Suratul Lail (الليل) ita ce sura ta 92 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 21. Ma’anar sunanta ita ce “Dare”. Sura ce Makkiya, wadda ta sauka a Makka kafin Hijira, kuma tana cikin juz’i na 30.
A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Lail gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.
Suratul Lail cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ
-
وَٱلَّيْلِ إِذَا يَغْشَىٰ١
Waallayli itha yaghsha
Inã rantsuwa da dare a lõkacin da yake rufẽwa.
-
وَٱلنَّهَارِ إِذَا تَجَلَّىٰ٢
Waalnnahari itha tajalla
Da yini a lõkacin da yake kuranyẽwa.
-
وَمَا خَلَقَ ٱلذَّكَرَ وَٱلْأُنثَىٰٓ٣
Wama khalaqa alththakara waalontha
Da abin da ya halitta namiji da mace.
-
إِنَّ سَعْيَكُمْ لَشَتَّىٰ٤
Inna saʿyakum lashatta
Lãlle ne ayyukanku, dabam-dabam suke.
-
فَأَمَّا مَنْ أَعْطَىٰ وَٱتَّقَىٰ٥
Faamma man aʿta waittaqa
To, amma wanda ya yi kyauta, kuma ya yi taƙawa.
-
وَصَدَّقَ بِٱلْحُسْنَىٰ٦
Wasaddaqa bialhusna
Kuma ya gaskata kalma1 mai kyãwo.
Bayanai
[1] Kalma mai kyãwo ita ce Kalmar shahãda da abin da ta ƙunsa na addinin Musulunci, wanda yake yinsa kamar yadda Allah Ya ce, ta hanyan Manzon Sa, shi ne taƙawa. -
فَسَنُيَسِّرُهُۥ لِلْيُسْرَىٰ٧
Fasanuyassiruhu lilyusra
To, zã Mu sauƙaƙe masa har ya kai ga sauƙi.
-
وَأَمَّا مَنۢ بَخِلَ وَٱسْتَغْنَىٰ٨
Waamma man bakhila waistaghna
Kuma amma wanda ya yi rõwa, kuma ya wadãtu da kansa.
-
وَكَذَّبَ بِٱلْحُسْنَىٰ٩
Wakaththaba bialhusna
Kuma ya ƙaryatar da kalma mai kyãwo.
-
فَسَنُيَسِّرُهُۥ لِلْعُسْرَىٰ١٠
Fasanuyassiruhu lilʿusra
To, zã Mu sauƙaƙke masa har ya kai ga tsanani.
-
وَمَا يُغْنِى عَنْهُ مَالُهُۥٓ إِذَا تَرَدَّىٰٓ١١
Wama yughnee ʿanhu maluhu itha taradda
Kuma dũkiyarsa ba ta wadãtar masa da kõme ba, a lõkacin da ya gangara (a wuta).
-
إِنَّ عَلَيْنَا لَلْهُدَىٰ١٢
Inna ʿalayna lalhuda
Lãlle aikin Mu ne, Mu bayyana shiriya.
-
وَإِنَّ لَنَا لَلْـَٔاخِرَةَ وَٱلْأُولَىٰ١٣
Wainna lana lalakhirata waaloola
Kuma lalle ne Lãhira da duniya Namu ne.
-
فَأَنذَرْتُكُمْ نَارًا تَلَظَّىٰ١٤
Faanthartukum naran talaththa
Sabõda haka, Na yi maku gargaɗi da wuta mai babbaka.
-
لَا يَصْلَىٰهَآ إِلَّا ٱلْأَشْقَى١٥
La yaslaha illa alashqa
Bãbu mai shigarta sai mafi Tabewa
-
ٱلَّذِى كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰ١٦
Allathee kaththaba watawalla
Wanda ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya.
-
وَسَيُجَنَّبُهَا ٱلْأَتْقَى١٧
Wasayujannabuha alatqa
Kuma mafi taƙawa1 zai nisance ta.
Bayanai
[1] Mafi taƙawa da Mafi shaƙãwa suna ma'anar mai taƙawa da shaƙiyyi. -
ٱلَّذِى يُؤْتِى مَالَهُۥ يَتَزَكَّىٰ١٨
Allathee yutee malahu yatazakka
Wanda yake bãyar da dũkiyarsa, alhãli yana tsarkaka.
-
وَمَا لِأَحَدٍ عِندَهُۥ مِن نِّعْمَةٍ تُجْزَىٰٓ١٩
Wama liahadin ʿindahu min niʿmatin tujza
Alhãli bãbu wani mai wata ni'ima wurinsa wadda ake nẽman sakamakonta.
-
إِلَّا ٱبْتِغَآءَ وَجْهِ رَبِّهِ ٱلْأَعْلَىٰ٢٠
Illa ibtighaa wajhi rabbihi alaʿla
Fãce dai nẽman yardar Ubangijinsa Mafi ɗaukaka.
-
وَلَسَوْفَ يَرْضَىٰ٢١
Walasawfa yarda
To, lalle ne zai yarda (da sakamakon da zã a bã shi).
Tambayoyin da ake yawan yi
Mece ce ma’anar sunan Suratul Lail?
Ma’anar Lail ita ce “Dare”.
Suratul Lail tana cikin juz’i na nawa?
Suratul Lail tana cikin juz’i na 30.
Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Lail?
Suratul Lail tana da ayoyi 21.
Suratul Lail Makkiya ce ko Madaniya?
Suratul Lail sura ce Makkiya.
Suratul Lail ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?
Ita ce sura ta 92 a cikin Alƙur’ani.
Majiyoyi
- Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
- Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
- Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
- Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
- Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
- Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.
Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.