سورة التكوير

Suratul Takwir da fassarar Hausa

Naɗewa

Mushafi

Mishary Rashid AlafasySauke MP3Sauke PDF

Suratul Takwir (التكوير) ita ce sura ta 81 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 29. Ma’anar sunanta ita ce “Naɗewa”. Sura ce Makkiya, wadda ta sauka a Makka kafin Hijira, kuma tana cikin juz’i na 30.

A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Takwir gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.

Suratul Takwir cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. إِذَا ٱلشَّمْسُ كُوِّرَتْ۝١

    Itha alshshamsu kuwwirat

    Idan rãna aka shafe haskenta

  2. وَإِذَا ٱلنُّجُومُ ٱنكَدَرَتْ۝٢

    Waitha alnnujoomu inkadarat

    Kuma idan taurãri suka gurɓãce (wani ya shiga a cikin wani).

  3. وَإِذَا ٱلْجِبَالُ سُيِّرَتْ۝٣

    Waitha aljibalu suyyirat

    Kuma idan duwãtsu aka tafiyar da su.

  4. وَإِذَا ٱلْعِشَارُ عُطِّلَتْ۝٤

    Waitha alʿisharu ʿuttilat

    Kuma idan rãƙuma mãsu cikunna1 aka sakẽ su wãwai, bã ga kõwa ba.

    Bayanai
    [1] Rãƙuma mãsu ciki ɗan wata gõma.
  5. وَإِذَا ٱلْوُحُوشُ حُشِرَتْ۝٥

    Waitha alwuhooshu hushirat

    Kuma idan dabbõbin dãji aka tattara su.

  6. وَإِذَا ٱلْبِحَارُ سُجِّرَتْ۝٦

    Waitha albiharu sujjirat

    Kuma idan tẽkuna aka mayar da su wuta.

  7. وَإِذَا ٱلنُّفُوسُ زُوِّجَتْ۝٧

    Waitha alnnufoosu zuwwijat

    Kuma idan rãyuka aka haɗa1 su da jikunkunansu.

    Bayanai
    [1] Ko kuma, aka haɗa kõwane mutum da irin mutãnensa a Aljanna ko a wuta.
  8. وَإِذَا ٱلْمَوْءُۥدَةُ سُئِلَتْ۝٨

    Waitha almawoodatu suilat

    Kuma idan wadda aka turbuɗe1 ta da rai aka tambaye ta.

    Bayanai
    [1] A cikin zãmanin jahiliyya Lãrabãwa bã su son a haifa musu 'ya'ya mãta dõmin haka har sukan turbuɗe 'ya'yansu dõmin kada su yi abin kunya ko kuma su talauce wajen yi musu aure.
  9. بِأَىِّ ذَنۢبٍ قُتِلَتْ۝٩

    Biayyi thanbin qutilat

    "Sabõda wane laifi ne aka kashe ta?"

  10. وَإِذَا ٱلصُّحُفُ نُشِرَتْ۝١٠

    Waitha alssuhufu nushirat

    Idan takardun ayyuka aka wãtsa su (ga mãsu su).

  11. وَإِذَا ٱلسَّمَآءُ كُشِطَتْ۝١١

    Waitha alssamao kushitat

    Kuma idan sama aka fẽɗe ta.

  12. وَإِذَا ٱلْجَحِيمُ سُعِّرَتْ۝١٢

    Waitha aljaheemu suʿʿirat

    Kuma idan Jahĩm aka hũra ta

  13. وَإِذَا ٱلْجَنَّةُ أُزْلِفَتْ۝١٣

    Waitha aljannatu ozlifat

    Kuma idan Aljanna aka kusantar da ita.

  14. عَلِمَتْ نَفْسٌ مَّآ أَحْضَرَتْ۝١٤

    ʿAlimat nafsun ma ahdarat

    Rai ya san abin da ya halartar (a rãnar nan).

  15. فَلَآ أُقْسِمُ بِٱلْخُنَّسِ۝١٥

    Fala oqsimu bialkhunnasi

    To, ba sai Na yi rantsuwa da taurãri matafã1 ba.

    Bayanai
    [1] Masu tafiya suna kõmawa bãya.
  16. ٱلْجَوَارِ ٱلْكُنَّسِ۝١٦

    Aljawari alkunnasi

    Mãsu gudu suna ɓũya.

  17. وَٱلَّيْلِ إِذَا عَسْعَسَ۝١٧

    Waallayli itha ʿasʿasa

    Da dare idan ya bãyar da bãya.

  18. وَٱلصُّبْحِ إِذَا تَنَفَّسَ۝١٨

    Waalssubhi itha tanaffasa

    Da sãfiya idan ta yi lumfashi.

  19. إِنَّهُۥ لَقَوْلُ رَسُولٍ كَرِيمٍ۝١٩

    Innahu laqawlu rasoolin kareemin

    Lalle ne shi (Alƙur'ãni) haƙƙan, maganar wani manzon (Allah) ne mai girma ga Allah.

  20. ذِى قُوَّةٍ عِندَ ذِى ٱلْعَرْشِ مَكِينٍ۝٢٠

    Thee quwwatin ʿinda thee alʿarshi makeenin

    Mai ƙarfi, mai daraja a wurin Mai Al'arshi.

  21. مُّطَاعٍ ثَمَّ أَمِينٍ۝٢١

    Mutaʿin thamma ameenin

    Wanda ake yi wa ɗã'a (wato shugaban malã'iku) ne a can, amintacce.

  22. وَمَا صَاحِبُكُم بِمَجْنُونٍ۝٢٢

    Wama sahibukum bimajnoonin

    Kuma abokinku ba mahaukaci ba ne.

  23. وَلَقَدْ رَءَاهُ بِٱلْأُفُقِ ٱلْمُبِينِ۝٢٣

    Walaqad raahu bialofuqi almubeeni

    Kuma lalle ne, yã gan shi1 a cikin sararin sama mabayyani.

    Bayanai
    [1] Annabi ya ga Mala'ika Jibirilu ya san shi. Sabõda haka wani aljani bã zai yi kama da shi ba balle ya kãwo masa ƙarya.
  24. وَمَا هُوَ عَلَى ٱلْغَيْبِ بِضَنِينٍ۝٢٤

    Wama huwa ʿala alghaybi bidaneenin

    Kuma shi, ga gaibi1 bã mai rowa ba ne.

    Bayanai
    [1] Ma'anar gaibi a nan, ilmin da Allah Ya aiko Jibirilu da shi zuwa ga Annabi Annabi ba ya ɓõye shi daga mutãne. Ga wata ƙira'a, wanda ake tuhuma, wãto ba a tuhumar Annabi, ga gaibin da ya faɗi cewa daga Allah yake, wato Alƙur'ãni duka gaskiya ne.
  25. وَمَا هُوَ بِقَوْلِ شَيْطَـٰنٍ رَّجِيمٍ۝٢٥

    Wama huwa biqawli shaytanin rajeemin

    Kuma shi (Alƙur'ani) bã maganar shaiɗani, wanda aka la'ana, ba ce.

  26. فَأَيْنَ تَذْهَبُونَ۝٢٦

    Faayna tathhaboona

    Shin, a inã zã ku tafi?

  27. إِنْ هُوَ إِلَّا ذِكْرٌ لِّلْعَـٰلَمِينَ۝٢٧

    In huwa illa thikrun lilʿalameena

    Lalle ne shi (Alƙur'ãni), bã kõme ba ne fãce gargaɗi ga talikai.

  28. لِمَن شَآءَ مِنكُمْ أَن يَسْتَقِيمَ۝٢٨

    Liman shaa minkum an yastaqeema

    Ga wanda ya so, daga cikinku, ya shiryu.

  29. وَمَا تَشَآءُونَ إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُ رَبُّ ٱلْعَـٰلَمِينَ۝٢٩

    Wama tashaoona illa an yashaa Allahu rabbu alʿalameena

    Kuma bã zã ku so ba sai idan Allah Ubangijin halitta Yã yarda.

Tambayoyin da ake yawan yi

Mece ce ma’anar sunan Suratul Takwir?

Ma’anar Takwir ita ce “Naɗewa”.

Suratul Takwir tana cikin juz’i na nawa?

Suratul Takwir tana cikin juz’i na 30.

Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Takwir?

Suratul Takwir tana da ayoyi 29.

Suratul Takwir Makkiya ce ko Madaniya?

Suratul Takwir sura ce Makkiya.

Suratul Takwir ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?

Ita ce sura ta 81 a cikin Alƙur’ani.

Majiyoyi

  • Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
  • Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
  • Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
  • Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
  • Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
  • Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.

Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.

Saitunan karatu

Rubutun Alƙur’ani
Girman Larabci
100%
Girman fassara
100%
Kamanni

Ƙara zuwa Allon Gida

ReadSurahBuɗe ReadSurah daga allon gida, a cikakken allo. Surorin da kuka karanta suna buɗewa ko da babu intanet.

  1. A cikin Safari, taɓa maɓallin “Share”. A sababbin iPhone yana cikin menu na •••.
  2. Taɓa “Add to Home Screen”. Gungura ƙasa idan ba ku gan shi ba.
  3. Taɓa “Add”.