سورة عبس

Suratul Abasa da fassarar Hausa

Ya ɗaure fuska

Mushafi

Mishary Rashid AlafasySauke MP3Sauke PDF

Suratul Abasa (عبس) ita ce sura ta 80 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 42. Ma’anar sunanta ita ce “Ya ɗaure fuska”. Sura ce Makkiya, wadda ta sauka a Makka kafin Hijira, kuma tana cikin juz’i na 30.

A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Abasa gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.

Suratul Abasa cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. عَبَسَ وَتَوَلَّىٰٓ۝١

    ʿAbasa watawalla

    Yã game huska1 kuma ya jũya bãya.

    Bayanai
    [1] Wani makãho, Abdullahi bin Ummi Maktũm ya je wurin Annabi dõmin ya musulunta, sai ya iske a lõkacin nan Annabi na ƙõƙarin shiryar da wasu manyan mutãne na Ƙuraishãwa, sai wannan makãhon ya yanke maganar Annabi da su, bã da saninsa ba, alhãli Annabi na bũrin su musulunta dõmin darajarsu ga idon mutãnensu. Saboda haka Annabi, (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), ya ɓata Fuska, ya tafi dõmin ɓacin ransa, saboda rashin musuluntarsu. Bãyan haka Annabi nã girmama Abdullahi ƙwarai, idan ya je wurinsa sai ya ce masa "Maraba da wanda Ubangijina Ya zarge ni sabõda shi." Kuma ya shimfiɗa masa mayafinsa, idan ya fita tafiya, yakan sanya shi riƙon garin Madina, ƙissar tana nũna girmamawar Allah ga Annabi da Ya ce: "Ya game Fuska." Bai ce masa: "Domin ka game Fuska" ba, sai ya faɗa a cikin hali mai sauƙi.".
  2. أَن جَآءَهُ ٱلْأَعْمَىٰ۝٢

    An jaahu alaʿma

    Sabõda makãho yã je masa.

  3. وَمَا يُدْرِيكَ لَعَلَّهُۥ يَزَّكَّىٰٓ۝٣

    Wama yudreeka laʿallahu yazzakka

    To, me ya sanar da kai cẽwa watakila shi ne zai tsarkaka.

  4. أَوْ يَذَّكَّرُ فَتَنفَعَهُ ٱلذِّكْرَىٰٓ۝٤

    Aw yaththakkaru fatanfaʿahu alththikra

    Ko ya tuna, dõmin tunãwar ta amfane shi?

  5. أَمَّا مَنِ ٱسْتَغْنَىٰ۝٥

    Amma mani istaghna

    Amma wanda ya wadãtu da dũkiya.

  6. فَأَنتَ لَهُۥ تَصَدَّىٰ۝٦

    Faanta lahu tasadda

    Sa'an nan kai kuma ka ɗora bijira zuwa gare shi!

  7. وَمَا عَلَيْكَ أَلَّا يَزَّكَّىٰ۝٧

    Wama ʿalayka alla yazzakka

    To, me zai cũce ka idan bai tsarkaka ba?

  8. وَأَمَّا مَن جَآءَكَ يَسْعَىٰ۝٨

    Waamma man jaaka yasʿa

    Kuma, amma wanda ya zomaka yana gaugãwa.

  9. وَهُوَ يَخْشَىٰ۝٩

    Wahuwa yakhsha

    Alhãli shĩ yanã jin tsõrõn Allah.

  10. فَأَنتَ عَنْهُ تَلَهَّىٰ۝١٠

    Faanta ʿanhu talahha

    Kai kuma kã shagala ga barinsa!

  11. كَلَّآ إِنَّهَا تَذْكِرَةٌ۝١١

    Kalla innaha tathkiratun

    A'aha! Lalle ne, wannan tunãtarwa ce.

  12. فَمَن شَآءَ ذَكَرَهُۥ۝١٢

    Faman shaa thakarahu

    Sabõda wanda ya so ya tuna Shi (Allah).

  13. فِى صُحُفٍ مُّكَرَّمَةٍ۝١٣

    Fee suhufin mukarramatin

    (Tunãtarwa ce) ta cikin littafai abãban girmamãwa,

  14. مَّرْفُوعَةٍ مُّطَهَّرَةٍۭ۝١٤

    Marfooʿatin mutahharatin

    Abãban ɗaukakãwa, abãban tsarkakẽwa.

  15. بِأَيْدِى سَفَرَةٍ۝١٥

    Biaydee safaratin

    A cikin hannãyen mala'iku marubũta.

  16. كِرَامٍۭ بَرَرَةٍ۝١٦

    Kiramin bararatin

    Mãsu daraja, mãsu ɗã'a ga Allah.

  17. قُتِلَ ٱلْإِنسَـٰنُ مَآ أَكْفَرَهُۥ۝١٧

    Qutila alinsanu ma akfarahu

    An la'ani mutum (kafiri). Mẽ yã yi kãfircinsa!

  18. مِنْ أَىِّ شَىْءٍ خَلَقَهُۥ۝١٨

    Min ayyi shayin khalaqahu

    Daga wane abu, (Allah) Ya halitta shi?

  19. مِن نُّطْفَةٍ خَلَقَهُۥ فَقَدَّرَهُۥ۝١٩

    Min nutfatin khalaqahu faqaddarahu

    Daga ɗigon maniyyi, Ya halitta shi sa'an nan Ya ƙaddarã shi (ga halaye).

  20. ثُمَّ ٱلسَّبِيلَ يَسَّرَهُۥ۝٢٠

    Thumma alssabeela yassarahu

    Sa'an nan, hanyarsa ta fita Ya sauƙaƙe masa.

  21. ثُمَّ أَمَاتَهُۥ فَأَقْبَرَهُۥ۝٢١

    Thumma amatahu faaqbarahu

    Sa'an nan, Ya matar da shi sai Ya sanya shi a cikin kabari.

  22. ثُمَّ إِذَا شَآءَ أَنشَرَهُۥ۝٢٢

    Thumma itha shaa ansharahu

    Sa'an nan, idan Ya so lalle ne zai tãyar da shi.

  23. كَلَّا لَمَّا يَقْضِ مَآ أَمَرَهُۥ۝٢٣

    Kalla lamma yaqdi ma amarahu

    Haƙĩƙa bai i da aikata abin da Allah Ya umurce shi ba (lõkacin sanya shi a cikin kabari).

  24. فَلْيَنظُرِ ٱلْإِنسَـٰنُ إِلَىٰ طَعَامِهِۦٓ۝٢٤

    Falyanthuri alinsanu ila taʿamihi

    To, mutum ya dũba zuwa ga abincinsa.

  25. أَنَّا صَبَبْنَا ٱلْمَآءَ صَبًّا۝٢٥

    Anna sababna almaa sabban

    Lalle ne Mũ, Mun zuo ruwa, zubõwa.

  26. ثُمَّ شَقَقْنَا ٱلْأَرْضَ شَقًّا۝٢٦

    Thumma shaqaqna alarda shaqqan

    Sa'an nan, Muka tsattsãge ƙasa tsattsagewa.

  27. فَأَنۢبَتْنَا فِيهَا حَبًّا۝٢٧

    Faanbatna feeha habban

    Sa'an nan, Muka tsirar da ƙwaya, a cikinta.

  28. وَعِنَبًا وَقَضْبًا۝٢٨

    Waʿinaban waqadban

    Da inabi da ciyãwa.

  29. وَزَيْتُونًا وَنَخْلًا۝٢٩

    Wazaytoonan wanakhlan

    Da zaitũni da itãcen dabĩno.

  30. وَحَدَآئِقَ غُلْبًا۝٣٠

    Wahadaiqa ghulban

    Da lambuna, mãsu yawan itãce.

  31. وَفَـٰكِهَةً وَأَبًّا۝٣١

    Wafakihatan waabban

    Da 'yã'yan itãcen marmari, da makiyãyã ta dabbõbi.

  32. مَّتَـٰعًا لَّكُمْ وَلِأَنْعَـٰمِكُمْ۝٣٢

    Mataʿan lakum walianʿamikum

    Domin jin dãɗi a gare ku, ku da dabbobinku.

  33. فَإِذَا جَآءَتِ ٱلصَّآخَّةُ۝٣٣

    Faitha jaati alssakhkhatu

    To, idan mai tsãwa (busa ta biyu) ta zo.

  34. يَوْمَ يَفِرُّ ٱلْمَرْءُ مِنْ أَخِيهِ۝٣٤

    Yawma yafirru almaro min akheehi

    Rãnar da mutum yake gudu daga ɗan'uwansa.

  35. وَأُمِّهِۦ وَأَبِيهِ۝٣٥

    Waommihi waabeehi

    Da uwarsa da ubansa.

  36. وَصَـٰحِبَتِهِۦ وَبَنِيهِ۝٣٦

    Wasahibatihi wabaneehi

    Da mãtarsa da ɗiyansa.

  37. لِكُلِّ ٱمْرِئٍ مِّنْهُمْ يَوْمَئِذٍ شَأْنٌ يُغْنِيهِ۝٣٧

    Likulli imriin minhum yawmaithin shanun yughneehi

    Ga kõwane mutum daga cikinsu, a rãnar nan akwai wani sha'ani da ya ishe shi.

  38. وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ مُّسْفِرَةٌ۝٣٨

    Wujoohun yawmaithin musfiratun

    Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu haske ne.

  39. ضَاحِكَةٌ مُّسْتَبْشِرَةٌ۝٣٩

    Dahikatun mustabshiratun

    Mãsu dãriya ne, mãsu bushãra.

  40. وَوُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ عَلَيْهَا غَبَرَةٌ۝٤٠

    Wawujoohun yawmaithin ʿalayha ghabaratun

    Wasu huskõki, a rãnar nan, akwai ƙũra a kansu.

  41. تَرْهَقُهَا قَتَرَةٌ۝٤١

    Tarhaquha qataratun

    Baƙi zai rufe su.

  42. أُو۟لَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلْكَفَرَةُ ٱلْفَجَرَةُ۝٤٢

    Olaika humu alkafaratu alfajaratu

    Waɗannan sũ ne kãfirai fãjirai (ga ayyukansu).

Tambayoyin da ake yawan yi

Mece ce ma’anar sunan Suratul Abasa?

Ma’anar Abasa ita ce “Ya ɗaure fuska”.

Suratul Abasa tana cikin juz’i na nawa?

Suratul Abasa tana cikin juz’i na 30.

Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Abasa?

Suratul Abasa tana da ayoyi 42.

Suratul Abasa Makkiya ce ko Madaniya?

Suratul Abasa sura ce Makkiya.

Suratul Abasa ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?

Ita ce sura ta 80 a cikin Alƙur’ani.

Majiyoyi

  • Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
  • Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
  • Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
  • Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
  • Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
  • Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.

Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.

Saitunan karatu

Rubutun Alƙur’ani
Girman Larabci
100%
Girman fassara
100%
Kamanni

Ƙara zuwa Allon Gida

ReadSurahBuɗe ReadSurah daga allon gida, a cikakken allo. Surorin da kuka karanta suna buɗewa ko da babu intanet.

  1. A cikin Safari, taɓa maɓallin “Share”. A sababbin iPhone yana cikin menu na •••.
  2. Taɓa “Add to Home Screen”. Gungura ƙasa idan ba ku gan shi ba.
  3. Taɓa “Add”.