Suratul Hujurat (الحجرات) ita ce sura ta 49 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 18. Ma’anar sunanta ita ce “Ɗakuna”. Sura ce Madaniya, wadda ta sauka a Madina bayan Hijira, kuma tana cikin juz’i na 26.
A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Hujurat gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.
Suratul Hujurat cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ
-
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ لَا تُقَدِّمُوا۟ بَيْنَ يَدَىِ ٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ ۖ وَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَمِيعٌ عَلِيمٌ١
Ya ayyuha allatheena amanoo la tuqaddimoo bayna yadayi Allahi warasoolihi waittaqoo Allaha inna Allaha sameeʿun ʿaleemun
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku gabãta (da kõme) gaba ga Allah da Manzon Sa.1 Kuma ku yi ɗã'ã ga Allah da taƙawa. Lalle Allah Mai ji ne, Masani.
Bayanai
[1] Wannan yã nũna mana cewa bã yã halatta ga Musulmi ya yi wani aiki ko ya faɗi wata magana sai yã san hukuncin Allah a cikinsu. Kuma kada ya ƙãra wãyõnsa a kan abinda Allah Yã ce, kuma kada ya rage idan yanã da ĩkon cikãwa. Dukan wannan yakan ja Musulmi ga ɓãcin ayyukansa, watau ya yi ridda daga Musulunci. -
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ لَا تَرْفَعُوٓا۟ أَصْوَٰتَكُمْ فَوْقَ صَوْتِ ٱلنَّبِىِّ وَلَا تَجْهَرُوا۟ لَهُۥ بِٱلْقَوْلِ كَجَهْرِ بَعْضِكُمْ لِبَعْضٍ أَن تَحْبَطَ أَعْمَـٰلُكُمْ وَأَنتُمْ لَا تَشْعُرُونَ٢
Ya ayyuha allatheena amanoo la tarfaʿoo aswatakum fawqa sawti alnnabiyyi wala tajharoo lahu bialqawli kajahri baʿdikum libaʿdin an tahbata aʿmalukum waantum la tashʿuroona
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Kada ku ɗaukaka saututtukanku1 bisa sautin Annabi, kuma kada ku bayyana sauti gare shi a magana, kamar bayyanãwar sãshenku ga sãshe, dõmin kada ayyukanku su ɓãci, alhãli kuwa kũ ba ku sani ba.
Bayanai
[1] Ladubban zama da shugaba.Annabi shi ne kan shugabanni, sai dai ɗã'a gare shi wãjibi ne ga kõme, sauran shũgabanni kuwa ga abin da bai sãɓawa shari'a ba. -
إِنَّ ٱلَّذِينَ يَغُضُّونَ أَصْوَٰتَهُمْ عِندَ رَسُولِ ٱللَّهِ أُو۟لَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ ٱمْتَحَنَ ٱللَّهُ قُلُوبَهُمْ لِلتَّقْوَىٰ ۚ لَهُم مَّغْفِرَةٌ وَأَجْرٌ عَظِيمٌ٣
Inna allatheena yaghuddoona aswatahum ʿinda rasooli Allahi olaika allatheena imtahana Allahu quloobahum lilttaqwa lahum maghfiratun waajrun ʿatheemun
Lalle waɗanda ke runtsẽwar saututtukansu a wurin Manzon Allah waɗannan ne waɗanda Allah Yã, jarrabi zukãtansu ga taƙawa. Sunã da wata irin gãfara da ijãra mai girma.
-
إِنَّ ٱلَّذِينَ يُنَادُونَكَ مِن وَرَآءِ ٱلْحُجُرَٰتِ أَكْثَرُهُمْ لَا يَعْقِلُونَ٤
Inna allatheena yunadoonaka min warai alhujurati aktharuhum la yaʿqiloona
Lalle waɗanda ke kiranka daga bãyan ɗakuna, mafi Yawansu bã su aiki da hankali.
-
وَلَوْ أَنَّهُمْ صَبَرُوا۟ حَتَّىٰ تَخْرُجَ إِلَيْهِمْ لَكَانَ خَيْرًا لَّهُمْ ۚ وَٱللَّهُ غَفُورٌ رَّحِيمٌ٥
Walaw annahum sabaroo hatta takhruja ilayhim lakana khayran lahum waAllahu ghafoorun raheemun
Kuma dã lalle sũ, sun yi haƙuri har ka fita zuwa gare su, haƙĩƙa, dã yã kasance mafi alhẽri gare su, kuma Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
-
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓا۟ إِن جَآءَكُمْ فَاسِقٌۢ بِنَبَإٍ فَتَبَيَّنُوٓا۟ أَن تُصِيبُوا۟ قَوْمًۢا بِجَهَـٰلَةٍ فَتُصْبِحُوا۟ عَلَىٰ مَا فَعَلْتُمْ نَـٰدِمِينَ٦
Ya ayyuha allatheena amanoo in jaakum fasiqun binabain fatabayyanoo an tuseeboo qawman bijahalatin fatusbihoo ʿala ma faʿaltum nadimeena
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan fãsiƙi1 Yã zo muku da wani babban lãbãri, to, ku nẽmi bayãni, dõmin kada ku cũci waɗansu mutãne a cikin jãhilci, sabõda haka ku wãyi gari a kan abin da kuka aikata kunã mãsu nadãma.
Bayanai
[1] Idan wani yã kai lãbãrin ɓarna, kada a yi aiki da shi sai bãyan an bincika an san gaskiyar al'amarin, kãfin a yi aiki da shi. fãsiƙi ga asalin kalma shi ne duka wanda ya karkace daga hanyar ƙwarai wadda aka sani. A nan, fãsiƙi, shi ne mai kai lãbãrin da yake akwai tãshin hankali a cikinsa, ko kuma abin tsõro dõmin ya sanya rũɗu a tsakãnin jama'a tun ba a san haƙĩƙanin al'amarin ba. -
وَٱعْلَمُوٓا۟ أَنَّ فِيكُمْ رَسُولَ ٱللَّهِ ۚ لَوْ يُطِيعُكُمْ فِى كَثِيرٍ مِّنَ ٱلْأَمْرِ لَعَنِتُّمْ وَلَـٰكِنَّ ٱللَّهَ حَبَّبَ إِلَيْكُمُ ٱلْإِيمَـٰنَ وَزَيَّنَهُۥ فِى قُلُوبِكُمْ وَكَرَّهَ إِلَيْكُمُ ٱلْكُفْرَ وَٱلْفُسُوقَ وَٱلْعِصْيَانَ ۚ أُو۟لَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلرَّٰشِدُونَ٧
Waiʿlamoo anna feekum rasoola Allahi law yuteeʿukum fee katheerin mina alamri laʿanittum walakinna Allaha habbaba ilaykumu aleemana wazayyanahu fee quloobikum wakarraha ilaykumu alkufra waalfusooqa waalʿisyana olaika humu alrrashidoona
Kuma ku sani (cẽwa) lalle ne, a cikinku akwai Manzon Allah. Dã Yana bin ku ga (hãlãye) mãsu Yawa na al'amarin, dã kun auku a cikin zunubi, kuma amma Allah Yã sõyar da ĩmãni a gare ku, kuma Yã ƙawãta shi a cikin zukãtanku kuma Yã ƙyãmantar da kãfirci da fãsicci da sãɓo zuwa gare ku. Waɗannan (da suka lazimci sifõfin nan) su ne shiryayyu.
-
فَضْلًا مِّنَ ٱللَّهِ وَنِعْمَةً ۚ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ٨
Fadlan mina Allahi waniʿmatan waAllahu ʿaleemun hakeemun
Bisa ga falala daga Allah da ni'ima. Kuma Allah Masani ne, Mai hikima.
-
وَإِن طَآئِفَتَانِ مِنَ ٱلْمُؤْمِنِينَ ٱقْتَتَلُوا۟ فَأَصْلِحُوا۟ بَيْنَهُمَا ۖ فَإِنۢ بَغَتْ إِحْدَىٰهُمَا عَلَى ٱلْأُخْرَىٰ فَقَـٰتِلُوا۟ ٱلَّتِى تَبْغِى حَتَّىٰ تَفِىٓءَ إِلَىٰٓ أَمْرِ ٱللَّهِ ۚ فَإِن فَآءَتْ فَأَصْلِحُوا۟ بَيْنَهُمَا بِٱلْعَدْلِ وَأَقْسِطُوٓا۟ ۖ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلْمُقْسِطِينَ٩
Wain taifatani mina almumineena iqtataloo faaslihoo baynahuma fain baghat ihdahuma ʿala alokhra faqatiloo allatee tabghee hatta tafeea ila amri Allahi fain faat faaslihoo baynahuma bialʿadli waaqsitoo inna Allaha yuhibbu almuqsiteena
Kuma idan jama'a biyu ta mũminai suka yi yãki, to, kuyi sulhu, a tsakãninsu. Sai idan ɗayansu ta yi zãlunci a kan gudar, to, sai ku yãƙi wadda ke yin zãlunci har ta kõma, zuwa ga umurnin Allah. To, idan ta kõma, sai ku yi sulhu a tsakãninsu da ãdalci kuma ku daidaita.1 Lalle Allah na son mãsu daidaitãwa.
Bayanai
[1] Wannan tsãri na sulhu a tsãkanin al'umma biyu mãsu faɗa, shĩ ne hanya mafi kyau wadda har yanzu wayon dũniya bai kai ga yin aiki da shi ba. Dã yanzu an zauna lãfiya, dã Majalisar Ɗinkin Dũniya na iya aiki da shi. haka Yake kuma ga sauran hukunce-hukuncen mutãnen dũniya. Shari'ar Musulunci sabõda ãdalcin da ke cikinta kuma wayon dũniya bai kai ta ga anã iya zartar da shi ba, shĩ ne ya sa ƙasãshen Musulunci ke kaucewa gare ta, dõmin son ran shugabanninsu. Allah Yã mayar da mu ga addininmu! Dukan Musulmin da ya kaucewa sharĩ'ar Musulunci, to, ya kauce ne dõmin ya sami damar yin zãlunci, kuma idan yã halatta kaucewar, yã zama bã Musulmi ba. -
إِنَّمَا ٱلْمُؤْمِنُونَ إِخْوَةٌ فَأَصْلِحُوا۟ بَيْنَ أَخَوَيْكُمْ ۚ وَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ لَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ١٠
Innama almuminoona ikhwatun faaslihoo bayna akhawaykum waittaqoo Allaha laʿallakum turhamoona
Mũminai 'yan'uwan jũna kawai ne, sabõda haka ku yi sulhu a tsakãnin 'yan'uwanku biyu, kuma ku bi Allah da taƙawa tsammãninku, a yi muku rahama.
-
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ لَا يَسْخَرْ قَوْمٌ مِّن قَوْمٍ عَسَىٰٓ أَن يَكُونُوا۟ خَيْرًا مِّنْهُمْ وَلَا نِسَآءٌ مِّن نِّسَآءٍ عَسَىٰٓ أَن يَكُنَّ خَيْرًا مِّنْهُنَّ ۖ وَلَا تَلْمِزُوٓا۟ أَنفُسَكُمْ وَلَا تَنَابَزُوا۟ بِٱلْأَلْقَـٰبِ ۖ بِئْسَ ٱلِٱسْمُ ٱلْفُسُوقُ بَعْدَ ٱلْإِيمَـٰنِ ۚ وَمَن لَّمْ يَتُبْ فَأُو۟لَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلظَّـٰلِمُونَ١١
Ya ayyuha allatheena amanoo la yaskhar qawmun min qawmin ʿasa an yakoonoo khayran minhum wala nisaon min nisain ʿasa an yakunna khayran minhunna wala talmizoo anfusakum wala tanabazoo bialalqabi bisa alismu alfusooqu baʿda aleemani waman lam yatub faolaika humu alththalimoona
"Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada waɗansu mutãne su yi izgili game da waɗansu mutãne, mai yiwuwa ne (abin yi wa izgilin) su kasance mafifita daga gare su (mãsu izgilin), kuma waɗansu mãtã kada su yi izgili game da waɗansu mãtã mai yiwuwa ne su kasancc mafĩfĩta daga gare su. Kuma kada ku aibanta kanku, kuma kada ku jẽfi jũna da miyãgun sunãye na laƙabõbĩ. Tir da sũna na fãsicci a bãyãn ĩmãni. Kuma wanda bai tũba ba, to, waɗannan sũ ne azzãlumai."
-
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ ٱجْتَنِبُوا۟ كَثِيرًا مِّنَ ٱلظَّنِّ إِنَّ بَعْضَ ٱلظَّنِّ إِثْمٌ ۖ وَلَا تَجَسَّسُوا۟ وَلَا يَغْتَب بَّعْضُكُم بَعْضًا ۚ أَيُحِبُّ أَحَدُكُمْ أَن يَأْكُلَ لَحْمَ أَخِيهِ مَيْتًا فَكَرِهْتُمُوهُ ۚ وَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ تَوَّابٌ رَّحِيمٌ١٢
Ya ayyuha allatheena amanoo ijtaniboo katheeran mina alththanni inna baʿda alththanni ithmun wala tajassasoo wala yaghtab baʿdukum baʿdan ayuhibbu ahadukum an yakula lahma akheehi maytan fakarihtumoohu waittaqoo Allaha inna Allaha tawwabun raheemun
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku nĩsanci abu mai yãwa na zato. Lalle sãshen zato laifi ne. Kuma kada ku yi rahõto, kuma kada sãshenku yã yi gulmar sãshe. Shin, ɗayanku nã son yã ci naman ɗan'uwansa yanã matacce? To, kun ƙĩ shi (cin nãman). Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle Allah Mai karɓar tũba ne, Mai jin ƙai.
-
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِنَّا خَلَقْنَـٰكُم مِّن ذَكَرٍ وَأُنثَىٰ وَجَعَلْنَـٰكُمْ شُعُوبًا وَقَبَآئِلَ لِتَعَارَفُوٓا۟ ۚ إِنَّ أَكْرَمَكُمْ عِندَ ٱللَّهِ أَتْقَىٰكُمْ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمٌ خَبِيرٌ١٣
Ya ayyuha alnnasu inna khalaqnakum min thakarin waontha wajaʿalnakum shuʿooban waqabaila litaʿarafoo inna akramakum ʿinda Allahi atqakum inna Allaha ʿaleemun khabeerun
Yã kũ mutãne!1 Lalle ne Mũ, Mun halitta ku daga namiji da mace, kuma Muka sanya ku dangõgi da kabĩlõli, dõmin ku san jũna. Lalle mafĩfĩcinku daraja a wurin Allah, (shĩ ne) wanda yake mafĩfĩcinku a taƙawa. Lalle nẽ Allah Masani ne, Mai ƙididdigẽwa.
Bayanai
[1] Yã kirãyi mãsu ĩmãni a cikin wannan sũra sau biyar ga abin da ya keɓanta da su na umurni da hani kamar yadda Lukmãn ya kirãyi ɗansa wajen yi masa wasiyyõyi. Kuma ya kirãyi mutãne a wannan ãyã ga abin da ya haɗa mũminai da kãfirai wajen halitta, watau alfahari da dangantaka. Dangantaka bã ta ɗaukaka wanda taƙawarsa ba ta ɗaukaka shi ba, kuma bã ta rage wanda taƙawarsa ta ɗaukaka shi. Fĩfĩkon taƙawa, shĩ ne fĩfĩko tabbatacce. -
۞ قَالَتِ ٱلْأَعْرَابُ ءَامَنَّا ۖ قُل لَّمْ تُؤْمِنُوا۟ وَلَـٰكِن قُولُوٓا۟ أَسْلَمْنَا وَلَمَّا يَدْخُلِ ٱلْإِيمَـٰنُ فِى قُلُوبِكُمْ ۖ وَإِن تُطِيعُوا۟ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ لَا يَلِتْكُم مِّنْ أَعْمَـٰلِكُمْ شَيْـًٔا ۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ١٤
Qalati alaʿrabu amanna qul lam tuminoo walakin qooloo aslamna walamma yadkhuli aleemanu fee quloobikum wain tuteeʿoo Allaha warasoolahu la yalitkum min aʿmalikum shayan inna Allaha ghafoorun raheemun
¡auyãwa suka ce: "Mun yi ĩmãni." Ka ce: "Ba ku yi ĩmãni ba, amma dai ku ce, 'Mun mĩƙawuya, ĩmani bai gama shiga a cikinzukãtanku ba. Kuma idan kun yi ɗã'a ga Allah da Manzon Sa, to, bã zai rage muku kõme daga ayyukanku ba. Lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai."
-
إِنَّمَا ٱلْمُؤْمِنُونَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ ثُمَّ لَمْ يَرْتَابُوا۟ وَجَـٰهَدُوا۟ بِأَمْوَٰلِهِمْ وَأَنفُسِهِمْ فِى سَبِيلِ ٱللَّهِ ۚ أُو۟لَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلصَّـٰدِقُونَ١٥
Innama almuminoona allatheena amanoo biAllahi warasoolihi thumma lam yartaboo wajahadoo biamwalihim waanfusihim fee sabeeli Allahi olaika humu alssadiqoona
Mũminan gaskiya kawai, sũ ne waɗanda suka yi ĩmãni da Allah da ManzonSa, sa'an nan ba su yi shakka ba, kuma suka yi jihãdi da dũkiyarsu da kuma rãyukansu, cikin tafarkin Allah. Waɗannan sũ ne mãsu gaskiya.
-
قُلْ أَتُعَلِّمُونَ ٱللَّهَ بِدِينِكُمْ وَٱللَّهُ يَعْلَمُ مَا فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَمَا فِى ٱلْأَرْضِ ۚ وَٱللَّهُ بِكُلِّ شَىْءٍ عَلِيمٌ١٦
Qul atuʿallimoona Allaha bideenikum waAllahu yaʿlamu ma fee alssamawati wama fee alardi waAllahu bikulli shayin ʿaleemun
Ka ce: "Kuna sanar da Allah ne game da addininku, alhãli kuwa Allah Yã san abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa, kuma Allah Masani ne ga dukan kõme?"
-
يَمُنُّونَ عَلَيْكَ أَنْ أَسْلَمُوا۟ ۖ قُل لَّا تَمُنُّوا۟ عَلَىَّ إِسْلَـٰمَكُم ۖ بَلِ ٱللَّهُ يَمُنُّ عَلَيْكُمْ أَنْ هَدَىٰكُمْ لِلْإِيمَـٰنِ إِن كُنتُمْ صَـٰدِقِينَ١٧
Yamunnoona ʿalayka an aslamoo qul la tamunnoo ʿalayya islamakum bali Allahu yamunnu ʿalaykum an hadakum lileemani in kuntum sadiqeena
Suna yin gõri a kanka wai sun musulunta. Ka ce: "Kada ku yi gõrin kun musulunta a kaina. Ã'a, Allah ne ke yi muku gõri dõmin Ya shiryar da ku ga ĩmãni, idan kun kasance mãsu gaskiya."
-
إِنَّ ٱللَّهَ يَعْلَمُ غَيْبَ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ۚ وَٱللَّهُ بَصِيرٌۢ بِمَا تَعْمَلُونَ١٨
Inna Allaha yaʿlamu ghayba alssamawati waalardi waAllahu baseerun bima taʿmaloona
"Lalle Allah yanã sanin gaibin sammai da ¡asa, kuma Allah Mai gani ne ga abin da kuke aikatãwa."
Tambayoyin da ake yawan yi
Mece ce ma’anar sunan Suratul Hujurat?
Ma’anar Hujurat ita ce “Ɗakuna”.
Suratul Hujurat tana cikin juz’i na nawa?
Suratul Hujurat tana cikin juz’i na 26.
Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Hujurat?
Suratul Hujurat tana da ayoyi 18.
Suratul Hujurat Makkiya ce ko Madaniya?
Suratul Hujurat sura ce Madaniya.
Suratul Hujurat ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?
Ita ce sura ta 49 a cikin Alƙur’ani.
Majiyoyi
- Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
- Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
- Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
- Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
- Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
- Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.
Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.