سورة القيامة
Suratul Ƙiyama da fassarar Hausa
Tashin Ƙiyama
- 75
- ayoyi 40
- Makkiya
- Juz’i 29
- Shafuka 577–578
Suratul Ƙiyama (القيامة) ita ce sura ta 75 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 40. Ma’anar sunanta ita ce “Tashin Ƙiyama”. Sura ce Makkiya, wadda ta sauka a Makka kafin Hijira, kuma tana cikin juz’i na 29.
A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Ƙiyama gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.
Suratul Ƙiyama cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ
-
لَآ أُقْسِمُ بِيَوْمِ ٱلْقِيَـٰمَةِ١
La oqsimu biyawmi alqiyamati
Bã sai Nã yi rantsuwa1 da Rãnar ¡iyãma ba.
Bayanai
[1] Wasu na fassarawa: lna rantsuwa da Rãnar Ƙiyama. A ganina, da tabbatar da rantsuwar da kuma kore ta duka ɗaya ne, maƙasũdi dai jan hankalin mai karãtu ga abin da yake a ciki, na hikimar Allah. -
وَلَآ أُقْسِمُ بِٱلنَّفْسِ ٱللَّوَّامَةِ٢
Wala oqsimu bialnnafsi allawwamati
Bã sai Nã yi rantsuwa da rai mai yawan zargin1 kansa ba.
Bayanai
[1] Kowane rai na zargin kansa idan bai yi aikin alheri ba, ko kuma bai yi fiye da wanda ya yi ba, ko kuma bai aikata wanda ya fi kyãwo ba a lokacin aikinsa. -
أَيَحْسَبُ ٱلْإِنسَـٰنُ أَلَّن نَّجْمَعَ عِظَامَهُۥ٣
Ayahsabu alinsanu allan najmaʿa ʿithamahu
Sin, mutum yana zaton cẽwa bã zã Mu tãra ƙasusuwansa ba?
-
بَلَىٰ قَـٰدِرِينَ عَلَىٰٓ أَن نُّسَوِّىَ بَنَانَهُۥ٤
Bala qadireena ʿala an nusawwiya bananahu
Na'am! Mãsu ĩkon yi Muke a kan Mu daidaita gaɓõɓin yãtsunsa.
-
بَلْ يُرِيدُ ٱلْإِنسَـٰنُ لِيَفْجُرَ أَمَامَهُۥ٥
Bal yureedu alinsanu liyafjura amamahu
Ba haka ba! Mutum so yake, ya yi fãjirci, ya ƙaryata abin da yake a gabansa.
-
يَسْـَٔلُ أَيَّانَ يَوْمُ ٱلْقِيَـٰمَةِ٦
Yasalu ayyana yawmu alqiyamati
Yanã tambaya: "Yaushe ne Rãnar ¡iyãma?"
-
فَإِذَا بَرِقَ ٱلْبَصَرُ٧
Faitha bariqa albasaru
To, idan gani ya ɗimauta (ya yi ƙyalli).
-
وَخَسَفَ ٱلْقَمَرُ٨
Wakhasafa alqamaru
Kuma, watã ya yi husũfi (haskensa ya dushe).
-
وَجُمِعَ ٱلشَّمْسُ وَٱلْقَمَرُ٩
Wajumiʿa alshshamsu waalqamaru
Aka tãra rãnã da watã
-
يَقُولُ ٱلْإِنسَـٰنُ يَوْمَئِذٍ أَيْنَ ٱلْمَفَرُّ١٠
Yaqoolu alinsanu yawmaithin ayna almafarru
Mutum zai ce a rãn nan "Ina wurin gudu?"
-
كَلَّا لَا وَزَرَ١١
Kalla la wazara
A'aha! bãbu mafaka.
-
إِلَىٰ رَبِّكَ يَوْمَئِذٍ ٱلْمُسْتَقَرُّ١٢
Ila rabbika yawmaithin almustaqarru
zuwa ga Ubangijinka wurin tabbata, a rãnar nan, yake.
-
يُنَبَّؤُا۟ ٱلْإِنسَـٰنُ يَوْمَئِذٍۭ بِمَا قَدَّمَ وَأَخَّرَ١٣
Yunabbao alinsanu yawmaithin bima qaddama waakhkhara
Ana gayã wa mutum, a rãnar nan, abin da ya gabatar da wanda ya jinkirtar.
-
بَلِ ٱلْإِنسَـٰنُ عَلَىٰ نَفْسِهِۦ بَصِيرَةٌ١٤
Bali alinsanu ʿala nafsihi baseeratun
Ba haka ba! Mutum, ga abin da ya shafi kansa, masani ne.
-
وَلَوْ أَلْقَىٰ مَعَاذِيرَهُۥ١٥
Walaw alqa maʿatheerahu
Kuma ko da yã jẽfa uzurorinsa (bã zã a saurãre shi ba).
-
لَا تُحَرِّكْ بِهِۦ لِسَانَكَ لِتَعْجَلَ بِهِۦٓ١٦
La tuharrik bihi lisanaka litaʿjala bihi
Kada ka mõtsar1 da harshenka game da shi dõmin ka yi gaugãwar riƙe shi (Alƙur'ãni).
Bayanai
[1] Dangantakar wannan ãya da ta sama da ita, ita ce bambancin Annabi mai gaggawar karɓar umurnin Allah da ƙyamar kãfiri ga karɓarsa, da bayãnin sauƙaƙewar Allah ga mai bin umurninSa. -
إِنَّ عَلَيْنَا جَمْعَهُۥ وَقُرْءَانَهُۥ١٧
Inna ʿalayna jamʿahu waquranahu
Lalle ne, wãjibi ne a gare Mu, Mu tãra shi. Mu (tsare maka) karãtunsa.
-
فَإِذَا قَرَأْنَـٰهُ فَٱتَّبِعْ قُرْءَانَهُۥ١٨
Faitha qaranahu faittabiʿ quranahu
To idan Muka karanta shi sai ka bi karatunsa.
-
ثُمَّ إِنَّ عَلَيْنَا بَيَانَهُۥ١٩
Thumma inna ʿalayna bayanahu
sa'an nan, lalle wãjibi ne a gare Mu, bayãninsa.
-
كَلَّا بَلْ تُحِبُّونَ ٱلْعَاجِلَةَ٢٠
Kalla bal tuhibboona alʿajilata
A'aha! Bã haka ba kunã son mai gaugawar nan (duniya) ne.
-
وَتَذَرُونَ ٱلْـَٔاخِرَةَ٢١
Watatharoona alakhirata
Kunã barin ta ƙarshen (Lãhira).
-
وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ نَّاضِرَةٌ٢٢
Wujoohun yawmaithin nadiratun
Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu annuri ne.
-
إِلَىٰ رَبِّهَا نَاظِرَةٌ٢٣
Ila rabbiha nathiratun
Zuwa ga Ubangijinsu mãsu kallo ne.
-
وَوُجُوهٌ يَوْمَئِذٍۭ بَاسِرَةٌ٢٤
Wawujoohun yawmaithin basiratun
Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu gintsẽwa ne.
-
تَظُنُّ أَن يُفْعَلَ بِهَا فَاقِرَةٌ٢٥
Tathunnu an yufʿala biha faqiratun
Sunã zaton a sako musu masĩfa mai karya tsatso.
-
كَلَّآ إِذَا بَلَغَتِ ٱلتَّرَاقِىَ٢٦
Kalla itha balaghati alttaraqiya
A'aha! Iadan (rai) ya kai ga karankarmai.
-
وَقِيلَ مَنْ ۜ رَاقٍ٢٧
Waqeela man raqin
kuma aka ce: "Wãne ne mai tawada?"
-
وَظَنَّ أَنَّهُ ٱلْفِرَاقُ٢٨
Wathanna annahu alfiraqu
Kuma ya tabbata cẽwa rabuwa dai ce.
-
وَٱلْتَفَّتِ ٱلسَّاقُ بِٱلسَّاقِ٢٩
Wailtaffati alssaqu bialssaqi
Kuma ƙwabri ya lauye da wani ƙwabri.
-
إِلَىٰ رَبِّكَ يَوْمَئِذٍ ٱلْمَسَاقُ٣٠
Ila rabbika yawmaithin almasaqu
Zuwa ga Ubangijinka, a rãnar nan, magargaɗa1 take.
Bayanai
[1] Ranar kora mutane, kamar ana gargaɗa tumãki, zuwa ga tsayuwa a gaba ga Allah, dõmin hisabi. -
فَلَا صَدَّقَ وَلَا صَلَّىٰ٣١
Fala saddaqa wala salla
To, bai gaskatã ba, kuma bai yi salla ba!
-
وَلَـٰكِن كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰ٣٢
Walakin kaththaba watawalla
Amma dai ya ƙaryata, kuma ya jũya baya!
-
ثُمَّ ذَهَبَ إِلَىٰٓ أَهْلِهِۦ يَتَمَطَّىٰٓ٣٣
Thumma thahaba ila ahlihi yatamatta
Sa'an nan, ya tafi zuwa ga mutãnensa, yana tãƙama.
-
أَوْلَىٰ لَكَ فَأَوْلَىٰ٣٤
Awla laka faawla
Halaka tã tabbata a gare ka, sa'an nan ita ce mafi dãcewa.
-
ثُمَّ أَوْلَىٰ لَكَ فَأَوْلَىٰٓ٣٥
Thumma awla laka faawla
Sa'an nan, wata halaka tã tabbata a gare ka dõmin tã fi dãce wa.
-
أَيَحْسَبُ ٱلْإِنسَـٰنُ أَن يُتْرَكَ سُدًى٣٦
Ayahsabu alinsanu an yutraka sudan
Shin, mutum nã zaton a bar shi sagaga (wãto bãbu nufin kõme game da shi)?
-
أَلَمْ يَكُ نُطْفَةً مِّن مَّنِىٍّ يُمْنَىٰ٣٧
Alam yaku nutfatan min manayyin yumna
Bai kasance ɗigo na maniyyi ba, wanda ake jefarwa (a cikin mahaifa)
-
ثُمَّ كَانَ عَلَقَةً فَخَلَقَ فَسَوَّىٰ٣٨
Thumma kana ʿalaqatan fakhalaqa fasawwa
Sa'an nan, ya zama gudan jini, sa'an nan Allah Ya halitta shi, sa'an nan Ya daidaita gaɓõɓinsa;
-
فَجَعَلَ مِنْهُ ٱلزَّوْجَيْنِ ٱلذَّكَرَ وَٱلْأُنثَىٰٓ٣٩
Fajaʿala minhu alzzawjayni alththakara waalontha
Sa'an nan, Ya sanya daga gare shi, nau'i biyu: namiji damace?
-
أَلَيْسَ ذَٰلِكَ بِقَـٰدِرٍ عَلَىٰٓ أَن يُحْـِۧىَ ٱلْمَوْتَىٰ٤٠
Alaysa thalika biqadirin ʿala an yuhyiya almawta
Ashẽ wannan bai zama Mai iko ba bisa ga rãyar da matattu?1
Bayanai
[1] Ana son mai karãtu a nan ya ce: a ɓoye بلى وأنا على ذلك من الشاهدين.
Tambayoyin da ake yawan yi
Mece ce ma’anar sunan Suratul Ƙiyama?
Ma’anar Ƙiyama ita ce “Tashin Ƙiyama”.
Suratul Ƙiyama tana cikin juz’i na nawa?
Suratul Ƙiyama tana cikin juz’i na 29.
Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Ƙiyama?
Suratul Ƙiyama tana da ayoyi 40.
Suratul Ƙiyama Makkiya ce ko Madaniya?
Suratul Ƙiyama sura ce Makkiya.
Suratul Ƙiyama ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?
Ita ce sura ta 75 a cikin Alƙur’ani.
Majiyoyi
- Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
- Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
- Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
- Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
- Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
- Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.
Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.