Suratul Gashiya (الغاشية) ita ce sura ta 88 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 26. Ma’anar sunanta ita ce “Mai rufewa”. Sura ce Makkiya, wadda ta sauka a Makka kafin Hijira, kuma tana cikin juz’i na 30.
A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Gashiya gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.
Suratul Gashiya cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ
-
هَلْ أَتَىٰكَ حَدِيثُ ٱلْغَـٰشِيَةِ١
Hal ataka hadeethu alghashiyati
Lalle ne labãrin (¡iyãma) mai rufe mutãne da tsoronta yã zo maka?
-
وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ خَـٰشِعَةٌ٢
Wujoohun yawmaithin khashiʿatun
Wasu huskõki a rãnar nan ƙasƙantattu ne.
-
عَامِلَةٌ نَّاصِبَةٌ٣
ʿamilatun nasibatun
Mãsu aikin wahala ne, mãsu gajiya.
-
تَصْلَىٰ نَارًا حَامِيَةً٤
Tasla naran hamiyatan
Zã su shiga wata wuta mai zãfi.
-
تُسْقَىٰ مِنْ عَيْنٍ ءَانِيَةٍ٥
Tusqa min ʿaynin aniyatin
Ana shãyar da su daga wani marmaro mai zãfin ruwa.
-
لَّيْسَ لَهُمْ طَعَامٌ إِلَّا مِن ضَرِيعٍ٦
Laysa lahum taʿamun illa min dareeʿin
Ba su da wani abinci fãce dai daga danyi.
-
لَّا يُسْمِنُ وَلَا يُغْنِى مِن جُوعٍ٧
La yusminu wala yughnee min jooʿin
Bã ya sanya ƙiba, kuma bã zai wadãtar daga yunwa ba.
-
وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ نَّاعِمَةٌ٨
Wujoohun yawmaithin naʿimatun
Wasu huskõki a rãnar nan mãsu ni'ima ne.
-
لِّسَعْيِهَا رَاضِيَةٌ٩
Lisaʿyiha radiyatun
Game da aikinsu, masu yarda ne.
-
فِى جَنَّةٍ عَالِيَةٍ١٠
Fee jannatin ʿaliyatin
(Suna) a cikin Aljanna maɗaukakiya.
-
لَّا تَسْمَعُ فِيهَا لَـٰغِيَةً١١
La tasmaʿu feeha laghiyatan
Bã zã su ji yãsassar magana ba, a cikinta.
-
فِيهَا عَيْنٌ جَارِيَةٌ١٢
Feeha ʿaynun jariyatun
A cikinta akwai marmaro mai gudãna.
-
فِيهَا سُرُرٌ مَّرْفُوعَةٌ١٣
Feeha sururun marfooʿatun
A cikinta akwai gadãje maɗaukaka.
-
وَأَكْوَابٌ مَّوْضُوعَةٌ١٤
Waakwabun mawdooʿatun
Da kõfuna ar'aje.
-
وَنَمَارِقُ مَصْفُوفَةٌ١٥
Wanamariqu masfoofatun
Da filõli1 jẽre,
Bayanai
[1] Matãsan kai. -
وَزَرَابِىُّ مَبْثُوثَةٌ١٦
Wazarabiyyu mabthoothatun
Da katifu shimfiɗe.
-
أَفَلَا يَنظُرُونَ إِلَى ٱلْإِبِلِ كَيْفَ خُلِقَتْ١٧
Afala yanthuroona ila alibili kayfa khuliqat
Ashe to bã zã su dũbãwa ba ga rãƙumã yadda aka halitta su?
-
وَإِلَى ٱلسَّمَآءِ كَيْفَ رُفِعَتْ١٨
Waila alssamai kayfa rufiʿat
Da zuwa ga sama yadda aka ɗaukaka ta?
-
وَإِلَى ٱلْجِبَالِ كَيْفَ نُصِبَتْ١٩
Waila aljibali kayfa nusibat
Da zuwa ga duwãtsu yadda aka kafa su?
-
وَإِلَى ٱلْأَرْضِ كَيْفَ سُطِحَتْ٢٠
Waila alardi kayfa sutihat
Da zuwa ga ƙasa yadda aka shimfiɗã ta?
-
فَذَكِّرْ إِنَّمَآ أَنتَ مُذَكِّرٌ٢١
Fathakkir innama anta muthakkirun
sabõda haka, ka yi wa'azi, kai mai yin wa'azi ne kawai.
-
لَّسْتَ عَلَيْهِم بِمُصَيْطِرٍ٢٢
Lasta ʿalayhim bimusaytirin
Ba ka zama mai ĩkon tanƙwasãwa a kansu ba.
-
إِلَّا مَن تَوَلَّىٰ وَكَفَرَ٢٣
Illa man tawalla wakafara
Fãce dai duk wanda ya jũya bãya, kuma ya kãfirta.
-
فَيُعَذِّبُهُ ٱللَّهُ ٱلْعَذَابَ ٱلْأَكْبَرَ٢٤
Fayuʿaththibuhu Allahu alʿathaba alakbara
To, Allah zai yi masa azãba, azãbar nan da take mafi girma.
-
إِنَّ إِلَيْنَآ إِيَابَهُمْ٢٥
Inna ilayna iyabahum
Lalle ne, zuwa gare Mu kõmõwarsu take.
-
ثُمَّ إِنَّ عَلَيْنَا حِسَابَهُم٢٦
Thumma inna ʿalayna hisabahum
Sa'an nan lalle ne aikinMu ne Mu yi musu hisãbi.
Tambayoyin da ake yawan yi
Mece ce ma’anar sunan Suratul Gashiya?
Ma’anar Gashiya ita ce “Mai rufewa”.
Suratul Gashiya tana cikin juz’i na nawa?
Suratul Gashiya tana cikin juz’i na 30.
Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Gashiya?
Suratul Gashiya tana da ayoyi 26.
Suratul Gashiya Makkiya ce ko Madaniya?
Suratul Gashiya sura ce Makkiya.
Suratul Gashiya ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?
Ita ce sura ta 88 a cikin Alƙur’ani.
Majiyoyi
- Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
- Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
- Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
- Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
- Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
- Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.
Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.