سورة الفجر

Suratul Fajr da fassarar Hausa

Alfijir

Mushafi

Mishary Rashid AlafasySauke MP3Sauke PDF

Suratul Fajr (الفجر) ita ce sura ta 89 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 30. Ma’anar sunanta ita ce “Alfijir”. Sura ce Makkiya, wadda ta sauka a Makka kafin Hijira, kuma tana cikin juz’i na 30.

A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Fajr gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.

Suratul Fajr cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. وَٱلْفَجْرِ۝١

    Waalfajri

    Inã rantsuwa da alfijiri.

  2. وَلَيَالٍ عَشْرٍ۝٢

    Walayalin ʿashrin

    Da darũruwa gõma.

  3. وَٱلشَّفْعِ وَٱلْوَتْرِ۝٣

    Waalshshafʿi waalwatri

    Da (adadi na) cikã da (na) mãrã.

  4. وَٱلَّيْلِ إِذَا يَسْرِ۝٤

    Waallayli itha yasri

    Da dare idan yana shũɗewa.

  5. هَلْ فِى ذَٰلِكَ قَسَمٌ لِّذِى حِجْرٍ۝٥

    Hal fee thalika qasamun lithee hijrin

    Ko a cikin waɗannan akwai abin rantsuwa ga mai hankali (da yake kange shi daga zunubi)?

  6. أَلَمْ تَرَ كَيْفَ فَعَلَ رَبُّكَ بِعَادٍ۝٦

    Alam tara kayfa faʿala rabbuka biʿadin

    Ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata da Ãdãwa ba?

  7. إِرَمَ ذَاتِ ٱلْعِمَادِ۝٧

    Irama thati alʿimadi

    Iramawa mãsu sakon1 ƙĩrar jiki.

    Bayanai
    [1] Tsawo mai ma'ana.
  8. ٱلَّتِى لَمْ يُخْلَقْ مِثْلُهَا فِى ٱلْبِلَـٰدِ۝٨

    Allatee lam yukhlaq mithluha fee albiladi

    Waɗanda ba a halitta kwatankwacinsu ba a cikin garũruwa (na dũniya).

  9. وَثَمُودَ ٱلَّذِينَ جَابُوا۟ ٱلصَّخْرَ بِٱلْوَادِ۝٩

    Wathamooda allatheena jaboo alssakhra bialwadi

    Da samũdãwa waɗanda suka fasa duwãtsu a cikin Wadi1 suka yi gidãje)?

    Bayanai
    [1] Wãdil-ƙura, sunan wuri ne kusa da Madina wajen Syria, wato Sham.
  10. وَفِرْعَوْنَ ذِى ٱلْأَوْتَادِ۝١٠

    Wafirʿawna thee alawtadi

    Da Fir'auna mai turãku.

  11. ٱلَّذِينَ طَغَوْا۟ فِى ٱلْبِلَـٰدِ۝١١

    Allatheena taghaw fee albiladi

    Waɗanda suka ƙẽtare iyãkarsu, a cikin garũruwa?

  12. فَأَكْثَرُوا۟ فِيهَا ٱلْفَسَادَ۝١٢

    Faaktharoo feeha alfasada

    Sabõda haka, suka yawaita yin ɓarna a cikinsu.

  13. فَصَبَّ عَلَيْهِمْ رَبُّكَ سَوْطَ عَذَابٍ۝١٣

    Fasabba ʿalayhim rabbuka sawta ʿathabin

    Sabõda haka Ubangijinka Ya zuba musu bũlãlar azãba.

  14. إِنَّ رَبَّكَ لَبِٱلْمِرْصَادِ۝١٤

    Inna rabbaka labialmirsadi

    Lalle ne, Ubangijinka Yana nan a mafaka.

  15. فَأَمَّا ٱلْإِنسَـٰنُ إِذَا مَا ٱبْتَلَىٰهُ رَبُّهُۥ فَأَكْرَمَهُۥ وَنَعَّمَهُۥ فَيَقُولُ رَبِّىٓ أَكْرَمَنِ۝١٥

    Faamma alinsanu itha ma ibtalahu rabbuhu faakramahu wanaʿʿamahu fayaqoolu rabbee akramani

    To, amma fa mutum idan Ubangijibsa Ya jarraba shi, wãto Yã girmama shi kuma Ya yi masa ni'ima, sai ya ce: "Ubangijina Ya girmama ni."

  16. وَأَمَّآ إِذَا مَا ٱبْتَلَىٰهُ فَقَدَرَ عَلَيْهِ رِزْقَهُۥ فَيَقُولُ رَبِّىٓ أَهَـٰنَنِ۝١٦

    Waamma itha ma ibtalahu faqadara ʿalayhi rizqahu fayaqoolu rabbee ahanani

    Kuma idan Ya jarraba shi, wãto Ya ƙuntata masa abincinsa, sai ya ce: "Ubangijina Ya walãkanta ni."

  17. كَلَّا ۖ بَل لَّا تُكْرِمُونَ ٱلْيَتِيمَ۝١٧

    Kalla bal la tukrimoona alyateema

    A'aha! Bari wannan, ai bã ku girmama marãya!

  18. وَلَا تَحَـٰٓضُّونَ عَلَىٰ طَعَامِ ٱلْمِسْكِينِ۝١٨

    Wala tahaddoona ʿala taʿami almiskeeni

    Bã ku kwaɗaitã wa jũnanku ga (tattalin) abincin matalauci!

  19. وَتَأْكُلُونَ ٱلتُّرَاثَ أَكْلًا لَّمًّا۝١٩

    Watakuloona altturatha aklan lamman

    Kuma kuna cin dũkiyar gãdo, ci na tãrãwa.

  20. وَتُحِبُّونَ ٱلْمَالَ حُبًّا جَمًّا۝٢٠

    Watuhibboona almala hubban jamman

    Kuma kuna son dũkiya, so mai yawa.

  21. كَلَّآ إِذَا دُكَّتِ ٱلْأَرْضُ دَكًّا دَكًّا۝٢١

    Kalla itha dukkati alardu dakkan dakkan

    A'aha! Idan aka niƙa ƙasa niƙewa sosai.

  22. وَجَآءَ رَبُّكَ وَٱلْمَلَكُ صَفًّا صَفًّا۝٢٢

    Wajaa rabbuka waalmalaku saffan saffan

    Kuma Ubangijinka Ya zo, alhãli malã'iku na jẽre, sahu- sahu.

  23. وَجِا۟ىٓءَ يَوْمَئِذٍۭ بِجَهَنَّمَ ۚ يَوْمَئِذٍ يَتَذَكَّرُ ٱلْإِنسَـٰنُ وَأَنَّىٰ لَهُ ٱلذِّكْرَىٰ۝٢٣

    Wajeea yawmaithin bijahannama yawmaithin yatathakkaru alinsanu waanna lahu alththikra

    Kuma a ranar nan aka zo da Jahannama. A ranar nan mutum zai yi tunãni. To, inã fa tunãni yake a gare shi!

  24. يَقُولُ يَـٰلَيْتَنِى قَدَّمْتُ لِحَيَاتِى۝٢٤

    Yaqoolu ya laytanee qaddamtu lihayatee

    Yana dinga cẽwa, "Kaitona, dã na gabatar (da aikin ƙwarai) domin rãyuwata!"

  25. فَيَوْمَئِذٍ لَّا يُعَذِّبُ عَذَابَهُۥٓ أَحَدٌ۝٢٥

    Fayawmaithin la yuʿaththibu ʿathabahu ahadun

    To, a rãnar nan bãbu wani mai yin azãba irin azãbar Allah.

  26. وَلَا يُوثِقُ وَثَاقَهُۥٓ أَحَدٌ۝٢٦

    Wala yoothiqu wathaqahu ahadun

    Kuma bãbu wani mai ɗauri irin ɗaurin Sa.

  27. يَـٰٓأَيَّتُهَا ٱلنَّفْسُ ٱلْمُطْمَئِنَّةُ۝٢٧

    Ya ayyatuha alnnafsu almutmainnatu

    Yã kai rai mai natsuwa!

  28. ٱرْجِعِىٓ إِلَىٰ رَبِّكِ رَاضِيَةً مَّرْضِيَّةً۝٢٨

    Irjiʿee ila rabbiki radiyatan mardiyyatan

    Ka koma zuwa ga Ubangijinka, alhãli kana mai yarda (da abin da Ya ƙaddara maka a dũniya) abar yardarwa (da sakamakon da zã a ba ka a Lãhira).

  29. فَٱدْخُلِى فِى عِبَـٰدِى۝٢٩

    Faodkhulee fee ʿibadee

    Sabõbda haka, ka shiga cikin bãyi Na (mãsu bin umurui a dũniya).

  30. وَٱدْخُلِى جَنَّتِى۝٣٠

    Waodkhulee jannatee

    Kuma ka shiga AljannaTa (a Lãhira).

Tambayoyin da ake yawan yi

Mece ce ma’anar sunan Suratul Fajr?

Ma’anar Fajr ita ce “Alfijir”.

Suratul Fajr tana cikin juz’i na nawa?

Suratul Fajr tana cikin juz’i na 30.

Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Fajr?

Suratul Fajr tana da ayoyi 30.

Suratul Fajr Makkiya ce ko Madaniya?

Suratul Fajr sura ce Makkiya.

Suratul Fajr ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?

Ita ce sura ta 89 a cikin Alƙur’ani.

Majiyoyi

  • Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
  • Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
  • Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
  • Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
  • Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
  • Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.

Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.

Saitunan karatu

Rubutun Alƙur’ani
Girman Larabci
100%
Girman fassara
100%
Kamanni

Ƙara zuwa Allon Gida

ReadSurahBuɗe ReadSurah daga allon gida, a cikakken allo. Surorin da kuka karanta suna buɗewa ko da babu intanet.

  1. A cikin Safari, taɓa maɓallin “Share”. A sababbin iPhone yana cikin menu na •••.
  2. Taɓa “Add to Home Screen”. Gungura ƙasa idan ba ku gan shi ba.
  3. Taɓa “Add”.