سورة النبإ

Suratul Naba’i da fassarar Hausa

Babban labari

Mushafi

Mishary Rashid AlafasySauke MP3Sauke PDF

Suratul Naba’i (النبإ) ita ce sura ta 78 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 40. Ma’anar sunanta ita ce “Babban labari”. Sura ce Makkiya, wadda ta sauka a Makka kafin Hijira, kuma tana cikin juz’i na 30.

A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Naba’i gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.

Suratul Naba’i cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. عَمَّ يَتَسَآءَلُونَ۝١

    ʿAmma yatasaaloona

    A kan mẽ suke tambayar jũna?

  2. عَنِ ٱلنَّبَإِ ٱلْعَظِيمِ۝٢

    ʿAni alnnabai alʿatheemi

    A kan muhimmin lãbãri mai girma (Alƙur'ãni)?

  3. ٱلَّذِى هُمْ فِيهِ مُخْتَلِفُونَ۝٣

    Allathee hum feehi mukhtalifoona

    Wanda suke sãɓa wa jũna a cikinsa?

  4. كَلَّا سَيَعْلَمُونَ۝٤

    Kalla sayaʿlamoona

    A'aha! Zã su sani.

  5. ثُمَّ كَلَّا سَيَعْلَمُونَ۝٥

    Thumma kalla sayaʿlamoona

    Kuma, a'aha! Zã su sani.

  6. أَلَمْ نَجْعَلِ ٱلْأَرْضَ مِهَـٰدًا۝٦

    Alam najʿali alarda mihadan

    Ashe, ba Mu sanya ƙasa shimfiɗa ba?

  7. وَٱلْجِبَالَ أَوْتَادًا۝٧

    Waaljibala awtadan

    Da duwãtsu turaku (ga riƙe ƙasa)?

  8. وَخَلَقْنَـٰكُمْ أَزْوَٰجًا۝٨

    Wakhalaqnakum azwajan

    Kuma, Mun halitta ku mazã da mãtã?

  9. وَجَعَلْنَا نَوْمَكُمْ سُبَاتًا۝٩

    Wajaʿalna nawmakum subatan

    Kuma, Muka sanya barcinku hũtãwa?

  10. وَجَعَلْنَا ٱلَّيْلَ لِبَاسًا۝١٠

    Wajaʿalna allayla libasan

    Kuma, Muka sanya dare (ya zama) sutura?

  11. وَجَعَلْنَا ٱلنَّهَارَ مَعَاشًا۝١١

    Wajaʿalna alnnahara maʿashan

    Kuma, Muka sanya yini (yazama) lõkacin nẽman abinci?

  12. وَبَنَيْنَا فَوْقَكُمْ سَبْعًا شِدَادًا۝١٢

    Wabanayna fawqakum sabʿan shidadan

    Kuma, Muka gina, a samanku, sammai bakwai mãsu ƙarfi?

  13. وَجَعَلْنَا سِرَاجًا وَهَّاجًا۝١٣

    Wajaʿalna sirajan wahhajan

    Kuma, Muka sanya fitila mai tsanin haske (rãnã)?

  14. وَأَنزَلْنَا مِنَ ٱلْمُعْصِرَٰتِ مَآءً ثَجَّاجًا۝١٤

    Waanzalna mina almuʿsirati maan thajjajan

    Kuma, Muka saukar daga cikakkun girãgizai, ruwa mai yawan zuba?

  15. لِّنُخْرِجَ بِهِۦ حَبًّا وَنَبَاتًا۝١٥

    Linukhrija bihi habban wanabatan

    Dõmin, Mu fitar da ƙwaya da tsiri game da shi?

  16. وَجَنَّـٰتٍ أَلْفَافًا۝١٦

    Wajannatin alfafan

    Da itãcen lambuna mãsu lillibniya?

  17. إِنَّ يَوْمَ ٱلْفَصْلِ كَانَ مِيقَـٰتًا۝١٧

    Inna yawma alfasli kana meeqatan

    Lalle ne, rãnar rarrabẽwa tã kasance abin ƙayyadẽ wa lõkaci.

  18. يَوْمَ يُنفَخُ فِى ٱلصُّورِ فَتَأْتُونَ أَفْوَاجًا۝١٨

    Yawma yunfakhu fee alssoori fatatoona afwajan

    Rãnar da zã a yi bũsa a cikin ƙaho, sai ku zo, jama'a jama'a.

  19. وَفُتِحَتِ ٱلسَّمَآءُ فَكَانَتْ أَبْوَٰبًا۝١٩

    Wafutihati alssamao fakanat abwaban

    Kuma, aka buɗe sama, sai ta kasance ƙõfõfi.

  20. وَسُيِّرَتِ ٱلْجِبَالُ فَكَانَتْ سَرَابًا۝٢٠

    Wasuyyirati aljibalu fakanat saraban

    Kuma, aka tafiyar da duwãtsu, sai suka kasance ƙũra.

  21. إِنَّ جَهَنَّمَ كَانَتْ مِرْصَادًا۝٢١

    Inna jahannama kanat mirsadan

    Lalle ne, Jahannama tã kasance madãkata.

  22. لِّلطَّـٰغِينَ مَـَٔابًا۝٢٢

    Lilttagheena maaban

    Ga mãsu ƙẽtare iyãkõki, tã zama makõma.

  23. لَّـٰبِثِينَ فِيهَآ أَحْقَابًا۝٢٣

    Labitheena feeha ahqaban

    Sunã, mãsu zama a cikinta, zãmunna.

  24. لَّا يَذُوقُونَ فِيهَا بَرْدًا وَلَا شَرَابًا۝٢٤

    La yathooqoona feeha bardan wala sharaban

    Bã su ɗanɗanãwar wani sanyi a cikinta, kuma bã su ɗanɗana abin sha.

  25. إِلَّا حَمِيمًا وَغَسَّاقًا۝٢٥

    Illa hameeman waghassaqan

    Fãce tafasasshen ruwa da ruɓaɓɓen jini.

  26. جَزَآءً وِفَاقًا۝٢٦

    Jazaan wifaqan

    Sakamako mai dãcẽwa.

  27. إِنَّهُمْ كَانُوا۟ لَا يَرْجُونَ حِسَابًا۝٢٧

    Innahum kanoo la yarjoona hisaban

    Lalle ne, sũ, sun kasance bã su fãtar sauƙin wani hisãbi.

  28. وَكَذَّبُوا۟ بِـَٔايَـٰتِنَا كِذَّابًا۝٢٨

    Wakaththaboo biayatina kiththaban

    Kuma, suka ƙaryata game da ãyõyin Mu, ƙaryatãwa!

  29. وَكُلَّ شَىْءٍ أَحْصَيْنَـٰهُ كِتَـٰبًا۝٢٩

    Wakulla shayin ahsaynahu kitaban

    Alhãli, kõwane abu Mun ƙididdigẽ shi, a rubũce.

  30. فَذُوقُوا۟ فَلَن نَّزِيدَكُمْ إِلَّا عَذَابًا۝٣٠

    Fathooqoo falan nazeedakum illa ʿathaban

    Sabõda haka, ku ɗanɗana domin haka, bã zã Mu ƙara muku kõme ba fãce azãba.

  31. إِنَّ لِلْمُتَّقِينَ مَفَازًا۝٣١

    Inna lilmuttaqeena mafazan

    Lalle ne, mãsu taƙawã nã da wani wurin sãmun babban rabo.

  32. حَدَآئِقَ وَأَعْنَـٰبًا۝٣٢

    Hadaiqa waaʿnaban

    Lambuna da inabõbi.

  33. وَكَوَاعِبَ أَتْرَابًا۝٣٣

    Wakawaʿiba atraban

    Da yan Mata tsaraikun Juna

  34. وَكَأْسًا دِهَاقًا۝٣٤

    Wakasan dihaqan

    Da hinjãlan giya cikakku.

  35. لَّا يَسْمَعُونَ فِيهَا لَغْوًا وَلَا كِذَّٰبًا۝٣٥

    La yasmaʿoona feeha laghwan wala kiththaban

    Bã su jin yãsassar magana, a cikinta, kuma bã su jin ƙaryatãwa.

  36. جَزَآءً مِّن رَّبِّكَ عَطَآءً حِسَابًا۝٣٦

    Jazaan min rabbika ʿataan hisaban

    Dõmin sakamako daga Ubangijinka, kyautã mai yawa.

  37. رَّبِّ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا ٱلرَّحْمَـٰنِ ۖ لَا يَمْلِكُونَ مِنْهُ خِطَابًا۝٣٧

    Rabbi alssamawati waalardi wama baynahuma alrrahmani la yamlikoona minhu khitaban

    Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, Mai rahama, bã su da ikon yin wata magana daga gare Shi.

  38. يَوْمَ يَقُومُ ٱلرُّوحُ وَٱلْمَلَـٰٓئِكَةُ صَفًّا ۖ لَّا يَتَكَلَّمُونَ إِلَّا مَنْ أَذِنَ لَهُ ٱلرَّحْمَـٰنُ وَقَالَ صَوَابًا۝٣٨

    Yawma yaqoomu alrroohu waalmalaikatu saffan la yatakallamoona illa man athina lahu alrrahmanu waqala sawaban

    Rãnar da Rũhi da malã'iku zã su tsaya a cikin safu, bã su magana, sai wanda Allah Ya yi masa izni, kuma ya faɗi abin da ke daidai.

  39. ذَٰلِكَ ٱلْيَوْمُ ٱلْحَقُّ ۖ فَمَن شَآءَ ٱتَّخَذَ إِلَىٰ رَبِّهِۦ مَـَٔابًا۝٣٩

    Thalika alyawmu alhaqqu faman shaa ittakhatha ila rabbihi maaban

    Wancan, shi ne yini na gaskiya; to wanda ya so, ya riƙa makõma zuwa ga Ubangijinsa.

  40. إِنَّآ أَنذَرْنَـٰكُمْ عَذَابًا قَرِيبًا يَوْمَ يَنظُرُ ٱلْمَرْءُ مَا قَدَّمَتْ يَدَاهُ وَيَقُولُ ٱلْكَافِرُ يَـٰلَيْتَنِى كُنتُ تُرَٰبًۢا۝٤٠

    Inna antharnakum ʿathaban qareeban yawma yanthuru almaro ma qaddamat yadahu wayaqoolu alkafiru ya laytanee kuntu turaban

    Lalle ne, Mũ, Mun yi muku gargaɗin azãba makusanciya, rãnar da mutum ke dũbi zuwa ga abin da hannãyensa suka aikata, kuma kafiri ya ce: "Kaitona, dã dai nã zama turɓãya!"

Tambayoyin da ake yawan yi

Mece ce ma’anar sunan Suratul Naba’i?

Ma’anar Naba’i ita ce “Babban labari”.

Suratul Naba’i tana cikin juz’i na nawa?

Suratul Naba’i tana cikin juz’i na 30.

Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Naba’i?

Suratul Naba’i tana da ayoyi 40.

Suratul Naba’i Makkiya ce ko Madaniya?

Suratul Naba’i sura ce Makkiya.

Suratul Naba’i ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?

Ita ce sura ta 78 a cikin Alƙur’ani.

Majiyoyi

  • Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
  • Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
  • Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
  • Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
  • Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
  • Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.

Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.

Saitunan karatu

Rubutun Alƙur’ani
Girman Larabci
100%
Girman fassara
100%
Kamanni

Ƙara zuwa Allon Gida

ReadSurahBuɗe ReadSurah daga allon gida, a cikakken allo. Surorin da kuka karanta suna buɗewa ko da babu intanet.

  1. A cikin Safari, taɓa maɓallin “Share”. A sababbin iPhone yana cikin menu na •••.
  2. Taɓa “Add to Home Screen”. Gungura ƙasa idan ba ku gan shi ba.
  3. Taɓa “Add”.