سورة العاديات

Suratul Adiyat da fassarar Hausa

Masu sukuwa

Mushafi

Mishary Rashid AlafasySauke MP3Sauke PDF

Suratul Adiyat (العاديات) ita ce sura ta 100 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 11. Ma’anar sunanta ita ce “Masu sukuwa”. Sura ce Makkiya, wadda ta sauka a Makka kafin Hijira, kuma tana cikin juz’i na 30.

A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Adiyat gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.

Suratul Adiyat cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. وَٱلْعَـٰدِيَـٰتِ ضَبْحًا۝١

    Waalʿadiyati dabhan

    Ina rantsuwa da dawãki mãsu gudu suna fitar da kũkan ciki.

  2. فَٱلْمُورِيَـٰتِ قَدْحًا۝٢

    Faalmooriyati qadhan

    Mãsu ƙyasta wuta (da kõfatansu a kan duwatsu) ƙyastawa.

  3. فَٱلْمُغِيرَٰتِ صُبْحًا۝٣

    Faalmugheerati subhan

    Sa'an nan mãsu yin hari a lokacin asuba.

  4. فَأَثَرْنَ بِهِۦ نَقْعًا۝٤

    Faatharna bihi naqʿan

    Sai su motsar da ƙũra game da shi.

  5. فَوَسَطْنَ بِهِۦ جَمْعًا۝٥

    Fawasatna bihi jamʿan

    Sai su shiga, game da ita (ƙũrar), a tsakãnin jama'ar maƙiya.

  6. إِنَّ ٱلْإِنسَـٰنَ لِرَبِّهِۦ لَكَنُودٌ۝٦

    Inna alinsana lirabbihi lakanoodun

    Lalle ne mutum mai tsananin butulci ne ga Ubangijinsa.

  7. وَإِنَّهُۥ عَلَىٰ ذَٰلِكَ لَشَهِيدٌ۝٧

    Wainnahu ʿala thalika lashaheedun

    Lalle ne shi mai shaida ne a kan laifinsa da haka.

  8. وَإِنَّهُۥ لِحُبِّ ٱلْخَيْرِ لَشَدِيدٌ۝٨

    Wainnahu lihubbi alkhayri lashadeedun

    Kuma alle ne ga dũkiya shi mai tsananin so ne.

  9. ۞ أَفَلَا يَعْلَمُ إِذَا بُعْثِرَ مَا فِى ٱلْقُبُورِ۝٩

    Afala yaʿlamu itha buʿthira ma fee alquboori

    Shin, bã ya da sanin lõkacin da aka tõne abin da yake cikin kaburbura.

  10. وَحُصِّلَ مَا فِى ٱلصُّدُورِ۝١٠

    Wahussila ma fee alssudoori

    Aka bayyana abin da ke cikin zukata.

  11. إِنَّ رَبَّهُم بِهِمْ يَوْمَئِذٍ لَّخَبِيرٌۢ۝١١

    Inna rabbahum bihim yawmaithin lakhabeerun

    Lalle ne Ubangijinsu, game da su a ranar nan Mai ƙididdigewa ne?

Tambayoyin da ake yawan yi

Mece ce ma’anar sunan Suratul Adiyat?

Ma’anar Adiyat ita ce “Masu sukuwa”.

Suratul Adiyat tana cikin juz’i na nawa?

Suratul Adiyat tana cikin juz’i na 30.

Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Adiyat?

Suratul Adiyat tana da ayoyi 11.

Suratul Adiyat Makkiya ce ko Madaniya?

Suratul Adiyat sura ce Makkiya.

Suratul Adiyat ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?

Ita ce sura ta 100 a cikin Alƙur’ani.

Majiyoyi

  • Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
  • Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
  • Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
  • Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
  • Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
  • Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.

Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.

Saitunan karatu

Rubutun Alƙur’ani
Girman Larabci
100%
Girman fassara
100%
Kamanni

Ƙara zuwa Allon Gida

ReadSurahBuɗe ReadSurah daga allon gida, a cikakken allo. Surorin da kuka karanta suna buɗewa ko da babu intanet.

  1. A cikin Safari, taɓa maɓallin “Share”. A sababbin iPhone yana cikin menu na •••.
  2. Taɓa “Add to Home Screen”. Gungura ƙasa idan ba ku gan shi ba.
  3. Taɓa “Add”.