سورة النازعات
Suratul Nazi’at da fassarar Hausa
Masu fizgewa
- 79
- ayoyi 46
- Makkiya
- Juz’i 30
- Shafuka 583–584
Suratul Nazi’at (النازعات) ita ce sura ta 79 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 46. Ma’anar sunanta ita ce “Masu fizgewa”. Sura ce Makkiya, wadda ta sauka a Makka kafin Hijira, kuma tana cikin juz’i na 30.
A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Nazi’at gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.
Suratul Nazi’at cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ
-
وَٱلنَّـٰزِعَـٰتِ غَرْقًا١
Waalnnaziʿati gharqan
Ina rantsuwa da mala'iku mãsu fisgar rãyuka (na kafirai) da ƙarfi.
-
وَٱلنَّـٰشِطَـٰتِ نَشْطًا٢
Waalnnashitati nashtan
Da mãsu ɗibar rãyuka (na mũminai) da sauƙi a cikin nishãɗi.
-
وَٱلسَّـٰبِحَـٰتِ سَبْحًا٣
Waalssabihati sabhan
Da mãsu sauka daga sama da umurnin Allah kamar suna iyo.
-
فَٱلسَّـٰبِقَـٰتِ سَبْقًا٤
Faalssabiqati sabqan
Sa'an nan, su zama mãsu gaugãwa (da umarnin Allah) kamar suna tsẽre.
-
فَٱلْمُدَبِّرَٰتِ أَمْرًا٥
Faalmudabbirati amran
Sa, an nan, su kasance masu shirya gudanar da umarni.
-
يَوْمَ تَرْجُفُ ٱلرَّاجِفَةُ٦
Yawma tarjufu alrrajifatu
Rãnar da mai girgiza abũbuwa (bũsar farko) zã ta kaɗa.
-
تَتْبَعُهَا ٱلرَّادِفَةُ٧
Tatbaʿuha alrradifatu
Mai biyar ta (bũsa ta biyu) nã biye.
-
قُلُوبٌ يَوْمَئِذٍ وَاجِفَةٌ٨
Quloobun yawmaithin wajifatun
Wasu zukãta, a rãnar nan, mãsu jin tsõro ne.
-
أَبْصَـٰرُهَا خَـٰشِعَةٌ٩
Absaruha khashiʿatun
Alhãli idãnunsu na ƙasƙantattu.
-
يَقُولُونَ أَءِنَّا لَمَرْدُودُونَ فِى ٱلْحَافِرَةِ١٠
Yaqooloona ainna lamardoodoona fee alhafirati
Sunã cẽwa "Ashe lalle zã a iya mayar da mu a kan sãwunmu?
-
أَءِذَا كُنَّا عِظَـٰمًا نَّخِرَةً١١
Aitha kunna ʿithaman nakhiratan
"Ashe, idan muka zama ƙasusuwa rududdugaggu?"
-
قَالُوا۟ تِلْكَ إِذًا كَرَّةٌ خَاسِرَةٌ١٢
Qaloo tilka ithan karratun khasiratun
Suka ce: "Waccan kam kõmãwa ce, tãɓaɓɓiya!"
-
فَإِنَّمَا هِىَ زَجْرَةٌ وَٰحِدَةٌ١٣
Fainnama hiya zajratun wahidatun
To, ita kam, tsãwa guda kawai ce.
-
فَإِذَا هُم بِٱلسَّاهِرَةِ١٤
Faitha hum bialssahirati
Sai kawai gã su a bãyan ƙasa.
-
هَلْ أَتَىٰكَ حَدِيثُ مُوسَىٰٓ١٥
Hal ataka hadeethu moosa
Shin, lãbãrin Mũsã ya zo maka?
-
إِذْ نَادَىٰهُ رَبُّهُۥ بِٱلْوَادِ ٱلْمُقَدَّسِ طُوًى١٦
Ith nadahu rabbuhu bialwadi almuqaddasi tuwan
A lõkacin da Ubangijinsa Ya kirãye shi, a cikin kwari mai tsarki, wato Duwã?
-
ٱذْهَبْ إِلَىٰ فِرْعَوْنَ إِنَّهُۥ طَغَىٰ١٧
Ithhab ila firʿawna innahu tagha
Ka tafi zuwa ga Fir'auna, lalle ne shi, ya ƙẽtare haddi.
-
فَقُلْ هَل لَّكَ إِلَىٰٓ أَن تَزَكَّىٰ١٨
Faqul hal laka ila an tazakka
"Sai ka ce masa, Kõ zã ka so ka tsarkaka.
-
وَأَهْدِيَكَ إِلَىٰ رَبِّكَ فَتَخْشَىٰ١٩
Waahdiyaka ila rabbika fatakhsha
"Kuma in shiryar da kai zuwa ga Ubangijinka domin ka ji tsoron Sa?"
-
فَأَرَىٰهُ ٱلْـَٔايَةَ ٱلْكُبْرَىٰ٢٠
Faarahu alayata alkubra
Sai ya nũna masa ãyar1 nan mafi girma.
Bayanai
[1] Ãyar Mũsã da ta fi girma ita ce sandarsa mai zama maciji ko hannunsa mai haske kamar tõcila idan yã sanya cikin hammata yã fitar. -
فَكَذَّبَ وَعَصَىٰ٢١
Fakaththaba waʿasa
Sai ya ƙaryata, kuma ya sãɓa (umurni),
-
ثُمَّ أَدْبَرَ يَسْعَىٰ٢٢
Thumma adbara yasʿa
Sa'an nan ya jũya bãya, yanã tafiya da sauri.
-
فَحَشَرَ فَنَادَىٰ٢٣
Fahashara fanada
Sai ya yi gayya, sa'an nan ya yi kira.
-
فَقَالَ أَنَا۠ رَبُّكُمُ ٱلْأَعْلَىٰ٢٤
Faqala ana rabbukumu alaʿla
Sai ya ce: "Nĩ ne Ubangijinku mafi ɗaudaka."
-
فَأَخَذَهُ ٱللَّهُ نَكَالَ ٱلْـَٔاخِرَةِ وَٱلْأُولَىٰٓ٢٥
Faakhathahu Allahu nakala alakhirati waaloola
Sabõda haka Allah Ya kama shi, dõmin azãbar maganar ƙarshe da ta farko.
-
إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَعِبْرَةً لِّمَن يَخْشَىٰٓ٢٦
Inna fee thalika laʿibratan liman yakhsha
Lalle ne, a cikin wannan haƙiƙa akwai abin kula ga wanda yake tsõron Allah.
-
ءَأَنتُمْ أَشَدُّ خَلْقًا أَمِ ٱلسَّمَآءُ ۚ بَنَىٰهَا٢٧
Aantum ashaddu khalqan ami alssamao banaha
Shin, kũ ne mafi wuyar halitta ko sama? Allah Ya gina ta.
-
رَفَعَ سَمْكَهَا فَسَوَّىٰهَا٢٨
Rafaʿa samkaha fasawwaha
Ya ɗaukaka rufinta, sa'an nan Ya daidaita ta.
-
وَأَغْطَشَ لَيْلَهَا وَأَخْرَجَ ضُحَىٰهَا٢٩
Waaghtasha laylaha waakhraja duhaha
Kuma Ya duhuntar da darenta, kuma Ya fitar da hantsinta.
-
وَٱلْأَرْضَ بَعْدَ ذَٰلِكَ دَحَىٰهَآ٣٠
Waalarda baʿda thalika dahaha
Kuma, ƙasa a bayan haka Ya mulmula ta.
-
أَخْرَجَ مِنْهَا مَآءَهَا وَمَرْعَىٰهَا٣١
Akhraja minha maaha wamarʿaha
Ya fitar da ruwanta daga gare ta da makiyãyarta.
-
وَٱلْجِبَالَ أَرْسَىٰهَا٣٢
Waaljibala arsaha
Da duwatsu, Yã kafe ta.
-
مَتَـٰعًا لَّكُمْ وَلِأَنْعَـٰمِكُمْ٣٣
Mataʿan lakum walianʿamikum
Domin jiyarwa dãɗi a gare ku, kuma ga dabbõbinku.
-
فَإِذَا جَآءَتِ ٱلطَّآمَّةُ ٱلْكُبْرَىٰ٣٤
Faitha jaati alttammatu alkubra
To, idan uwar masĩfu, mafi girma, ta zo.
-
يَوْمَ يَتَذَكَّرُ ٱلْإِنسَـٰنُ مَا سَعَىٰ٣٥
Yawma yatathakkaru alinsanu ma saʿa
Rãnar da mutum zai yi tunãnin abin da ya aikata.
-
وَبُرِّزَتِ ٱلْجَحِيمُ لِمَن يَرَىٰ٣٦
Waburrizati aljaheemu liman yara
Kuma, a bayyana Jahĩm ga mai gani.
-
فَأَمَّا مَن طَغَىٰ٣٧
Faamma man tagha
To, amma wanda ya yi girman kai.
-
وَءَاثَرَ ٱلْحَيَوٰةَ ٱلدُّنْيَا٣٨
Waathara alhayata alddunya
Kuma, ya zãɓi rãyuwa ta kusa, (wato dũniya).
-
فَإِنَّ ٱلْجَحِيمَ هِىَ ٱلْمَأْوَىٰ٣٩
Fainna aljaheema hiya almawa
To, lalle ne Jahĩm, ita ce makõma.
-
وَأَمَّا مَنْ خَافَ مَقَامَ رَبِّهِۦ وَنَهَى ٱلنَّفْسَ عَنِ ٱلْهَوَىٰ٤٠
Waama man khafa maqama rabbihi wanaha alnnafsa ʿani alhawa
Kuma, amma wanda ya ji tsõron tsayi a gaba ga Ubangijinsa, kuma ya kange kansa daga son rai.
-
فَإِنَّ ٱلْجَنَّةَ هِىَ ٱلْمَأْوَىٰ٤١
Fainna aljannata hiya almawa
To, lalle ne Aljanna ita ce makõma.
-
يَسْـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلسَّاعَةِ أَيَّانَ مُرْسَىٰهَا٤٢
Yasaloonaka ʿani alssaʿati ayyana mursaha
Sunã tambayar ka game da sa'a, wai yaushe ne matabbatarta?
-
فِيمَ أَنتَ مِن ذِكْرَىٰهَآ٤٣
Feema anta min thikraha
Me ya haɗã ka da ambatonta?
-
إِلَىٰ رَبِّكَ مُنتَهَىٰهَآ٤٤
Ila rabbika muntahaha
Zuwa ga Ubangijinka ƙarshen al'amarinta yake.
-
إِنَّمَآ أَنتَ مُنذِرُ مَن يَخْشَىٰهَا٤٥
Innama anta munthiru man yakhshaha
Kai mai gargaɗi kawai ne ga mai tsõron ta.
-
كَأَنَّهُمْ يَوْمَ يَرَوْنَهَا لَمْ يَلْبَثُوٓا۟ إِلَّا عَشِيَّةً أَوْ ضُحَىٰهَا٤٦
Kaannahum yawma yarawnaha lam yalbathoo illa ʿashiyyatan aw duhaha
Kamar sũ a rãnar da zã su gan ta, ba su zauna ba fãce a lõkacin marẽce ko hantsinsa.
Tambayoyin da ake yawan yi
Mece ce ma’anar sunan Suratul Nazi’at?
Ma’anar Nazi’at ita ce “Masu fizgewa”.
Suratul Nazi’at tana cikin juz’i na nawa?
Suratul Nazi’at tana cikin juz’i na 30.
Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Nazi’at?
Suratul Nazi’at tana da ayoyi 46.
Suratul Nazi’at Makkiya ce ko Madaniya?
Suratul Nazi’at sura ce Makkiya.
Suratul Nazi’at ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?
Ita ce sura ta 79 a cikin Alƙur’ani.
Majiyoyi
- Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
- Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
- Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
- Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
- Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
- Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.
Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.