سورة المطففين
Suratul Muɗaffifin da fassarar Hausa
Masu tauye awo
- 83
- ayoyi 36
- Makkiya
- Juz’i 30
- Shafuka 587–589
Suratul Muɗaffifin (المطففين) ita ce sura ta 83 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 36. Ma’anar sunanta ita ce “Masu tauye awo”. Sura ce Makkiya, wadda ta sauka a Makka kafin Hijira, kuma tana cikin juz’i na 30.
A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Muɗaffifin gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.
Suratul Muɗaffifin cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ
-
وَيْلٌ لِّلْمُطَفِّفِينَ١
Waylun lilmutaffifeena
Bone ya tabbata ga mãsu naƙƙasãwa.
-
ٱلَّذِينَ إِذَا ٱكْتَالُوا۟ عَلَى ٱلنَّاسِ يَسْتَوْفُونَ٢
Allatheena itha iktaloo ʿala alnnasi yastawfoona
Waɗanda suke idan suka auna daga mutãne suna cika mũdu.
-
وَإِذَا كَالُوهُمْ أَو وَّزَنُوهُمْ يُخْسِرُونَ٣
Waitha kaloohum aw wazanoohum yukhsiroona
Kuma idan sun auna musu da zakka1 ko da sikẽli, suna ragẽwa
Bayanai
[1] Mũdu. -
أَلَا يَظُنُّ أُو۟لَـٰٓئِكَ أَنَّهُم مَّبْعُوثُونَ٤
Ala yathunnu olaika annahum mabʿoothoona
Ashe! Waɗancan bã su tabbata cẽwa lalle sũ, ana tãyar da su ba?
-
لِيَوْمٍ عَظِيمٍ٥
Liyawmin ʿatheemin
Domin yini mai girma.
-
يَوْمَ يَقُومُ ٱلنَّاسُ لِرَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ٦
Yawma yaqoomu alnnasu lirabbi alʿalameena
Yinin da mutãne ke tãshi zuwa ga Ubangijin halitta?
-
كَلَّآ إِنَّ كِتَـٰبَ ٱلْفُجَّارِ لَفِى سِجِّينٍ٧
Kalla inna kitaba alfujjari lafee sijjeenin
Haƙĩƙa lalle ne littãfin fãjirai dãhir, yana a cikin Sijjĩn.
-
وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا سِجِّينٌ٨
Wama adraka ma sijjeenun
Kuma, mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽ wa Sijjĩn?
-
كِتَـٰبٌ مَّرْقُومٌ٩
Kitabun marqoomun
Wani ittãfi ne rubũtacce.
-
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ١٠
Waylun yawmaithin lilmukaththibeena
Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa.
-
ٱلَّذِينَ يُكَذِّبُونَ بِيَوْمِ ٱلدِّينِ١١
Allatheena yukaththiboona biyawmi alddeeni
Waɗanda suke ƙaryatãwa game da rãnar sakamako.
-
وَمَا يُكَذِّبُ بِهِۦٓ إِلَّا كُلُّ مُعْتَدٍ أَثِيمٍ١٢
Wama yukaththibu bihi illa kullu muʿtadin atheemin
Babũ mai ƙaryatãwa gare shi fãce dukan mai ƙẽtare haddi mai yawan zunubi.
-
إِذَا تُتْلَىٰ عَلَيْهِ ءَايَـٰتُنَا قَالَ أَسَـٰطِيرُ ٱلْأَوَّلِينَ١٣
Itha tutla ʿalayhi ayatuna qala asateeru alawwaleena
Idan ana karãtun ãyõyinmu, a kansa, sai ya ce: tãtsũniyõyin mutãnen farko ne.
-
كَلَّا ۖ بَلْ ۜ رَانَ عَلَىٰ قُلُوبِهِم مَّا كَانُوا۟ يَكْسِبُونَ١٤
Kalla bal rana ʿala quloobihim ma kanoo yaksiboona
A'aha! Bã haka ba, abin da suka kasance suna aikatãwa dai, yã yi tsãtsa a cikin zukãtãnsu.
-
كَلَّآ إِنَّهُمْ عَن رَّبِّهِمْ يَوْمَئِذٍ لَّمَحْجُوبُونَ١٥
Kalla innahum ʿan rabbihim yawmaithin lamahjooboona
A'aha! Haƙĩƙa, lalle ne sũ daga Ubangijinsu, rãnar nan, waɗanda ake shãmakancẽwa ne.
-
ثُمَّ إِنَّهُمْ لَصَالُوا۟ ٱلْجَحِيمِ١٦
Thumma innahum lasaloo aljaheemi
Sa'an nan, lalle ne, sũ mãsu shiga cikin Jahĩm ne.
-
ثُمَّ يُقَالُ هَـٰذَا ٱلَّذِى كُنتُم بِهِۦ تُكَذِّبُونَ١٧
Thumma yuqalu hatha allathee kuntum bihi tukaththiboona
Sa'an nan a ce: "Wannan shi ne abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi."
-
كَلَّآ إِنَّ كِتَـٰبَ ٱلْأَبْرَارِ لَفِى عِلِّيِّينَ١٨
Kalla inna kitaba alabrari lafee ʿilliyyeena
A'aha! Haƙĩƙa lalle ne littãfin mãsu ɗã'ã yana a cikin Illiyyĩna?
-
وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا عِلِّيُّونَ١٩
Wama adraka ma ʿilliyyoona
Kuma mẽne ne yã sanar da kai abin da ake cẽwa Illiyyũna?
-
كِتَـٰبٌ مَّرْقُومٌ٢٠
Kitabun marqoomun
Wani littãfi ne rubũtacce.
-
يَشْهَدُهُ ٱلْمُقَرَّبُونَ٢١
Yashhaduhu almuqarraboona
Muƙarrabai1 suke halarta shi.
Bayanai
[1] Malã'iku masu daraja. -
إِنَّ ٱلْأَبْرَارَ لَفِى نَعِيمٍ٢٢
Inna alabrara lafee naʿeemin
Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah tabbas suna cikin ni'ima.
-
عَلَى ٱلْأَرَآئِكِ يَنظُرُونَ٢٣
ʿAla alaraiki yanthuroona
A kan karagu, suna ta kallo.
-
تَعْرِفُ فِى وُجُوهِهِمْ نَضْرَةَ ٱلنَّعِيمِ٢٤
Taʿrifu fee wujoohihim nadrata alnnaʿeemi
Kana sani a cikin fuskõkinsu, akwai kwarjinin ni'ima.
-
يُسْقَوْنَ مِن رَّحِيقٍ مَّخْتُومٍ٢٥
Yusqawna min raheeqin makhtoomin
Ana shãyar da sũ daga wata giya wadda aka yunƙe a kan rufinta.
-
خِتَـٰمُهُۥ مِسْكٌ ۚ وَفِى ذَٰلِكَ فَلْيَتَنَافَسِ ٱلْمُتَنَـٰفِسُونَ٢٦
Khitamuhu miskun wafee thalika falyatanafasi almutanafisoona
¡arshen kurɓinta miski ne. To, a cikin wannan, mãsu gwagwarmaya su yi ta gwagwarmayar nẽma.
-
وَمِزَاجُهُۥ مِن تَسْنِيمٍ٢٧
Wamizajuhu min tasneemin
Kuma abin da ake gauraya ta da shi, daga tasnĩm yake.
-
عَيْنًا يَشْرَبُ بِهَا ٱلْمُقَرَّبُونَ٢٨
ʿAynan yashrabu biha almuqarraboona
(Wato) wani marmaro ne wanda muƙarrabai ke sha daga gare shi.
-
إِنَّ ٱلَّذِينَ أَجْرَمُوا۟ كَانُوا۟ مِنَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ يَضْحَكُونَ٢٩
Inna allatheena ajramoo kanoo mina allatheena amanoo yadhakoona
Lalle ne, waɗanda suka kãfirta sun kasance (a dũniya) suna yi wa waɗanda suka yi ĩmãni dãriya.
-
وَإِذَا مَرُّوا۟ بِهِمْ يَتَغَامَزُونَ٣٠
Waitha marroo bihim yataghamazoona
Kuma idan sun shuɗe su sai su dinga yin zunɗe.
-
وَإِذَا ٱنقَلَبُوٓا۟ إِلَىٰٓ أَهْلِهِمُ ٱنقَلَبُوا۟ فَكِهِينَ٣١
Waitha inqalaboo ila ahlihimu inqalaboo fakiheena
Kuma idan suka jũya zuwa ga iyãlansu, sai su tafi suna kãkãci.
-
وَإِذَا رَأَوْهُمْ قَالُوٓا۟ إِنَّ هَـٰٓؤُلَآءِ لَضَآلُّونَ٣٢
Waitha raawhum qaloo inna haolai ladalloona
Kuma idan sun gan su sai su ce: "Lalle waɗannan ɓatattu ne."
-
وَمَآ أُرْسِلُوا۟ عَلَيْهِمْ حَـٰفِظِينَ٣٣
Wama orsiloo ʿalayhim hafitheena
Alhãli kuwa, ba a aike su ba dõmin su zama mãsu tsaro a kansu.
-
فَٱلْيَوْمَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ مِنَ ٱلْكُفَّارِ يَضْحَكُونَ٣٤
Faalyawma allatheena amanoo mina alkuffari yadhakoona
To, yau fa (a Lãhira] waɗanda suka yi ĩmãni, sũ ke yi wa kãfirai dãriya.
-
عَلَى ٱلْأَرَآئِكِ يَنظُرُونَ٣٥
ʿAla alaraiki yanthuroona
A kan karagu, suna ta kallo.
-
هَلْ ثُوِّبَ ٱلْكُفَّارُ مَا كَانُوا۟ يَفْعَلُونَ٣٦
Hal thuwwiba alkuffaru ma kanoo yafʿaloona
Shin an sãka ma kãfirai abin da suka kasance suna aikatawa?1
Bayanai
[1] Amsar tambaya "na'am.".
Tambayoyin da ake yawan yi
Mece ce ma’anar sunan Suratul Muɗaffifin?
Ma’anar Muɗaffifin ita ce “Masu tauye awo”.
Suratul Muɗaffifin tana cikin juz’i na nawa?
Suratul Muɗaffifin tana cikin juz’i na 30.
Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Muɗaffifin?
Suratul Muɗaffifin tana da ayoyi 36.
Suratul Muɗaffifin Makkiya ce ko Madaniya?
Suratul Muɗaffifin sura ce Makkiya.
Suratul Muɗaffifin ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?
Ita ce sura ta 83 a cikin Alƙur’ani.
Majiyoyi
- Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
- Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
- Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
- Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
- Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
- Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.
Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.