Suratul Insan (الانسان) ita ce sura ta 76 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 31. Ma’anar sunanta ita ce “Mutum”. Sura ce Madaniya, wadda ta sauka a Madina bayan Hijira, kuma tana cikin juz’i na 29.
A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Insan gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.
Suratul Insan cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ
-
هَلْ أَتَىٰ عَلَى ٱلْإِنسَـٰنِ حِينٌ مِّنَ ٱلدَّهْرِ لَمْ يَكُن شَيْـًٔا مَّذْكُورًا١
Hal ata ʿala alinsani heenun mina alddahri lam yakun shayan mathkooran
Lalle ne, wata mudda ta zamani tã zo a kan mutum, bai kasance kõme ba wanda ake ambata.
-
إِنَّا خَلَقْنَا ٱلْإِنسَـٰنَ مِن نُّطْفَةٍ أَمْشَاجٍ نَّبْتَلِيهِ فَجَعَلْنَـٰهُ سَمِيعًۢا بَصِيرًا٢
Inna khalaqna alinsana min nutfatin amshajin nabtaleehi fajaʿalnahu sameeʿan baseeran
Lalle ne, Mũ Mun halitta mutum daga ɗigon ruwa garwayayye, Muna jarraba shi, sabõda haka Muka sanya shi mai ji mai gani,
-
إِنَّا هَدَيْنَـٰهُ ٱلسَّبِيلَ إِمَّا شَاكِرًا وَإِمَّا كَفُورًا٣
Inna hadaynahu alssabeela imma shakiran waimma kafooran
Lalle ne, Mũ, Mun shiryar da shi ga hanyar ƙwarai, ko ya zama mai gõdiya, kuma ko ya zama mai kãfirci.
-
إِنَّآ أَعْتَدْنَا لِلْكَـٰفِرِينَ سَلَـٰسِلَا۟ وَأَغْلَـٰلًا وَسَعِيرًا٤
Inna aʿtadna lilkafireena salasila waaghlalan wasaʿeeran
Lalle ne, Mũ, Mun yi tattali, dõmin kãfirai, sarƙoƙi da ƙuƙumma da sa'ĩr.
-
إِنَّ ٱلْأَبْرَارَ يَشْرَبُونَ مِن كَأْسٍ كَانَ مِزَاجُهَا كَافُورًا٥
Inna alabrara yashraboona min kasin kana mizajuha kafooran
Lalle ne, mutãnen kirki zã su sha daga finjãlin giya abin gaurayarta yã kãsance kãfur ne.
-
عَيْنًا يَشْرَبُ بِهَا عِبَادُ ٱللَّهِ يُفَجِّرُونَهَا تَفْجِيرًا٦
ʿAynan yashrabu biha ʿibadu Allahi yufajjiroonaha tafjeeran
Wani marmaro ne, daga gare shi bayin Allah suke sha, suna ɓuɓɓugar da shi ɓuɓɓugarwa.
-
يُوفُونَ بِٱلنَّذْرِ وَيَخَافُونَ يَوْمًا كَانَ شَرُّهُۥ مُسْتَطِيرًا٧
Yoofoona bialnnathri wayakhafoona yawman kana sharruhu mustateeran
Suna cikãwa da alwãshin (da suka bãkanta), kuma suna tsõron wani yini wanda sharrinsa ya kasance mai tartsatsi ne.
-
وَيُطْعِمُونَ ٱلطَّعَامَ عَلَىٰ حُبِّهِۦ مِسْكِينًا وَيَتِيمًا وَأَسِيرًا٨
Wayutʿimona alttaʿama ʿala hubbihi miskeenan wayateeman waaseeran
Kuma suna ciyar da abinci, a kan suna bukãtarsa, ga matalauci da marãya da kãmamme.
-
إِنَّمَا نُطْعِمُكُمْ لِوَجْهِ ٱللَّهِ لَا نُرِيدُ مِنكُمْ جَزَآءً وَلَا شُكُورًا٩
Innama nutʿimukum liwajhi Allahi la nureedu minkum jazaan wala shukooran
(Suna cẽwa): "Munã ciyar da ku ne dõmin nẽman yardar Allah kawai, bã mu nufin sãmun wani sakamako daga gare ku, kuma bã mu nufin gõdiya.
-
إِنَّا نَخَافُ مِن رَّبِّنَا يَوْمًا عَبُوسًا قَمْطَرِيرًا١٠
Inna nakhafu min rabbina yawman ʿaboosan qamtareeran
"Lalle ne, mũ muna tsõro daga Ubangijinmu, wani yini mai gintsẽwa, mai murtukẽwa."
-
فَوَقَىٰهُمُ ٱللَّهُ شَرَّ ذَٰلِكَ ٱلْيَوْمِ وَلَقَّىٰهُمْ نَضْرَةً وَسُرُورًا١١
Fawaqahumu Allahu sharra thalika alyawmi walaqqahum nadratan wasurooran
Sabõda haka Allah Ya tsare musu sharrin wannan yini, kuma Ya hlɗa su da annũrin huska da farin ciki,
-
وَجَزَىٰهُم بِمَا صَبَرُوا۟ جَنَّةً وَحَرِيرًا١٢
Wajazahum bima sabaroo jannatan wahareeran
Kuma Ya sãka musu sabõda haƙurin da suka yi, da Aljanna da tufãfin alharini.
-
مُّتَّكِـِٔينَ فِيهَا عَلَى ٱلْأَرَآئِكِ ۖ لَا يَرَوْنَ فِيهَا شَمْسًا وَلَا زَمْهَرِيرًا١٣
Muttakieena feeha ʿala alaraiki la yarawna feeha shamsan wala zamhareeran
Sunã mãsu zaman ginciri,1 a cikinta, a kan karagu, bã su ganin rãnã a cikinta, kuma bã su ganin jaura.
Bayanai
[1] Kishingiɗa. -
وَدَانِيَةً عَلَيْهِمْ ظِلَـٰلُهَا وَذُلِّلَتْ قُطُوفُهَا تَذْلِيلًا١٤
Wadaniyatan ʿalayhim thilaluha wathullilat qutoofuha tathleelan
Kuma, inuwõyinta suna kusa, a kansu, an hõre nunannun 'yã'yan itãcenta, hõrẽwa.
-
وَيُطَافُ عَلَيْهِم بِـَٔانِيَةٍ مِّن فِضَّةٍ وَأَكْوَابٍ كَانَتْ قَوَارِيرَا۠١٥
Wayutafu ʿalayhim bianiyatin min fiddatin waakwabin kanat qawareera
Kuma ana kẽwayãwa a kansu da finjãlai na azurfa da kofuna waɗanda suka kasance na ƙarau.
-
قَوَارِيرَا۟ مِن فِضَّةٍ قَدَّرُوهَا تَقْدِيرًا١٦
Qawareera min fiddatin qaddarooha taqdeeran
¡arau na azurfa, sun ƙaddara su ƙaddarawa, daidai bukãta.
-
وَيُسْقَوْنَ فِيهَا كَأْسًا كَانَ مِزَاجُهَا زَنجَبِيلًا١٧
Wayusqawna feeha kasan kana mizajuha zanjabeelan
Ana shayarwa da su, a cikinta, finjalan giya, wadda abin gaurayarta ya kasance zanjabil ne.
-
عَيْنًا فِيهَا تُسَمَّىٰ سَلْسَبِيلًا١٨
ʿAynan feeha tusamma salsabeelan
Wani marmaro ne, a cikinta, ana kiran sa salsabil.
-
۞ وَيَطُوفُ عَلَيْهِمْ وِلْدَٰنٌ مُّخَلَّدُونَ إِذَا رَأَيْتَهُمْ حَسِبْتَهُمْ لُؤْلُؤًا مَّنثُورًا١٩
Wayatoofu ʿalayhim wildanun mukhalladoona itha raaytahum hasibtahum luluan manthooran
Kuma wasu yara samãrin dindindin na kẽwayãwa, a kansu, idan ka gan su, zã ka zaci sũ lu'ulu'u ne wanda aka wãtsa.
-
وَإِذَا رَأَيْتَ ثَمَّ رَأَيْتَ نَعِيمًا وَمُلْكًا كَبِيرًا٢٠
Waitha raayta thamma raayta naʿeeman wamulkan kabeeran
Kuma idan kã ga wannan wurin, to, kã ga wata irin ni'ima da mulki babba.
-
عَـٰلِيَهُمْ ثِيَابُ سُندُسٍ خُضْرٌ وَإِسْتَبْرَقٌ ۖ وَحُلُّوٓا۟ أَسَاوِرَ مِن فِضَّةٍ وَسَقَىٰهُمْ رَبُّهُمْ شَرَابًا طَهُورًا٢١
ʿaliyahum thiyabu sundusin khudrun waistabraqun wahulloo asawira min fiddatin wasaqahum rabbuhum sharaban tahooran
Tufãfinsu na sama na alharĩ ni ne, kõre da mai walƙiya, kuma an ƙawãce su da mundãye na wata curin azurfa kuma Ubangijinsu, Ya shãyar da su abin sha mai tsarkakẽwar (ciki).
-
إِنَّ هَـٰذَا كَانَ لَكُمْ جَزَآءً وَكَانَ سَعْيُكُم مَّشْكُورًا٢٢
Inna hatha kana lakum jazaan wakana saʿyukum mashkooran
(A ce musu) "Lalle ne, wannan ya kasance, a gare ku sakamako, kuma aikink. ya kasance abin gõdewa."
-
إِنَّا نَحْنُ نَزَّلْنَا عَلَيْكَ ٱلْقُرْءَانَ تَنزِيلًا٢٣
Inna nahnu nazzalna ʿalayka alqurana tanzeelan
Lalle, Mũ ne Muka saukar da Alƙur'ãni a gare ka, saukarwa.
-
فَٱصْبِرْ لِحُكْمِ رَبِّكَ وَلَا تُطِعْ مِنْهُمْ ءَاثِمًا أَوْ كَفُورًا٢٤
Faisbir lihukmi rabbika wala tutiʿ minhum athiman aw kafooran
Sabõda haka ka yi haƙuri ga hukuncin Ubangijinka, kuma kada ka bi, daga cikinsu, mai zunubi ko mai kãfirci.
-
وَٱذْكُرِ ٱسْمَ رَبِّكَ بُكْرَةً وَأَصِيلًا٢٥
Waothkuri isma rabbika bukratan waaseelan
Kuma ka ambaci sũnan Ubangijinka, sãfe da maraice.
-
وَمِنَ ٱلَّيْلِ فَٱسْجُدْ لَهُۥ وَسَبِّحْهُ لَيْلًا طَوِيلًا٢٦
Wamina allayli faosjud lahu wasabbihhu laylan taweelan
Daga dare, sai ka yi sujũda gare Shi, kuma ka tsarkake Shi darẽ mai tsawo.
-
إِنَّ هَـٰٓؤُلَآءِ يُحِبُّونَ ٱلْعَاجِلَةَ وَيَذَرُونَ وَرَآءَهُمْ يَوْمًا ثَقِيلًا٢٧
Inna haolai yuhibboona alʿajilata wayatharoona waraahum yawman thaqeelan
Lalle ne, waɗannan suna son mai gaugãwa (dũniya) kuma suna bari, a bãyansu, wani yini mai nauyi.
-
نَّحْنُ خَلَقْنَـٰهُمْ وَشَدَدْنَآ أَسْرَهُمْ ۖ وَإِذَا شِئْنَا بَدَّلْنَآ أَمْثَـٰلَهُمْ تَبْدِيلًا٢٨
Nahnu khalaqnahum washadadna asrahum waitha shina baddalna amthalahum tabdeelan
Mũ ne Muka halitta su kuma Muka, ƙarfafa halittarsu, kuma idan Mun so, za Mu musanyâ su da wasu mutane kwatankwacinsu, musanyawa.
-
إِنَّ هَـٰذِهِۦ تَذْكِرَةٌ ۖ فَمَن شَآءَ ٱتَّخَذَ إِلَىٰ رَبِّهِۦ سَبِيلًا٢٩
Inna hathihi tathkiratun faman shaa ittakhatha ila rabbihi sabeelan
Lalle ne, wannan wata tunãtarwa ce, saboda wanda ya so ya riƙa hanyar kirki zuwa ga Ubangijinsa.
-
وَمَا تَشَآءُونَ إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلِيمًا حَكِيمًا٣٠
Wama tashaoona illa an yashaa Allahu inna Allaha kana ʿaleeman hakeeman
Kuma, bã zã ku so ba, sai Allah Ya so, lalle ne Allah Yã kasance Masani' Mai hikima.
-
يُدْخِلُ مَن يَشَآءُ فِى رَحْمَتِهِۦ ۚ وَٱلظَّـٰلِمِينَ أَعَدَّ لَهُمْ عَذَابًا أَلِيمًۢا٣١
Yudkhilu man yashao fee rahmatihi waalththalimeena aʿadda lahum ʿathaban aleeman
Yana shigar da wanda Ya so a cikin rahamarsa, kuma azzãlumai, Yã yi musu tattalin wata azãba mai raɗaɗi.
Tambayoyin da ake yawan yi
Mece ce ma’anar sunan Suratul Insan?
Ma’anar Insan ita ce “Mutum”.
Suratul Insan tana cikin juz’i na nawa?
Suratul Insan tana cikin juz’i na 29.
Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Insan?
Suratul Insan tana da ayoyi 31.
Suratul Insan Makkiya ce ko Madaniya?
Suratul Insan sura ce Madaniya.
Suratul Insan ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?
Ita ce sura ta 76 a cikin Alƙur’ani.
Majiyoyi
- Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
- Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
- Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
- Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
- Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
- Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.
Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.