Suratul Tin (التين) ita ce sura ta 95 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 8. Ma’anar sunanta ita ce “Ɓaure”. Sura ce Makkiya, wadda ta sauka a Makka kafin Hijira, kuma tana cikin juz’i na 30.
A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Tin gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.
Suratul Tin cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko
بِّسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ
-
وَٱلتِّينِ وَٱلزَّيْتُونِ١
Waaltteeni waalzzaytooni
Inã rantsuwa da Attinu da Azzaitũn.1
Bayanai
[1] Ibn Abbas ya ce: 'Attinu shi ne masallacin Nuhu a kan Judiyyi, Azzaitun Masallacin Baitil Muƙaddas.'. -
وَطُورِ سِينِينَ٢
Watoori seeneena
Da Dũr Sĩnĩna.1
Bayanai
[1] Dutsen da Allah Ya yi magana da Musa a kansa. Ma'anarsa dutse mai albarka sabõda itacen da ke kansa. -
وَهَـٰذَا ٱلْبَلَدِ ٱلْأَمِينِ٣
Wahatha albaladi alameeni
Da wannan gari1 amintacce.
Bayanai
[1] Gari amintacce shi ne Makkah. -
لَقَدْ خَلَقْنَا ٱلْإِنسَـٰنَ فِىٓ أَحْسَنِ تَقْوِيمٍ٤
Laqad khalaqna alinsana fee ahsani taqweemin
Lalle ne, Mun halitta mutum a cikin mafi kyawon tsayuwa.
-
ثُمَّ رَدَدْنَـٰهُ أَسْفَلَ سَـٰفِلِينَ٥
Thumma radadnahu asfala safileena
Sa'an nan, Muka mayar da shi mafi ƙasƙantar masu rauni
-
إِلَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ فَلَهُمْ أَجْرٌ غَيْرُ مَمْنُونٍ٦
Illa allatheena amanoo waʿamiloo alssalihati falahum ajrun ghayru mamnoonin
Face waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, saboda haka suna da sakamako wanda bã ya yankewa.
-
فَمَا يُكَذِّبُكَ بَعْدُ بِٱلدِّينِ٧
Fama yukaththibuka baʿdu bialddeeni
To, bãyan haka mẽ ya sanya ka ka ƙaryata sakamako (wanda za a yi a bãyan Tãshin ¡iyãma)?
-
أَلَيْسَ ٱللَّهُ بِأَحْكَمِ ٱلْحَـٰكِمِينَ٨
Alaysa Allahu biahkami alhakimeena
Ashe Allah bã Shi ne Mafi mãsu hukunci kyãwon hukunci ba?1
Bayanai
[1] Ana son wanda ya karanta sũrar har ƙarshe ya ce بلى ,wato na'am, Allah Ya fi kowa kyãwon hukunci.
Tambayoyin da ake yawan yi
Mece ce ma’anar sunan Suratul Tin?
Ma’anar Tin ita ce “Ɓaure”.
Suratul Tin tana cikin juz’i na nawa?
Suratul Tin tana cikin juz’i na 30.
Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Tin?
Suratul Tin tana da ayoyi 8.
Suratul Tin Makkiya ce ko Madaniya?
Suratul Tin sura ce Makkiya.
Suratul Tin ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?
Ita ce sura ta 95 a cikin Alƙur’ani.
Majiyoyi
- Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
- Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
- Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
- Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
- Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
- Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.
Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.