Suratul Ra’ad (الرعد) ita ce sura ta 13 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 43. Ma’anar sunanta ita ce “Tsawa”. Sura ce Madaniya, wadda ta sauka a Madina bayan Hijira, kuma tana cikin juz’i na 13.
A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Ra’ad gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.
Suratul Ra’ad cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ
-
الٓمٓر ۚ تِلْكَ ءَايَـٰتُ ٱلْكِتَـٰبِ ۗ وَٱلَّذِىٓ أُنزِلَ إِلَيْكَ مِن رَّبِّكَ ٱلْحَقُّ وَلَـٰكِنَّ أَكْثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يُؤْمِنُونَ١
Aliflammeemra tilka ayatu alkitabi waallathee onzila ilayka min rabbika alhaqqu walakinna akthara alnnasi la yuminoona
A. L̃. M̃.R. Waɗancan ayõyin littãfi ne kuma abin da aka saukar gare ka daga Ubangijinka ne gaskiya, kuma amma mafi yawan mutãne bã su yin ĩmãni.
-
ٱللَّهُ ٱلَّذِى رَفَعَ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ بِغَيْرِ عَمَدٍ تَرَوْنَهَا ۖ ثُمَّ ٱسْتَوَىٰ عَلَى ٱلْعَرْشِ ۖ وَسَخَّرَ ٱلشَّمْسَ وَٱلْقَمَرَ ۖ كُلٌّ يَجْرِى لِأَجَلٍ مُّسَمًّى ۚ يُدَبِّرُ ٱلْأَمْرَ يُفَصِّلُ ٱلْـَٔايَـٰتِ لَعَلَّكُم بِلِقَآءِ رَبِّكُمْ تُوقِنُونَ٢
Allahu allathee rafaʿa alssamawati bighayri ʿamadin tarawnaha thumma istawa ʿala alʿarshi wasakhkhara alshshamsa waalqamara kullun yajree liajalin musamman yudabbiru alamra yufassilu alayati laʿallakum biliqai rabbikum tooqinoona
Allah Shi ne wanda Ya ɗaukaka sammai, bã da ginshiƙai ba waɗanda kuke ganin su. Sa'an nan kuma Ya daidaita a kan Al'arshi, kuma Ya hõre rãnã da watã, kõwane yanã gudãna zuwa ga ajali ambatacce. Yanã shirya al'amari, Yanã rarrabe ãyõyi daki-daki, mai yiwuwa ne ku yi yaƙĩni da haɗuwa da Ubangijinku.
-
وَهُوَ ٱلَّذِى مَدَّ ٱلْأَرْضَ وَجَعَلَ فِيهَا رَوَٰسِىَ وَأَنْهَـٰرًا ۖ وَمِن كُلِّ ٱلثَّمَرَٰتِ جَعَلَ فِيهَا زَوْجَيْنِ ٱثْنَيْنِ ۖ يُغْشِى ٱلَّيْلَ ٱلنَّهَارَ ۚ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَـٰتٍ لِّقَوْمٍ يَتَفَكَّرُونَ٣
Wahuwa allathee madda alarda wajaʿala feeha rawasiya waanharan wamin kulli alththamarati jaʿala feeha zawjayni ithnayni yughshee allayla alnnahara inna fee thalika laayatin liqawmin yatafakkaroona
Kuma shĩ, ne wanda Ya shimfiɗa kasa, kuma Ya sanya duwãtsu da kõguna a cikinta, kuma daga dukan 'ya'yan itãce Ya sanya ma'aura biyu cikinsu. Yanã sanya dare ya rufe yini. Lalle ne a cikin wancan, haƙĩƙa akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda suke yin tunãni.
-
وَفِى ٱلْأَرْضِ قِطَعٌ مُّتَجَـٰوِرَٰتٌ وَجَنَّـٰتٌ مِّنْ أَعْنَـٰبٍ وَزَرْعٌ وَنَخِيلٌ صِنْوَانٌ وَغَيْرُ صِنْوَانٍ يُسْقَىٰ بِمَآءٍ وَٰحِدٍ وَنُفَضِّلُ بَعْضَهَا عَلَىٰ بَعْضٍ فِى ٱلْأُكُلِ ۚ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَـٰتٍ لِّقَوْمٍ يَعْقِلُونَ٤
Wafee alardi qitaʿun mutajawiratun wajannatun min aʿnabin wazarʿun wanakheelun sinwanun waghayru sinwanin yusqa bimain wahidin wanufaddilu baʿdaha ʿala baʿdin fee alokuli inna fee thalika laayatin liqawmin yaʿqiloona
Kuma a cikin ƙasa akwai yankuna mãsu maƙwabtaka, da gõnaki na inabõbi da shũka da dabĩnai iri guda, da waɗanda bã iri guda ba, anã shayar da su da ruwa guda. Kuma Munã fĩfĩta sãshen sa a kan sãshe a wajen ci. Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi ga muiãne waɗan da suke hankalta.
-
۞ وَإِن تَعْجَبْ فَعَجَبٌ قَوْلُهُمْ أَءِذَا كُنَّا تُرَٰبًا أَءِنَّا لَفِى خَلْقٍ جَدِيدٍ ۗ أُو۟لَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ بِرَبِّهِمْ ۖ وَأُو۟لَـٰٓئِكَ ٱلْأَغْلَـٰلُ فِىٓ أَعْنَاقِهِمْ ۖ وَأُو۟لَـٰٓئِكَ أَصْحَـٰبُ ٱلنَّارِ ۖ هُمْ فِيهَا خَـٰلِدُونَ٥
Wain taʿjab faʿajabun qawluhum aitha kunna turaban ainna lafee khalqin jadeedin olaika allatheena kafaroo birabbihim waolaika alaghlalu fee aʿnaqihim waolaika ashabu alnnari hum feeha khalidoona
Kuma idan ka yi mãmãki, to, mãmãkin kam shi ne maganarsu, "Shin, idan muka kasance turɓãya, zã mu zama a cikin wata halitta sãbuwa?" Waɗancan ne waɗanda suka kãfirta da Ubangijinsu, kuma waɗanda akwai ƙuƙumai a cikin wuyõyinsu, kuma waɗancan ne abõkan wuta. Sũ, a cikinta, mãsu dawwama ne.
-
وَيَسْتَعْجِلُونَكَ بِٱلسَّيِّئَةِ قَبْلَ ٱلْحَسَنَةِ وَقَدْ خَلَتْ مِن قَبْلِهِمُ ٱلْمَثُلَـٰتُ ۗ وَإِنَّ رَبَّكَ لَذُو مَغْفِرَةٍ لِّلنَّاسِ عَلَىٰ ظُلْمِهِمْ ۖ وَإِنَّ رَبَّكَ لَشَدِيدُ ٱلْعِقَابِ٦
Wayastaʿjiloonaka bialssayyiati qabla alhasanati waqad khalat min qablihimu almathulatu wainna rabbaka lathoo maghfiratin lilnnasi ʿala thulmihim wainna rabbaka lashadeedu alʿiqabi
Kuma sunã nẽman ka da gaggãwa da azãba a gabãnin rahama, alhãli kuwa abũbuwan misãli sun gabãta a gabãninsu. Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Ma'abũcin gãfara ne ga mutãne a kan zãluncinsu, kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Mai tsananin uƙũba ne.
-
وَيَقُولُ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ لَوْلَآ أُنزِلَ عَلَيْهِ ءَايَةٌ مِّن رَّبِّهِۦٓ ۗ إِنَّمَآ أَنتَ مُنذِرٌ ۖ وَلِكُلِّ قَوْمٍ هَادٍ٧
Wayaqoolu allatheena kafaroo lawla onzila ʿalayhi ayatun min rabbihi innama anta munthirun walikulli qawmin hadin
Kuma waɗanda suka kãfirta sunã cẽwa don me ba a saukar da wata ãyã a gare shi ba daga Ubangijin sa? Abin sani kawai, kai dai mai gargaɗi ne kuma a cikin kõwaɗanne mutãne akwai mai shiryarwa.
-
ٱللَّهُ يَعْلَمُ مَا تَحْمِلُ كُلُّ أُنثَىٰ وَمَا تَغِيضُ ٱلْأَرْحَامُ وَمَا تَزْدَادُ ۖ وَكُلُّ شَىْءٍ عِندَهُۥ بِمِقْدَارٍ٨
Allahu yaʿlamu ma tahmilu kullu ontha wama tagheedu alarhamu wama tazdadu wakullu shayin ʿindahu bimiqdarin
Allah Yanã sanin abin da kõwace mace take ɗauke da shi a cikinta da abin da mahaifu suke ragẽwa1 da abin da suke ƙãrãwa. Kuma dukkan kõme, a wurinSa, da gwargwado yake.
Bayanai
[1] Ragõwar lõkacin cikin ko ƙãruwarsa. -
عَـٰلِمُ ٱلْغَيْبِ وَٱلشَّهَـٰدَةِ ٱلْكَبِيرُ ٱلْمُتَعَالِ٩
ʿalimu alghaybi waalshshahadati alkabeeru almutaʿali
Shi ne Masanin fake da bayyane, Mai girma, Maɗaukaki.
-
سَوَآءٌ مِّنكُم مَّنْ أَسَرَّ ٱلْقَوْلَ وَمَن جَهَرَ بِهِۦ وَمَنْ هُوَ مُسْتَخْفٍۭ بِٱلَّيْلِ وَسَارِبٌۢ بِٱلنَّهَارِ١٠
Sawaon minkum man asarra alqawla waman jahara bihi waman huwa mustakhfin biallayli wasaribun bialnnahari
Daidai ne daga gare ku, wanda ya asirta magana da wanda ya bayyana game da ita, da wanda yake shi mai nẽman ɓõyewa ne da dare, da mai bayyana a cikin tafiyarsa a hanya da rãna1.
Bayanai
[1] Hasken rãnã mai kama da ruwa ga idon mai dũbi daga nesa. -
لَهُۥ مُعَقِّبَـٰتٌ مِّنۢ بَيْنِ يَدَيْهِ وَمِنْ خَلْفِهِۦ يَحْفَظُونَهُۥ مِنْ أَمْرِ ٱللَّهِ ۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُغَيِّرُ مَا بِقَوْمٍ حَتَّىٰ يُغَيِّرُوا۟ مَا بِأَنفُسِهِمْ ۗ وَإِذَآ أَرَادَ ٱللَّهُ بِقَوْمٍ سُوٓءًا فَلَا مَرَدَّ لَهُۥ ۚ وَمَا لَهُم مِّن دُونِهِۦ مِن وَالٍ١١
Lahu muʿaqqibatun min bayni yadayhi wamin khalfihi yahfathoonahu min amri Allahi inna Allaha la yughayyiru ma biqawmin hatta yughayyiroo ma bianfusihim waitha arada Allahu biqawmin sooan fala maradda lahu wama lahum min doonihi min walin
(Kowannenku) Yanã da waɗansu malã'iku mãsu maye wa jũna a gaba gare shi da bãya gare shi, sunã tsare shi daga umurnin Allah. Lalle ne Allah bã Ya canja abin da yake ga, mutãne sai sun canja abin da yake ga zukatansu. Kuma idan Allah Ya yi nufin wata azãba game da mutãne, to, bãbu mai mayar da ita, kuma bã su da wani majiɓinci1 baicin Shi.
Bayanai
[1] Bãbu wani majiɓinci baicin Allah, wanda zai iya tsĩrar da su daga azãbarsa. -
هُوَ ٱلَّذِى يُرِيكُمُ ٱلْبَرْقَ خَوْفًا وَطَمَعًا وَيُنشِئُ ٱلسَّحَابَ ٱلثِّقَالَ١٢
Huwa allathee yureekumu albarqa khawfan watamaʿan wayunshio alssahaba alththiqala
Shĩ ne Wanda Yake nũna muku walƙiya dõmin tsõro da tsammãni, kuma Ya ƙãga halittar girãgizai mãsu nauyi.
-
وَيُسَبِّحُ ٱلرَّعْدُ بِحَمْدِهِۦ وَٱلْمَلَـٰٓئِكَةُ مِنْ خِيفَتِهِۦ وَيُرْسِلُ ٱلصَّوَٰعِقَ فَيُصِيبُ بِهَا مَن يَشَآءُ وَهُمْ يُجَـٰدِلُونَ فِى ٱللَّهِ وَهُوَ شَدِيدُ ٱلْمِحَالِ١٣
Wayusabbihu alrraʿdu bihamdihi waalmalaikatu min kheefatihi wayursilu alssawaʿiqa fayuseebu biha man yashao wahum yujadiloona fee Allahi wahuwa shadeedu almihali
Kuma arãdu tanã tasbĩhi game da gõde Masa, da malã'iku dõmin tsoronsa. Kuma Yanã aiko tsãwawwaki, sa'an nan Ya sãmi wanda Yake so da su alhãli kuwa sũ, sunã jãyayya a cikin (al'amarin) Allah kuma shĩ ne mai tsananin hĩla.1
Bayanai
[1] Hĩla, ita ce mãkirci, Allah Yanã azabta mãsu yin hĩla ga addininsa, da azãba mai tsanani, kuma Ya kãmã su da hĩlarsu ta hanyar da ba su sani ba. -
لَهُۥ دَعْوَةُ ٱلْحَقِّ ۖ وَٱلَّذِينَ يَدْعُونَ مِن دُونِهِۦ لَا يَسْتَجِيبُونَ لَهُم بِشَىْءٍ إِلَّا كَبَـٰسِطِ كَفَّيْهِ إِلَى ٱلْمَآءِ لِيَبْلُغَ فَاهُ وَمَا هُوَ بِبَـٰلِغِهِۦ ۚ وَمَا دُعَآءُ ٱلْكَـٰفِرِينَ إِلَّا فِى ضَلَـٰلٍ١٤
Lahu daʿwatu alhaqqi waallatheena yadʿoona min doonihi la yastajeeboona lahum bishayin illa kabasiti kaffayhi ila almai liyablugha fahu wama huwa bibalighihi wama duʿao alkafireena illa fee dalalin
Yanã da kiran gaskiya, kuma waɗanda (kãfirai) suke kira baicinsa, bã su karɓa musu da kõme fãce kamar mai shimfiɗa tãfukansa Zuwa ga ruwa (na girgije) dõmin (ruwan) ya kai ga bãkinsa, kuma shi bã mai kaiwa gare shi ba. Kuma kiran kãfirai (ga wanin Allah) bai zama1 ba fãce yanã a cikin ɓata.
Bayanai
[1] Allah Mamallakin ruwa, Yanã kiran mutãne dõmin Ya bã su ruwan su shã. Su kuma kãfirai sunã kiran waɗansu abũbuwa dabam waɗanda kõ karɓa musu kiran bã zã su iya yi ba, kuma sunã neman ruwa daga gare su, alhãli kuma ba su mallaki kõme ba. Watau Mai abu Yanã kiran su dõmin Ya bã su, sun ƙi karɓa Masa sai sunã kiran wani wanda bai mallaki kõme ba, sunã rõƙon Sa ruwa. -
وَلِلَّهِ يَسْجُدُ مَن فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ طَوْعًا وَكَرْهًا وَظِلَـٰلُهُم بِٱلْغُدُوِّ وَٱلْـَٔاصَالِ ۩١٥
Walillahi yasjudu man fee alssamawati waalardi tawʿan wakarhan wathilaluhum bialghuduwwi waalasali
Kuma sabõda Allah wanda yake a cikin sammai da ƙasa suke yin sujada, so da ƙi, kuma da inuwõyinsu, a sãfe da maraice.
-
قُلْ مَن رَّبُّ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ قُلِ ٱللَّهُ ۚ قُلْ أَفَٱتَّخَذْتُم مِّن دُونِهِۦٓ أَوْلِيَآءَ لَا يَمْلِكُونَ لِأَنفُسِهِمْ نَفْعًا وَلَا ضَرًّا ۚ قُلْ هَلْ يَسْتَوِى ٱلْأَعْمَىٰ وَٱلْبَصِيرُ أَمْ هَلْ تَسْتَوِى ٱلظُّلُمَـٰتُ وَٱلنُّورُ ۗ أَمْ جَعَلُوا۟ لِلَّهِ شُرَكَآءَ خَلَقُوا۟ كَخَلْقِهِۦ فَتَشَـٰبَهَ ٱلْخَلْقُ عَلَيْهِمْ ۚ قُلِ ٱللَّهُ خَـٰلِقُ كُلِّ شَىْءٍ وَهُوَ ٱلْوَٰحِدُ ٱلْقَهَّـٰرُ١٦
Qul man rabbu alssamawati waalardi quli Allahu qul afaittakhathtum min doonihi awliyaa la yamlikoona lianfusihim nafʿan wala darran qul hal yastawee alaʿma waalbaseeru am hal tastawee alththulumatu waalnnooru am jaʿaloo lillahi shurakaa khalaqoo kakhalqihi fatashabaha alkhalqu ʿalayhim quli Allahu khaliqu kulli shayin wahuwa alwahidu alqahharu
Ka ce: "Wãne ne Ubangijin sammai da ƙasa?" Ka ce: "Allah". Ka ce: "Ashe fa, kun riƙi waɗansu masõya baicin Shi, waɗanda ba su mallaka wa kansu wani amfãni ba kuma haka bã su tũre wata cũta?" Ka ce: "Shin makãho da mai gani sunã daidaita? Kõ shin duhu da haske sunã daidaita? ko sun sanya ga Allah waɗansu abõkan tãrayya waɗanda suka yi halitta kamar halittarSa sa'an nan halittar ta yi kama da jũna a gare su?" Ka ce: "Allah ne Mai halitta kõme kuma Shĩ ne Maɗaukaki, Marinjãyi."
-
أَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءً فَسَالَتْ أَوْدِيَةٌۢ بِقَدَرِهَا فَٱحْتَمَلَ ٱلسَّيْلُ زَبَدًا رَّابِيًا ۚ وَمِمَّا يُوقِدُونَ عَلَيْهِ فِى ٱلنَّارِ ٱبْتِغَآءَ حِلْيَةٍ أَوْ مَتَـٰعٍ زَبَدٌ مِّثْلُهُۥ ۚ كَذَٰلِكَ يَضْرِبُ ٱللَّهُ ٱلْحَقَّ وَٱلْبَـٰطِلَ ۚ فَأَمَّا ٱلزَّبَدُ فَيَذْهَبُ جُفَآءً ۖ وَأَمَّا مَا يَنفَعُ ٱلنَّاسَ فَيَمْكُثُ فِى ٱلْأَرْضِ ۚ كَذَٰلِكَ يَضْرِبُ ٱللَّهُ ٱلْأَمْثَالَ١٧
Anzala mina alssamai maan fasalat awdiyatun biqadariha faihtamala alssaylu zabadan rabiyan wamimma yooqidoona ʿalayhi fee alnnari ibtighaa hilyatin aw mataʿin zabadun mithluhu kathalika yadribu Allahu alhaqqa waalbatila faamma alzzabadu fayathhabu jufaan waamma ma yanfaʿu alnnasa fayamkuthu fee alardi kathalika yadribu Allahu alamthala
Ya saukar da ruwa daga sama1, sai magudanai suka gudãna da gwargwadonsu, Sa'an nan kõgi ya ɗauki kumfa mai ƙãruwa, kuma daga abin da suke zuga a kansa (azurfa ko zinari kõ ƙarfe) a cikin wuta dõmin nẽman ado kõ kuwa kãyan ɗãki akwai kumfa misãlinsa (kumfar ruwa). Kamar wancan ne Allah Yake bayyana gaskiya da ƙarya. To, amma kumfa, sai ya tafi ƙẽƙasasshe, kumaamma abin da yake amfãnin mutãne sai ya zauna a cikin ƙasa. Kamar wancan ne Allah Yake bayyana misãlai.
Bayanai
[1] Idan ruwa ya sauka daga sama sa'an nan ya gudãna a cikin rãfuna zai yi kumfa. Sai ruwa mai amfãnin mutãne ya nutse a ƙasa ya zauna, sa'an nan kumfan kuma ya ƙeƙashe ya lãlãce. Haka kuma idan an sanya ƙarfe na zinãri kõ na azurfa kõ baƙin ƙarfe a cikin wuta, aka zuga ta a kansa, zai fitar da kumfa, wãtau tsakin tama wanda zã a fitar dõmin rashin amfãninsa, dõmin zĩnariyar ƙwarai mai amfãni ta wanzu. To haka ga kõme akwai kumfa marashin amfãni da mai kyãwo mai amfani. -
لِلَّذِينَ ٱسْتَجَابُوا۟ لِرَبِّهِمُ ٱلْحُسْنَىٰ ۚ وَٱلَّذِينَ لَمْ يَسْتَجِيبُوا۟ لَهُۥ لَوْ أَنَّ لَهُم مَّا فِى ٱلْأَرْضِ جَمِيعًا وَمِثْلَهُۥ مَعَهُۥ لَٱفْتَدَوْا۟ بِهِۦٓ ۚ أُو۟لَـٰٓئِكَ لَهُمْ سُوٓءُ ٱلْحِسَابِ وَمَأْوَىٰهُمْ جَهَنَّمُ ۖ وَبِئْسَ ٱلْمِهَادُ١٨
Lillatheena istajaboo lirabbihimu alhusna waallatheena lam yastajeeboo lahu law anna lahum ma fee alardi jameeʿan wamithlahu maʿahu laiftadaw bihi olaika lahum sooo alhisabi wamawahum jahannamu wabisa almihadu
Ga waɗanda1 suka karɓa wa Ubangijinsu akwai abu mafi kyau a gare su, kuma waɗanda suke ba su karɓa Masa ba, to, lalle dã sunã da abin da yake a cikin ƙasa gaba ɗaya da misãlinsa tãre da shi, haƙĩƙa, dã sun yi fansa da shi. Waɗancan sunã da mummunan bincike kuma matabbatarsu Jahannama ce, kuma tir da ita ta zama shimfida.
Bayanai
[1] Bãyan da ya faɗi cewa Allah Yanã kira, kiran gaskiya a cikin ãyã ta l4, kuma waɗansu mutãne sun ƙi karɓar kiran Allah, sai sunã kiran waɗansu abũbuwa dabam, sai ya bayyana, a nan, sakamakon wanda ya karɓi kiran Allah sãmun ruwan sha, sabõda Mai abu ne Ya kirãwo shi, Ya kuma bã shi, ya sha a hankali kwance, sa'an nan kuma Allah zai bã shi abin da ya fi ruwan kyau, watau Aljanna. Amma wanda ya ƙi karɓãwa, to, yã yi hasãra biyu, bai sãmi ruwan da ya yi kiran wani ya bã shi ba, sa'an nan kuma ya haɗu da azãbar da take zai iya bãyar da dukan abin da ya mallaka dõmin ya yi fansar kansa da ita. -
۞ أَفَمَن يَعْلَمُ أَنَّمَآ أُنزِلَ إِلَيْكَ مِن رَّبِّكَ ٱلْحَقُّ كَمَنْ هُوَ أَعْمَىٰٓ ۚ إِنَّمَا يَتَذَكَّرُ أُو۟لُوا۟ ٱلْأَلْبَـٰبِ١٩
Afaman yaʿlamu annama onzila ilayka min rabbika alhaqqu kaman huwa aʿma innama yatathakkaru oloo alalbabi
Shin, fa, wanda yake sanin cẽwa lalle abin da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka ne gaskiya yanã zama kamar wanda yake makãho? Abin sani kawai masu hankali sũ ke yin tunãni.
-
ٱلَّذِينَ يُوفُونَ بِعَهْدِ ٱللَّهِ وَلَا يَنقُضُونَ ٱلْمِيثَـٰقَ٢٠
Allatheena yoofoona biʿahdi Allahi wala yanqudoona almeethaqa
Sũ ne waɗan da suke cikãwa da alkawarin Allah, kuma bã su warware alkawari.
-
وَٱلَّذِينَ يَصِلُونَ مَآ أَمَرَ ٱللَّهُ بِهِۦٓ أَن يُوصَلَ وَيَخْشَوْنَ رَبَّهُمْ وَيَخَافُونَ سُوٓءَ ٱلْحِسَابِ٢١
Waallatheena yasiloona ma amara Allahu bihi an yoosala wayakhshawna rabbahum wayakhafoona sooa alhisabi
Kuma sũ ne waɗan da suke sãdar da abin da Allah Ya yi umurni da shi dõmin a sãdar da shi kuma sunã tsõron Ubangijinsu, kuma sunã tsõron mummũnan bincike.
-
وَٱلَّذِينَ صَبَرُوا۟ ٱبْتِغَآءَ وَجْهِ رَبِّهِمْ وَأَقَامُوا۟ ٱلصَّلَوٰةَ وَأَنفَقُوا۟ مِمَّا رَزَقْنَـٰهُمْ سِرًّا وَعَلَانِيَةً وَيَدْرَءُونَ بِٱلْحَسَنَةِ ٱلسَّيِّئَةَ أُو۟لَـٰٓئِكَ لَهُمْ عُقْبَى ٱلدَّارِ٢٢
Waallatheena sabaroo ibtighaa wajhi rabbihim waaqamoo alssalata waanfaqoo mimma razaqnahum sirran waʿalaniyatan wayadraoona bialhasanati alssayyiata olaika lahum ʿuqba alddari
Kuma waɗanda suka yi haƙuri dõmin nẽman yardar Ubangijinsu, kuma suka tsayar da salla, kuma suka ciyar da abin da Muka azurta su da shi, a asirce da bayyane, kuma sunã tunkuɗe mummunan aiki da mai kyau. Waɗancan sunã da ãƙibar gida mai kyau.
-
جَنَّـٰتُ عَدْنٍ يَدْخُلُونَهَا وَمَن صَلَحَ مِنْ ءَابَآئِهِمْ وَأَزْوَٰجِهِمْ وَذُرِّيَّـٰتِهِمْ ۖ وَٱلْمَلَـٰٓئِكَةُ يَدْخُلُونَ عَلَيْهِم مِّن كُلِّ بَابٍ٢٣
Jannatu ʿadnin yadkhuloonaha waman salaha min abaihim waazwajihim wathurriyyatihim waalmalaikatu yadkhuloona ʿalayhim min kulli babin
Gidãjen Aljannar zama sunã shigarsu, sũ da waɗandasuka kyautatu daga iyãyensu, da mãtansu da zũriyarsu. Kuma malã'iku sunã shiga zuwa gunsu ta kõwace kõfa.
-
سَلَـٰمٌ عَلَيْكُم بِمَا صَبَرْتُمْ ۚ فَنِعْمَ عُقْبَى ٱلدَّارِ٢٤
Salamun ʿalaykum bima sabartum faniʿma ʿuqba alddari
"Aminci1 ya tabbata a kanku sabõda abin da kuka yi wa haƙuri. Sãbõda haka madalla da ni'imar ãƙibar gida."
Bayanai
[1] Sallamar malã'iku a kansu idan sun shiga a gare su, ita ce su ce musu: "Aminci ya tabbata a gare ku.". -
وَٱلَّذِينَ يَنقُضُونَ عَهْدَ ٱللَّهِ مِنۢ بَعْدِ مِيثَـٰقِهِۦ وَيَقْطَعُونَ مَآ أَمَرَ ٱللَّهُ بِهِۦٓ أَن يُوصَلَ وَيُفْسِدُونَ فِى ٱلْأَرْضِ ۙ أُو۟لَـٰٓئِكَ لَهُمُ ٱللَّعْنَةُ وَلَهُمْ سُوٓءُ ٱلدَّارِ٢٥
Waallatheena yanqudoona ʿahda Allahi min baʿdi meethaqihi wayaqtaʿoona ma amara Allahu bihi an yoosala wayufsidoona fee alardi olaika lahumu allaʿnatu walahum sooo alddari
Kuma waɗanda1 suka warware alkawarin Allah daga bãyan ƙulla shi, kuma sunã yanke abin da Allah Ya yi umurui da shi dõmin a sãdar da shi kuma sunã ɓarna a cikin ƙasar. Waɗancan sunã da wata la'ana, kuma sunã da mũnin gida.
Bayanai
[1] Bayãnin siffõfin waɗanda suka ƙi karɓar kiran Allah. Watau akasin waɗanda aka yi bayaninsu a bãyã. -
ٱللَّهُ يَبْسُطُ ٱلرِّزْقَ لِمَن يَشَآءُ وَيَقْدِرُ ۚ وَفَرِحُوا۟ بِٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا وَمَا ٱلْحَيَوٰةُ ٱلدُّنْيَا فِى ٱلْـَٔاخِرَةِ إِلَّا مَتَـٰعٌ٢٦
Allahu yabsutu alrrizqa liman yashao wayaqdiru wafarihoo bialhayati alddunya wama alhayatu alddunya fee alakhirati illa mataʿun
Allah ne Yake1 shimfiɗa arziki ga wanda Yake so, kuma Yanã ƙuntatãwa. Kuma sun yi farin ciki da rãyuwar dũniya, alhalikuwa rãyuwar dũniya ba ta zama ba dangane ga ta Lãhira fãce jin dãɗi kaɗan.
Bayanai
[1] Ta'aƙĩbi da tambĩhi ne da ƙãrin bayãni ga mai hankali dõmin ya zãbura ga karɓar kiran Allah. -
وَيَقُولُ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ لَوْلَآ أُنزِلَ عَلَيْهِ ءَايَةٌ مِّن رَّبِّهِۦ ۗ قُلْ إِنَّ ٱللَّهَ يُضِلُّ مَن يَشَآءُ وَيَهْدِىٓ إِلَيْهِ مَنْ أَنَابَ٢٧
Wayaqoolu allatheena kafaroo lawla onzila ʿalayhi ayatun min rabbihi qul inna Allaha yudillu man yashao wayahdee ilayhi man anaba
Kuma wanɗanda suka kãfirta, sunã cẽwa, "Don me ba a saukar da wata ãyã ba a kansa daga Ubangijinsa?" Ka ce: "Lalle ne Allah Yanã ɓatar da wanda Yake so kuma Yanã shiryar da wanda ya tũba zuwa gare shi."
-
ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَتَطْمَئِنُّ قُلُوبُهُم بِذِكْرِ ٱللَّهِ ۗ أَلَا بِذِكْرِ ٱللَّهِ تَطْمَئِنُّ ٱلْقُلُوبُ٢٨
Allatheena amanoo watatmainnu quloobuhum bithikri Allahi ala bithikri Allahi tatmainnu alquloobu
Waɗanda suka yi ĩmãni kuma zukãtansu sukan natsu da ambaton Allah. To, da ambaton Allah1 zukãta suke natsuwa.
Bayanai
[1] Ambaton Allah, shĩ ne bin hukunce-hukuncensa ga kõme. Umar ɗan Khattãb ya ce: "Mafificin ambaton Allah, shi ne wanda aka yi a wurin umurninsa ko haninsa. Wanda yake yin zikirin bãki ba da yanã aiki da hukunce-hukuncen Allah ba a cikin ibãdarsa da mu'amalarsa, to, shi mai izgili kawai ne da sũnan Ubangijinsa, ba mai yin zikiri ba ne.". -
ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ طُوبَىٰ لَهُمْ وَحُسْنُ مَـَٔابٍ٢٩
Allatheena amanoo waʿamiloo alssalihati tooba lahum wahusnu maabin
Waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata aiki nagari, farin ciki yã tabbata a gare su, da kyakkyawar makõma.
-
كَذَٰلِكَ أَرْسَلْنَـٰكَ فِىٓ أُمَّةٍ قَدْ خَلَتْ مِن قَبْلِهَآ أُمَمٌ لِّتَتْلُوَا۟ عَلَيْهِمُ ٱلَّذِىٓ أَوْحَيْنَآ إِلَيْكَ وَهُمْ يَكْفُرُونَ بِٱلرَّحْمَـٰنِ ۚ قُلْ هُوَ رَبِّى لَآ إِلَـٰهَ إِلَّا هُوَ عَلَيْهِ تَوَكَّلْتُ وَإِلَيْهِ مَتَابِ٣٠
Kathalika arsalnaka fee ommatin qad khalat min qabliha omamun litatluwa ʿalayhimu allathee awhayna ilayka wahum yakfuroona bialrrahmani qul huwa rabbee la ilaha illa huwa ʿalayhi tawakkaltu wailayhi matabi
Kamar wancan ne Muka aika ka a cikin al'umma wanda take waɗansu al'ummai sun shũɗe daga gabaninta, dõmin ka karanta musu abin da Muka yi wahayi zuwa a gare ka, alhãli kuwa sũ, sunãkãfirta da Rahaman.1 Ka ce: "Shi ne Ubangijĩna, bãbu abin, bautãwa fãce Shi, a gare Shi na dõgara, kuma zuwa gare Shi tũbãta take."
Bayanai
[1] Sũnan Allah Rahmãn, daga rahama, watau Mai Rahama wadda yake dukan alheri yanã shiga a cikin ma'anarta a wajen halitta da rãyuwa da bãyar da lãfiya da shiryarwa. Mafi girman nĩ'imarsa shĩ ne aikõwar Manzon Allah daga gare mu zuwa gare mu. Kãfirai ba su yi tunãni ba a kan waɗannan rahamõmi, balle su yi gõdiya, sabõda haka sai kãfirci suke yi. -
وَلَوْ أَنَّ قُرْءَانًا سُيِّرَتْ بِهِ ٱلْجِبَالُ أَوْ قُطِّعَتْ بِهِ ٱلْأَرْضُ أَوْ كُلِّمَ بِهِ ٱلْمَوْتَىٰ ۗ بَل لِّلَّهِ ٱلْأَمْرُ جَمِيعًا ۗ أَفَلَمْ يَا۟يْـَٔسِ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓا۟ أَن لَّوْ يَشَآءُ ٱللَّهُ لَهَدَى ٱلنَّاسَ جَمِيعًا ۗ وَلَا يَزَالُ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ تُصِيبُهُم بِمَا صَنَعُوا۟ قَارِعَةٌ أَوْ تَحُلُّ قَرِيبًا مِّن دَارِهِمْ حَتَّىٰ يَأْتِىَ وَعْدُ ٱللَّهِ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُخْلِفُ ٱلْمِيعَادَ٣١
Walaw anna quranan suyyirat bihi aljibalu aw quttiʿat bihi alardu aw kullima bihi almawta bal lillahi alamru jameeʿan afalam yayasi allatheena amanoo an law yashao Allahu lahada alnnasa jameeʿan wala yazalu allatheena kafaroo tuseebuhum bima sanaʿoo qariʿatun aw tahullu qareeban min darihim hatta yatiya waʿdu Allahi inna Allaha la yukhlifu almeeʿada
Kuma dã lalle an saukar da wani littafi abin karatu wanda ake tafiyar da duwãtsu game da shi, kõ kuma aka yanyanke ƙasa da shi, ko kuwa aka yi magana da matattu da shi (dã ba su yi ĩmãni ba). Ã'a ga Allah al'amari yake gabã ɗaya! Shin fa, waɗanda suka yi ĩmãni ba su yanke tsammãni ba da cẽwa da Allah Yã so, dã Yã shiryar da mutãne gabã ɗaya? Kuma waɗanda suka yi kãfirci ba zã su gushe ba wata masĩfa tanã samun su sabõda abin da suka aikata, kõ kuwa ka saukã1 kusa da gidãjẽnsu, har wa'adin Allah ya zo. Kuma lalle ne Allah bã ya sãɓã wa lõkacin alkawari.
Bayanai
[1] Annabi ya sauka kusa da gidãjen Ƙuraishãwa a rãnar bũɗe Makka. Kuma wannan hukunci yanã nan yanã aiki ga mãsu ƙiyayya da addini, kullum masĩfu sunã aukuwa a kansu har rãnar da Musulunci ya rinjãye su. -
وَلَقَدِ ٱسْتُهْزِئَ بِرُسُلٍ مِّن قَبْلِكَ فَأَمْلَيْتُ لِلَّذِينَ كَفَرُوا۟ ثُمَّ أَخَذْتُهُمْ ۖ فَكَيْفَ كَانَ عِقَابِ٣٢
Walaqadi istuhzia birusulin min qablika faamlaytu lillatheena kafaroo thumma akhathtuhum fakayfa kana ʿiqabi
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, an yi izgili da Manzanni kãfinka, sai Na yi jinkiri ga waɗanda suka kãfirta, sa'an nan Na kãma su. To, yãya uƙũbãta take?
-
أَفَمَنْ هُوَ قَآئِمٌ عَلَىٰ كُلِّ نَفْسٍۭ بِمَا كَسَبَتْ ۗ وَجَعَلُوا۟ لِلَّهِ شُرَكَآءَ قُلْ سَمُّوهُمْ ۚ أَمْ تُنَبِّـُٔونَهُۥ بِمَا لَا يَعْلَمُ فِى ٱلْأَرْضِ أَم بِظَـٰهِرٍ مِّنَ ٱلْقَوْلِ ۗ بَلْ زُيِّنَ لِلَّذِينَ كَفَرُوا۟ مَكْرُهُمْ وَصُدُّوا۟ عَنِ ٱلسَّبِيلِ ۗ وَمَن يُضْلِلِ ٱللَّهُ فَمَا لَهُۥ مِنْ هَادٍ٣٣
Afaman huwa qaimun ʿala kulli nafsin bima kasabat wajaʿaloo lillahi shurakaa qul sammoohum am tunabbioonahu bima la yaʿlamu fee alardi am bithahirin mina alqawli bal zuyyina lillatheena kafaroo makruhum wasuddoo ʿani alssabeeli waman yudlili Allahu fama lahu min hadin
Shin fa, wanda shĩ Yake tsaye a kan kõwane rai game da abin da ya tanada (zai zama kamar wanda ba haka ba)? Kuma suka sanya abõkan tãrayya ga Allah! Ka ce: "Ku ambaci sũnãyensu."Ko kunã bai wa Allah lãbãri ne game da abin da bai sani ba a cikin ƙasa? Kõ da bayyananniyar magana kuke yin shirka, (banda a cikin zũciya)? Ã'a, an dai ƙawãta wa waɗanda suka kafirta mãkircinsu kuma an kange su daga hanya. Kuma wanda Allah Ya ɓatar to, bãbu wani mai shiryarwa a gare shi!"
-
لَّهُمْ عَذَابٌ فِى ٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا ۖ وَلَعَذَابُ ٱلْـَٔاخِرَةِ أَشَقُّ ۖ وَمَا لَهُم مِّنَ ٱللَّهِ مِن وَاقٍ٣٤
Lahum ʿathabun fee alhayati alddunya walaʿathabu alakhirati ashaqqu wama lahum mina Allahi min waqin
Sunã da wata azãba a cikin rãyuwar dũniya, kuma haƙĩƙa azãbar Lãhira ce mafi tsanani kuma bãbu wani mai tsare su daga Allah.
-
۞ مَّثَلُ ٱلْجَنَّةِ ٱلَّتِى وُعِدَ ٱلْمُتَّقُونَ ۖ تَجْرِى مِن تَحْتِهَا ٱلْأَنْهَـٰرُ ۖ أُكُلُهَا دَآئِمٌ وَظِلُّهَا ۚ تِلْكَ عُقْبَى ٱلَّذِينَ ٱتَّقَوا۟ ۖ وَّعُقْبَى ٱلْكَـٰفِرِينَ ٱلنَّارُ٣٥
Mathalu aljannati allatee wuʿida almuttaqoona tajree min tahtiha alanharu okuluha daimun wathilluha tilka ʿuqba allatheena ittaqaw waʿuqba alkafireena alnnaru
Misãlin Aljanna wadda aka yi alkawarinta ga mãsu taƙawa, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinta. Abincinta yana madawwami da inuwarta. Waccan ce ãƙibar waɗanda suka yi taƙawa, kuma ãƙibar kãfirai, ita ce wuta,
-
وَٱلَّذِينَ ءَاتَيْنَـٰهُمُ ٱلْكِتَـٰبَ يَفْرَحُونَ بِمَآ أُنزِلَ إِلَيْكَ ۖ وَمِنَ ٱلْأَحْزَابِ مَن يُنكِرُ بَعْضَهُۥ ۚ قُلْ إِنَّمَآ أُمِرْتُ أَنْ أَعْبُدَ ٱللَّهَ وَلَآ أُشْرِكَ بِهِۦٓ ۚ إِلَيْهِ أَدْعُوا۟ وَإِلَيْهِ مَـَٔابِ٣٦
Waallatheena ataynahumu alkitaba yafrahoona bima onzila ilayka wamina alahzabi man yunkiru baʿdahu qul innama omirtu an aʿbuda Allaha wala oshrika bihi ilayhi adʿoo wailayhi maabi
Kuma waɗanda Muka bã su Littãfi sunã farin ciki da abin da aka saukar zuwa gare ka, kuma daga ƙungiyõyi akwai mai musun sãshensa. Ka ce: "Abin sani kawai, an umurce ni da in bauta wa Allah kuma kada in yi shirka da Shi, zuwa gare Shi nake kira, kuma zuwa gare Shi makõmata take."
-
وَكَذَٰلِكَ أَنزَلْنَـٰهُ حُكْمًا عَرَبِيًّا ۚ وَلَئِنِ ٱتَّبَعْتَ أَهْوَآءَهُم بَعْدَ مَا جَآءَكَ مِنَ ٱلْعِلْمِ مَا لَكَ مِنَ ٱللَّهِ مِن وَلِىٍّ وَلَا وَاقٍ٣٧
Wakathalika anzalnahu hukman ʿarabiyyan walaini ittabaʿta ahwaahum baʿda ma jaaka mina alʿilmi ma laka mina Allahi min waliyyin wala waqin
Kuma kamar wancan ne Muka saukar da shi1, Hukunci a cikin Lãrabci. Kuma lalle ne idan kã bi son zuciyõyinsu a bãyan abin da ya zo maka na ilmi, bãbu wani masõyi a gare ka mai kãre ka daga Allah, kuma bãbu matsari.
Bayanai
[1] Kamar yadda littattafan farko suke, haka Alƙur'ãni yake daga Allah, sai dai shi Alƙur'ãni an saukar da shi a cikin Lãrabci. -
وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا رُسُلًا مِّن قَبْلِكَ وَجَعَلْنَا لَهُمْ أَزْوَٰجًا وَذُرِّيَّةً ۚ وَمَا كَانَ لِرَسُولٍ أَن يَأْتِىَ بِـَٔايَةٍ إِلَّا بِإِذْنِ ٱللَّهِ ۗ لِكُلِّ أَجَلٍ كِتَابٌ٣٨
Walaqad arsalna rusulan min qablika wajaʿalna lahum azwajan wathurriyyatan wama kana lirasoolin an yatiya biayatin illa biithni Allahi likulli ajalin kitabun
Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun aika waɗansu manzanni, daga gabãninka, kuma Muka sanya mãtan aure a gare su da zũriyya, kuma ba ya kasancẽwa ga wani Manzo ya zo da wata ãyã, sai da iznin Allah. Ga kõwane ajali1 akwai littãfi.
Bayanai
[1] Aikõwar Manzanni da littattafai ba ya hana Allah Ya aiko wani Manzo daga bãya da wani littãfi wanda ya shãfe abin da yake cikin littattafan farko. Allah Yã tabbatar da abin da yake so na hukunce-hukuncen da suka gabãta dõmin dõgewar aikinsu ga mutãne har yanzu, kuma Ya shãfe abin da yake so sabõda amfãninsu da hukuncinsu yã shige, sabõda wata hikima da Allah Ya sani amma asalin littattãfan duka wanda bã zai canja ba a cikin sanin Allah, yanã wurinsa.". -
يَمْحُوا۟ ٱللَّهُ مَا يَشَآءُ وَيُثْبِتُ ۖ وَعِندَهُۥٓ أُمُّ ٱلْكِتَـٰبِ٣٩
Yamhoo Allahu ma yashao wayuthbitu waʿindahu ommu alkitabi
Allah Yanã shafe abin da Yake so, kuma Yanã tabbatarwa kuma a wurinsa asalin Littãfin yake.
-
وَإِن مَّا نُرِيَنَّكَ بَعْضَ ٱلَّذِى نَعِدُهُمْ أَوْ نَتَوَفَّيَنَّكَ فَإِنَّمَا عَلَيْكَ ٱلْبَلَـٰغُ وَعَلَيْنَا ٱلْحِسَابُ٤٠
Wain ma nuriyannaka baʿda allathee naʿiduhum aw natawaffayannaka fainnama ʿalayka albalaghu waʿalayna alhisabu
Kuma imma lalle Mu nũna1 maka sãshen abin da Muke yi musu wa'adi, kõ kuwa lalle Mu karɓi ranka to abin sani kawai iyarwa ce a kanka, kuma hisãbi yana gare Mu.
Bayanai
[1] Idan Mun so Mu yi musu azãba a gaban idonka zã Mu yi musu, kuma idan Mun so Mu jinkirta musu har a bãyan ka mutu, wannan bã aikinka ba ne, Nãmu ne. Abin da yake aikinka shĩ ne iyar da manzanci kawai. Yin hisãbi a kansu alhakin Allah ɗai ne. -
أَوَلَمْ يَرَوْا۟ أَنَّا نَأْتِى ٱلْأَرْضَ نَنقُصُهَا مِنْ أَطْرَافِهَا ۚ وَٱللَّهُ يَحْكُمُ لَا مُعَقِّبَ لِحُكْمِهِۦ ۚ وَهُوَ سَرِيعُ ٱلْحِسَابِ٤١
Awalam yaraw anna natee alarda nanqusuha min atrafiha waAllahu yahkumu la muʿaqqiba lihukmihi wahuwa sareeʿu alhisabi
Shin, kuma ba su gani ba cẽwa lalle ne, Muna jẽ wa ƙasar (su), Munã rage ta daga gẽfunanta? Kuma Allah ne Yake yin hukuncinsa. Babu mai bincike ga hukuncinsa. Kuma shĩ ne Mai gaggãwar sakamako.1
Bayanai
[1] Gaggãwar sakamako ga wanda ya ƙi bin umurnin Allah wanda Annabinsa ya iyar zuwa gare shi. Asalin hisãbi, shine bincike dõmin a sãmi abin da aka yi na alhħri kõ na sharri amma abin da ake nufi a nan maƙasũdin bincike shĩ ne sakamako da alhħri kõ da azãba, gwargwadon nufinSa. -
وَقَدْ مَكَرَ ٱلَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ فَلِلَّهِ ٱلْمَكْرُ جَمِيعًا ۖ يَعْلَمُ مَا تَكْسِبُ كُلُّ نَفْسٍ ۗ وَسَيَعْلَمُ ٱلْكُفَّـٰرُ لِمَنْ عُقْبَى ٱلدَّارِ٤٢
Waqad makara allatheena min qablihim falillahi almakru jameeʿan yaʿlamu ma taksibu kullu nafsin wasayaʿlamu alkuffaru liman ʿuqba alddari
Kuma lalle ne waɗanda suke a gabãninsu sun yi mãkirci. To, ga Allah mãkircin yake gabã ɗaya. Ya san abin da kõwane rai yake tãnada. Kuma kãfirai zã su sani, ga wane ãƙibar gida take.
-
وَيَقُولُ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ لَسْتَ مُرْسَلًا ۚ قُلْ كَفَىٰ بِٱللَّهِ شَهِيدًۢا بَيْنِى وَبَيْنَكُمْ وَمَنْ عِندَهُۥ عِلْمُ ٱلْكِتَـٰبِ٤٣
Wayaqoolu allatheena kafaroo lasta mursalan qul kafa biAllahi shaheedan baynee wabaynakum waman ʿindahu ʿilmu alkitabi
Kuma waɗanda suka kãfirta sunã cẽwa: "Ba a aiko ka ba." Ka ce, "Allah Yã isa zama shaida a tsakãnina da tsakãninku da wanda yake a wurinsa akwai ilmin1 Littãfi."
Bayanai
[1] Allah Yã isa zama shaida, haka wanda yake a kan wani ilmi daga Allah kamar Yahudu da Nasãra sunã isa zama shaida a tsakãnĩna da ku a kan gaskiyar da'awã ta cewa nĩ abin aikõwa ne daga Allah zuwa gare ku dõmin akwai wannan magana a cikin littattafanku.
Tambayoyin da ake yawan yi
Mece ce ma’anar sunan Suratul Ra’ad?
Ma’anar Ra’ad ita ce “Tsawa”.
Suratul Ra’ad tana cikin juz’i na nawa?
Suratul Ra’ad tana cikin juz’i na 13.
Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Ra’ad?
Suratul Ra’ad tana da ayoyi 43.
Suratul Ra’ad Makkiya ce ko Madaniya?
Suratul Ra’ad sura ce Madaniya.
Suratul Ra’ad ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?
Ita ce sura ta 13 a cikin Alƙur’ani.
Majiyoyi
- Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
- Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
- Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
- Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
- Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
- Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.
Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.