Suratul Inshiƙaƙ (الإنشقاق) ita ce sura ta 84 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 25. Ma’anar sunanta ita ce “Kecewa”. Sura ce Makkiya, wadda ta sauka a Makka kafin Hijira, kuma tana cikin juz’i na 30.
A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Inshiƙaƙ gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.
Suratul Inshiƙaƙ cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ
-
إِذَا ٱلسَّمَآءُ ٱنشَقَّتْ١
Itha alssamao inshaqqat
Idan sama ta kẽce,
-
وَأَذِنَتْ لِرَبِّهَا وَحُقَّتْ٢
Waathinat lirabbiha wahuqqat
Ta saurari Ubangijinta, kuma aka wajabta mata yin saurãron,
-
وَإِذَا ٱلْأَرْضُ مُدَّتْ٣
Waitha alardu muddat
Kuma idan ƙasã aka mĩƙe ta,
-
وَأَلْقَتْ مَا فِيهَا وَتَخَلَّتْ٤
Waalqat ma feeha watakhallat
Kuma ta jẽfar da abin da yake a cikinta, tã wõfinta daga kõme.
-
وَأَذِنَتْ لِرَبِّهَا وَحُقَّتْ٥
Waathinat lirabbiha wahuqqat
Kuma ta saurãri Ubangijinta, aka wajabta mata yin saurãren,
-
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلْإِنسَـٰنُ إِنَّكَ كَادِحٌ إِلَىٰ رَبِّكَ كَدْحًا فَمُلَـٰقِيهِ٦
Ya ayyuha alinsanu innaka kadihun ila rabbika kadhan famulaqeehi
Ya kai mutum! Lalle ne kai mai aikin wahal da kai ne zuwa ga Ubangijinka, wahala mai tsanani, To, kai mai haɗuwa da Shi ne.
-
فَأَمَّا مَنْ أُوتِىَ كِتَـٰبَهُۥ بِيَمِينِهِۦ٧
Faama man ootiya kitabahu biyameenihi
To, amma wanda aka bai wa littãfinsa da damansa.
-
فَسَوْفَ يُحَاسَبُ حِسَابًا يَسِيرًا٨
Fasawfa yuhasabu hisaban yaseeran
To, za a yi masa hisãbi, hisãbi mai sauƙi.
-
وَيَنقَلِبُ إِلَىٰٓ أَهْلِهِۦ مَسْرُورًا٩
Wayanqalibu ila ahlihi masrooran
Kuma ya jũya zuwa ga iyãlinsa (a cikin Aljanna), yanã mai raha.
-
وَأَمَّا مَنْ أُوتِىَ كِتَـٰبَهُۥ وَرَآءَ ظَهْرِهِۦ١٠
Waamma man ootiya kitabahu waraa thahrihi
Kuma amma wanda aka bai wa littãfinsa, daga wajen bãyansa.
-
فَسَوْفَ يَدْعُوا۟ ثُبُورًا١١
Fasawfa yadʿoo thubooran
To, zã shi dinga kiran halaka!
-
وَيَصْلَىٰ سَعِيرًا١٢
Wayasla saʿeeran
Kuma ya shiga sa'ĩr.
-
إِنَّهُۥ كَانَ فِىٓ أَهْلِهِۦ مَسْرُورًا١٣
Innahu kana fee ahlihi masrooran
Lale ne shi, yã kasance (a dũniya) cikin iyãlinsa yanã mai raha.
-
إِنَّهُۥ ظَنَّ أَن لَّن يَحُورَ١٤
Innahu thanna an lan yahoora
Lalle ne yã yi zaton bã zai kõmo ba.
-
بَلَىٰٓ إِنَّ رَبَّهُۥ كَانَ بِهِۦ بَصِيرًا١٥
Bala inna rabbahu kana bihi baseeran
Na'am! Lalle ne, Ubangijinsa Ya kasance Mai gani gare shi.
-
فَلَآ أُقْسِمُ بِٱلشَّفَقِ١٦
Fala oqsimu bialshshafaqi
To, ba sai Nã rantse da shafaƙi ba.
-
وَٱلَّيْلِ وَمَا وَسَقَ١٧
Waallayli wama wasaqa
Da dare, da abin da ya ƙunsa.
-
وَٱلْقَمَرِ إِذَا ٱتَّسَقَ١٨
Waalqamari itha ittasaqa
Da watã idan (haskensa) ya cika.
-
لَتَرْكَبُنَّ طَبَقًا عَن طَبَقٍ١٩
Latarkabunna tabaqan ʿan tabaqin
Lalle ne kunã hawan wani hãli daga wani hãli.
-
فَمَا لَهُمْ لَا يُؤْمِنُونَ٢٠
Fama lahum la yuminoona
To, mẽ ya sãme su, ba su yin ĩmãni?
-
وَإِذَا قُرِئَ عَلَيْهِمُ ٱلْقُرْءَانُ لَا يَسْجُدُونَ ۩٢١
Waitha quria ʿalayhimu alquranu la yasjudoona
Kuma idan an karanta Alkur'ãni a kansu, bã su yin tawãli'u?
-
بَلِ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ يُكَذِّبُونَ٢٢
Bali allatheena kafaroo yukaththiboona
Ba haka ba! waɗanda suka kãfirta, sai ƙaryatãwa suke yi.
-
وَٱللَّهُ أَعْلَمُ بِمَا يُوعُونَ٢٣
WaAllahu aʿlamu bima yooʿoona
Alhãli Allah Shĩ ne Mafi sani ga abin a suke tãrãwa.
-
فَبَشِّرْهُم بِعَذَابٍ أَلِيمٍ٢٤
Fabashshirhum biʿathabin aleemin
Saboda haka, ka yi musu bushãra da azãba mai raɗaɗi.
-
إِلَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ لَهُمْ أَجْرٌ غَيْرُ مَمْنُونٍۭ٢٥
Illa allatheena amanoo waʿamiloo alssalihati lahum ajrun ghayru mamnoonin
Fãce waɗanda suka yi ĩmãni, suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da wani sakamako wanda bã ya yankẽwa.
Tambayoyin da ake yawan yi
Mece ce ma’anar sunan Suratul Inshiƙaƙ?
Ma’anar Inshiƙaƙ ita ce “Kecewa”.
Suratul Inshiƙaƙ tana cikin juz’i na nawa?
Suratul Inshiƙaƙ tana cikin juz’i na 30.
Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Inshiƙaƙ?
Suratul Inshiƙaƙ tana da ayoyi 25.
Suratul Inshiƙaƙ Makkiya ce ko Madaniya?
Suratul Inshiƙaƙ sura ce Makkiya.
Suratul Inshiƙaƙ ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?
Ita ce sura ta 84 a cikin Alƙur’ani.
Majiyoyi
- Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
- Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
- Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
- Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
- Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
- Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.
Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.