سورة الزخرف
Suratul Zukhruf da fassarar Hausa
Kayan adon zinariya
- 43
- ayoyi 89
- Makkiya
- Juz’i 25
- Shafuka 489–495
Suratul Zukhruf (الزخرف) ita ce sura ta 43 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 89. Ma’anar sunanta ita ce “Kayan adon zinariya”. Sura ce Makkiya, wadda ta sauka a Makka kafin Hijira, kuma tana cikin juz’i na 25.
A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Zukhruf gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.
Suratul Zukhruf cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ
-
حمٓ١
Hameem
Ḥ. M̃.
-
وَٱلْكِتَـٰبِ ٱلْمُبِينِ٢
Waalkitabi almubeeni
Ina rantsuwa da Littãfi Mabayyani.
-
إِنَّا جَعَلْنَـٰهُ قُرْءَٰنًا عَرَبِيًّا لَّعَلَّكُمْ تَعْقِلُونَ٣
Inna jaʿalnahu quranan ʿarabiyyan laʿallakum taʿqiloona
Lalle Mũ, Mun sanya shi abin karãtu na Lãrabci, tsammãninku, kunã hankalta.
-
وَإِنَّهُۥ فِىٓ أُمِّ ٱلْكِتَـٰبِ لَدَيْنَا لَعَلِىٌّ حَكِيمٌ٤
Wainnahu fee ommi alkitabi ladayna laʿaliyyun hakeemun
Kuma lalle, shĩ, a cikin uwar littãfi a wurin Mu, haƙĩƙa, maɗaukaki ne, bayyananne.
-
أَفَنَضْرِبُ عَنكُمُ ٱلذِّكْرَ صَفْحًا أَن كُنتُمْ قَوْمًا مُّسْرِفِينَ٥
Afanadribu ʿankumu alththikra safhan an kuntum qawman musrifeena
Shin, zã Mu kau da kai daga saukar da hukunci daga gare ku ne dõmin kun kasance mutane mãsu ɓarna?
-
وَكَمْ أَرْسَلْنَا مِن نَّبِىٍّ فِى ٱلْأَوَّلِينَ٦
Wakam arsalna min nabiyyin fee alawwaleena
Alhãli kuwa sau nawa Muka1aika wani Annabi a cikin mutãnen fãrko!
Bayanai
[1] Tun da ba Mu bar mutãnen farko mãsu ɓarna ba, sai da Muka aika musu Manzanni, kuma kõwace ƙungiya daga cikin waɗanda aka aikawa wani Manzo sai da ta yi izgili game da Manzonsu, har abin ya kai ga halakar shũgabanninsu. To, haka mutãnenka, bã zã Mu bar su ba, sabõda ɓarnarsu, sai Mun aike ka zuwa gare su, su yi izgili game da kai, har a halaka shũgabanninsu, sa'an nan sauransu, su bi abin da aka umurce su da shi. -
وَمَا يَأْتِيهِم مِّن نَّبِىٍّ إِلَّا كَانُوا۟ بِهِۦ يَسْتَهْزِءُونَ٧
Wama yateehim min nabiyyin illa kanoo bihi yastahzioona
Kuma wani Annabi bai je musu ba fãce sun kasance, game da shi, sunã mãsu yin izgili.
-
فَأَهْلَكْنَآ أَشَدَّ مِنْهُم بَطْشًا وَمَضَىٰ مَثَلُ ٱلْأَوَّلِينَ٨
Faahlakna ashadda minhum batshan wamada mathalu alawwaleena
Sai Muka halakar da waɗanda suke sũ ne mafiya ƙarfin damƙa daga gare su. Kuma abin misãlin mutãnen farkon ya shũɗe.
-
وَلَئِن سَأَلْتَهُم مَّنْ خَلَقَ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضَ لَيَقُولُنَّ خَلَقَهُنَّ ٱلْعَزِيزُ ٱلْعَلِيمُ٩
Walain saaltahum man khalaqa alssamawati waalarda layaqoolunna khalaqahunna alʿazeezu alʿaleemu
Kuma lalle ne, idan ka tambaye su, "Wãne ne ya halitta sammai da ƙasa?" Lalle zã su ce, "Mabuwãyi Mai ilmi ne Ya halitta su."
-
ٱلَّذِى جَعَلَ لَكُمُ ٱلْأَرْضَ مَهْدًا وَجَعَلَ لَكُمْ فِيهَا سُبُلًا لَّعَلَّكُمْ تَهْتَدُونَ١٠
Allathee jaʿala lakumu alarda mahdan wajaʿala lakum feeha subulan laʿallakum tahtadoona
Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa kuma Ya sanya muku hanyõyi a cikinta, tsammãninku za ku nẽmi shiryuwa.'
-
وَٱلَّذِى نَزَّلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءًۢ بِقَدَرٍ فَأَنشَرْنَا بِهِۦ بَلْدَةً مَّيْتًا ۚ كَذَٰلِكَ تُخْرَجُونَ١١
Waallathee nazzala mina alssamai maan biqadarin faansharna bihi baldatan maytan kathalika tukhrajoona
Kuma Wanda Ya saukar da ruwa daga sama, a kan wani gwargwado, sai Muka rãyar da gari matacce game da shi. Kamar haka nan ake fitar da ku (daga kabari).
-
وَٱلَّذِى خَلَقَ ٱلْأَزْوَٰجَ كُلَّهَا وَجَعَلَ لَكُم مِّنَ ٱلْفُلْكِ وَٱلْأَنْعَـٰمِ مَا تَرْكَبُونَ١٢
Waallathee khalaqa alazwaja kullaha wajaʿala lakum mina alfulki waalanʿami ma tarkaboona
Kuma Wanda Ya halitta ma'aura dukansu, kuma Ya sanya muku, daga jirgi da dabbõbin ni'ima, abin da kuke hawa.
-
لِتَسْتَوُۥا۟ عَلَىٰ ظُهُورِهِۦ ثُمَّ تَذْكُرُوا۟ نِعْمَةَ رَبِّكُمْ إِذَا ٱسْتَوَيْتُمْ عَلَيْهِ وَتَقُولُوا۟ سُبْحَـٰنَ ٱلَّذِى سَخَّرَ لَنَا هَـٰذَا وَمَا كُنَّا لَهُۥ مُقْرِنِينَ١٣
Litastawoo ʿala thuhoorihi thumma tathkuroo niʿmata rabbikum itha istawaytum ʿalayhi wataqooloo subhana allathee sakhkhara lana hatha wama kunna lahu muqrineena
Domin ku daidaitu a kan bãyansa, sa'an nan ku tuna ni'imar Ubangijinku a lõkacin da kuka daidaita a kansa kuma ku ce, "Tsarki ya tabbata ga Wanda Ya hõre mana wannan alhãli kuwa ba mu kasance mãsu iya rinjãya gare Shi ba.
-
وَإِنَّآ إِلَىٰ رَبِّنَا لَمُنقَلِبُونَ١٤
Wainna ila rabbina lamunqaliboona
"Kuma lalle mũ haƙĩƙa mãsu1 jũyãwa muke, zuwa ga Ubangijinmu."
Bayanai
[1] Ku yi dalĩli da hõrewar abin hawa gare ku zuwa ga tabbatar tãshinku dõmin hisãbin Ƙiyãma, dõmin ku bi umurninsa a dũniya, kuma ku bar al'adunku. -
وَجَعَلُوا۟ لَهُۥ مِنْ عِبَادِهِۦ جُزْءًا ۚ إِنَّ ٱلْإِنسَـٰنَ لَكَفُورٌ مُّبِينٌ١٥
Wajaʿaloo lahu min ʿibadihi juzan inna alinsana lakafoorun mubeenun
Kuma suka sanya1Masa juz'i daga bãyinsa. Lalle ne mutum, haƙĩƙa, mai yawan kãfirci ne, mai bayyanãwar kãfircin.
Bayanai
[1] suka ce malã'iku 'ya'ya mãtane na Allah, sunã bauta musu ne dõmin su kusantar da su zuwa ga Allah, watau dõmin su cece su daga azãba. Sun yi wannan ƙarya ne dõmin su tabbatar da al'ãdarsu ta surkulle. Sabõda haka suka yi wa Allah ƙarya suka naƙasa shi da haka, kuma suka naƙasa malã'iku mãsu daraja a wurin Allah kuma suka kãfirce wa ni'imar da Allah Ya yi musu wajen aiko musu Manzo mai shiryar da su. Sa'an suka kafa hujja da ƙarya dõmin su danne gaskiya. -
أَمِ ٱتَّخَذَ مِمَّا يَخْلُقُ بَنَاتٍ وَأَصْفَىٰكُم بِٱلْبَنِينَ١٦
Ami ittakhatha mimma yakhluqu banatin waasfakum bialbaneena
Kõ zã Ya ɗauki 'ya'ya mãtã daga abin da Yake halittawa ne, kuma Ya zãɓe ku da ɗiya maza?
-
وَإِذَا بُشِّرَ أَحَدُهُم بِمَا ضَرَبَ لِلرَّحْمَـٰنِ مَثَلًا ظَلَّ وَجْهُهُۥ مُسْوَدًّا وَهُوَ كَظِيمٌ١٧
Waitha bushshira ahaduhum bima daraba lilrrahmani mathalan thalla wajhuhu muswaddan wahuwa katheemun
Alhãli kuwa idan an bãyar da bushãra ga ɗayansu da abin da ya buga misãli da shi ga Mai rahama, sai fuskarsa ta yini tanã wadda aka baƙanta launinta, kuma yanã cike da baƙin ciki.
-
أَوَمَن يُنَشَّؤُا۟ فِى ٱلْحِلْيَةِ وَهُوَ فِى ٱلْخِصَامِ غَيْرُ مُبِينٍ١٨
Awaman yunashshao fee alhilyati wahuwa fee alkhisami ghayru mubeenin
Ashe, kuma (Allah zai zãɓi) wanda ake rẽno a cikin ƙawa alhãli kuwa gã shi a husũma bã mai iya bayyanawar magana ba?
-
وَجَعَلُوا۟ ٱلْمَلَـٰٓئِكَةَ ٱلَّذِينَ هُمْ عِبَـٰدُ ٱلرَّحْمَـٰنِ إِنَـٰثًا ۚ أَشَهِدُوا۟ خَلْقَهُمْ ۚ سَتُكْتَبُ شَهَـٰدَتُهُمْ وَيُسْـَٔلُونَ١٩
Wajaʿaloo almalaikata allatheena hum ʿibadu alrrahmani inathan ashahidoo khalqahum satuktabu shahadatuhum wayusaloona
Kuma suka mayar da malã'iku ('yã'ya) mãtã, alhãli kuwa sũ, waɗanda suke bãyin (Allah) Mai rahama ne! Shin, sun halarci halittarsu ne? zã a rubũta shaidarsu kuma a tambaye su.
-
وَقَالُوا۟ لَوْ شَآءَ ٱلرَّحْمَـٰنُ مَا عَبَدْنَـٰهُم ۗ مَّا لَهُم بِذَٰلِكَ مِنْ عِلْمٍ ۖ إِنْ هُمْ إِلَّا يَخْرُصُونَ٢٠
Waqaloo law shaa alrrahmanu ma ʿabadnahum ma lahum bithalika min ʿilmin in hum illa yakhrusoona
Kuma suka ce: "Dã Mai rahama ya so, dã ba mu bauta musu ba." Bã su da wani ilmi game da wancan! Bãbu abin da suke yi fãce yanki-faɗi.
-
أَمْ ءَاتَيْنَـٰهُمْ كِتَـٰبًا مِّن قَبْلِهِۦ فَهُم بِهِۦ مُسْتَمْسِكُونَ٢١
Am ataynahum kitaban min qablihi fahum bihi mustamsikoona
Kõ Mun bã su wani littãfi ne a gabãninsa (Alƙur'ãni) sabõda haka da shĩ suke riƙe?
-
بَلْ قَالُوٓا۟ إِنَّا وَجَدْنَآ ءَابَآءَنَا عَلَىٰٓ أُمَّةٍ وَإِنَّا عَلَىٰٓ ءَاثَـٰرِهِم مُّهْتَدُونَ٢٢
Bal qaloo inna wajadna abaana ʿala ommatin wainna ʿala atharihim muhtadoona
Ã'a, sun ce dai, "Lalle mũ, mun sãmi ubanninmu a kan wani addini (na al'ãda) kuma lalle mũ, a kan gurãbansu muke mãsu nẽman shiryuwa."
-
وَكَذَٰلِكَ مَآ أَرْسَلْنَا مِن قَبْلِكَ فِى قَرْيَةٍ مِّن نَّذِيرٍ إِلَّا قَالَ مُتْرَفُوهَآ إِنَّا وَجَدْنَآ ءَابَآءَنَا عَلَىٰٓ أُمَّةٍ وَإِنَّا عَلَىٰٓ ءَاثَـٰرِهِم مُّقْتَدُونَ٢٣
Wakathalika ma arsalna min qablika fee qaryatin min natheerin illa qala mutrafooha inna wajadna abaana ʿala ommatin wainna ʿala atharihim muqtadoona
Kuma kamar haka, ba Mu aika wani mai gargaɗi ba a gabãninka, a cikin wata alƙarya, fãce mani'imtanta sun ce, "Lalle mũ, mun sãmi ubanninmu a kan wani addini kuma lalle mũ, mãsu kõyi nea kan gurãbansu."
-
۞ قَـٰلَ أَوَلَوْ جِئْتُكُم بِأَهْدَىٰ مِمَّا وَجَدتُّمْ عَلَيْهِ ءَابَآءَكُمْ ۖ قَالُوٓا۟ إِنَّا بِمَآ أُرْسِلْتُم بِهِۦ كَـٰفِرُونَ٢٤
Qala awalaw jitukum biahda mimma wajadtum ʿalayhi abaakum qaloo inna bima orsiltum bihi kafiroona
(Sai mai gargaɗin) ya ce: "Shin, ban zo muku da abin da ya fi zama shiriya daga abin da kuka sãmi ubanninku a kansa ba?" Suka ce, "Lalle mũ dai mãsu kafirta ne game da abin da aka aiko ku da shi."
-
فَٱنتَقَمْنَا مِنْهُمْ ۖ فَٱنظُرْ كَيْفَ كَانَ عَـٰقِبَةُ ٱلْمُكَذِّبِينَ٢٥
Faintaqamna minhum faonthur kayfa kana ʿaqibatu almukaththibeena
Sabõda haka Muka yi musu azãbar rãmuwa. To, ka dũbi yadda ãƙibar mãsu ƙaryatãwa take.
-
وَإِذْ قَالَ إِبْرَٰهِيمُ لِأَبِيهِ وَقَوْمِهِۦٓ إِنَّنِى بَرَآءٌ مِّمَّا تَعْبُدُونَ٢٦
Waith qala ibraheemu liabeehi waqawmihi innanee baraon mimma taʿbudoona
Kuma (ka ambaci) lõkacin da Ibrãhĩm ya ce wa ubansada mutãnensa, "Lalle nĩ mai barranta ne daga abin da kuke bautãwa."
-
إِلَّا ٱلَّذِى فَطَرَنِى فَإِنَّهُۥ سَيَهْدِينِ٢٧
Illa allathee fataranee fainnahu sayahdeeni
"Fãce wannan1da Ya ƙãga halittata, to, lalle Shĩ ne zai shiryar da ni."
Bayanai
[1] Bã ni bauta wa gumãka, amma inã bautawa Allah wanda Ya ƙãgi halittata. -
وَجَعَلَهَا كَلِمَةًۢ بَاقِيَةً فِى عَقِبِهِۦ لَعَلَّهُمْ يَرْجِعُونَ٢٨
Wajaʿalaha kalimatan baqiyatan fee ʿaqibihi laʿallahum yarjiʿoona
Kuma (Ibrãhĩm) ya sanya (ita wannan magana) kalma mai wanzuwa a cikin zuriyarsa, tsammãninsu su kõmo daga ɓata.
-
بَلْ مَتَّعْتُ هَـٰٓؤُلَآءِ وَءَابَآءَهُمْ حَتَّىٰ جَآءَهُمُ ٱلْحَقُّ وَرَسُولٌ مُّبِينٌ٢٩
Bal mattaʿtu haolai waabaahum hatta jaahumu alhaqqu warasoolun mubeenun
Ã'a, Na jiyar da waɗannan mutãne dãɗi sũ da ubanninsu har gaskiya, da Manzo mai bayyanawar gaskiyar, ya zo musu.
-
وَلَمَّا جَآءَهُمُ ٱلْحَقُّ قَالُوا۟ هَـٰذَا سِحْرٌ وَإِنَّا بِهِۦ كَـٰفِرُونَ٣٠
Walamma jaahumu alhaqqu qaloo hatha sihrun wainna bihi kafiroona
Kuma a lõkacin da gaskiyar ta jẽ musu sai suka ce: "Wannan sihiri ne kuma mũ mãsu kãfirta da shi ne."
-
وَقَالُوا۟ لَوْلَا نُزِّلَ هَـٰذَا ٱلْقُرْءَانُ عَلَىٰ رَجُلٍ مِّنَ ٱلْقَرْيَتَيْنِ عَظِيمٍ٣١
Waqaloo lawla nuzzila hatha alquranu ʿala rajulin mina alqaryatayni ʿatheemun
Kuma suka ce: "Don me ba a saukar da wannan Alƙur'ãni a kan wani mutum mai girma daga alƙaryun1 nan biyu ba?"
Bayanai
[1] Sunã nufin Makka da tã'ifa, kuma sunã nufi a saukar da Alƙur'ãni ga walĩdu ɗan Mugĩra na Makka kõ ga Urwatu ɗan Mas'ũdi As saƙafi a Ta'ifa. Watau sunã sũkar Muhammadu dõmin bã shi da dũkiya. A gare su mai dũkiya shĩ ne babban mutum, wanda ya cancanta Allah Ya aiko shi ga mutãne. -
أَهُمْ يَقْسِمُونَ رَحْمَتَ رَبِّكَ ۚ نَحْنُ قَسَمْنَا بَيْنَهُم مَّعِيشَتَهُمْ فِى ٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا ۚ وَرَفَعْنَا بَعْضَهُمْ فَوْقَ بَعْضٍ دَرَجَـٰتٍ لِّيَتَّخِذَ بَعْضُهُم بَعْضًا سُخْرِيًّا ۗ وَرَحْمَتُ رَبِّكَ خَيْرٌ مِّمَّا يَجْمَعُونَ٣٢
Ahum yaqsimoona rahmata rabbika nahnu qasamna baynahum maʿeeshatahum fee alhayati alddunya warafaʿna baʿdahum fawqa baʿdin darajatin liyattakhitha baʿduhum baʿdan sukhriyyan warahmatu rabbika khayrun mimma yajmaʿoona
Shin, sũ ne ke raba rahamar Ubangijinka? Mũ ne, Muka raba musu abincinsu a cikin rãyuwar dũniya, kuma Muka ɗaukaka waɗansunsu a kan waɗansu da darajõji dõmin waɗansunsu su riƙi waɗansu lẽburori kumarahamar Ubangijinka (ta Annabci1), ita ce mafificiya daga abin da suke tãrãwa.
Bayanai
[1] Tun da ba Mu bar rabon abincin rãyuwarsu ta dũniya a hannunsu ba, to, ta yãya ne zã Mu bar babban abu kamar Annabci da shiryar da mutãne ga hannãyensu? Wãtau bã zai yiwu Mu yi ba sai yadda Muke so kawai, kõ su bi, kõ su kãfirta, duka daidai ne a gare Mu. -
وَلَوْلَآ أَن يَكُونَ ٱلنَّاسُ أُمَّةً وَٰحِدَةً لَّجَعَلْنَا لِمَن يَكْفُرُ بِٱلرَّحْمَـٰنِ لِبُيُوتِهِمْ سُقُفًا مِّن فِضَّةٍ وَمَعَارِجَ عَلَيْهَا يَظْهَرُونَ٣٣
Walawla an yakoona alnnasu ommatan wahidatan lajaʿalna liman yakfuru bialrrahmani libuyootihim suqufan min fiddatin wamaʿarija ʿalayha yathharoona
Kuma bã dõmin mutane su kasance al'umma ɗaya ba, lalle ne, dã Mun sanya wa mãsu kãfircẽ wa Mai Rahama, a gidãjensu, rufi na azurfa, kuma da matãkalai, ya zama a kanta suke tãƙãwa.
-
وَلِبُيُوتِهِمْ أَبْوَٰبًا وَسُرُرًا عَلَيْهَا يَتَّكِـُٔونَ٣٤
Walibuyootihim abwaban wasururan ʿalayha yattakioona
Kuma a gidãjensu, Mu sanya) ƙyamãre da gadãje, a kansu suke kishingiɗa.
-
وَزُخْرُفًا ۚ وَإِن كُلُّ ذَٰلِكَ لَمَّا مَتَـٰعُ ٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا ۚ وَٱلْـَٔاخِرَةُ عِندَ رَبِّكَ لِلْمُتَّقِينَ٣٥
Wazukhrufan wain kullu thalika lamma mataʿu alhayati alddunya waalakhiratu ʿinda rabbika lilmuttaqeena
Da zĩnãriya. Kuma dukan wancan abu bai zama ba, sai jin dãɗin rãyuwar dũniya nekawai' alhãli kuwa Lãhira, a wurin Ubangijinka, ta mãsu taƙawa ce.
-
وَمَن يَعْشُ عَن ذِكْرِ ٱلرَّحْمَـٰنِ نُقَيِّضْ لَهُۥ شَيْطَـٰنًا فَهُوَ لَهُۥ قَرِينٌ٣٦
Waman yaʿshu ʿan thikri alrrahmani nuqayyid lahu shaytanan fahuwa lahu qareenun
Kuma wanda ya makanta daga barin hukuncin Mai rahama, to, zã Mu lulluɓe shi da shaiɗan, watau shĩ ne abõkinsa.
-
وَإِنَّهُمْ لَيَصُدُّونَهُمْ عَنِ ٱلسَّبِيلِ وَيَحْسَبُونَ أَنَّهُم مُّهْتَدُونَ٣٧
Wainnahum layasuddoonahum ʿani alssabeeli wayahsaboona annahum muhtadoona
Kuma lalle su haƙĩƙa sunã kange su daga hanya, kuma sunã Zaton cẽwa sũ mãsu shiryuwa ne.
-
حَتَّىٰٓ إِذَا جَآءَنَا قَالَ يَـٰلَيْتَ بَيْنِى وَبَيْنَكَ بُعْدَ ٱلْمَشْرِقَيْنِ فَبِئْسَ ٱلْقَرِينُ٣٨
Hatta itha jaana qala ya layta baynee wabaynaka buʿda almashriqayni fabisa alqareenu
Har a lõkacin da (abõkin Shaiɗan) ya zo Mana (ya mutu) sai ya ce: (wa Shaiɗan) "Dã dai a tsakãnina da tsakãninka akwai nĩsan gabas da yamma, sabõda haka, tir da kai ga zama abõkin mutum!"
-
وَلَن يَنفَعَكُمُ ٱلْيَوْمَ إِذ ظَّلَمْتُمْ أَنَّكُمْ فِى ٱلْعَذَابِ مُشْتَرِكُونَ٣٩
Walan yanfaʿakumu alyawma ith thalamtum annakum fee alʿathabi mushtarikoona
Kuma (wannan magana) bã za ta amfãne ku ba, a yau, dõmin kun yi zãlunci, lalle ku mãsu tãrẽwa ne a cikin azãba.
-
أَفَأَنتَ تُسْمِعُ ٱلصُّمَّ أَوْ تَهْدِى ٱلْعُمْىَ وَمَن كَانَ فِى ضَلَـٰلٍ مُّبِينٍ٤٠
Afaanta tusmiʿu alssumma aw tahdee alʿumya waman kana fee dalalin mubeenin
Shin to, kai kanã jiyar da kurma ne, ko kanã shiryar da makãho da wanda ke a cikin ɓata bayyananna?
-
فَإِمَّا نَذْهَبَنَّ بِكَ فَإِنَّا مِنْهُم مُّنتَقِمُونَ٤١
Faimma nathhabanna bika fainna minhum muntaqimoona
To, kõ dai Mu tafi1da kai to, lalle Mũ, mãsu yin azãbarrãmu, wa ne a kansu.
Bayanai
[1] Mu tafi da kai, watau Mu karɓi ranka, ka mutu, to, dã Mun yi musu azãba ke nan, dõmin sun rasa mai shiryar da su. -
أَوْ نُرِيَنَّكَ ٱلَّذِى وَعَدْنَـٰهُمْ فَإِنَّا عَلَيْهِم مُّقْتَدِرُونَ٤٢
Aw nuriyannaka allathee waʿadnahum fainna ʿalayhim muqtadiroona
Kõ kuma Mu nũna maka abin da Muka yi musu wa'adi, to, lalle Mũ, Mãsu ĩkon tasarrufi a kansu ne.
-
فَٱسْتَمْسِكْ بِٱلَّذِىٓ أُوحِىَ إِلَيْكَ ۖ إِنَّكَ عَلَىٰ صِرَٰطٍ مُّسْتَقِيمٍ٤٣
Faistamsik biallathee oohiya ilayka innaka ʿala siratin mustaqeemin
Sabõda haka, ka yi riƙo ga abin da aka yi wahayi da shi zuwa gaie ka. Lalle ne kai, kanã a kan hanya madaidaiciya.
-
وَإِنَّهُۥ لَذِكْرٌ لَّكَ وَلِقَوْمِكَ ۖ وَسَوْفَ تُسْـَٔلُونَ٤٤
Wainnahu lathikrun laka waliqawmika wasawfa tusaloona
Kuma shi (abin wahayin) ambato (na ɗaukaka) ne a gare ka da kuma ga mutãnenka, kuma zã a tambaye ku.
-
وَسْـَٔلْ مَنْ أَرْسَلْنَا مِن قَبْلِكَ مِن رُّسُلِنَآ أَجَعَلْنَا مِن دُونِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ءَالِهَةً يُعْبَدُونَ٤٥
Waisal man arsalna min qablika min rusulina ajaʿalna min dooni alrrahmani alihatan yuʿbadoona
Kuma ka tambayi waɗanda Muka aika a gabãninka daga Manzannin Mu, "Shin, Mun sanya waɗansu gumãka, wasun (Allah), Mai rahama, anã bauta musu?"
-
وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا مُوسَىٰ بِـَٔايَـٰتِنَآ إِلَىٰ فِرْعَوْنَ وَمَلَإِي۟هِۦ فَقَالَ إِنِّى رَسُولُ رَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ٤٦
Walaqad arsalna moosa biayatina ila firʿawna wamalaihi faqala innee rasoolu rabbi alʿalameena
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika Mũsã, game da ãyõyin Mu, zuwa ga Fir'auna da mashãwartansa, sai ya ce: "Lalle nĩ, Manzo ne daga Ubangijin halittu."
-
فَلَمَّا جَآءَهُم بِـَٔايَـٰتِنَآ إِذَا هُم مِّنْهَا يَضْحَكُونَ٤٧
Falamma jaahum biayatina itha hum minha yadhakoona
To, a lõkacin da ya jẽ musu da ãyõyin Mu, sai gã su sunã yi musu dãriya.
-
وَمَا نُرِيهِم مِّنْ ءَايَةٍ إِلَّا هِىَ أَكْبَرُ مِنْ أُخْتِهَا ۖ وَأَخَذْنَـٰهُم بِٱلْعَذَابِ لَعَلَّهُمْ يَرْجِعُونَ٤٨
Wama nureehim min ayatin illa hiya akbaru min okhtiha waakhathnahum bialʿathabi laʿallahum yarjiʿoona
Kuma ba Mu nũna musu wata ãyã ba, fãce ita ce mafi girma daga 'yar'uwarta. Kuma Muka kãma su da azãba, tsammãninsu kõ sunã kõmõwa.
-
وَقَالُوا۟ يَـٰٓأَيُّهَ ٱلسَّاحِرُ ٱدْعُ لَنَا رَبَّكَ بِمَا عَهِدَ عِندَكَ إِنَّنَا لَمُهْتَدُونَ٤٩
Waqaloo ya ayyuha alsahiru odʿu lana rabbaka bima ʿahida ʿindaka innana lamuhtadoona
Kuma suka ce: "Yã kai mai sihiri! Ka rõƙa mana Ubangijinka da albarkacin abin da yi alkawari a wurinka, lalle mũ, haƙĩƙa, mãsu shiryuwa ne."
-
فَلَمَّا كَشَفْنَا عَنْهُمُ ٱلْعَذَابَ إِذَا هُمْ يَنكُثُونَ٥٠
Falamma kashafna ʿanhumu alʿathaba itha hum yankuthoona
To, a lõkacin da duk Muka kuranye musu azãba, sai gã su sunã warware alkawarinsu.
-
وَنَادَىٰ فِرْعَوْنُ فِى قَوْمِهِۦ قَالَ يَـٰقَوْمِ أَلَيْسَ لِى مُلْكُ مِصْرَ وَهَـٰذِهِ ٱلْأَنْهَـٰرُ تَجْرِى مِن تَحْتِىٓ ۖ أَفَلَا تُبْصِرُونَ٥١
Wanada firʿawnu fee qawmihi qala ya qawmi alaysa lee mulku misra wahathihi alanharu tajree min tahtee afala tubsiroona
Kuma Fir'auna ya yi kira a cikin mutãnensa, ya ce: "Ya mutãnẽna! Ashe mulkin Masar bã a gare ni yake ba, kuma waɗannan kõguna sunã gudãna daga ƙarƙashĩna? Ashe, ba ku gani ba?"
-
أَمْ أَنَا۠ خَيْرٌ مِّنْ هَـٰذَا ٱلَّذِى هُوَ مَهِينٌ وَلَا يَكَادُ يُبِينُ٥٢
Am ana khayrun min hatha allathee huwa maheenun wala yakadu yubeenu
"Kõ kuma bã nĩ ne mafĩfĩci ba daga wannan wanda yake shĩ wulakantacce ne kuma bã ya iya bayyanawar magana sai da ƙyar?
-
فَلَوْلَآ أُلْقِىَ عَلَيْهِ أَسْوِرَةٌ مِّن ذَهَبٍ أَوْ جَآءَ مَعَهُ ٱلْمَلَـٰٓئِكَةُ مُقْتَرِنِينَ٥٣
Falawla olqiya ʿalayhi aswiratun min thahabin aw jaa maʿahu almalaikatu muqtarineena
"To, don me, ba a jẽfa mundãye na zĩnãriya a kansaba, kõ kuma malã'iku su taho tãre da shi haɗe?"
-
فَٱسْتَخَفَّ قَوْمَهُۥ فَأَطَاعُوهُ ۚ إِنَّهُمْ كَانُوا۟ قَوْمًا فَـٰسِقِينَ٥٤
Faistakhaffa qawmahu faataʿoohu innahum kanoo qawman fasiqeena
Sai ya sassabce hankalin mutãnensa, sabõda haka suka bĩ shi. Lalle sũ, sun kasance waɗansu irin mutãne ne fãsiƙai.
-
فَلَمَّآ ءَاسَفُونَا ٱنتَقَمْنَا مِنْهُمْ فَأَغْرَقْنَـٰهُمْ أَجْمَعِينَ٥٥
Falamma asafoona intaqamna minhum faaghraqnahum ajmaʿeena
Sabõda haka a lõkacin da suka husãtar da Mu, Muka yi musu azãbar rãmuwa sai Muka nutsar da su gabã ɗaya.
-
فَجَعَلْنَـٰهُمْ سَلَفًا وَمَثَلًا لِّلْـَٔاخِرِينَ٥٦
Fajaʿalnahum salafan wamathalan lilakhireena
Sai Muka sanya su magabãta kuma abin misãli ga mutãnen ƙarshe.
-
۞ وَلَمَّا ضُرِبَ ٱبْنُ مَرْيَمَ مَثَلًا إِذَا قَوْمُكَ مِنْهُ يَصِدُّونَ٥٧
Walamma duriba ibnu maryama mathalan itha qawmuka minhu yasiddoona
Kuma a lõkacin da aka buga misãli da ¦an Maryama, sai gã mutãnenka daga gare shi (shi misalin) sunã dãriya da izgili.
-
وَقَالُوٓا۟ ءَأَـٰلِهَتُنَا خَيْرٌ أَمْ هُوَ ۚ مَا ضَرَبُوهُ لَكَ إِلَّا جَدَلًۢا ۚ بَلْ هُمْ قَوْمٌ خَصِمُونَ٥٨
Waqaloo aalihatuna khayrun am huwa ma daraboohu laka illa jadalan bal hum qawmun khasimoona
Kuma suka ce: "Shin, gumãkanmu ne mafĩfĩta kõ shi (¦an Maryama)?" Ba su buga wannan misãli ba a gare ka fãce dõmin yin jidãli.1 Ã'a, sũ mutãne nemãsu husũma.
Bayanai
[1] Wãtau da aka ce gumãka damãsu bauta musu duka abincin wutar Jahannama ne kamar yadda yake a cikin sura ta 21 ãyã ta 98 da 99, sai suka ce sun yarda gumakansu su zama tãre da ɗan Maryama. -
إِنْ هُوَ إِلَّا عَبْدٌ أَنْعَمْنَا عَلَيْهِ وَجَعَلْنَـٰهُ مَثَلًا لِّبَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ٥٩
In huwa illa ʿabdun anʿamna ʿalayhi wajaʿalnahu mathalan libanee israeela
Shi (¦an Maryama) bai zama ba fãce wani bãwa ne, Mun yi ni'ima a gare shi, kuma Muka sanya shi abin kõyi ga Banĩ Isrã'ĩla.
-
وَلَوْ نَشَآءُ لَجَعَلْنَا مِنكُم مَّلَـٰٓئِكَةً فِى ٱلْأَرْضِ يَخْلُفُونَ٦٠
Walaw nashao lajaʿalna minkum malaikatan fee alardi yakhlufoona
Kuma dã Munã so lalle ne dã Mun sanya malã'iku, daga ci, kinku, a cikin ƙasa, sunã mayẽwa1
Bayanai
[1] Dã Mun so dã Mun sanya ɗiyansu su zama malã'iku, su fi Ĩsa ɗan Maryama zama abin mãmãki ga halitta, sa'an nan su maye muku a cikin ƙasã maimakon ɗiya masu siffõfi irin na jikunkunanku. Zai fi zama abin mãmãki mutum yahaifi malã'ika bisa mace ta haifi ɗã bã da wani namiji yã kusance ta ba. -
وَإِنَّهُۥ لَعِلْمٌ لِّلسَّاعَةِ فَلَا تَمْتَرُنَّ بِهَا وَٱتَّبِعُونِ ۚ هَـٰذَا صِرَٰطٌ مُّسْتَقِيمٌ٦١
Wainnahu laʿilmun lilssaʿati fala tamtarunna biha waittabiʿooni hatha siratun mustaqeemun
Kuma lalle shĩ, haƙĩƙa, wani ilmi ne na Sa'a, sabõda haka, kada ku yi shakka a gare ta, kuma ku bĩ Ni. Wannan ita ce hanya madaidaiciya.
-
وَلَا يَصُدَّنَّكُمُ ٱلشَّيْطَـٰنُ ۖ إِنَّهُۥ لَكُمْ عَدُوٌّ مُّبِينٌ٦٢
Wala yasuddannakumu alshshaytanu innahu lakum ʿaduwwun mubeenun
Kuma kada Shaiɗan ya taushe ku (daga hanyar). Lalle shĩ maƙiyi ne a gare ku, mai bayyanãwar ƙiyayya.
-
وَلَمَّا جَآءَ عِيسَىٰ بِٱلْبَيِّنَـٰتِ قَالَ قَدْ جِئْتُكُم بِٱلْحِكْمَةِ وَلِأُبَيِّنَ لَكُم بَعْضَ ٱلَّذِى تَخْتَلِفُونَ فِيهِ ۖ فَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ٦٣
Walamma jaa ʿeesa bialbayyinati qala qad jitukum bialhikmati waliobayyina lakum baʿda allathee takhtalifoona feehi faittaqoo Allaha waateeʿooni
Kuma a lõkacin da Ĩsã ya jẽ da hujjõji bayyanannu, ya ce: "Lalle ne nã zo muku da hikima kuma dõmin in bayyana muku, sãshen abin da kuke sãɓã wa jũna acikinsa, sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'a."
-
إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ رَبِّى وَرَبُّكُمْ فَٱعْبُدُوهُ ۚ هَـٰذَا صِرَٰطٌ مُّسْتَقِيمٌ٦٤
Inna Allaha huwa rabbee warabbukum faoʿbudoohu hatha siratun mustaqeemun
"Lalle ne, Allah Shĩ ne Ubangijina kuma Shi ne Ubangijinku sabõda haka ku bauta Masa. Wannan ita ce hanya madaidaiciya."
-
فَٱخْتَلَفَ ٱلْأَحْزَابُ مِنۢ بَيْنِهِمْ ۖ فَوَيْلٌ لِّلَّذِينَ ظَلَمُوا۟ مِنْ عَذَابِ يَوْمٍ أَلِيمٍ٦٥
Faikhtalafa alahzabu min baynihim fawaylun lillatheena thalamoo min ʿathabi yawmin aleemin
Sai ƙungiyõyi1suka sãɓa a tsakãninsu. To, bone yã tabbata ga waɗanda suka yi zãlunci daga azãbar yini mai raɗaɗi!
Bayanai
[1] Nasãra suka kasu a cikin ƙungiyõyi a bayan Ĩsã. Ya'akubiyya, mãsu cewa Ĩsã ɗan Allah ne, da Malakãniyya, mãsu cewa Ĩsa ɗayan uku ne. Waɗansu kuma suka ce bãwan Allah ne watau su ne Musulminsu, kuma waɗansu daga Musulmin suka kãfirta a bãyan zakuwar, Muhammadu tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi, sabõda sun ƙi yarda da Annabcinsa. Yahũdu suka ce: "Ĩsã bã Annabi ba ne dan zina ne." Allah Ya la'ani kãfirai dukansu. -
هَلْ يَنظُرُونَ إِلَّا ٱلسَّاعَةَ أَن تَأْتِيَهُم بَغْتَةً وَهُمْ لَا يَشْعُرُونَ٦٦
Hal yanthuroona illa alssaʿata an tatiyahum baghtatan wahum la yashʿuroona
Shin sunã jiran wani abu ne? sai dai Sa'a ta jẽ musu bisaga abke, alhãli kuwa ba su sani ba.
-
ٱلْأَخِلَّآءُ يَوْمَئِذٍۭ بَعْضُهُمْ لِبَعْضٍ عَدُوٌّ إِلَّا ٱلْمُتَّقِينَ٦٧
Alakhillao yawmaithin baʿduhum libaʿdin ʿaduwwun illa almuttaqeena
Masõya a yinin nan, sãshensu zuwa ga sãshe maƙiya ne, fãce mãsu taƙawa (sũ kam mãsu son jũna ne).
-
يَـٰعِبَادِ لَا خَوْفٌ عَلَيْكُمُ ٱلْيَوْمَ وَلَآ أَنتُمْ تَحْزَنُونَ٦٨
Ya ʿibadi la khawfun ʿalaykumu alyawma wala antum tahzanoona
Ya bãyĩNa! Bãbu tsõro a kanku a yau, kuma bã zã ku yi baƙin ciki ba.
-
ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ بِـَٔايَـٰتِنَا وَكَانُوا۟ مُسْلِمِينَ٦٩
Allatheena amanoo biayatina wakanoo muslimeena
Waɗanda suka yi ĩmãni da ãyõyin Mu, kuma suka kasance mãsu sallamawar al'amari (ga Allah).
-
ٱدْخُلُوا۟ ٱلْجَنَّةَ أَنتُمْ وَأَزْوَٰجُكُمْ تُحْبَرُونَ٧٠
Odkhuloo aljannata antum waazwajukum tuhbaroona
Ku shiga Aljanna, kũ da mãtan aurenku, anã girmama ku.
-
يُطَافُ عَلَيْهِم بِصِحَافٍ مِّن ذَهَبٍ وَأَكْوَابٍ ۖ وَفِيهَا مَا تَشْتَهِيهِ ٱلْأَنفُسُ وَتَلَذُّ ٱلْأَعْيُنُ ۖ وَأَنتُمْ فِيهَا خَـٰلِدُونَ٧١
Yutafu ʿalayhim bisihafin min thahabin waakwabin wafeeha ma tashtaheehi alanfusu watalaththu alaʿyunu waantum feeha khalidoona
Anã kẽwayãwa a kansu da akussa na zĩnãriya da kõfuna, alhãli kuwa a cikinsu akwai abin da rãyuka ke marmari kuma idãnu su ji dãɗi, kuma kũ, a cikinta (Aljannar), madawwama ne.
-
وَتِلْكَ ٱلْجَنَّةُ ٱلَّتِىٓ أُورِثْتُمُوهَا بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ٧٢
Watilka aljannatu allatee oorithtumooha bima kuntum taʿmaloona
Kuma waccan ita ce Aljannar, wannan da aka gãdar da ku ita sabõda abin da kuka kasance kunã aikatãwa.
-
لَكُمْ فِيهَا فَـٰكِهَةٌ كَثِيرَةٌ مِّنْهَا تَأْكُلُونَ٧٣
Lakum feeha fakihatun katheeratun minha takuloona
Kunã sãmu, a cikinta, 'yã'yan itãcen marmari mãsu yawa, daga cikinsu kuke ci.
-
إِنَّ ٱلْمُجْرِمِينَ فِى عَذَابِ جَهَنَّمَ خَـٰلِدُونَ٧٤
Inna almujrimeena fee ʿathabi jahannama khalidoona
Lalle mãsu laifi madawwama ne a cikin azãbar Jahannama.
-
لَا يُفَتَّرُ عَنْهُمْ وَهُمْ فِيهِ مُبْلِسُونَ٧٥
La yufattaru ʿanhum wahum feehi mublisoona
Bã a sauƙaƙar da ita (azãbar) daga gare su, alhãli kuwa sũ, a cikinta, mãsu kãsa magana ne.
-
وَمَا ظَلَمْنَـٰهُمْ وَلَـٰكِن كَانُوا۟ هُمُ ٱلظَّـٰلِمِينَ٧٦
Wama thalamnahum walakin kanoo humu alththalimeena
Kuma ba Mu zãlunce su ba, amma sũ ne suka kasance azzãlumai.
-
وَنَادَوْا۟ يَـٰمَـٰلِكُ لِيَقْضِ عَلَيْنَا رَبُّكَ ۖ قَالَ إِنَّكُم مَّـٰكِثُونَ٧٧
Wanadaw ya maliku liyaqdi ʿalayna rabbuka qala innakum makithoona
Kuma suka yi kira, "Ya Mãliku! Ubangijinka Ya kashe mu mana1 " (Mãliku) ya ce: "Lalle kũ mazauna ne."
Bayanai
[1] Watau sunã neman su mutu su huta da ɗaukar aZãba. -
لَقَدْ جِئْنَـٰكُم بِٱلْحَقِّ وَلَـٰكِنَّ أَكْثَرَكُمْ لِلْحَقِّ كَـٰرِهُونَ٧٨
Laqad jinakum bialhaqqi walakinna aktharakum lilhaqqi karihoona
Lalle ne, haƙĩƙa, Mun jẽ muku da gaskiya, kuma amma mafi yawanku mãsu ƙi ga gaskiyar ne.
-
أَمْ أَبْرَمُوٓا۟ أَمْرًا فَإِنَّا مُبْرِمُونَ٧٩
Am abramoo amran fainna mubrimoona
Kõ kuma sun tukka wani al'amari ne? To, lalle Mũ, Mãsu tukkãwa ne.
-
أَمْ يَحْسَبُونَ أَنَّا لَا نَسْمَعُ سِرَّهُمْ وَنَجْوَىٰهُم ۚ بَلَىٰ وَرُسُلُنَا لَدَيْهِمْ يَكْتُبُونَ٨٠
Am yahsaboona anna la nasmaʿu sirrahum wanajwahum bala warusuluna ladayhim yaktuboona
Ko sunã zaton lalle Mũ, bã Mu jin asĩrinsu da gãnãwarsu? Na'am! Kuma manzannin Mu na tãre da su sunã rubũtãwa.
-
قُلْ إِن كَانَ لِلرَّحْمَـٰنِ وَلَدٌ فَأَنَا۠ أَوَّلُ ٱلْعَـٰبِدِينَ٨١
Qul in kana lilrrahmani waladun faana awwalu alʿabideena
Ka ce: "Idan har akwai ɗã ga Mai rahama, to, nĩ ne farkon mãsu bauta (wa ɗan)."
-
سُبْحَـٰنَ رَبِّ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ رَبِّ ٱلْعَرْشِ عَمَّا يَصِفُونَ٨٢
Subhana rabbi alssamawati waalardi rabbi alʿarshi ʿamma yasifoona
Tsarkin Ubangijin sammai da ƙasa, Ubangijin Al'arshi, ya tabbata daga abin da suke sifantãwa.
-
فَذَرْهُمْ يَخُوضُوا۟ وَيَلْعَبُوا۟ حَتَّىٰ يُلَـٰقُوا۟ يَوْمَهُمُ ٱلَّذِى يُوعَدُونَ٨٣
Fatharhum yakhoodoo wayalʿaboo hatta yulaqoo yawmahumu allathee yooʿadoona
Sabõda haka, ka ƙyãlẽ su, su kũtsa kuma su yi wãsã har su haɗu da yininsu, wanda ake yi musu wa'adi da shi.
-
وَهُوَ ٱلَّذِى فِى ٱلسَّمَآءِ إِلَـٰهٌ وَفِى ٱلْأَرْضِ إِلَـٰهٌ ۚ وَهُوَ ٱلْحَكِيمُ ٱلْعَلِيمُ٨٤
Wahuwa allathee fee alssamai ilahun wafee alardi ilahun wahuwa alhakeemu alʿaleemu
Kuma Shĩ ne wanda ke abin bautãwa a sama kuma abin bautãwa a ƙasa, kuma, Shĩ ne Mai hikima, Masani.
-
وَتَبَارَكَ ٱلَّذِى لَهُۥ مُلْكُ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا وَعِندَهُۥ عِلْمُ ٱلسَّاعَةِ وَإِلَيْهِ تُرْجَعُونَ٨٥
Watabaraka allathee lahu mulku alssamawati waalardi wama baynahuma waʿindahu ʿilmu alssaʿati wailayhi turjaʿoona
Kuma albarkar wanda ke da mulkin sammai da ƙasã abin da ke a tsakãninsu tã bayyana, kuma a wurin Sa ne ilmin Sa'a yake, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku.
-
وَلَا يَمْلِكُ ٱلَّذِينَ يَدْعُونَ مِن دُونِهِ ٱلشَّفَـٰعَةَ إِلَّا مَن شَهِدَ بِٱلْحَقِّ وَهُمْ يَعْلَمُونَ٨٦
Wala yamliku allatheena yadʿoona min doonihi alshshafaʿata illa man shahida bialhaqqi wahum yaʿlamoona
Kuma waɗanda suke kira baicin Sa ba su mallaki cẽto ba, fãce wanda ya yi shaida da gaskiya, kuma sũ, sunã sane1 (da haka).
Bayanai
[1] Su waɗanda suka yi shaida da gaskiya sun san bãbu mai mallakar ceto ga wani fãce Allah. Sabõda haka Allah nã yi musu izni su ceci wanda Yake son su cece shi, ba wanda su suke so ba. Ma'anar iznin da ceto ga bãyin Allah sãlihai ita ce dõmin Allah Ya bayyana darajar mai ceton ne kawai, bã don yanã da wani hakki ba, ga Allah. Allah Ya tsarkaka daga wata halittar Sa ta sãmi wani hakki a kan Sa. Kõwa bãwan Sa ne. -
وَلَئِن سَأَلْتَهُم مَّنْ خَلَقَهُمْ لَيَقُولُنَّ ٱللَّهُ ۖ فَأَنَّىٰ يُؤْفَكُونَ٨٧
Walain saaltahum man khalaqahum layaqoolunna Allahu faanna yufakoona
Kuma lalle idan ka tambaye su: "Wãne ne ya halitta su?" Lalle ne zã su ce Allah ne. To, yãya ake jũyar da su?
-
وَقِيلِهِۦ يَـٰرَبِّ إِنَّ هَـٰٓؤُلَآءِ قَوْمٌ لَّا يُؤْمِنُونَ٨٨
Waqeelihi yarabbi inna haolai qawmun la yuminoona
Kuma da (ilmin) maganar Sa (Annabi) "Ya Ubangijĩna! Lalle waɗannan mutãne ne waɗanda bã zã su yi ĩmãni ba."
-
فَٱصْفَحْ عَنْهُمْ وَقُلْ سَلَـٰمٌ ۚ فَسَوْفَ يَعْلَمُونَ٨٩
Faisfah ʿanhum waqul salamun fasawfa yaʿlamoona
To, sai ka kau da kai daga gare su, kuma ka ce, "salãmã." Sa'an nan kuma zã su sani.
Tambayoyin da ake yawan yi
Mece ce ma’anar sunan Suratul Zukhruf?
Ma’anar Zukhruf ita ce “Kayan adon zinariya”.
Suratul Zukhruf tana cikin juz’i na nawa?
Suratul Zukhruf tana cikin juz’i na 25.
Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Zukhruf?
Suratul Zukhruf tana da ayoyi 89.
Suratul Zukhruf Makkiya ce ko Madaniya?
Suratul Zukhruf sura ce Makkiya.
Suratul Zukhruf ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?
Ita ce sura ta 43 a cikin Alƙur’ani.
Majiyoyi
- Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
- Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
- Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
- Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
- Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
- Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.
Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.