Suratul Ƙaf (ق) ita ce sura ta 50 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 45. Sura ce Makkiya, wadda ta sauka a Makka kafin Hijira, kuma tana cikin juz’i na 26.
A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Ƙaf gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.
Suratul Ƙaf cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ
-
قٓ ۚ وَٱلْقُرْءَانِ ٱلْمَجِيدِ١
Qaf waalqurani almajeedi
K. Inã rantsuwa da Alƙur'ãni Mai girma.
-
بَلْ عَجِبُوٓا۟ أَن جَآءَهُم مُّنذِرٌ مِّنْهُمْ فَقَالَ ٱلْكَـٰفِرُونَ هَـٰذَا شَىْءٌ عَجِيبٌ٢
Bal ʿajiboo an jaahum munthirun minhum faqala alkafiroona hatha shayon ʿajeebun
Ã'a, sun yi mãmãki, cewa mai gargaɗi, daga gare su, yã zo musu, sai kãfirai suka ce: "Wannan wani abu ne mai ban mãmãki."
-
أَءِذَا مِتْنَا وَكُنَّا تُرَابًا ۖ ذَٰلِكَ رَجْعٌۢ بَعِيدٌ٣
Aitha mitna wakunna turaban thalika rajʿun baʿeedun
"Shin idan muka mutu kuma muka kasance turɓãya (zã a kõmo da mu)? Waccan kõmowa ce mai nĩsa."
-
قَدْ عَلِمْنَا مَا تَنقُصُ ٱلْأَرْضُ مِنْهُمْ ۖ وَعِندَنَا كِتَـٰبٌ حَفِيظٌۢ٤
Qad ʿalimna ma tanqusu alardu minhum waʿindana kitabun hafeethun
Lalle ne Mun san abin da ƙasã ke ragẽwo daga gare su, kuma wurin Mu akwai wani littãfi mai tsarẽwa.
-
بَلْ كَذَّبُوا۟ بِٱلْحَقِّ لَمَّا جَآءَهُمْ فَهُمْ فِىٓ أَمْرٍ مَّرِيجٍ٥
Bal kaththaboo bialhaqqi lamma jaahum fahum fee amrin mareejin
Ã'a, sun ƙaryata ne game da gaskiyar a lõkacin da ta je musu, sabõda haka sunã a cikin wani al'amari mai raurawa.
-
أَفَلَمْ يَنظُرُوٓا۟ إِلَى ٱلسَّمَآءِ فَوْقَهُمْ كَيْفَ بَنَيْنَـٰهَا وَزَيَّنَّـٰهَا وَمَا لَهَا مِن فُرُوجٍ٦
Afalam yanthuroo ila alssamai fawqahum kayfa banaynaha wazayyannaha wama laha min furoojin
Shin, to, ba su yi dubi ba zuwa ga samã a bisa gare su, yadda Muka gĩna ta, kuma Muka ƙawãce ta, kuma bã ta da waɗansu tsãgogi?
-
وَٱلْأَرْضَ مَدَدْنَـٰهَا وَأَلْقَيْنَا فِيهَا رَوَٰسِىَ وَأَنۢبَتْنَا فِيهَا مِن كُلِّ زَوْجٍۭ بَهِيجٍ٧
Waalarda madadnaha waalqayna feeha rawasiya waanbatna feeha min kulli zawjin baheejin
Da ƙasã, Mun mĩƙe ta, kuma Mun jẽfa kafaffun duwãtsu a cikinta, kuma Mun tsirar, a cikinta daga kõwane ma'auri mai ban sha'awa?
-
تَبْصِرَةً وَذِكْرَىٰ لِكُلِّ عَبْدٍ مُّنِيبٍ٨
Tabsiratan wathikra likulli ʿabdin muneebin
Dõmin wãyar da ido da tunãtarwa ga dukan bãwa mai tawakkali?
-
وَنَزَّلْنَا مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءً مُّبَـٰرَكًا فَأَنۢبَتْنَا بِهِۦ جَنَّـٰتٍ وَحَبَّ ٱلْحَصِيدِ٩
Wanazzalna mina alssamai maan mubarakan faanbatna bihi jannatin wahabba alhaseedi
Kuma Mun sassakar, daga samã ruwa mai albarka sa'an nan Muka tsirar game da shi (itãcen) lambuna da ƙwãya abin girbẽwa.
-
وَٱلنَّخْلَ بَاسِقَـٰتٍ لَّهَا طَلْعٌ نَّضِيدٌ١٠
Waalnnakhla basiqatin laha talʿun nadeedun
Da itãcen dabĩno dõgãye, sunã da'ya'yan itãce gunda mãsu hauhawar jũna.
-
رِّزْقًا لِّلْعِبَادِ ۖ وَأَحْيَيْنَا بِهِۦ بَلْدَةً مَّيْتًا ۚ كَذَٰلِكَ ٱلْخُرُوجُ١١
Rizqan lilʿibadi waahyayna bihi baldatan maytan kathalika alkhurooju
Dõmin arziki ga bãyi, kuma Muka rãyar da ƙasa matacciya game da shi. Kamar wannan ne fitar daga kabari kake.
-
كَذَّبَتْ قَبْلَهُمْ قَوْمُ نُوحٍ وَأَصْحَـٰبُ ٱلرَّسِّ وَثَمُودُ١٢
Kaththabat qablahum qawmu noohin waashabu alrrassi wathamoodu
Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu (mutãnen yanzu) da ma'abũta Rassi,1da Samũdãwa.
Bayanai
[1] Rassi sunan wata rijĩya ce. Mutãnenta na zaune a gefenta da dabbõbinsu, sunã bauta wa gumãka, aka aika musu wani Annabi, anã ce da shi Hanzala bn safwan kõ kuma waninsa. -
وَعَادٌ وَفِرْعَوْنُ وَإِخْوَٰنُ لُوطٍ١٣
Waʿadun wafirʿawnu waikhwanu lootin
Da Ãdãwa da Fir'auna da 'yan'uwan Lũɗu.
-
وَأَصْحَـٰبُ ٱلْأَيْكَةِ وَقَوْمُ تُبَّعٍ ۚ كُلٌّ كَذَّبَ ٱلرُّسُلَ فَحَقَّ وَعِيدِ١٤
Waashabu alaykati waqawmu tubbaʿin kullun kaththaba alrrusula fahaqqa waʿeedi
Da ma'abũta ƙunci1da mutãnen Tubba'u,2 kõwanensu ya ƙaryata Manzanni, sai ƙyacẽwaTa ta tabbata.
Bayanai
[1] Ma'abũta ƙunci, mutãnen shu'aibu ne na farko. Bãyan an halaka su, sa'an nan ya tafi Madayana. [2] Tubba'u, sarkin Himyar ne,a Yemen, yã musulunta amma mutãnensa suka ƙi bin sa ga addini, aka halaka su, shi kuma ya tsĩra. Shĩ ne sarki wanda ya sãɓãwa ƙã'ida; ya musulunta amma mabiyansa ba su musulunta ba. -
أَفَعَيِينَا بِٱلْخَلْقِ ٱلْأَوَّلِ ۚ بَلْ هُمْ فِى لَبْسٍ مِّنْ خَلْقٍ جَدِيدٍ١٥
Afaʿayeena bialkhalqi alawwali bal hum fee labsin min khalqin jadeedin
Shin, to, Mun kãsa ne game da halittar farko? Ã'a, su sunã a cikin rikici daga halitta sãbuwa.
-
وَلَقَدْ خَلَقْنَا ٱلْإِنسَـٰنَ وَنَعْلَمُ مَا تُوَسْوِسُ بِهِۦ نَفْسُهُۥ ۖ وَنَحْنُ أَقْرَبُ إِلَيْهِ مِنْ حَبْلِ ٱلْوَرِيدِ١٦
Walaqad khalaqna alinsana wanaʿlamu ma tuwaswisu bihi nafsuhu wanahnu aqrabu ilayhi min habli alwareedi
Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halitta mutum kuma Mun san abin da ransa ke yin waswãsi da shi, kuma Mũ ne mafi kusanta zuwa gare shi daga lakar hannayẽnsa.
-
إِذْ يَتَلَقَّى ٱلْمُتَلَقِّيَانِ عَنِ ٱلْيَمِينِ وَعَنِ ٱلشِّمَالِ قَعِيدٌ١٧
Ith yatalaqqa almutalaqqiyani ʿani alyameeni waʿani alshshimali qaʿeedun
A lõkacin da mãsu haɗuwa biyu suke haɗuwa daga dãma, kuma daga hagu akwai wani (malã'ika) zaunanne.
-
مَّا يَلْفِظُ مِن قَوْلٍ إِلَّا لَدَيْهِ رَقِيبٌ عَتِيدٌ١٨
Ma yalfithu min qawlin illa ladayhi raqeebun ʿateedun
Bã ya lafazi da wata magana fãce a lĩƙe da shi akwai mai tsaro halartacce.
-
وَجَآءَتْ سَكْرَةُ ٱلْمَوْتِ بِٱلْحَقِّ ۖ ذَٰلِكَ مَا كُنتَ مِنْهُ تَحِيدُ١٩
Wajaat sakratu almawti bialhaqqi thalika ma kunta minhu taheedu
Kuma mãyen mutuwa ya jẽ da gaskiya. Wannan shĩ ne abin da ka kasance daga gare shi kanã bijirẽwa.
-
وَنُفِخَ فِى ٱلصُّورِ ۚ ذَٰلِكَ يَوْمُ ٱلْوَعِيدِ٢٠
Wanufikha fee alssoori thalika yawmu alwaʿeedi
Kuma aka hũra a cikin ƙaho. Wancan yinin ƙyacẽwar ne fa.
-
وَجَآءَتْ كُلُّ نَفْسٍ مَّعَهَا سَآئِقٌ وَشَهِيدٌ٢١
Wajaat kullu nafsin maʿaha saiqun washaheedun
Kuma kõwane rai ya zo, tãre da shi akwai mai kõra da mai shaida.
-
لَّقَدْ كُنتَ فِى غَفْلَةٍ مِّنْ هَـٰذَا فَكَشَفْنَا عَنكَ غِطَآءَكَ فَبَصَرُكَ ٱلْيَوْمَ حَدِيدٌ٢٢
Laqad kunta fee ghaflatin min hatha fakashafna ʿanka ghitaaka fabasaruka alyawma hadeedun
(Sai a ce masa): "Lalle ne, haƙĩƙa, ka kasance a cikin gafala daga wannan. To, Mun kuranye maka rufinka, sabõda haka ganinka a yau, mai kaifi ne."
-
وَقَالَ قَرِينُهُۥ هَـٰذَا مَا لَدَىَّ عَتِيدٌ٢٣
Waqala qareenuhu hatha ma ladayya ʿateedun
Kuma abõkin haɗinsa1 ya ce: "Wannan shi ne abin da ke tãre da ni halarce."
Bayanai
[1] Malã'ika mai rubũtun aikinsa. Bã ya rabuwa da shi sai a hãlãye uku, wurin jimã'i da salga da wanka. Malã'ikan da aka haɗa shi da shi dõmin ya rubũta ayyukansa. -
أَلْقِيَا فِى جَهَنَّمَ كُلَّ كَفَّارٍ عَنِيدٍ٢٤
Alqiya fee jahannama kulla kaffarin ʿaneedin
(A ce wa Malã'iku), "Ku jẽfa, a cikin Jahannama, dukan mai yawan kãfirci, mai tsaurin rai."
-
مَّنَّاعٍ لِّلْخَيْرِ مُعْتَدٍ مُّرِيبٍ٢٥
Mannaʿin lilkhayri muʿtadin mureebin
"Mai yawan hanãwa ga alhẽri, mai zãlunci, mai shakka."
-
ٱلَّذِى جَعَلَ مَعَ ٱللَّهِ إِلَـٰهًا ءَاخَرَ فَأَلْقِيَاهُ فِى ٱلْعَذَابِ ٱلشَّدِيدِ٢٦
Allathee jaʿala maʿa Allahi ilahan akhara faalqiyahu fee alʿathabi alshshadeedi
"Wanda ya sanya, tãre da Allah wani abin bautãwa na dabam, sabõda haka kujẽfa shi a cikin azãba mai tsanani."
-
۞ قَالَ قَرِينُهُۥ رَبَّنَا مَآ أَطْغَيْتُهُۥ وَلَـٰكِن كَانَ فِى ضَلَـٰلٍۭ بَعِيدٍ٢٧
Qala qareenuhu rabbana ma atghaytuhu walakin kana fee dalalin baʿeedin
Abõkin haɗinsa1 ya ce: "Ya Ubangijinmu! Ban sanya shi girman kai ba, kuma amma ya kasance a cikin ɓata mai nĩsa."
Bayanai
[1] Shaiɗanin da ke tãre dashi. A cikin hadĩsi an ruwaito cewa kõwa yana da Shaiɗani tãre da shi, sai dai idan ya rinjãye shi, da abin da Allah Ya aza masa, ko kuma shi sai shaiɗãnin ya rinjãye shi da bin son zũciyarsa. -
قَالَ لَا تَخْتَصِمُوا۟ لَدَىَّ وَقَدْ قَدَّمْتُ إِلَيْكُم بِٱلْوَعِيدِ٢٨
Qala la takhtasimoo ladayya waqad qaddamtu ilaykum bialwaʿeedi
Ya ce: "Kada ku yi husũma a wur Nalhãli Na gabãtar da ƙyacewa zuwa gare ku."
-
مَا يُبَدَّلُ ٱلْقَوْلُ لَدَىَّ وَمَآ أَنَا۠ بِظَلَّـٰمٍ لِّلْعَبِيدِ٢٩
Ma yubaddalu alqawlu ladayya wama ana bithallamin lilʿabeedi
"Ba a musanya magana a wuriNa, Kuma Ban zama Mai zãlunci ba ga bãyi Na."
-
يَوْمَ نَقُولُ لِجَهَنَّمَ هَلِ ٱمْتَلَأْتِ وَتَقُولُ هَلْ مِن مَّزِيدٍ٣٠
Yawma naqoolu lijahannama hali imtalati wataqoolu hal min mazeedin
Rãnar da Muke cẽwa ga Jahannama "Shin, kin cika?" Kuma ta ce: "Ashe,1 akwai wani ƙãri?"
Bayanai
[1] Wannan jawãbi na Jahannama yanã ɗaukar ma'anõni biyu. Ta farko tanã nũna ta cika ƙwarai, amma tanã kũkan a ƙara mata wani abu a cikinta. Wannan fassara ta yi daidai da ayãr da ta ce, "Lalle na cika Jahannama daga aljannu da mutãne gabã ɗaya." Sura ta 32, ãyã ta 13. Fassara ta biyu, ita ce Jahannama nã neman ƙãri tanã hushi sabõda mãsu sãɓawa umurnin Allah. Sũra ta 67 ãyõyi 6, 7 da 8. -
وَأُزْلِفَتِ ٱلْجَنَّةُ لِلْمُتَّقِينَ غَيْرَ بَعِيدٍ٣١
Waozlifati aljannatu lilmuttaqeena ghayra baʿeedin
Kuma a kusantar dã Aljanna ga mãsu taƙawa, ba da nĩsa ba.
-
هَـٰذَا مَا تُوعَدُونَ لِكُلِّ أَوَّابٍ حَفِيظٍ٣٢
Hatha ma tooʿadoona likulli awwabin hafeethin
"Wannan shĩ ne abin da ake yi muku wa'adi da shi ga dukan mai yawan kõmawa ga Allah, mai tsarewar (umurninSa).
-
مَّنْ خَشِىَ ٱلرَّحْمَـٰنَ بِٱلْغَيْبِ وَجَآءَ بِقَلْبٍ مُّنِيبٍ٣٣
Man khashiya alrrahmana bialghaybi wajaa biqalbin muneebin
"Wanda ya ji tsõron Mai rahama a fake,1kuma ya zo da wata irin zũciya mai tawakkali."
Bayanai
[1] Tsoron Allah a fake, shĩ ne a bauta masa, bã da riya ba, ɓayyane da ɓõye duka ɗaya. -
ٱدْخُلُوهَا بِسَلَـٰمٍ ۖ ذَٰلِكَ يَوْمُ ٱلْخُلُودِ٣٤
Odkhulooha bisalamin thalika yawmu alkhuloodi
(A ce musu) "Ku shige ta da aminci,1waccan ita ce rãnar dawwama."
Bayanai
[1] Kõ kuma ku shiga da sallama. -
لَهُم مَّا يَشَآءُونَ فِيهَا وَلَدَيْنَا مَزِيدٌ٣٥
Lahum ma yashaoona feeha waladayna mazeedun
Sunã da abin da suke so a cikinta, kuma tãre da Mũ akwai ƙãrin ni'ima,
-
وَكَمْ أَهْلَكْنَا قَبْلَهُم مِّن قَرْنٍ هُمْ أَشَدُّ مِنْهُم بَطْشًا فَنَقَّبُوا۟ فِى ٱلْبِلَـٰدِ هَلْ مِن مَّحِيصٍ٣٦
Wakam ahlakna qablahum min qarnin hum ashaddu minhum batshan fanaqqaboo fee albiladi hal min maheesin
Kuma da yawa Muka halakar, a gabãninsu, (mutãnen yanzu) ɗaga waɗansu al'ummomi, (waɗanda suke) sũ ne mafi ƙarfin damƙa daga gare su, sa'an nan suka yi bincike a cikin ƙasãshe: 'Kõ akwai wurin tsĩra'?1 (Babu).
Bayanai
[1] Sun nħmi wurin tsĩra, ba su sãmu ba, sabõda haka kãfiran yanzu ma ba su iya samun wurin tsĩra, sai dai idan sunkõma ga Allah ta hanyar Manzon Sa kawai, watau taƙawa ga Allah ke nan. Anã kãre azãbar Sa da ibãdar Sa kamar yadda Yake so. -
إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَذِكْرَىٰ لِمَن كَانَ لَهُۥ قَلْبٌ أَوْ أَلْقَى ٱلسَّمْعَ وَهُوَ شَهِيدٌ٣٧
Inna fee thalika lathikra liman kana lahu qalbun aw alqa alssamʿa wahuwa shaheedun
Lalle ne, a cikin wancan, akwai tunãtarwa ga wanda zũciyarsa ta kasance gare shi, kõ kuwa ya jẽfa saurãro, alhãli kuwa yanã halarce (da hankalinsa).
-
وَلَقَدْ خَلَقْنَا ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا فِى سِتَّةِ أَيَّامٍ وَمَا مَسَّنَا مِن لُّغُوبٍ٣٨
Walaqad khalaqna alssamawati waalarda wama baynahuma fee sittati ayyamin wama massana min lughoobin
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu, a cikin kwãnaki shida, alhãli wata'yar wahala ba ta shãfe Mu ba.
-
فَٱصْبِرْ عَلَىٰ مَا يَقُولُونَ وَسَبِّحْ بِحَمْدِ رَبِّكَ قَبْلَ طُلُوعِ ٱلشَّمْسِ وَقَبْلَ ٱلْغُرُوبِ٣٩
Faisbir ʿala ma yaqooloona wasabbih bihamdi rabbika qabla tulooʿi alshshamsi waqabla alghuroobi
Sabõda haka, ka yi haƙuri a kan abin da suke fadã, kuma ka yi tasĩhi1 game da gõdẽ wa Ubangijinka (watau ka yi salla) a gabãnin fitõwar rãnã da gabãnin ɓacẽwarta.
Bayanai
[1] Tasbĩhi game da gõdewa Allah a gabãnin fitar rãnã, shi ne sallar asuba, na gabãnin ɓacewarta, shi ne sallar Azahar da La'asar. Daga dare kuwa, shĩ ne sallar Magariba da Isha'i. Bãyan sujada, shĩ ne sallõli na nafila kuma ma'anarsa a nan tasbĩhi da tahmĩdi da kabbarõri a bãyan sallõli farillai talãtin da uku kõwace, sa'annan a cika ɗari da addu'ar da aka ruwaito a nan. -
وَمِنَ ٱلَّيْلِ فَسَبِّحْهُ وَأَدْبَـٰرَ ٱلسُّجُودِ٤٠
Wamina allayli fasabbihhu waadbara alssujoodi
Kuma daga dare, sai ka yi tasbĩhi a gare Shi da bãyan sujada.
-
وَٱسْتَمِعْ يَوْمَ يُنَادِ ٱلْمُنَادِ مِن مَّكَانٍ قَرِيبٍ٤١
Waistamiʿ yawma yunadi almunadi min makanin qareebin
Kuma ka saurãra a rãnar da mai kira ke yin kira daga wuri1makusanci.
Bayanai
[1] Mai kira shĩ ne Isrãfĩlu a cikin ƙaho a Baitil Maƙadis dõmin a nan ƙasa ta fi zama kusa da samã. -
يَوْمَ يَسْمَعُونَ ٱلصَّيْحَةَ بِٱلْحَقِّ ۚ ذَٰلِكَ يَوْمُ ٱلْخُرُوجِ٤٢
Yawma yasmaʿoona alssayhata bialhaqqi thalika yawmu alkhurooji
Rãnar da suke saurãron tsãwa da gaskiya. Wancan shĩ ne yinin fita (daga kabari).
-
إِنَّا نَحْنُ نُحْىِۦ وَنُمِيتُ وَإِلَيْنَا ٱلْمَصِيرُ٤٣
Inna nahnu nuhyee wanumeetu wailayna almaseeru
Lalle Mũ ne haƙĩƙa, Mu ne ke rãyarwa, kuma Mũ ne ke kashẽwa, kuma zuwa gare Mu kawai ne makõmar take.
-
يَوْمَ تَشَقَّقُ ٱلْأَرْضُ عَنْهُمْ سِرَاعًا ۚ ذَٰلِكَ حَشْرٌ عَلَيْنَا يَسِيرٌ٤٤
Yawma tashaqqaqu alardu ʿanhum siraʿan thalika hashrun ʿalayna yaseerun
Rãnar da ƙasã ke tsattsãgẽwa daga gare su, sunã mãsu gaggãwa. Wancan tãrãwar mutãne ne, mai sauƙi a gare Mu.
-
نَّحْنُ أَعْلَمُ بِمَا يَقُولُونَ ۖ وَمَآ أَنتَ عَلَيْهِم بِجَبَّارٍ ۖ فَذَكِّرْ بِٱلْقُرْءَانِ مَن يَخَافُ وَعِيدِ٤٥
Nahnu aʿlamu bima yaqooloona wama anta ʿalayhim bijabbarin fathakkir bialqurani man yakhafu waʿeedi
Mũ ne mafi sani game da abin da suke faɗi, kuma bã zã ka zama mai tĩlasta su ba. Sabõda haka ka tunatar game da Alƙur'ani,1 ga wanda ke tsõron ƙyacewaTa.
Bayanai
[1] Wannan ya nũna ba a wa'azi da ilmin da bã daga Alƙur'ãni aka fitar da shi ba, sai fa idan bai sãɓawa abin da ke cikin Alƙur'ani ba.
Tambayoyin da ake yawan yi
Suratul Ƙaf tana cikin juz’i na nawa?
Suratul Ƙaf tana cikin juz’i na 26.
Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Ƙaf?
Suratul Ƙaf tana da ayoyi 45.
Suratul Ƙaf Makkiya ce ko Madaniya?
Suratul Ƙaf sura ce Makkiya.
Suratul Ƙaf ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?
Ita ce sura ta 50 a cikin Alƙur’ani.
Majiyoyi
- Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
- Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
- Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
- Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
- Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
- Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.
Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.