سورة الطارق

Suratul Ɗariƙ da fassarar Hausa

Mai zuwa da dare

Mushafi

Mishary Rashid AlafasySauke MP3Sauke PDF

Suratul Ɗariƙ (الطارق) ita ce sura ta 86 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 17. Ma’anar sunanta ita ce “Mai zuwa da dare”. Sura ce Makkiya, wadda ta sauka a Makka kafin Hijira, kuma tana cikin juz’i na 30.

A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Ɗariƙ gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.

Suratul Ɗariƙ cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. وَٱلسَّمَآءِ وَٱلطَّارِقِ۝١

    Waalssamai waalttariqi

    Inã rantsuwa da sama da mai aukõwa da dare.

  2. وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا ٱلطَّارِقُ۝٢

    Wama adraka ma alttariqu

    To, mẽ yã sanar da kai abin da ake cẽwa mai aukõwa da dare?

  3. ٱلنَّجْمُ ٱلثَّاقِبُ۝٣

    Alnnajmu alththaqibu

    Shi ne taurãron nan mai tsananin haske.1

    Bayanai
    [1] Wannan ya yi kama da zuwan Annabi a cikin jahiliyya don ya haskaka duniya da ilimi kamar yadda girgije ke ba da ruwa saboda tsiron ƙasa, hantsar uwa ta ba da nono saboda jariri kuma maniyi ya zo lokacin Jima'i.
  4. إِن كُلُّ نَفْسٍ لَّمَّا عَلَيْهَا حَافِظٌ۝٤

    In kullu nafsin lamma ʿalayha hafithun

    Bãbu wani rai fãce a kansa akwai wani mai tsaro.

  5. فَلْيَنظُرِ ٱلْإِنسَـٰنُ مِمَّ خُلِقَ۝٥

    Falyanthuri alinsanu mimma khuliqa

    To, mutum ya dũba, daga mẽ aka halittã shi?

  6. خُلِقَ مِن مَّآءٍ دَافِقٍ۝٦

    Khuliqa min main dafiqin

    An halittã shi daga wani ruwa mai tunkuɗar jũna.

  7. يَخْرُجُ مِنۢ بَيْنِ ٱلصُّلْبِ وَٱلتَّرَآئِبِ۝٧

    Yakhruju min bayni alssulbi waalttaraibi

    Yanã fita daga tsakanin tsatso da karankarman ƙirji.

  8. إِنَّهُۥ عَلَىٰ رَجْعِهِۦ لَقَادِرٌ۝٨

    Innahu ʿala rajʿihi laqadirun

    Lalle ne Shi (Allah), ga mayar da shi (mutum), tabbas Mai iyãwa ne.

  9. يَوْمَ تُبْلَى ٱلسَّرَآئِرُ۝٩

    Yawma tubla alssarairu

    Rãnar da ake jarrabawar asirai.

  10. فَمَا لَهُۥ مِن قُوَّةٍ وَلَا نَاصِرٍ۝١٠

    Fama lahu min quwwatin wala nasirin

    Saboda haka, bã shi da wani ƙarfi, kuma bã shi da wani mai taimako (da zai iya kãre shi daga azãbar Allah).

  11. وَٱلسَّمَآءِ ذَاتِ ٱلرَّجْعِ۝١١

    Waalssamai thati alrrajʿi

    Ina rantsuwa da sama ma'abũciyar ruwa mai kõmãwa yana yankẽwa.

  12. وَٱلْأَرْضِ ذَاتِ ٱلصَّدْعِ۝١٢

    Waalardi thati alssadʿi

    Da ƙasa ma'abociyar tsãgẽwa,1

    Bayanai
    [1] Dõmin fitar tsiro.
  13. إِنَّهُۥ لَقَوْلٌ فَصْلٌ۝١٣

    Innahu laqawlun faslun

    Lalle ne shĩ (Alƙur'ãni), haƙĩƙa magana ce daki-daki1

    Bayanai
    [1] Mai rabewa tsakanin ƙarya da gaskiya.
  14. وَمَا هُوَ بِٱلْهَزْلِ۝١٤

    Wama huwa bialhazli

    Kuma shĩ bã bananci1 bane

    Bayanai
    [1] Kãkãci.
  15. إِنَّهُمْ يَكِيدُونَ كَيْدًا۝١٥

    Innahum yakeedoona kaydan

    Lalle ne sũ, suna ƙulla kaidi na sõsai.

  16. وَأَكِيدُ كَيْدًا۝١٦

    Waakeedu kaydan

    Kuma Ni, Ina mayar da kaidi (gare su) kamar yadda suke ƙulla kaidi.

  17. فَمَهِّلِ ٱلْكَـٰفِرِينَ أَمْهِلْهُمْ رُوَيْدًۢا۝١٧

    Famahhili alkafireena amhilhum ruwaydan

    Saboda haka, ka yi wa kafirai jinkiri, ka dakata musu, sannu-sannu.

Tambayoyin da ake yawan yi

Mece ce ma’anar sunan Suratul Ɗariƙ?

Ma’anar Ɗariƙ ita ce “Mai zuwa da dare”.

Suratul Ɗariƙ tana cikin juz’i na nawa?

Suratul Ɗariƙ tana cikin juz’i na 30.

Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Ɗariƙ?

Suratul Ɗariƙ tana da ayoyi 17.

Suratul Ɗariƙ Makkiya ce ko Madaniya?

Suratul Ɗariƙ sura ce Makkiya.

Suratul Ɗariƙ ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?

Ita ce sura ta 86 a cikin Alƙur’ani.

Majiyoyi

  • Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
  • Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
  • Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
  • Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
  • Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
  • Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.

Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.

Saitunan karatu

Rubutun Alƙur’ani
Girman Larabci
100%
Girman fassara
100%
Kamanni

Ƙara zuwa Allon Gida

ReadSurahBuɗe ReadSurah daga allon gida, a cikakken allo. Surorin da kuka karanta suna buɗewa ko da babu intanet.

  1. A cikin Safari, taɓa maɓallin “Share”. A sababbin iPhone yana cikin menu na •••.
  2. Taɓa “Add to Home Screen”. Gungura ƙasa idan ba ku gan shi ba.
  3. Taɓa “Add”.