Suratul Fil (الفيل) ita ce sura ta 105 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 5. Ma’anar sunanta ita ce “Giwa”. Sura ce Makkiya, wadda ta sauka a Makka kafin Hijira, kuma tana cikin juz’i na 30.
A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Fil gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.
Suratul Fil cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ
-
أَلَمْ تَرَ كَيْفَ فَعَلَ رَبُّكَ بِأَصْحَـٰبِ ٱلْفِيلِ١
Alam tara kayfa faʿala rabbuka biashabi alfeeli
Ashe, ba ka ga yadda Ubangijin ka Ya aikata ga mutanen giwa1 ba?
Bayanai
[1] An yi Yãƙin Gĩwa shekarar haihuwar Annabi tsakãnin halaka su da haihuwarsa kwãna hamsin. Bayan shekara arba'in Annabi ya fara karantar da mutane. Ya karantar da su cikin shekara ashirin da uku, sa'an nan ya ƙaura. Bayansa da shekara hamsin waanda suka bi shi suka cinye duniya. Wannan yana nuna cewa mutane ba su samun daraja sai da riƙon addini da ilimi. -
أَلَمْ يَجْعَلْ كَيْدَهُمْ فِى تَضْلِيلٍ٢
Alam yajʿal kaydahum fee tadleelin
Ashe, bai sanya kaidin su a cikin ɓata ba?
-
وَأَرْسَلَ عَلَيْهِمْ طَيْرًا أَبَابِيلَ٣
Waarsala ʿalayhim tayran ababeela
Kuma Ya sako, a kansu, wasu tsuntsãye, jama'a-jama'a.
-
تَرْمِيهِم بِحِجَارَةٍ مِّن سِجِّيلٍ٤
Tarmeehim bihijaratin min sijjeelin
Suna jifar su da wasu duwatsu na yumɓun wuta.
-
فَجَعَلَهُمْ كَعَصْفٍ مَّأْكُولٍۭ٥
Fajaʿalahum kaʿasfin makoolin
Sa'an nan Ya sanya su kamar karmami wanda aka cinye?
Tambayoyin da ake yawan yi
Mece ce ma’anar sunan Suratul Fil?
Ma’anar Fil ita ce “Giwa”.
Suratul Fil tana cikin juz’i na nawa?
Suratul Fil tana cikin juz’i na 30.
Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Fil?
Suratul Fil tana da ayoyi 5.
Suratul Fil Makkiya ce ko Madaniya?
Suratul Fil sura ce Makkiya.
Suratul Fil ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?
Ita ce sura ta 105 a cikin Alƙur’ani.
Majiyoyi
- Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
- Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
- Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
- Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
- Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
- Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.
Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.