Suratul Duha (الضحى) ita ce sura ta 93 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 11. Ma’anar sunanta ita ce “Hantsi”. Sura ce Makkiya, wadda ta sauka a Makka kafin Hijira, kuma tana cikin juz’i na 30.
A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Duha gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.
Suratul Duha cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ
-
وَٱلضُّحَىٰ١
Waaldduha
Inã rantsuwa da hantsi.
-
وَٱلَّيْلِ إِذَا سَجَىٰ٢
Waallayli itha saja
Da dare a lõkacin da ya rufe (da duhunsa).
-
مَا وَدَّعَكَ رَبُّكَ وَمَا قَلَىٰ٣
Ma waddaʿaka rabbuka wama qala
Ubangijinka bai yi maka bankwana ba, kuma bai ƙĩ kaba.
-
وَلَلْـَٔاخِرَةُ خَيْرٌ لَّكَ مِنَ ٱلْأُولَىٰ٤
Walalakhiratu khayrun laka mina aloola
Kuma lalle ta ƙarshe1 ce mafi alheri a gare ka daga ta farko.
Bayanai
[1] Ta ƙarshe, wãto, Lãhira; kuma ta farko, wato, dũniya. -
وَلَسَوْفَ يُعْطِيكَ رَبُّكَ فَتَرْضَىٰٓ٥
Walasawfa yuʿteeka rabbuka fatarda
Kuma lalle ne, Ubangijinka zai yi ta bã ka kyauta sai ka yarda.
-
أَلَمْ يَجِدْكَ يَتِيمًا فَـَٔاوَىٰ٦
Alam yajidka yateeman faawa
Ashe, bai sãme ka marãya ba, sa'an nan Ya yi maka makõma?
-
وَوَجَدَكَ ضَآلًّا فَهَدَىٰ٧
Wawajadaka dallan fahada
Kuma Ya sãme ka bã ka da shari'ã, sai Ya shiryar da kai?
-
وَوَجَدَكَ عَآئِلًا فَأَغْنَىٰ٨
Wawajadaka ʿailan faaghna
Kuma Ya sãme ka matalauci, sai Ya wadãtã ka?
-
فَأَمَّا ٱلْيَتِيمَ فَلَا تَقْهَرْ٩
Faamma alyateema fala taqhar
Sabõda haka, amma marãya, to, kada ka rinjãye shi.
-
وَأَمَّا ٱلسَّآئِلَ فَلَا تَنْهَرْ١٠
Waamma alssaila fala tanhar
Kuma amma mai tambaya, kada ka yi masa tsãwa.
-
وَأَمَّا بِنِعْمَةِ رَبِّكَ فَحَدِّثْ١١
Waamma biniʿmati rabbika fahaddith
Kuma amma ni'imar Ubangijinka, sai ka faɗa (dõmin gõdiya).
Tambayoyin da ake yawan yi
Mece ce ma’anar sunan Suratul Duha?
Ma’anar Duha ita ce “Hantsi”.
Suratul Duha tana cikin juz’i na nawa?
Suratul Duha tana cikin juz’i na 30.
Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Duha?
Suratul Duha tana da ayoyi 11.
Suratul Duha Makkiya ce ko Madaniya?
Suratul Duha sura ce Makkiya.
Suratul Duha ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?
Ita ce sura ta 93 a cikin Alƙur’ani.
Majiyoyi
- Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
- Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
- Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
- Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
- Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
- Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.
Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.