سورة الأعلى

Suratul A’ala da fassarar Hausa

Maɗaukaki

Mushafi

Mishary Rashid AlafasySauke MP3Sauke PDF

Suratul A’ala (الأعلى) ita ce sura ta 87 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 19. Ma’anar sunanta ita ce “Maɗaukaki”. Sura ce Makkiya, wadda ta sauka a Makka kafin Hijira, kuma tana cikin juz’i na 30.

A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul A’ala gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.

Suratul A’ala cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. سَبِّحِ ٱسْمَ رَبِّكَ ٱلْأَعْلَى۝١

    Sabbihi isma rabbika alaʿla

    Ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mafi ɗaukaka.

  2. ٱلَّذِى خَلَقَ فَسَوَّىٰ۝٢

    Allathee khalaqa fasawwa

    Wanda Yã yi halitta sa'an nan Ya daidaita abin halittar.

  3. وَٱلَّذِى قَدَّرَ فَهَدَىٰ۝٣

    Waallathee qaddara fahada

    Kuma Wanda Ya ƙaddara (abin da Ya so) sannan Ya shiryar, (da mutum ga hanyar alhẽri da ta sharri).

  4. وَٱلَّذِىٓ أَخْرَجَ ٱلْمَرْعَىٰ۝٤

    Waallathee akhraja almarʿa

    Kuma Wanda Ya fitar da makiyãyã.

  5. فَجَعَلَهُۥ غُثَآءً أَحْوَىٰ۝٥

    Fajaʿalahu ghuthaan ahwa

    Sa'an nan Ya mayar da ita ƙeƙasassa, baƙa.

  6. سَنُقْرِئُكَ فَلَا تَنسَىٰٓ۝٦

    Sanuqrioka fala tansa

    Za mu karantar da kai (Alƙur'ãni) sabõda haka bã zã ka mantã (shi) ba.

  7. إِلَّا مَا شَآءَ ٱللَّهُ ۚ إِنَّهُۥ يَعْلَمُ ٱلْجَهْرَ وَمَا يَخْفَىٰ۝٧

    Illa ma shaa Allahu innahu yaʿlamu aljahra wama yakhfa

    Fãce abin da Allah Ya so, lalle ne Shi (Allah) Ya san bayyane da abin da yake bõye.

  8. وَنُيَسِّرُكَ لِلْيُسْرَىٰ۝٨

    Wanuyassiruka lilyusra

    Kuma za Mu sauƙaƙe maka (al'amari) zuwa ga (Shari'a) mai sauƙi.

  9. فَذَكِّرْ إِن نَّفَعَتِ ٱلذِّكْرَىٰ۝٩

    Fathakkir in nafaʿati alththikra

    Sabõda baka, ka tunãtar, idan tunatarwa zã ta yi amfãni.

  10. سَيَذَّكَّرُ مَن يَخْشَىٰ۝١٠

    Sayaththakkaru man yakhsha

    Wanda yake tsõron (Allah) Zai tuna.

  11. وَيَتَجَنَّبُهَا ٱلْأَشْقَى۝١١

    Wayatajannabuha alashqa

    Kuma shaƙiyyi, zai nisanceta,

  12. ٱلَّذِى يَصْلَى ٱلنَّارَ ٱلْكُبْرَىٰ۝١٢

    Allathee yasla alnnara alkubra

    Wanda zai shiga wutar da tã fi girma.

  13. ثُمَّ لَا يَمُوتُ فِيهَا وَلَا يَحْيَىٰ۝١٣

    Thumma la yamootu feeha wala yahya

    Sa'an nan bã zai mutu ba a cikinta, kuma bã zai rãyu ba.

  14. قَدْ أَفْلَحَ مَن تَزَكَّىٰ۝١٤

    Qad aflaha man tazakka

    Lalle ne wanda ya tsarkaka (da ĩmãni) yã sãmu babban rabo.

  15. وَذَكَرَ ٱسْمَ رَبِّهِۦ فَصَلَّىٰ۝١٥

    Wathakara isma rabbihi fasalla

    Kuma ya ambaci sũnan1 Ubangijinsa, sa'an nan yã yi salla.

    Bayanai
    [1] Ya ambaci sũnan Allah ga ayyukansa duka, ya yi sallolin nan biyar da sauran.
  16. بَلْ تُؤْثِرُونَ ٱلْحَيَوٰةَ ٱلدُّنْيَا۝١٦

    Bal tuthiroona alhayata alddunya

    Ba haka ba! Kunã zãɓin rãyuwa ta kusa dũniya.1

    Bayanai
    [1] Rayuwa iri biyu ce, ta dũniya da ta Lãhira.
  17. وَٱلْـَٔاخِرَةُ خَيْرٌ وَأَبْقَىٰٓ۝١٧

    Waalakhiratu khayrun waabqa

    Alhãli Lãhira ita ce mafi alheri kuma mafi wanzuwa.

  18. إِنَّ هَـٰذَا لَفِى ٱلصُّحُفِ ٱلْأُولَىٰ۝١٨

    Inna hatha lafee alssuhufi aloola

    Lalle ne, wannan1 yanã a cikin littafan farko.

    Bayanai
    [1] Kamanta rãyuwar ciyãwa da rãyar da ummiyyi da ilmi bãbu mantuwa, da rãyar da mãtattu cikin sa'ãda ko cikin shaƙãwa yana cikin litaffan farko.
  19. صُحُفِ إِبْرَٰهِيمَ وَمُوسَىٰ۝١٩

    Suhufi ibraheema wamoosa

    Littaffan Ibrãhĩm da Mũsã.

Tambayoyin da ake yawan yi

Mece ce ma’anar sunan Suratul A’ala?

Ma’anar A’ala ita ce “Maɗaukaki”.

Suratul A’ala tana cikin juz’i na nawa?

Suratul A’ala tana cikin juz’i na 30.

Ayoyi nawa ne a cikin Suratul A’ala?

Suratul A’ala tana da ayoyi 19.

Suratul A’ala Makkiya ce ko Madaniya?

Suratul A’ala sura ce Makkiya.

Suratul A’ala ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?

Ita ce sura ta 87 a cikin Alƙur’ani.

Majiyoyi

  • Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
  • Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
  • Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
  • Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
  • Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
  • Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.

Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.

Saitunan karatu

Rubutun Alƙur’ani
Girman Larabci
100%
Girman fassara
100%
Kamanni

Ƙara zuwa Allon Gida

ReadSurahBuɗe ReadSurah daga allon gida, a cikakken allo. Surorin da kuka karanta suna buɗewa ko da babu intanet.

  1. A cikin Safari, taɓa maɓallin “Share”. A sababbin iPhone yana cikin menu na •••.
  2. Taɓa “Add to Home Screen”. Gungura ƙasa idan ba ku gan shi ba.
  3. Taɓa “Add”.