سورة الكافرون

Suratul Kafirun da fassarar Hausa

Kafirai

Mushafi

Mishary Rashid AlafasySauke MP3Sauke PDF

Suratul Kafirun (الكافرون) ita ce sura ta 109 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 6. Ma’anar sunanta ita ce “Kafirai”. Sura ce Makkiya, wadda ta sauka a Makka kafin Hijira, kuma tana cikin juz’i na 30.

A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Kafirun gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.

Suratul Kafirun cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. قُلْ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلْكَـٰفِرُونَ۝١

    Qul ya ayyuha alkafiroona

    Ka ce: "Ya kũ kãfirai!"

  2. لَآ أَعْبُدُ مَا تَعْبُدُونَ۝٢

    La aʿbudu ma taʿbudoona

    "Bã zan bautã wa abin da kuke bautã wa ba."

  3. وَلَآ أَنتُمْ عَـٰبِدُونَ مَآ أَعْبُدُ۝٣

    Wala antum ʿabidoona ma aʿbudu

    "Kuma kũ, ba ku zama masu bauta wa abin da nake bautã wa ba."

  4. وَلَآ أَنَا۠ عَابِدٌ مَّا عَبَدتُّمْ۝٤

    Wala ana ʿabidun ma ʿabadtum

    "Kuma nĩ ban zama mai bautã wa abin da kuka bautã wa ba."

  5. وَلَآ أَنتُمْ عَـٰبِدُونَ مَآ أَعْبُدُ۝٥

    Wala antum ʿabidoona ma aʿbudu

    "Kuma kũ, ba ku zama mãsu bautã wa abin da nake1 bautã wa ba."

    Bayanai
    [1] Ãya ta 4 da ta 5 sun nũna addinin ƙarya yakan canza amma na gaskiya bã ya canzawa.
  6. لَكُمْ دِينُكُمْ وَلِىَ دِينِ۝٦

    Lakum deenukum waliya deeni

    "Addininku na garẽ ku, kuma addinina yanã gare ni."

Tambayoyin da ake yawan yi

Mece ce ma’anar sunan Suratul Kafirun?

Ma’anar Kafirun ita ce “Kafirai”.

Suratul Kafirun tana cikin juz’i na nawa?

Suratul Kafirun tana cikin juz’i na 30.

Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Kafirun?

Suratul Kafirun tana da ayoyi 6.

Suratul Kafirun Makkiya ce ko Madaniya?

Suratul Kafirun sura ce Makkiya.

Suratul Kafirun ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?

Ita ce sura ta 109 a cikin Alƙur’ani.

Majiyoyi

  • Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
  • Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
  • Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
  • Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
  • Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
  • Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.

Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.

Saitunan karatu

Rubutun Alƙur’ani
Girman Larabci
100%
Girman fassara
100%
Kamanni

Ƙara zuwa Allon Gida

ReadSurahBuɗe ReadSurah daga allon gida, a cikakken allo. Surorin da kuka karanta suna buɗewa ko da babu intanet.

  1. A cikin Safari, taɓa maɓallin “Share”. A sababbin iPhone yana cikin menu na •••.
  2. Taɓa “Add to Home Screen”. Gungura ƙasa idan ba ku gan shi ba.
  3. Taɓa “Add”.