سورة القارعة

Suratul Ƙari’a da fassarar Hausa

Masifa

Mushafi

Mishary Rashid AlafasySauke MP3Sauke PDF

Suratul Ƙari’a (القارعة) ita ce sura ta 101 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 11. Ma’anar sunanta ita ce “Masifa”. Sura ce Makkiya, wadda ta sauka a Makka kafin Hijira, kuma tana cikin juz’i na 30.

A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Ƙari’a gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.

Suratul Ƙari’a cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. ٱلْقَارِعَةُ۝١

    Alqariʿatu

    Mai ƙwanƙwasar (zukata da tsõro)!

  2. مَا ٱلْقَارِعَةُ۝٢

    Ma alqariʿatu

    Mẽnẽ ne mai ƙwanƙwasa?

  3. وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا ٱلْقَارِعَةُ۝٣

    Wama adraka ma alqariʿatu

    Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa mai ƙwanƙwasa?

  4. يَوْمَ يَكُونُ ٱلنَّاسُ كَٱلْفَرَاشِ ٱلْمَبْثُوثِ۝٤

    Yawma yakoonu alnnasu kaalfarashi almabthoothi

    Rãnar da mutãne za su kasance kamar 'ya'yan fari mãsu wãtsuwa.

  5. وَتَكُونُ ٱلْجِبَالُ كَٱلْعِهْنِ ٱلْمَنفُوشِ۝٥

    Watakoonu aljibalu kaalʿihni almanfooshi

    Kuma duwãtsu su kasance kamar gãshin sũfin da aka saɓe.

  6. فَأَمَّا مَن ثَقُلَتْ مَوَٰزِينُهُۥ۝٦

    Faamma man thaqulat mawazeenuhu

    To, amma wanda ma'aunansa suka yi nauyi.

  7. فَهُوَ فِى عِيشَةٍ رَّاضِيَةٍ۝٧

    Fahuwa fee ʿeeshatin radiyatin

    To, shi yana a cikin wata rayuwa yardadda.

  8. وَأَمَّا مَنْ خَفَّتْ مَوَٰزِينُهُۥ۝٨

    Waamma man khaffat mawazeenuhu

    Kuma amma wanda ma'aunansa suka yi sauƙi (bãbu nauyi).

  9. فَأُمُّهُۥ هَاوِيَةٌ۝٩

    Faommuhu hawiyatun

    To, uwarsa Hãwiya ce.

  10. وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا هِيَهْ۝١٠

    Wama adraka ma hiyah

    Kuma me ya sanar da kai mece ce ita?

  11. نَارٌ حَامِيَةٌۢ۝١١

    Narun hamiyatun

    Wata wuta ce mai kuna.

Tambayoyin da ake yawan yi

Mece ce ma’anar sunan Suratul Ƙari’a?

Ma’anar Ƙari’a ita ce “Masifa”.

Suratul Ƙari’a tana cikin juz’i na nawa?

Suratul Ƙari’a tana cikin juz’i na 30.

Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Ƙari’a?

Suratul Ƙari’a tana da ayoyi 11.

Suratul Ƙari’a Makkiya ce ko Madaniya?

Suratul Ƙari’a sura ce Makkiya.

Suratul Ƙari’a ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?

Ita ce sura ta 101 a cikin Alƙur’ani.

Majiyoyi

  • Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
  • Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
  • Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
  • Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
  • Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
  • Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.

Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.

Saitunan karatu

Rubutun Alƙur’ani
Girman Larabci
100%
Girman fassara
100%
Kamanni

Ƙara zuwa Allon Gida

ReadSurahBuɗe ReadSurah daga allon gida, a cikakken allo. Surorin da kuka karanta suna buɗewa ko da babu intanet.

  1. A cikin Safari, taɓa maɓallin “Share”. A sababbin iPhone yana cikin menu na •••.
  2. Taɓa “Add to Home Screen”. Gungura ƙasa idan ba ku gan shi ba.
  3. Taɓa “Add”.