsa ga Allah da muƙãminsa na Annabci. -
وَجَعَلَنِى مُبَارَكًا أَيْنَ مَا كُنتُ وَأَوْصَـٰنِى بِٱلصَّلَوٰةِ وَٱلزَّكَوٰةِ مَا دُمْتُ حَيًّا٣١
Wajaʿalanee mubarakan ayna ma kuntu waawsanee bialssalati waalzzakati ma dumtu hayyan
"Kuma Yã sanya ni mai albarka a inda duk na kasance kuma Ya umurce ni da yin salla da zakka matuƙar inã da rai."
-
وَبَرًّۢا بِوَٰلِدَتِى وَلَمْ يَجْعَلْنِى جَبَّارًا شَقِيًّا٣٢
Wabarran biwalidatee walam yajʿalnee jabbaran shaqiyyan
"Kuma mai biyayya ga uwãta, kuma bai sanya ni mai kaushin zũciya ba marashin alhẽri."
-
وَٱلسَّلَـٰمُ عَلَىَّ يَوْمَ وُلِدتُّ وَيَوْمَ أَمُوتُ وَيَوْمَ أُبْعَثُ حَيًّا٣٣
Waalssalamu ʿalayya yawma wulidtu wayawma amootu wayawma obʿathu hayyan
"Kuma aminci ya tabbata a gare ni a rãnar da aka haife ni da rãnar da nake mutũwa da rãnar da ake tãyar da ni inã mai rai."
-
ذَٰلِكَ عِيسَى ٱبْنُ مَرْيَمَ ۚ قَوْلَ ٱلْحَقِّ ٱلَّذِى فِيهِ يَمْتَرُونَ٣٤
Thalika ʿeesa ibnu maryama qawla alhaqqi allathee feehi yamtaroona
Wancan ne Ĩsã ɗan Maryamu, maganar gaskiya wadda suke shakka a cikinta.
-
مَا كَانَ لِلَّهِ أَن يَتَّخِذَ مِن وَلَدٍ ۖ سُبْحَـٰنَهُۥٓ ۚ إِذَا قَضَىٰٓ أَمْرًا فَإِنَّمَا يَقُولُ لَهُۥ كُن فَيَكُونُ٣٥
Ma kana lillahi an yattakhitha min waladin subhanahu itha qada amran fainnama yaqoolu lahu kun fayakoonu
Bã ya kasancẽwa ga Allah Ya riƙi wani ɗã1. Tsarki ya tabbata a gare shi! Idan Yã hukunta wani al'amari sai kawai Ya ce masa, "Kasance." Sai ya dinga kasan cẽwa.
Bayanai
[1] Ba ya kasancewa ga Allah Ya riƙi ɗã, dõmin bã Ya mutuwa balle Ya yi bukãtar mai gãdo ga tsaron dũkiya. Shi kaɗai ne, bã Ya bukãtar wani ɗã mai tsaron dangi dõmin kada su bar hanya. -
وَإِنَّ ٱللَّهَ رَبِّى وَرَبُّكُمْ فَٱعْبُدُوهُ ۚ هَـٰذَا صِرَٰطٌ مُّسْتَقِيمٌ٣٦
Wainna Allaha rabbee warabbukum faoʿbudoohu hatha siratun mustaqeemun
"Kuma lalle Allah ne Ubangijina1 kuma Ubangijinku, sai ku bauta Masa. Wannan shi ne tafarki madaidaici."
Bayanai
[1] Tana a cikin maganar Ĩsã a lõkacin da ya girma yana wa'azi ga mutãnensa, sabõda haka aka raba ta da maganar farko a lõkacin da yake jãrĩri. -
فَٱخْتَلَفَ ٱلْأَحْزَابُ مِنۢ بَيْنِهِمْ ۖ فَوَيْلٌ لِّلَّذِينَ كَفَرُوا۟ مِن مَّشْهَدِ يَوْمٍ عَظِيمٍ٣٧
Faikhtalafa alahzabu min baynihim fawaylun lillatheena kafaroo min mashhadi yawmin ʿatheemin
Sai ƙungiyõyin1 suka sãɓã wa jũna a tsakãnins u. To, bõne ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta daga halartar yini mai girma.
Bayanai
[1] Bãyan ɗauke Annabin Allah Ĩsã ɗan Maryama ƙungiyõyin mutãne sun sãɓa wa jũnansu a cikin sha'aninsa. Yahũdu suna sũkar sa, Nasãra suka kasu uku: Nasũriyya suka ce: "Shi ɗan Allah ne" Malakaniyya suka ce: "Shi ne na uku ɗin uku," Ya'aƙũbiyya suka ce: "Shi ne Allah." Sabõda haka Nasara sukahaihaye kuma suka zurfafa, sa'an nan Yahũdu suka taƙaita kuma suka yi sũka gare shi. -
أَسْمِعْ بِهِمْ وَأَبْصِرْ يَوْمَ يَأْتُونَنَا ۖ لَـٰكِنِ ٱلظَّـٰلِمُونَ ٱلْيَوْمَ فِى ضَلَـٰلٍ مُّبِينٍ٣٨
Asmiʿ bihim waabsir yawma yatoonana lakini alththalimoona alyawma fee dalalin mubeenin
Mẽne ne ya yi jinsu1, kuma mẽne ne ya yi ganinsu a rãnar da suke zo Mana! Amma azzãlumai sunã a cikin ɓata bayyananna.
Bayanai
[1] A rãnar Lãhira a lõkacin da ake yi musu hisãbi a gaban Allah ganinsu da jinsu sunã da kyau ƙwarai, amma a nan dũniya sunã a cikin makanta da kurumci sabõda ɓatar da suka yi, suka ƙaryata Ĩsã, aminci ya tabbata a gare shi. -
وَأَنذِرْهُمْ يَوْمَ ٱلْحَسْرَةِ إِذْ قُضِىَ ٱلْأَمْرُ وَهُمْ فِى غَفْلَةٍ وَهُمْ لَا يُؤْمِنُونَ٣٩
Waanthirhum yawma alhasrati ith qudiya alamru wahum fee ghaflatin wahum la yuminoona
Kuma ka yi musu gargaɗi da rãnar nadãma a lõkacin da aka hukunta al'amari alhãli kuwa sunã a cikin ɓãta, kuma sũ bã su yin ĩmãni.
-
إِنَّا نَحْنُ نَرِثُ ٱلْأَرْضَ وَمَنْ عَلَيْهَا وَإِلَيْنَا يُرْجَعُونَ٤٠
Inna nahnu narithu alarda waman ʿalayha wailayna yurjaʿoona
Lalle ne Mũ, Mũ ne ke gãdon ƙasa1 da wanda yake a kanta, kuma zuwa gare Mu ake mayar da su.
Bayanai
[1]Tun da yake Mũ ke gãdon ƙasa da wanda yake a cikinta,bã zã Mu yi bukãtar sãmun wani magãji ba. -
وَٱذْكُرْ فِى ٱلْكِتَـٰبِ إِبْرَٰهِيمَ ۚ إِنَّهُۥ كَانَ صِدِّيقًا نَّبِيًّا٤١
Waothkur fee alkitabi ibraheema innahu kana siddeeqan nabiyyan
Kuma ambaci Ibrãhĩm1 a cikin Littafi. Lalle shi ya kasance mai yawan gaskatãwa, Annabi.
Bayanai
[1] Ibrãhĩm ya yi ƙõƙarin shiryar da ubansa, sai dai Allah bainufi shiryuwarsa ba. Daga cikin amfãnin haihuwa akwai abin haihuwa ya shiryar da mahaifinsa, ya yi masa nasĩha gwargwadon hãli. -
إِذْ قَالَ لِأَبِيهِ يَـٰٓأَبَتِ لِمَ تَعْبُدُ مَا لَا يَسْمَعُ وَلَا يُبْصِرُ وَلَا يُغْنِى عَنكَ شَيْـًٔا٤٢
Ith qala liabeehi ya abati lima taʿbudu ma la yasmaʿu wala yubsiru wala yughnee ʿanka shayan
A lõkacin da ya ce wa ubansa, "Yã bãba! Don me kake bauta wa abin da bã ya ji, kuma bã ya ga ni, kuma ba ya wadãtar da kõme daga barinka?"
-
يَـٰٓأَبَتِ إِنِّى قَدْ جَآءَنِى مِنَ ٱلْعِلْمِ مَا لَمْ يَأْتِكَ فَٱتَّبِعْنِىٓ أَهْدِكَ صِرَٰطًا سَوِيًّا٤٣
Ya abati innee qad jaanee mina alʿilmi ma lam yatika faittabiʿnee ahdika siratan sawiyyan
"Yã bãba! Lalle ni, haƙĩƙa abin da bai je maka ba na ilmi ya zo mini, sabõda haka ka bĩ ni in shiryar da kai wani tafarki madaidaici."
-
يَـٰٓأَبَتِ لَا تَعْبُدِ ٱلشَّيْطَـٰنَ ۖ إِنَّ ٱلشَّيْطَـٰنَ كَانَ لِلرَّحْمَـٰنِ عَصِيًّا٤٤
Ya abati la taʿbudi alshshaytana inna alshshaytana kana lilrrahmani ʿasiyyan
"Yã bãba! Kada ka bauta wa Shaiɗan. Lalle Shaiɗan ya kasance mai saɓãwa ga Mai rahama."
-
يَـٰٓأَبَتِ إِنِّىٓ أَخَافُ أَن يَمَسَّكَ عَذَابٌ مِّنَ ٱلرَّحْمَـٰنِ فَتَكُونَ لِلشَّيْطَـٰنِ وَلِيًّا٤٥
Ya abati innee akhafu an yamassaka ʿathabun mina alrrahmani fatakoona lilshshyatani waliyyan
"Yã bãba! Lalle ne ni inã tsõron wata azãba daga Mai rahama ta shãfe ka, har ka zama masõyi ga Shaiɗan."
-
قَالَ أَرَاغِبٌ أَنتَ عَنْ ءَالِهَتِى يَـٰٓإِبْرَٰهِيمُ ۖ لَئِن لَّمْ تَنتَهِ لَأَرْجُمَنَّكَ ۖ وَٱهْجُرْنِى مَلِيًّا٤٦
Qala araghibun anta ʿan alihatee ya ibraheemu lain lam tantahi laarjumannaka waohjurnee maliyyan
Ya ce: "Ashe, mai gudu ne kai daga gumãkãna? Yã Ibrãĩm! Lalle ne, idan ba ka hanu ba, haƙĩ ƙa, zan jẽfe ka. Kuma ka ƙaurace mini tun kanã mai mutunci."
-
قَالَ سَلَـٰمٌ عَلَيْكَ ۖ سَأَسْتَغْفِرُ لَكَ رَبِّىٓ ۖ إِنَّهُۥ كَانَ بِى حَفِيًّا٤٧
Qala salamun ʿalayka saastaghfiru laka rabbee innahu kana bee hafiyyan
Ya ce: "Aminci ya tabbata a gare ka! zan nẽmi Ubangijina Ya gãfarta maka.1 Lalle Shi Ya kasance Mai girmamãwa gare ni."
Bayanai
[1] Ibrãhĩm yã mayar da magana mai kyau da laushi da aminci ga maganar ubansa mai mũni da gautsi da tsõratarwa. Wannan yanã kõyar da yadda ake kira zuwa ga Allah da kuma yadda ya kamãta a tausasa wa uba kõ dã shi kãfiri ne. -
وَأَعْتَزِلُكُمْ وَمَا تَدْعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَأَدْعُوا۟ رَبِّى عَسَىٰٓ أَلَّآ أَكُونَ بِدُعَآءِ رَبِّى شَقِيًّا٤٨
Waaʿtazilukum wama tadʿoona min dooni Allahi waadʿoo rabbee ʿasa alla akoona biduʿai rabbee shaqiyyan
"Kuma inã nĩsantar ku da abin da kuke kira, baicin Allah kuma inã kiran Ubangijina, tsammãnin kada in zama marashin arziki game da kiran Ubangijina."
-
فَلَمَّا ٱعْتَزَلَهُمْ وَمَا يَعْبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَهَبْنَا لَهُۥٓ إِسْحَـٰقَ وَيَعْقُوبَ ۖ وَكُلًّا جَعَلْنَا نَبِيًّا٤٩
Falamma iʿtazalahum wama yaʿbudoona min dooni Allahi wahabna lahu ishaqa wayaʿqooba wakullan jaʿalna nabiyyan
To, sa'ad da ya nĩsance su da abin da suke bautãwa baicin Allah, Muka bã shi Is'hãƙa da Ya'aƙuba alhãli kuwa kõwanensu Mun mayar da shi Annabi.
-
وَوَهَبْنَا لَهُم مِّن رَّحْمَتِنَا وَجَعَلْنَا لَهُمْ لِسَانَ صِدْقٍ عَلِيًّا٥٠
Wawahabna lahum min rahmatina wajaʿalna lahum lisana sidqin ʿaliyyan
Kuma Muka yi musu kyauta daga Rahamar Mu, kuma Muka sanya musu harshen gaskiya1 maɗaukaki.
Bayanai
[1] Harshen gaskiya, shi ne yabo mai kyau daga Allah da mutãne. Wanda ya yankewa mutãnenSa dõmin Allah, to, zai sãka masa da waɗansu mutãnen kirki dõmin su ɗebe masa kewa. -
وَٱذْكُرْ فِى ٱلْكِتَـٰبِ مُوسَىٰٓ ۚ إِنَّهُۥ كَانَ مُخْلَصًا وَكَانَ رَسُولًا نَّبِيًّا٥١
Waothkur fee alkitabi moosa innahu kana mukhlasan wakana rasoolan nabiyyan
Kuma ka ambaci Mũsã a cikin Littãfi. Lalle ne shi, yã kasance zãɓaɓɓe, kuma yã kasance Manzo, Annabi.
-
وَنَـٰدَيْنَـٰهُ مِن جَانِبِ ٱلطُّورِ ٱلْأَيْمَنِ وَقَرَّبْنَـٰهُ نَجِيًّا٥٢
Wanadaynahu min janibi alttoori alaymani waqarrabnahu najiyyan
Kuma Muka kira shi daga gẽfen dũtse na dãma kuma Muka kusanta shi yanã abõkin gãnãwa.
-
وَوَهَبْنَا لَهُۥ مِن رَّحْمَتِنَآ أَخَاهُ هَـٰرُونَ نَبِيًّا٥٣
Wawahabna lahu min rahmatina akhahu haroona nabiyyan
Kuma Muka yi masa kyauta daga Rahamar Mu da ɗan'uwan sa Hãrũna, ya zama Annabi.
-
وَٱذْكُرْ فِى ٱلْكِتَـٰبِ إِسْمَـٰعِيلَ ۚ إِنَّهُۥ كَانَ صَادِقَ ٱلْوَعْدِ وَكَانَ رَسُولًا نَّبِيًّا٥٤
Waothkur fee alkitabi ismaʿeela innahu kana sadiqa alwaʿdi wakana rasoolan nabiyyan
Kuma ka ambaci Ismã'ila a cikin Littãfi. Lalle shi, yã kasance mai gaskiyar alkawari, kuma yã kasance Manzo, Annabi.
-
وَكَانَ يَأْمُرُ أَهْلَهُۥ بِٱلصَّلَوٰةِ وَٱلزَّكَوٰةِ وَكَانَ عِندَ رَبِّهِۦ مَرْضِيًّا٥٥
Wakana yamuru ahlahu bialssalati waalzzakati wakana ʿinda rabbihi mardiyyan
Kuma yã kasance yanã umurnin mutãnens1da salla da zakka. Kuma yã kasance yardajje a wurin Ubangijinsa.
Bayanai
[1] Mãtarsa da 'ya'yansa da Jurhum, yanã umurninsu da salla da zakka. Yanã wajaba ga mutum ya umurci iyalinsa da tsare haƙƙõƙin Allah. -
وَٱذْكُرْ فِى ٱلْكِتَـٰبِ إِدْرِيسَ ۚ إِنَّهُۥ كَانَ صِدِّيقًا نَّبِيًّا٥٦
Waothkur fee alkitabi idreesa innahu kana siddeeqan nabiyyan
Kuma ka ambaci Idrĩsa a cikin Littãfi. Lalle shi, ya kasance mai yawan gaskatãwa, Annabi.
-
وَرَفَعْنَـٰهُ مَكَانًا عَلِيًّا٥٧
Warafaʿnahu makanan ʿaliyyan
Muka ɗaukaka shi a wuri maɗaukaki.
-
أُو۟لَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ أَنْعَمَ ٱللَّهُ عَلَيْهِم مِّنَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ مِن ذُرِّيَّةِ ءَادَمَ وَمِمَّنْ حَمَلْنَا مَعَ نُوحٍ وَمِن ذُرِّيَّةِ إِبْرَٰهِيمَ وَإِسْرَٰٓءِيلَ وَمِمَّنْ هَدَيْنَا وَٱجْتَبَيْنَآ ۚ إِذَا تُتْلَىٰ عَلَيْهِمْ ءَايَـٰتُ ٱلرَّحْمَـٰنِ خَرُّوا۟ سُجَّدًا وَبُكِيًّا ۩٥٨
Olaika allatheena anʿama Allahu ʿalayhim mina alnnabiyyeena min thurriyyati adama wamimman hamalna maʿa noohin wamin thurriyyati ibraheema waisraeela wamimman hadayna waijtabayna itha tutla ʿalayhim ayatu alrrahmani kharroo sujjadan wabukiyyan
Waɗancan sũ ne waɗanda Allah Ya yi wa ni'ima daga Annabãwa daga zurriyar Ãdamu, kuma daga waɗanda muka ɗauka tãre da Nũhu, kuma daga zurriyar Ibrãhĩm da Isrã'ila, kuma daga waɗanda Muka shiryar kuma Muka zãɓe su. Idan anã karãtun ãyõyin Mai rahama a kansu, sai su fãɗi sunã mãsu sujada kuma mãsu kũka.
-
۞ فَخَلَفَ مِنۢ بَعْدِهِمْ خَلْفٌ أَضَاعُوا۟ ٱلصَّلَوٰةَ وَٱتَّبَعُوا۟ ٱلشَّهَوَٰتِ ۖ فَسَوْفَ يَلْقَوْنَ غَيًّا٥٩
Fakhalafa min baʿdihim khalfun adaʿoo alssalata waittabaʿoo alshshahawati fasawfa yalqawna ghayyan
Sai waɗansu 'yan bãya1 suka maye a bãyansu suka tõzarta salla, kuma suka bi sha'awõwinsu. To, da sannu zã su hau da wani sharri.
Bayanai
[1] An ruwaito cewa wannan zai auku a lõkacin Tãshin Ƙiyãma ne a bãyan tafiyar sãlihan wannan al'umma ta Muhammadu. Zã su dinga barbarar jũnansu a cikin hanyõyi. Su tõzarta salla, su gina manyan gidãje su hau dukan abin da aka hana su, su tufanci abin da aka hana su, Ƙurɗabi. -
إِلَّا مَن تَابَ وَءَامَنَ وَعَمِلَ صَـٰلِحًا فَأُو۟لَـٰٓئِكَ يَدْخُلُونَ ٱلْجَنَّةَ وَلَا يُظْلَمُونَ شَيْـًٔا٦٠
Illa man taba waamana waʿamila salihan faolaika yadkhuloona aljannata wala yuthlamoona shayan
Fãce wanda ya tũba, kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aiki na ƙwarai. To, waɗannan sunã shiga Aljanna, kuma bã a zãluntar su da kõme.
-
جَنَّـٰتِ عَدْنٍ ٱلَّتِى وَعَدَ ٱلرَّحْمَـٰنُ عِبَادَهُۥ بِٱلْغَيْبِ ۚ إِنَّهُۥ كَانَ وَعْدُهُۥ مَأْتِيًّا٦١
Jannati ʿadnin allatee waʿada alrrahmanu ʿibadahu bialghaybi innahu kana waʿduhu matiyyan
Gidãjen Aljannar zama wadda Mai rahama ya yi alkawarin bãyarwa ga bãyinSa (mãsu aikin ĩmãni) a fake. Lalle ne shĩ, alkawarin ya kasance abin riskuwa.
-
لَّا يَسْمَعُونَ فِيهَا لَغْوًا إِلَّا سَلَـٰمًا ۖ وَلَهُمْ رِزْقُهُمْ فِيهَا بُكْرَةً وَعَشِيًّا٦٢
La yasmaʿoona feeha laghwan illa salaman walahum rizquhum feeha bukratan waʿashiyyan
Bã su jin yasassar magana a cikinta, fãce sallama. Kuma sunã da abinci, a cikinta, sãfe da maraice.
-
تِلْكَ ٱلْجَنَّةُ ٱلَّتِى نُورِثُ مِنْ عِبَادِنَا مَن كَانَ تَقِيًّا٦٣
Tilka aljannatu allatee noorithu min ʿibadina man kana taqiyyan
Wancan Aljannar ce wadda Muke gãdar da wanda ya kasance mai aiki da taƙawa daga bãyiNa.
-
وَمَا نَتَنَزَّلُ إِلَّا بِأَمْرِ رَبِّكَ ۖ لَهُۥ مَا بَيْنَ أَيْدِينَا وَمَا خَلْفَنَا وَمَا بَيْنَ ذَٰلِكَ ۚ وَمَا كَانَ رَبُّكَ نَسِيًّا٦٤
Wama natanazzalu illa biamri rabbika lahu ma bayna aydeena wama khalfana wama bayna thalika wama kana rabbuka nasiyyan
(Sunã mãsu cẽwa) "Kuma bã mu sauka1 Fãce da umuruin Ubangijinka (Muhammad). Shĩ ne da mulkin abin da ke a gaba gare mu da abin da ke a bãyanmu da abin da ke a tsakãnin wannan." Kuma2 (Ubangijinka bai kasance wanda ake mantãwa ba.
Bayanai
[1] 'Yan Aljanna sunã cewa ba mu sauka a waɗannan gidãje ba sai da umurnin Ubangijinka, kai mai karatu, A1lahne Mai mallakar kõme, kuma kõme ãyã ne mai nũni zuwa gare shi, sabõda haka bã a mantãwa da shi. [2] Maganar Allah ce a bãyan maganar 'yan Aljanna dõmin ta'aƙĩbi da ƙãrin bayãni ga maganarsu. -
رَّبُّ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا فَٱعْبُدْهُ وَٱصْطَبِرْ لِعِبَـٰدَتِهِۦ ۚ هَلْ تَعْلَمُ لَهُۥ سَمِيًّا٦٥
Rabbu alssamawati waalardi wama baynahuma faoʿbudhu waistabir liʿibadatihi hal taʿlamu lahu samiyyan
Shi ne Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãnin su. sai ka bauta Masa, kuma ka yi haƙuri ga bautar sa. Shin kã san wani takwara a gare shi?
-
وَيَقُولُ ٱلْإِنسَـٰنُ أَءِذَا مَا مِتُّ لَسَوْفَ أُخْرَجُ حَيًّا٦٦
Wayaqoolu alinsanu aitha ma mittu lasawfa okhraju hayyan
Kuma mutum yana cẽwa, "Shin idan na mutu lalle ne haƙĩ ƙa da sannu zã a fitar da ni inã mai rai?"
-
أَوَلَا يَذْكُرُ ٱلْإِنسَـٰنُ أَنَّا خَلَقْنَـٰهُ مِن قَبْلُ وَلَمْ يَكُ شَيْـًٔا٦٧
Awala yathkuru alinsanu anna khalaqnahu min qablu walam yaku shayan
Shin, kuma mutum bã zai tuna ba cẽwa lalle ne Mun halitta shi a gabãni, alhãli kuwa bai kasance kõme ba?
-
فَوَرَبِّكَ لَنَحْشُرَنَّهُمْ وَٱلشَّيَـٰطِينَ ثُمَّ لَنُحْضِرَنَّهُمْ حَوْلَ جَهَنَّمَ جِثِيًّا٦٨
Fawarabbika lanahshurannahum waalshshayateena thumma lanuhdirannahum hawla jahannama jithiyyan
To, Munã rantsuwa da Ubangijin ka, lalle ne, Muna tãyar da su da kuma shaianun sa'an nan, kuma lalle Muna halatar da su da kuma Shaiɗanun sa'an nan, kuma, lalle Muna halatar da su a gẽfen Jahannama sunã gurfãne.
-
ثُمَّ لَنَنزِعَنَّ مِن كُلِّ شِيعَةٍ أَيُّهُمْ أَشَدُّ عَلَى ٱلرَّحْمَـٰنِ عِتِيًّا٦٩
Thumma lananziʿanna min kulli sheeʿatin ayyuhum ashaddu ʿala alrrahmani ʿitiyyan
Sa'an nan kuma lalle Munã fizge wanda yake mafi tsananin girman kai ga Mai rahama daga kõwace ƙungiya.
-
ثُمَّ لَنَحْنُ أَعْلَمُ بِٱلَّذِينَ هُمْ أَوْلَىٰ بِهَا صِلِيًّا٧٠
Thumma lanahnu aʿlamu biallatheena hum awla biha siliyyan
Sa'an nan kuma lalle Mũ ne Mafi sani ga waɗan da suke sũ ne mafiya cancantar ƙõnuwa da ita.
-
وَإِن مِّنكُمْ إِلَّا وَارِدُهَا ۚ كَانَ عَلَىٰ رَبِّكَ حَتْمًا مَّقْضِيًّا٧١
Wain minkum illa wariduha kana ʿala rabbika hatman maqdiyyan
Kuma bãbu kõwa daga gare ku sai mai tuzga mata.1 Yã kasance wajibi ga Ubangijinka, hukuntacce.
Bayanai
[1] Idan an tãra mutãne dõmin hisabi, anã ajiye wuta a tsakãnin mutãne da Aljanna, Sa'annan a gitta sirãɗi a cikan wutar dõmin mutãne su bi akansa su ƙetare wutar zuwa Aljanna kuma waɗansu su fãɗa a cikin wutar dõmin azãba dawwamamma kõ kuma ta ɗan lõkaci gwargwadon laifi. -
ثُمَّ نُنَجِّى ٱلَّذِينَ ٱتَّقَوا۟ وَّنَذَرُ ٱلظَّـٰلِمِينَ فِيهَا جِثِيًّا٧٢
Thumma nunajjee allatheena ittaqaw wanatharu alththalimeena feeha jithiyyan
Sa'an nan kuma Mu tsẽrar da waɗanda suka yi aiki da taƙawa, kuma Mu bar azzãlumai a cikinta gurfãne.
-
وَإِذَا تُتْلَىٰ عَلَيْهِمْ ءَايَـٰتُنَا بَيِّنَـٰتٍ قَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ لِلَّذِينَ ءَامَنُوٓا۟ أَىُّ ٱلْفَرِيقَيْنِ خَيْرٌ مَّقَامًا وَأَحْسَنُ نَدِيًّا٧٣
Waitha tutla ʿalayhim ayatuna bayyinatin qala allatheena kafaroo lillatheena amanoo ayyu alfareeqayni khayrun maqaman waahsanu nadiyyan
Kuma idan anã karatun ãyõyinMu, bayyanannu a kansu, sai waɗanda suka kãfirta su ce wa waɗanda suka yi ĩmãni, "Wanne daga ƙungiyõyin biyu ya fi zama mafi alhẽri ga matsayi, kuma mafi kyaun majalisa?"
-
وَكَمْ أَهْلَكْنَا قَبْلَهُم مِّن قَرْنٍ هُمْ أَحْسَنُ أَثَـٰثًا وَرِءْيًا٧٤
Wakam ahlakna qablahum min qarnin hum ahsanu athathan wariyan
Kuma da yawa daga mutãnen ƙarni Muka halakar a gabãninsu sũ (waɗandaMuka halakar) in ne mafi kyaun kãyan ãki da magãnã.1
Bayanai
[1] Kãyan ɗãki na jin dãɗi kamar gadãje da kujeri da kãyan cin abinci. Magãnã kuwa ita ce wurin da ake ganĩ ga mutum kamar tufãfinsa da sũrar jikinsa da dukan abin gani daga gare shi. -
قُلْ مَن كَانَ فِى ٱلضَّلَـٰلَةِ فَلْيَمْدُدْ لَهُ ٱلرَّحْمَـٰنُ مَدًّا ۚ حَتَّىٰٓ إِذَا رَأَوْا۟ مَا يُوعَدُونَ إِمَّا ٱلْعَذَابَ وَإِمَّا ٱلسَّاعَةَ فَسَيَعْلَمُونَ مَنْ هُوَ شَرٌّ مَّكَانًا وَأَضْعَفُ جُندًا٧٥
Qul man kana fee alddalalati falyamdud lahu alrrahmanu maddan hatta itha raaw ma yooʿadoona imma alʿathaba waimma alssaʿata fasayaʿlamoona man huwa sharrun makanan waadʿafu jundan
Ka ce: "Wanda ya kasance a cikin ɓata sai Mai rahama Ya yalwata masa yalwatãwa, har idan sun ga abin da ake yi musu wa'adi, imma azãba kõ sã'a, to zã su sani, wane ne yake shĩ ne, mafi sharri ga wuri, kuma mafi rauni ga runduna!"
-
وَيَزِيدُ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ٱهْتَدَوْا۟ هُدًى ۗ وَٱلْبَـٰقِيَـٰتُ ٱلصَّـٰلِحَـٰتُ خَيْرٌ عِندَ رَبِّكَ ثَوَابًا وَخَيْرٌ مَّرَدًّا٧٦
Wayazeedu Allahu allatheena ihtadaw hudan waalbaqiyatu alssalihatu khayrun ʿinda rabbika thawaban wakhayrun maraddan
Kuma Allah na ƙãra wa wa ɗanda suka nẽmi shiryuwa da shiriya. Kuma ayyuka mãsu wanzuwa na ƙwarai ne mafi alhẽri awurin Ubangijinka ga lãda, kuma mafi alhẽri ga makõma.
-
أَفَرَءَيْتَ ٱلَّذِى كَفَرَ بِـَٔايَـٰتِنَا وَقَالَ لَأُوتَيَنَّ مَالًا وَوَلَدًا٧٧
Afaraayta allathee kafara biayatina waqala laootayanna malan wawaladan
Shin, ka ga wanda ya kãfirta da ayõyinMu, kuma ya ce: "Lalle ne zã a bã ni dũkiya da ɗiya?"
-
أَطَّلَعَ ٱلْغَيْبَ أَمِ ٱتَّخَذَ عِندَ ٱلرَّحْمَـٰنِ عَهْدًا٧٨
Attalaʿa alghayba ami ittakhatha ʿinda alrrahmani ʿahdan
Shin, yã tsinkãyi gaibi ne, kõ kuwa yã ɗauki wani alkawari daga Mai rahama ne?
-
كَلَّا ۚ سَنَكْتُبُ مَا يَقُولُ وَنَمُدُّ لَهُۥ مِنَ ٱلْعَذَابِ مَدًّا٧٩
Kalla sanaktubu ma yaqoolu wanamuddu lahu mina alʿathabi maddan
Ã'aha! zã mu rubũta abin da yake faɗa, kuma Mu yalwata masa, daga azãba, yalwatãwa.
-
وَنَرِثُهُۥ مَا يَقُولُ وَيَأْتِينَا فَرْدًا٨٠
Wanarithuhu ma yaqoolu wayateena fardan
Kuma Mu gãde shi ga abin da yake faɗa, kuma ya zo Mana yanã shi kɗai.
-
وَٱتَّخَذُوا۟ مِن دُونِ ٱللَّهِ ءَالِهَةً لِّيَكُونُوا۟ لَهُمْ عِزًّا٨١
Waittakhathoo min dooni Allahi alihatan liyakoonoo lahum ʿizzan
Kuma suka riƙi gumãka,1 baicin Allah, dõmin su kãsance mataimaka a gare su.
Bayanai
[1] Gunki, shi ne dukan abin bautawa wanda bã Allah ba. Wanda ya riƙi wani sãlihi ko malã'iki ko aljani, yanã bauta masa, to, yã riƙe shi gunki ke nan. Bauta ita ce bin umurni da barin hani. Wanda ya bi umurnin da bã na Allah ba, kõ ya bar abin banin da ba na Allah ba, to, ya bauta wa mai umurnin ko mai hanin, yã riƙe shi gunki baicin Allah. -
كَلَّا ۚ سَيَكْفُرُونَ بِعِبَادَتِهِمْ وَيَكُونُونَ عَلَيْهِمْ ضِدًّا٨٢
Kalla sayakfuroona biʿibadatihim wayakoonoona ʿalayhim diddan
Ã'aha! Zã su kãfirta da ibãdarsu, kuma su kasance maƙiya a kansu.
-
أَلَمْ تَرَ أَنَّآ أَرْسَلْنَا ٱلشَّيَـٰطِينَ عَلَى ٱلْكَـٰفِرِينَ تَؤُزُّهُمْ أَزًّا٨٣
Alam tara anna arsalna alshshayateena ʿala alkafireena taozzuhum azzan
Shin, ba ka gani ba cẽwa Mun saki shaiɗanu1 a kan kãfirai sunã shũshũta su ga zunubi shũshũtãwa?
Bayanai
[1] Idan shaiɗanu sun ga mai wa'azin gaskiya, sai su dinga shũshũta mabiyansu dõmin su yi faɗa da mai wa'azin, dõmin kada su saurare shi har su gãne ɓatarsu. Shaidan shi ne mai ɓatar da wani, mutum ne kõ aljani. -
فَلَا تَعْجَلْ عَلَيْهِمْ ۖ إِنَّمَا نَعُدُّ لَهُمْ عَدًّا٨٤
Fala taʿjal ʿalayhim innama naʿuddu lahum ʿaddan
Sabõda haka kada ka yi gaggawa a kansu, Munã yi musu ƙidãyar Ajali ne kawai, ƙidãyãwa.
-
يَوْمَ نَحْشُرُ ٱلْمُتَّقِينَ إِلَى ٱلرَّحْمَـٰنِ وَفْدًا٨٥
Yawma nahshuru almuttaqeena ila alrrahmani wafdan
A rãnar da Muka tãra mãsu taƙawa zuwa ga Mai rahama sunã bãƙin girma.
-
وَنَسُوقُ ٱلْمُجْرِمِينَ إِلَىٰ جَهَنَّمَ وِرْدًا٨٦
Wanasooqu almujrimeena ila jahannama wirdan
Kuma Munã kõra mãsu laifi zuwa Jahannama, gargaãwa.
-
لَّا يَمْلِكُونَ ٱلشَّفَـٰعَةَ إِلَّا مَنِ ٱتَّخَذَ عِندَ ٱلرَّحْمَـٰنِ عَهْدًا٨٧
La yamlikoona alshshafaʿata illa mani ittakhatha ʿinda alrrahmani ʿahdan
Ba su malakar cẽto fãce wanda ya riƙi alkawari a wurin Mai rahama.
-
وَقَالُوا۟ ٱتَّخَذَ ٱلرَّحْمَـٰنُ وَلَدًا٨٨
Waqaloo ittakhatha alrrahmanu waladan
Kuma suka ce: "Mai rahama Yã riƙi ã!"
-
لَّقَدْ جِئْتُمْ شَيْـًٔا إِدًّا٨٩
Laqad jitum shayan iddan
Lalle ne haƙĩƙa kun zo da wani abu mai girman mũni.
-
تَكَادُ ٱلسَّمَـٰوَٰتُ يَتَفَطَّرْنَ مِنْهُ وَتَنشَقُّ ٱلْأَرْضُ وَتَخِرُّ ٱلْجِبَالُ هَدًّا٩٠
Takadu alssamawatu yatafattarna minhu watanshaqqu alardu watakhirru aljibalu haddan
Sammai sunã kusa su tsattsage sabõda shi, kuma ƙasa ke kẽce kuma duwãtsu su faɗi sunã karyayyu.
-
أَن دَعَوْا۟ لِلرَّحْمَـٰنِ وَلَدًا٩١
An daʿaw lilrrahmani waladan
Dõmin sun yi da'awar ɗã ga Mai rahama.
-
وَمَا يَنۢبَغِى لِلرَّحْمَـٰنِ أَن يَتَّخِذَ وَلَدًا٩٢
Wama yanbaghee lilrrahmani an yattakhitha waladan
Alhãli bã ya kamata ga Mai rahama ya riƙi wani ɗã.
-
إِن كُلُّ مَن فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ إِلَّآ ءَاتِى ٱلرَّحْمَـٰنِ عَبْدًا٩٣
In kullu man fee alssamawati waalardi illa atee alrrahmani ʿabdan
Dukkan wanda yake a cikin sammai da ƙasa bai zama ba fãce mai jẽ wa Mai rahama ne yanã bãwã.
-
لَّقَدْ أَحْصَىٰهُمْ وَعَدَّهُمْ عَدًّا٩٤
Laqad ahsahum waʿaddahum ʿaddan
Lalle ne haƙĩƙa Yã lissafe su, kuma ya ƙidãye su, ƙidãya.
-
وَكُلُّهُمْ ءَاتِيهِ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ فَرْدًا٩٥
Wakulluhum ateehi yawma alqiyamati fardan
Kuma dukan kõwanensu mai jẽ Masa ne a Rãnar ¡iyãma yanã shi kaɗai.
-
إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ سَيَجْعَلُ لَهُمُ ٱلرَّحْمَـٰنُ وُدًّا٩٦
Inna allatheena amanoo waʿamiloo alssalihati sayajʿalu lahumu alrrahmanu wuddan
Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, Mai rahama zai sanya musu so.1
Bayanai
[1] Wanda ya bi Allah da gaskiya, Allah zai sanya zukãtan mutãne su sõ shi kamar yadda yake a cikin Hadisi wanda Imãm Tirmizi ya ruwaito daga sa'ad da Abu Huraira. -
فَإِنَّمَا يَسَّرْنَـٰهُ بِلِسَانِكَ لِتُبَشِّرَ بِهِ ٱلْمُتَّقِينَ وَتُنذِرَ بِهِۦ قَوْمًا لُّدًّا٩٧
Fainnama yassarnahu bilisanika litubashshira bihi almuttaqeena watunthira bihi qawman luddan
Sa'an nan Ibin sani kawai Mun sauƙaƙar da shi (Alƙur'ãni) a harshenka, dõmin ka yi bushãra da shi ga mãsu aiki da taƙawa kuma ka yi gargaɗi da shi ga mutãne mãsu tsananin husũma.
-
وَكَمْ أَهْلَكْنَا قَبْلَهُم مِّن قَرْنٍ هَلْ تُحِسُّ مِنْهُم مِّنْ أَحَدٍ أَوْ تَسْمَعُ لَهُمْ رِكْزًۢا٩٨
Wakam ahlakna qablahum min qarnin hal tuhissu minhum min ahadin aw tasmaʿu lahum rikzan
Kuma da yawa Muka halakar da mutãnen ƙarnõni a gabãninsu. Shin kanã jin mõtsin wani guda daga gare su, kõ kuwa kanã jin wata ɗuriya tãsu?
Tambayoyin da ake yawan yi
Suratul Maryam tana cikin juz’i na nawa?
Suratul Maryam tana cikin juz’i na 16.
Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Maryam?
Suratul Maryam tana da ayoyi 98.
Suratul Maryam Makkiya ce ko Madaniya?
Suratul Maryam sura ce Makkiya.
Suratul Maryam ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?
Ita ce sura ta 19 a cikin Alƙur’ani.
Majiyoyi
- Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
- Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
- Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
- Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
- Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
- Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.
Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.