سورة الماعون

Suratul Ma’un da fassarar Hausa

Ƙananan taimako

Mushafi

Mishary Rashid AlafasySauke MP3Sauke PDF

Suratul Ma’un (الماعون) ita ce sura ta 107 a cikin Alƙur’ani, kuma tana da ayoyi 7. Ma’anar sunanta ita ce “Ƙananan taimako”. Sura ce Makkiya, wadda ta sauka a Makka kafin Hijira, kuma tana cikin juz’i na 30.

A wannan shafi, za ku iya karanta Suratul Ma’un gaba ɗaya da Larabci, tare da fassarar Hausa ta Abubakar Mahmoud Gumi aya-aya da rubutun boko, kuma ku saurari karatunta.

Suratul Ma’un cikakkiya: Larabci, fassarar Hausa da rubutun boko

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. أَرَءَيْتَ ٱلَّذِى يُكَذِّبُ بِٱلدِّينِ۝١

    Araayta allathee yukaththibu bialddeeni

    Shin, ka ga wanda ke ƙaryatãwa game da sakamako?

  2. فَذَٰلِكَ ٱلَّذِى يَدُعُّ ٱلْيَتِيمَ۝٢

    Fathalika allathee yaduʿʿu alyateema

    To, wan nan shi ne ke tunkure marãya (daga haƙƙinsa).

  3. وَلَا يَحُضُّ عَلَىٰ طَعَامِ ٱلْمِسْكِينِ۝٣

    Wala yahuddu ʿala taʿami almiskeeni

    Kuma bã ya kwaaitarwa bisa bãyar da abinci ga matalauci.

  4. فَوَيْلٌ لِّلْمُصَلِّينَ۝٤

    Fawaylun lilmusalleena

    To, bone yã tabbata ga masallata.

  5. ٱلَّذِينَ هُمْ عَن صَلَاتِهِمْ سَاهُونَ۝٥

    Allatheena hum ʿan salatihim sahoona

    Waɗan da suke masu shagala daga sallar su.

  6. ٱلَّذِينَ هُمْ يُرَآءُونَ۝٦

    Allatheena hum yuraoona

    Waɗan da suke yin riya (ga ayyukansu)

  7. وَيَمْنَعُونَ ٱلْمَاعُونَ۝٧

    Wayamnaʿoona almaʿoona

    Kuma suna hana taimako.

Tambayoyin da ake yawan yi

Mece ce ma’anar sunan Suratul Ma’un?

Ma’anar Ma’un ita ce “Ƙananan taimako”.

Suratul Ma’un tana cikin juz’i na nawa?

Suratul Ma’un tana cikin juz’i na 30.

Ayoyi nawa ne a cikin Suratul Ma’un?

Suratul Ma’un tana da ayoyi 7.

Suratul Ma’un Makkiya ce ko Madaniya?

Suratul Ma’un sura ce Makkiya.

Suratul Ma’un ita ce sura ta nawa a cikin Alƙur’ani?

Ita ce sura ta 107 a cikin Alƙur’ani.

Majiyoyi

  • Arabic text: Tanzil Quran Text (Uthmani) (Tanzil Project, CC BY 3.0), reproduced without changes.
  • Translation: Abubakar Mahmoud Gumi, from QuranEnc.com, version 1.2.2, reproduced without changes.
  • Transliteration: Tanzil.net English transliteration.
  • Recitation: Mishary Rashid Alafasy, via QuranicAudio.com and EveryAyah.com.
  • Word by word: recordings and meanings from Quran.com (Quran Foundation), played when you tap a word.
  • Madinah and IndoPak fonts (Settings): the text in those scripts and their fonts come from the Quran Foundation (Quran.com); the Madinah font is the King Fahd Glorious Quran Printing Complex's Uthmanic Hafs font.

Found a mistake? Report a mistake and we will check it against the source.

Saitunan karatu

Rubutun Alƙur’ani
Girman Larabci
100%
Girman fassara
100%
Kamanni

Ƙara zuwa Allon Gida

ReadSurahBuɗe ReadSurah daga allon gida, a cikakken allo. Surorin da kuka karanta suna buɗewa ko da babu intanet.

  1. A cikin Safari, taɓa maɓallin “Share”. A sababbin iPhone yana cikin menu na •••.
  2. Taɓa “Add to Home Screen”. Gungura ƙasa idan ba ku gan shi ba.
  3. Taɓa “Add”.