Suratul Balad (البلد) ita ce sura ta 90 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 20. Ma’anar sunanta ita ce “Birni”. Sura ce Makkiya, wadda ta sauka a Makka kafin Hijira, kuma tana cikin juz’i na 30.
A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Balad gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.
Suratul Balad cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ
-
لَآ أُقْسِمُ بِهَـٰذَا ٱلْبَلَدِ١
La oqsimu bihatha albaladi
Bã sai Na yi rantsuwa da wannan gari1 ba.
Bayanai
[1] Allah Ya ce ba sai Ya yi rantsuwa da Makka ba, sa'an nan zã a san darajarta a lõkacinda Annabi yake a cikinta, kuma shi yana da haƙƙin zama a cikinta mahaifansa da zurriyarsa duka, ko da yake zai yi hijira sabõda fitinar kãfirai mãsu halaka dũkiyarsu kan adãwa da shi. Dã sun yi amfãni da dukiyar ga ayyukan alheri, dã yã fi musu. -
وَأَنتَ حِلٌّۢ بِهَـٰذَا ٱلْبَلَدِ٢
Waanta hillun bihatha albaladi
Alhãli kai kanã mai sauka a cikin wannan gari.
-
وَوَالِدٍ وَمَا وَلَدَ٣
Wawalidin wama walada
Da mahaifi da abin da ya haifa.
-
لَقَدْ خَلَقْنَا ٱلْإِنسَـٰنَ فِى كَبَدٍ٤
Laqad khalaqna alinsana fee kabadin
Lalle ne, Mun halitta mutum cikin wahala.
-
أَيَحْسَبُ أَن لَّن يَقْدِرَ عَلَيْهِ أَحَدٌ٥
Ayahsabu an lan yaqdira ʿalayhi ahadun
Kõ yanã zaton bãbu wani mai iya sãmun iko, a kansa?
-
يَقُولُ أَهْلَكْتُ مَالًا لُّبَدًا٦
Yaqoolu ahlaktu malan lubadan
Yana cẽwa "Na1 halakarda dũkiya mai yawa,"
Bayanai
[1] Nã halaka dukiya mai yawa dõmin faɗã da addĩni. -
أَيَحْسَبُ أَن لَّمْ يَرَهُۥٓ أَحَدٌ٧
Ayahsabu an lam yarahu ahadun
Shin, yana zaton cewa wani bai gan shi ba?
-
أَلَمْ نَجْعَل لَّهُۥ عَيْنَيْنِ٨
Alam najʿal lahu ʿaynayni
Shin, ba Mu sanya masa idãnu biyu ba?
-
وَلِسَانًا وَشَفَتَيْنِ٩
Walisanan washafatayni
Da harshe, da leɓɓa biyu.
-
وَهَدَيْنَـٰهُ ٱلنَّجْدَيْنِ١٠
Wahadaynahu alnnajdayni
Kuma ba Mu shiryar da shi ga hanyõyi1 biyu ba?
Bayanai
[1] Hanyar alheri da ta sharri. -
فَلَا ٱقْتَحَمَ ٱلْعَقَبَةَ١١
Fala iqtahama alʿaqabata
To, don mene ne bai shiga Aƙabã ba?
-
وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا ٱلْعَقَبَةُ١٢
Wama adraka ma alʿaqabatu
Kuma mene ne ya sanar da kai abin da ake cẽ wa Aƙabã?
-
فَكُّ رَقَبَةٍ١٣
Fakku raqabatin
Ita ce fansar wuyan bãwa.
-
أَوْ إِطْعَـٰمٌ فِى يَوْمٍ ذِى مَسْغَبَةٍ١٤
Aw itʿamun fee yawmin thee masghabatin
Ko kuwa ciyarwa, a cikin yini ma'abũcin yunwa.
-
يَتِيمًا ذَا مَقْرَبَةٍ١٥
Yateeman tha maqrabatin
Ga marãya ma'abũcin zumunta.
-
أَوْ مِسْكِينًا ذَا مَتْرَبَةٍ١٦
Aw miskeenan tha matrabatin
Ko kuwa wani matalauci ma'abũcin turɓãya.
-
ثُمَّ كَانَ مِنَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَتَوَاصَوْا۟ بِٱلصَّبْرِ وَتَوَاصَوْا۟ بِٱلْمَرْحَمَةِ١٧
Thumma kana mina allatheena amanoo watawasaw bialssabri watawasaw bialmarhamati
Sa'an nan kuma ya kasance daga waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi wa jũna wasiyya da yin haƙuri, kuma suka yi wa jũna wasiyya da tausayi.
-
أُو۟لَـٰٓئِكَ أَصْحَـٰبُ ٱلْمَيْمَنَةِ١٨
Olaika ashabu almaymanati
Waɗannan ne ma'abũta albarka1
Bayanai
[1] Ko kuwa waɗanda ake bai wa takardunsu da dãma, a Lãhira. -
وَٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ بِـَٔايَـٰتِنَا هُمْ أَصْحَـٰبُ ٱلْمَشْـَٔمَةِ١٩
Waallatheena kafaroo biayatina hum ashabu almashamati
Kuma waɗanda suka kãfirta da ãyõyin Mu, sũ ne ma'abũta shu'umci1
Bayanai
[1] Ko kuwa waɗanda ake bai wa takardunsu da hagu, a Lãhira. -
عَلَيْهِمْ نَارٌ مُّؤْصَدَةٌۢ٢٠
ʿAlayhim narun musadatun
A kansu akwai wata wuta abar kullewa.
Tambayoyin da ake yawan yi
Mece ce ma’anar sunan Suratul Balad?
Ma’anar Balad ita ce “Birni”.
Suratul Balad tana cikin juz’i na nawa?
Suratul Balad tana cikin juz’i na 30.
Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Balad?
Suratul Balad tana da ayoyi 20.
Suratul Balad Makkiya ce ko Madaniya?
Suratul Balad sura ce Makkiya.
Suratul Balad ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?
Ita ce sura ta 90 a cikin Alƙur’ani.
Majiyoyi
- Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
- Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
- Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
- Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
- Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
- Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.
Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.