سورة الأنبياء

Suratul Anbiya’i da fassarar Hausa

Annabawa

Mushafi

Mishary Rashid AlafasySauke MP3Sauke PDF

Suratul Anbiya’i (الأنبياء) ita ce sura ta 21 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 112. Ma’anar sunanta ita ce “Annabawa”. Sura ce Makkiya, wadda ta sauka a Makka kafin Hijira, kuma tana cikin juz’i na 17.

A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Anbiya’i gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.

Suratul Anbiya’i cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. ٱقْتَرَبَ لِلنَّاسِ حِسَابُهُمْ وَهُمْ فِى غَفْلَةٍ مُّعْرِضُونَ۝١

    Iqtaraba lilnnasi hisabuhum wahum fee ghaflatin muʿridoona

    Hisãbin mutãne ya kusanta gare su, ahãli kuwa sunã a cikin gafala, sunã mãsu bijirẽwa.

  2. مَا يَأْتِيهِم مِّن ذِكْرٍ مِّن رَّبِّهِم مُّحْدَثٍ إِلَّا ٱسْتَمَعُوهُ وَهُمْ يَلْعَبُونَ۝٢

    Ma yateehim min thikrin min rabbihim muhdathin illa istamaʿoohu wahum yalʿaboona

    Wani ambatõ daga Ubangijinsu sãbo, bã ya zuwa gare su fãce sun saurãre shi, alhãli kuwa sunã mãsu yin wãsa.

  3. لَاهِيَةً قُلُوبُهُمْ ۗ وَأَسَرُّوا۟ ٱلنَّجْوَى ٱلَّذِينَ ظَلَمُوا۟ هَلْ هَـٰذَآ إِلَّا بَشَرٌ مِّثْلُكُمْ ۖ أَفَتَأْتُونَ ٱلسِّحْرَ وَأَنتُمْ تُبْصِرُونَ۝٣

    Lahiyatan quloobuhum waasarroo alnnajwa allatheena thalamoo hal hatha illa basharun mithlukum afatatoona alssihra waantum tubsiroona

    Sanã mãsu shagaltacin zukãtansu, kuma su asirta gãnãwa: Waɗanda suka yi zãlunce (sunã cẽwa) "Wannan bã Kõwa ba ne fãce mutum misãlinku. Shin, to, kunã jẽ wa sihiri, ahãli kuwa kũ, kunã fahimta?"

  4. قَالَ رَبِّى يَعْلَمُ ٱلْقَوْلَ فِى ٱلسَّمَآءِ وَٱلْأَرْضِ ۖ وَهُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلْعَلِيمُ۝٤

    Qala rabbee yaʿlamu alqawla fee alssamai waalardi wahuwa alssameeʿu alʿaleemu

    Ya ce: "Ubangijina Yanã sanin magana a cikin sama da ƙasa kuma Shi ne Mai ji, Masani."

  5. بَلْ قَالُوٓا۟ أَضْغَـٰثُ أَحْلَـٰمٍۭ بَلِ ٱفْتَرَىٰهُ بَلْ هُوَ شَاعِرٌ فَلْيَأْتِنَا بِـَٔايَةٍ كَمَآ أُرْسِلَ ٱلْأَوَّلُونَ۝٥

    Bal qaloo adghathu ahlamin bali iftarahu bal huwa shaʿirun falyatina biayatin kama orsila alawwaloona

    Ã'a, suka ce: "Yãye-yãyen mafarki ne. Ã'a, yã ƙirƙira shi ne. Ã'a, shi mawãƙi ne. Sai ya zo mana da wata ãyã kamar yadda aka aiko manzanni na farko."

  6. مَآ ءَامَنَتْ قَبْلَهُم مِّن قَرْيَةٍ أَهْلَكْنَـٰهَآ ۖ أَفَهُمْ يُؤْمِنُونَ۝٦

    Ma amanat qablahum min qaryatin ahlaknaha afahum yuminoona

    Wata alƙarya da Muka halaka ta a gabãninsu, ba ta yi ĩmãni ba. Shin, to, sũ, sunã yin ĩmãni?

  7. وَمَآ أَرْسَلْنَا قَبْلَكَ إِلَّا رِجَالًا نُّوحِىٓ إِلَيْهِمْ ۖ فَسْـَٔلُوٓا۟ أَهْلَ ٱلذِّكْرِ إِن كُنتُمْ لَا تَعْلَمُونَ۝٧

    Wama arsalna qablaka illa rijalan noohee ilayhim faisaloo ahla alththikri in kuntum la taʿlamoona

    Kuma ba Mu aika ba a gabãninka fãce mazãje, Munã yin wahayi zuwa gare su. Ku tambayi ma'abũta ambato1 idan kun kasance ba ku sani ba.

    Bayanai
    [1] Ma'abũta ambato, watau mutãnen da aka bai wa littattafan sama: Yahũdu da Nasãra.
  8. وَمَا جَعَلْنَـٰهُمْ جَسَدًا لَّا يَأْكُلُونَ ٱلطَّعَامَ وَمَا كَانُوا۟ خَـٰلِدِينَ۝٨

    Wama jaʿalnahum jasadan la yakuloona alttaʿama wama kanoo khalideena

    Kuma ba Mu sanya su jiki, bã su cin abin ci ba, kuma ba su kasance madawwama ba.

  9. ثُمَّ صَدَقْنَـٰهُمُ ٱلْوَعْدَ فَأَنجَيْنَـٰهُمْ وَمَن نَّشَآءُ وَأَهْلَكْنَا ٱلْمُسْرِفِينَ۝٩

    Thumma sadaqnahumu alwaʿda faanjaynahum waman nashao waahlakna almusrifeena

    Sa'an nan kuma Muka gaskata musu alkawari; sai Muka tsẽrar da su da wanda Muke so, kuma Muka halakar da mãsu yawaitãwa.1

    Bayanai
    [1] Mãsu yawaitãwa, sũ ne mãsu wuce haddõdin Allah ga Kõme, fãsiƙai da mãsu bidi'õ'i.
  10. لَقَدْ أَنزَلْنَآ إِلَيْكُمْ كِتَـٰبًا فِيهِ ذِكْرُكُمْ ۖ أَفَلَا تَعْقِلُونَ۝١٠

    Laqad anzalna ilaykum kitaban feehi thikrukum afala taʿqiloona

    Lalle haƙĩƙa Mun saukar da wani littãfi zuwa gare ku,1 a cikinsa akwai ambatonku. Shin, to, bã ku hankalta?

    Bayanai
    [1] Al'ummar Muhammad, tsirar Allah da amincinsa su tabbata a gare shi. An saukar musu da Alƙur'ãni, a cikinsa akwai ɗaukakarsu da darajarsu, dõmin wanda aka ambata, to, an ɗaukaka shi.
  11. وَكَمْ قَصَمْنَا مِن قَرْيَةٍ كَانَتْ ظَالِمَةً وَأَنشَأْنَا بَعْدَهَا قَوْمًا ءَاخَرِينَ۝١١

    Wakam qasamna min qaryatin kanat thalimatan waanshana baʿdaha qawman akhareena

    Kuma da yawa Muka karya wata alƙarya tã kasance mai zãlunci, kuma Muka ƙãga halittar waɗansu mutãne na dabam a bãyanta.

  12. فَلَمَّآ أَحَسُّوا۟ بَأْسَنَآ إِذَا هُم مِّنْهَا يَرْكُضُونَ۝١٢

    Falamma ahassoo basana itha hum minha yarkudoona

    Sai a lõkacin da suka hangi azãbar Mu, sai gã su sunã gudu daga gare ta.

  13. لَا تَرْكُضُوا۟ وَٱرْجِعُوٓا۟ إِلَىٰ مَآ أُتْرِفْتُمْ فِيهِ وَمَسَـٰكِنِكُمْ لَعَلَّكُمْ تُسْـَٔلُونَ۝١٣

    La tarkudoo wairjiʿoo ila ma otriftum feehi wamasakinikum laʿallakum tusaloona

    "Kada ku yi gudu. Ku kõmo zuwa ga abin da aka ni'imtar da ku a cikinsa da gidãjenku tsammãninku anã tambayar ku."

  14. قَالُوا۟ يَـٰوَيْلَنَآ إِنَّا كُنَّا ظَـٰلِمِينَ۝١٤

    Qaloo ya waylana inna kunna thalimeena

    Suka ce: "Kaitonmu! Lalle mũ ne muka kasance mãsu zãlunci."

  15. فَمَا زَالَت تِّلْكَ دَعْوَىٰهُمْ حَتَّىٰ جَعَلْنَـٰهُمْ حَصِيدًا خَـٰمِدِينَ۝١٥

    Fama zalat tilka daʿwahum hatta jaʿalnahum haseedan khamideena

    Sa'an nan waccan ba ta gushe ba, ita ce da'awarsu har Muka mayar da su girbabbu, bitattu.

  16. وَمَا خَلَقْنَا ٱلسَّمَآءَ وَٱلْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا لَـٰعِبِينَ۝١٦

    Wama khalaqna alssamaa waalarda wama baynahuma laʿibeena

    Kuma ba Mu halitta sama da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu Muna Mãsu wãsã ba.

  17. لَوْ أَرَدْنَآ أَن نَّتَّخِذَ لَهْوًا لَّٱتَّخَذْنَـٰهُ مِن لَّدُنَّآ إِن كُنَّا فَـٰعِلِينَ۝١٧

    Law aradna an nattakhitha lahwan laittakhathnahu min ladunna in kunna faʿileena

    Da Mun yi nufin Mu riƙi wani abin wãsa dã Mun1 riƙe shi daga gunMu, idan Mun kasance mãsu aikatãwa.

    Bayanai
    [1] Abin wãsã, shi ne mãtã, kõɗã, kõ wani abin da ake shagaltuwa da shi.
  18. بَلْ نَقْذِفُ بِٱلْحَقِّ عَلَى ٱلْبَـٰطِلِ فَيَدْمَغُهُۥ فَإِذَا هُوَ زَاهِقٌ ۚ وَلَكُمُ ٱلْوَيْلُ مِمَّا تَصِفُونَ۝١٨

    Bal naqthifu bialhaqqi ʿala albatili fayadmaghuhu faitha huwa zahiqun walakumu alwaylu mimma tasifoona

    Ã'a, Munã jĩfa da gaskiya a kan ƙarya, sai ta darkãke ta, sai ga tã halakakka. Kuma bone yã tabbata a gare ku sabõda abin da kuke siffantãwa.

  19. وَلَهُۥ مَن فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ۚ وَمَنْ عِندَهُۥ لَا يَسْتَكْبِرُونَ عَنْ عِبَادَتِهِۦ وَلَا يَسْتَحْسِرُونَ۝١٩

    Walahu man fee alssamawati waalardi waman ʿindahu la yastakbiroona ʿan ʿibadatihi wala yastahsiroona

    Kuma shĩ ne da mallakar wanda yake a cikin sammai da ƙasa. Kuma waɗanda suke wurin Sa (watau malã'iku), bã su yin girman kai ga ibãdar Sa. kuma bã su gajiya.

  20. يُسَبِّحُونَ ٱلَّيْلَ وَٱلنَّهَارَ لَا يَفْتُرُونَ۝٢٠

    Yusabbihoona allayla waalnnahara la yafturoona

    Sunã tasbĩhi dare da rãnã, bã su yin rauni.

  21. أَمِ ٱتَّخَذُوٓا۟ ءَالِهَةً مِّنَ ٱلْأَرْضِ هُمْ يُنشِرُونَ۝٢١

    Ami ittakhathoo alihatan mina alardi hum yunshiroona

    Kõ (kãfirai) sun riƙi waɗansu abũbuwan bautãwa ne ga ƙasã, su ne mãsu tãyarwa (gare su)?

  22. لَوْ كَانَ فِيهِمَآ ءَالِهَةٌ إِلَّا ٱللَّهُ لَفَسَدَتَا ۚ فَسُبْحَـٰنَ ٱللَّهِ رَبِّ ٱلْعَرْشِ عَمَّا يَصِفُونَ۝٢٢

    Law kana feehima alihatun illa Allahu lafasadata fasubhana Allahi rabbi alʿarshi ʿamma yasifoona

    Dã waɗansu abũbuwan bautawa sun kasance a cikinsu (sama da ƙasa) fãce Allah, haƙĩƙa dã su biyun sun ɓãci. Sabõda haka tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin Al'arshi daga abin da suke siffantãwa.

  23. لَا يُسْـَٔلُ عَمَّا يَفْعَلُ وَهُمْ يُسْـَٔلُونَ۝٢٣

    La yusalu ʿamma yafʿalu wahum yusaloona

    Bã a tambayar Sa ga abin da Yake aikatãwa, alhãli kuwa sũanã tambayar su.

  24. أَمِ ٱتَّخَذُوا۟ مِن دُونِهِۦٓ ءَالِهَةً ۖ قُلْ هَاتُوا۟ بُرْهَـٰنَكُمْ ۖ هَـٰذَا ذِكْرُ مَن مَّعِىَ وَذِكْرُ مَن قَبْلِى ۗ بَلْ أَكْثَرُهُمْ لَا يَعْلَمُونَ ٱلْحَقَّ ۖ فَهُم مُّعْرِضُونَ۝٢٤

    Ami ittakhathoo min doonihi alihatan qul hatoo burhanakum hatha thikru man maʿiya wathikru man qablee bal aktharuhum la yaʿlamoona alhaqqa fahum muʿridoona

    Kõ sun riƙi waɗansu abũbuwan bautãwa baicinSa? Ka ce: "Ku kãwo hujjarku, wannan shi ne ambaton wanda yake tãre da ni, kuma shi ne ambaton wanda yake a gabãnĩna. Ã'a, mafi yawansubã su sanin gaskiya, sabõda haka sũ mãsu bijirẽwa ne."

  25. وَمَآ أَرْسَلْنَا مِن قَبْلِكَ مِن رَّسُولٍ إِلَّا نُوحِىٓ إِلَيْهِ أَنَّهُۥ لَآ إِلَـٰهَ إِلَّآ أَنَا۠ فَٱعْبُدُونِ۝٢٥

    Wama arsalna min qablika min rasoolin illa noohee ilayhi annahu la ilaha illa ana faoʿbudooni

    Kuma ba Mu aiki wani Manzo ba a gabãninka fãce Munã yin wahayi zuwa gare shi, cẽwa "Lalle ne Shi, bãbu abin bautãwa fãce Nĩ, sai ku bauta Mini."

  26. وَقَالُوا۟ ٱتَّخَذَ ٱلرَّحْمَـٰنُ وَلَدًا ۗ سُبْحَـٰنَهُۥ ۚ بَلْ عِبَادٌ مُّكْرَمُونَ۝٢٦

    Waqaloo ittakhatha alrrahmanu waladan subhanahu bal ʿibadun mukramoona

    Kuma suka ce: "Mai rahama ya riƙi ɗã." Tsarkinsa, ya tabbata! Ã'a, (malã'iku) bãyi ne mãsu daraja.

  27. لَا يَسْبِقُونَهُۥ بِٱلْقَوْلِ وَهُم بِأَمْرِهِۦ يَعْمَلُونَ۝٢٧

    La yasbiqoonahu bialqawli wahum biamrihi yaʿmaloona

    Bã su gabãtarSa da magana, kuma su da umurnin Sa suke aiki.

  28. يَعْلَمُ مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ وَلَا يَشْفَعُونَ إِلَّا لِمَنِ ٱرْتَضَىٰ وَهُم مِّنْ خَشْيَتِهِۦ مُشْفِقُونَ۝٢٨

    Yaʿlamu ma bayna aydeehim wama khalfahum wala yashfaʿoona illa limani irtada wahum min khashyatihi mushfiqoona

    Yanã sanin abin da yake gaba gare su da abin da yake a bãyansu, kuma bã su yin cẽto fãce ga wanda Ya yarda, kuma sũmasu sauna ne sabõda tsõron Sa.

  29. ۞ وَمَن يَقُلْ مِنْهُمْ إِنِّىٓ إِلَـٰهٌ مِّن دُونِهِۦ فَذَٰلِكَ نَجْزِيهِ جَهَنَّمَ ۚ كَذَٰلِكَ نَجْزِى ٱلظَّـٰلِمِينَ۝٢٩

    Waman yaqul minhum innee ilahun min doonihi fathalika najzeehi jahannama kathalika najzee alththalimeena

    Kuma wanda ya ce daga gare su, "Lalle nĩ abin bautãwa ne baicinSa," to, wannan Munã sãkã masa da, Jahannama. Kamar haka Muke sãkã wa azzãlumai.

  30. أَوَلَمْ يَرَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓا۟ أَنَّ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضَ كَانَتَا رَتْقًا فَفَتَقْنَـٰهُمَا ۖ وَجَعَلْنَا مِنَ ٱلْمَآءِ كُلَّ شَىْءٍ حَىٍّ ۖ أَفَلَا يُؤْمِنُونَ۝٣٠

    Awalam yara allatheena kafaroo anna alssamawati waalarda kanata ratqan fafataqnahuma wajaʿalna mina almai kulla shayin hayyin afala yuminoona

    Shin kuma waɗanda suka kãfirta ba, su gani da cẽwa lalle sammai da ƙasa sun kasance ɗinke,1 sai Muka bũɗe su, kuma Muka sanya dukan kome mai rai daga ruwa? Shin, bã zã su yi ĩmãni ba?

    Bayanai
    [1] Abin wãsã, shi ne mãtã, kõɗã, Kõ wani abin da ake shagaltuwa da shi.
  31. وَجَعَلْنَا فِى ٱلْأَرْضِ رَوَٰسِىَ أَن تَمِيدَ بِهِمْ وَجَعَلْنَا فِيهَا فِجَاجًا سُبُلًا لَّعَلَّهُمْ يَهْتَدُونَ۝٣١

    Wajaʿalna fee alardi rawasiya an tameeda bihim wajaʿalna feeha fijajan subulan laʿallahum yahtadoona

    Kuma Mun sanya tabbatattun duwãtsu a cikin ƙasa dõmin kada ta karkata da su kuma Mun sanya ranguna, hanyõyi, a cikinsu (duwãtsun), tsammãninsu sunã shiryuwa.

  32. وَجَعَلْنَا ٱلسَّمَآءَ سَقْفًا مَّحْفُوظًا ۖ وَهُمْ عَنْ ءَايَـٰتِهَا مُعْرِضُونَ۝٣٢

    Wajaʿalna alssamaa saqfan mahfoothan wahum ʿan ayatiha muʿridoona

    Kuma Mun sanya sama rufi tsararre, alhãli kuwa su daga ãyõyinta mãsu bijirẽwa ne.

  33. وَهُوَ ٱلَّذِى خَلَقَ ٱلَّيْلَ وَٱلنَّهَارَ وَٱلشَّمْسَ وَٱلْقَمَرَ ۖ كُلٌّ فِى فَلَكٍ يَسْبَحُونَ۝٣٣

    Wahuwa allathee khalaqa allayla waalnnahara waalshshamsa waalqamara kullun fee falakin yasbahoona

    Kuma shĩ ne wanda Ya halitta dare da yini da rãnã da watã dukansu1 a cikin wani sarari suKe iyo.

    Bayanai
    [1] Wannan yã nũna cewa rãnã da watã a cikin sarari guda suke, Kõ da yake akwai nĩsan gaske a tsakãninsu.
  34. وَمَا جَعَلْنَا لِبَشَرٍ مِّن قَبْلِكَ ٱلْخُلْدَ ۖ أَفَإِي۟ن مِّتَّ فَهُمُ ٱلْخَـٰلِدُونَ۝٣٤

    Wama jaʿalna libasharin min qablika alkhulda afain mitta fahumu alkhalidoona

    Kuma ba Mu sanya dawwama ga wani mutum ba, a gabãninka. Shin to idan ka mutu to sũ ne madawwama?

  35. كُلُّ نَفْسٍ ذَآئِقَةُ ٱلْمَوْتِ ۗ وَنَبْلُوكُم بِٱلشَّرِّ وَٱلْخَيْرِ فِتْنَةً ۖ وَإِلَيْنَا تُرْجَعُونَ۝٣٥

    Kullu nafsin thaiqatu almawti wanablookum bialshsharri waalkhayri fitnatan wailayna turjaʿoona

    Kõwane rai mai ɗanɗanar mutuwa ne. Kuma Munã jarraba ku da sharri da alhẽri dõmin fitina. Kuma zuwa gare Mu ake mayar da ku.

  36. وَإِذَا رَءَاكَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓا۟ إِن يَتَّخِذُونَكَ إِلَّا هُزُوًا أَهَـٰذَا ٱلَّذِى يَذْكُرُ ءَالِهَتَكُمْ وَهُم بِذِكْرِ ٱلرَّحْمَـٰنِ هُمْ كَـٰفِرُونَ۝٣٦

    Waitha raaka allatheena kafaroo in yattakhithoonaka illa huzuwan ahatha allathee yathkuru alihatakum wahum bithikri alrrahmani hum kafiroona

    Kuma idan waɗanda suka kãfirta suka gan ka, bã su riƙon ka fãce da izgili (sunã cẽwa), "Shin, wannan ne ke ambatar gumãkanku?" Alhãli kuwa sũ, ga ambatar Mai rahama, mãsu kãfirta ne1.

    Bayanai
    [1] Sun kasance sunã aibanta wanda yake musun gumãkansu alhãli kuwa sũ, sunã musun zaman Allah Mai rahama ya kasance abin bautãwa guda. Wannan shi ne gãyar jãhilci.
  37. خُلِقَ ٱلْإِنسَـٰنُ مِنْ عَجَلٍ ۚ سَأُو۟رِيكُمْ ءَايَـٰتِى فَلَا تَسْتَعْجِلُونِ۝٣٧

    Khuliqa alinsanu min ʿajalin saoreekum ayatee fala tastaʿjiloona

    An halitta mutum daga gaggãwa, zan nũna muku ãyõyiNa. Sabõda haka kada ku nẽmiyin gaggãwa.

  38. وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هَـٰذَا ٱلْوَعْدُ إِن كُنتُمْ صَـٰدِقِينَ۝٣٨

    Wayaqooloona mata hatha alwaʿdu in kuntum sadiqeena

    Kuma sunã cẽwa, "A yaushe wannan wa'adi zai tabbata, idan kun kasance mãsu gaskiya?"

  39. لَوْ يَعْلَمُ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ حِينَ لَا يَكُفُّونَ عَن وُجُوهِهِمُ ٱلنَّارَ وَلَا عَن ظُهُورِهِمْ وَلَا هُمْ يُنصَرُونَ۝٣٩

    Law yaʿlamu allatheena kafaroo heena la yakuffoona ʿan wujoohihimu alnnara wala ʿan thuhoorihim wala hum yunsaroona

    Dã waɗanda suka kãfirta sunã sanin lõkacin da bã su kange wuta daga fuskõkinsu, kuma haka daga bãyayyakinsu, alhãli kuwa ba su zama ana taimakon su ba.

  40. بَلْ تَأْتِيهِم بَغْتَةً فَتَبْهَتُهُمْ فَلَا يَسْتَطِيعُونَ رَدَّهَا وَلَا هُمْ يُنظَرُونَ۝٤٠

    Bal tateehim baghtatan fatabhatuhum fala yastateeʿoona raddaha wala hum yuntharoona

    Ã'a, tanã jẽ musu bisa ga auke sai ta ɗimautar da su, sa'an nan bã su iya mayar da ita, kuma ba su zama anã yi musu jinkiri ba.

  41. وَلَقَدِ ٱسْتُهْزِئَ بِرُسُلٍ مِّن قَبْلِكَ فَحَاقَ بِٱلَّذِينَ سَخِرُوا۟ مِنْهُم مَّا كَانُوا۟ بِهِۦ يَسْتَهْزِءُونَ۝٤١

    Walaqadi istuhzia birusulin min qablika fahaqa biallatheena sakhiroo minhum ma kanoo bihi yastahzioona

    Kuma lalle ne, haƙĩƙa, an yi izgili ga waɗansu Manzanni daga gabãninka, sai abin da suka kasance sunã izgili da shi ya auku ga waɗanda suka yi izgilin daga gare su.

  42. قُلْ مَن يَكْلَؤُكُم بِٱلَّيْلِ وَٱلنَّهَارِ مِنَ ٱلرَّحْمَـٰنِ ۗ بَلْ هُمْ عَن ذِكْرِ رَبِّهِم مُّعْرِضُونَ۝٤٢

    Qul man yaklaokum biallayli waalnnahari mina alrrahmani bal hum ʿan thikri rabbihim muʿridoona

    Ka ce: "Wãne ne yake tsare ku a dare da yini daga Mai rahama?" Ã'a, sũ mãsu bijirẽwa ne daga ambaton Ubangijinsu.

  43. أَمْ لَهُمْ ءَالِهَةٌ تَمْنَعُهُم مِّن دُونِنَا ۚ لَا يَسْتَطِيعُونَ نَصْرَ أَنفُسِهِمْ وَلَا هُم مِّنَّا يُصْحَبُونَ۝٤٣

    Am lahum alihatun tamnaʿuhum min doonina la yastateeʿoona nasra anfusihim wala hum minna yushaboona

    Ko kuwa sunã da waɗansu abũbuwan bautãwa waɗanda ke tsare su, daga gare Mu? Bã su iya taimakon kansu kuma ba su kasance anã abũtar su1 ba daga gare Mu.

    Bayanai
    [1] Bã su iya sãmun wani abõki wanda zai tsare su daga azãbarMu. Kuma wanda bai tsarekansa ba yãya zaĩ iya tsare wani?.
  44. بَلْ مَتَّعْنَا هَـٰٓؤُلَآءِ وَءَابَآءَهُمْ حَتَّىٰ طَالَ عَلَيْهِمُ ٱلْعُمُرُ ۗ أَفَلَا يَرَوْنَ أَنَّا نَأْتِى ٱلْأَرْضَ نَنقُصُهَا مِنْ أَطْرَافِهَآ ۚ أَفَهُمُ ٱلْغَـٰلِبُونَ۝٤٤

    Bal mattaʿna haolai waabaahum hatta tala ʿalayhimu alʿumuru afala yarawna anna natee alarda nanqusuha min atrafiha afahumu alghaliboona

    Ã'a, Mun yalwata wa waɗannan da ubanninsu ni'imarMu, har rãyuwa ta yi tsawo a kansu. Shin, to, bã su ganin cẽwa lalle Mũ, Munã je wa ƙasarsu, Munã rage1 ta daga sãsanninta? Shin, to, su ne marinjaya?

    Bayanai
    [1] Munã rage ƙasarsu daga sãsanninta, watau mutãnen da ke bin su ga ɓatarsu kullum sunã raguwa, sunã shiga Musulunci, Musulunci na ƙãruwa.
  45. قُلْ إِنَّمَآ أُنذِرُكُم بِٱلْوَحْىِ ۚ وَلَا يَسْمَعُ ٱلصُّمُّ ٱلدُّعَآءَ إِذَا مَا يُنذَرُونَ۝٤٥

    Qul innama onthirukum bialwahyi wala yasmaʿu alssummu aldduʿaa itha ma yuntharoona

    Ka ce: "Abin sani, inã yi muku gargaɗi kawai da wahayi," kuma kurma ba ya jin kira a lõkacin da ake yi musu gargaɗi.

  46. وَلَئِن مَّسَّتْهُمْ نَفْحَةٌ مِّنْ عَذَابِ رَبِّكَ لَيَقُولُنَّ يَـٰوَيْلَنَآ إِنَّا كُنَّا ظَـٰلِمِينَ۝٤٦

    Walain massathum nafhatun min ʿathabi rabbika layaqoolunna ya waylana inna kunna thalimeena

    Kuma haƙĩƙa idan wata iska daga azãbar Ubangiji ta shãfe su, haƙĩƙa sunã cẽwa, "Yã kaitonmu! Lalle mũ ne muka kasance mãsu zãlunci."

  47. وَنَضَعُ ٱلْمَوَٰزِينَ ٱلْقِسْطَ لِيَوْمِ ٱلْقِيَـٰمَةِ فَلَا تُظْلَمُ نَفْسٌ شَيْـًٔا ۖ وَإِن كَانَ مِثْقَالَ حَبَّةٍ مِّنْ خَرْدَلٍ أَتَيْنَا بِهَا ۗ وَكَفَىٰ بِنَا حَـٰسِبِينَ۝٤٧

    Wanadaʿu almawazeena alqista liyawmi alqiyamati fala tuthlamu nafsun shayan wain kana mithqala habbatin min khardalin atayna biha wakafa bina hasibeena

    Kuma Munã aza ma'aunan ãdalci ga Rãnar ¡iyãma, sabõda haka ba a zãluntar rai da kõme. Kuma kõ dã ya kasance nauyin ƙwãya daga kõmayya ne Mun zo da ita. Kuma Mun isa zama Mãsu hisãbi.

  48. وَلَقَدْ ءَاتَيْنَا مُوسَىٰ وَهَـٰرُونَ ٱلْفُرْقَانَ وَضِيَآءً وَذِكْرًا لِّلْمُتَّقِينَ۝٤٨

    Walaqad atayna moosa waharoona alfurqana wadiyaan wathikran lilmuttaqeena

    Kuma lalle, haƙĩƙa, Mun kãwo wa Mũsã da Hãrũna Rarrabewa da haske da ambato ga mãsu aiki da taƙawa.

  49. ٱلَّذِينَ يَخْشَوْنَ رَبَّهُم بِٱلْغَيْبِ وَهُم مِّنَ ٱلسَّاعَةِ مُشْفِقُونَ۝٤٩

    Allatheena yakhshawna rabbahum bialghaybi wahum mina alssaʿati mushfiqoona

    Waɗanda suke tsãron Ubangijinsu a fake, alhãli kuwa sũ, mãsu sauna ne daga Sa'a.

  50. وَهَـٰذَا ذِكْرٌ مُّبَارَكٌ أَنزَلْنَـٰهُ ۚ أَفَأَنتُمْ لَهُۥ مُنكِرُونَ۝٥٠

    Wahatha thikrun mubarakun anzalnahu afaantum lahu munkiroona

    Kuma wannan ambato ne mai albarka Mun saukar da shi. Shin, to, kũ mãsu musu ne gare shi?

  51. ۞ وَلَقَدْ ءَاتَيْنَآ إِبْرَٰهِيمَ رُشْدَهُۥ مِن قَبْلُ وَكُنَّا بِهِۦ عَـٰلِمِينَ۝٥١

    Walaqad atayna ibraheema rushdahu min qablu wakunna bihi ʿalimeena

    Kuma lalle haƙĩƙa Mun kãwo wa Ibrãhĩm shiryuwarsa daga gabãni, kuma Mun kasance Masana gare shi.

  52. إِذْ قَالَ لِأَبِيهِ وَقَوْمِهِۦ مَا هَـٰذِهِ ٱلتَّمَاثِيلُ ٱلَّتِىٓ أَنتُمْ لَهَا عَـٰكِفُونَ۝٥٢

    Ith qala liabeehi waqawmihi ma hathihi alttamatheelu allatee antum laha ʿakifoona

    Ya ce wa ubansa da mutanensa, "Mẽne ne waɗannan mutummutumai waɗanda kuke mãsu lazimta a kansu?"

  53. قَالُوا۟ وَجَدْنَآ ءَابَآءَنَا لَهَا عَـٰبِدِينَ۝٥٣

    Qaloo wajadna abaana laha ʿabideena

    Suka ce: "Mun sãmi Ubanninmu mãsu lazimta a kansu."

  54. قَالَ لَقَدْ كُنتُمْ أَنتُمْ وَءَابَآؤُكُمْ فِى ضَلَـٰلٍ مُّبِينٍ۝٥٤

    Qala laqad kuntum antum waabaokum fee dalalin mubeenin

    Ya ce: "Lalle, haƙĩƙa, kun kasance kũ da Ubanninku a cikin ɓata bayyananne."

  55. قَالُوٓا۟ أَجِئْتَنَا بِٱلْحَقِّ أَمْ أَنتَ مِنَ ٱللَّـٰعِبِينَ۝٥٥

    Qaloo ajitana bialhaqqi am anta mina allaʿibeena

    Suka ce: "Shin kã zo mana da gaskiya ne, Kõ kuwa kai kanã daga mãsu wãsã ne?"

  56. قَالَ بَل رَّبُّكُمْ رَبُّ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ٱلَّذِى فَطَرَهُنَّ وَأَنَا۠ عَلَىٰ ذَٰلِكُم مِّنَ ٱلشَّـٰهِدِينَ۝٥٦

    Qala bal rabbukum rabbu alssamawati waalardi allathee fatarahunna waana ʿala thalikum mina alshshahideena

    Ya ce: "Ã'a, Ubangijinku Shi ne Ubangijin sammai da ƙasa, wanda Ya ƙãga halittarsu. Kuma Ni inã daga mãsu shaida a kan haka."

  57. وَتَٱللَّهِ لَأَكِيدَنَّ أَصْنَـٰمَكُم بَعْدَ أَن تُوَلُّوا۟ مُدْبِرِينَ۝٥٧

    WataAllahi laakeedanna asnamakum baʿda an tuwalloo mudbireena

    "Kuma inã rantsuwa da Allah, lalle zan yi wani shiri ga gumãkanku a bãyan kun jũya kunã mãsu bãyar da bãya."

  58. فَجَعَلَهُمْ جُذَٰذًا إِلَّا كَبِيرًا لَّهُمْ لَعَلَّهُمْ إِلَيْهِ يَرْجِعُونَ۝٥٨

    Fajaʿalahum juthathan illa kabeeran lahum laʿallahum ilayhi yarjiʿoona

    Sai ya sanya su guntu-guntu fãce wani babba gare su, tsammãninsũ sunã Kõmãwa zuwa gare shi.

  59. قَالُوا۟ مَن فَعَلَ هَـٰذَا بِـَٔالِهَتِنَآ إِنَّهُۥ لَمِنَ ٱلظَّـٰلِمِينَ۝٥٩

    Qaloo man faʿala hatha bialihatina innahu lamina alththalimeena

    Suka ce: "Wane ne ya aikata wannan ga gumãkanmu? Lalle shĩ, haƙĩƙa, yanã daga azzãlumai."

  60. قَالُوا۟ سَمِعْنَا فَتًى يَذْكُرُهُمْ يُقَالُ لَهُۥٓ إِبْرَٰهِيمُ۝٦٠

    Qaloo samiʿna fatan yathkuruhum yuqalu lahu ibraheemu

    Suka ce: "Mun ji wani saurayi yanã ambatar su. Anã ce masa Ibrahĩm."

  61. قَالُوا۟ فَأْتُوا۟ بِهِۦ عَلَىٰٓ أَعْيُنِ ٱلنَّاسِ لَعَلَّهُمْ يَشْهَدُونَ۝٦١

    Qaloo fatoo bihi ʿala aʿyuni alnnasi laʿallahum yashhadoona

    Suka ce: "To, ku zo da shi a kan idanun mutãne, tsammãnin su zã su bãyar da shaida."

  62. قَالُوٓا۟ ءَأَنتَ فَعَلْتَ هَـٰذَا بِـَٔالِهَتِنَا يَـٰٓإِبْرَٰهِيمُ۝٦٢

    Qaloo aanta faʿalta hatha bialihatina ya ibraheemu

    Suka ce: "Shin kai ne ka aikata wannan ga gumãkanmu? Yã Ibrahĩm!"

  63. قَالَ بَلْ فَعَلَهُۥ كَبِيرُهُمْ هَـٰذَا فَسْـَٔلُوهُمْ إِن كَانُوا۟ يَنطِقُونَ۝٦٣

    Qala bal faʿalahu kabeeruhum hatha faisaloohum in kanoo yantiqoona

    Ya ce: "Ã'a, babbansu, wannan, shĩ ya aikata, shi. Sai ku tambaye su idan sun kasance sunã yin magana."

  64. فَرَجَعُوٓا۟ إِلَىٰٓ أَنفُسِهِمْ فَقَالُوٓا۟ إِنَّكُمْ أَنتُمُ ٱلظَّـٰلِمُونَ۝٦٤

    Farajaʿoo ila anfusihim faqaloo innakum antumu alththalimoona

    Sai suka kõma wa jũnansu suka ce: "Lalle ne kũ, kũ ne azzãlumai."

  65. ثُمَّ نُكِسُوا۟ عَلَىٰ رُءُوسِهِمْ لَقَدْ عَلِمْتَ مَا هَـٰٓؤُلَآءِ يَنطِقُونَ۝٦٥

    Thumma nukisoo ʿala ruoosihim laqad ʿalimta ma haolai yantiqoona

    Sa'an nan kuma aka sunkuyar da su a kan kãwunansu (sukace,) "Lalle, haƙĩƙa, kã sani waɗannan bã su yin magana."

  66. قَالَ أَفَتَعْبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَنفَعُكُمْ شَيْـًٔا وَلَا يَضُرُّكُمْ۝٦٦

    Qala afataʿbudoona min dooni Allahi ma la yanfaʿukum shayan wala yadurrukum

    Ya ce: "Shin to, kunã bautã wa abin da, bã ya, amfãnin ku da Kõme kuma bã ya cũtar da ku baicin Allah?"

  67. أُفٍّ لَّكُمْ وَلِمَا تَعْبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ ۖ أَفَلَا تَعْقِلُونَ۝٦٧

    Offin lakum walima taʿbudoona min dooni Allahi afala taʿqiloona

    "Tir da ku, kuma da abin da kuke bauta wa, baicin Allah! Shin to, bã ku hankalta?"

  68. قَالُوا۟ حَرِّقُوهُ وَٱنصُرُوٓا۟ ءَالِهَتَكُمْ إِن كُنتُمْ فَـٰعِلِينَ۝٦٨

    Qaloo harriqoohu waonsuroo alihatakum in kuntum faʿileena

    Suka ce: "Ku ƙõne shi kuma ku taimaki gumãkanku, idan kun kasance mãsu aikatãwa."

  69. قُلْنَا يَـٰنَارُ كُونِى بَرْدًا وَسَلَـٰمًا عَلَىٰٓ إِبْرَٰهِيمَ۝٦٩

    Qulna ya naru koonee bardan wasalaman ʿala ibraheema

    Muka ce: "Yã wuta! Ki kasance sanyi da aminci ga Ibrahĩm."

  70. وَأَرَادُوا۟ بِهِۦ كَيْدًا فَجَعَلْنَـٰهُمُ ٱلْأَخْسَرِينَ۝٧٠

    Waaradoo bihi kaydan fajaʿalnahumu alakhsareena

    Kuma suka yi nufin wani mũgun shiri da shi, sai Mukasanya su mafiya hasãra.

  71. وَنَجَّيْنَـٰهُ وَلُوطًا إِلَى ٱلْأَرْضِ ٱلَّتِى بَـٰرَكْنَا فِيهَا لِلْعَـٰلَمِينَ۝٧١

    Wanajjaynahu walootan ila alardi allatee barakna feeha lilʿalameena

    Kuma Muka tsẽrar da shi da Lũɗu zuwa ga ƙasar nan wadda Muka sanya albarka a cikinta ga tãlikai.

  72. وَوَهَبْنَا لَهُۥٓ إِسْحَـٰقَ وَيَعْقُوبَ نَافِلَةً ۖ وَكُلًّا جَعَلْنَا صَـٰلِحِينَ۝٧٢

    Wawahabna lahu ishaqa wayaʿqooba nafilatan wakullan jaʿalna saliheena

    Kuma Muka ba shi Is'haka da Ya'aƙuba a kan daɗi alhãli kuwa dukansu Mun sanya su sãlihai.

  73. وَجَعَلْنَـٰهُمْ أَئِمَّةً يَهْدُونَ بِأَمْرِنَا وَأَوْحَيْنَآ إِلَيْهِمْ فِعْلَ ٱلْخَيْرَٰتِ وَإِقَامَ ٱلصَّلَوٰةِ وَإِيتَآءَ ٱلزَّكَوٰةِ ۖ وَكَانُوا۟ لَنَا عَـٰبِدِينَ۝٧٣

    Wajaʿalnahum aimmatan yahdoona biamrina waawhayna ilayhim fiʿla alkhayrati waiqama alssalati waeetaa alzzakati wakanoo lana ʿabideena

    Kuma Muka sanya su shugabanni, sunã shiryarwa da umurnin Mu. Kuma Muka yi wahayi zuwa gare su da ayyukan alhẽri da tsayar da salla da bãyar da zakka. Kuma sun kasance mãsu bauta gare Mu.

  74. وَلُوطًا ءَاتَيْنَـٰهُ حُكْمًا وَعِلْمًا وَنَجَّيْنَـٰهُ مِنَ ٱلْقَرْيَةِ ٱلَّتِى كَانَت تَّعْمَلُ ٱلْخَبَـٰٓئِثَ ۗ إِنَّهُمْ كَانُوا۟ قَوْمَ سَوْءٍ فَـٰسِقِينَ۝٧٤

    Walootan ataynahu hukman waʿilman wanajjaynahu mina alqaryati allatee kanat taʿmalu alkhabaitha innahum kanoo qawma sawin fasiqeena

    Kuma Lũɗu Mun bã shi hukunci da ilmi. Kuma Mun tsĩrar da shi daga alƙaryar nan wadda ke aikata mũnãnan ayyuka. Lallesũ, sun kasance mutãnen mũgun aiki, fãsiƙai.

  75. وَأَدْخَلْنَـٰهُ فِى رَحْمَتِنَآ ۖ إِنَّهُۥ مِنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ۝٧٥

    Waadkhalnahu fee rahmatina innahu mina alssaliheena

    Kuma Muka shigar da shi a cikin rahamarMu. Lalle ne shĩ, yanã daga sãlihai.

  76. وَنُوحًا إِذْ نَادَىٰ مِن قَبْلُ فَٱسْتَجَبْنَا لَهُۥ فَنَجَّيْنَـٰهُ وَأَهْلَهُۥ مِنَ ٱلْكَرْبِ ٱلْعَظِيمِ۝٧٦

    Wanoohan ith nada min qablu faistajabna lahu fanajjaynahu waahlahu mina alkarbi alʿatheemi

    Kuma Nũhu, a sa'ad da ya yi kira a gabãni, sai Muka karɓa masa, sa'an nan Muka tsirar da shi da mutãnensa daga baƙin ciki mai girma.

  77. وَنَصَرْنَـٰهُ مِنَ ٱلْقَوْمِ ٱلَّذِينَ كَذَّبُوا۟ بِـَٔايَـٰتِنَآ ۚ إِنَّهُمْ كَانُوا۟ قَوْمَ سَوْءٍ فَأَغْرَقْنَـٰهُمْ أَجْمَعِينَ۝٧٧

    Wanasarnahu mina alqawmi allatheena kaththaboo biayatina innahum kanoo qawma sawin faaghraqnahum ajmaʿeena

    Kuma Muka taimake shi daga mutãnen nan waɗanda suka ƙaryata da ãyõyinMu. Lalle ne sũ, sun kasance mutãnen mugun aiki. Sai Muka nutsar da su gabã ɗaya.

  78. وَدَاوُۥدَ وَسُلَيْمَـٰنَ إِذْ يَحْكُمَانِ فِى ٱلْحَرْثِ إِذْ نَفَشَتْ فِيهِ غَنَمُ ٱلْقَوْمِ وَكُنَّا لِحُكْمِهِمْ شَـٰهِدِينَ۝٧٨

    Wadawooda wasulaymana ith yahkumani fee alharthi ith nafashat feehi ghanamu alqawmi wakunna lihukmihim shahideena

    Kuma Dãwũda da Sulaimãn sa'ad da suke yin hukunci a cikin sha'anin shũka a lõkacin da tumãkin mutãne suka yi kiĩwon dare a cikinsa. Kuma Mun kasance Mãsu halarta ga hukuncinsu.

  79. فَفَهَّمْنَـٰهَا سُلَيْمَـٰنَ ۚ وَكُلًّا ءَاتَيْنَا حُكْمًا وَعِلْمًا ۚ وَسَخَّرْنَا مَعَ دَاوُۥدَ ٱلْجِبَالَ يُسَبِّحْنَ وَٱلطَّيْرَ ۚ وَكُنَّا فَـٰعِلِينَ۝٧٩

    Fafahhamnaha sulaymana wakullan atayna hukman waʿilman wasakhkharna maʿa dawooda aljibala yusabbihna waalttayra wakunna faʿileena

    Sai Muka fahimtar da ita (mats'alar)1 ga Sulaiman. Kuma dukansu Mun bã su hukunci da ilmi kuma Muka hõre duwatsu tãre da Dãwũda, sunã tasbĩhi, da tsuntsãye. Kuma Mun kasance Mãsu aikatãwa.

    Bayanai
    [1] Asalin mats'alar, tumãkin wani mutum suka yi kĩwon ɓarna a gõnar wani a cikin dare alhãli kuwa anã kallafa wa mai dabbõbi ya kange dabbõbinsa da dare kamar yadda ake kallafa wa mai shũka da tsare shũkarsa a cikin yini. Sai Dãwũdu ya yi hukunci da cewa mai shũkar ya mallaki tumakin, shi kuma mai tumãki ya mallaki shũkar ɓãtacciya. Sai Sulaimãn ya gyãra hukuncin da cħwa mai gõna ya riƙi tumãkin ya rãyu a kansu har a lõkacin da mai dabbõbin ya gyãra masa gonarsa har ta Koma yadda take a farKon lõkacin,sa'an nan ya mayar da tumãkin ya karɓi gõnarsa. A cikin ƙissar akwai nũnin cewa Annabãwa bã su saunar faɗin gaskiya, sabõda wani mutum duk yadda yake, kuma anã warware hukunci idan kuskure ya auku a ciki, kuma Annabãwa sunã yin kuskure ga abin da bai shãfi wahayiba. Kuma kõmãwa ga askiya idan tã bayyana wajibi ne.
  80. وَعَلَّمْنَـٰهُ صَنْعَةَ لَبُوسٍ لَّكُمْ لِتُحْصِنَكُم مِّنۢ بَأْسِكُمْ ۖ فَهَلْ أَنتُمْ شَـٰكِرُونَ۝٨٠

    Waʿallamnahu sanʿata laboosin lakum lituhsinakum min basikum fahal antum shakiroona

    Kuma Muka sanar da shi sana'ar1 wata tufa sabõda ku dõmin ya tsare ku daga makãminku. To, shin, ku mãsu gõdẽwa ne?

    Bayanai
    [1] Wannan yanã nũna wajabcin yin sana'a wadda mutum ke rãyuwa a kanta. Kuma yanã nũna wajabcin aiki da sabubba dõmin neman tsaron kai. Bã ya halatta ga mutum ya yi kwance bãbu sanã'ar da zai tsayu a kanta Kõ kuma ya gĩtta kansa ga halaka da tãwilin tawakkali. Tawakkali shĩ ne mayar da ãƙibar al'amura ga Allah a bãyan mutum ya yi abinda yake iya yi.
  81. وَلِسُلَيْمَـٰنَ ٱلرِّيحَ عَاصِفَةً تَجْرِى بِأَمْرِهِۦٓ إِلَى ٱلْأَرْضِ ٱلَّتِى بَـٰرَكْنَا فِيهَا ۚ وَكُنَّا بِكُلِّ شَىْءٍ عَـٰلِمِينَ۝٨١

    Walisulaymana alrreeha ʿasifatan tajree biamrihi ila alardi allatee barakna feeha wakunna bikulli shayin ʿalimeena

    Kuma (Muka hõre) wa Sulaimãn iska mai tsananin bugãwa, tanã gudãna da umuruinsa zuwa ga ƙasar nan wadda Muka sanya albarka a cikinta. Kuma Mun kasance Masana ga dukkan Kõme.

  82. وَمِنَ ٱلشَّيَـٰطِينِ مَن يَغُوصُونَ لَهُۥ وَيَعْمَلُونَ عَمَلًا دُونَ ذَٰلِكَ ۖ وَكُنَّا لَهُمْ حَـٰفِظِينَ۝٨٢

    Wamina alshshayateeni man yaghoosoona lahu wayaʿmaloona ʿamalan doona thalika wakunna lahum hafitheena

    Kuma daga Shaiɗannu (Mun hõre) wanda ke nutso sabõda shi. Kuma sunã yin wani aiki baicin wancan. Kuma Mun kasance Mãsu tsaro a gare su.

  83. ۞ وَأَيُّوبَ إِذْ نَادَىٰ رَبَّهُۥٓ أَنِّى مَسَّنِىَ ٱلضُّرُّ وَأَنتَ أَرْحَمُ ٱلرَّٰحِمِينَ۝٨٣

    Waayyooba ith nada rabbahu annee massaniya alddurru waanta arhamu alrrahimeena

    Kuma da Ayyũba a sã'ad da ya yi kiran Ubangijinsa, (ya ce:) "Lalle nĩ, cũta ta shãfe ni, alhãli kuwa Kai ne Mafi rahamar mãsu rahama."

  84. فَٱسْتَجَبْنَا لَهُۥ فَكَشَفْنَا مَا بِهِۦ مِن ضُرٍّ ۖ وَءَاتَيْنَـٰهُ أَهْلَهُۥ وَمِثْلَهُم مَّعَهُمْ رَحْمَةً مِّنْ عِندِنَا وَذِكْرَىٰ لِلْعَـٰبِدِينَ۝٨٤

    Faistajabna lahu fakashafna ma bihi min durrin waataynahu ahlahu wamithlahum maʿahum rahmatan min ʿindina wathikra lilʿabideena

    Sai Muka karɓa masa, sa'an nan Muka kuranye abin da ke a gare shi na cũta, kuma Muka kãwo masa mutãnesa da kwatank wacinsu tãre da su, sabõda rahama daga wurin Mu da tunãtarwa1 ga mãsu ibãda.

    Bayanai
    [1] Ayyuba Manzon Allah, an jarrabe shi da wahalõlĩ ga jikinsa da halakar ɗiyansa ya yi haƙuri da hukuncin Allah, sai Allah Ya mayar masa da abin da ya halaka, sa'an nankuma ya ƙãrã masa wani kamarsa, dõmin rahamarSa ga mãsu mayar da al'amari a gare shi, da kuma wa'azi ga mãsuibãda dõmin kada aukuwar wata masĩfa ta sanya su kãtsewa da rashin ɗaukar haƙuri.
  85. وَإِسْمَـٰعِيلَ وَإِدْرِيسَ وَذَا ٱلْكِفْلِ ۖ كُلٌّ مِّنَ ٱلصَّـٰبِرِينَ۝٨٥

    Waismaʿeela waidreesa watha alkifli kullun mina alssabireena

    Kuma da Ismãĩla da Idrĩsa da Zulkifli, dukansu sunã daga mãsu haƙuri.

  86. وَأَدْخَلْنَـٰهُمْ فِى رَحْمَتِنَآ ۖ إِنَّهُم مِّنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ۝٨٦

    Waadkhalnahum fee rahmatina innahum mina alssaliheena

    Kuma Muka shigar da su a cikin rahamar Mu. Lalle ne, sunã daga sãlihai.

  87. وَذَا ٱلنُّونِ إِذ ذَّهَبَ مُغَـٰضِبًا فَظَنَّ أَن لَّن نَّقْدِرَ عَلَيْهِ فَنَادَىٰ فِى ٱلظُّلُمَـٰتِ أَن لَّآ إِلَـٰهَ إِلَّآ أَنتَ سُبْحَـٰنَكَ إِنِّى كُنتُ مِنَ ٱلظَّـٰلِمِينَ۝٨٧

    Watha alnnooni ith thahaba mughadiban fathanna an lan naqdira ʿalayhi fanada fee alththulumati an la ilaha illa anta subhanaka innee kuntu mina alththalimeena

    Kuma mai kifi1 a sã'ad da ya tafi yanã mai hushi, sai ya yi zaton cẽwa ba zã Mu ƙuƙunta masa ba. Sai ya yi kira a cikin duffai cẽwa, "Bãbu abĩn bautãwa fãce Kai. Tsarki ya tabbata a gare Ka. Lalle ne nĩ, na kasance daga azzãlumai."

    Bayanai
    [1] Shĩ ne Yũnus bn Matta. Yãyi hushi da mutãnensa dõmin ba su karɓi addini ba, sai ya bar su tun a gabãnin a yi masa iznin barinsu. Sai Allah Ya jarrabe shi da fãɗãwã cikin ruwa har wani kĩfi ya haɗiye Shi, sa'an nan kuma ya amãyo Shi a bãyan wahala, ya kõma wa mutãnensa. Suka yĩ ĩmãni.
  88. فَٱسْتَجَبْنَا لَهُۥ وَنَجَّيْنَـٰهُ مِنَ ٱلْغَمِّ ۚ وَكَذَٰلِكَ نُـۨجِى ٱلْمُؤْمِنِينَ۝٨٨

    Faistajabna lahu wanajjaynahu mina alghammi wakathalika nunjee almumineena

    Sai Muka karɓa masa kuma Muka tsĩrar da shi daga baƙin ciki. Kamar haka ne Muke tsĩrarda masu ĩmãni.

  89. وَزَكَرِيَّآ إِذْ نَادَىٰ رَبَّهُۥ رَبِّ لَا تَذَرْنِى فَرْدًا وَأَنتَ خَيْرُ ٱلْوَٰرِثِينَ۝٨٩

    Wazakariyya ith nada rabbahu rabbi la tatharnee fardan waanta khayru alwaritheena

    Kuma da Zakariyya a sa'ad da ya kirãyi Ubangijinsa cẽwa, "Ya Ubangiji! Kada Ka bar ni makaɗaici alhãli kuwa Kai ne Mafi alhẽrin mãsu gãdo."

  90. فَٱسْتَجَبْنَا لَهُۥ وَوَهَبْنَا لَهُۥ يَحْيَىٰ وَأَصْلَحْنَا لَهُۥ زَوْجَهُۥٓ ۚ إِنَّهُمْ كَانُوا۟ يُسَـٰرِعُونَ فِى ٱلْخَيْرَٰتِ وَيَدْعُونَنَا رَغَبًا وَرَهَبًا ۖ وَكَانُوا۟ لَنَا خَـٰشِعِينَ۝٩٠

    Faistajabna lahu wawahabna lahu yahya waaslahna lahu zawjahu innahum kanoo yusariʿoona fee alkhayrati wayadʿoonana raghaban warahaban wakanoo lana khashiʿeena

    Sai Muka karɓa masa kuma Muka kyautata1 masa mãtarsa. Lalle ne sũ, sun kasance sunã gudun tsẽre zuwa ga ayyukan alhẽri. Kuma sunã kiran Mu a kan kwaɗayi da fargaba. Kuma sun kasance mãsu saunar (aikata sãɓo) gare Mu.

    Bayanai
    [1] Bãyan mãtarsa ta tsũfa ba ta haihu ba Allah Ya kyautata mahaifarta, ta sãmi cikin Yahaya daga gare shi.
  91. وَٱلَّتِىٓ أَحْصَنَتْ فَرْجَهَا فَنَفَخْنَا فِيهَا مِن رُّوحِنَا وَجَعَلْنَـٰهَا وَٱبْنَهَآ ءَايَةً لِّلْعَـٰلَمِينَ۝٩١

    Waallatee ahsanat farjaha fanafakhna feeha min roohina wajaʿalnaha waibnaha ayatan lilʿalameena

    Kuma da wadda ta tsare farJinta daga alfãsha. Sai Muka hũra a cikinta daga rũhinMu.1 Kuma Muka sanya ta ita da ɗanta wata ãyã ga dũniya.

    Bayanai
    [1] Rũhin Allah a nan, shi ne Malã'ika jibrĩla. Shĩ ne ya hũra a cikin wuyan rĩgarta, sai ta yi cikĩ da Ĩsã. Maryamu bã Annabiya ba ce, an ambace ta ne dõmin shimfiɗa ga maganar Ĩsã, amincin Allah ya tabbata a gare Shi. Zamanta ãyã shi ne ta sãmi ɗã bãda namiji ba, kuma wanda ya yi haƙuri ga tsaron haddojin Allah, Allah zai ɗaukaka shi da ni'imar dũniya da ta Lãhira. Ɗanta ya zama ãyã sabõda magana yana yãro, da Annabci da ɗaukar haƙuri ga zartar da umurnin Allah.
  92. إِنَّ هَـٰذِهِۦٓ أُمَّتُكُمْ أُمَّةً وَٰحِدَةً وَأَنَا۠ رَبُّكُمْ فَٱعْبُدُونِ۝٩٢

    Inna hathihi ommatukum ommatan wahidatan waana rabbukum faoʿbudooni

    Lalle ne wannan1 ita ce al'ummarku ta zama al'umma guda, kuma Nĩ ne Ubangijinku. Sai ku bauta Mini.

    Bayanai
    [1] Al'ummar Musulmi duka guda ce kõ da yake Annabãwansu sun zo dabam-dabam, a cikin lõkuta mãsu nĩSa tsakãninsu da harsuna dabam-dabam dõmin duk aƙĩdarsu guda ce a kan Ubangiji guda ne. Sa'an nan daga bãya waɗanda suka fita daga wannan aƙĩdar suka rarrabu ƙungiya-ƙungiya.
  93. وَتَقَطَّعُوٓا۟ أَمْرَهُم بَيْنَهُمْ ۖ كُلٌّ إِلَيْنَا رَٰجِعُونَ۝٩٣

    Wataqattaʿoo amrahum baynahum kullun ilayna rajiʿoona

    Kuma suka kakkãtse al'amarinsu a tsakaninsu. Dukan Kõwanensu mãsu Kõmõwa zuwa gare Ni

  94. فَمَن يَعْمَلْ مِنَ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ وَهُوَ مُؤْمِنٌ فَلَا كُفْرَانَ لِسَعْيِهِۦ وَإِنَّا لَهُۥ كَـٰتِبُونَ۝٩٤

    Faman yaʿmal mina alssalihati wahuwa muminun fala kufrana lisaʿyihi wainna lahu katiboona

    Dõmin wanda ya aikata daga ayyukan kwarai alhãli kuwa yanã mai ĩmãni, to, bãbu musu ga aikinsa, kuma Mu Mãsu rubũtãwa gare shi ne.

  95. وَحَرَٰمٌ عَلَىٰ قَرْيَةٍ أَهْلَكْنَـٰهَآ أَنَّهُمْ لَا يَرْجِعُونَ۝٩٥

    Waharamun ʿala qaryatin ahlaknaha annahum la yarjiʿoona

    Kuma hananne ne a kan wata alƙarya da Muka halakar cẽwa lalle sũ, bã su kõmõwa.

  96. حَتَّىٰٓ إِذَا فُتِحَتْ يَأْجُوجُ وَمَأْجُوجُ وَهُم مِّن كُلِّ حَدَبٍ يَنسِلُونَ۝٩٦

    Hatta itha futihat yajooju wamajooju wahum min kulli hadabin yansiloona

    Har sa'ad da aka bũde Yãjũju da Mãjũju alhãli kuwa sunã gaggãwa daga kõwane tudun ƙasa.

  97. وَٱقْتَرَبَ ٱلْوَعْدُ ٱلْحَقُّ فَإِذَا هِىَ شَـٰخِصَةٌ أَبْصَـٰرُ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ يَـٰوَيْلَنَا قَدْ كُنَّا فِى غَفْلَةٍ مِّنْ هَـٰذَا بَلْ كُنَّا ظَـٰلِمِينَ۝٩٧

    Waiqtaraba alwaʿdu alhaqqu faitha hiya shakhisatun absaru allatheena kafaroo ya waylana qad kunna fee ghaflatin min hatha bal kunna thalimeena

    Kuma wa'adin nan tabbatacce ya kusanto, sai gã ta idãnun waɗanda suka kãfirta sunã bayyanannu, (sunã cẽwa), "Yã kaitonmu! Haƙĩƙa mun kasance a cikin gafala daga wannan! Ã'a, mun kasance dai mãsu zãlunci!"

  98. إِنَّكُمْ وَمَا تَعْبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ حَصَبُ جَهَنَّمَ أَنتُمْ لَهَا وَٰرِدُونَ۝٩٨

    Innakum wama taʿbudoona min dooni Allahi hasabu jahannama antum laha waridoona

    (A ce musu) "Lalle ne, kũ da abin1 da kuke bautãwa, baicin Allah makãmashin Jahannama ne. Kũ mãsu tusgãwa gare ta ne."

    Bayanai
    [1] Bãyin Allah sãlihai da malãiku waɗanda waɗansu mutãne suka bauta musu da tsammãnin cewa zã su cecesu daga Allah, bã zai sanya su Wuta ba sabõda ibãdar da aka yi musu, dõmin yabon Allah yã rigãyi hushinsa zuwa gare su. Bãyansu da mai bautar da wanda ake bautawar kamar gumãka da waɗansunsu, Wuta za su shiga.
  99. لَوْ كَانَ هَـٰٓؤُلَآءِ ءَالِهَةً مَّا وَرَدُوهَا ۖ وَكُلٌّ فِيهَا خَـٰلِدُونَ۝٩٩

    Law kana haolai alihatan ma waradooha wakullun feeha khalidoona

    Dã waɗannan (abũbuwanbautãwar) sun kasance abũbuwan bautãwar gaskiya ne, dã ba su tusga mata ba, alhãli kuwa dukansu madawwama a cikinta ne.

  100. لَهُمْ فِيهَا زَفِيرٌ وَهُمْ فِيهَا لَا يَسْمَعُونَ۝١٠٠

    Lahum feeha zafeerun wahum feeha la yasmaʿoona

    Sunã da wata hargõwa a cikinta, alhãli kuwa sũ, a cikinta, bã su saurãren kõme.

  101. إِنَّ ٱلَّذِينَ سَبَقَتْ لَهُم مِّنَّا ٱلْحُسْنَىٰٓ أُو۟لَـٰٓئِكَ عَنْهَا مُبْعَدُونَ۝١٠١

    Inna allatheena sabaqat lahum minna alhusna olaika ʿanha mubʿadoona

    Lalle ne waɗanda kalmar yabo tã gabãta a garẽ su daga garẽ Mu, waɗannan waɗanda ake nĩsantarwa daga barinta ne.

  102. لَا يَسْمَعُونَ حَسِيسَهَا ۖ وَهُمْ فِى مَا ٱشْتَهَتْ أَنفُسُهُمْ خَـٰلِدُونَ۝١٠٢

    La yasmaʿoona haseesaha wahum fee ma ishtahat anfusuhum khalidoona

    Bã su jin sautin mõtsinta alhãli kuwa sũ madawwamãne a cikin abin da rãyukansu suka yi marmarinsa.

  103. لَا يَحْزُنُهُمُ ٱلْفَزَعُ ٱلْأَكْبَرُ وَتَتَلَقَّىٰهُمُ ٱلْمَلَـٰٓئِكَةُ هَـٰذَا يَوْمُكُمُ ٱلَّذِى كُنتُمْ تُوعَدُونَ۝١٠٣

    La yahzunuhumu alfazaʿu alakbaru watatalaqqahumu almalaikatu hatha yawmukumu allathee kuntum tooʿadoona

    Firgitar nan mafi girma, bã zã ta baƙantã musu rai ba. Kuma malã'iku na yi musu marãba (sunã cẽwa) "Wannan yininku nẽ wanda kuka kasance anã yi muku wa'adi da shi."

  104. يَوْمَ نَطْوِى ٱلسَّمَآءَ كَطَىِّ ٱلسِّجِلِّ لِلْكُتُبِ ۚ كَمَا بَدَأْنَآ أَوَّلَ خَلْقٍ نُّعِيدُهُۥ ۚ وَعْدًا عَلَيْنَآ ۚ إِنَّا كُنَّا فَـٰعِلِينَ۝١٠٤

    Yawma natwee alssamaa katayyi alssijlli lilkutubi kama badana awwala khalqin nuʿeeduhu waʿdan ʿalayna inna kunna faʿileena

    A rãnar da Muke naɗe sãma kamar neɗẽwar takarda ga abũbuwan rubũtãwa kamar yadda Muka fãra a farKon1 halitta Muke mãyar da ita. Wa'adi ne a Kanmu. Lalle ne Mun kasance Mãsu aikatãwa.

    Bayanai
    [1] Tun da fãrãwa bai buwãye Mu ba mayarwa ba za ta buwãye Mu ba. A Rãnar Ƙiyãma ake naɗe sama kan abin da yake a cikinta kamar yadda ake naɗe takarda a kan abin da ta ƙunsa na rubutun malã'iku a kan bãyin Allah.
  105. وَلَقَدْ كَتَبْنَا فِى ٱلزَّبُورِ مِنۢ بَعْدِ ٱلذِّكْرِ أَنَّ ٱلْأَرْضَ يَرِثُهَا عِبَادِىَ ٱلصَّـٰلِحُونَ۝١٠٥

    Walaqad katabna fee alzzaboori min baʿdi alththikri anna alarda yarithuha ʿibadiya alssalihoona

    Kuma lalle haƙĩƙa Mun rubũta a cikin Littãfi baicin Ambato1 (Lauhul Mahfũz) cẽwa ƙasã, bayĩna sãlihai, sunã gãdonta.

    Bayanai
    [1] Allah Yanã mallakar da ƙasa bãyinsa sãlihai, bã zã ta fita daga gare su ba sai idan sun musanya addininsu na ƙwarai da wani mugu.
  106. إِنَّ فِى هَـٰذَا لَبَلَـٰغًا لِّقَوْمٍ عَـٰبِدِينَ۝١٠٦

    Inna fee hatha labalaghan liqawmin ʿabideena

    Lalle ne a cikin wannan (Alƙur'ãni), haƙĩƙa, akwai iyarwa (ga maganar da ta gabãta1 ga waɗansu mutãne mãsu ibãda.

    Bayanai
    [1] Ita ce cewar, Allah sãlihai sunã gadon ƙasa.
  107. وَمَآ أَرْسَلْنَـٰكَ إِلَّا رَحْمَةً لِّلْعَـٰلَمِينَ۝١٠٧

    Wama arsalnaka illa rahmatan lilʿalameena

    Kuma ba Mu aike ka ba fãce dõmin wata rahama ga talikai.

  108. قُلْ إِنَّمَا يُوحَىٰٓ إِلَىَّ أَنَّمَآ إِلَـٰهُكُمْ إِلَـٰهٌ وَٰحِدٌ ۖ فَهَلْ أَنتُم مُّسْلِمُونَ۝١٠٨

    Qul innama yooha ilayya annama ilahukum ilahun wahidun fahal antum muslimoona

    Ka ce: "Abin sani kawai, anã yin wahayi zuwa gare ni ne, cẽwa, lalle ne, Abin bautãwarku, Abin bautãwa ne Guda. To shin kũ mãsu mĩƙa wuya ne?"

  109. فَإِن تَوَلَّوْا۟ فَقُلْ ءَاذَنتُكُمْ عَلَىٰ سَوَآءٍ ۖ وَإِنْ أَدْرِىٓ أَقَرِيبٌ أَم بَعِيدٌ مَّا تُوعَدُونَ۝١٠٩

    Fain tawallaw faqul athantukum ʿala sawain wain adree aqareebun am baʿeedun ma tooʿadoona

    Sa'an nan idan suka jũya, to, ka ce: "Nã sanar da ku, a kan daidaita, kuma ban sani ba, shin, abin da ake yi muku wa'adi makusanci ne Kõ kuwa manĩsanci?"

  110. إِنَّهُۥ يَعْلَمُ ٱلْجَهْرَ مِنَ ٱلْقَوْلِ وَيَعْلَمُ مَا تَكْتُمُونَ۝١١٠

    Innahu yaʿlamu aljahra mina alqawli wayaʿlamu ma taktumoona

    "Lalle ne Shĩ (Allah) Yanã sanin bayyane daga magana, kuma Yanã sanin abin da kuke ɓõyẽwa.

  111. وَإِنْ أَدْرِى لَعَلَّهُۥ فِتْنَةٌ لَّكُمْ وَمَتَـٰعٌ إِلَىٰ حِينٍ۝١١١

    Wain adree laʿallahu fitnatun lakum wamataʿun ila heenin

    "Kuma ban sani ba, tsammãninsa ya zama fitina a gare ku, kõ kuma don jin dãɗi, zuwa ga wani ɗan lõkaci."

  112. قَـٰلَ رَبِّ ٱحْكُم بِٱلْحَقِّ ۗ وَرَبُّنَا ٱلرَّحْمَـٰنُ ٱلْمُسْتَعَانُ عَلَىٰ مَا تَصِفُونَ۝١١٢

    Qala rabbi ohkum bialhaqqi warabbuna alrrahmanu almustaʿanu ʿala ma tasifoona

    Ya ce: "Yã Ubangiji! Ka yi hukunci da gaskiya. Kuma Ubangijinmu Mai rahama ne Wanda ake nẽman taimakonSa a kan abinda kuke siffantãwa."

Tambayoyin da ake yawan yi

Mece ce ma’anar sunan Suratul Anbiya’i?

Ma’anar Anbiya’i ita ce “Annabawa”.

Suratul Anbiya’i tana cikin juz’i na nawa?

Suratul Anbiya’i tana cikin juz’i na 17.

Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Anbiya’i?

Suratul Anbiya’i tana da ayoyi 112.

Suratul Anbiya’i Makkiya ce ko Madaniya?

Suratul Anbiya’i sura ce Makkiya.

Suratul Anbiya’i ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?

Ita ce sura ta 21 a cikin Alƙur’ani.

Majiyoyi

  • Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
  • Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
  • Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
  • Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
  • Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
  • Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.

Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.

Saitunan karatu

Rubutun Alƙur’ani
Girman Larabci
100%
Girman fassara
100%
Kamanni

Ƙara zuwa Allon Gida

ReadSurahBuɗe ReadSurah daga allon gida, a cikakken allo. Surorin da kuka karanta suna buɗewa ko da babu intanet.

  1. A cikin Safari, taɓa maɓallin “Share”. A sababbin iPhone yana cikin menu na •••.
  2. Taɓa “Add to Home Screen”. Gungura ƙasa idan ba ku gan shi ba.
  3. Taɓa “Add”.