سورة العلق

Suratul Alaƙ da fassarar Hausa

Gudan jini

Mushafi

Mishary Rashid AlafasySauke MP3Sauke PDF

Suratul Alaƙ (العلق) ita ce sura ta 96 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 19. Ma’anar sunanta ita ce “Gudan jini”. Sura ce Makkiya, wadda ta sauka a Makka kafin Hijira, kuma tana cikin juz’i na 30.

A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Alaƙ gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.

Suratul Alaƙ cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. ٱقْرَأْ بِٱسْمِ رَبِّكَ ٱلَّذِى خَلَقَ۝١

    Iqra biismi rabbika allathee khalaqa

    Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, wanda Ya yi halitta.

  2. خَلَقَ ٱلْإِنسَـٰنَ مِنْ عَلَقٍ۝٢

    Khalaqa alinsana min ʿalaqin

    Ya hahitta mutum daga gudan jini.

  3. ٱقْرَأْ وَرَبُّكَ ٱلْأَكْرَمُ۝٣

    Iqra warabbuka alakramu

    Ka yi karatu, kuma Ubangijinka shi ne Mafi karimci.

  4. ٱلَّذِى عَلَّمَ بِٱلْقَلَمِ۝٤

    Allathee ʿallama bialqalami

    Wanda Ya sanar (da mutum) game da alƙalami.

  5. عَلَّمَ ٱلْإِنسَـٰنَ مَا لَمْ يَعْلَمْ۝٥

    ʿAllama alinsana ma lam yaʿlam

    Ya sanar da mutum abin da bai sani ba.

  6. كَلَّآ إِنَّ ٱلْإِنسَـٰنَ لَيَطْغَىٰٓ۝٦

    Kalla inna alinsana layatgha

    A'aha! Lalle, ne mutum haƙĩƙa, yana girman kai (ya ƙi karatu).

  7. أَن رَّءَاهُ ٱسْتَغْنَىٰٓ۝٧

    An raahu istaghna

    Dõmin yã ga kansa, yã wadãta.

  8. إِنَّ إِلَىٰ رَبِّكَ ٱلرُّجْعَىٰٓ۝٨

    Inna ila rabbika alrrujʿa

    Lalle ne zuwa ga Ubangijinka makoma take.

  9. أَرَءَيْتَ ٱلَّذِى يَنْهَىٰ۝٩

    Araayta allathee yanha

    Shin, kã ga wanda ke hana.

  10. عَبْدًا إِذَا صَلَّىٰٓ۝١٠

    ʿAbdan itha salla

    Bãwã idan yã yi salla?

  11. أَرَءَيْتَ إِن كَانَ عَلَى ٱلْهُدَىٰٓ۝١١

    Araayta in kana ʿala alhuda

    Ashe, kã gani, idan (shi bãwan) ya kasance a kan shiriya?

  12. أَوْ أَمَرَ بِٱلتَّقْوَىٰٓ۝١٢

    Aw amara bialttaqwa

    Ko ya yi umurni da taƙawa?

  13. أَرَءَيْتَ إِن كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰٓ۝١٣

    Araayta in kaththaba watawalla

    Ashe, kã gani, idan (shi mai hanin) ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya?

  14. أَلَمْ يَعْلَم بِأَنَّ ٱللَّهَ يَرَىٰ۝١٤

    Alam yaʿlam bianna Allaha yara

    Ashe, bai sani ba cewa Allah Yanã gani?

  15. كَلَّا لَئِن لَّمْ يَنتَهِ لَنَسْفَعًۢا بِٱلنَّاصِيَةِ۝١٥

    Kalla lain lam yantahi lanasfaʿan bialnnasiyati

    A'aha! Lalle ne, idan bai hanu ba, lalle ne zã Mu ja gãshin makwarkwaɗa.

  16. نَاصِيَةٍ كَـٰذِبَةٍ خَاطِئَةٍ۝١٦

    Nasiyatin kathibatin khatiatin

    Makwarkwaɗa maƙaryaciya, mai laifi.

  17. فَلْيَدْعُ نَادِيَهُۥ۝١٧

    Falyadʿu nadiyahu

    Sai ya kirayi ƙungiyarsa.

  18. سَنَدْعُ ٱلزَّبَانِيَةَ۝١٨

    Sanadʿu alzzabaniyata

    Zã Mu kirayi zabaniyãwa (mala'iku mãsu girma).

  19. كَلَّا لَا تُطِعْهُ وَٱسْجُدْ وَٱقْتَرِب ۩۝١٩

    Kalla la tutiʿhu waosjud waiqtarib

    A'aha kada ka bĩ shi. Kuma ka yi tawali'u,1 kuma ka nemi kusanta (zuwa ga Ubangijinka).

    Bayanai
    [1] Wato salla da sauran ibãdu.

Tambayoyin da ake yawan yi

Mece ce ma’anar sunan Suratul Alaƙ?

Ma’anar Alaƙ ita ce “Gudan jini”.

Suratul Alaƙ tana cikin juz’i na nawa?

Suratul Alaƙ tana cikin juz’i na 30.

Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Alaƙ?

Suratul Alaƙ tana da ayoyi 19.

Suratul Alaƙ Makkiya ce ko Madaniya?

Suratul Alaƙ sura ce Makkiya.

Suratul Alaƙ ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?

Ita ce sura ta 96 a cikin Alƙur’ani.

Majiyoyi

  • Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
  • Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
  • Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
  • Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
  • Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
  • Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.

Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.

Saitunan karatu

Rubutun Alƙur’ani
Girman Larabci
100%
Girman fassara
100%
Kamanni

Ƙara zuwa Allon Gida

ReadSurahBuɗe ReadSurah daga allon gida, a cikakken allo. Surorin da kuka karanta suna buɗewa ko da babu intanet.

  1. A cikin Safari, taɓa maɓallin “Share”. A sababbin iPhone yana cikin menu na •••.
  2. Taɓa “Add to Home Screen”. Gungura ƙasa idan ba ku gan shi ba.
  3. Taɓa “Add”.