سورة الإنفطار

Suratul Infiɗar da fassarar Hausa

Tsagewa

Mushafi

Mishary Rashid AlafasySauke MP3Sauke PDF

Suratul Infiɗar (الإنفطار) ita ce sura ta 82 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 19. Ma’anar sunanta ita ce “Tsagewa”. Sura ce Makkiya, wadda ta sauka a Makka kafin Hijira, kuma tana cikin juz’i na 30.

A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Infiɗar gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.

Suratul Infiɗar cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. إِذَا ٱلسَّمَآءُ ٱنفَطَرَتْ۝١

    Itha alssamao infatarat

    Idan sama ta tsãge.

  2. وَإِذَا ٱلْكَوَاكِبُ ٱنتَثَرَتْ۝٢

    Waitha alkawakibu intatharat

    Kuma idan taurãri suka wãtse.

  3. وَإِذَا ٱلْبِحَارُ فُجِّرَتْ۝٣

    Waitha albiharu fujjirat

    Kuma idan tẽkuna aka facce su.

  4. وَإِذَا ٱلْقُبُورُ بُعْثِرَتْ۝٤

    Waitha alqubooru buʿthirat

    Kuma idan kaburbura aka tõne su.

  5. عَلِمَتْ نَفْسٌ مَّا قَدَّمَتْ وَأَخَّرَتْ۝٥

    ʿAlimat nafsun ma qaddamat waakhkharat

    Rai yã san abin da ya gabatar, da abin da yã jinkirtar.

  6. يَـٰٓأَيُّهَا ٱلْإِنسَـٰنُ مَا غَرَّكَ بِرَبِّكَ ٱلْكَرِيمِ۝٦

    Ya ayyuha alinsanu ma gharraka birabbika alkareemi

    Yã kai mutum! Mẽ ya rũɗe ka game da Ubangijinka, Mai karamci.

  7. ٱلَّذِى خَلَقَكَ فَسَوَّىٰكَ فَعَدَلَكَ۝٧

    Allathee khalaqaka fasawwaka faʿadalaka

    Wanda Ya halitta ka sa'an nan ya daidaitã ka, Ya kuma tsakaitã ka.

  8. فِىٓ أَىِّ صُورَةٍ مَّا شَآءَ رَكَّبَكَ۝٨

    Fee ayyi sooratin ma shaa rakkabaka

    A cikin kõwace irin sũra Ya so Ya ginã ka a kanta.

  9. كَلَّا بَلْ تُكَذِّبُونَ بِٱلدِّينِ۝٩

    Kalla bal tukaththiboona bialddeeni

    A'aha, bã haka ba, kuna ƙaryatãwa game da sakamako!

  10. وَإِنَّ عَلَيْكُمْ لَحَـٰفِظِينَ۝١٠

    Wainna ʿalaykum lahafitheena

    Lalle ne, a kanku, haƙiƙa akwai matsara.

  11. كِرَامًا كَـٰتِبِينَ۝١١

    Kiraman katibeena

    Mãsu daraja, marubũta.

  12. يَعْلَمُونَ مَا تَفْعَلُونَ۝١٢

    Yaʿlamoona ma tafʿaloona

    Sunã sanin abin da kuke aikatãwa.

  13. إِنَّ ٱلْأَبْرَارَ لَفِى نَعِيمٍ۝١٣

    Inna alabrara lafee naʿeemin

    Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah, dãhir, suna cikin ni'ima.

  14. وَإِنَّ ٱلْفُجَّارَ لَفِى جَحِيمٍ۝١٤

    Wainna alfujjara lafee jaheemin

    Kuma lalle ne, fãjirai, dãhir, sunã cikin Jahĩm.

  15. يَصْلَوْنَهَا يَوْمَ ٱلدِّينِ۝١٥

    Yaslawnaha yawma alddeeni

    Zã su shigẽ ta a rãnar sakamako.

  16. وَمَا هُمْ عَنْهَا بِغَآئِبِينَ۝١٦

    Wama hum ʿanha bighaibeena

    Bã zã su faku daga gare ta ba.

  17. وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا يَوْمُ ٱلدِّينِ۝١٧

    Wama adraka ma yawmu alddeeni

    Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa ranar sakamako?

  18. ثُمَّ مَآ أَدْرَىٰكَ مَا يَوْمُ ٱلدِّينِ۝١٨

    Thumma ma adraka ma yawmu alddeeni

    Sa'an nan, mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rãnar sakamako?

  19. يَوْمَ لَا تَمْلِكُ نَفْسٌ لِّنَفْسٍ شَيْـًٔا ۖ وَٱلْأَمْرُ يَوْمَئِذٍ لِّلَّهِ۝١٩

    Yawma la tamliku nafsun linafsin shayan waalamru yawmaithin lillahi

    Rãnã ce da wani rai ba ya iya mallakar kõme dõmin wani rai al'amari, a rãnar nan, ga Allah (ɗai) yake.

Tambayoyin da ake yawan yi

Mece ce ma’anar sunan Suratul Infiɗar?

Ma’anar Infiɗar ita ce “Tsagewa”.

Suratul Infiɗar tana cikin juz’i na nawa?

Suratul Infiɗar tana cikin juz’i na 30.

Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Infiɗar?

Suratul Infiɗar tana da ayoyi 19.

Suratul Infiɗar Makkiya ce ko Madaniya?

Suratul Infiɗar sura ce Makkiya.

Suratul Infiɗar ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?

Ita ce sura ta 82 a cikin Alƙur’ani.

Majiyoyi

  • Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
  • Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
  • Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
  • Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
  • Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
  • Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.

Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.

Saitunan karatu

Rubutun Alƙur’ani
Girman Larabci
100%
Girman fassara
100%
Kamanni

Ƙara zuwa Allon Gida

ReadSurahBuɗe ReadSurah daga allon gida, a cikakken allo. Surorin da kuka karanta suna buɗewa ko da babu intanet.

  1. A cikin Safari, taɓa maɓallin “Share”. A sababbin iPhone yana cikin menu na •••.
  2. Taɓa “Add to Home Screen”. Gungura ƙasa idan ba ku gan shi ba.
  3. Taɓa “Add”.