سورة الشمس

Suratul Shams da fassarar Hausa

Rana

Mushafi

Mishary Rashid AlafasySauke MP3Sauke PDF

Suratul Shams (الشمس) ita ce sura ta 91 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 15. Ma’anar sunanta ita ce “Rana”. Sura ce Makkiya, wadda ta sauka a Makka kafin Hijira, kuma tana cikin juz’i na 30.

A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Shams gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.

Suratul Shams cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. وَٱلشَّمْسِ وَضُحَىٰهَا۝١

    Waalshshamsi waduhaha

    Ina rantsuwa da rãnã da hantsinta.

  2. وَٱلْقَمَرِ إِذَا تَلَىٰهَا۝٢

    Waalqamari itha talaha

    Kuma da wata idan ya bi ta.

  3. وَٱلنَّهَارِ إِذَا جَلَّىٰهَا۝٣

    Waalnnahari itha jallaha

    Da yini a lõkacin da ya bayyana ta.

  4. وَٱلَّيْلِ إِذَا يَغْشَىٰهَا۝٤

    Waallayli itha yaghshaha

    Da dare a lõkacin da ya ke rufe ta.

  5. وَٱلسَّمَآءِ وَمَا بَنَىٰهَا۝٥

    Waalssamai wama banaha

    Da sama da abin da ya gina ta.

  6. وَٱلْأَرْضِ وَمَا طَحَىٰهَا۝٦

    Waalardi wama tahaha

    Da ƙasã da abin da ya shimfiɗa ta.

  7. وَنَفْسٍ وَمَا سَوَّىٰهَا۝٧

    Wanafsin wama sawwaha

    Da rai da abin da ya daidaita shi.

  8. فَأَلْهَمَهَا فُجُورَهَا وَتَقْوَىٰهَا۝٨

    Faalhamaha fujooraha wataqwaha

    Sa'an nan ya yi masa Ilhamar fãjircinsa da shiryuwarsa.

  9. قَدْ أَفْلَحَ مَن زَكَّىٰهَا۝٩

    Qad aflaha man zakkaha

    Lalle ne wanda ya tsarkake1 shi (rai) ya sãmi babban rabo.

    Bayanai
    [1] Karɓar imãni da aiki da abinda ya ƙunsa tsarkake rai ne.
  10. وَقَدْ خَابَ مَن دَسَّىٰهَا۝١٠

    Waqad khaba man dassaha

    Kuma lalle ne wanda ya turbuɗe1 shi (da laifi) ya tãɓe.

    Bayanai
    [1] Kãfirci turbuɗe rai ne da zunubi.
  11. كَذَّبَتْ ثَمُودُ بِطَغْوَىٰهَآ۝١١

    Kaththabat thamoodu bitaghwaha

    Samũdãwa sun ƙaryata (Annabinsu), dõmin girman kansu.

  12. إِذِ ٱنۢبَعَثَ أَشْقَىٰهَا۝١٢

    Ithi inbaʿatha ashqaha

    A lõkacin da mafi shaƙãwarsu ya tafi (wurin sõke rãkumar sãlihu).

  13. فَقَالَ لَهُمْ رَسُولُ ٱللَّهِ نَاقَةَ ٱللَّهِ وَسُقْيَـٰهَا۝١٣

    Faqala lahum rasoolu Allahi naqata Allahi wasuqyaha

    Sai Manzon Allah ya gaya musu cewa: "Ina tsõratar da ku ga rãƙumar Allah da ruwan shanta!"

  14. فَكَذَّبُوهُ فَعَقَرُوهَا فَدَمْدَمَ عَلَيْهِمْ رَبُّهُم بِذَنۢبِهِمْ فَسَوَّىٰهَا۝١٤

    Fakaththaboohu faʿaqarooha fadamdama ʿalayhim rabbuhum bithanbihim fasawwaha

    Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan suka sõke ta. Sabõda haka Ubangijinsu Ya darkãke su, sabõda zunubinsu. Sa'an nan Ya daidaita ta (azãbar ga mai laifi da maras laifi).

  15. وَلَا يَخَافُ عُقْبَـٰهَا۝١٥

    Wala yakhafu ʿuqbaha

    Kuma bã ya tsõron ãƙibarta (ita halakãwar).

Tambayoyin da ake yawan yi

Mece ce ma’anar sunan Suratul Shams?

Ma’anar Shams ita ce “Rana”.

Suratul Shams tana cikin juz’i na nawa?

Suratul Shams tana cikin juz’i na 30.

Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Shams?

Suratul Shams tana da ayoyi 15.

Suratul Shams Makkiya ce ko Madaniya?

Suratul Shams sura ce Makkiya.

Suratul Shams ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?

Ita ce sura ta 91 a cikin Alƙur’ani.

Majiyoyi

  • Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
  • Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
  • Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
  • Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
  • Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
  • Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.

Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.

Saitunan karatu

Rubutun Alƙur’ani
Girman Larabci
100%
Girman fassara
100%
Kamanni

Ƙara zuwa Allon Gida

ReadSurahBuɗe ReadSurah daga allon gida, a cikakken allo. Surorin da kuka karanta suna buɗewa ko da babu intanet.

  1. A cikin Safari, taɓa maɓallin “Share”. A sababbin iPhone yana cikin menu na •••.
  2. Taɓa “Add to Home Screen”. Gungura ƙasa idan ba ku gan shi ba.
  3. Taɓa “Add”.