سورة الحجر

Suratul Hijr da fassarar Hausa

Ƙasa mai duwatsu

Mushafi

Mishary Rashid AlafasySauke MP3Sauke PDF

Suratul Hijr (الحجر) ita ce sura ta 15 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 99. Ma’anar sunanta ita ce “Ƙasa mai duwatsu”. Sura ce Makkiya, wadda ta sauka a Makka kafin Hijira, kuma tana cikin juz’i na 14.

A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Hijr gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.

Suratul Hijr cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. الٓر ۚ تِلْكَ ءَايَـٰتُ ٱلْكِتَـٰبِ وَقُرْءَانٍ مُّبِينٍ۝١

    Aliflamra tilka ayatu alkitabi waquranin mubeenin

    A. L̃.R. Waɗan can ãyoyin littãfi ne da abin karantãwa mai bayyanãwa.

  2. رُّبَمَا يَوَدُّ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ لَوْ كَانُوا۟ مُسْلِمِينَ۝٢

    Rubama yawaddu allatheena kafaroo law kanoo muslimeena

    Da yawa waɗanda suka kãfirta suke gũrin dã dai sun kasance Musulmi.1

    Bayanai
    [1] Kõwane kãfiri yanã gũrin yã zama Musulmi dõmin abin da yake gani na shiriya da ladubban Musulunci, waɗanda ya tabbata bãbu zama lãfiya ga mutum fãce idan yã sãme su, amma shaiɗan yanã hana shi musulunta sabõda waɗansu dalĩlai da yake sanyãwa a ganinsa.
  3. ذَرْهُمْ يَأْكُلُوا۟ وَيَتَمَتَّعُوا۟ وَيُلْهِهِمُ ٱلْأَمَلُ ۖ فَسَوْفَ يَعْلَمُونَ۝٣

    Tharhum yakuloo wayatamattaʿoo wayulhihimu alamalu fasawfa yaʿlamoona

    Ka bar su su ci kuma su ji dãdi, kuma gũri ya shagaltar da su, sa'an nan da sannu zã su sani.

  4. وَمَآ أَهْلَكْنَا مِن قَرْيَةٍ إِلَّا وَلَهَا كِتَابٌ مَّعْلُومٌ۝٤

    Wama ahlakna min qaryatin illa walaha kitabun maʿloomun

    Kuma ba Mu halakar da wata alƙarya ba fãce tanã da littafi sananne.

  5. مَّا تَسْبِقُ مِنْ أُمَّةٍ أَجَلَهَا وَمَا يَسْتَـْٔخِرُونَ۝٥

    Ma tasbiqu min ommatin ajalaha wama yastakhiroona

    Wata al'umma bã ta gabãtar ajalinta, kuma bã zã su jinkirta ba.

  6. وَقَالُوا۟ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِى نُزِّلَ عَلَيْهِ ٱلذِّكْرُ إِنَّكَ لَمَجْنُونٌ۝٦

    Waqaloo ya ayyuha allathee nuzzila ʿalayhi alththikru innaka lamajnoonun

    Suka ce: "Yã kai wanda aka saukar da Ambato (Alƙur'ãni) a kansa! Lalle ne kai, haƙĩƙa, mahaukaci ne."

  7. لَّوْ مَا تَأْتِينَا بِٱلْمَلَـٰٓئِكَةِ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّـٰدِقِينَ۝٧

    Law ma tateena bialmalaikati in kunta mina alssadiqeena

    "Dõmin me bã zã ka zo mana da malã'ĩku ba idan ka kasance daga mãsu gaskiya?"

  8. مَا نُنَزِّلُ ٱلْمَلَـٰٓئِكَةَ إِلَّا بِٱلْحَقِّ وَمَا كَانُوٓا۟ إِذًا مُّنظَرِينَ۝٨

    Ma nunazzilu almalaikata illa bialhaqqi wama kanoo ithan munthareena

    Bã Mu sassaukar da malã'iku fãce da gaskiya,1 bã zã su kasance, a wannan lõkacin, waɗanda ake yi wa jinkĩri ba.

    Bayanai
    [1] Gaskiya a nan anã nufin azãba dõmin zuwanta tabbatacce ne. Dukan abin da yake tabbatacce shĩ ne haƙƙun, watau gaskiya.
  9. إِنَّا نَحْنُ نَزَّلْنَا ٱلذِّكْرَ وَإِنَّا لَهُۥ لَحَـٰفِظُونَ۝٩

    Inna nahnu nazzalna alththikra wainna lahu lahafithoona

    Lalle Mũ ne, Muka saukar da Ambato (Alƙur'ãni), kuma lale Mũ, haƙĩƙa, Mãsu kiyayẽwane gare shi.

  10. وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا مِن قَبْلِكَ فِى شِيَعِ ٱلْأَوَّلِينَ۝١٠

    Walaqad arsalna min qablika fee shiyaʿi alawwaleena

    Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika Manzanni a cikin ƙungiyõyin farko, gabãnin ka.

  11. وَمَا يَأْتِيهِم مِّن رَّسُولٍ إِلَّا كَانُوا۟ بِهِۦ يَسْتَهْزِءُونَ۝١١

    Wama yateehim min rasoolin illa kanoo bihi yastahzioona

    Kuma wani Manzo bã ya zuwa gare su fãce sun kasance sunã mãsu, izgili a gare shi.

  12. كَذَٰلِكَ نَسْلُكُهُۥ فِى قُلُوبِ ٱلْمُجْرِمِينَ۝١٢

    Kathalika naslukuhu fee quloobi almujrimeena

    Kamar wancan ne Muke shigar da shi1 a cikin zukãtan mãsu laifi.

    Bayanai
    [1] Shirki da kãfirci da ƙaryatãwa, su duka izgili ne da addini.
  13. لَا يُؤْمِنُونَ بِهِۦ ۖ وَقَدْ خَلَتْ سُنَّةُ ٱلْأَوَّلِينَ۝١٣

    La yuminoona bihi waqad khalat sunnatu alawwaleena

    Bã su yin ĩmãni da shi,(4( kuma haƙĩƙa, hanyar mutãnen farko ta shige1 .

    Bayanai
    [1] Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Hanyar mutãnen farko ta ƙaryata Manzanni har a lõkacin da Allah zai halaka su da azãbarsa.
  14. وَلَوْ فَتَحْنَا عَلَيْهِم بَابًا مِّنَ ٱلسَّمَآءِ فَظَلُّوا۟ فِيهِ يَعْرُجُونَ۝١٤

    Walaw fatahna ʿalayhim baban mina alssamai fathalloo feehi yaʿrujoona

    Kuma dã Mun bũɗe wata ƙõfa daga sama a kansu har suka wuni a ciki sunã tãkãwa.

  15. لَقَالُوٓا۟ إِنَّمَا سُكِّرَتْ أَبْصَـٰرُنَا بَلْ نَحْنُ قَوْمٌ مَّسْحُورُونَ۝١٥

    Laqaloo innama sukkirat absaruna bal nahnu qawmun mashooroona

    Lalle ne dã sun ce: "Abin sani kawai, an rufe idãnuwanmu ne. Ã'a, mũ mutãne ne waɗanda aka sihirce."

  16. وَلَقَدْ جَعَلْنَا فِى ٱلسَّمَآءِ بُرُوجًا وَزَيَّنَّـٰهَا لِلنَّـٰظِرِينَ۝١٦

    Walaqad jaʿalna fee alssamai buroojan wazayyannaha lilnnathireena

    Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun sanya waɗansu masaukai a, cikin sama, kuma Muka ƙawãta ta ga masu kallo.

  17. وَحَفِظْنَـٰهَا مِن كُلِّ شَيْطَـٰنٍ رَّجِيمٍ۝١٧

    Wahafithnaha min kulli shaytanin rajeemin

    Kuma Muka kiyãye ta daga dukan Shaiɗani wanda ake jĩfa.

  18. إِلَّا مَنِ ٱسْتَرَقَ ٱلسَّمْعَ فَأَتْبَعَهُۥ شِهَابٌ مُّبِينٌ۝١٨

    Illa mani istaraqa alssamʿa faatbaʿahu shihabun mubeenun

    Fãce wanda ya sãci saurãre sai wutar yũlã bayyananniya ta bĩ shi.

  19. وَٱلْأَرْضَ مَدَدْنَـٰهَا وَأَلْقَيْنَا فِيهَا رَوَٰسِىَ وَأَنۢبَتْنَا فِيهَا مِن كُلِّ شَىْءٍ مَّوْزُونٍ۝١٩

    Waalarda madadnaha waalqayna feeha rawasiya waanbatna feeha min kulli shayin mawzoonin

    Kuma ƙasa Mun mĩkẽ ta kuma Mun jẽfa duwãtsu tabbatattu a cikinta kuma Mun tsirar a cikinta, daga dukan abu wanda ake aunãwa da sikẽli.

  20. وَجَعَلْنَا لَكُمْ فِيهَا مَعَـٰيِشَ وَمَن لَّسْتُمْ لَهُۥ بِرَٰزِقِينَ۝٢٠

    Wajaʿalna lakum feeha maʿayisha waman lastum lahu biraziqeena

    Kuma Muka sanyã muku, a cikinta, abũbuwan rãyuwã1 da wanda ba ku zamã mãsu ciyarwa gare shi ba.

    Bayanai
    [1] Muka sanya muku abũbuwan rãyuwa a cikinta, kuma Muka mallaka muku bãyi waɗanda suke bã kũ ne kuke ciyar da su ba, Mũ ne ke ciyar da su game da ku duka. Wãtau aza abũbuwa a kan ma'auni shĩ ne maslaha rashin yarda da tsaron ma'aunin nan shĩ ne izgili.
  21. وَإِن مِّن شَىْءٍ إِلَّا عِندَنَا خَزَآئِنُهُۥ وَمَا نُنَزِّلُهُۥٓ إِلَّا بِقَدَرٍ مَّعْلُومٍ۝٢١

    Wain min shayin illa ʿindana khazainuhu wama nunazziluhu illa biqadarin maʿloomin

    Kuma bãbu wani abu fãce a wurinMu, akwai taskõkĩnsa kuma ba Mu saukar da shi ba fãce kan gwargwado sananne.

  22. وَأَرْسَلْنَا ٱلرِّيَـٰحَ لَوَٰقِحَ فَأَنزَلْنَا مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءً فَأَسْقَيْنَـٰكُمُوهُ وَمَآ أَنتُمْ لَهُۥ بِخَـٰزِنِينَ۝٢٢

    Waarsalna alrriyaha lawaqiha faanzalna mina alssamai maan faasqaynakumoohu wama antum lahu bikhazineena

    Kuma Muka aika iskõki mãsu barbarar jũna sa'an nan Muka saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Muka shãyar da ku shi, kuma ba ku zama mãsu taskacẽwa a gare shi ba.

  23. وَإِنَّا لَنَحْنُ نُحْىِۦ وَنُمِيتُ وَنَحْنُ ٱلْوَٰرِثُونَ۝٢٣

    Wainna lanahnu nuhyee wanumeetu wanahnu alwarithoona

    Kuma lalle ne Mu Muke rãyarwa, kuma Muke kashẽwa kuma Mũ ne magada.

  24. وَلَقَدْ عَلِمْنَا ٱلْمُسْتَقْدِمِينَ مِنكُمْ وَلَقَدْ عَلِمْنَا ٱلْمُسْتَـْٔخِرِينَ۝٢٤

    Walaqad ʿalimna almustaqdimeena minkum walaqad ʿalimna almustakhireena

    Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun san mãsu gabãta daga cikinku, kuma Mun san mãsu jinkiri.

  25. وَإِنَّ رَبَّكَ هُوَ يَحْشُرُهُمْ ۚ إِنَّهُۥ حَكِيمٌ عَلِيمٌ۝٢٥

    Wainna rabbaka huwa yahshuruhum innahu hakeemun ʿaleemun

    Kuma lalle ne Ubangijinka Shĩ ne Yake tãra su, lalle Shĩ ne Mai hikima, Masani.

  26. وَلَقَدْ خَلَقْنَا ٱلْإِنسَـٰنَ مِن صَلْصَـٰلٍ مِّنْ حَمَإٍ مَّسْنُونٍ۝٢٦

    Walaqad khalaqna alinsana min salsalin min hamain masnoonin

    Kuma lalle ne Mun halicci mutum daga ƙeƙasasshiyar lãka, daga baƙin yumɓu wanda ya canja.

  27. وَٱلْجَآنَّ خَلَقْنَـٰهُ مِن قَبْلُ مِن نَّارِ ٱلسَّمُومِ۝٢٧

    Waaljanna khalaqnahu min qablu min nari alssamoomi

    Kuma Aljani Mun haliccẽ shi daga gabãni, daga wutar1 iskar zafi.

    Bayanai
    [1] Halittar Ãdamu daga yumbu kekasasshe, ya fi daraja bisa halittar Shaiɗan daga harshen wuta, dõmin wuta tanã nũni ga sassabcin hankali da rashin natsuwa.
  28. وَإِذْ قَالَ رَبُّكَ لِلْمَلَـٰٓئِكَةِ إِنِّى خَـٰلِقٌۢ بَشَرًا مِّن صَلْصَـٰلٍ مِّنْ حَمَإٍ مَّسْنُونٍ۝٢٨

    Waith qala rabbuka lilmalaikati innee khaliqun basharan min salsalin min hamain masnoonin

    Kuma a lõkacin da Ubangijinka ya ce wa malã'iku: "Lalle Nĩ mai halittar wani jiki ne daga ƙẽƙasasshen yumɓu wanda ya canja."

  29. فَإِذَا سَوَّيْتُهُۥ وَنَفَخْتُ فِيهِ مِن رُّوحِى فَقَعُوا۟ لَهُۥ سَـٰجِدِينَ۝٢٩

    Faitha sawwaytuhu wanafakhtu feehi min roohee faqaʿoo lahu sajideena

    "To idan Na daidaitã shi kuma Na hũra daga RũhĩNa1 a cikinsa, to, ku fãɗi a gare shi, kunã mãsu yin sujada."

    Bayanai
    [1] Wannan ya nũnã Ãdamu an yi halittarsa ne da lãka da Rũhi daga Allah kamar yadda aka halitta Isã, amincin Allah ya tabbata a gare shi. Sabõda haka halittar Ãdamu ta fi zama abin mãmãki daga halittar Ĩsã, dõmin Ĩsã asali guda kawai ya rasa daga halittar ɗiyan Adam ta al'ãda, amma halittar Ãdamu tã rasa dukan asalan biyu na uwa da na uba. Haka kuma halittar Hawwã'u, matar Ãdamu tã fi ta Ĩsã ban mãmãki dõmin rashin asalin uwa da ta yi inda ɗã yake ɗaukar lõkacin sũrantãwa, ya fi ban mãmãki daga rashin asalin uba.
  30. فَسَجَدَ ٱلْمَلَـٰٓئِكَةُ كُلُّهُمْ أَجْمَعُونَ۝٣٠

    Fasajada almalaikatu kulluhum ajmaʿoona

    Sai malã'iku suka yi sujada dukkansu gaba ɗaya.

  31. إِلَّآ إِبْلِيسَ أَبَىٰٓ أَن يَكُونَ مَعَ ٱلسَّـٰجِدِينَ۝٣١

    Illa ibleesa aba an yakoona maʿa alssajideena

    Fãce Iblĩs, ya ƙi kasancẽwa daga mãsu yin sujadar.

  32. قَالَ يَـٰٓإِبْلِيسُ مَا لَكَ أَلَّا تَكُونَ مَعَ ٱلسَّـٰجِدِينَ۝٣٢

    Qala ya ibleesu ma laka alla takoona maʿa alssajideena

    Ya ce: "Yã Iblĩs mẽne ne a gare ka, ba ka kasance tãre da mãsu yin sujuda ba?"

  33. قَالَ لَمْ أَكُن لِّأَسْجُدَ لِبَشَرٍ خَلَقْتَهُۥ مِن صَلْصَـٰلٍ مِّنْ حَمَإٍ مَّسْنُونٍ۝٣٣

    Qala lam akun liasjuda libasharin khalaqtahu min salsalin min hamain masnoonin

    Ya ce: "Ban kasance inã yin sujada ba ga mutum wanda Ka halicce shi daga bũsasshen yumɓun lãka wadda ta canja."

  34. قَالَ فَٱخْرُجْ مِنْهَا فَإِنَّكَ رَجِيمٌ۝٣٤

    Qala faokhruj minha fainnaka rajeemun

    Ya ce: "To, ka fita daga gare ta, dõmin lalle kai abin jĩfa ne."

  35. وَإِنَّ عَلَيْكَ ٱللَّعْنَةَ إِلَىٰ يَوْمِ ٱلدِّينِ۝٣٥

    Wainna ʿalayka allaʿnata ila yawmi alddeeni

    "Kuma lalle ne akwai la'ana a kanka har ya zuwa rãnar sakamako."

  36. قَالَ رَبِّ فَأَنظِرْنِىٓ إِلَىٰ يَوْمِ يُبْعَثُونَ۝٣٦

    Qala rabbi faanthirnee ila yawmi yubʿathoona

    Ya ce: "Yã Ubangjĩna! Sai Ka yi mini jinkiri zuwa rãnar da ake tãshin su."

  37. قَالَ فَإِنَّكَ مِنَ ٱلْمُنظَرِينَ۝٣٧

    Qala fainnaka mina almunthareena

    Ya ce: "To, lalle ne kanã daga waɗanda ake yi wa jinkiri."

  38. إِلَىٰ يَوْمِ ٱلْوَقْتِ ٱلْمَعْلُومِ۝٣٨

    Ila yawmi alwaqti almaʿloomi

    "Zuwa ga Yinin Lõkacin nan sanan ne."

  39. قَالَ رَبِّ بِمَآ أَغْوَيْتَنِى لَأُزَيِّنَنَّ لَهُمْ فِى ٱلْأَرْضِ وَلَأُغْوِيَنَّهُمْ أَجْمَعِينَ۝٣٩

    Qala rabbi bima aghwaytanee laozayyinanna lahum fee alardi walaoghwiyannahum ajmaʿeena

    Ya ce: "Yã Ubangijina! Inã rantsuwa da abin da Ka ɓatar da ni da shi, haƙĩƙa inã ƙawãta musu (rãyuwa) a cikin ƙasã kuma haƙĩƙa inã ɓatar da su gabã ɗaya."

  40. إِلَّا عِبَادَكَ مِنْهُمُ ٱلْمُخْلَصِينَ۝٤٠

    Illa ʿibadaka minhumu almukhlaseena

    "Fãce bãyinKa daga gare su, waɗanda Ka tsarkake."

  41. قَالَ هَـٰذَا صِرَٰطٌ عَلَىَّ مُسْتَقِيمٌ۝٤١

    Qala hatha siratun ʿalayya mustaqeemun

    Ya ce: "Wannan tafarki ne a gare Ni, madaidaici."

  42. إِنَّ عِبَادِى لَيْسَ لَكَ عَلَيْهِمْ سُلْطَـٰنٌ إِلَّا مَنِ ٱتَّبَعَكَ مِنَ ٱلْغَاوِينَ۝٤٢

    Inna ʿibadee laysa laka ʿalayhim sultanun illa mani ittabaʿaka mina alghaweena

    "Lalle ne bãyĩNa, bã ka da ĩkõ a kansu, fãce wanda ya bĩ ka daga ɓatattu."

  43. وَإِنَّ جَهَنَّمَ لَمَوْعِدُهُمْ أَجْمَعِينَ۝٤٣

    Wainna jahannama lamawʿiduhum ajmaʿeena

    Kuma lalle Jahannama ce haƙĩƙa, ma'akawartarsu gabã ɗaya.

  44. لَهَا سَبْعَةُ أَبْوَٰبٍ لِّكُلِّ بَابٍ مِّنْهُمْ جُزْءٌ مَّقْسُومٌ۝٤٤

    Laha sabʿatu abwabin likulli babin minhum juzon maqsoomun

    Tanã da ƙõfõfi bakwai,1 ga kõwace ƙõfa akwai wani juz'i daga gare su rababbe.

    Bayanai
    [1] Ƙõfofin Jahannama bakwai ne, watau ɗabaƙõƙinta ta farko ita ce Jahannama, sa'an nan Lazza, sa'an nan Alhuɗama sa'an nan Assa'ĩra, sa'an nan saƙar, sa'an nan Aljahĩm, sa'an nan Alhãwiya. Kõwace ɗabaƙa tanã da juz'i sananne, watau ƙõfa ga Yahudu, wata ga Nasãra, wata Saba'ãwa, wata ga Majũsãwa, wata ga Mushirikai, wata ga munãfukai, wata ga Musulmi waɗanda aka yi musu hushi (mummunan aiki). Anã fatan fita ga mãsu tauhĩdi daga gare ta. Ba a fatan kõme ga sauran, sunã dawwama a cikinta har abada.
  45. إِنَّ ٱلْمُتَّقِينَ فِى جَنَّـٰتٍ وَعُيُونٍ۝٤٥

    Inna almuttaqeena fee jannatin waʿuyoonin

    Lalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna mai idandunan ruwa.

  46. ٱدْخُلُوهَا بِسَلَـٰمٍ ءَامِنِينَ۝٤٦

    Odkhulooha bisalamin amineena

    "Ku shigẽ ta da aminci, kunã amintattu."

  47. وَنَزَعْنَا مَا فِى صُدُورِهِم مِّنْ غِلٍّ إِخْوَٰنًا عَلَىٰ سُرُرٍ مُّتَقَـٰبِلِينَ۝٤٧

    Wanazaʿna ma fee sudoorihim min ghillin ikhwanan ʿala sururin mutaqabileena

    Kuma Muka ɗẽbe abinda ke a cikin zukãtansu na daga ƙullin zũci, suka zama 'yan'uwa a kan gadãje, sunã mãsu fuskantar junã.

  48. لَا يَمَسُّهُمْ فِيهَا نَصَبٌ وَمَا هُم مِّنْهَا بِمُخْرَجِينَ۝٤٨

    La yamassuhum feeha nasabun wama hum minha bimukhrajeena

    Wata wahala bã zã ta shãfe su bã a cikinta kuma ba su zama mãsu fita daga, cikin ta ba.

  49. ۞ نَبِّئْ عِبَادِىٓ أَنِّىٓ أَنَا ٱلْغَفُورُ ٱلرَّحِيمُ۝٤٩

    Nabbi ʿibadee annee ana alghafooru alrraheemu

    Ka bai wa bãyiNa lãbari cẽwa lalle ne Ni, Mai gãfarane, Mai jin ƙai.

  50. وَأَنَّ عَذَابِى هُوَ ٱلْعَذَابُ ٱلْأَلِيمُ۝٥٠

    Wa anna ʿathabee huwa alʿathabu alaleemu

    Kuma azãbãTa ita ce Azãba mai raɗaɗi.

  51. وَنَبِّئْهُمْ عَن ضَيْفِ إِبْرَٰهِيمَ۝٥١

    Wanabbihum ʿan dayfi ibraheema

    Kuma ka bã su lãbãrin bãƙin Ibrãhĩm.

  52. إِذْ دَخَلُوا۟ عَلَيْهِ فَقَالُوا۟ سَلَـٰمًا قَالَ إِنَّا مِنكُمْ وَجِلُونَ۝٥٢

    Ith dakhaloo ʿalayhi faqaloo salaman qala inna minkum wajiloona

    A lõkacin da suka shiga gunsa, sai suka ce: "Sallama." Ya ce: "Lalle mũ, daga gare ku, mãsu firgita ne."

  53. قَالُوا۟ لَا تَوْجَلْ إِنَّا نُبَشِّرُكَ بِغُلَـٰمٍ عَلِيمٍ۝٥٣

    Qaloo la tawjal inna nubashshiruka bighulamin ʿaleemin

    Suka ce: "Kada ka firgita. Lalle ne mũ, munã yi makabushãra game da wani yãro masani."

  54. قَالَ أَبَشَّرْتُمُونِى عَلَىٰٓ أَن مَّسَّنِىَ ٱلْكِبَرُ فَبِمَ تُبَشِّرُونَ۝٥٤

    Qala abashshartumoonee ʿala an massaniya alkibaru fabima tubashshirooni

    Ya ce: "Shin kun bã ni bushãra1 ne a kan tsũfa yã shãfe ni? To, da me kuke bã ni bushara?"

    Bayanai
    [1] Ibrahĩm yanã yi musu tambayã ne dõmin yanã ganin kamar sunã yi masa magana ta izgili ne a kan sãmun ɗã a bãyan tsũfansa da na mãtarsa. Sabõda haka suka gaya masa cewa sũ masu gaskiya ne.
  55. قَالُوا۟ بَشَّرْنَـٰكَ بِٱلْحَقِّ فَلَا تَكُن مِّنَ ٱلْقَـٰنِطِينَ۝٥٥

    Qaloo bashsharnaka bialhaqqi fala takun mina alqaniteena

    Suka ce: "Munã yi maka bushãra da gaskiya ne, sabõda haka, kada da kasance daga mãsu yanke tsammãni."

  56. قَالَ وَمَن يَقْنَطُ مِن رَّحْمَةِ رَبِّهِۦٓ إِلَّا ٱلضَّآلُّونَ۝٥٦

    Qala waman yaqnatu min rahmati rabbihi illa alddalloona

    Ya ce: "Kuma wãne ne yake yanke tsammãni daga rahamar Ubangijin sa, fãce ɓatattu?"

  57. قَالَ فَمَا خَطْبُكُمْ أَيُّهَا ٱلْمُرْسَلُونَ۝٥٧

    Qala fama khatbukum ayyuha almursaloona

    Ya ce: "To, mẽne ne babban al'amarinku? Yã kũ manzanni!"

  58. قَالُوٓا۟ إِنَّآ أُرْسِلْنَآ إِلَىٰ قَوْمٍ مُّجْرِمِينَ۝٥٨

    Qaloo inna orsilna ila qawmin mujrimeena

    Suka ce: "Lalle ne mũ, an aika mu zuwa ga wasu mutãne mãsu laifi."

  59. إِلَّآ ءَالَ لُوطٍ إِنَّا لَمُنَجُّوهُمْ أَجْمَعِينَ۝٥٩

    Illa ala lootin inna lamunajjoohum ajmaʿeena

    "Fãce mutãnen Lũɗu, lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu tsĩrar dasu ne gabã ɗaya."

  60. إِلَّا ٱمْرَأَتَهُۥ قَدَّرْنَآ ۙ إِنَّهَا لَمِنَ ٱلْغَـٰبِرِينَ۝٦٠

    Illa imraatahu qaddarna innaha lamina alghabireena

    "Fãce mãtarsa mun ƙaddara cẽwa lalle ne ita, haƙĩƙa, tanã daga mãsu halaka."

  61. فَلَمَّا جَآءَ ءَالَ لُوطٍ ٱلْمُرْسَلُونَ۝٦١

    Falamma jaa ala lootin almursaloona

    To, a lõkacin da mazannin suka jẽ wa mutãnen Lũɗu,

  62. قَالَ إِنَّكُمْ قَوْمٌ مُّنكَرُونَ۝٦٢

    Qala innakum qawmun munkaroona

    Ya ce: "Lalle ne ku mutãne ne waɗanda ba a sani ba."

  63. قَالُوا۟ بَلْ جِئْنَـٰكَ بِمَا كَانُوا۟ فِيهِ يَمْتَرُونَ۝٦٣

    Qaloo bal jinaka bima kanoo feehi yamtaroona

    Suka ce: "Ã'a, mun zo maka sabõda abin da suka kasance sunã shakka a cikinsa."

  64. وَأَتَيْنَـٰكَ بِٱلْحَقِّ وَإِنَّا لَصَـٰدِقُونَ۝٦٤

    Waataynaka bialhaqqi wainna lasadiqoona

    "Kuma mun zo maka da gaskiya. Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu gaskiya ne."

  65. فَأَسْرِ بِأَهْلِكَ بِقِطْعٍ مِّنَ ٱلَّيْلِ وَٱتَّبِعْ أَدْبَـٰرَهُمْ وَلَا يَلْتَفِتْ مِنكُمْ أَحَدٌ وَٱمْضُوا۟ حَيْثُ تُؤْمَرُونَ۝٦٥

    Faasri biahlika biqitʿin mina allayli waittabiʿ adbarahum wala yaltafit minkum ahadun waimdoo haythu tumaroona

    "Sai ka yi tafiya da iyãlinka, a wani yanki na dare, kuma ka bi bãyansu, kuma kada wani daga cikinku ya yi waiwaye, kuma ku bi ta inda aka aumurce ku."

  66. وَقَضَيْنَآ إِلَيْهِ ذَٰلِكَ ٱلْأَمْرَ أَنَّ دَابِرَ هَـٰٓؤُلَآءِ مَقْطُوعٌ مُّصْبِحِينَ۝٦٦

    Waqadayna ilayhi thalika alamra anna dabira haolai maqtooʿun musbiheena

    Kuma Muka hukunta wancan al'amarin zuwa gare shi cẽwa lalle ne ƙarshen waɗancan abin yankẽwa ne a lõkacin da suke mãsu shiga Asuba.

  67. وَجَآءَ أَهْلُ ٱلْمَدِينَةِ يَسْتَبْشِرُونَ۝٦٧

    Wajaa ahlu almadeenati yastabshiroona

    Kuma mutãnen alƙaryar suka je sunã mãsu bushãra.

  68. قَالَ إِنَّ هَـٰٓؤُلَآءِ ضَيْفِى فَلَا تَفْضَحُونِ۝٦٨

    Qala inna haolai dayfee fala tafdahooni

    Ya ce: "Lalle ne waɗannan bãƙĩna ne, sabõda haka kada ku kunyata ni."

  69. وَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَلَا تُخْزُونِ۝٦٩

    Waittaqoo Allaha wala tukhzooni

    "Kuma ku bi Allah da taƙawa, kuma kada ku sanya ni a baƙin ciki."

  70. قَالُوٓا۟ أَوَلَمْ نَنْهَكَ عَنِ ٱلْعَـٰلَمِينَ۝٧٠

    Qaloo awalam nanhaka ʿani alʿalameena

    Suka ce: "Ashe ba mu hana ka daga tãlikai ba?"

  71. قَالَ هَـٰٓؤُلَآءِ بَنَاتِىٓ إِن كُنتُمْ فَـٰعِلِينَ۝٧١

    Qala haolai banatee in kuntum faʿileena

    Ya ce: "Ga waɗannan, 'ya'yãna1 idan kun kasance mãsu aikatãwa ne."

    Bayanai
    [1] Yanã nufin mãtan garin, dõmin Annabin mutãne shĩ ne ubansu.
  72. لَعَمْرُكَ إِنَّهُمْ لَفِى سَكْرَتِهِمْ يَعْمَهُونَ۝٧٢

    Laʿamruka innahum lafee sakratihim yaʿmahoona

    Rantsuwa da1 rãyuwarka! Lalle ne sũ a cikin mãyensu sunã ta ɗĩmuwa.

    Bayanai
    [1] Allah Yã yi rantsuwã da rãyuwar Annabi Muhammadu, tsĩrã da amincin Allah su tabbata a gare shi. Wannan shĩ ne matuƙar girmamãwar wadda Allah Yake yi wa mutum. Kuma yanã nũna cewa rãyuwar Annabi tanã da muhimmanci ƙwarai.
  73. فَأَخَذَتْهُمُ ٱلصَّيْحَةُ مُشْرِقِينَ۝٧٣

    Faakhathathumu alssayhatu mushriqeena

    Sa'an nan tsãwa ta kãma su, sunã mãsu shiga lõkacin hũdõwar rãnã.

  74. فَجَعَلْنَا عَـٰلِيَهَا سَافِلَهَا وَأَمْطَرْنَا عَلَيْهِمْ حِجَارَةً مِّن سِجِّيلٍ۝٧٤

    Fajaʿalna ʿaliyaha safilaha waamtarna ʿalayhim hijaratan min sijjeelin

    Sa'an nan Muka sanya samanta ya kõma ƙasanta, kuma Muka yi ruwan duwãtsu na lãkar wuta a kansu.

  75. إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَـٰتٍ لِّلْمُتَوَسِّمِينَ۝٧٥

    Inna fee thalika laayatin lilmutawassimeena

    Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi ga mãsu tsõkaci da hankali.

  76. وَإِنَّهَا لَبِسَبِيلٍ مُّقِيمٍ۝٧٦

    Wainnaha labisabeelin muqeemin

    Kuma lalle ne ita, haƙĩƙa sunã a gẽfen wata hanyã tabbatacciya.1

    Bayanai
    [1] Hanya tabbatacciya ta mutãnen Makka zuwa Syria (Sham).
  77. إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً لِّلْمُؤْمِنِينَ۝٧٧

    Inna fee thalika laayatan lilmumineena

    Lalle ne a cikin wancan akwai ãyã ga mãsu ĩmãni.

  78. وَإِن كَانَ أَصْحَـٰبُ ٱلْأَيْكَةِ لَظَـٰلِمِينَ۝٧٨

    Wain kana ashabu alaykati lathalimeena

    Kuma lalle ne ma'abũta Al'aika1 sun kasance, haƙĩƙa, mãsu zãlunci!

    Bayanai
    [1] Ma'abũta Al'aika, sũ ne mutãnen shu'aibu.
  79. فَٱنتَقَمْنَا مِنْهُمْ وَإِنَّهُمَا لَبِإِمَامٍ مُّبِينٍ۝٧٩

    Faintaqamna minhum wainnahuma labiimamin mubeenin

    Sai Muka yi azãbar rãmuwã a gare su, kuma lalle sũ biyun, haƙĩƙa, sunã a gẽfen wani tafarki mabayyani.

  80. وَلَقَدْ كَذَّبَ أَصْحَـٰبُ ٱلْحِجْرِ ٱلْمُرْسَلِينَ۝٨٠

    Walaqad kaththaba ashabu alhijri almursaleena

    Kuma lalle ne haƙĩƙa ma'abũta Hijiri1 sun ƙaryata Manzanni.

    Bayanai
    [1] Ma'abũta Hijiri, sũ ne samũdãwa.
  81. وَءَاتَيْنَـٰهُمْ ءَايَـٰتِنَا فَكَانُوا۟ عَنْهَا مُعْرِضِينَ۝٨١

    Waataynahum ayatina fakanoo ʿanha muʿrideena

    Kuma Kuka kai musu ãyõyinMu, sai suka kasance mãsu bijirẽwa daga gare su.

  82. وَكَانُوا۟ يَنْحِتُونَ مِنَ ٱلْجِبَالِ بُيُوتًا ءَامِنِينَ۝٨٢

    Wakanoo yanhitoona mina aljibali buyootan amineena

    Kuma sun kasance sunã sassaƙa gidãje daga duwãtsu, alhãli sunã amintattu.

  83. فَأَخَذَتْهُمُ ٱلصَّيْحَةُ مُصْبِحِينَ۝٨٣

    Faakhathathumu alssayhatu musbiheena

    Sai tsãwa ta kãma su sunã mãsu shiga Asuba.

  84. فَمَآ أَغْنَىٰ عَنْهُم مَّا كَانُوا۟ يَكْسِبُونَ۝٨٤

    Fama aghna ʿanhum ma kanoo yaksiboona

    Sa'an nan abin da suka kasance sunã tsirfantãwa bai wadãtar ga barinsu ba.

  85. وَمَا خَلَقْنَا ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَآ إِلَّا بِٱلْحَقِّ ۗ وَإِنَّ ٱلسَّاعَةَ لَـَٔاتِيَةٌ ۖ فَٱصْفَحِ ٱلصَّفْحَ ٱلْجَمِيلَ۝٨٥

    Wama khalaqna alssamawati waalarda wama baynahuma illa bialhaqqi wainna alssaʿata laatiyatun faisfahi alssafha aljameela

    Kuma ba Mu halicci sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu ba fãce da gaskiya. Kuma lalle ne Sã'a (Rãnar Alƙiyãma) haƙĩƙa mai zuwa ce. Sabõdahaka ka yi rangwame, rangwame mai kyau.

  86. إِنَّ رَبَّكَ هُوَ ٱلْخَلَّـٰقُ ٱلْعَلِيمُ۝٨٦

    Inna rabbaka huwa alkhallaqu alʿaleemu

    Lalle ne Ubangijinka, shi ne Mai yawan halitta, Masani.

  87. وَلَقَدْ ءَاتَيْنَـٰكَ سَبْعًا مِّنَ ٱلْمَثَانِى وَٱلْقُرْءَانَ ٱلْعَظِيمَ۝٨٧

    Walaqad ataynaka sabʿan mina almathanee waalqurana alʿatheema

    Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bã ka bakwai waɗan da ake maimaita karatunsu1 da Alƙur'ãni mai girma.

    Bayanai
    [1] Bakwai waɗanda ake maimaita karatunsu su ne Fãtiha mai ãyõyi bakwai. Anã karanta su a cikin kõwace raka'a ta salla.
  88. لَا تَمُدَّنَّ عَيْنَيْكَ إِلَىٰ مَا مَتَّعْنَا بِهِۦٓ أَزْوَٰجًا مِّنْهُمْ وَلَا تَحْزَنْ عَلَيْهِمْ وَٱخْفِضْ جَنَاحَكَ لِلْمُؤْمِنِينَ۝٨٨

    La tamuddanna ʿaynayka ila ma mattaʿna bihi azwajan minhum wala tahzan ʿalayhim waikhfid janahaka lilmumineena

    Kada lalle kaƙĩƙa idãnunka biyu zuwa ga abin da Muka jiyar da su dãɗi game da shi, nau'i-nau'i a gare su, kuma kada ka yi baƙin ciki a kansu, kuma sassauta fikãfikanka ga mãsu ĩmãni.

  89. وَقُلْ إِنِّىٓ أَنَا ٱلنَّذِيرُ ٱلْمُبِينُ۝٨٩

    Waqul innee ana alnnatheeru almubeenu

    Kuma ka ce: "Lalle nĩ nĩ ne mai gargaɗi bayyanan ne."

  90. كَمَآ أَنزَلْنَا عَلَى ٱلْمُقْتَسِمِينَ۝٩٠

    Kama anzalna ʿala almuqtasimeena

    Kamar yadda Muka saukar a kan mãsu yin rantsuwa,1

    Bayanai
    [1] Mãsu rantsuwa a kan sãɓa wa Annabãwa, watau kamar sun yi rantsuwa wa bã zã su bi abin da Annabãwa suka zoda shi ba. Wãtau su ne mãsu tsananin izgili da Addini.
  91. ٱلَّذِينَ جَعَلُوا۟ ٱلْقُرْءَانَ عِضِينَ۝٩١

    Allatheena jaʿaloo alqurana ʿideena

    Waɗanda suka sanya Alƙur'ãni tãtsuniyõyi.

  92. فَوَرَبِّكَ لَنَسْـَٔلَنَّهُمْ أَجْمَعِينَ۝٩٢

    Fawarabbika lanasalannahum ajmaʿeena

    To, rantsuwa da Ubangijinka!1 Haƙĩƙa, Munã tambayarsugabã ɗaya.

    Bayanai
    [1] Allah Ya yi rantsuwa da ZãtinSa a kan Shĩ ne Ubangijin Annabi Muhammadu tsira da aminci su tabbata a gare shi, dõmin Ya natsar da ransa daga tsõron mãsu yi masa izgili, kuma dõmin Ya ƙarfafa shi ga zartar da aikin da Ya sanya shi na iyar da Manzanci bã da wata fargaba ba.
  93. عَمَّا كَانُوا۟ يَعْمَلُونَ۝٩٣

    ʿAmma kanoo yaʿmaloona

    Daga abin da suka kasance sunã aikatãwa.

  94. فَٱصْدَعْ بِمَا تُؤْمَرُ وَأَعْرِضْ عَنِ ٱلْمُشْرِكِينَ۝٩٤

    Faisdaʿ bima tumaru waaʿrid ʿani almushrikeena

    Sai ka tsage gaskiya game da abin da ake umurnin ka kuma ka kau da kai daga masu shirki.

  95. إِنَّا كَفَيْنَـٰكَ ٱلْمُسْتَهْزِءِينَ۝٩٥

    Inna kafaynaka almustahzieena

    Lalle ne Mũ Mun isar maka daga mãsu1 izgili.

    Bayanai
    [1] Mãsu tsananin izgili ga Annabi waɗanda Allah Ya isar masa daga gare su su biyar ne, daga Bani Asad bn Abdul'uzza bn Kusayyi akwai Aswadu bn el Muttalib, Abu zam'ah, kuma daga Bani Zuhrah akwai el Aswad bn Abdu Yagũth. Daga Bani Makhzumi akwai el walid bn Mugira. Daga Bani Sahmi akwai el Ãs bn wã'il. Daga Banĩ Khuzã'a akwai el Harith bn el-Tulãtilah. Su ne mãsu darajar mutãnensu. A lõkacin da suka dõge da sharri, Allah Ya hũtar da Annabi daga sharrinsu da nau'i-nau'i na masĩfu suka halaka. Dubi ƙarin bayãni daga tafsĩrin bn Kathĩr. tsare Annabi daga gare su, tun yanã shi kaɗaia Makka yã isa ya sanya shi ya dõgara ga Allah bãyan abubuwa sun ƙãra yawa da sauƙi.
  96. ٱلَّذِينَ يَجْعَلُونَ مَعَ ٱللَّهِ إِلَـٰهًا ءَاخَرَ ۚ فَسَوْفَ يَعْلَمُونَ۝٩٦

    Allatheena yajʿaloona maʿa Allahi ilahan akhara fasawfa yaʿlamoona

    Waɗanda suke sanyãwar wani abin bautãwa na dabam tare da Allah, sa'an nan da sannu zã su sani.

  97. وَلَقَدْ نَعْلَمُ أَنَّكَ يَضِيقُ صَدْرُكَ بِمَا يَقُولُونَ۝٩٧

    Walaqad naʿlamu annaka yadeequ sadruka bima yaqooloona

    Kuma lalle ne haƙĩƙa Munã sanin cẽwa lalle kai, ƙirjinka yanã yin ƙunci game da abin da suke faɗã (na izgili).

  98. فَسَبِّحْ بِحَمْدِ رَبِّكَ وَكُن مِّنَ ٱلسَّـٰجِدِينَ۝٩٨

    Fasabbih bihamdi rabbika wakun mina alssajideena

    Sabõda haka ka yi tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinka, kuma ka kasance daga mãsu sujada.

  99. وَٱعْبُدْ رَبَّكَ حَتَّىٰ يَأْتِيَكَ ٱلْيَقِينُ۝٩٩

    Waoʿbud rabbaka hatta yatiyaka alyaqeenu

    Kuma ka bauta wa Ubangijinka, har mutuwa ta zo maka.

Tambayoyin da ake yawan yi

Mece ce ma’anar sunan Suratul Hijr?

Ma’anar Hijr ita ce “Ƙasa mai duwatsu”.

Suratul Hijr tana cikin juz’i na nawa?

Suratul Hijr tana cikin juz’i na 14.

Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Hijr?

Suratul Hijr tana da ayoyi 99.

Suratul Hijr Makkiya ce ko Madaniya?

Suratul Hijr sura ce Makkiya.

Suratul Hijr ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?

Ita ce sura ta 15 a cikin Alƙur’ani.

Majiyoyi

  • Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
  • Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
  • Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
  • Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
  • Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
  • Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.

Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.

Saitunan karatu

Rubutun Alƙur’ani
Girman Larabci
100%
Girman fassara
100%
Kamanni

Ƙara zuwa Allon Gida

ReadSurahBuɗe ReadSurah daga allon gida, a cikakken allo. Surorin da kuka karanta suna buɗewa ko da babu intanet.

  1. A cikin Safari, taɓa maɓallin “Share”. A sababbin iPhone yana cikin menu na •••.
  2. Taɓa “Add to Home Screen”. Gungura ƙasa idan ba ku gan shi ba.
  3. Taɓa “Add”.