سورة المرسلات
Suratul Mursalat da fassarar Hausa
Waɗanda aka aiko
- 77
- ayoyi 50
- Makkiya
- Juz’i 29
- Shafuka 580–581
Suratul Mursalat (المرسلات) ita ce sura ta 77 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 50. Ma’anar sunanta ita ce “Waɗanda aka aiko”. Sura ce Makkiya, wadda ta sauka a Makka kafin Hijira, kuma tana cikin juz’i na 29.
A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Mursalat gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.
Suratul Mursalat cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ
-
وَٱلْمُرْسَلَـٰتِ عُرْفًا١
Waalmursalati ʿurfan
Ina rantsuwa da iskõkin da ake sakõwa jẽre, sunã bin jũna.
-
فَٱلْعَـٰصِفَـٰتِ عَصْفًا٢
Faalʿasifati ʿasfan
Sa'an nan, su zamã iskõki mãsu ƙarfi suna kaɗãwa da ƙarfi.
-
وَٱلنَّـٰشِرَٰتِ نَشْرًا٣
Waalnnashirati nashran
Kuma, mãsu watsa rahama wãtsãwa.
-
فَٱلْفَـٰرِقَـٰتِ فَرْقًا٤
Faalfariqati farqan
sa'an nan, da ãyõyi1 mãsu rarrabe gaskiya da ƙarya rarrabẽwa.
Bayanai
[1] Yã kamanta Manzanin Allah masu kãwo ayõyinsa da iskõki mãsu kãwo ruwa dõmin rahamar da ke cikin kowannensu. -
فَٱلْمُلْقِيَـٰتِ ذِكْرًا٥
Faalmulqiyati thikran
Sa'an nan da malã'iku mãsu jẽfa tunãtarwa ga Manzanni.
-
عُذْرًا أَوْ نُذْرًا٦
ʿUthran aw nuthran
Domin yanke hamzari ko dõmin gargadi.
-
إِنَّمَا تُوعَدُونَ لَوَٰقِعٌ٧
Innama tooʿadoona lawaqiʿun
Lalle ne, abin da ake yi muku wa'adi da shi tabbas mai aukuwa ne
-
فَإِذَا ٱلنُّجُومُ طُمِسَتْ٨
Faitha alnnujoomu tumisat
To, idan taurãri aka shãfe haskensu.
-
وَإِذَا ٱلسَّمَآءُ فُرِجَتْ٩
Waitha alssamao furijat
Kuma, idan sama aka tsãge ta.
-
وَإِذَا ٱلْجِبَالُ نُسِفَتْ١٠
Waitha aljibalu nusifat
Kuma, idan duwãtsu aka nike su.
-
وَإِذَا ٱلرُّسُلُ أُقِّتَتْ١١
Waitha alrrusulu oqqitat
Kuma, idan manzanni aka ƙayyade lõkacin tãra su.
-
لِأَىِّ يَوْمٍ أُجِّلَتْ١٢
Liayyi yawmin ojjilat
Domin babbar rãnar da aka yi wa ajali.
-
لِيَوْمِ ٱلْفَصْلِ١٣
Liyawmi alfasli
Domin rãnar rarrabẽwa.1
Bayanai
[1] Yin hukunci a tsakanin tãlikai. -
وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا يَوْمُ ٱلْفَصْلِ١٤
Wama adraka ma yawmu alfasli
Kuma, me ya sanar da kai rãnar rarrabẽwa?
-
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ١٥
Waylun yawmaithin lilmukaththibeena
Bone yã tabbata a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
-
أَلَمْ نُهْلِكِ ٱلْأَوَّلِينَ١٦
Alam nuhliki alawwaleena
Ashe, ba Mu halakar da (mãsu ƙaryatãw) na farko ba.
-
ثُمَّ نُتْبِعُهُمُ ٱلْـَٔاخِرِينَ١٧
Thumma nutbiʿuhumu alakhireena
Sa'an nan, kuma zã Mu biyar musu da na ƙarshe?
-
كَذَٰلِكَ نَفْعَلُ بِٱلْمُجْرِمِينَ١٨
Kathalika nafʿalu bialmujrimeena
Haka nan, Muke aikatãwa da mãsu yin laifi.
-
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ١٩
Waylun yawmaithin lilmukaththibeena
Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa!
-
أَلَمْ نَخْلُقكُّم مِّن مَّآءٍ مَّهِينٍ٢٠
Alam nakhluqkum min main maheenin
Ashe, ba Mu halitta ku daga wani ruwa wulakantacce ba.
-
فَجَعَلْنَـٰهُ فِى قَرَارٍ مَّكِينٍ٢١
Fajaʿalnahu fee qararin makeenin
Sa'an nan Muka sanya shi a cikin wani wurin natsuwa amintacce.
-
إِلَىٰ قَدَرٍ مَّعْلُومٍ٢٢
Ila qadarin maʿloomin
Zuwa ga wani gwargwadon mudda sananna.
-
فَقَدَرْنَا فَنِعْمَ ٱلْقَـٰدِرُونَ٢٣
Faqadarna faniʿma alqadiroona
Sa'an nan, Muka nũna iyãwar Mu? Madalla da Mu, Mãsu nũna iyãwa.
-
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ٢٤
Waylun yawmaithin lilmukaththibeena
Bone ya tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa!
-
أَلَمْ نَجْعَلِ ٱلْأَرْضَ كِفَاتًا٢٥
Alam najʿali alarda kifatan
Ashe, ba Mu sanya ƙasa matattarã ba.
-
أَحْيَآءً وَأَمْوَٰتًا٢٦
Ahyaan waamwatan
Ga rãyayyu da matattu,
-
وَجَعَلْنَا فِيهَا رَوَٰسِىَ شَـٰمِخَـٰتٍ وَأَسْقَيْنَـٰكُم مَّآءً فُرَاتًا٢٧
Wajaʿalna feeha rawasiya shamikhatin waasqaynakum maan furatan
Kuma, Muka sanya, a cikinta, kafaffun duwãtsu maɗaukaka, kuma Muka shayar da ku ruwa mai dãɗi?
-
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ٢٨
Waylun yawmaithin lilmukaththibeena
Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
-
ٱنطَلِقُوٓا۟ إِلَىٰ مَا كُنتُم بِهِۦ تُكَذِّبُونَ٢٩
Intaliqoo ila ma kuntum bihi tukaththiboona
Ku tafi zuwa ga abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi!
-
ٱنطَلِقُوٓا۟ إِلَىٰ ظِلٍّ ذِى ثَلَـٰثِ شُعَبٍ٣٠
Intaliqoo ila thillin thee thalathi shuʿabin
Ku tafi zuwa ga wata inuwa mai rassa uku.
-
لَّا ظَلِيلٍ وَلَا يُغْنِى مِنَ ٱللَّهَبِ٣١
La thaleelin wala yughnee mina allahabi
Ita ba inuwar ba, kuma ba ta wadãtarwa daga harshen wuta.
-
إِنَّهَا تَرْمِى بِشَرَرٍ كَٱلْقَصْرِ٣٢
Innaha tarmee bishararin kaalqasri
Lalle ne, ita, tanã jifã da tartsatsi kamar sõraye.
-
كَأَنَّهُۥ جِمَـٰلَتٌ صُفْرٌ٣٣
Kaannahu jimalatun sufrun
Kamar dai su raƙumma ne baƙãƙe.
-
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ٣٤
Waylun yawmaithin lilmukaththibeena
Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
-
هَـٰذَا يَوْمُ لَا يَنطِقُونَ٣٥
Hatha yawmu la yantiqoona
Wannan, yini ne da bã zã su iya yin magana ba.
-
وَلَا يُؤْذَنُ لَهُمْ فَيَعْتَذِرُونَ٣٦
Wala yuthanu lahum fayaʿtathiroona
Bã zã a yi musu izni ba, balle su kãwo hanzari.
-
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ٣٧
Waylun yawmaithin lilmukaththibeena
Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
-
هَـٰذَا يَوْمُ ٱلْفَصْلِ ۖ جَمَعْنَـٰكُمْ وَٱلْأَوَّلِينَ٣٨
Hatha yawmu alfasli jamaʿnakum waalawwaleena
Wannan rãnar rarrabẽwa ce, Mun tattara ku tare da mutãnen farko.
-
فَإِن كَانَ لَكُمْ كَيْدٌ فَكِيدُونِ٣٩
Fain kana lakum kaydun fakeedooni
To, idan akwai wata dabara gare ku, sai ku yi ma Ni ita.
-
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ٤٠
Waylun yawmaithin lilmukaththibeena
Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
-
إِنَّ ٱلْمُتَّقِينَ فِى ظِلَـٰلٍ وَعُيُونٍ٤١
Inna almuttaqeena fee thilalin waʿuyoonin
Lalle ne, mãsu taƙawa suna a cikin inuwõwi da marẽmari.
-
وَفَوَٰكِهَ مِمَّا يَشْتَهُونَ٤٢
Wafawakiha mimma yashtahoona
Da wasu 'ya'yan itãce irin waɗanda suke marmari.
-
كُلُوا۟ وَٱشْرَبُوا۟ هَنِيٓـًٔۢا بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ٤٣
Kuloo waishraboo haneean bima kuntum taʿmaloona
(A ce musu) "Ku ci ku sha cikin ni'ima sabõda abin da kuka kasance kuna aikatãwa."
-
إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجْزِى ٱلْمُحْسِنِينَ٤٤
Inna kathalika najzee almuhsineena
Lalle ne, Mũ haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
-
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ٤٥
Waylun yawmaithin lilmukaththibeena
Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
-
كُلُوا۟ وَتَمَتَّعُوا۟ قَلِيلًا إِنَّكُم مُّجْرِمُونَ٤٦
Kuloo watamattaʿoo qaleelan innakum mujrimoona
(Ana ce musu) "Ku ci ku ji ɗan dãdi kaɗan, lalle ne dai ku mãsu laifi ne."
-
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ٤٧
Waylun yawmaithin lilmukaththibeena
Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
-
وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ ٱرْكَعُوا۟ لَا يَرْكَعُونَ٤٨
Waitha qeela lahumu irkaʿoo la yarkaʿoona
Kuma, idan an ce musu: "Ku yi rukũ'i; bã zã su yi rukũ'in (salla) ba."
-
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ٤٩
Waylun yawmaithin lilmukaththibeena
Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
-
فَبِأَىِّ حَدِيثٍۭ بَعْدَهُۥ يُؤْمِنُونَ٥٠
Fabiayyi hadeethin baʿdahu yuminoona
To, da wane lãbãri (Littãfi), waninsa (Alƙur'ãni) zã su yi ĩmãni
Tambayoyin da ake yawan yi
Mece ce ma’anar sunan Suratul Mursalat?
Ma’anar Mursalat ita ce “Waɗanda aka aiko”.
Suratul Mursalat tana cikin juz’i na nawa?
Suratul Mursalat tana cikin juz’i na 29.
Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Mursalat?
Suratul Mursalat tana da ayoyi 50.
Suratul Mursalat Makkiya ce ko Madaniya?
Suratul Mursalat sura ce Makkiya.
Suratul Mursalat ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?
Ita ce sura ta 77 a cikin Alƙur’ani.
Majiyoyi
- Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
- Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
- Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
- Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
- Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
- Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.
Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.