سورة البروج

Suratul Buruj da fassarar Hausa

Gidajen taurari

Mushafi

Mishary Rashid AlafasySauke MP3Sauke PDF

Suratul Buruj (البروج) ita ce sura ta 85 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 22. Ma’anar sunanta ita ce “Gidajen taurari”. Sura ce Makkiya, wadda ta sauka a Makka kafin Hijira, kuma tana cikin juz’i na 30.

A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Buruj gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.

Suratul Buruj cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. وَٱلسَّمَآءِ ذَاتِ ٱلْبُرُوجِ۝١

    Waalssamai thati alburooji

    Inã rantsuwa da sama mai taurãrin lissafin shekara.

  2. وَٱلْيَوْمِ ٱلْمَوْعُودِ۝٢

    Waalyawmi almawʿoodi

    Da yinin da aka yi alkawarin zuwansa,1

    Bayanai
    [1] Rãnar Ƙiyãma.
  3. وَشَاهِدٍ وَمَشْهُودٍ۝٣

    Washahidin wamashhoodin

    Da yini mai shaidu, da yini da ake halarta1 a cikinsa

    Bayanai
    [1] Rãnar Arafa.
  4. قُتِلَ أَصْحَـٰبُ ٱلْأُخْدُودِ۝٤

    Qutila ashabu alukhdoodi

    An la'ani mutãnen rãmi.1

    Bayanai
    [1] Mutãnen Najiran ne suka yi rãmi suka hũra wuta a ciki, dõmin su ƙõne wanda yã yi ĩmãni da addinin Masĩh Ĩsa dõmin su hana yãɗuwarsa. Suka umurci kõwane Musulmi ya jefa kansa a ciki, su kuma suna zazzaune suna kallo.
  5. ٱلنَّارِ ذَاتِ ٱلْوَقُودِ۝٥

    Alnnari thati alwaqoodi

    Wato wuta wadda aka hura.

  6. إِذْ هُمْ عَلَيْهَا قُعُودٌ۝٦

    Ith hum ʿalayha quʿoodun

    A lõkacin da suke a kan (gefen) ta a zazzaune.

  7. وَهُمْ عَلَىٰ مَا يَفْعَلُونَ بِٱلْمُؤْمِنِينَ شُهُودٌ۝٧

    Wahum ʿala ma yafʿaloona bialmumineena shuhoodun

    Alhãli sũ, bisa ga abin da suke aikatãwa ga mũminai, sunã halarce.

  8. وَمَا نَقَمُوا۟ مِنْهُمْ إِلَّآ أَن يُؤْمِنُوا۟ بِٱللَّهِ ٱلْعَزِيزِ ٱلْحَمِيدِ۝٨

    Wama naqamoo minhum illa an yuminoo biAllahi alʿazeezi alhameedi

    Kuma ba su tuhumce su ba, fãce kawai domin sun yi ĩmãni da Allah Mabuwãyi, wanda ake gõdewa.

  9. ٱلَّذِى لَهُۥ مُلْكُ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ۚ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍ شَهِيدٌ۝٩

    Allathee lahu mulku alssamawati waalardi waAllahu ʿala kulli shayin shaheedun

    Wanda Yake shi ne da mulkin sammai da ƙasa, kuma Allah a kan kõme halarce Yake.

  10. إِنَّ ٱلَّذِينَ فَتَنُوا۟ ٱلْمُؤْمِنِينَ وَٱلْمُؤْمِنَـٰتِ ثُمَّ لَمْ يَتُوبُوا۟ فَلَهُمْ عَذَابُ جَهَنَّمَ وَلَهُمْ عَذَابُ ٱلْحَرِيقِ۝١٠

    Inna allatheena fatanoo almumineena waalmuminati thumma lam yatooboo falahum ʿathabu jahannama walahum ʿathabu alhareeqi

    Lalle ne waɗanda suka fitini mũminai maza da mũminai mãta, sa'an nan ba su tũba ba to, sunã da azãbar Jahannama, kuma sunã da azãbar gõbara.

  11. إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ لَهُمْ جَنَّـٰتٌ تَجْرِى مِن تَحْتِهَا ٱلْأَنْهَـٰرُ ۚ ذَٰلِكَ ٱلْفَوْزُ ٱلْكَبِيرُ۝١١

    Inna allatheena amanoo waʿamiloo alssalihati lahum jannatun tajree min tahtiha alanharu thalika alfawzu alkabeeru

    Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashin gidãjen. Wancan abu fa shi ne rabo babba.

  12. إِنَّ بَطْشَ رَبِّكَ لَشَدِيدٌ۝١٢

    Inna batsha rabbika lashadeedun

    Lalle ne damƙar Ubangijinka mai tsanani ce ƙwarai.

  13. إِنَّهُۥ هُوَ يُبْدِئُ وَيُعِيدُ۝١٣

    Innahu huwa yubdio wayuʿeedu

    Lalle ne Shĩ, Shi ne Mai ƙãga halitta, kuma Ya mayar da ita (bãyan mutuwa).

  14. وَهُوَ ٱلْغَفُورُ ٱلْوَدُودُ۝١٤

    Wahuwa alghafooru alwadoodu

    Kuma Shi ne Mai gãfara, Mai bayyana sõyayya.

  15. ذُو ٱلْعَرْشِ ٱلْمَجِيدُ۝١٥

    Thoo alʿarshi almajeedi

    Mai Al'arshi mai girma

  16. فَعَّالٌ لِّمَا يُرِيدُ۝١٦

    Faʿʿalun lima yureedu

    Mai aikatãwa ga abin da Yake nufi.

  17. هَلْ أَتَىٰكَ حَدِيثُ ٱلْجُنُودِ۝١٧

    Hal ataka hadeethu aljunoodi

    Ko lãbãrin rundanõni yã zo maka.

  18. فِرْعَوْنَ وَثَمُودَ۝١٨

    Firʿawna wathamooda

    Fir'auna da samũdãwa?

  19. بَلِ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ فِى تَكْذِيبٍ۝١٩

    Bali allatheena kafaroo fee taktheebin

    Ã'aha! waɗanda suka kãfirta sunã cikin ƙaryatãwa.

  20. وَٱللَّهُ مِن وَرَآئِهِم مُّحِيطٌۢ۝٢٠

    WaAllahu min waraihim muheetun

    Alhãli, Allah daga bãyansu, Mai kẽwaye su ne (da sanin Sa).

  21. بَلْ هُوَ قُرْءَانٌ مَّجِيدٌ۝٢١

    Bal huwa quranun majeedun

    Ã'aha! Shi Alƙur'ãni ne mai girma.

  22. فِى لَوْحٍ مَّحْفُوظٍۭ۝٢٢

    Fee lawhin mahfoothin

    A cikin Allo tsararre.

Tambayoyin da ake yawan yi

Mece ce ma’anar sunan Suratul Buruj?

Ma’anar Buruj ita ce “Gidajen taurari”.

Suratul Buruj tana cikin juz’i na nawa?

Suratul Buruj tana cikin juz’i na 30.

Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Buruj?

Suratul Buruj tana da ayoyi 22.

Suratul Buruj Makkiya ce ko Madaniya?

Suratul Buruj sura ce Makkiya.

Suratul Buruj ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?

Ita ce sura ta 85 a cikin Alƙur’ani.

Majiyoyi

  • Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
  • Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
  • Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
  • Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
  • Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
  • Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.

Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.

Saitunan karatu

Rubutun Alƙur’ani
Girman Larabci
100%
Girman fassara
100%
Kamanni

Ƙara zuwa Allon Gida

ReadSurahBuɗe ReadSurah daga allon gida, a cikakken allo. Surorin da kuka karanta suna buɗewa ko da babu intanet.

  1. A cikin Safari, taɓa maɓallin “Share”. A sababbin iPhone yana cikin menu na •••.
  2. Taɓa “Add to Home Screen”. Gungura ƙasa idan ba ku gan shi ba.
  3. Taɓa “Add”.